Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Waiku Dan allah me yarinyar nan take tsare muku ne dabakwason kuga ta huta"

"Amma dai umma ai zaki tsaya kiji metayimin da har nabiyora ko"

"Mezanji mamman yau nafara sanin iron tsanar dakukayiwa yaeinyar nan ne aiba yau ne farauba , Dan haka bawani abinda zan tsaya saurara,"

Gaba daya falon muryarsu kawai kakeji ,
Hankalin sauran gaba daya yayi kan zayyad ganin abinda yafaru dakuma jiran matakin dazai dauka,
Wasu acikinsu nayiwa khadija addu'ar allah yakubutar da ita yayinda irinsu baba karami suke murnar abinda yafaru,
Kasancewar yau ta tabowa kanta.

Afusace Dr zayyad yamike batareda umma ta luraba yafisgo khadija gamida daga hannunsa zai zundumamata mari,

Khadija kuwa ganin Dr zayyad zai mareta yasa atsorace tafada ajikinsa gamida cukuy kyeshi gaba daya tahada jikinta danashi ta kadaddabeshi sosai,

Tuni wani mahaukacin shocking yaziyarci Dr zayyad Wanda yasaka ajikinsa gaba daya mutuwa,
Gaba daya khadija tasaka Dr zayyad rasa zafin zuciyar dayamike dashi,

Banbareta yafara kokarinyi daga ajikinsa amma ina,
Ita kara kokarin manna masa gaba daya nonuwanta takeyi akirjinsa,
Jin tudun nonuwanta akirjinsa sosai bakaramin tada masa hankali yayiba,

Tuni bananarsa tafara Neman malasa,

Dr zayyad ganin yarinyar nan nema take tasakashi cikin wani hali batareda tasaniba yasashi banbareta da karfi daga ajikinsa tareda yin wurgi da ita gefe guda,

Fuuuuuuuuuuu yayi waje abinda tareda nufar dakinsa,


Abangaren fareeda kuwa suna zaune adaki itada kawarta maryam wacce suke kira da merry,

Kasancewar mahaifin fareeda yarasu itakuma mahaifiyarta batada wata kula saboda itama ba tarbiyyar gareta ba,
Itadai kawai abinda tasani shine fareeda takawo musu kudi yasa bata damu da koma me fareeda takeyiba,

Zaune suke sun saka wasu hotuna agabansu,
Merry ce take ta sababi akan cewa,

"In wllhy kawata kin bani mamaki ban taba tunanin cewar wait zaki iya zaucewa haka akan namiji ba wllhy,"

"Uhm merry kenan bazaki gaba ganewaba,kinsman cewa zayyad makura ne ahaduwa sannan ke kanki kinsha jin cewar iron zayyad ne namijin da nake bukatar aure arayuwata,
Merry INA me tabbatar miki dacewa zan iya yin komai gameda zayyad koda kuwa kisane "

Merry tadafa kafadar fareeda tareda cewa ,


"Hmmm kawata kenan abinma bai kai nakisaba,
Muda Mike da makami ahannun mu,
Ao shiyasa nace miki ki yaudari zayyad ta hanyar daukar hotonku kedashi alokacin da kuke tsaka da harka,

To kisani matukar kawai wannan hoton dolene zayyad ya yarda ya aure ki ko musallama har gida mu mikawa mahaifinsa"

"That's good kawata shiyasa wllhy nake sonki saboda kinada basira wllhy,"

"Haba kawata karki taba damuwa da hakan meye taren in har zakiso wani Abu in masa taimakamiki akai ,
Kedai kawai kisha kuruminki, Dr zayyad kuwa kamar kin aureshi kingama kawata"

Ahaka suka cigaba da hirar tasu duk dai akan Dr zayyad
Daga karshe Sai karfe Tara suka shirya suka tafi yawon kwana,



To abangaren Dr zayyad kuwa yau abinna khadija baimasa tasiri kamar jiyaba kasancewar jiya yasamu yadan rage zafi sosai,


Wsnka yayi tareda alwalla yafito da Sauri2 yawuce masallaci kasancewar anata kiraye2 sallar magarib,

A can ya iske yan uwansa saida akayi sallar issha tukunna suka fito daga masallacin,

Tafe suke suna Dan taba hira tsakaninsa da baba Isuhu akan yanayin rayuwa dakuma yanayin aiki har suka shiga part din ammi,

To afalo suka iske ammi da ummy,
Ammi CE zaune akan kujera 2seater ummy nakwance ta daura kanta visa cinyar ammin suna taba hira,

Jin shigowarsu Abba tareda yaya zayyad yasa ummy mikewa zaune tare da cewa,

"Abba sannu da shigowwa,yaya zayyyad barka da dare"

"Yawwa"
shine kawai abinda Dr zayyad yafada ganin cewar kamar yaran sun fara rainashi tare da kara tamke fuskarsa tunawa da abinda yafaru tsakaninsa da waccan yarinyar,tsaki yaja Wanda baimasan yafitoba saida Abba yace,
"Zayyad lafiya dai ko?

Yaso daburcewa amma kasancewarsa jarumi yasa ya wayance tare da cewa ,

" bakomai Abba kawai dai natuna wani abune"

"OK badamuwa amma in antuna wani Abu addu,a yakamata ayi bawai tsaki ba"

Sosa kai yayi tare da cewa ,
"Ayi hakuri Abba insha allahu za'a gyara"

Ammi CE tadawo daukeda kayan abinci acikin kwando kasancewar Abba ba'a nan take con abinciba,

Mikewa Abba yayi tare da cewa ,
"Am zayyad dauki abincinnan mutafi part din hajiya,

Gsky da'ace ason ran Dr zayyad ne to bazai ta zuwa bangaren hajiyar yanzuba saboda shifa baya son haduwa da wannan Mayyar yarinyar Dan komai ma zai iya faruwa..........YAR MUTAN MURAYECE9

Sabin bashida yacce zaiyine yasa yamike cikin mutuwar jiki yadauki basket din suka yi gaba,
Har sunkai baking kofa ammi takira sunanshi,

"Zayyad"
"Na'am ammi" yajuyo tare da amsawa,

"Amma inka kaimasa abincin zaka dawo nan kaci naka ko?"

Abba be yayi saurin karbe zancen da cewa,

"A'a wanna abinci zai dawo ci bayan ga abinci anan ai duk zai isa aci"

Badan son ran Dr zayyad ba amma haka suka dunguma zuwa part din hajiyar,

Tafiya suke Abba nayimasa hira amma zayyad acikin ransa ayyanawa kawai yake wllhy idan har sukaje yarinyar nan takawo masa raini saiya ci ubanta koda kuwa hajjaju zata ji haushinsa,


Abangaren hajiyar kuwa ana idar da sallar issha baba Ummaru yayi part din,Inda yasamu hajiyar da sauran yaran mata tare da aunty maimuna gaba dayansu azaune sunata hira da raga gwanin dadi,kasancewar aunty maimuna Mayan gidan duk sun girmeta yasa a irin wannan lokacin sukan hadu a part din hajiyar itada yammatan gidan suyita sharholiyarsu,

Al'hussain yana jikin aunty zainab amma ganin baffan kamar yadda yake fada yasa aguje yasauka daga jikin aunty zainab din tare da fadawa jikin baba ummaru,

Rungumesa yakarayi tare da zaunawa akan kujerar da khadija ta tashi tabashi,

Khadijar CE tadawo jikin kafafunsa daga kasa tazauna tareda rungume kafar tasa da hannuwanta biyu,

Aunty zainab CE tadubeta cikin raha tace,
Gsky khadija kincika mage,yanzu kiduba daga zaman Abba har kinsamu naraba,

Dukansu dakin dariya sukayi,yayinda fateema tafakaici ido tayimata gwalo😜,

"Shagwabe fuska da murya yayi tareda cewa hajiya kindaiga Fatee ko?,

"Aifa sun fara tsokanarki kenan,nidai wllhy khadija da inada Inda zan maidaki Dana kaiki"

"A'a hajiya kekuwa kikeda gurin kaita,kyace bakida gurin kaita kuwa?" Cewar yaya munir dayake shigowwa yanzu,


Kafin kace me gabaki daya falon yacika sai hira akeyi anata raha,


Sallamar baba Isuhu da Dr zayyad CE tasa falon yin tsit,kasancewar Dama anacewa Dr zayyad din yadebo zafin zafin baba Isuhu ne, sai dai shi baba Isuhu bakowanne lokaci yake kasancewar baya wasa ba,sabanin Dr zayyad dabaya son wasa da kannensa ko kadan,

Guri yaya al'amin da yaya aliyu ne suka basu kujera suka zauna,
Dr zayyad ne yafar gaisar da iyayenshi suka amsa cikin aakewa,
Saida yasakko wayarsa yafara dannawa kafin yace
"Hajiya barka da wuni", kansa yana jikin screen din wayarsa batareda yadago yakalletaba,

Batareda yadamu da yanayin dazata amsaba yacigaba da latsa wayarsa,

Baba Isuhu ne yayiwa yan'uwansa musaba yagaida hajiya tareda amsa gaisuwar da yarannasu keyimasa,

Dr zayyad kuwa cigaba yayi da danna wayarsa batareda yasake koda kallon wani daga cikin yan dakin ba,
Danshifa har ga allah zamannan dayakeyi takuramasa akayi Shifa bayamaso yadago idonsa Dan kar yayi gamo da wannan jarababbiyar yarinyar,


Sosai wal walar yaran gurin taragu kasancewar dodon gidan naxaune kamar yadda hajiya take cewa wani lokacin,

" gsky zaidu kana tareda wahala muddin haka kace zakayi taka rayuwar,yo INA mafani ace kai kazama dodo acikin yan uwanka,"taci gaba da cewa,

"Yanzu Dan allah zaidu ji nan gurin gaba dayansu kacire iyayenka kowwa jikinsa yayi sanyi saboda kai,zaidu INA dalili kazama kamar mala'ika agida?"

Idan ka kalli zayyad zaka rantse da allah badashi takeba kokuma karantse baisan metake yibama,

Kara zamewa yayi tareda manna jikinsa da kujera yacigaba da abinda yakeyi wato danna waya,
Kasancewar kujerarsa na kallon kujerar baba Ummaru ne sai ta baba Isuhu agefenasa,

Yasa duk hara rar da khadijar ke antaya masa idonsa nakanta batareda tasaniba,

Saboda ita duk agunaninta hankalinsa nakan wayarsa,

Wani lokacin yakanga tayi Mimi da baki amma baya fahimtar metake fada,

Yanadaida tabbacin ba alkhairi take fada game dashi dinba,
Wata zuciyarce take cemasa kilama zaginka take,
Yayinda wata zuciyar tayivsaurin kawar masa da zancen tareda cemasa,kai baba koda Giwa tafadi ai tafi karfin dauka aka,

Amma wannan yarinyar munafukace yacigaba da ayyanawa zauciyarsa,

Yanzu inda zance ga abinda tayimin itakuma wannan tamishasshiyar tsohuwar ko girmana bazata ganiba zata karyatani agaban yara,

Wani malalacin murmushi yayi tareda ayyanawa aransa,yarinya inta biyo saikin raina kanki da kanki,

Murmushin yasakeyi tareda kara zamewa cikin nishadi danshi aganinsa wannan tamkar wani wasane dazai farashi da nasara,

Abba Ummaru ne yakatsewa kowwa NASA tunanin tahanyar cewa aunty zainab tafara zuba abinci,

Tashi zaune tayi tareda kallon khadija tace,
Khadija taso muje kitchen,

Badan khadija tasoba suka nufi kitchen din ,

Duk kwakwarka bazaka taba cewa Dr zayyad khadija yake kallo ba,

Saboda yadda zakaga idanunsa akan waya,
Amma azahiri gaba daya idanunsa da hankalinsa suna kan kugun khadijar,

Wadda ayanayin yadda take tafiya zaka iya rantsuwa da allah da gayya take juyasu,

Bgabaki daya zayyad yazuba idanunsa da nutsuwarsa akan kugunna khadija tareda kamo lebensa na kasa yana dan ciccizawa ahankali,

Saida suka shiga kitchen kafin Dr zayyad tayi wata boyayyar ajiyar zuciya tareda tambayar kansa wai meyasa baya iya hana kansa kallon waccan abar,
Shedaniyar zuciyar tasa ce takecemasa aiba iya kake kallo ba jikintane yake tafiya dakai,

Tabe Baki yayi tareda ayyanawa aransa koma dai meye shifa yarinyar batayimasaba saboda bayan izza ma tahada da munafurci,

Ahankali yakara juaya idanunsa batareda yadauke kansa daga jikin wayarba yazura idanunnasa akan kirjinta dayake cike da dukiyar Fulani,

Doguwar rigace ajikinta mai duwatsu tadanyana mayafin akanta yarifo har kirjinta amma duk da haka bai hana tudun nonuwanta bayyanaba,

Plate din hannunta taduka zata ajiye gaban yaya munir,
Kasancewar rigarta ta robace yasa dataje dukawar rigar tadan bude kirjinta yadan bayyana Wanda zayyad dinne da idonsa yake kai kadai yakula,

Wata mahaukaciyar tsawa yabugamata wadda duk rashin tsoro irinna khadija saidata firgita tafada jikin munir din,

Baisan kome yasaba fadawar tata jikin munir tasa yaji kamar an buga masa wani mugun large azuciyarsa,

Wanda sanadin hakan saida yayi saurin dafe saitin zuciyarsa,

Afusace yamike gamida fizgota daga jikin munir din tareda dalla mata wani mahaukacin mari gamida kama kunnenta da karfi yarike,
Wanda saidata saki wata mahaukaciyar kara,

Gaba daya iyayennasa bawanda yayi kokarin tashi kasancewar basu fiya son abinda zasuyiwa babba fada agaban karami ba,

Hajjaju ce ta mike ahanzarce tareda kama hannun zayyad ta fisgoshi da karfi,

Ko motsi baiyiba kasancewarsa kakkarfa gabaki daya jiyjiyoyin kansa sunyi wani irin tashi idanunsa sunyi ja duka fuskarta yayi wani irin ja,

Su Kansu tunda suke basu taba ganin zayyad din cikin irin wannan Bacin ranba koda kasancewar baya wasa amma baitaba shiga cikin wannan yanayinba,

"Zaidu aiba khadija zaka dakaba nizaka daka,saboda kawai nayimaka fada akan yan uwanka shine zaka kama karamar yarinya har kanayimata wannan dukan,"

"Zaidu bafa tun yau na fahimci cewar bakason hadizaba wllhy,
Amma duk yarannan ace karasa wadda zaka yiwa sai wannan abar?"
Hajiya tafada tana kumfar baki,

Ko kallonta baiyiba yawulla khadijar can gefe guda tareda Nuna ta da yatsa yace,

"Wllhy wllhy duk ranar da nakuma ganin kin mikawa wani Abu koma meye kafin ki mikomin zaki raina kanki,
Danna kin rainamin hankali saikin fara mikawa munir Abu kafin ki mikomin,"

Yafada yana nuna kansa tareda Jan tsaki yawuce yana fadar useless kawai,

Afusace yafita tareda yin part din ammi,

Ko ayanyin dayashigo ammi tasan antabo mata dannata hakan yasa koda yakwanta akan kujerar batcemasa uffan ba hasalima chating tacigaba dayi saboda tasan halin dannata,

Gabadayama kwakwalwarsa ta kulle shin wait wanne irin tunani zaiyi?,

Tomema yasakasa dukan yarinyar can?

Wani meyasa yaji wani yanayi Dan kawai yayi tunanin ko munir zai iya ganin bres dinta?,

Shu'umar zuciyar tasa ce tafada sakamasa cewar to danme bazakayi kishin kanwarkaba ai kanwarkace sannan kuma tarbiyya ce Dan kayi hakan,

Amma meyasa baka fadi dalilin dayasa nayi hakanba,

Toma kokafada waccan rubabbiyar tsohuwar aisaita San metayi ta doramaka laifi,

Mtssssasss yana wani mahaukacin tsaki,

WA"IZA ASABATUM MUSIBATUN K'ALU INNALILLAHI WA,INNA ILAIHIRAJI'UN,

shine kawai abinda ammi tacemasa tacigaba da chating dinta,
INNALILLAHIN yayita maimaitawa aransa har yafarajin saukin abinda yakeji,

Ahankali yafara sauke ajiyar zuciya kafin daga bisani yafarajin zuciyarsa tafara saukaka masa,


Abangaren hajjaju kuwa kasancewar babu Wanda yasan asalin abinda yafaru koda kuwa iya khadijan sai aka bar abin da cewa zayyad yayi hakan ne saboda tafara bawa munir abincin dakuma zafin fadan da hajiya tayimasa Wanda ayanayin dabi'arsa tason manyance dakuma kasancewarsa babba acikin yaran dama baidace tayimasa fada agaban kannensaba,


To hakadai akaci abincin daga bisani kuma aka fara bankwana kasancewar large Tara da Rani tayi,


Tuni khadija da zafin jifar da zayyad yayi da ita yasata lomawa jikin baba ummaru talafe tayi bacci saboda wahala Dan gsky tamaru,10


jin zuciyarsa tadan fara sanyi yasa yamike tsaye tareda yin hanyar fita,

Aciki ciki yace,
"Ammi sai da safe"

Kallonsa tayi tareda danyin murmushi tace zayyad,

Juyowa yayi yakalleta ganin hankalinta nakan waya yasan dawowa take so yayi,

Dawowa yayi yazauna inda yatashi ita kuma tamike tayi dining

Dauke da plate da Kofi ahannunta tadawo tazauna kusadashi tareda ajiye plate din akan cinyarta,

Ahankali ta ebo abincin tanufi bakinsa,

Kamar karamin yaro yabude bakinsa tafara bashi abincin,

Gabaki dayansu bawanda yayi magana,
Falon shiru,sai motsin cokalin da ammi take bashi abinci kawai,


Mama babba ce tashigo watau hajiya safiya matar baba safiyanu mahaifiyarsu aminatu,

Dasallama tashigo falon,turus taja ta tsaya ganin ammi na bawa yaya zayyad abinci abakinsa,

Wani kululun bakin cikine yatasomata amma kasancewar tasan halin mutant gdn yasa tadan danne abinda takeji,

Aranta kuwa cewa take lallai kincika makira duk tsanar dayayiwa yarki amma kamar abin baya damunki,

Dan tabe Baki tayi Wanda tayi daidai da dagowwar Dr zayyad,

Aikuwa akan idonsa,
Dasuri ta wayance tareda samun baking kujera tazauna,

Ammi ce takalleta da fara'a akan fuskarta tace,

"Sannu da zuwa maman yara kece dakanki kuma adarennan,"

Mama babba tadanji zafin maganar amma ta wayance da cewa,

"Ammm dama khadija nazo nema naga ya jikinnata kasancewar naji abbansu yace zayyad yadaketa"

Dasauri zayyad yadago kansa tareda doramata mayun idanunsa akanta,

Dauke nata idanin tayi kamar bata ganshiba tacigaba dacewa,

"Nifa abinnan yana bani mamaki ganin irin tsanar da zayyad yayiwa khadija agaskiya yakamata adauki wani mataki Dan gudun abinda zaije yazo"

Tunda tafara maganarta ammi take hai'lala azuciyarta Dan gudun tasirin shedan dakuma shedanci irinna hajiya safiya,

Batun yau ba hajiya safiya kan zowa ammi da wannan batun amma ta kan share bata taba kulawa ba kuma har kawo yau hajiya safiyar bata taba nuna gazawarta kojin zafin rashin daukar mugayen shawar warin datake kawomataba,

Sannan kuma koda wasa ammin bata taba tunkarar wani da wannan batun ba,

"Nifa ganinake kamar bakwason khadija.....

"Dakata maman yara"

Ammi takatseta tareda cigaba da cewa,

"Meye rashin so anan aganina zayyad ai ubane ba yaya ba Dan haka yanada cikakkiyar damar datafi ta yaya agurin gabaki daya yaran gidannan bama khadija kadai ba"

Sannan kuma wllhy ban taba ganin tsanar khadija a idon zayyad ba hasali ma ni nafi kowa ganin soyayyar khadija a acikin idanun zayyad "

Arazane gabaki dayansu suka kalli ammi saboda jin kalaman da suka fito daga bakinta,

Gabaki dayansu kowa da abinda yake sakawa acikin zuciyarsa tsakanin mama babba da Dr zayyad,

Ammi ce tacigaba da maganarta,

"Ai ni a nawa tunanin bakada Wanda yake son ka sama da Wanda zaice ka gyara halayenka kinga kuwa zayyad bai taba tsanar khadija Dan komai ba saidan wasu daga cikin halayenta da koni dana haifeta basuminba"

Wata boyayyar ajiyar zuciya zayyad yasauke jin kalaman ammi na yanzu,

Sosai har yanzu hajiya safiya take arude dajin kalaman ammi na cewar zayyad masoyin khadija ne, kayyyy INA bazai taba yiwuwa ba wllhy duk yadda zatayi saitayi ganin hakan bata kasanceba,


Jin shirun yayi yawa yasa ammi cewa ,

"Kiyi hakuri maman yara idan maganata ta bata miki rai"

Cikin dakiya da kokarin boye sirrin zuciyarta tadan kakaro murmushi tayi tareda cewa,

"Bakomai amminsu Nima yanzu nafuskance dama rashin fahimtane"

Juyawa tayi tareda kallon zayyad tace,

"Zayyad kayi hakuri rashin fahimtane yajawo hakan"

Ko kallon ta baiyiba saida ammi tadan mutsilesa kafin yace mata
"Bakomai yawuce", adakile,

"Sallama tayi musu tareda yin hangar part dinta tana sake saken abubuwa iri2,


Zayyad ma ammi bata bashi wata damar magana ba yakuwa ji dadin hakan kasancewar bashida abinda zai fada din,

Koda yagama cin abincin har baking falo tarakoshi tareda yimasa addu'a tayi part dinta abinshi,

Tunda ammi ta kwanta bacci bai dauketaba shin me hajiya safiya take nufi da hakan,
Batun yau ba takaranci hajiya safiya sosai,mace ce datafiya son kanta kuma bazata tabayin Abu batareda tanada manufaba,

Ko maganar dazu da'akwai manufarta tayinta bawai tayine Dan khadijar ba,

Haka dai tayita tunani batareda abban yasan metake cikiba saboda ita macece dabata fiya son saka mutane a harkar taba musamnan wannan lamarin dayake bukatar addu'a dakuma bincike,

Tashi tayi tayo alwalla tafara jero WA allah ibada tareda kirari akan bukatunta,


To abangaren zayyad ma haka abin yakasance sai dai shi sabanin ammi tunaninsa yatafine akan maganar da ammin tayi nacewa soyayyar khadija ce tasakashi yin hakan,

Yakan tambayi kansa meyasa ammi take fadar hakan kodai tanason Sabin rayuwarsane kokuma tana bit Bihar rayuwarsane,

"Zayyad yakamata kagaskata zuciyarka Sannan kuma kadaina boyewa kanka abinda kasani da kank"

Cewar wani bangare na zuciyarsa,


Saurin watsadda maganar yayi tareda rumtse idanuwansa da karfi,

Baidamu da abinda hajiya safiya tayiba domin yasaba da wannan kuma yana daukarsa amatsayin rashin kauna,

Ahaka bacci yayi awon taba dashi,


Abangaren mama babba kuwa afusace tashiga part dinsu ganin mama karama tareda sauran yaran gidan yasa ta wayance daga baya kuma tayi daki,

Ko minti biyu batayi da shigaba fateema tabiyota,

Safa da marwa kawai takeyi shigowwa fateeman ne yasa tayi saurin rarumar hannunta suka zauna abakin gado,

"Mama meyafaru ne?"

"Hmmm fateema kenan ai infadamiki tsinanniyar matar can kinga kuwa yadda take bawa zayyad abinci abaki kamar wani karamin yaro"

"Hmmm aini abinma daure min kai yayi, nan mama ta labarta mata abinda yafaru"

Cikin yanayin damuwa da zubar da hawaye fateema take fadamata cewa,

"Mama dama ai nafadamiki cewar naji umma tana cewa ita da abinda zai yiwuma aida yar gida za'ayi da ya zayyad da khadija"


"Amma ai run awancan lokacin kincemin babanku Ummaru yace tabar maganar ma kar wani yaji ko?"

"Eh hakan yace wai bazai taba yiwuwaba"

"To ki kwantar da hankalinki fateema nayi mini alkwarin saikin mallaki zayyad ahannunki"

Murmushine yasubucewa fateema tareda cewa,
"Allah shi yadda mamanah"

"Amn yar kirki yanzu kije ki wanke fuskarki ,Sannan kuma kamar yadda nafadamiki karki yadda ko yar uwarki Amina tasan kinason zayyad"

"Insha allahu mama babu Wanda zai SANI"


Washe gari da safe kuwa yakasance ranar alhamis zayyad ya tashi da shirinsa na zuwa gurin aiki,

Bangaren su umma yafara shiga atsakar gidan ya isketa tana aikace aikacen gida kasancewar zainab tayi safiyar tafiya school,
Dasallama yashigo tareda gaisheda umman tasa,

Ko kallonsa batayiba Yakima maimaita gaisuwar tasa nan ma ba amsa ,
Daya daga bakinsa zai sake maimaitawa tsam yaga tabar gurin tashige falo,

Ko ba'a fara masaba tasan tabbas ta tsuniyar gizo bata wuce ta koki,

Kada kansa kawai yayi tareda sauke nannauyar ajiyar zuciya,

Aransa yaketa sake saken wai yanzu ita wannan yarinyar badama wani ya ta bata sai su kama sababi saboda antabo yar gwal,

Tabe bakinsa yayi tareda yin sallama afalon bakowwa,hakan yasa yanufi bedroom din umman tareda yin sallama,

Aciki ciki ta amsa yashiga tareda dukawa agabnta ya sunkuyar da kansa kasa tareda fara cewa,

"Umma Dan allah kiyi hakuri"

"Ashe kama San kayi laipi kenan,Dan zayyad wai meyake damunkane?"

"Ai ni ban taba sanin bakada kunya ba,shin zayyad wai bakajin kunyar ammi ne?"

"Zayyad koni Dana haifeka bana dawainiyar da ammi takeyi akanka,yanzu haka inka bincika bataci abinciba saboda bakajeba"

"Zayyad ina guje maka hakkin wannan baiwar allah,ace bakada abin tsana aduniya sai jinin matar da tafi kowwa kainarka,"

"Ni bance maka idan khadija tayi laifi karka hukun ta taba kayimata kamar yadda kake yiwa kowwa,amma meyasa ita zaka dinga yimata abubuwa har asamu wasu su rings ganin tsanar dakakeyimata tafara yawa"


Ko ba'a fada masa ba yasan yarinyar nan itace Munafukar data fadawa ummansa abinda yafaru,amma wllhy zai canza salo akan ta munafuka kawai,

"Shi kenan umma kiyi hakuri insha allahu hakan bazai sake daruwaba"

"Da dai ka kyautatawa kanka zayyad nidai nafadamaka gsky"

"Insha allahu"

"To allah yatsare"

"Amn" yafada gamida mikewa yayi waje abinsa,

Yana ganin bangaren baba safiyanu yadauke kansa kasancewar abinda mama tayimasa jiya,

Aguguje yashiga part din baba Iro abakin kofar falo ya iskesu aunty maimuna tarako amininin NASA kuma uba agareshi zai tafi gurin aiki,
Kasancewar baba Iro bawai yagirmi yaya zayyad sosai bane,

"Gsky auntynmu kin rike wuta,watam har yanzu oga bai tafi kasuwarba ko?"

"Cikin raha baba Iro yace,

" gwauro ma bai tafi gurin aiki ba bare kuma mai iyali"

Haka dai suka Dan taba raha tareda gaisawa suka fito,

Adaidai part din ammi suka rabu inda baba Iro yawuce zai hau abin hawansa yatafi,

Dr zayyad kuwa bangaren ammi yashiga,

Akan dining ya isketa tazuba abinci ta ijiye agabanta tanata juya cokalin,

Bata ma San zayyad yashigoba kasancewar ammi akwai saka Abu arai Dan run jiya take wannan tunanin gaba daya ma Rabin kanta ciwo yakeyimata sosai ma kuwa,

Cokalin yazare daga hannunta hakan yasatayi firgigit gamida sakin wata boyayyar ajiyar zuciya,
Murmushi ta kakalo tayimasa tareda cewa,

"Gsky zayyad bakada dama to Dana tsorata da na zura da gufu fa"

"Hmmm ammi kenan ainasan ammita jarumace shiyasa Nana wani dar akanki"

Zayyad yafada lokacin da take zama akan dining daukeda murmushi afuskarsa yana kokarin kwantarwa da ammi hankali kasancewar yahango damuwa karara akan idanunta,

Amma dayake ammi macece mai kokari yasa bats bukatar wani yasan halin da take ciki musamman ma zayyad din,

Doya da kwai taxuba masa a plate tareda zuba NASA hadadden kunun gyadar dayaji madara acikin Kofi ta turamasa gabansa,

Ahankali yafara kai hannunsa yadauki doyar tareda kaiwa bakinsa ya gutsura,
Lumshe idonsa yayi tareda bude su ahankali aranshi yake ayyana baiwar tsafta dakuma iya girki irinna ammi,

Kara dauka yayi yakaiwa ammin bakinta,

"Zayyad kaci abincinka karka makara lokacin aiki banaso kazamto daya saga cikin masu cin haram,"

"Zayyad karka manta cewar koda da minti daya ka makara agurin aiki da gangan sannan kuma kacimusu kudin albashi complete to kaci haram"

"Hakan yasa kaga kullum nake karfafa maka gwiwa akan karinga tafiya aiki da wuri hakanne zai bamu kwarin gwiwar ragargazar albaahinmu cikin kwanciyar hankali kasancewar halal din danane" ammi tafada tana murmushi,

"To shikenan ammi zan tafi amma sai kinyimin alkawarin zakici abinci ki koshi"

"Zanci zayyad dina amma kaimafa saikayi min alkawarin zakaje kagaisheda hajiya"

Badan ran zayyad yaso ba ya amsawa ammi saidan yakara kwantar mata da hankali,

Ya amsamata da confidence tareda daukar brief case dinshi dakuma mukullin motarshi ammi tayomasa rakiya kamar yadda tasaba

Please Login or Register in order to submit comment