Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dazata kaiwa dr zayyad ɗin,
Jin sallamar hajiya yasata ajiyewa tayo falon tana amsa sallamar hajiyar,
kamar yadda tayi tunani haka tasamu watakam ganin hajiya da khadija,
Hakan yasakata ɗan haɗe fuska ko kallon khadijar batayiba tacewa hajiya,
"hajiya akwai abinda kike buƙata ne"
Ɗan murmushi hajiya tayi tareda cewa,
"hmmm babu abinda nake buƙata uwar zaidu afuwa dai mukazo nema"
Yanayin yadda hajajjun tayi magana neyaɗan saka ammi sakin fuskarta tareda ɗan sunkuyar da kanta ƙasa kafin ta fara magana,
"amma hajiya sai nake ganin kamar ƙyale khadija da akeyi ba'a hukuntata shine yakesakata aikata duk abubuwan datake wani lokacin"
"Nasani amma dai to dan allah a taimaka daga wannan insha allahu bazata sake ba"
"Hmmmm hajiya kenan kullum ace daga wannan,yanzu girman laipin da khadija tayi baici ace kin ƙyaleta an hukuntataba,wllhy da ace zayyad ya mutu to da khadija nada haƙƙi rai akanta,wai wannan wacce orin tsanace yarinyar nan take nunawa bawan allah nan ne,haba hajiya ace babu wanda zaka nunawa tsana sai ɗan uwanka,wllhy basau ɗaya ba bakuma sau biyu ba gata nan a gabanta nasha nuna mata irin abinda takeyi bashida amfani amma har yau ta gagara fahimta"
sosai jikin hajiya yayi sanyi da maganganun ammi sai dai kuma duk da haka tana kan bakanta na bawa ammin haƙuri hakan yasa itama tacigaba da cewa,
"Nasan da haka kuma nasan duk abinda kike faɗa akan gaskiyane sai dai fa kisani nunawa hadiza ɓacin rai bashi zaisa zucoyarta sauyawa ba,"
Sai da ta ɗan ƙara tsahirtawa kafin ta dubi khadija tace,
"Hadiza wuce gurin maimuna kafin innemeki,"
Da sauri khadija ta nufi part ɗin aunty maimuna wadda itama yazuwa yanzu ummy ta sanar da ita gabaki ɗayan abinda khadijan ta aikatawa yaya zayyad ɗin,
hajiya ce ta kalli ammi da tsantsar fahimta kafin ta cigaba da magana,
"haƙiƙa naso ace nasamu gabaki ɗaya surikkaina halinku ɗaya sai dai kuma kash!
tun ba'aje ko inaba nafara samun nara gurbi da kuma tangarɗa wanda bazan taɓa lamuntar hakanba,
ALLAH yasani gabaki ɗayanku daidai kuke a guna sai dai kuma ita kyatatawa da biyayya kansa kaji wani sama da wani a ranka,
Haƙiƙa nasan ina tauyeki akan abubuwa dadama musamman akan hadiza,
Sai dai kuma inaso ki fahimta ni inaji ajikina cewar akwai wani ɓoyayyen lamari da hukunci zartacce akan hadiza da zaidu,
Dan haka kisani bawai da ƙarfi zaki iya cire ƙiyayyar zaidu daga ziciyar hadiza ba,aa zai fi kyau ki ɗauki wasu dabaru a matsayinki na uwa wanda zaki tisa wa hadiza ƙaunar zaidu ki kuma yi nasarar cire ƙiyayyarsa azuciyarta,
Muddin kikayi haka ni kika taimaka da kuma wani ɓoyayyen sirri na wasu zukata masu tarin yawa"
Tunda hajiya ta fara magana ammi take saurarenta tareda yiwa maganarta kyakkyawar fahimta dakuma ɗaurata a mizani na tunani da hankali,
Sosai ta karɓi maganar hajiya tareda yimata mazauni a gurbin tunaninta wanda hakan yasakata yiwa hajiya godiya tareda nunamata insha allahu abin yariga ya wuce,
Itama hajiya sosai taji daɗi tareda sake bawa ammi ƴan shawarwari kafin tayi mata sallama ta nufi part ɗinta,
Tunda hajiya tafita ammi ta koma ta zauna tashiga tunanin maganganun hajajju tabbas komai na babba yafi na yaro haƙiƙa ita kam tafi khadija tinani amma itama hajiya tafita tunani da hangen nesa,
Sannnan kuma muddon abinda hajiya ta faɗa tayimasa kyakkyawar fassara dakuma fahimta to tabbas a kwai ƙura dankuwa ƙuru ƙuru ta hango wutar soyayya dakuɓa ƙaunar zayyad a idanun aminatu da mahaifiyarta dake muradin da goyon bayan ƴarta,
Any way dai aminatu da khadija harma da zayyad ƴaƴantane dan haka bazata taɓa son ganin an ɓata wa kowwa ba dan haka zata dage da addu'ar Allah ya zaɓa musu mafi alkairi baki ɗayansu,
Amma dolene zata dagewa khadoja kamar yadda hajiya ta faɗa ta hanyar ƙara jawota a jiki da nuna mata illar abinda take aikatawa uwa uba zata dage mata da addu'a sanin kowace mama babba akan burin datasa a gaba,
Da wannan tunanin daia ammi ta tashi tacigaba da aikinta ganin lokacin tashin zayyad ya ƙarato,
Tunda khadija tashiga parta ɗin aunty maimuna suka ƙule a ɗaki tana nuna mata kuskuren da ta aikata da kuma illolin ƙiyayya ga ɗan uwa,
To dayake dai ance mai laya kiyayi mai zamani tuni auntu maimuna ta samu kan khadija a hankali take cusamata wasu ra'ayiyyika cikin tsabagen wayewa da hikima,
A haka dai suka ci gaba da hira har aunty maimuna ta shawo kan khadija akan zata je tabawa zayyad ɗin haƙuri akan abinda ta aikata kodan ammi ma,
Bata barta ba har sai da ta yadda suka shiga khitchen dan haɗawa marar lafiya delicious,
tun khadija na ɗari ɗari harta saki jikinta dayake aunty maimuna ma gwanace haka suka ɓata lokaci wajen yimasa farfesun kayan ciki dayaji kayan yaji da attaruhukafin akayimasa ƴan snacks da shayi mai kayan ƙamshi,
Sai da aka kusa gama kafin aunty maimuna ta cewa khadija ta wuce part ɗin hajajju ta gyara jikinta kasancewar sun shiga khitchen kafin su wuce part ɗin yaya zayyad,
Haka kuwa akayi part ɗin hajajjun ta wuce sai dai batayi mamakin ganim babu hajjaju a part ɗinba ta tabbatar tana part ɗin yaya zayyad,
Ba tareda ɓata lokaci ba ta yi wanka tareda turare jikinta kafin ta shirya jikinta cikin wata A sharp ta less bluee mai adon fulawoyon sky blue tareda taje gashinta ta ɗaureshi a can ƙasan ƙeya kafin tayimasa ɗaurin ture kaga tsiya,
Gsky khadija kyakkyawa ce ta ajin ƙarshe dan shigar ba ƙaramin karɓarta tayiba,
plate shoes ta saka baƙi tareda maƙala fashion ɗan kunne baƙi mai ɗan yalwar girma,
ba tareda ɓata lokaci ba ta fito dan a ƙofar part ɗin aunty maimunan ma ta ganta,
Tunda ta taho aunty maimuna ke ƙissiɓa abubuwa dayawa a zuciyarta akan khadijar gaskiya khadija kyakkyawace dan haka ma babu da wanda ta dace face zayyad,
Da murmushi ta tareta tareda koɗa iron kyanta kafin suka kama hanya,
Har suka isa aunty maimuna na jaddadawa lhadija akan tabawa yaya zayyad haƙurin abindatayimasa,
A falon auka sami kusan rabin gidan amma banda umma babba kasancewarta mace mai kara da kawadda kai,
Da sallama suka shiga wanda dayawa daga cikin mutanen falon sun amsa amma banda mama babba da aminatu,
Da suke aikawa khadijar dawata muguwar harara sosai kishin kyawun khadijar ke takurawa mama babba,
A hankali khadija ta gaisheda mutanen falon sai dai kuma kowa ya kula da otin amsawar da maman tayi,
Ganin batayiwa zayyad maganaba yasa ammi bamka mata wata uwar harara wadda saida ƴan hanjinta sukayi zallo,
Babu shiri wani siririn hawaye yazubomata,
Auntu maimuna gamin khadija zata ɓata musu shiri akan huɗubar sirrin datayimata yasata ɗan mintsinar khadijar,
A hankali kamar wadda ƙwai ya fashewa tamiƙe tareda komawa kusada yaya zayyad ɗin da tunda tashigo yake ƙaremata kallo ta ƙasan idanu tareda addabarsa da fitinannen ƙamshinta yayi,
Jin ta akusadashi ba ƙaramin tsinkewa zuciyarsa tayiba tareda karɓar dukan take masa wanda yake daidai da ƙariwar ciwonsa,
A hankali ta ɗauki hannunta ta ɗora akan ƙafafunsa wanda yakasance daga cikin huɗubar aunty maimuna,
Cikin airoroyar shagwaɓaɓɓiyar muryarta mai kamada anyi gudun tsere tace,
"pls kayi haƙuri yaya zayyad"
Da sauri ya rumtse idanunsa dalilin wani tsimkewa da jininsa yayi gabaki ɗaya ji yake kamar ya rumgumota saboda jin wani abu dayake addabar zuciyarsa,
A hankali hawayenta suka sauka akan ƙafarsa wanda ya kasance tamkar saukar mashi a ƙahon zuciyarsa dan kuwa jin danshin ruwa a ƙafarsa ya tabbatar masa da hawaye take,
Kenan akwai abinda tayi masa wanda baisaniba,
Koma dai menene shi kansa ransa fansa ne akan ƙannensa musamman ma ita dayake jinta har cikin ƙoƙon zuciyarsa,
A hankali ya kai hannunsa saman kanta yasake jawo kanta zuwa kan dantsen ƙafarsa yana bubbuga kannata alamun sorry batareda yayi magana ba,
ɗif!!!
Wuta ta ɗaukewa gabaki ɗaya zukatan dake falon wanda dayawansu hamdala sukeyi akan daidaituwar zukatan biyu dasuka fara gani yayinda wasu zukatan tsayawarsu take daidai da barazanar tsinkewar ruhim na har abada,
Musamman aminatu da tun ɗazu take ɗauke wasu zafafan ƙwalla dasuka ɓalle wa fuskarta tamkar famfo,
Ƙyasss!!!
Hasken camera ya fallasa asirin ɗaukar da aunty maimuna'aunty ruƙayya da aunty zainab sukeyi,
Wanda ya saukar da wani rugugin azaba da raɗaɗi a zuciyar aminatu,
Da gudu ta miƙe tayi waje wanda har ga allah dayawan mutanen gurin basu wani damu da hakan ba wasuma basu ganiba saboda yadda hankalinsu yakoma kan su zayyad,
Hajajju ma a hankali ta ɗauke wasu ƙwallan farinciki ganin burinta naneman cika tarefa yiwa allah godiya,
haskaen camera ne ya maido yaya zayyad duniyar tumaninsa kafin yayi nasarar saɓule hannunsa,
a hankali dai itama mama babba tabi ƴarta dan gaskiya tata zuciyar zata iya bugawa,
To itama dai ammi ganin su aunty maimuna nason canza tashar datake ne yasakata sulalewa ita da umma da mama ƙarama kafin aka barsu suda hajajjau,
a ahnkali yaya zayyad ya ɗaga kansa tareda kallon aunty maimuna yace,
"Aunty me kika kawomin ne"
dariya ta ɗanyi tareda nunamasa khadijan ta wutsiyar idamu batareda gabaki ɗaya ƴan guron sun fahimta ba,
So shima dayake ɗan duniyane ya luma fahimceta sai yayi murmushi tareda basarwa yace,
"wai ko bano kika kawowaba"
"kodai banina kawoba dan inda ninakawo ma ai da tuni na miƙo maka dan haka wanda yakawo maka da kansa zai baka"
A ransa yace,
kai wannan matar ƴar tada ɓalli ce wallahy,
kamar kuwa tasan me yace sai kuwa ta ɗanyi murmuahi tareda cewa,
"ai ni haka nake kamar ciwon ajali imnakama sai na kawas"
"Hmmm ai kinma fishi"
Hajiya dai ganin tana gyangyaɗi yasakatayin part ɗinta dankuwa ba lokacin bacci bane dan yamma tayi sosai,
yadda aunty maimuna ke kallon khadijane yasakata tashi a hankali taredalallai ta tafka babban kuskuren barin ammi ta shigo gidan har take nemanzame mata ƙarfen ƙafa,
inkuwa har ammin tafara neman kawomata cikas ko tsaiko a kan buƙatar ta to yazama dole ta ɗaura ɗamarar kawaddda ita daga gidan.kai ita akan buƙatarta fa babu abinda bazata iyayiba sannan kuma babu wanda bazata kara dashi ba ciki kuwa har da hajjajun data haifi uban zayyad takuma haifi uban aminatu take kuma a matsayin uwar mijinta,
tirƙashi!!!
a haka mamatacigaba da ƴan tunane2 Har zuwan yaya fu'ad,
Bayan zuwan yaya fu'ad ɗinne ya umurcesu da fita dan duba jikin yaya zayyad ɗin,
To haka dai suma gabaki ɗayan iyayen suka fita harda hajjaju,
Kowa ya nufi parta ɗinsa da alhinin jikin yaya zayyad ɗin musamman ammi da gabaki ɗaya hankalinta da tunaninta suke akan zayyad ɗin,
Sosai yaya fu'ad ya shiga cikin aikin binciken jikin yaya zayyad ɗin sai dai kuma kamar yadda yayi tunani haka yasamu watakam dai matsalar datake daɓun zayyad ɗin ada yanzuma itace,
Sai dai fa yanzu sosai ciwonnasa yayi girma yakuma canza salo duba da daɗewar ciwonnasa dakuma yadda yanzu mataalar take ƙara ta'azzara dubada yadda ƙarfin sha'awar zayyad ɗin ke ƙara ƙarfi,
Kawo yanzu shi kansa fu'ad ɗin ya fara tsorata da lamarin zayyad,
Taya za'ace mutum ya karanta sannan kuma yasan matsalar datake taredashi babbar matsalace sannan kuma yasan bata da wani magani dayawuce aure amma yatsaya yana ɓata lokacinsa ta hanyar ahan ƙwayoyin dayasan koda sun masa magani baaifi na ƴan awannni ba kuma ciwon zai sake dawowz fiye dana da?
Gsky yazama dole yayi wani abu domin ceton lafiyar abokinsa tundashi bazai taɓa ɗaukar wani mataki ba,
ba sau ɗaya ba yasha bawa zayyad ɗin shawarar tin aure tunda yasan halin abokinsa sarai bazai taɓa iyayin sex da wata wadda ba matarsa ba,
Haka dai fu'ad yayita ƴan tinane tinane amma yakasa samun mafitar abin sai dai yabari har zayyad ɗin yasamu lafiya kafin su tattauna sosai akan lamarin,
Ganin yana buƙatar hutu yasa ya haɗa masa da allurar bacci kafin yasaka masa drip,
Ya jima a zaune agurin kafin ya miƙe zuwa part ɗin ammi kasancewarsa tamkar ɗan gida a gidansu zayyad ɗin,
Itama ammin daga part ɗin zayyad part ɗinta ta wuce dan sama masa abinda zai ɗanci dan ta tabbatar baici komai ba sannan ga aman dayayi tasan yana buƙatar abinci,
A ƙasan ranta kuwa sosai lamarin khadijar ya ƙonamata rai wanda bata taɓa tunanin ƙiyayyar da khadijar takeyiwa zayyad takai har taganshi a halin dayake ciki sannan takuma yi biris dashi saboda tsabar ƙiyayyar datake masa,
ita kanta ta tabbatar da zayyad ɗinne yaga khadija a cikin irin wannan halin bazai taɓa barintaba,
A haka ammi ta cigaba da saƙe saƙe dakuma alwashin hukunta khadijar akan abinda tayi,
tana khitchen yaya fu'ad yayi sallama ganinta a khitchen yasashi nufar babban falon dan jiran ammi,
Bata wani jimaba itama ta shigo falonbayansake gaisawa dasukayi ta tambayeshi jikin zayyad ɗin da tambayar abinda yake damunsa,
Ya so faɗamata amma sai yayi runanin zayyad bazai taɓa jin daɗin abinda zai yinba,
Koda ace ma zai faɗa ɗin to bai dace ya faɗawa ammi ba yafi cancanta ya faɗawa wani daga cikin iyayensa maza,
Wannan tunanin dayayine yasakashi furzadda ɗan zazzafan iska kafin yace,
"ammi zazzaɓine kawai amma nama sakamasa ruwa tareda allurai nasan insha allahu idan ya tashi zai ɗan warware,sai dai kuma zai ɗan samu hutun kwana biyu saboda yanayin jikinsa, sannan kuma inya tashi yasamu yaɗanci wani abu ko ba yawa,"
"Ok badamuwa allah ya baahi lafiya insha allahu idanyatashi ɗin zai ɗan samu yaci wani abin"
"ba damuwa ammi,nima bara na ɗanje kafin yatashi insha allahu zan dawo"
"OK badamuwa fu'ad sai kadawo ɗin"
Bayan fitarsane ammi ta aiki ummy ta kiramata khadija a part hajiya,
__________________________________________________________tunda mama babba ta dawo part ɗin ta takasa zaune ta kasa tsaye ta rasa ta hanyar da zata ɓullowa lamarin duk hanyar data ƙulla sai taga bazata taɓa ɓille mata ba,
A haka dai tacigaba da ƴan saƙe saƙe kafin daga bisani ta ɗauko wayarta tareda latsawa ta fara neman wata nmb,
Har wayar ta kusa tsinkewa kafin aka ɗaga
tun kafin tayi magana ma daga ɗayan ɓangaren aka sheƙe da wata dariyar duniyanci tareda cewa,
"Dama nace ina nan zaune zaki neme ni hajiyata kuma gaki"
Wata ajiyar zuciya mai sanyi mama ta sauke kafin tace,
"look hajiya ruƙayya dan allah kiyi haƙuri kimance da dukkan abinda ya faru ellhyina cikin yanayin damuwa"
Daga ɗayan ɓangaren cikin yanayi na kwantar da hankali aka cigaba,
Haba ƙawata aini dama ban wani ƙullacekiba nadai barkine kawai kiganeda kanki cewar gidanku zumane dan haka dole saida wuta sannan kuma duk abinda nake faɗa miki ada nasone ki zama shugaba a gidan ma'ana sai abinda kika ce amma kika ƙi gashinan yanzu tun ba'aje ko inaba,"
Da sauri mama babba ta katse ƙawarta hajiya ruƙayya dacewa,
"wllhy ƙawata ima cikin matsala sosai musamman nakeso mu haɗu muyi magana inasone kibani shawara"
"shikenan ƙawata amma fa kisani bazan zo gidankiba dan banmanta tsanar da wannan uwar mijin taki tayimin ba dan haka inkinshirya kya zo gidana"
"Shikenan ba damuwa hajiya ruƙayya nagode"
"karki damu ƙawata sai nazo"
Da haka suka tsinke wayar mama babba natuna irin duniyanci da makirci na tsohuwar aminiyar tata wato hajiya ruƙayya"
A ɓangaren hajiya kuwa tunda ta koma ta rufe khadija da faɗa akan abinda tayi kafin daga bisani ta shiga lallaɓa khadijar da nunamata abinda takeyi ɗin ba abune mai kyau ba da nunamata zayyad fa ɗan uwantane bai dace tana nuna masa hakanba,
Kamar wata ta allah haka khafija ta nutsu tana sauraren hajiya daabindatake faɗa mata akanhalayen kirkin zayyadɗin,
Sai dai fa kwata kwata babu abinda ke shiga kan khadija acikin maganganun hajiya na zayyad ɗin kawai dai tana saurarene dan kar hajiya tace ta rainata,
A haka ummy tayi sallama ta samu guri ta zauna kafin tace,
"khadija kije ammi na kiranki"
tunda ummy tashigo gaban khadija ke faɗuwa,
Hakan yasa tanajin an ambaci ammi cikinta yayi wani mummunan kaɗawa,
Ai ba shiri ta kwasa da gudu zuwa banɗaki gabaki ɗayansu binta sukayi da kallo cikin mamakin tsoron da syka gani a tattare da ita,
Lallai yau kuwa khadija ba ƙaramin saɓawa ammi tayiba,
Daƙyar ta fito gabaki ɗaya gwiwoyinta sunyi sanyi sai data ɗan tsugunna a bakin ƙofar banɗakin kafin ta taso tana goge ƙwallab idanunta,
A gaban hajiya ta tsugunna kamar mai neman gafara tareda ɗora hannuwanta bisan cinyarta ta fara magana tana hawaye,
"hajiya! kiyiwa allah dan annabi da al'qur'ani dan darajar tsohon mijinki dayake ƙasa ki rakani gurin ammi kibata haƙuri wllhy yau Innaje ni ɗaya kasheni zatayi,
ummy datake zaune tanakallonsu jitayi gaakiya idan tacogaba da riƙe dariyarta zata iya mutuwa hakan yasa tasaki bakinta tareda sheƙewa da dariya,
Ko hajiya da akewa magiyar kasa daurewa tayi saida ta dara dan gaskiya ba ƙaramar dariya khadijan ta bata ba,
dama haka khadika takeda tsoro haka?cabb,
Duk dariyar da suke bai wani dametaba inda abinda yake damunta a yanzu bai wuce yadda zasu ƙare da ammi ba,
Ganin bata tashiba yasa ummy cewa,
"wai kodai inje incemata bazakizoba?"
A fusace ta juyo tareda cewa,
"kutumar........"
"Kai!kai!!kai!!!"
hajiya ce ta tareta da sauri tareda cewa,
"wllhy kika ƙarasa khadija bazaniba"
Ai da sauri itama khadijar tace,
"wllhy hajiya bazan ƙarasaba yi haƙuri,dan allah ummy kiyi haƙuri"
Sosai dariya take sake neman ƙwacewa ummy hakan yasa tayi saurin ficewa daga ɗakin kafin daƙyar hajiya ta yadda zata raka khadija part ɗin ammin,
WAI INA LABARIN MERRY DA FAREEDA
__________________________________________________________to har yanzu dai fareeda na kinyar ciwon da khadija ta jimata a ta ɗayan ɓangaren kuwa tana tunanin bin shawarar ƙawarta merry kawai zata yadda tasaka hotunan a emblope ta bawa wani ya kai gidansu zayyaddan hakanne kawai zai saka su su yanke hukuncin aurawa zayyad ita dan a yadda merry ta faɗa mata a yadda mahaifin zayyad yake da adalci muddin yaga videos ɗinnan dolene zai tirsasa wa zayyad aurenta dan zata ɗaura alhakin ɓata tarbiyyarta akan zayyadɗin dan har ga allah bazata taɓa iya rayuwa babu shiba ta gwammaci ko wacce wahala a gidan zayyad ɗin data rayu bataredashiba,
Wannan hukuncin data yankene yasakata neman layin ƙawartata,
Bugu biyu merry ta ɗaga dan kuwa itama a nata ɓangaren tana zaunene tana tunaninta hanyar dazata raba zayyad da fareeda ko ta wacce hanya ma koda kuwa zatabi ta ƙarfin tsiya kai itafa a wannan karon ma zata iya nuna fareeda manufarta kai tsaye muddin bata yadda an bada hotunan nan ba,
to ganin kiran fareedar ne yasa merry saurin ɗagawa tareda nunamata damuwa akan jikinta,
A ɗayan ɓangaren fareeda tafara magana,
"ƙawata dama akan maganar zayyad ne yanzu kwata-kwata ma ya daina ɗaga kirana tun jiya hakan yasa na yanke shawarar kawai zamu shirya ne muje mukai wannan saƙonda kanmu,
Kamar anzuba merry ruwan rahama haka taji wanisanyi na ziyartar ruhinta,
Da wani salon duniyanci ta kaɗa idanunta tareda sauke kan wayartayi wani fito irinna ƴan-ƴan bariki kafin ta maida wayar kunnenta,
Cikin nuna halin ko inkula da zance tacemata,
"to ƙawata yadda kika gani sai ki fitar da lokaci sai muje mukai, amma fa zamu tsaya nesa ne da gidan sai mubawa yaro yakai"
" Sannan kuma zai fi kyau ki fitar mana da lokacin da gabaki ɗaya ƴan godan sunanan musamman iyayensu maza"qDate: Jul 30, 2022
Subject: DR zayyad 42&43

Har baccivya fara dan daukar hajiya da khadija, da ummy ta shigo part din Wanda hakan yasa su firgita suka tashibda sauri,
Cikin kidima da rudewa ummy ta fara korawa hajiya bayanin halinda yaya zayyad din gudu ciki,
Ko kafin ummyn ta kai karshema tuni hajiya ta rabata ta fice hankali a tashe,
Ganin hakannema yasa ummy ta bi bayan hajiyar itama hankalinta a tashe,
A tsaye suka bar khadija a sake da

Please Login or Register in order to submit comment