Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baki tana tunanin mafita,
Ba kalar shawarar da batayi da zuciyarka ba kafin daga karshe taja matasan kafafunta ta nufi dakinta,
A can part din yaya zayyad kuwa a rude ammi ta isa part din,
Ba karamin sakw tashi hankalinta yayi ba ganin halinda zayyad yake ciki,
Da sauri ta karasa gareshi tareda tallafoshi ta samu ta maidashi saman gadon kafin ta fara aikin gyara gurin daya bata da amai,
Tana tsaka da aikin gyara gurinne hajiya da su ummy suka karaso sosai itama hajiya tashiga damuwar ganin jikin yaya zayyad din,
Gefen gadon dayake hajiyar ta zauna tareda kai hannunta ta dafa jikinsa,
Sosai har yanzu zazzabin yake jikinsa cikin tausaya wa hajiya tace,
"Sannu zaidu! Allah ya bada lafiya ubangij yasa kaffarar jikine"
Bai iya amsamata ba saima sake dukunkune kansa cikin bargon dayayi,
Ana hakane su umma karama da aunty zainab da aunty rukayya suka shigo,
Sai dai sanin halin zayyad din akan wannan taron dasukayimasane yasa ammi yi wa yaran magana ceqar gabaki dayansu su koma cikin gida,
Haka kuwa akayi kowwa ya tashi amma banda aminatu da take zaune tundazu tana faman kuka,
Ganin hakan yasa hajjaju yimata tsawa,
"Watakam ke bazaki tashi ba kenan gaki isassa kowa ya fita amma ke kintsaya kina kukan munafurci, kokuwa ancemiki zqidun mutuwa zaiyi!?! Ko su sauran ba yan uwansa bane ke kikafi kowa sonshi? "
Kamar bazata tashiba kuma sai ta tashi tana tura baki ta nufi hanyar fita,
Da kallo hajiya ta buta kafin tace,
"Asssha wllhy amina kam kinyi asarar halin munafurcin kinnan,mtsss" taja tsaki tareda sake maida kallonta kan zayyad dayake kwance,
Ko sallama babu mama babba ta banko a firgice ta shigo part din kai tsaye gaban zayyad din ta nufa ba tareda tayiwa kowwa maganaba,
Da azama takai hannunta tana kokarin yaye bargonda zayyad din ya lulluva dashi,
Cikin sauri hajiya dake kokarin yiwa zayyad din magana ta mika hannunta tareda yin azqmar kama hannun Mamar,
Da sauri Mamar ta dago kanta a fusace,
Sai dai kuma ganin fuskar hajiya yasata yin sarander gabaki daya jikinta ya mutu,
Ta dan jima a haka kafin a hankali ta janye hannunta tareda yin baya ta zauna akan kujera,
Daganan babu Wanda yasake magana sai ammi datake faman gyara guri tagama tasaka turare kafin ta dauki wayar Dr zayyad din yafara neman nmbr abokinsa,
Tunda mama babba ta zauna babu abinda takeyi face aikawa da ammi wata uwar harara a fakaice,
Itafa ba karamin bata mata rai ammin nan takeyiba,sai yanzu ma take datasanin barin ammin tashigo gidan har ta zauna take neman nuna mata isa da takama,lallai dolene tasan abinyi tun kafin lokaci ya kuremata,

AYIMIN AFUWA WANNAN MA KOKARI NAYI SABODA MATSALAR WAYA DANA SAMU, NA TUNA DAKUNE KAWAI DAN KUNA RAINA,INA KAUNARKU NA HAR ABADA MY FANS,

YAR MUTAN MURAYE CE

---
Shared using https://www.writediary.com/getappyadda aunty maimuna ke kallon khadijanne yasakata tashi a hankali kamar wadda ƙwai ya fashewa ta nufi inda suka ajiye food flaks ɗin,
ƙaramin kofin ta ɗauka tafara tsiyaya black tea aciki kafin ta ɗauki plate ta buɗe flask ɗin farfesun kayan cikin,
aikuwa dandanan ƙamshi ya buɗe gabaki ɗayan illahirin falon,
sosai shima yayi maraba da ƙamshin tunkafin ta kawo masa,
zubawa ta fara yi cikin saiɓi take yi komai kamar mai tsoron yin laifi ko mai koya,
yadda take saraffa hannunta ne ya shagaltar dashi da kallonta har baisan sadda aunty maimuna tayiwa su zainab alama dasu tashiba,
bai lura da fitarsu gabaki ɗaya daga ɗakin ba sai da tagama zuba masa zata miƙe kafin yayi azamar ɗauke idanunsa daga kanta,
wayam! yaga ɗakin babu kowa sai dai bai damuba dan baisan uzurin su kuma ma ko ba komai shi hakan yayi masa,
kamar mai koyon tafiya ya ƙaraso gabansa tareda dire plate da cup ɗin a hankali lafin ta miƙe da nufi fita,
kawai jin tausasan hannunsa tayi cikinnata wanda hakan yasa ta sauke wata ajiyar zuciya batare da ta shirya ba tareda lumshe zara zaran gashin idanunta,
Jin shiru bai saketa ba bai kuma yimata magana ba hakan yasakata juyowwa da nufin yimasa magana,
Kawai tsintar idanunta tayi cikin nasa wanda hakan yasaka jijiyoyin jikinta daina aiki,
Bazata taɓa iya jurewa kallon cikin idanunsa ba hakan yasaka tayin azamar zare nata idanun daga cikin nasa,
"sit down"
Haka kawai taji ya furta wanda har ga Allah da ace bata kusa dashi sosai bazata taɓa jin abinda yace ba,
Bata wani musa ba ta zauna a kusa da ƙafafunsa tareda zurawa yatsun ƙagarta idanu tana wasa da su
Shima cup ɗin shayin ya ɗauka ya fara kurɓa batareda yasake yin magana ba,
sosai yake jin daɗin shayinhar cikin ransa hakan yasa baimasan ya shanye ba,
sai da yaji babu komai a cup ɗin kafin ya ajiye tareda jawo plate ɗin farfesun,
Shima dai yayi masa daɗi hakan yasa yaci sosai har sai da yaji cikinsa ya cika sosai kafin ya ture tareda kai dubansa gareta,
"zan wanke hannu da baki"
Kawai jin maganar tayi ta doki kunnenta,
Ita fa har ga Allah ta fara gajiya daga kuma tayi laifi kuma ta bada haƙuri dan dai kar ace bata da kunya fa yasa duk abinda akace tayi takeyi amma kuma sai mutum yayita wani ikon banza da wofi yana gadara tsabar miskilanci da gadara da muguwar baƙar ƙazantar tsiya ruwan wanke hannunma sai ankawowa mutum kan gado,
wllhy bazata iya ba,
haka tayi biros dashi kamar bata ki me yace ba,
ya kusan minti biyar a haka kafin yasake maimaita mata a ɗan harzuƙe
"nace miki zan wanke hannu da baki ko"
Sai da ta ɗan kumburo baki kafin ta tashi,
Shima ɗan tsaki yayi a ransa kafin yace,
"yarinya daga an sakarmiki rai sai raini da raahin mutunci"
Bayi tashiga har ta ɗebo ruwan a bokiti kuma ko me ta tuna oho,
Da sauri ta koma ta juye ruwan cikin masai tareda kunna hot water ta tara bokitin kafon ta ɗauko tana murmushi ta nufi gurinsa,
tana zuwa ta ajiye a gabansa tarefa cewa yaya gashi,
kamar wata ta Allah,
haka ya ambata a ransa tareda ɗan kallonta ta wutsiyar idanu,
Gani tana murmushi baisa ya kawo komai a ransa ba da dukkan comfidence ɗinsa ya tsoma hannunsa a bokitin da niyyar wanke hannunsa,
sai dai kuma yana tsoma yaji wani zafi ya zoyarci hannun nasa aikuwa bashiri yayo saurin cire hannunsa yana yarfawa dan gaskiya yaji zafi sosai
yanayin yadda yake yarfe hannuwa da yadda ya kyaɓe fuska yasaka ta kasa riƙe fariyarta aikuwa ta kwashe dariya,
Tun tanayi daga tsaye har takai da duƙawa ta dafe cikinta tana ta dariya,
Tunda ta fara dariyar ya shagala da kallonta gabaki ɗaya ma ya manta da zafin da hannunsa yakeyimasa dan a zahirin gaskiya ta tafi da imaninsa,
jin shiru yasakata tsagaitawa da dariyar tareda ɗaga kanta,
da sauri ta miƙe tareda tsayadda dariyarta,
cikin in ina ta fara magana,
"dan Allah yaya zayyad kayi haƙuri"
sauke ajiyar zuciya yayi kafin yasamu guri ya zauna a gefen gado gami da miƙa mata hannun,
da mamaki tabishi da kallo kafin taji yace,
"oya kiyita hura iska wa hannun nan da bakinki har sai ankira sallar magrib"
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un"
khadija ta furta ganin datayi a jikin agogon dake manne a bangon saura kusan minti arba'in a kira sallah,
buɗe baki tayi da niyyar bashi haƙuri ya katseta,
"wllhy muddin kikayi magana anan zamuyi magrib da issha nidake"
Ba shiri kuwa taja bakinta ta rufe,sai dai kuma da gani ba alkhairi take saƙawa ranta ba,
Yadda take hura masa iskar slow ba ƙaramin ratsasa yakeyi ba da shiga jikinsa,
Sosai yayi dauriyar ganin bai jawota jikinsa ba,
Wani ni'imtaccen bacci ne ya kwashesa wanda baisan lokacin da ta sulale ta gudu ba,
Sai da aka fara kiraye kirayen sallar magrib kafin yayi firgigit ya tashi,
Ganin bata nan yasa yayi hanyar banɗaki,
Bai wani jima ba ya fito ɗaure da towel kafin a gaggauce ya shirya jikinsa ya nufi masallaci,
Ana idarwa ya nufi part ɗin hajiya dan shi kansa ya gaji da zaman ɗakinnasa,
A part ɗin ya tarar da da yawan yaran gifan musamman maza inda kowwa yayi masa sannu kafin aka shiga hirarraki,
suna haka su baba ummaru da ƴan uwansa suka shigo inda yaran suka sassakko dan basu gurin zama,
To shima dai zayyad miƙewa yayi saida suka zazzauna kafin ya zauna ya gaishesu suka yimasa ya jiki,
daga haka aka cigaba da hira har lokacin sallar issha,
bayam sun dawo daga sallar issha nan ma part ɗin hajiya suka dawo amma har yanzu shiru baba isuhu bai dawo ba,
hakan yasa baba ummaru ya lira ya tambayeshi ko lafiya?
bayan sun gaisa yake basu uzurin dubo abokin kasuwancinsu da gamayyar ƙungiyar kasuwa ta wakilta su amma yanzu zai dawo,
Da haka baba ummaru ya kashe wayarsa kafin suka cigaba da hira,
___________________________________________________________tun bayan issha suka gama shirin su kaf tareda saka farin gam ajikin emblope ɗin kafin suka hawo motar merru suka kama hanyar gidansu zayyad,
ba ƙaramin nishaɗi da farinciki merry takejiba yayinda ga baki ɗaya fareeda ta rasa abinda yakeyimata daɗi ,
Gaban tane ke wani mugiwar faɗuwa gani take batayiwa zayyad halacci ba datazama mai tona asirinsa amma wata zucoyar nacemata in batayi hakan ba zayyad zai kuɓuce mata na har abada,
Sai wajejen ƙarfe tara suka ƙaraso ƙofar gidan kasancewar sun taradda ho slow akan hanya,
Sim ɗan jima a ƙofar gidan amma shiru babu yaro,
Suna nan wata mota tayo gidan wanda hakan ya tabbatar musu ɗayane daga a halin gidan,
but amma ta ya zasu bashi saƙon babu yaron aiki,
har ya ƙaraso basu gama yanke hukunci ba,
sai da ya kashe motarsa kafin ya buɗe gate ɗin yashiga da motar,
bai jima da shiga ba suka sami almajiri suka bashi emblope ɗin tareda bashi naira hamsin sukace duk wanda yasamu ya bashi yace abawa baban zayyad,
Sai da suka tabbatar yaron yashiga gidan kafin suka ja motar suka bar layin,koda yaron ya shiga gidan baiga kowa ba hakan yasakashi yin ɗan dabur dabur alamar neman wanda zai bawa,
daga can wajen parking space ya hango ana rufe mota hakan yasakashi nufar hanyar parcking space ɗin,
da sauri ya fara nufar wanda yagani dan ya nufi hanyar shiga gidan,
Ganin yana neman shigewa yasaka yaron ɗan ɗaga murya yace,
"wai gashi abawa baban zayyad inji wasu ƴan mata a waje"
Karaf maganar ta sauka akan kunnen mama babba wadda take a laɓe tana waya da aminiyarta hajiya ruƙayya,
Da mamaki tasake nanata maganar yaron,
"inji wasu ƴan mata kuma abawa baban zayyad?"
Cikin sauri ta fito daga malaɓarta tareda yo inda yaron yake dan karɓar saƙon,
Sai dai kuma ko kafin tazo ma tuni baba isuhu ya rigata tana ƙarasowwa yana miƙa hannu ya karɓi emblope ɗin tareda kallon yaron,
"ƴammata kuma"
Cikin rashin wayau irinna yara yace,
"eh acikin mota ma suke suka kirani sukabani"
Baba isuhu ya dafa kan yaron tareda sake cemasa,
"to kuma baban zayyad suka cemaka kodai ka manta zayyad sukace?"
"A'a wllhy baban zayyad sukace nabawa"
"Shi kenan jeka abinka ba damuwa angode kaji"
Ba tareda wata damuwa ba yaron ya kama gabansa kafin shima ya juya da nufin shiga gida,
Gamin mutum a tsaye yaso yaɗan razana shi saboda bai ga kowwa ba a farko,
Auziya yayi kafin yace,
"waye"
A daburce mama ta fara kame kame,
"uhm ummm dama uyyymmm dama naɗan fitone"
Daƙyar tasamu ta haɗa kalmar kafin tayi saurin yin gaba,
Sosai mamaki ya kashe baba isuhu ya tsaye shin me hakan yake nufi kenan,
Ganin ba amsa yasakashi yin gaba tareda mamakin wannan emblope ɗin kuma ace wai inji wasu ƴammata abawa baban zayyad shin kodai yaron yayi kuskurene?
To amma in zayyad suke nufin a bawa ai yasan bazasu rasa contact da zayyad ɗin ba dan haka koma meye zasu iya yinshi a waya ko yasamesu,
Any way dai bazai taɓa bawa kowa emblope ɗin ba batareda ya duba yaga abinda yake ciki ba,

koda ya shiga gidan direct part ɗin hajjaju ya wuce wanda hakan shine tamkar al'adar mutanen gidan,

Bayan ƴan gaishe gaiahe tsakaninsa da ƴan uwansa akan ɗan taɓa hira kafin kowwa ya fara tashi dan zuwa ga iyalansu,

Kamar kowa shima baba isuhu haka ya miƙe ya nufi ɓangarensa da nufin inya gama ganin abinda ke cikin emblope ɗin da safe ya bawa yayannansa,

To kasancewarsa ajazi dakuma kasancewar mutim mai iyali yasa yana shiga part ɗin bayan ƴan abubuwan al'ada da yagabatar kamar yadda yasaba sai kuma yashiga wata sabgar shaf ya manta da maganar emblope ɗin kwata kwata,

Kasancewar kayan daya ke jikinsa dama yasakasu wannan maimaicine yasa yana cirewa ammi ta sakasu acikin doesving ɗin ɗakinsa na wanki,

daga haka kuma aka mance da wani babi na emblope,

Washe gari tun da safe mama babba tashirya da nufin zuwa asibiti dubo wata daga danginsu,

Tana fita ta kirawo wayar hajiya ruƙayya ta faɗa mata inda zasu haɗu dan zuwa gurin boka,

A ɓangaren zayyad kuwa yau ba laifi yaɗan tashi da sauƙi hakan yasa yana dawowa daga masallaci yayi wanka kafin yasake kwanciya,

ƙarfe tara ammi da abba suka ahigo part ɗin dan duba jikin zayyad saidai ganin yana bacci yasa suka juya da nufin komawa,

Jin motsin mutum yasa zayyad shima ya farka tareda yin miƙa gami da salati,

Ganin ya farka yasa suka dawo,
tashi yayi zaune cikin girmamawa ya fara gaishesu,

Suma dai kamar koqane lokaci cikin nuna tsantsar so da kulawa suka amsa da yimasa ya jiki,

Sai a lokacin aaƙon kiya ya faɗowa baba isuhu a rai,cikin hikima ya fara tambayar zayyad ɗin shin ko akwai wani saƙo dasukayi da wani za'a kawo gidan?,

Cikin alamun rashin damuwa zayyad ɗin ya amsa masa da a'a,

Jin hakannema ya ƙara ƙarfafawa baba osuhu gwiwa akan lallai ya duba saƙon gudun kuskure,

Ganin yana niyyar makara yasa sukayiwa zayyad ɗin sallama ammi na sanar ɓasa cewa brek first ɗinsa na part ɗinta,

Shima zayyad ɗin ya amsa mata da cewar idan ya kimtsa zai shigo ya karya,

Suna fitowwa baba isuhu ya nufi gurin motarsa da nufin idan ya dawo zai duba saƙon ganin yanzu ya makara,

So bayan kowwa ya fita masu lactures ɗim safe ma sunfita saɓanin su khadija da zasu shiga ƙarfe ɗaya da rabi,

ita dai aminatu ganin mama ta fita yasa itama yau kwata kwata bata fito ba ta ƙule a ɗaki tana tunamin da bazai amfana mata komai ba,

Kamar kullum yau ma khadija ta gamawa hajjaju aikace aikacenta kafin ta shirya tsaf cikin riga da sket na atamfa tareda murza ɗauri mai matuƙar kyau,

Duk da bawata kwalliya tayiba face hoda data shafa amma dai kunsan shi mai kyau kome yayi kyau yake,

A hankali take tafiya cikin talunta mai ɗaukar hankali ta nufi part ɗin ammi,

A falo ta iske ammin dan itama tuni suka gama dukkan aikace aikacen su itada ummy kafin ummyn ta wuce gurin aminiyarta fateema,

Da sallama tashigo falon ammi ta amsa,ta duƙa ta gaisheda ammin kafin tasamu guri a kusa da ammin ta zauna,

Sun ɗan fara taɓa hira cikin dabara ammi ke sako mata magamar yaya zayyad da irin karamcinsa da ɗaukar ammin dayayi a matsayin uwa,

cikin salon manyance da dabara take muna khafdijar ba wai zayyad ya tsaneta bane a'a sai dai wasu halaye nata da bayaso dasuke sakawa tana ganin kamar tsana ce,

Suna cikin wannan maganar zayyad ɗin yashigo cikin shigar ƙananun kaya datayi matuƙar karɓarsa,

da sallama yashigo suka amsa itada ammin yasami kujera ya zauna ammi na tambayarsa ƙarfon jiki,

Cikin dabara ta ɗaga idanunta ta ɗan saci kallonsa dan tun a shigowwarsa shigarsa ta ɗan birgeta,

A rashin sa'a kuwa shima ita yake kallo hakan yasa taji wata muguwar kunya ta lulluɓeta,

Sai da ta ɗan murguɗa masa baki kafin ta ɗauke idanunta daga kansa,

Sosai murmushi ya kusa ƙwace masa kafin yayi nasarar danneshi ya wani haɗe rai,

Ɗan mintsininta ammi tayi kafin tayo firgigit tace,

"yaya zayyad ina kwana,ya jiki"
Ta faɗa tareda turo baki wanda ammi bata ganiba amma shi sarai akan idanunsa,

"haɗomin breack ki kawomin"
Shine kawai abinda yace mata,

"ɗan iko mugu kawai"

Ta faɗa a ƙasan maƙoshi wanda babu wanda yaji acikinsu,

Kamar bazata tashi ba amma dai ta daure saboda idanin ammi taje ta haɗo masa ta kawomasa,

Yakusa minti biyar kafin ya miƙe yafara ci,

Bai wani ci sosai ba ya koma kan kujerar yasake kwanciya,

Ganin ya gama yasakata tashi ta ɗauke kayan tun kafin ammi tayi ƙorafi,

Ko kafin ta dawo ma ammin ta tashi a hanya suka haɗu dan haka tace mata ta je ɗakin abbansu ta ɗakko manyan kayan cikin basket ɗinsa ta kawo gali zai zo yanzu ya karɓa,

Ammi na gama faɗa ta wuce ɗaki dan gabatar da nata uzurin kafin khafija ma tawuce ɗakin abba,

Tana zuwa ta kwaso kayan ta taho,
Lokacinda tazo falo ya sauko ƙasa yawani baje ƙafafu,

Ai kuwa tsautsayi tana gittawa yasa mata ƙafa ta faɗa kan kujera kayan kuma suka zube,
Zubewar da kayan sukayine yasaka emblope ɗin tarwatsewa aikuwa hotunan suka bayyana a ƙasa a watse,

Ba ƙaramin tashin hankaline ya ziyarcesu gabaki ɗayansu ba ganin wannan mugun bala'in a ƙasa kuma daga cikin kayan abban,

"INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN,shine kawai kalmar da suke maimaitawa gabaki ɗayansu,
tuni zayyad ya jiƙe da wani uban gumi wanda zaka iya rantsuwa ruwa aka kwara masa,

Saɓanin khadija da hawaye suka ɓallewa fuskarta kamar famfo,

jin motsin ana shigowwa shi ya ƙara tada hankalinsu gabaki ɗaya musamman ma dasuka fara jiyo mitar hajjaju,

Har ta zuro ƙafarta cikin falo gabaki ɗaya zayyad ya gama sarewa dacewar yau ranar tonon asirinsa ce wadda bazai taɓa fatan ko maƙiyinsa ya kasance aciki ba,

Wata uwar sifa khadija tayi ta baza babbar rigar abban gabaki ɗaya a ƙasa tareda malalewa akanta ta rife hotunan,

Har lokacin kuma hawayen basu daina ambaliya a idanunta ba,

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment