Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi tace, "Ya Kamal wai wane dadi ne da soyayyar nan haka ne,"
"In kin fara kyaji,"
Baki Hafsat ta tabe, tace, "in zaku ki taso, in kuma soyayyar zaki tsaya sha to asha lpy, Hauwa tashi mu tafi," ta fada tana mai kallon Hauwan.

Hauwa ce ta mike, tana rataya jakar ta, Hafsat ta dubi Ya Haidar da tin da ta fito idon sa ke akan ta, tace,
"Ya Haidar mu zamu fita, sai mun dawo,"
Mikewa yayi yana cewa, "Muje in taka miki zuwa bakin gate," muka fita na shiga dakin Ummu nai mata sallamar zamu fita tai mana a dawo lpy, a gate kuwa Ya Haidar ne da Hauwa ke tsaye, sai ga Ya Kamal da Faiza sun fito,
harararta nayi, nace, "wallahi Faiza baki da kunya, tinda mu baki ji kunyar mu ba ai kya ji ta Ya Haudar ko?"
Ya Haidar ta kalla ta sunkuyar dakai, Hauwa, tace, "ke Hafsy baki san so kan makantar ba, yasa ba wanda kake gani sai masoyin ka, to ina jin abinda ya faru da ita kenan, ba wanda take gani Sai yayan mu ko?," ta fada tana dafa kafadar Faizan.
Ya kamal yace, "kai kar ky takuraea Faiza ta, mene dan ta kuka da masoyin ta,

Ya Haidar ne yace, "ai laifin sane bana ta ba,"
duk sukai dariya.

"Uhmm ni dan Allah kuzo mu tafi, Ya Kamal anan din ma sai iun tsayar damu da surutun,"
"Hasfat wallahi kibi a hankali, kar in kin fara kina sin ganin jarumin da ya sace zuciyar ki, kizo kina min kukan na nemo miki shi,"
"Ka fara ko?" Ta fada tare dayin gaba,
Ya Haidar ne yayi murmushi, yace, "Gaskiya Kamal ka daina takurawa Hafsat da zancen wata soyayya," ya fada yana bin bayan ta.


Ya Kamal dariya ya dinga yi, "Ai Hafsat ba wacce ake goyan baya bace, gara ka barni da ita."



Tare da Ya Haidar da Hfsat sukayi titi, muna tsaye sai gasu a motar ya Kamal, yace, "to ku shigo mu tafi,"
Hararasa Hafsat tayi, sannan ta nufi motr zata bude, da sauri Ya Haidar ya karasa ya bude mata, ta shiga ya rufe mata, ya shiga gaba suka hau kan titi.



Zoo road mukaje karbar dinki daga nan ya Kamal ya kaimu goran dutse gidan su Khadija, a wajen sa muka bar kayan da muka amso.
A gidan su Khadija mukai sallahar azahar sannan muka dau hanyar gidan su Zainab, sai 3:30 muka isa saboda cunkoson hanyar, daga nan su Waseela mukayi can gwale, anan nake cewa,
"Dan Allah muyo gida na gaji,"
Faiza tace, "wallahi hafsay naga mai yi miki naki rabon da an fara zaki shagwabe kice kin gaji, dan a lokacin Hauwa ina jin tana da ciki ko da, nima kuma ina da ciki yaro ko ya tsufa,"
Hafsat tace, "wallahi sai kun dire ko me kuke dashi kun min dan kunsan bazan iya ba, sai dai a hakura da rabon,"
"Rabu da ita ai dole ma muyi miki, dan nasan halin ki, sai ki hakuta da rabon,"


Faiza tace, "Au ke zaki baro mijin ki, kiyi mata rabo, ai kam ni bazan iya ba na barwa wa kenan,"
Hafsat, ta dubeta, tace, "ah lalai Sis zata kular min da bro, sai dai kiyi a hankali, naga irin kune masu dadi miji ko, tin kan ki shiga ma,"
Hauwa dariya tayi tace, "wallahi ina son ou kawayena,"
Faiza tace, "wallahi Hafsat irin su in sun tashi salon su na soyyayya yafi na kowa,"
"Ke kika ga hakan,"


Da haka mukayo gidan mu, muna shiga ana sallahar magariba, alwala mukai mukai sallah, Khadija ta kawo mana abinci, kichen na tafi naje, na dauko cake da lemo, na dire mana.

Faiza tace, "wallahi ina ganin abinci bazan ci abinda bazai kosar dani ba,"
"To daman nace, kici ne,"
"A'ah Sis rabu da ita, dan Allah kina daurewa kina cin mai dumi a cikin ki ba kullun sanyi ba,"
"Kai Sis duk safiyya sai nasha bakin tea akam ina dumama cikina," ta fada tana kashe musu ido daya.
Hauwa cw ta bude baki rike da haba tace, "ina jin tean kadai kike sha ki biredi baza kici ba bare dan kali ko wani abun, Allah Sis ki daina,"
"kinsan akwai wata yar uwar mu da ulcer taci karfin ta sosai, wallahi aman jini ta fara, sabida taci har kayan cikin ta, daga baya mutuwa tayi, bawai nace kema zai yi haka ba ko in mutuwa zaki ba a'ah ko daya, dan da lpy da babu indai mutuwa tazo tafiya zamuyi, dan Allah kina kiyaye wa Sis, ba mutuwa ake ji ba wahalar da akesha ita akeji. dan Allah kina kiyayewa,"

"Insha Allahu Sis, kar ki damu,"
"To matso kici abincin,"

Ba musu ta matsa suka fara ci, duk da kadan Hafsat taci ta koma gefe kan cake din ta.


Ya Kamal ne yayi sallama dan ya kawo mana kayan mu, karba mukayi kowa ya dau nasa, shi ya kai hauwa da faiza gida, bayan sunyiwa Ummu sallama.





MS INDABAWA
MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY




BY MARYAM S INDABAWA
MANS





Page 18



Dedicated to you Swt Maryam Yusuf, ina son ki, ki daya daga cikin masu son littafai naki, nagode kwarai da gaske Allah biya miki bukatun ki na alheri Ameen.





Kullim sai mun fita, Momy mai gyaran jiki ta dauko daga maiduguri, Hauwa kam tace, tare za ai mana gyaran, duk da bana so dole sukai min sai an min, dan har Momy sai da tasa baki, ko banje ba sai Hauwq ko Faiza sun zo sun dauke ni.


Gyara ake musu duk kansu sai kace amare, fatar su tayi kyau sosai sai ga wani kamshi da suke tayarwa koya suka gifta ka, dan ta tsuma su da hadin turaruka masu dadi wanda suka dade da hadawa dan a cikin kasa tace, suka ajiye shi ya dade ciki sai yanzu ta dauko shi, bayan kayan gyaran mata da take dirkawa Hauwa, Faiza kam har sha takeyi, Hafsa kuwa ko dan danawq batayi dukda taga, wasu da madara ko noni ake sha, amman kalli ma basu ishe ta ba.





In suna tare kuwa dasu Hauwa, kullum cikin waya suke ita da angon ta, haka Faiza da Ya Kamal, Hafsat kuwa sai dai tayi ta buga game abinta, sai dai wani lokacin Ya Haidar ko Ya Kamal su kira waya su gaisa, tinda yanzu sun tare a gidan su Hauwa, duk yadda Hafsa taso taki zuwa, amman suka nace dan har gun Ummu sukaje suka tambayebta kuna ta amince dan dole suka hado mata kaya, dan da tace ita sai ran kamu zata je ta kwana.




***********

Ya Haidar ne zaune a dakin Ya Kamal, sanye yake da Wandon jeans da ruwan omon riga mai digon hannu, sai tashin kamshin turare yake, idon sa a lumshe, fuskar nan tayi wani kyau sai kace wanda ya shafa mata hoda, leban sa sai kyali yake ke kya ce, man lebe ya shafa, gashin kamsa sai sheki yake yayi luf daki, murmushi ne ke tashi akan fuskar sa wanda ya karawa fuskar sa kyau sosai. Karfar sa da ke mike wacce take da zara zaran yatsu yake jijigawa a hankali.



Ya Kamal ne ya shigo dakin da sallama, yaji shiru, Ya Hiadar ya duba ganin idon sa alumshe ya dauka bacci yake, to murmushin da yaga yana tashi akan fuskar sa da kafat da yake jijigawa yasa yasan ba baccin yake ba, wannan yasa ya kira sunan sa har sau uku amman shiru, hannun sa ya daura kan kafadar sa, wannan yasa ya bude shayayun idon sa wanda suke kamar mai jin bacci.


"Lpy dqi Ya Haidar, ina ta magana shiru, ko kewar Gimbiyyar ka ne ya jefa ka cikin wannan zurzurfan tunanin,"
Murmushi ya Haidar yayi sannan, yace, "uhmm kadai bari, nazo kano a dai dai da kuma sa'a, dan daga duk kanin alamu da kafar dama na shigo, dan na samu wacce nake so, nima kwanan nan zanyi aure,"

Dariya Ya Kamal yayi, yace, "Kace, har kun dai dai ta,'
"Ko daya ko magana ma ban mata ba, kasan tin ba yanzu ba nake fama da son yarinyar, duk da a lokacin in tsammanin tausayi ne dan a lokacin sai naga kamar ta min yarinya, duk da in abin ya fadan a can baya ina danne abun na kawar dashi, sai gashi yanzu abin ya tayar min sosai, gaskiya in ban sameta ba zan shiga wani hali, dan da son ta nayi wayo, ita ce irin matar da nake da bukatar nake da sha'awar aura, duk abinda nake da bukata tana dashi, na dade ina mafarki da ita sai yanzu da na daura ido akan ta na gane ashe da ita na saba mafarki, ina sonta in ban same ta ba zan shiga wani hali, zan zamo mai rai amman bazab amfanu ba,"
Ido Ya Kamal ya zaro, sannan yace, "Allah ma ya mallaka maka ita, amman yakamata ka sanar da ita dan kar kaje ko tana son wani daban,"


Murmushi Ya Kamal ya karayi, sannan yace, "ai shiyasa nace maka irin matar da nake danake son aura ce, a tsari na ban san yrinyar da ta gama soyewa da samaririka da yawa kai saboda kishina ma bana son wacce ta taba soyayya ko da saurayi dayanne balle kuma da samari da yawa, sai Allah ya bani wacce soyayyar ma bata sa a gaba ba,"
Yayi shiru yana kara fadada murmushin sa, ya kalli ya Kamal yace,
"Yarinyar tayi, irin ta ma'iaki (SAW) yace mu nemawa 'ya'yayen mu, wati yarinyar tafito daga tsatso mai kyau, wati tana da nasaba, ga hankali, nutsuwa, tarbiyya wacce nake gwadayin samu yara masu irin tata tarbiyar, ga ilimi dukka biyun, ga addini, wajen kyau ba a bar ta a baya ba, In ka ganta sai kaji duk mata ba mata bane, komai yayi dari bisa dari, ga tada....."

"Haba Ya Haidar! Wannan wacce irin yarinya ce, komai yayi, kar dai kaje da aljanna kake soyayya,"
"Wacce irin aljanna kuma, yarinyar nan in takaice maka ma jinina ce, kuma kaima haka, nasan da ka gano abinda na gano da tini ka shige tinda kungi kusa, kuma gari daya, toh sai Allah ya taimaken duk baka ga abubuwan da na gani ba, amman da nasan ka shige wajen kai dai, Allah nagode maka Allah ka mallaka min wannan yatinyar a matsayin matar aure na."

"Ameen, amman wace wannan yarinyar,"
"Kar ka damu a cikin ya'yan yan uwa ne da muka kai ziyara naga gano abata, zaka sani nan gaba kadan, dan kaine mai kular min da ita in bana nan,"

"Ya Haidar kenan, kace, xaga yan uwa da mukai ashe idon ka na kan gano matar aure ko, Allah nuna min wannan yarinyar ni kam,"
"A'ah daman ta dade a zuciyata ba yanzu na fara son ta ba, yanzu je abin ke son fin karfi na dai, yarinyar ai kasanta farin sani ma kuwa fada maka itane dai bazan ba tukkuna sai komai ya daidai ta,"

"Tog Allag yasa Alheri a ciki, Ameen,"
"Ameen kamalun Faiza," (In Ya Haidar na neman tsokar Ya Kamal, Kamalu yake ce masa,"
"Naji tinda ka hada da Faiza ai sunan yayi dadi kamar alawa, shi yasa banga tsokanr bama," ya fada yana dariya, "kuma Allah yasa Bbyn ka mai sunan tsofafi ce, Allah akanta zan rama,"

"Yaro ka makaro, sunan ta mai dadi ne dan kaji,"
"Oh Ya Haidar da Mata!"


"Kai dai bari bro, kai ne babban aboki sannan kuma yayan amarya kanin ango, duk kai daya,"
Darita sosai Ya Kamal yayi, "Wai baka jin kunya ta,"


"Mene abin jin kunya dan gidan ku, kai duk rashin kunyar da kake yi a gabana ina magana ne, sai dan na dan yabi matata,"
"Wayii my Cwt Faiza, har ka tunon da ruhina,"

Dariya Ya Haidar yayi, yace, "Au zaka fara din ko,"
"A'ah babban yaya, Dan Allah tasi.muje, na ganta ma,"


"Ni da nake son in je in gaida Ummu,"
"Ka bari in mun dawi ma biya, tana gidan su Hauwa ma,"


"To shikenan," ya fada yana mikewa, Shima Ya Kamal din mikewa yayi suka fice, jan bulo suka nufa kai tsaye kuma har cikin gate din su Hauwa, yayi parking a ma'ajiyar motoci, sannan suka fito.



Kiran Faiza ya tafiyi.

A daidai lokacin sun gama ciye ciyen su, suna zaune, Hauwa na waya da abokin Ya Nura, kiran Ya Kamal ya shigo wayar Faiza.





MS INDABAWA
MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY



BY MARYAM S INDABAWA
MANS




page 19




Da hanzari ta dauki wayar dan tayi kewar sa, wajen satin su daya basu gadu ba, Murya ta makale, tana wani yanga kamar a gaban sa take,
"Hello Cweet na, ya kike?"
"Uhmm, lpy lou yayan mu," ta fada tana satar kallon hafsat, da ta dauke kai.

"Baby kinsan me?"
"A'ah sai ka fada,"

"Gani fa a gidan su Hauwa,"
Ido ta zaro, sannan ta dan juya su, "da gaske!"

"Eh, ki fito ina jiran ki,"
"Toh ganin nan," ta fada tana mikewa, jakar Hafsat ta jawo, ta dauki hoda da man lebe ta shafa, sannanbta dauki turare ta kara fesawa, dai dai nan Hauwa ta gama wayar, tace,

"Sai ina kuma,"
"Wallahi yayan mu ne yazo," ( haka suke kiran Ya Kamal kasancewar yayan Hafsat ne, kuma saurayin Faiza, kuma su ga aladar su duk saurayin dayar su Yaya suke kira, wannan yasa shi suke ce masa yayanmu, tinda kowa a cikin sy yace, yayan sane, bana mutun daya ba.)

"Ah haba, lallai Yayan mu., ya kasa jurewa kenan,"
"Ke dai vari," ta fada tana daukar mayafin ta, "ku taso muje man,"



Hauwa ce ta mike, tana daukar mayafi, Hafsat kuwa gyara kwanciya tayi ta mike akan gado, tace, "ku gaishe shi,"

Fita sukayi, a can lambun gidan sukaje suka zauna, bayan sun gaisa ne, Ya Haidar yake cewa,
"yau yan biyu ne kenan, ina ta ukun taku,"
Hauwa tayi dariya, "kai dai bari, kasan halin Gimbiya Hafsat din ai, tana ciki taki ta fito,"

Wani sanyi yaji, ganin tana gidan, murmushi yayi yace, "au shibe taki ta fito ta gaida Yayan nata,"

hannu yasa a aljihu ya dauko wayar sa, lambar ta ya tafi kira, sai da ta kusan tsinkewa ta daga cikin santin murya tayi sallama, lumshe idanun sa yayi sannan ya amsa mata, gaisawa sukai sannan yace,

"Hafsat Shine munzo wajen ku, amman ke kika ki fitowa mu gaisa ko,"
"Lah! Ya Haidar, ai bansan tare kuke ba, kasan Ya Kamal yanzu zai cika ni da surutu,"

Haka ne, to fito kizo wajena bazan bar shi ya takura miki ba,"
"Toh," kadai tace ta mike ta dauko mayafin damoguwar rigar dake jikin ta tayo wajen lambum.


Da fara'a ta karasa wajen, kai tsaye gefen Ya Haidar tayi suka kara gaisawa, sannan ta dubi Ya Kamal, tace,
"Sannu Yayan mu, Ya kake,"
"Bazan amsa ba bayan kin fitowa kikai ki gaida mu,"

Ya Haidar ne, yace, "to ba gata ba, ai shikenan,"
Ya kalli Hafat yace, "taso mu fita wajen muga unguwar,"

Mikewa kawai tayi tayo gaba yana bayan ta, unguwar muke zagayawa a hankali, yana bani labarin inda yayi karatu da dai yadda suke rayuwa a can, a haka mukai tafiya mai yawa bamu sani ba, dan sai Napep muka hau muka dawi gida.



Su Faiza kam ana can ana ta hira, Hauwa kam waya take, sai magarba suka tafi, dan sai da sukai sallah ma sannan suka wuce.




Biki ya kayata ran laraba akayi kamu, da lecture inda Malama Marayam Sani Aliyu, tayi lecture mai shiga jiki, Alhamis mukai children day nasu Khairat, Juma'a akayi Mother even na Ummi, Asabar yinin amarya, Lahadi aka daura aure, sannan da dare mukaje dinner, sai litinin aka kai amarya.


Biki ya kayatar inda akayi komai aka gama lpy, kuma komai tare akai da Ya Kamal da Ya Haidar, inda a harkar bikin tasa suka zama abokai juna su ukun ganin Ya Kamal shi zai auri aminiyar matar sa, ga shi kuma yayan aminiyar matar san. Sun zama kamar abokan da suka san juna, bama da yahi Ya Haidar a Lagos yake da zama.


Haka nan Ni da Ya Haidar kullum muma tarebdan ko a wajen bikin muna tare, bai bari na najeko ina ni kadai, sai yayi ta kare ni, wannan yasa muka saba sosai dan shima yana biyen sai abinda nake so.





Rijiyar zaki muka kai amarya ranar littinin da dadadre, mun sha kuka kamar wanda muka rabu kenan dasu Ya Kamal suke rarrashin mu.

Wata daya zasuyi a kano, su koma lagos wajen aikin mijin ta, daga gidan amarya gidan mu, su Ya Kamal suka kai mu, dan tin da za a kai amarya muka hada kayan mu mukasa a motar sa. Tare da Faiza muka kwana.







************
Washe gari da asuba, muka tashi mukai sallah, Faiza komawa tayi kamar yadda Khadija ma ta koma baccin ta.


Duk da ciwon jikin da nake ji van fasa fita hada mana karin kumallo ba, ruwan zafi na dafa sai kwallaan dankalu da nayi na soya kwai sai farfesun kifi tarwada danayi, kamar yadda na saba daki na koma na gyara falon, Sannan naje nayi wanka na saka diguwar riga mara nauyi na wuce bangaren Baba lami muka gaisa tana min ya gajiyar biki, dan suma duk sun halatta. A nan nasha bakin tea na zauna sai 10 nayi cikin gida.



Har lokacin bacci suke yi., karatun alqur'ani na sanya sannan na mike akan doguwar kujera, idona a lumshe, wajen karfe 11 sai ga kiran amarya, na daga da sallamata, muryar ta kasa kasa. Nace,
"Amarya kin tashi lafiya ya gajiyar biki,"
"Lafita lou Sis, ya taku gajiyar,"


"Gajiya tabi jiki, ina angon,"
"Yana kitcehn,"

Ido na ware nace, "Sis kitchen ki kuma fa,"
"Ina daki man,"

"Ki ka barshi a kitchen," ta fada fuskar ta a hade,
"To Sis bashi ya jawan gajiyar ba, wallahi Sis baki san azabar abin bane, amman zakiyi ne zakiji,"



Dariya Hafsat tayi, tace, "haba jarumar mu, sannu to, Allah ya sauwake, bai dai kamata ba ki barshi da aiki, shi yana kitchen ya kamata kije ki dan taya shi,"
"Allah bazan iya ba,"



"To shikenan ki gaishe shi,"
"Zai ji, sai yaushe zaku taho ne,"

"Ina zamuje,"
"Nan man,"


"Me? Muzi nan, tabb."
"Haba Sis me kike nufi ne,"

"Sai kin kwana biyu mazo, kafin ku tafi,"
Ai tini muryar ta ta canja dan ina jin ma ta fara hawaye,
"Haba Sis kufa ba kawaye na bane, da zakuce sai nan gaba, wallahi yan uwana na dauke ku, ashe ke ba haka kika dauke ni ba, so kike kice ni kadai zan zauna bayan kinsan anjima zasu fita, in baku zo ba su waye zasu zo," ta karashe tana sheshekar kuka.

"To shikenan yi hakuri, ki daina kukan sai munzo," na fada ba har rai na ba dan ni ba inda zani. Mukai sallama akan sai munzo.



Kwanciya nayi, sai ga shigowar Ummu nan, na mike na sauka har kasa na gaida ta, ta amsa tana tambayar ya gajiyar biki, nace ta waree.


Mukai shiru, can sai ga kiran Ummin su Hauwa nan, na daga na gaidata cikin girmamawa ina mata ban gajiyar biki.
"Hasfa sai yauahe zaki zo, kuje gidan hauwan ne, ga kaya ina son ku tafi mata dashi."
"Ummi da sai nan da kwana biyu,"

"Ah haba dai Hafsat, ko Ummu ce ta hanaku zuwa,"
"A'ah wallahi,"

"To maza ku shirya kuzo kuje, ban da abin ki ai ku ba kawaye bane da zakuce sai ta kwan biyu, ku yan uwan tane dole kuje mata, kuga mai kuke so a gyara muku wanda bai muku ba, sannan ga kayan ku da na dibar muku a cikin lefen ta, dan haka ku shirya kar rana tayi, bari ma na kira Ummun taku na fada mata, haka ma Momy Faiza duk zan kira su ai an zama daya in bakuje ba waye zaije,"
"Toh Ummi,"

"Yauwah ku tashi fa, ina faizan?"
"Bacci take yi,"

"To maza jeki taso ta,"
"Toh," ta kashe wayar.


Daki na shiga, dai dai lokacin Faiza ta tashi, gefen ta na zauna, nace, "Sis kin tashi Lafiya,?"
"Lafiya lou,"
"Ya gajiya?"
"Uhmm gajiya kam akwai ta kyanta an min aure., Ya Kamak ya huce min ita wallahi,"

Tsaki Hafsat tayi, ta mike, tana cewa, "kinji Ummi wai sai munje gidan Hauwa, wai muyi maza mu shirya, ni wallahi banyi niyyar zuwa ba dan dai Ummi ce kawai,"
"To kar kije man nidai bansan irin halin ki ba wallahi, da haka kike so mu bar ta ita kadai, naga mai zuwar miki ke kam, yanzu in bamuje ba waye zaije mata,"

Kallon mamaki Hafsat take mata, sannan tace, "to ai sai ki mike ki shirya ko,"
"Ba sai kin fada ba, yanzun nan zan mike," ta fada tana tashu ta shige bandaki.

Falo nayi ina mita, Ummu tace, "lafiya?, yanzu Ummin ku tai min waya ku shirya kuje gidan hauwa sannan ku biya ku karbo sako a wajen ta,"
"Ummu wai dole ne zuwan,"


"A'ah amman dai aladace, ya kamata kuje, mu lokacin mu yan gidan mu ne ke zuwa, ko ku tace kune yan uwan nata, ai ba kwa bada mata kasa a ido ba ko.





MUJE ZUWA


INDABAWA
MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY




BY MARYAM S INDABAWA
MANS




page 21







Yau tun kan na kwanta bacci na fara jin ciwon mara kayan magunguna na duba naga babu maganin da nake sha a ciki, kwanciyya nayi, ina adduar Allah yasa ya zon da sauki.


Cikin dare kuwa ciwo ya tasar min, gashi bana son in tada Khadija da Ummu, ni kadai nayi ta fama kan asuba na gala baita dan bansan ina ina nake ba duk na fita a hayyacina.


Ummu na zaune kan abun sallah, yau sam bata ji motsin tashin mu ba, wannan yasa ta mike ta zo dakinmu.



Ko da tashigo ta ga halin da nake ciki yasa ta rude, tace, "Hafsa lafiya?"
Ganin ba na cikin hankali ne ne yasa ta kuma rudeea dan tasan marata ce tinda na fita a hayyacina haka, amai na dinga yi ina daga kwancen nan.


Ummu waya ta daukobta kira Ya Kamal daga masallaci yayo gida, Ummu da Khadija su suka gyara ni sannan Ummu ta dinga duran ruwan dumi tana gasa min mara.



Ya kamal na zuwa mukayi asibiti, muna zuwa suka amshe ni a shiga dani ana min taimakon gaggawa, ni ce har da su karin ruwa, sannan ya yi min alluarai ya ban gado. Duk da haka Ummu mara ta ta dinga gasa min dan in samu sasauci.



Ranar yini nayi ina baccin wahala, sai dare na tashi, Ummu ita ta kaini bandaki nayi wanka duk jikina ba dadi ga jiri ina gani, na fito na canja kaya, tea ta hadab wanda ko sugar bata zuba min ba, da kyar na iya sha.


Ummu sai sannu take min, bayan nagama ne sai ga sallamar su Hauwa da Ya Nura tare da Ya Kaml da Ummu suka gaisa sukai mata ya mai jiki. Sannan Ummu ta fice, gefena Hauwa tayo, tace,
"Sis kiga wahalar da kike sha amman kinki rage shan zaki ko, dan Allah ki rage,"

Toh,Kadai na iya ce mata, tace, "sannu,"

Waya naji ya Kamal nayi, sai naji yana cewa, Eh gata nan, ina ba lafita muna asibiti," yayi shiru alamar yama sauraron.me ake fada daga can bangaren.
"Eh wayar ta na gida," ya fada yana kara yin shiru,
"Ok to gata," ya mikon wayar yana cewa,
"Ya Haidar ne,"


Na amsa ina karawa a kunne na, murmushin karfin hali nayi, na amshi wayar da sallama murya ta can kasa,
"Yar gida na yajikin?"
"Da sauki,"

"Allah kara sauki, kanwata, me yake damun kine,?" kasa nayi da ido, nace,
"Ciwon ciki ne,"


"Ayyah Sannu Allah sauwake, kace na taho dubiya,"
"Ah haba dai Ya Haidar yau fa kwanan ka shida da tafiya,"


"To mene ai kanwata zan zo duba wa,"
"To ai naji sauki,"

"Da gaske,"
"Eh!"

"To shikenan Allah kara miki lafiya,"
"Ameen,"


"Kinsha dai magani ko?"
"Eh nasha,"

"To me kike so yanzu?"
"Ba komai,"

"Kin tabbata,"
"Eh,"

"To shi kenan bari na barki sai anjima princess," na kashe wayar ina ajiyewa



Sallamar Faiza muka jiyo, muka amsa ta shigo, su Ya Nura ta gaisar tayo wajen mu, ita ma dayan gefen nawa ta zauna, suka sani a tsakiya.


"Sannu Sis ya Jiki?"
"Da sauki, wai wa ya fada muku bani da lafiya ne?"


"Na kira wayar ki shiru, shine na kira Khadija ita take fada mana," murmushi nayi nace, "ai na warke,"

"Tare muke da Momy ma tana wajen Ummu ne,"
"Allah sarki kika taso ta,"


Lokacin su Ya Kamal suka fice.


"Amaryar mu ya amarci, cewar Faiza,
"Amarci muna nan muna shan sa,"


"Kice kin zama yar hannu,"
"Sosai ma,"

Dariya nayi nace, "Allah ya shirya ku."
"Ameen Sis,"

"Sis baza ki daina wahalar da kan ki ba ko,"
"Dame fa?"

"Da shan kayan Zaki man,"
"Wai kuyi tacewa shan kayan zaki to ni ciwo ne daga Allah ya daura min,"


"Ba wani nan,"
"Wallahi da gaske,"



Dariya sukayi, Faiza tace, "to ai shikenan, ko dai aure zamuyi miki ne mu hata,"
Duka na kai mata bana son iskanci fa, na fada ido na na kawo hawaye,

"Ayyah yi hakuri na daina," Faiza ta fada tana jawo ni jikin ta, tana lallashi na.

Muna zaune Hauwa tace, "ga fa

Please Login or Register in order to submit comment