Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sallah akai da anyi zai mike kome yake yi wannan ma ya dade yana burge ni tare da shi.

Kowa in ana maganar Ya Haidar zai ce yana da hankali da nutsuwa.

Tashi mu shiga ciki, zaman tunani ba naki bane kin san kina da matsala.

Haka muka tashi muka koma ciki duk na kasa sakewa.


Karfe 6:20 bayan munyi sallah magariba. Muka fara shiga wanka. Nice karshe ina fitowa na shafa mai na feshe turare.

Ves da 3 quarter ta saka farare tas ddoguwar riga ta dauko zata saka, Faiza da aka gama yiwa kwalliya ta kwace, Allah sai an miki kwalliya.

"Kinsan a halin da nake ciki, da zaki min kwalliya."
"Ynzu a lokacin biki na kike, shiga halin kunci, me kika mai dani ne da zakice baza kiyi ba. Hafsat?"
ta fada idon ta na cikowa da kwalla.

Hauwa da akewa kwalliya, tace,
"A'ah kar ki bata mana kwalliya malama. Ki rabu da ita kar tayin."

Rigar ta cilla mata, tayi gaba.
Kiran wayar tane ya shigo.
Dagawa tayi,
"Hello Baby nah."
"Na'am Yayan mu!"

"A'ah Amaryata yana ji muryar ki haka. Wa ya taba ki."
"Hafsat ce."

"Bata wayar."
Mika mata wayar tayi,

"Hafsyn mu, me ya faru?"
"Wai dan nace bazan yi kwalliya ba."

"Haba Hafsy! Daure kiyi biki nane fa."
"Yi hkri zanyi."

"Yauwah ko kefa. Bani Faizan."
Ta mika mata bansan me suke, cewa ba sai dai naji tace, kada ka damu ai yar hannun Momy ce.
Dazu ma boye mana ita tayi, sai kad itace amarya.

Wajen na bari, dan nasan akai na ake maganar.

Bayan an min kwalliya duk na canja kama. Wata doguwar riga na saka ruwan omo sai stones ruwan hoda. Ruwan hoda mayafi da takalmi cover shoe da jaka na saka.

Hauwa kuma jar ta saka, sai tai masa addon yellow.

Amarya kuma ta saka. Ruwan goro da ruwan kasar. Tayi kyau sosai.

Kamar yadda angon ya saka ruwan kasar jallabiya mai kyau da tsada,


Wajen yayi kyau sosai, amman ni ina can bayan wajen dan bason hayaniya nake ba. Tinda mukai hotuna na janye jiki na, na bar wajen.

Ni bam ma ga Ya Haidar ba,kuma naji dadin hakan ashe duk hotunan da akai har dashi.

Yana ganina nayi, can cikin wajen.sai da ya ganni ya debe minti na sannan ya biyo baya na.

Ina zaune, akan kujera na juya baya. Kamshin turare najiwo, kamar na Ya Haidar, sharewa nayi dan nasan baya wajen.

Ido na kawai naji an rufe, ai kam na tsorata sosai. Amman sai na fara yin addu'a a cikin raina, dariya ya saki. Yana buden idona, yana cewa ashe jaruma ce, gaskiya ne.




*INDABAWA*
08062882472
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY




BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*






🌐HAJOWπŸ“πŸŒ

πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§ HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾



Page *30*




Dedicated to *Maman Nur.* Allah bar kauna. Ina son ki irin da yawan nan.






"Kai Ya Haidar wallahi ka tsorata ni." Na fada ina juyowa gareshi.


Sanye yake da ruwan omon jallabiya, tayi kyay sosai sai kace balaraben. Sai tashin kamshi yake.

Kasa dauke ido na, nayi akan shi. Kamar yadda shi ma ya tsare ni da idanun sa.

Ido na na kawar, tuna abinda ya faru dazu da safe, kujera ya jawo ya zauna, sannan ya zaro wayar sa iphone 7.

"Muyi hoto, tinda kin gudo ba muyi ba."
Kai na na dukar amman a haka ya dinga daukar mu hoto.

"Kinga wani hoto," ya fada yana nuna mata jikin wayar.
Dago kan ta tayi sai gasken flash take yi.

Zaman yan kurame mukayi a wajen wanda har akatashi muna wajen, ya zuba min ido, ni kuma kaina a kasa.

Wayata na hannunsa, hauwa ta kira.
"Hafsat fito mu tafi kows ya watse fa."
"Kar ki damu muna tare zan kawo ta gida, kinji."

"Toh Ya Haidar sai kun karaso."

Mikewa yayi, ya kamo hannuna, nai saurin janyewa, kallona yayi.
"Ti tashi mu tafi."

A hankali na mike na fara tafiya yana gefena, har muka fito, ba kowa a wajen, motar sa muka shiga.

A hankali ya dinga driving din. Agogon hannuna na duba sai karfe 11:25.

"Ya Haidar dare fa yayi."
"Shine me to. Ni wallahi bana son na daina kallon ki. /na fison najiki a kusa dani."

Shiru tayi, sai ga kiran wayata nan. Faiza ce, shi ya amsa ya daga,

""Faiza gamu nan a hanya."
"To Allah kawo ku lpy."

"Ameen."


"Baby nah kawayen ki na son ki. Kinji dadin ki wallahi."
Shiru tayi masa.

Sai sha biyu saura, muka isa yana dire ni na fice,
"Haba Baby nah. Saurin fa."
"Dare yayi ne."

"To amshi wayar ki sai da safe ko?"
"Allah tashe mu lafiya." Ta amaa tayi cikin gida.


Faiza tace, "har kun iso."
"Eh," kawai dan tasan gulma take ji da ita. Muyi wannan uwar dadewa amman wai har mun dawo.


Dakin bacci ta shiga inda Hauwa take,
"Kun dawo kenan."
"Eh."

Kayan jikin ta ta cire ta shige dan tayi wanka, ruwa ta sakarwa kan ta. Ta wanke kwalliyar ta dauro alwala.

Kayan bacci ta saka tayi kwanciyar ta,

Faiza, ta kalli Hauwa ta kanne mata ido daya, suka saka dariya.

Tana jin su tai musu banza.


Washe gari akai yini. Momy, wata atamfa mukasa munyi kyau kamar yadda Amarya ma tasha kyau, kamar ka dauka ka gudu.

Anyi biki lpy an tashi lpy, sai ran lahafi mukai dinner, dinner da nace bazan je ba. Saboda nasan Ya Haidar zai je. Ni kam duk abinda zan guje masa shi nake nema.

Sai da su Momy suka saka baki sannan na fara shiri, cikin ruwan madarar material sai head ja, fashion da takalmi da jaka duk ja.

Amarya kuma ta saka maroon da ruwan madarar head. Tayi kyau sosai.


Sai da kowa ya tafi sannan Ya Kamal suka zo daukar Amarya.

Ya Haidar ne mai tukin, sai ya kamal dake gefen sa.

Fitowar Faiza yasa Ya Kamak fitowa ya koma gidan tare da amaryar sa.

Dayar motar kuma Ya Nura ne da Hauwa. Sai Khadija, Bishira da wata kawar su a baya.

Dayar motar kuma su yan biyu ne da Ya Muhseen sai abokin sa.

Juyawa nayi zan koma cikin gida. Da gudu Faiza ta fito.

"Ina kuma zaki?"
"Gani nayi ba mota."

Kallo na ta tsaya
"Bangane ba mota ba. kamar ya, wannan kuma da muke ciki fa."
"Bana ga ta amare bace."

"Hafsat kar ki batan rai mana a ranar aure na. In ke nayiwa haka zaki ji dadi." Ta fada tana sakin ta. Juyawa tayi ta nufi motar.

Juyowa Hafsat tayi., tace,
"Sis ba haka nake nufi ba, ki fahimceni."
"Ba wata fahimta." Ta fada tana shigewa cikin motar.

Wannan yasa Hafsat ta bude gidan gaba ta shiga.

Tana shiga wani sanyu da kamshin dadi ne ya doki hancin ta. Wanda yasa ta sakin ajiyar zuciya tare da lumshe ido.

"Ina yini Ya Haidar." Ta fada tana wasa da yatsun ta.

Bai amsa ba sai kallon ta da ya tsaya yi. Dan ba karamin kyau tayi masa ba.

Duk da ba wata kwalliya akai mata ba. Jagira ce kadai sai maroon din jan baki da ya amshi laben ta. Sau kwalli da ya karaea idanun ta girma da kyau.



*INDABAWA*

FOR COMMENT AND CORRECTION
08062882472
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY




BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*






?? *HAJOW* ????

??‍??‍????‍??‍????‍??‍?? *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* ✍??✍??✍??




Page *32*






Ya Haidar kuwa ya Kamal yace ya dan bani lokaci nayi tunani kar ya kirani ya dan janye jikin sa.

Waya dai baya kirana amman kullum text zai yi min safe, rana da dare.



Zaune nake sanye da jar riga da bakin siket dogo, kai na da na gyara. Ba dankali. Ina daki duk kewar hirar da muka sabayi da Ya Haidar ta isheni, ina son kira bana son wani abu ya biyo baya. danayi dailling zan kashe tin kafin ta shiga.

Sallamar sa najiyo daga tsakar gida ba kowa a gidan sai ni. Ni na amsa.

Babban falo ya shiga hijab dina na sanya nayi can falo.

Zaune yake sanye da bakin wando da jar riga mai dogon hannu sai waya dako hannun sa.

Da sallama na shiga, ya amsa yana bina da kallo.

Sosai na rikita shi dan kallo ya dinga bina dashi sai kace bai san ni ba.

Durkusawa nayi. Nace,
"Ina yini?"
"Lafiya lou Baby, Ya gidan."

"Gida lafiya."
"Ummu fa?"

"Ta fita."
"Haba dai kuma wajen ta nazo."

Kasan zuciyar sa kuwa cewa yake wajen ta yazo kuma ya ganta yaji dadi.


"Bari naje anjima na dawo."
"Bari na kawo maka lemo."

"A'ah barshi kawai."
"Dan Allah!" Na fada murya a narke kamar zanyi kuka,

"To shikenan."
Da sauri na fice. Dan bana son ya tafi nafison nai ta kallon sa.

Sosai yake jin ta har cikin ransa. Komai nata burgeshi yake yi. Ji yake kamar ya kamota ya tusa ta cikin jikin sa.


Lemon kankana ta kawo masa da yaji hadin dabino da madara. Sai fried rice da soyayyan nama kaji sai hadin kabeji da kwai.

Sosai yaci abincin. Ita dai tana zaune sai satar kallon sa take.

Bai bar gidan ba sai wajen isha'i dan har sai da Ummu ta dawi sukai hira.

Duk rashin son hayaniyar Hafsat zama tayi a wajen dan bata son ta daina ganin sa da jin muryar sa mai dadi.


Da zai tafi Ummu tace, Hafsat ta rakashi. Daga ita har Ya Haidar wani dadi suka ji.

Har bakin gate ta rakashi. Har ta juyo yace,
"Hafsat!"

Cak ta tsaya. Bata juyo ba. Gabanta yasha. Ya zuva mata narkakun idanun sa da son ta ya cika su.

"Hafsat na kasa komawa bakin aikina. Saboda ke. Dady sai waya yake amman na kasa barin ki.bazan taba komawa ba sai kin aminta dani."

Ya durkusa kan gwiwo yin sa. Ya kamo hannu na.
"Hafsat dan Allah ki fito da kome ke acikin zuciyar ki. in har baki sona to zan hakura. Amman nasan rayuwata ta gama amfani ne in babu ke."


Waige waige ta fara yi. Dan bata son wani yazo ya gansu a haka.

"Dan Allah Ya Haidar ka tashi kar wani ya ganka a haka."
Ta fada tana kokarin daga shi.

"A'ah ki bar ni haka shine dai dai dani agareki."
"Dan Allah nace."
Ta fada murya na rawa.

"Nifa A'ah sai kin amince." Ya fada yana kashe mata ido daya.


Shiri tayi.
"Kin amince?" ya fada yana kara kallon ta.

Kai ta daga ta kwace hannun ta tayi cikin gida da gudu.
murmushi ya tsaya ya yi ya bita da kallo.

Mota ya shige yayi gida tin daga lokacin Ya Haidar zai je gidan amman kuma sai yar buya tsakanin sa da Hafsat.

Dan wata kunyar sa take ji. Dan ko da ya sameta a falo in tai masa sannu da zuwa suka gaisa zata gudu. Ba tare da Ummu ta fahimta ba.

Kallon su kawai Ummu keyi amman ta fahimce su.

Sai dai in a waya ne tayi shiru ta kasa bashi reply har gara in a chatting ne suna dan hira da ya fara maganar soyayya na yadda yake son ta da makamantan su zata rufe fuska sai kace yana ganinta.

Daga nan tace bacci take ji. Sosai kunyar ta ke burgeshi. Dan ance kunya ado ce. To shi ya yadda dan yaga yadda take kara qawata masa Hafsat din.




Amarya Faiza da ango kamal soyayya suke sha kowa na kula da dan uwansa. Kullum zasuyi waya.

Haka ma Hauwa, dan basu koma ba. Yanzu naci takewa Hafsat kan taje amman taki. Wannan yasa tai zuciya ko wayar ta ta daina dagawa.

Ummu na fadawa. Tace ai bata kyau taba.

Dole tasa na shirya dan naje.

Cikin atamfa ruwan omo da yellow na shirya na yi ado da dan kunne yellow haka mayafi sai bakin takalmi da jaka.

Fuskata ba kwalliya sai dai nayi kyau daga hoda sai kwalli da man lebe.

Ummu nai wa sallama na fita. A bakin gate na hadu dashi zai shiga cikin gidan.

Sanye yake da shadda ruwan sararin samaniya sai bakin takalmi.
Kai na na sunkuyar. Waje na ya karaso





*INDABAWA*

For comment and correction
08062882472
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY




BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*






?? *HAJOW* ????

??‍??‍????‍??‍????‍??‍?? *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* ✍??✍??✍??





Page *31*






Kanta ta dauke ta dan juya tace,
"Ango ina yini. Ya hidima?"
"Ba ruwana da ke tinda kika bataea amaryata rai."

"Ni me nayi mata?"
shiru yayi mata ya juya gefen Faiza, su a magaba kasa kasa.

Juyowa tayi ta cigaba da kallon titi, ji tayi an kama hannun ta, wani sanyi ne ya ratsatta tare da jin tsigar jikin ta na tashi.

Kokarin cire hannun take amman ya rikeem gam, ba komai yake son kalla ba sai idanun ta masu kyau da girma. Amman sam taki dago kanta kamar tasan abinda yake son gani.

Daga hannun yayi. Yayi wajen bakin sa dashi. Da sauri ta daga kai ta kalle shi. Caraf idanun su ya hade ya shiga cikin na juna.

Gefeb titi yayi da motar. Ido ya lumshe dan ji yayi kamar an dada masa sonta.

Zame hannun ta tayi. Wata tafiya ya ringayi kamar bai son tukin. Har su Hauwa suka je bamu karasa ba.

Ko da muka isa ban san mun isa ba. Na tafi duniyar tunani,dan ashe har su Faiza sun sauka.

Jin rufe mitar ya dawi dani hayyaci na da sauri ya rufe motar. Janyi ni yayi, nayi saurin janye jikina.

"Dan Allah Hafsat ki bani dama zan wanke miki damuwar ki, ni mai son kine da kaunar ki."
Kwankwasa motar akai. Shi ya ja hankalin mu. Glass din yayi kasa dashi.

Ya Nura ne, dariya yayi. Yace,
"Kasan fa jiran ku ango da amarya suke "
"Affuwan kaga wacce ta tsatar damu nan."

Ya fada yana kallon ta, ita duk kunya ta kamata.
"To dai naji ku fito mu shiga." Ya fada yana juyawa.

Kallan ta yayi, yace,
"Muje ko kar kanina ya gaji da jiran yayansa."

Rafar yan dari biyar biyar ba bani guda biyu.
"Kiyiwa Amarya da Ango liki." Ya fada yana fita. Shi ya buden na fito.

Gefen Hauwa nayi. Mu muka shiga da amarya da ango. Anyi ruwan kudi dan ya haidar kamar bai san zafin kudin ba.

Haka ya dinga liku dasu Ya Nura.

Biki yayi kyau daga nan amarya aka mika gidan ta dake rijiyar zaki. Basu da nisa da Hauwa.

Gidan su Faiza muka kwana.

Amarya da Ango bayan anci ansha sukai sallah dan godiya ga Allah da ya nuna masu wannan ranar.
Addu'a sisai Ya Kamal yayi musu na zaman lafiya da zuri'a daiyiba. Daga nan yai mata tambayoyi game da adfini komai ta bashi amsa dai dai gwargwado.
ranar ansha amarci. Sosai suka raya daren su mai albarka.


Washe gari muka hada kayan mu dan tafiya. Amman Momy tace sai gove. Dan yanzu gidan amarya za'a kai mu.

Ni dai raina a bace muka tafi gidan. Dan su Yan biyu a safiyar suka koma dan suna da exam din safe. Sun tafi muna kewar junan mu.

Faiza muka tadda tayi tsaf da ita sai tashin kamshi take ko ina a gyarree.

Hauwa ita taje ta kara jan hankalin Faiza dan ni duk bana cikin tunani na. ina can wata duniya.

Tunani ne tin na ranar daurin aure ke damun kaina. Na rasa ya zanyi ina son naki amince masa amman zuciyata tana sin shi.
Na rasa yadda zanyi lura dani da sukai yasa kuma sukayo Kaina.

Hauwa tace, "Haba ukuti, kinsan fa kina da lalura amman kike neman sawa kan kidamuear da zata tayar miki da ciwon ki ko.kinsan an hanaki tunani."

Tayi shiru ta jawi hannun ta.
" Ya Haidar namiji ne da kowacce yarinya zara so ya zamo mijin ta."
"Nima dai haka na gani ban ga aibun sa ba. Ta komai yayu kivar wannan damuwar da tinani kiyi istihara yafi."

"Hmmm! ba komai wallahi tsoro nake ji na halin mazan nan. Amman zuciyata na yabawa da hankaki da nutsuwar shi da ilimi."

Tayi shiru idanun ta ya kawo ruwa.
"Kuna tayani da addua Allah ya zaban mafi alheri. Ban son na amince dashi abin yazo bai yi ba ya bata yan uwar takan mu, bans an da wane ido zan kalle shi ba ko Mama Fati."

"Kina tunanin mau kyau ki daina kawo wannan tunanin insha Allah zamu na miki addua ba abinda zai faru amsai alkhairi." Faiza ta fada tana kama dayan hannun nata.

"Kar ki damu indai addua ce kullun cikin yin ta muke sai dai fatan Allah ya amsa."
"Ameen Nagode."

"Ba komai kan mu mukaiwa." Daga haka suka dau hira da yan gyare gyare. Sai tamma muka tafi gida.

Hauwa a ranar Ya Nura yazo ya dauke ta. Sukati gidan su sai ya rage sai ni kadai.

Washe gari Mami tace sam sai na gama hutawa zan koma gida. Ba yadda zan yi haka na hakuri.

Ba abinda Momy take bari na nayi daga kwanciya sai kallo da chat.

Sai da nayi sati ta barni na koma gida. Da kanta ta kaini da uban kaya. Sai gidiya takewa *Ummu nah*



*INDABAWA*

For comment and correction
08062882472
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY




BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*






?? *HAJOW* ????

??‍??‍????‍??‍????‍??‍?? *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* ✍??✍??✍??





Page *33*




Dis page is ur *RUKKY YAKASAI* LOVE U BAE



"Wow kinga yadda kika yi kyau kuwa."

Kai na kuma dukar wa nace,
"Ina yini?"
"Lafiya. Ina zuwa?"

"Gidan Hauwa,"
"Amman ko ki kira na kai ki."

"Ayya wai dan kar naje ko kana wani aikin ne."
"Ba wani aiki ai ko da akwai akace sawon giwa ya danne na rakumi."

Ni dai shiru nayi.
"To taho ki shiga naje na gaida Ummu. Inzo mu tafi."

Shi ya buden motar sannan ya kunnan AC, duk abin nan kai a na kasa.

Cikin gida ya shige. Sai da ya dau minti wajen 10 sannan ya fito.

"Kiyi hakuri, kina ta jira ko?"
"A'ah."

Daga haka muka dau hanya.
Son kallon fuska ta yake, ni kuma nayi kasa da kai.

Hannuna ya kama. nayi saurin janyewa. Murmushi yayi.
"Hafsat!"
"Na'am."

"Dan Allah dago na kalle ki ki naji sanyi cikin zuciyata."
Nima son kallon san nake, amman kuma ina jin nauyinsa.

Kai na dago na kalleshi idon mu ya hadu na sakan uku nayi saurin janye nawa daga cikin nashi.

Dariya yayi yace,
"Allah yasa kar kunya ta hana min mata kula dani."

"Ya Salam!" Na fada cikin zuciya ta. Dan yana kara sani cikin kunyar sa indai ya kawon maganar aure.

"Eh! Mana, dan kinsan ni mutum ne me son kulawa da soyayya ina fatan zaki kula dani sannan ki bani dukkan soyayyar ki."
"Ya Haidar! Dan Allah kabar maganar nan." Ta fada murya a shawgabe.

"Akan me?"
"Ni dai kunya nake ji."

Murmushi yayi.
"Kar ki damu kunyar ta dan lokaci ce zata tafi. Wuyar ta kizo hannu ne kawai."
"Uhm uhmm"
ta fada kamar zatai kuka. Tana bubbuga kafa a kasa.

"A'ah yi hakuri na daina." Ya fada yana dariya.

"Amman ki sani ina son ki ba kuma zan daina son ki ba. Zan shayar dake soyayyar da ba wanda aka taba shayar da irin ta. Zan gatataki in kula dake in cire miki dukkan damuwar ki. Insha Allah."

Wani sanyi naji yana ratsani har cikin jikina. Hannuna ya kuma kamowa yana murzawa a hankali kasa hanashi nayi duk da baso nake ba.

Har muka isa hannun na na rike da hannun sa. Sai hira yake jana da ita.

Shi ya zagayo ya buden motar na fito.

Yana gaba ina bin sa abaya. Shi ya bubbuga kofar gdn.

Muryar Hauwa naji tana cewa.
"Waye?"
"Nine." Kawai yace.

Ita tazo ta bude, daya ke ina bayan sa bata ganni ba.
"Oyoyo! Ya Haidar yau kaine a gidan. Bismillah!" Ta fada tana bashi hanya.

Shigar shi ita ta bata damar ganina, da gudu ta zo ta rumgume ni.

"Wayyo Ya Nura!" Ta kwada masa kira.

"Amman fa naji dadi wallahi sis."
"Ai shiyasa nace zuwan bazata zan miki tin da fushi ake dani.

"Lafiya honey." Ya fada yana fitowa daga daki da sauri.

Turus yayi ya tsaya kallon su. Kai ya kada yayi wajen ya Haidar suka gaisa.
"Kece yau yan gidan ne suka zo."
"Wallahi kai dai bari."

Hannuna ta jawo mukai ciki. Kallo suka bimu dashi. Sai da muka zauna sannan nace,
"Ina yini?"
"Ina ai mu fushi muke."

"Kai da wa?" Hauwa ta fada tana shigewa jikina.

Ido ya zaro.
"Baby kasa zaki zuba min a ido. Ina taya ki fushi."

Dariya nayi nace,
"Wa yace ana shiga tsakanin mu."
"Oh haka ne fa. Zan kuma ai."

Dukkan su kai dariya. sanna suka gaisa.

Fita sukai mu kuma muka hau hira kamar mun dade bamu hadu ba. Haka muke jin kewar junan mu.

Sai wajen daya muka shiga kitchen. Dambun cus cus mukai dayaji kayan lambu su kabeji da koran wake da karas.

Yayi kyau yai washar washar dashi, sai fafesun kifi da jallop din taliya. Da itama taji kayan lambi da nama.

Lemon kankana muka hada muka saka a firiji sannan mukai daki mukai sallah.

Sai biyu da rabi suka dawo tare muka ci abinci sai santi suke xubawa.

Sai da suka koshi sannan sukai gidan Ya Kamal.

Karfe uku da kwata sai gasu har da Faiza nan.

Fita sukai suka bar mu. Mu kadai. kitchen muka shiga dan daura abincin dare.

Sai da muka gama muka zauna hira. Muhawara muka dauko. Dan mun saba indai ana tare sai munyi abinda zamu qaru da juna.

Hafsat, tace,
"Me kuke tunanin na kawo mutuwar aure."


Shiru sukai kowa ya tafi tunani. Sai can Faiza tace.....




*INDABAWA*


FOR COMMENT AND CORRECTION
08062882472
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY




BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*






?? *HAJOW* ????

??‍??‍????‍??‍????‍??‍?? *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* ✍??✍??✍??




Page *34*



Dis page is urs *Hindatu Khaleet Shattima* *Ashraf* love u sisto



Hafsat ce tace,
"Shin me kuke tunanin yana kawo mutuwar aure?"

shiru sukai kowa ya tafi nazari.

Sai can Faiza tace,
"Rashi ilinin zaman takewar auren. Da wasu basu dashi ga rashin ilimi, kinga kuwa ina za'a iya zaman aure ba tare da an san wani abu dan gane dashi ba. Ko in ba ilimi ai da matsala. Ya kamata kafin aure ana sanin ilimin auren."

Hauwa, tace,
"Ga al'adu da ake mai dasu wajibi.
Da bidi'a dan wasu wannan aladun da bidi'ar da zasu ta janyowa na kara rushe albarkan auren.
Ace sai anyi kaza da kaxa. Kuma yayi azo ai auren ya samu mace ba tarbiyya dole bakin cikin abinda ya kashe yana damun sa. Dama ya samu riba da da sauki."

Hafsat tace, "Gaskiya ga rashin ilimi tarbiyya. Bayan haka rashin bincike kafin aure. Wannan babbar matsala ce,
wani sai anyi aure zakiga matar ba ta da halin kirki ko ba tarbiya haka nan ko mijin ne bai dashi.
Ko rashi aikin yi da dai munann halaiya."


"Wani lokacin matsalar iyayen matar in masu son abin duniya ne, suyi ta sa yar roko da makamantan su.
haka in kuma iyayen mijin basa son ta to komai tayi ba dai dai tayi ba.

Wani abun ma wai sai ki samu mace bata iya tsafta da kwalliya ba.
Rashin iya magana kwanciyar aure, girki, duk wadan nan kan jawo mutuwar aure bare jahillici wato rashin ilumi."

"Haka ne Hafsat " Faiza ta fada
"Allah barmu da mazajen mu dai." Hauwa ta fada

"Ameen ya Allah!" Hafsat ta fada tana mikewa. Dan yin alwala.




Sai bayan magariba suka shigo gidan. Lokacin Hafsat har ta shirya. Dan ta kagu ta ganta a gida.

Sai da suka ci hadin kazar da sukayi wacce taji dankali da kayan dan dano, sai lemon kwakwa da yaji madara tai sanyi.

Bayan sun gama sai ma suka zauna hira. Mune har isha'i bayan sunje sun dawo. Naga yana kara zama.

"Ya Haidar!" Na fada murya kamar zanyi kuka. Dan in da da kaina zan tafi da tini, na tafi tin kafin magariba.

"Na'am!" Yace kamar bai san me nake nufi ba.
"Uhmm! Daman naceka kaini gida sai ka dawo kuyi hirar."

Hauwa ce, tayi dariya tace,
"Ki dai ce kina son kuje kuyi hira."
Faiza tace,
"Lallai kam!" Duka na kai mata.

"In ma hakan ne kunga laifin ta. Ku da zaku kwana da mazajen ku. Ita kam nan da anjima zamu rabu."

Dariya Sukai
"Ya Haidar na Hafsat"Ya Kamal ya fada yana dariya
"Ya ran ka."

"Fari taas wallahi!"
"Da dai yafi."

Ya fada yana kallon Hafsat
"Tashi mu tafi kinji." Ya fada yana mikewa.

Nima mikewa nayi, nabi bayan sa. Su Hauwa suka biyo bayan mu.

Sai da ya buden mota sannan ya rufe ya koma bangaren sa ya zauna.

Hauwa ce, ta zuron wata leda babba,
"Ki gaida Ummu da Khadija da Khairat."
"To na gode sai da safe."

"Ki gaisa Ummu da Khairat. Sai nazoo." Inji Faiza.
"Nagode sai kinzo."

Su Ya Kamal suna gefen Ya Haidar bayan sunyi sallama suka duka suka leko.
"To Antyn mu sai da safe a gaida Ummu."
Hararar su nayi nace, "Zataji nagode."

Muka tafi muna dagawa juna hannu.

Su Faiza ma basu koma ba sukai gidan su.

Tafiya muke ba mai cewa komai a cikin mu.

Hannuna Ya Haidar ya kamo, yana murzawa.
"Hafsat" ya kira sunana a hankali kamar me rada.


"Uhmm!"
"Ki kalle ni mana wai kunya ta kike jine."

Kai kadai na kada masa alamar A'ah.

"To indai ba kunya kike ji ba dago kanki, ki kallen."
"Ni bazan iya ba."

"Haba Baby ashe dai kunyar kike ji."
"A'ah!"

"To dago na gani."
Kai na, na dago a hankali na kalleahi.

Idona cikin nashi, wata kara naji. Ta alamar taka burki. Bansan lokacin da nabar wajen zamana ba. Na koma kan kafar sa na kudun dune a jikin sa.




*INDABAWA*
08062882472
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY




BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*






?? *HAJOW* ????

??‍??‍????‍??‍????‍??‍?? *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* ✍??✍??✍??






Page *35*



Dis page is ur *Ummiterh.*
Tnx for ur love dear





Bansan lokacin da nabar wajen zamana ba. Na kuma kan kafar sa. Kudun dunewa nayi a jikin sa. Munfi minti biyar a haka kowa na addua cikin ransa.

Ya Haidar kuwa wani abu yaji yana shigar sa, ga tsigar jikin sa sai tashi take. Sai kokarin cire ta daga jikin sa yake, amman hafsat sai kara matse

Please Login or Register in order to submit comment