Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nason ƙayatar dashi,

A haka suka isa har gidan merry,kafin su saukoma saida suka gama nishaɗantar da juna,

Hannun fareeda riƙe cikin na Alhaji Wada haka suka shiga gidan ba ko sallama,

Lokacin da suka shigo merry na falo tana waya,
Ganin fareeda yasa ta canza maganar datakeyi cikin duniyanci ƙarshe ma ta kashe wayar,

Kallon Alhajin tayi tareda yin wani farrr da idanunta, a yangance tace,

"manyan ƙasa dama talaka na ganinka"

Wata muguwar dariya ya saki shima cikin salon nasa duniyancin,

"ai bawani babba in ba kuba,tunda naji mutuniyar tace gidanki zatazo nasan tabbas yau akwai harka, shiyasa ma nace nima baza'a bar a baya ba,"

itama merryn dariya tayi,

"ai nima ina ganinka nasan tabbas yau akwai harka"

Tareda bawa fareeda hannu suka tafa, kafin ahima alhajin ya matso tareda rungume merryn,

"bama ko ɗan oyo'yo ɗinnan na runguma"

Yafada tareda jawo fareeda itama suka fara harka gabaki ɗayansu,


A can asibiti kuwa zayyad gaba ɗaya yaraba khadija da hijabin ta ya kafa bakinsa kan nononta sai wata jarababbiyar tsotsa yake yi musu,

tun khadija na iya daure wa har ta fara kasawa da yadda zayyad yake luliye mata kan bress ɗin nata,


Tun dazu ake buga ƙofar office ɗin zayyad ɗin amma ya gagara sakin khadija yaje yabuɗe,24


karo na biyar kenan lan line ɗin office ɗinsa na bugawa,

Daƙyar cikin kasala yaɗago kansa daga jikin nonuwan khadijar ya miƙa hannunsa ya latsa tare da ciro kan wayar yasa akunnensa,

"Dr lpy kuwa tun ɗazu ake buga ofgfice ɗinka amma shiru kuma ankira land line na office ɗinka shima shiru"


Duk ikin sauri dakuma alamun tashin hankali ake waƴan nan magan'ganun,

"what happen"

shine kawai abinda dr zayyad ya iya faɗa yana lunshe rinannun idanu wansa masu kama da na me jin barci,

"operation aka kawo maka kuma emergency"

"i'm coming"

Kawai yafaɗa kafi yasauke kan wayar,

wani kallo yayi wa khadija na bangaji da ɗan'ɗana daga garekiba,

"kar nasake ganin ki da wani,inkuma aure kike so to zaki iya faɗamin"

Yamiƙe tareda maida mata hijabinta,

A hankali ya nufi ƙofar fita daga office ɗin,

Ko motsi khadija batayiba,hakan yasa yaɗan tsaya a bakin office ɗin,kafin yace,

"ko zaki zauna da aljanunkine"

Zumbur ta miƙe tana ɗan turo bakinta,

Gani tayi yafara takowwa ziyo kanta,

Da sauri taja baya tareda cewa cikin tsoro,

"auncle zayyad dan girman allah kayi hakuri wllhy bada kai nakeba"

Sosai tabawa zayyad dariya har yakasaƙunshe dariya,

A'ikuwa saida yayi dariyarsa,

Tsayawa tayi tasaki baki tana kallon yaya zayyadnɗin yana dariya,

Tunda ta tashi agidansu takejin anacewa yaya zayyad yafi kowwa kyau,

Amma bata taɓa yadda da hakan ba sai yanzu datake kallon sa yana dariya,

"Lallai yaya zayyad ba ƙaramin kyakkyawa bane"

Har ga Allah bata taɓa tunanin maganarta zata fi fili ba bare kuma har yaya zayyad ɗin yaji abinda take faɗa,
Sai ji tayi kawai yace,

"kuma ƙwalelenki ba"

Da sauri ta rufe bakinta tareda ɗan zaro idanunta,

Sai a lokacin ya ƙaraso tareda kama hannunta yaɗan kalli yarsunta na ƴan seconds kafin yayimata kiss a yatsun yasaki tareda yin hanyar fita,

A gefe guda kuma tunda ta furta maganarta yaji wani abu da bai taɓa jiba yadira cikin zuciyarsa,

Da sauri ta bi bayansa suka fita,

Tana saurin ta kamosa kasancewar yamma tayi dayake aaibitin lungune yasa duhu yaɗan fara yi gashi kuma ƙafa taɗan fara raguwa,

hakan yasa tayadda suka jera amma ko kallonta baiyibaa,

kiciɓis sukayi da mama babba ta ta fito daga ɗakin zata kira khadijar autafi gida,

wani irin duka ƙirjin mama babba yayi ganin khadija da zayyad ajere,
To me gakan yake nufi?,

Gaba ki ɗayan su babu wanda ya lura da ita sai da sukaji muryarta,

"haba zayyad yazaka saka yariya cikin office tun ɗazu muna jiranta amma ka hanata fitowwa, kekuma daɗi namiji inkika lalata rayuwar ki ke kika jiyo,na tabbatar zayyad bazai taɓa aurar kiba misamman......"

"Mama!!!"

dr zayyad yafaɗa cikin wani eikitaccen amo mai tafe da ɓacin rai,

A fusace yaja hannun khadija dan gaky mudfin ya tsaya komai ma zai iya faruwa ciki kuwa harda wulaƙanta maman,

Baki aaake mama tabisu da kallo,

Saida zayyad yakai bakin ƙofar ɗakin mama kafin yasaki hannun khadija agurguje ya nufi inda ake nemansa,

Tunda yajawo hannun khadija tazama kamar raƙumi da akala, kwata2 hankalinta tunanin da nazarinta yana gurin kalaman mama da muryar maman keyimata wani irin amo acikin kunnuwanta,

"ke kuma daɗi namiji ko,in kika lalata rayuwarki ke kika jiyo zayyad dai bazai taɓa auren kiba"

ta rasada wanne ma'auni zata auna kalaman mamar ta yaya kuma zata tan'tancesu,

A haka maman tazo ta isketa kamar zata bangajeta haka ta wuce ta ta shige cikin ɗakin,

Kamar wlƙiya haka umma da hajiya suka ga mama na huci,

"a'a lpy dai ko?"

Cewar umma,

"hmmmm wai daga ganin khadija da zayyad na tambayeta ina taje shinefa tafara yimin rashin kunya kamar zata zageni,kuma gaban zayyad ko kallon mu baiyiba barema nayi tunanin zai yimata faɗa"

Tsamal hajjaju ta karɓe zancen dacewa,

"kay gsky sai dai ko iskokin hadizar amma dai hadiza bazata taɓa yimiki rashin kunya ba kuma zaidu na kallonta"

Sosai maganar hajiya ta ɓatawa mama rai amma dayake aharti take neman ƙullawa sai ta nuna bata damuba tace,

"wllhy hajiya kindaisan ai bazan yiwa khadija sharri ba daga office ɗin zayyad ɗinma suka fito,dama nan dana fita na tambayi wani saurayi shine yake cemin yaganta itada zayyad suna office ɗin shi"

Cikin sigar haɗa bom ɗin dazai tashi da khadijar take faɗar wannan maganar,

"Alhamdulillahi Allah nagodemaka daka fara daidaita tsakanin zaidu da hadiza"

Hajjaju tafaɗa tana tana ɗaga hannunta sama,

Wani mugun ƙudu'du ne yatasowwa mama babba, bata sake magana ba kuwa,

Sai da hajjaju tace mata ta tashi su tafi gida,

A ƙofar ɗakin suka taradda khadija a zaune tayi tagumi,

Umma ce ta isa gurinta tareda tambayarta
"lfy khadija"

"Lfy ƙalau umma"

"to tashi maza ku tafi gida"

kama hannunta tayi a hankali ta miƙar da ita,sai da umma tarakasu har bakin motar yaya munir kafin tayi musu sallama,

Tunda suka shiga motar mama babba bata sake maganaba har suka ƙarasa gida,

Koda sukaje gidama saida safe kawai tayi musu ta nufi ɓangarenta daga ka ganta zaka tabbatar akwai abinda ke damunta,

a ɓangaren khadija ma suku'ku haka take kamar wadda ƙwai yafashewa aciki haka take tafiya,

Duk da kasancewar hajiya ta lura da canzawar khadijar amma haka ta basar bata ma nuna ta kula da hakan ba,

Koda suka shiga part ɗin hajiya ɗakinta ta nufa,

To itama khadijar ɗakinta ta nufa tayi wanka bata tsaya wani shafa mai ko wani abun ba kawai turare ta fesa tasaka kayan bacci ta ɗakko zundumemen hijabinta dayake lokacin sallar issha yayi,

Tana idarwa ta fada kan gado,
Tana jiyo su ummy da fateema a falon hajiya amma ko saurarensu bata yiba tafaɗa dunoyar tunani,

to me mama take nufi da kalamanta?,
Ko taga wata alama ne atareda ita nacewar tana son yaya zayyad ɗin,
Ita fa wllhy ko maza sun ƙare bazata taɓa iya auren mai hali irinna yaya zayyad ba,

Wani ɓangarene na zuciyarta ya hasko mata fukar yaya zayyad ɗin lokacin da yake dariya,

Gsky yaya zayyad kyakkyawan gaske ne,
To dama meyasa bata ganin kyawun yaya zayyad ɗin,
Wata zuciyar ce tace mata saboda yatsaneki kawai,

Baki ta taɓe tareda cewa a fili,
"nima wllhy natsaneka yaya zayyad"
Ta gaɗa tareda jawo fillo ta rungume a haka bacci ya ɗauketa (ayi mafarkin kyakkyawa yaya zayyad ta gidana😀😀😀)25


kasancewar yau tanada school yasa tunda duku2 da ta tashi bata komaba tanayin sallah ta fita fallo ta fara gyarawa kafin ta gayara khitchen ta wanke yan kwanukan hajjajun daga nan ta wanke banɗaki,

Ɗakin ta ta koma ta shiga ta wanke toilet ɗinta ta yi wanka kafin ta fito ɗaute da towel,

tsayawa tayi a bakin mirrow tashafe jikinta da mai,
Sosai ta ɓata lokacin wajen gyara jikinta da mayuka da turarurruka,
Powder kawai ta saka da lipstick kafin ta ɗakko wata dakakkiyar shadda yallow ɗinkin doguwar riga tasaka,
Sosai ɗinkin ya karɓi jikinta yazauna,
blue ɗin mayafi tasaka da takalmi plate mai duwatsu
sai mayafi midium shima blue data saka,

Ɗas ta fito a budurwarta wata baƙar jaka ta goya irinta Ƴan jami'a,

Gsky khadija kyakkyawa ce,masha allah shine kawai abinda na iya furtawa,

da ɗan saurinta ta fito ganin har takwas saura minti tara,

A falo taga hajiya a zaune,
Itama bakin kujerar tasamu tazauna tareda cewa,
"Hajiya ina kwana"

"lafiya ƙalau hadiza ya gajiya"
Ɗan dafe kai khadija tayi cikin nuna damuwa kafin taɗan ja lokaci tasauke hannun da jan numfashi tace,
"Ba gajiya"
"hajiya bari in tafi school kar na makara"

"aa baki ysayawa ki karya"
"Gsky hajiya innace zan tsaya yin kari zan iya makara,kuma kimga in na makara wllhy baza'i barni inshiga aji ba,"

Muskutawa hajiya tayi tareda tura hannunta cikin aljihu ta zaro gudar naira dubu tabawa khadija,
"gaahi nan Allah yatsare hanya ya bada sa'a"

"Amn hajjajun mu"
"amma dai zaki biya ku tafi dasu ummy ko?, jiyama sunzo nemanki ita ummynma sai ɓangaren Iro ta kwana"
jim taɗanyi aranta tana tunani gsky in tace zata tsayasu ummy zasu iya haɗuwa da yaya zayyad ita kuma gsky yanzu ta saka aranta zata toshe duk hanyar dazata sake haɗata dashi barema aringa tunanin sonshi takeyi,


"hajiya gsky ni wllhy kinga ba ajinmu ɗaya ba yau, kuma zasu iya sawa na makara naje malamin ya koreni"

"to gsky dai kiyi sauri allah yakiyaye hanya sai kin dawo"

"Amn"
Khadija tace tareda yin hanyar fita,

da sauri2 tabar gidan ta tari napep tareda faɗamasa bayero univercity,

koda taje makarantar saura minti biyu lacturer ya fure aji da sauri ta shiga ta zauna ta nutsu,

Dan khadija afannin ɗaukar darasi gwanace,

a ɓangaren mama babba kuwa tunda taje goda tasaka aminatu gaba tana nuna mata yadda zata ringa kissa dan jawo hankalin dr zayyad kanta,
da kuma nuna mata dolene su haɗa da makirci dan ita tanada tabbacin akwai wani abu atsakanin khadija da zayyad ɗin kuma hajiya ma tasani,
Sosai aminatu ta buɗe kunnuwanta tana kwashe mugayen huɗubobin uwarta,

ai kuwa yau dayake aminatun batada lecrures hakan yasa tun da wuri ta tashi ta tsan'tsara kwalli ta nufi ɓangaren Aunty maimuna,

Kasancewar sun san muddin ammibata nan zayyad baya shiga ko ina yayi break sai ɓangaren aunty maimuna,
.
Da sallama ta shiga part ɗin auntyn,bata same ta a falo ba hakan yasa ta nufi khitchen aikuwa kamar yadda tayi tunani tana khitchen ɗin tana haɗa break,

Sosai aunty maimuna tayi mamakin ganin aminatu,amma kasancewar aunty maimuna wayayya yasa ta wayance bata wani nuna mata ba,

bayan sun gaisa aminatu taɗan fara kamawa aunty maimunan ayyukan khitchen ɗin,
ganin ankusa gamawa yasa auntyn sakar mata iata kuna ta wuce ɗaki,

ko kafin aminatu ta ƙarasa ayyukan tuni aunty maimuna ta shirya al'hussain daddynsa ma ya shirya,

A gaggauce ta bawa yaron kari kasancewar ya makara school ta zubawa babansa a lunch box shima zai wuce kasuwa dan amafi yawan lokuata da abin kari yake tafiya,

Sai da ta rakasu kafin tadawo a falo taga aminatu azaune tasake gyara fuskarta,

A fakaice aunty maimuna ta kalleta kafin taɗan taɓe baki,

"aminatu yau ba school ne"
"Eh wllhy aunty banida lectures yau"

"ok kice tare zamuje asibiti kenan"

shiru aminatun taɗanyi kafin tace,

"a'a ni sai anjima zanje aunty"

"ok shikenan bara muje part ɗin hajiya daga can nizan wuce asibitin kasancewar tau da wuri zanje saboda zayyad da ya kwana acan kuma kinga saina kai masa abinci zai karya"

tsilim taga aminatu ta miƙe tareda cew,
"aunty to muje asibitin tare mana"

"A'a yanzufa na tambayeki aminatu, kuma kukacemin bazakijeba,"

Sosa kai aminatu ta ɗanyi tareda cewa,
"wllhy aunty yanzu kawai naji inason tafiyar"
Ɗan taɓe baki aunty maimuna tayi kafin tace,
"kyadaia ji da iyayinki"
A ranta kuwa tana saƙe2 a bubuwa da dama akan aminatu,

A haka dai ta ɗauki basket ɗin sukayi ɓangaren hajiya,

Koda suka ƙarasa tuni hajiya itama ta shirya suna zaune a falo ita da ummy dakuma fateema,

Da sallama suka shiga aunty maimuna ta duƙa ta gaida hajiya,kafin tazauna kan kujera kusada aminatun,

Tunda syka shigo aminatu ke zuba idanu neman khadija amma shiru hakan yasata tunanin kodai khadijan na ɗakin tane,

a ranta tace,
"Munafuka yanzun haka tana ɗaki tanayiwa wanda bai damu da itaba kwalliya"

Wani kishi ne yasake tasomata tunowwa datayi cewar tabbas ko ita tasan khadijar ta fita kyau26

muryar hajiya taji tanacewa,

"to ai sai ku taso mutafi saboda mu dawo da wuri ko"

A sanyaye ta taso itafa gsky bata so atafi abar lhadija agidan saboda bataso ace yau ma zasu tafi ita da zayyad ɗin kamar jiya,

"hajiya wai ina khadija ko bazatajeba"
"a'i Tun ɗazu khadija ta tafi makaranta sai antaso zata biya"

Saurin washe baki tayi tareda yin gaba da azamar ta,

Da idanu hajiya tabita kafin ta taɓe baki itama tayi gaba,
A motar yaya munir zasu tafi dan haka suka nufi motar yaya munir ɗin,

Ko ƙarasawa basuyiba yaya munir shima yafito daga part ɗinsu shida yaya al'ameen,

har gaban hajiya suka ƙaraso kafin yaya al'ameen yace,

"hajiya har kun fito kenan"

"wllhy kuwa aminu mutanen jigawa tafiyar ce ko?"
"Wllhy kuwa hajiya gashi zamu hau hanya"
yaya al'ameen yafaɗa tareda kamo hannun hajiya,
Itama dafa kansa tayi tana cewa,
"Allah ubangiji yatsare yakuna bada sa'ar abinda akaje nema ayi ta haƙuri da rayuwa kaji aminu"
Mur'mushi yaya al'ammen yayi tareda cewa,
"insha allahu hajjajunmu"
Ya saki hannunta yayi gaba yana ɗaga musu hannu,
Suma mota suka shiga sukayi asibitin,


A ɓan garen su merry kuwa sai da suka gama masha'arsu kafin alhajin yatafi,

Sai da yatafi suka zauna kafin fareeda ta kalli merry,

"ƙawata ya ya dai naji wayarki shiru,kinsan fa ina cikin wani hali gashi inata kiran zayyad amma yaƙi ɗaga wayata"
"nifa ina tsoron ace zayyad yaƙi yadda da abinda nakeda buƙata"

Da yaƙe a fuskar merry ta kalli fareeda,
"hmmm ƙawata kenan nidai soyayyar ki da zayyad na bani mamaki, gsky dole mu kama zayyad ahannunmu"

"wllhy ƙawata al'amuran zayyad na bani mamaki,tunda nake da zayyad fa sex bai taɓa haɗani dashiba,"

"hmmm fareeda kenan ki kwantar da hankalinki kisaka aranki zayyad nakine ke kaɗai ƙawata"

A ran merry kuwa ashar take ɗirkawa fareedar dakuma mugun al'kaba'i,

Miƙewa fareeda tayi tafara juyi agaban merry,

"ƙawata kalleni fa shin wai me narasa a duniya da yasa sai na nemi alfarmar zayyad ya aureni"

zama tasakeyi agaban merry,
Ban taɓa tunanin cewar ni fareeda akwai ranar da zan so wani namiji da zummar aure ba sannan kuma ba taaɓa tunanin zan ringa bin namiji yana wulaƙantani ba"
"Yanzu dai ba wannan ba meye mafita"

A zuciyar merry tace anzo gurin,

"shiryawa zakiyi zuwa gobe muje asibiti mu sake nemansa da buƙatar mu"

ba tareda wani dogon tunani ba fareeda tayiwa merry godiya,
Daga nan suka canza akalar hirar da yawanci surutan fareeda duk akan soyayyar zayyad ɗinne


Koda suka je asibitin yau jikin ammi da sauƙi sosai ana tunaninma in basu sallameta zuwa anjima ba to idan allah yakaimu gobe zasu iya sallamarta da wuri ma kuwa,

Dan tunda sukaje aka barsu suka shiga gurinta sunata hirarsu da ammi,

A hankali ya turo ƙofar yashigo da sallama,
Ga baki ɗaya suka haɗa baki gurin amsa masa sallamarsa,

Shi kansa yarasa dalili tunda yashigo yake baza idanunsa kamar wanda yake neman wani abu,

cikin sauri ya kawadda idanunsa zuwa duba magungunan da suke kan ɗan ƙaramin table ɗin gabana gadon,

Hnnunsa yakai kan hannun ammin yaɗagoshi tareda ɗan dubawa,

Kallonta yayi da ɗan murmushi kafin yace,

"lallai ammina ansamu lafiya"
itama murmushin tayi kafin tace"

"sosai ma kuwa rabin raina,jikina kam masha allahu ga kuma ƙwarin gwiwar albishir ɗin sirika ta data zo dubani,kaga kuwa ai dole in zanzare in miƙe tunda mu ma bana za'a dainayimana gori"

Ammi ta faɗa da ɓurmushi tana satar kallon umma,

Aikuwa an taɓowa hajiya inda yakeyimata ƙai'ƙayi,

"wllhy kuwa kedan bakiga sirikar takiba da sai kinma fi haka murmurewa,gata saliha irin wacce kikeyiwa ɗanki fata"

"Aikuwa hajiya kinada babbar kyauta mai tsoakatunda kekika fara yaba sirikata"

Dukansu dariya sukayi banda aminatu datakejin kamar an aikomata da saƙon mutuwa,

Gabaki ɗaya zuciyarta ta dawo mata maƙoshi ta wani tokareta ko miyau ta kasa haɗiyawa,

"uhmmm allah dai yazaɓa mafi alkairi dan ba'a ganewa a hijabinnanfa hajiya"
Cewar aunty maimuna,

Umma ce tace,

"kashh maimuna dama baki faɗaba ai su idanunsu a rufe yaje yanzu zaau fara ƙidayaki a layin ƴan baƙin ciki"

"ai wllhy nasani dama keda maimuna tunda kukaga yarinyar nan a idanunku naga batayimuku ba to ai saiku zaɓo masa wata tunda ku kowwa ma baiyimukuba"

"haka fa kwanaki yarinya taringa zarya tanason zaidu tsakaninta da allah amma ke maimuna ke kika tsage kikace wai ba ajinshi bace"

Hjjaju ce take wannan maganganun,

Cikin raha itama aunty maimunan tace,

"wllhy hajiya ni idannayiwa zayyad zaɓe sai yaji duk duniya ba wanda yakauni iya zaɓe"

Gabaki ɗayansu dariya sukayi,
Har shi uban gayyar saida ya ɗan murmusa tareda girgiza ka,gsky aunty maimuna ba damace,

Fuuuuuu aminatu tayi waje kamar wata macijiya,

Baki asake hajiya ta bita har ta ƙule wa ganinta kafin tajuyo tanacewa,

"wai ni kwana biyunnan ina lura da amina wani lokacin kamar mai iska,"

"sai tana walwala kuma sai kaga gabaki ɗaya ranta ya ɓaci,yarinya sai kace wadda akewa girka"

aunty maimuna ce ta tace,

"hajiya kindai san halin amnatu da zurfin ciki,amma bari in mun koma gida zan lallaɓata naji abinda yake damunta,"

dr zayyad ne ya kalli aunty maimuna yaɗan shagwaɓe fuska kafin yace,

"yanzu dan allah aunty tun safe nakiraki nace kitahon da abin kari amma tunda kikazo kiketa zuba hira kinkasa bani koɗan shayima, saboda kawai ammina bata da lafy"

Yaƴarasa maganarsa yana kallon ammi,

"hmmm zaidu kenan inbanda abinka yo dama kullum itace zata dawwama ci dakai,ai duk rintsi wata rana sai naga fuskar wannan kilbabbiyar matar taka wadda ƙilama mummunace"

har yafara tafiya zai fita daga ɗakin ya juyo jin maganar hajiya ta ƙarshe,

"me kikeci na baka na zuba ai matata ma sai kingaji da ganinta,sannan wai nidakaina nacemiki ga wadda zan aura,dan haka karki ƙara haɗani da kowacce mace kina zaune zan kawomiki kyakkyawar matata"

Yana gama faɗar hakan ya juya yayi gaba abinsa,

"ba shakka zaidu! kayi baki. aikuwa wllhy tunda ni ka watsawa ƙasa a ido zaka sakw samun wadda zata ringa kareka a maganar aure amma badai niba kuma wllhy ubanka zai dawo sauna turashi ya sakaka fiddo matar aure"

Shi dai dr zayyad baimasan abinda take cewa ba yayi gaba abinsa,

Sai su ammi dasuke faman yimata dariya,

ƙofar ɗakin yaci karo da aminatu tana zaune tasha uban kukan ta,shidai ya ganta amma bai wani tabbatar da yanatinta ba ya wuce warsa abinsa,

bai jima da fitaba aunty maimuna ta fito da flaks ɗin abinci a hannunta,

I tama a bakin ƙofa ta ataradda aminatun tayi uban tagumi ita ɗaya,

Bata wani nuna mata tasan tana cikin damuwa ba saima cewa datayi,

"A'a mennata eai nan kika dawo ne"

A hankali ta ɗago kanta ta kalli aunty maimuna,
Duk wanda ya kalli idanun aminatu zai tabbatar tasha kuka,
"subahanallahi aminatu kuka kuma lfy"
Wani sabon hawayenne yasake sakkowa aminatu wanda ta kasa control ɗinsa yafara zuba daga cikin idanunta,

sauke abin hannunta auty maimuna tayi tareda duƙawa ta dafa cinyoyin aminatun,

"Ameenatu lafy da kuka haka kodai wani abun yana damunkine wanda kike ganin kukan yafi yimiki daɗi akan kifaɗa mana"

Haƙiƙa mama babba ta dasawa zucoyar aminatu tsanar mutane dayawa ciki huwa harda aunty maimuna,
sai dai kima ta koyamata mugun makirci da munafurci tayadda bazaka taɓa fahimtar gskyrta ba,

Amma innnna!
Tuni aunty maimuna batun yau ba ta fahimci aminatu na son zayyad saboda aunty maimuna irin mutanennan ne masu baiwar fahimta,

A hankali aminatu tasaka hannunta tashare fuskarta kafin takalli aunty maimuana ta ɗanyi yaƙe tace,
"wllhy aunty haka kawai nakejin raina yaɓaci sai luma wani ciwon kai danakeji"

duk da aunty maimuna tasan kome yake damun amimatun kuma tasan duniyanci tayimata na ɓoye mata damuwarta yasa tace,

"habbba aminatu meye abin kuka saboda ciwon kai keda kikeda yaya dr,uym ki kwanyar da hankalimki yanzu muje office ɗin yayanku sai yabaki ɓaganin kinji ta wajena"

Aunty maimuna tafaɗa tareda miƙar da ita tsaye ta ɗauki flask ɗin suka nufi office ɗin,

da sallama aunty maimuna suka shiga office ɗin dr zayyad,

Yana waya hakan yasa shi ɗaga musu hannu,
"ni ban wulaƴanta kiba kedai kike ganin hakan,inada baƙi ina zuwa"

Ɗib,ya kashe layin farreda dasuka kirashi itada merry,
Da ɗan murmushi ya kalli aunty maimuna tareda buɗe flask ɗin gabansa,
Sosai ƙamshin abincin ya daki gancinsa,
Ai kuwa ya wani lumshe idanunsa tareda shaƙar numfashinsa,
Cikin raha aunty maimuna tace,
"ba'a saba cin irin wannan ba ko?"
Shima murmushi yaɗanyi kafin yace,
"amma aikinsan bai kai na ammi ba ko"
Ɗan kallon sama tayi kafin tace,
"uymmmmm!amma dai kasan nafi amaryar da zaka aura ko"
Kallon sarious yayi mata kafin yace,

"wai ni aunty kinwani damu kanki kwanannan da maganar aurena ahin koko dai kinsamomin matar da zan aurane"

"In kabani dama zayyad kadaisan bnafika iya zaɓi tunda nazabo daddynka ko?"

"Kayyyy aunty abin harda zagi"

"ba zagi zayyad gsky nafaɗa"

"to nabaki aunty amma kisani infa batayiminba zance batayiminba"
"albishirinka"
"goro"
"fari ko ja"
"Fari tass auntyna"
"OK to meye goron albishir ɗin"
"me kike so"
"matar da zan samo maka ba itace zatace tanasonka ba kaine da kanka zaka faɗa tarkon ƙaunarta sannan kuma kace kanasonta, inhar hakan ta kasance zakabani kyautar sabuwar mota"

Dariya yayi sosai kafin yace,
"gsky aunty kin ɗaukeni yaro! karkimanta fa na girmeki amma zakiyimin wayo"
Kallonsa tayi ido cikin ido kafin taci sarious tafara magana da tsantsar gsky,

"Zayyad nasan ka girmeni amma a haka zaka faɗa tarkon zaɓin daznyimaka sannan kuma kai da kanka zayyad mai taƙama da gayu zaka zama bawan wadda na zaɓa maka inkuma haka takasance kayadda zaka bani mota sabiwa dal"

shima cikin sarious ya kalleta kafin yace,
"ni zayyad na yadda in har na faɗa ƙaramin tarko irinnaki zan baki kyautar sabuwar mota da naira dubu ɗari biyar cash"
Cikin tsabar murna da ɗoki ta kama hancinta kafin tace,
"wllhy badan muna asibitiba da sainayi guɗa da wannan al'ƙawarin da ka ɗauka"
Yifffffff,sulaji faɗuwar aminatu tsabar sanyin da ƙafafunta sukayi,
Da sauri aunty maimuna ta yi kanta dan ita har ga allah tama manta da maganar aminatun,

kamo hannunta tayi ta taimakamata tamiƙe tsaye tarda zaunar da ita gaban kujerar zayyad,

"kaga kasama na shagala da amunatu,wai kantane yake ciwo shine nace tazo muje kabata magani"
Zayyad kuwa dayake jikin kujera kallon aminatun yayi kafin a hankali ya taɓe bakinsa da cewa,
"ta sha paracetamol zai daina,ai shegen yawon tsiyane dasu,"
"in kunkoma aunty kice su umma su haɗa kayansu da ƙarfe biyu zaau tafi gida"
" Yawwa alhamdulillah"

A ɓangaren su merry kuwa tun ƙarfe goma merry tazo gidansu farreda wai dan ta ƙara yadda ta damu da ita da matsalarta,

Meeryn ce ma tasaka fareeda ta sake nacewa kiran zayyad ɗin har ya ɗaga sun ffara waya su aunty maimuna suka ahigo wanda hakan yasa ya kashe wayar gabaki ɗaya ma,

Sosai hakan yatadawa farreda hankali wanda merry ta turata wai ta shirya suje aaibitin,

haka kuwa akayi a take farreda ta tashi ta ahiga wanka,

Tana ahiga merry ta buɗe wadrobe ɗinta ta zaɓo mata wasu matsiyatan fitinannun kaya,
koda fareeda ta fito tasoyin ƙorafi akan kayanda merry ta zaɓo mata amma merryn taƙi bata dama,

Kasancewar itama merryn danata wayon akan fareeda tasaka wannan shigar banzar,
Tunda tasan oyayen zayyad suna nandan haka

Please Login or Register in order to submit comment