Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dole zasu ga fareedar kuma hakan zaisaka su takurawa zayyad akan sai yayi aure,
To daga nan ita kuma sai taci gaba da ahigemusu a mtsayin saliha kuma mai son ɗansu har tasamu damar aureshi,28&29

khadija kuwa sai ƙarfe biyu suka tashi dafa school ganin ana ƙwala rana yasata nufi gida da nufin idan ta sake shiri saita nufi aaibitin,

A gajiya take sosai koda taje gida ba kowwa a gidan sai su mama babba dasuke part ɗinsu da umma ƙarama,

Hakan yasa direct tanufi part ɗin hajjaju ta,
kanta ne yakeyimata wani irin ciwo hakan yasa tanayin wanka ta sha magani tafaɗa kan gado da nufin taɗan huta sai ta nufi aaibitin,

Aikuwa tana kwanciya bacci yayi awon gaba da ita.
Sai ƙarfe ukku da minti goma ta farka ganin lokacin da agogo ya nuna yasata miƙe cikin sauri tafara shirin zuwa asibitin.
Ba wani ɓata lokaci ta turare jikinta da turaren wutar ta kafin saka wando da riga na pakistan baƙi da adon golden,
Ba wani kwalliya ta tsaya yiwa fuskartaba iya powder da lipstick kawai tasaka sai ta ahafe jikinta da turaren gold amber gabaki ɗaya ƙamahin jikinta ya rikiɗe yabada wani ni'imtaccen ƙamshi na musamman,
Ganin yanayin ahigarta yasa ta dakki wani aah ɗin hijabi mai kyau kalar na zamani tasaka dogone har ƙasa,
Gsky khadija nada kyau na ban mamaki dankuwa ɗas ta fito acikin hijabin kamar zaka saceta ka gudu.

A can asbiti kuwa koda aunty maimuna ta kama hannun aminatu suka nufi komawa ɗakin da ammi take.
Gabaki ɗaya aminatu batasan inda take ɗora ƙafarta ba jinta take kamar ba itaba.
Babu abinda takeji sai maganganun su aunty maimuna da yaya zayyad wanda takejinsu kamar zasu fasa mata kunnuwa.
Itafa tama rasa me zata tunana.
shin wai me suke nufine,anya kuwa zuciyarta nayimata adalci akan soyayyar zayyad kuwa,
A gsky bazata taɓa iya jurewa ganin zayyad inuwa ɗaya da wata ba itaba taɗaukarwa ranta alwashin ganin bayan dukkan wanda yake burin rabata da soyayyar zayyad ko waye.
A haka batasan sun iso ɗakin da aka ajiye amminba,
saida aunty maimuna ta ɗan taɓota kafin tayi wata iriyar firgita.
Hannunta aunty maimuna taɗan murza da ƙarfi kafin ta daidaita amma daka kalleta zakasan tana cikin damuwa,
Hajiya ce ta kalleta cikin sigar lallashi tace,
"wai ni kam amina meyake damunkine naga duk kin canza kamar wadda batada lakka ajiki,ga wata faɗawa dakikayi"
a yanzu dai duk iya duniyaci na aminatu ta kasa koda yaƙenma sai raba idanu datake famanyi a tsaye,
Gudub karta sake faɗuwa yasa aunty maimuna nuna mata kujera da idanu.
Aikuwa kamar me jiran umarni ta zauna akan kujerar kamar saƙago,
Aunty maimunace takalli hajiya tace,
"wai kantane yake ciwo shinefa duk tashiga damuwa"
Ba tareda tabawa hajiyar wata dama ta yin maganaba tacigaba dacewa,
"uhmmm hajiya kingafa har zanshiga zance na manta zayyad yace mu haɗa kaya za'a sallamemu"
Hajiya da umma ne suka haɗa baki gurin cewa,
"Masha allahu"
cikin raha aunty maimuna taɗan kalli ammi datake lazimi tace,
"a'a fa hajiya kubar murna naga kamar har yanzu jikin ammi bai ƙarasa watssakewaba"
Aikuwa da sauri ammi ta ɗago idanunta tana murmushi ta kalli aunty maimuna tace,
"hmmm haba aunty ai wllhy ninasan nafiki lafiya"
"Kayyy ammi anya kuwa to kuma ai naga babu alamun hakan a jikinki"
A jiye carbin hannunta ammi tayi tareda yin bissimillah ta sauko daga kan gadon datake ta kalli aunty maimuna da murmushi,
"na sauko ƙanwata mezanyimiki a tabbatar nasamu lafiya"
"hmmm ammi anya kuwa"
"kina tan tamane"
"To goyo"
Aunty maimuna tafaɗa da yar dariya,
Gabaki ɗayansu dariyar suka yi kafin mama ta tashi tafara haɗa kayansu,
ana hakan dr zayyad ya shigo ɗakin da sallama a bakinsa daga ganinsa daga masallacin asibitin yake,
Ganin ammi a tsaye yasashi komawa daga gefenta a tsaya tareda kama hannuwanta ya ɗaura kansa a kafaɗarta,
"ammina ya naganki a tsaye"
Zayyad ya faɗa da husky voice ɗinsa,
"hmmmm to yarona ai jiki yayi kyau kaga gwamma in ringa ƙarfafawa ko?"

"kumafa hakane gaskiya"
Ya faɗa yana kallon ammin,kafin yajuya kallonsa ga aunty maimuna,
"auntyna maigidanki fa zaki kirawo yazo yatafi daku saboda gsky inada ooeration banda ƙarfe ukku da rabi dan haka bazan samu damar komawa gidaba sai zuwa dare"
"Ok ba matsala bara nakirashi sai yazo mutafi"
ammi ce ta kalli aunty maimuna tace,
"a'a gsky ba sai ankirashi ankatse masa kasuwarsa,sai dai ko akira ahmad ina ƙila yadawo daga school sai kabashi motarka yakaimu imyaso sai yadawo maka da ita shikuma ya hau abin hawa yakoma gida"
Tunda ammi tafara magana hajiya ke sakamata albarka da yaba baiwar hankali irinna ammi dama sauran pan uwanta sirikkan hajiyar,
"yadda kikace haka za'ayi ammina"
DR zayyad ya faɗa yana ɗaga wayarsa dankiran ahmad,
bugu biyu wayar tayi ahmad yaɗauka cikin girmamawa,
"Assalami alaikum"
"wa'alaykassalam"
"Yaya ya aiki"
"Maaha Allah,inason ganinka asibiti yanzu"
"OK badamuwa insh.... "
ko ƙaraswa baiyiba zayyad yakashe wayarsa gamida maidata cikin aljihunsa,
Yasake kallon su hajiya yace,
"bara na je office yanzu za'a kawo muku takardar sallama"
Bai tsaya jin me suke faɗaba yayi gaba abinsa ya nufi office ɗinsa,
"hmmmmmm"
Aminatu ta saki wata nannauyar ajiyar zuciya wadda tasasu gabaki ɗaya kallonta,
Ita har ga allah bama tasan me yake faruwaba,
Tunda zayyad ya tsaya idanunta suka tsaya akansa zuciyarta na ƴara azalzakarta da soyayyar zayyad ɗin. A ranta take cewa,
"gsky yaya zayyad duniyane ta tabbatar babu macen da zata iya ɗora idanunta akan yaya zayyad ɗin batareda ta saukesu da cikakkuyar ƙaunarsa ba,
Sheɗaniyar zuciyarta tacigaba da hankaɗa ta akan ra'ayinta na tabbatarwa kanta dole ne ta mallaki zayyad kota halin ƙaƙ"
ammi ce ta ɗan matso jikinta tareda dafa ta tace,
"Sannu kinji ɗiyata"
firgigit ta yi saurin ɗaga idanu suka haɗa ido da ammi,
"sannu ɗiayata kinji bari muje gida sai ki samu ki ɗab kwanta lozakusamu reliep"
Yaƙe taɗanyi kafin a ranta ta fara tsinewa ammi saboda a ganinta ammin katangace dake tsakaninta da zayyad.


A gsky ba namijiba ko mace ta kalli irin shigar da fareeda tayi sai taji wani tanayi ajikinta,
irin shigarda tabbas idan ke uwar kirkice kika kalli fareeda saikinyi gaggawar nema mata shiriya daga Allah,
Riga da wando tasaka waƴanda sukayi matuƴar karɓar jikinta sunti masifar yimata kyau rigar ƙaramace sosai wadda muddin zatayi kyakkyawan motsi sai ka hango cibiyarta,
Sai wani arnan wando data saka wanda yafitar da gabaki ɗaya sharp ɗinjikinta sosai ya ɗameta sai wata top mai dogon hannu wadda taji duwatsu mai kyau sosai wadda batada maraba da rariya,
Takalmi tasaka high hill mai shegen kyau wanda yaji duwatsu a samansa,
Sai kuma jakarta ƙarama datasaka wadda tayu daidai da tsarin sgigarta dakuma takalminta,
Sosai ɗaurin ɗankwalinta ya zauna daram akanta gakuma wivon na atach data saka,
Gsky ba ƙarya fareeda tayi kyau sosai ga wani sihirtaccen ƴamshi datake bazawa nai ɗaukar hankali,
A yangance tafara juyi tana nunawa ƙawarta merry tsarin,
A gsky da ace zaka buɗe zucoyar merry to da zaka tabbatar da itama ba baya bace a fagen danƙararriyar ƙaunar zayyad ɗin saboda yadda wani baƙinciki ya narke acikin zuciyarta da azababben kishin dayake taso mata,
Wai yanzu tana gani farreda zata tafi gurin mijinda zata aura kuma mallakin zuciyarta da wannan shigar,
gsky da badan plain ɗinta akan fareedar ba babu abinda zai hanata wulaƙanta fareedar dakuma nuna mata iyakar ta akan zayyad ɗin,
Sai dai kuma akwai lokacin da sai tasaka fareeda hawaye da idanunta wannan alwashine sai ta nunawa fareeda ceewar zayyad ba kalarta bane,
Lokaci na zuwa da fareeda zatayi nadamar saninta sannan kuma zata tabbatar mata itafa cikakkiyar ƴar barikice,
"gsky ƴawata dolene yau ɗinnan zayyad yashiga tarkinmu.irin wannan ado haka dole mu nuna wa zayyad mufa ba ƙasgin yar wa bane,
Sosai farreda taji daɗin yabon da merry tayimata ta wani washe baki tare da yin farrr da idanu,
A fa kaice merry ta bankamata wata muguwar harara kafin ta wayance da yin murmushin yaƙe,
"wannan farin a ajiyewa zayyad dan na tabbatar zai masa amfani"
Bata bata damar yin maganaba ta diba agogo tareda yin saurin cewa,
"gsky yakamata mutafi kingafa har ƙarfe ukku da rabi"
"ok ba matsala mutafi"
Itama merry ɓiƙewa tayi suka nufi hanyar fita,

A asibitin kuwa tuni sun gama haɗa kayansu har ahmad ma yazo yafara fita da kayan yanasaka su mota,
Sai da ahmad ya kammala tsaf kafin suka fito daga ɗakin,
A cikin corridoor ɗin ɗakin suka haɗu da zayyad yati shirinsa cikin kayan da zai shiga aikin,
Sosai kayan sun amshi tsarin jikin zayyad ɗin da farin glas ɗim dayake maƙale da idanunsa,
"masha allah"
duka suka faɗa amma muryar ammi tafi ta kowwa fita dayake tafaɗane da ɗan sauti tana murmushi ta kamosa jikinta,
"Allah yayimaka albarka da ƙannenka gabaki ɗaya ɗana,"
Mirmushi yayi yace,
"ammi na sai gida ko?"
"to ɗana tunda jiki ya warware ai zaman asibiti ba daɗi damma dakai"
Murmushin jin daɗi ya fitar me sauti,
hajjaju ce taja ƙafarta gaba tana mita,
Wanda hakan yasasu yim ƙaramar dariya,
A hankali suke tafiya sai da zayyad yaraka ammi har bakin mota yaga ahigarta da tafiyarsu kafin ya koma cikin aaibitin,

A daidai bakin gate zasu fita su kuma su farreda motarsu zatashigo,
To dayake aunty maimuna na ta jikin windoe kuma window ɗin abuɗe ne yasa sukayi ido biyu da merry da take driving,
Dayake suma nasu glass fin a ɗan sake yake,
Ai kuwa sosai gaban merry ya faɗi ganin sunyiwa juna kallon ido cikin ido da matarda ta tsaya acikin zuciyarta daram,
Tsabbb aunty maimuba ta ganeta tareda yimata kallon na fahimceki kuma na raina naki wayau,
Da sauri merry ta janye idanunta tareda yin azamar duƙar da kanta,
Tuni motarsu aunty maimuna ta wuce hakan yasa fareeda bata wani san meyake faruwa ba
30&31


Duk da aunty maimuna ta sake fahimtar abubuwa da dama a ɗan kallon dayashiga tsakaninta da merry hakan baiwani sa ta nuna damuwa a fuskarta ba,

A hankali merry ta parking motar a inda aka tanada dan ajiye motocin,
Sun ɗauki mintina acikin motar suna tattauna yadda fareeda zata jawo hankalin zayyad,

Amma agefe guda merry nayiwa fareeda shune ne ta hanyar da dole sai ahalin zayyad ɗin sunganta duk da kuwa bataso ganin fitar aunty maimunan ba taso ace sun haɗu da fareeda,

Amma kobasu haɗu yanzuba tasan dole fareeda zata hadu da ƴan uwan zayyad sannan kuma a yanayin shigar da ta tura fareedar tayi tasan duk wani mai mai mutunci bazai so ace fareeda ta kasance daga ahalinsa ba,

"fareeda wannan wata babbar damace da zamuyi amfani da ita dan haka kisan duk hanyar dazakibi dan ki tabbatar kinja ra'ayin zayyad akan abinda mukeda buƙata,karkiwani damu da cewar nan asibiti ne inason ki fara jan hankalin ɗaukacin mutanen asibitin yazamana kowwa yasan ke wacece kuma suga gurin eanda kikazo,hakan shine zai bamu damar cimma burikanmu"

"gsky ina aldahari dake ƙawata bazan taɓa baki kunya ina mai tabbatar miki saikin ganmu a inuwa ɗaya nida dr nah"
Wani malalacon kallo merry tayiwa fareeda wanda saika cika cikakken ɗan bariki zaka iya fahimtar inda kallon yadosa,
A hankali farreda ta buɗe murfin motar tareda sakko ƙafarta ta fito,
Ta ɗauku ƴan sakanni tana ƙarewa asibitin kallo kafin tafara taku cikin wani salo na musamman da ba kowwa ne zai iya kallonta sau ɗaya ya ɗauke kansa ba,
Yanayin yadda take karya jikinta dole mai ƙaramar shawa zai tsaya kallonta da ƙoƙarin damƙe hajiyarsa dan sosai take juya madaidaitan mazaunanta dasuka ɗame cikin fitinannen wandon datda saka,

Wata zazzafar ajiyar zuciya merry ta sauke tareda kwantar da kujerar ta tabi jikinta,
"lallai farreda bakida wayau naki wasane"

A haka fareeda ta osa har ɓangaren da office ɗin zayyad ɗin yake,
Batareda ta damu da yanayin kallon da mitanen gurin suke binta dashiba ta tsaya bakin office ɗin tarda yin nocking sai wani yauƙi take da sigar cikakkiyar ƴar bariki,
Dr zayyad kuwa dayake tsaye bakin ƙofa kuma a shirye tsaf da kayan aiki yabuɗe ƙofar tareda zuba idanunsa akan fareedar da bai tsammaci ganintaba,
dirar mikiya idanunsa suka saukar masa da ganinsa kan fareedar da ta tabbatar yanayin shigarta tabbas dole ya rikita gwarzonnata,
Aikuwa cak idanunsa suka tsayar dashi akan surar jikinnata da yake bi da wani kayataccen kallo,
ganin hakan yasa itama farredar ta fara neman canza salonsa da kashemasa idanu tareda lasar lips ɗinta,
Ko motsi dr zayyad baiyiba kuma har yanzu idanunsa na kanta da zazzafan kallonsa da ta tabbatar da zai iya juyewa ako da yaushe,
A hankali ta ranƙwafo ƙirjinta batareda ta ɗaga ƙafafaunta ba ta yo duƙo da niyyar hura masa iska a idanunsa,
Tana sane ta manna illahirin nonuwanta a jikin ƙirjinsa tareda hura masa sassanyar isakar bakinta datake tafe da ƙamshin sinadarin saka ƙamshin baki,
aikuwa ya wani lumshe idanunsa a cikin wani irin slow,
Ganin hakan yasa tasake goga masa ƙirjinta cikin wani salo dayasakashi sauke wani malalacin nishi da bai shiryawa zuwansaba,

Tunda ta fito daga gidan take ɗan sauri sauri dan ganin har ƙarfe ukku da arba'in a daidai bakin layinsu tasamu abin hawa ta tsayar tareda cemasa,
"Aminu kano"
ta shiga yaja suka kama hanyar asibitin,
kwata kwata bata ma kawo cewar ansallami ammi ba kasancewar babu waya a hannunta bare kuma wani yakirata ya faɗamata,
Hakan yasa batama wani lura da motarsu ammin ba lokacinda suka hau babban titin asibiti lokacin sukuama motarsu zata sauka zuwa layom dazai sadasu da gida,
Kodavsukaje asibitin ta sauka kafin ta biya mai adaidaita kuɗinsa,
A hamkali cikin nitsuwa ta nufi cikin katafaren asibitin,
Direct ɓangaren da aka kwantar da ammi can tanufa watakam emergency,
Koda ta shigo cikin harabar ɗakin da aka kwantar da ammi amma bataga kowwa ba hakan yasa direct ta nufi ɗakin da tasan ammin take a tunaninta ko suna ciki,
A hankali ta tura ƙofar ɗakin kasancewar ba wani daɗewa sukayi da fita ba yasa ba'a rufw ɗakinba,
Ganin datayi wayam ɗakin babu kowwa yasata tsayawa ta fara tunanin to ina suka nufa,
Kodai ansallamesune?,
To kuma inda ansallamesu aida sai wani yakirata ya faɗamata hakan,
To inama wayar da za'a kiratan bayan wancan mugun ya cillar mata da waya saboda tsabar zalinci da mugunta,
A sarari ta furta,
"Allah ya isa wllhy mugu kawai"
Kome ta tuna kuma!oho tadaiti saurin saka hannunta ta rufe bakinta tareda ɗan yin waige waige kafin ta ɗan ɗaure fiska tareda yin gungunin da na tabbatar ba alkairi ta faɗa ba,
"to kodai ciwon ammi ne ya tashi aka canzamata ɗaki"
Wata zuciyar ta faɗa mata,wanda hakan yasa zuciyarta bugawa da ƙarfi,
da sauri ta juya a guje ta fito daga ɗakin wanda hakan yayi daidai da shigowqar wani saurayi ɓangaren,
bata wani damu da sanin ko waye ba tayi gurinsa tareda tambayarsa acokin tashin hankali,
"dan allah ko kasan meyake fariwa da matar da aka kwantar a wannan room ɗin,"
"shima da ɗan tashin hankalin yadda yaga ta wani birkice ya fara magana,
"eh to gaskiya banida wata masaniya da hakan amma dai ɗazu naga wasu daga nan room ɗin sun nufi office ɗin DR zayyad,sai dai nasan patiete in ansallameshi ai bazai nufi office ɗin dr ba,amma ki ƴarasa office ɗin inada tabbacin zaki samu cikakken bayani acan ɗain,"
Ita har ga allah tama mance da wani hukunci data ɗauka na yanke duk wata alaƙa da abimda zai haɗa ta da yaya zayyad ɗin kamar yadda ta faɗa, dan kuwa ko kafin saurayin yaƙarasa faɗar abinda zai faɗa tayi office ɗin yaya zayyad ɗin aguje,
ɓangaren su zayyad kuwa jin nishin dayake sali yasa farreda taƙi bashi damar ko matsawa daga yadda suke saima sake matsemasa da tayi tareda saka ɗan yatsanta ta fara zagaya kyakkyawan sajensa dayayima fuskarsa wani masifaffen kyau,
Tuni ta fara canza salon dr zayyad ɗin da yanayin nata salon idanunsa har sunfara camza da maitarsa ta sh'awa datake shirin ɓallewa,
Bakinta takai saitin labbansa tareda zaro harshenta ta ɗora akan laɓɓan nasa tafara lasa,
sake lumshe shanyayyun idanunsa yayo dasuka yi masa wani irin nauyi,
Tareda ɗaukar hannunsa da ƙyar ya ɗaura akan bayanta ya ɗan sake turota jikinsa,
Aikuwa ta wani sake manna jikinsu gurin ɗaya tareda haɗe bakinsu,
Tuni suka fara bawa juna wani zazzafan kiss da sai ka rantse mayun watan zakunane,
Sosai zayyad yadage wajen shafa jikinta tareda mammatsa jikinnata zuwan kunnuwanta,
Da gudu tashigo ɗan coridor ɗin dazai sadata da office ɗinsa wanda gabaki ɗaya ma gurin babu mutane kasancewar ba gurine da mutane ke yawan zuwaba,
sai datazo dab da shiga office ɗin kafin idanunta sukayi mummunan ganin da yasakata cikin tashin hankali da nadamar zuwanta ofgice ɗin,
Da sauro ta fara ja da baya kafon ta saki wata razananniyar ƙara da saida suka dawo hayyacinsu tareda saurin saki juna suka kalli ɓangarenda khadija take gabaki ɗayansu,
Tuni hawaye sun ɓallewa idanun khadijar,
Zuciyarta ce ma ta tsaya cak takasa koda tuna mata meyake faruwa,
Gani khadijar kuwa ba ƙaramin girgiza zayyad yayiba amma dayake cikakken ɗan duniyane sai ya wani wayance da tsuramata idanunsa,
A hankali ya fara takawa zuwa inda take ganin hakan yasata fara ja da baya tana bim bango har tazo bakin office ɗinsa,
Bai bar binta hakan uasaka riƙe ƙofar da ƙarfi tareda dakewa tana zubarda hawayenta,
Sai da ya ƙaraso inda take kafin ya tsareta da idanunsa sosai yake kallon yadda hawaye ke ambaliya a fuskarta,
duk duniyanci da ƙwarewar bariki irinna zayyad yaji wani yanayi a jikinsa na babu daɗi,duk da bawai nadamar ganinsa danfarreda da khadija tayi bane yasashi jin ba daɗin danshi a ganinsa ba wani abubane tunda ba a wani hali ta iskeshi da fareedar ba,
Amma yaji ba daɗi da gani yadda ƴanwarsa take zubadda hawaye akan wani abu data gani daga gareshi wanda baimata daɗiba,
A hankali ya ɗaga hanninsa da niyyar kaiwa kan fuskarta ya sharemata hawayenta a karon farko da zai lallashi ɗaya daga cikin ƙannensa,
Sai dai kuma ganin abimda yake ahirin yi yasaka ɓangarorin biyu da suke a daskare saurin harzuƙowwa da niyyar ɗaukar matakai dabam daban,
A ɓangaren khadija wata ƙara ta ƙwalla tareda ƙanƙamewa guri ɗaya wanda yasa dr zayyad saurin janye hannunsa dan a tunaninsa wani abin ya faru da ita,
cikin shashhekar kuka tafara cewa,
"wllhy in kataɓani allah ya isa ai dama na daɗe da fara tunanin kai ɗan iskane ashe kuwa hakane tunda gashi har karuwai kake bi shine zaka ringa neman yimin sharri "
haka dai khadija tafara ihu da surutai da sai ka rantse bata cikin hamkalinta,
to farreda ma ganin zayyad zai kai hannunsa kan khadija yasata harzuƙowwa a fusace ta tsaya a gaban khadijar cikin ɗaga murya tafara magana,
" ke dallah sha'sha dabba kawai,baccinma hauka da rashin tunani da tsabar rashin ilimi da duhun kai kinga mutane a guri ki fara yimusu ihu aka,"
Sosai itama fareeda take ihu da hargowa tareda faɗawa khadija maganganu batareda tasan kowacece ba,
ita kanta khadija tayi mamakin yadda fareeda ta tsaya a gabanta take mata waƴannan magamnaganun to saidai kuma bata ita takeyi ba,
ita fa har ga allah hankalinta ya tashi da hakin dataga ɗan uwanta aciki,
muryar fareeda ce ta sake dakar dodon kunnenta a karo na farko da ta maida hankali dajin maganar bidurwar da zucoyarta ta raɗawa suna kilaki,
"nina tsani rashin wayewa da jahilci amma yanzu abinda yake cutar mafi yawan yara kenan kwata kwata oyayensu basu......"
Ai kafin merry ta ƙarasa maganarta tuni khadija ta ahammacesu gabaki ɗayansu daga ita har zayyad ɗin,
kawai sai jin khadija yayi ta yi kan fareeda,
da sauri shima yanufesu amma innnnna!
Ko kafin ya ƙarasa tuni khadija ta rarumi ƙafafun fareeda,
Abinka da takalmi hill aikuwa tawani yarɓar da ita da ƙarfi bakinta da goshinta suka daki ƙasan tiles ɗin wajen,


Please Login or Register in order to submit comment