Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

snack nasan kin fi kauri anan, sai dan farfesunda nayo miki,
"Nagode,"


Faiza kuma tace, "tufa, inibi da abarna na kawo miki nasan kina son kayan marmari ko,"
Hauwa tace, "ai kinsan tasan amfanin su,"
"Dan nasan amfanin su ai ba aure gareni ba,"


Faranti Hauwa ta dauko ta zuba farfeson tare da su muka ci sannan na dauki ayaba na ci guda daya,


A likacin Ummu ta shigi ita da Momy, ta duba ni tace zata gida ga Faiza nan zata kwana dani, na yi mata godiya. Ummu tace, "kinga jiki yayi kyau ma, da aminan nata suka zo,"
"Masha Allah Allah kara sauki," suka fita.

Sai ga Khairat da Khadija nan sun shigo, da gudu Khairat tayo guna. Tace, "taty ya jiki,"
"jiki Alhamdulilah,"


"Sannu Anty ya jikin," inji Khadija,
"Jiki yayi sauki,"

"Allah kara sauki,"
"Ameen," duk kan mu muka hada baki muka fada.
su Baba Lami ne suka shigo, rike da kwandon kayan abinci suka duba ni suka fita harabar asibitin.


Su Faiza suka turawa su Khadija kayan da suka kawo dan tabawa sukai suka rufe, sai giman dare Hauwa suka tafi.


Ummu taso ta kwana amman nace Khadija da Faiza ma sun isa, wannan yasa suka tafi gida Ya Kamal ya kaisu, nayi hakan ne dan Khairat ta samu kwanciyar hankali dan nasan in taga ba Ummu baza ta iya bacci ba.

Kafin nayi bacci sai da likita yayi min allura, sai da na kwana uku aka sallamoni, kuma duk tare muke da Faiza, Hauwa kullum sai tazo ta yini, Ummu tayi fadan har ta gaji dan gobe ma sai sun dawo, dan ita da Ummu zata yadda mma ai tare zamu na kwana da ita ranar da na dawo aranar nayi wankan tsarki.


Kullum sai munyi waya sau hudu sau uku da Ya Haidar, sosai muka shaku da shi, dan in bamuyi waya ba ma bana jin dadi.
Watan su Hauwa daya da aure tazo yiwa Ummu sallama, daga nan tayi gidan su Faiza dan jibi zasu tashi. Munyi da ita kan gobe zamuje.



Tin safe Faiza tazo ta azalzaleni muka tafi, kaya muka taya ta hadawa, sannan muka zauna hira kamar kar mu rabu muka taho kan cewat gobe zamu zo, dan Ya Kmal ne zai kai su airport.


A daren suka tafi dan yiwa Ummi sallama, da Abban su. Washe gari karfe biyu muka je, karfe uku muka tafi filin jirgi, sai hudu suka tashi tana kuka muna kuka dan mun dade rumgume da ita kamar kar mu rabu sai da kyar Ya Nura ya jata dan har an kira sunan su, sai rarrashin mu ake yi.



Haka muka rabubduk jikin mu a sanyaye, ai kam suna isa ta kira mu, sosai muka sha hira sai kace bamu muka sha kuka dazu ba.


Gidan ta mai kyau, falo biyu da dakin bacci guda uku kuma duk Ya Nura ya zuba mata kaya masu kyau da tsada a ciki. Zaman lafita suke kowa na kokarin farantawa dan uwansa. Sai tattalin ta yake dan yanzu Hauwa ta kara kyau ta murje kai baka ce ita bace.

Ya Nura da Ya Haidar kuwa ai sun zama abokai na kut da kut, dan kullum suna tare.


Faiza da Ya Kamal kuwa an sak rana, soyayyar su sai dada gaba take kamar sa cinye juna su.

Mijin Ummu nah kuwa sai abin da yayi gaba na kiyayyar mu dan kamar karawa ma yake.


Waji abun da yanzu ya shiga rayuwa ta shine kullum sai an turon sako safe da rana, yamma da dare, wani lokacin ma kawau sai a turo (thinking of u baby,) tunanin ki nake, abin har tsoro yake bani, dan har kama sunana yake. Wani lokacin ma ban san inda sakon suke dosa ba dan ba gane su nake ba, kuma baya taba turon sakon da hausa sai da turanci. Abinda zan san ina gane wa shine kalmar ina sonki ( I love you) ni kam soyaya bata gaba na dan admission kawai nake jira na koma karatu abuna. Duk da asibitoci da dama na nema na amman ni sam na fison ina na gama karatu na gaba daya na fara aiki.





MS INDABAWA
MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY




BY MARYAM S INDABAWA
MANS





page 22







Bayan watan ni uku




Zaune nake a daki ina sanye da dogon wando sai ves dake jikina kaina ya sha gyara nayi parking nasa da ribom kalar rigata ruwan hoda, ba kwalliya a fuskata sai kwalli da nasaka ya karawa ido na kyau da girma. Sai tashin kamshi naake, gabana faranti ne da alawa da chocolate kala kala ina sha ina masa wayar Hauwa, da muka wuce awa guda muna yi, tana bani labarin irin rayuwar da suke da mutanen da take muamala dasu, kara bata shawara nake da jan hankalin ta in naji wani abun da bai dace ba.

Anan take ce min wai ta min miji. Ni dai dariya kawi nakeyi mata bayan mun gama sako ya shigo, wanda ko ban duba ba nasan wanda ya saba turin ne, budewa nayi ga abinda yake ciki.

"Amincin Allah ya tabbata a gareki ya ma'abociyar Kyau da Nutsuwa, ina fatan kina lafiya kuma cikin farin cikin da annushuwa, in har hakan ta kasance zanfi kowa farin ciki. Na barki lafita daga masoyin ki mai kaunar ki zan iya sadaukar da farin cikina da rayuwata gaba daya gareki."






Murmushi Hafat tayi wanda bata san lokacin da ya subuce mata ba,
"wai masoyi na, Allah yasa toh, dan ina jin wani yanayi gane dashi yanzu, amman kuma basan ko waye ba, kar naje ko yaudarata kawai ya..." ina cikin Zancen zuci sai najiyo karar wayata ko dana duba sai naga Faiza ce,


Ina dagawa ta fara magana.
"Sis ya kike, ya gida, wallahi ina kewar ki kwana dayawa,"

Dariya nayi nace, "toh fah, ko gaisawa ai munyi amman kin cikani da surutu ko,"


Shagwabe murya Faiza tayi, tace,
"Ai na sani baki dauke ni yadda mu yadda muka dauke ki ba, wallahi ina maganar nayi kewar ki kina kautar da maganar,"


"Haba Ukuti! Kar kimin mumunar fahimta mana, kema kinsa matsayin ku a wajena kuma kin san ina son ku sosai, watakila ma na fiku son ku da yadda kuke sona,"

"To naji, amman me yasa bakta zuwa gida, nice kullum a tafe, yanzu rabon ki da gida wajen wata biyu da sati daya, ni kam na zo yafi sau shida,"

"Haba Ukuti! yanzu har lissafi kike gaskiya a gaishe,"
"Ba fa abin wasa bane Sis,"


"To yi hkauru Kin san fa, bana son yawan fita ne, na fison kullim na ganin a gefen Ummu na amman yi hakuri anjima zan shigo,"
"Yeee!" Ta saki wata kara a kunne wanda yasa na dauke wayar daga kunnene sai da naji ta fara magan na dawo da ita.


"Dan Allah da gaske za ki zo?"
"Insha Allahu."

"Dan Allah Sis ki kwana gobe ki rakani kasuwa,"
"A'ah ban miki wannan alkawarin ba,"

"Shikenan sai kin zo,"mukai sallama.

Karfe biyu bayan nayi sallah sannan na kara wanka na shirya cikin atamafata ruwan madara da da purple dinkin 3quarter mai zani, bakin takalmi da jaka na dauka sai purple din mayafi.


Banyi kwalliya ba daga hoda sai man lebe da kwalli sai turare da na fesa a falo na hadu da Ummu, tace,
"Har kin shirya,"
"Eh,"

"To ki gaishe min da Momyn tta sannan ga wannan ki kaiwa Faizan," na karba ina budewa kit kayan kwalliya ne a ciki, nace,
"Ai sai itan daman, an gode Ummu, ta mikob 2k "ga wannan ki hau napep."


"A'ah Ummu ina da kudi fa,"
"Karbi ki dada,"

"To nagide Allah kara budi,"
"Ameen, sai iin dawo,"

Har bakin gate dinsu aka dire ni, na shiga, tin ina bakin gate ta taho da gudu ta tareni.


Rumgume juna mukai, mukayi cikin bangaren Momy, mun dade muna hira da momy sannan muka tafi dakin Faiza wuce nan na bata aiken Ummu, ihu ta saka ta nufi Momyn su tana nuna mata, dan daman shintake so Dadyn su ya bata kudi ta siya, da ta fadawa Momy kudi sosai ta jinjinawa Ummu dan har waya tayi tana godiya, Ummu tace ai yar ta ce ita ma.


Kayan ciye ciye ta cika min gabana dasu da kayan xaki. Zakin naaha, Faiza na min tsiya.


Muna zaune sai ga kiran Ya Haidar nan muka zauna mukai ta hira, har Faiza na mamakin da wa nake hira haka dan tasan daga Ummu, Khadija, Khairat, Ya kamal sai su muke dadewa muna hira amman bayan nan babu wani sai yanzu da tagani.



Sai da muka gama ta dubeni, tace, "Sis waye wannan ya kamoki haka da wuri,"
"kamar ya, ya kamoni?"

"Eh man ya saki fara soyayya,"
"Oh ke komai soyayya toh Ya Haidar ne,"

"Ya Haida? Toh Allah yasa ayi dashi, dan gayen karshe ne wallahi. Koma yayi ga nutsuwa ga kyau ga ilimi dan Ya Kamal na bani kabarin shi wallahi yi kunyi dace da juna."
"Allah ya shirya ki Faiza, Ya Haidar ai yafi kargi na ba ma wannan ba, mu ba soyayya muke ba toh,"

"Ba wani ke dai kice ba zaki gada min ba, ni da har na farayiwa baban yayana kamu, amman tinda naga kungi jonewa da YaHaidar na hakura,"
"Kyaji dashi wallahi dai,"

Bayan sallah la'asar. Muna zaune Momy tazo wai mu tashi ta aike mu wudil, driver zai kai mu.


Nan da nan muka fice a mota sai labati Faiza ke bani, can Hauwa ta kira a fili na saka wayar muka dinga hira mu uku sai kace muna tare. Anan take kara fadawa faiza wai ta min miji. Ni dai dariya kawai nayi. Faiza ce take biye mata, wai zata fada mata amman sai bana nan a haka har muka je wudil gidan Kanwar Momy.

Sako muka kaimata inda ta rike ku sai mun kwana, tace driver ya tafi., momy ta kirabta fada mata, Momy kuma ta kira Ummu ta sanar ma tace, ai ba komai.



Yan mata Momyn wudil su biyu ne yan tagwaye kumadukkansu sa'anin mune, sosai suke dinga jana ajikin su bare ni da sukace wai ina burgesu, komai nawa yana musu kyau, kamar yadda nake kyakyawa. Ni dai sai dai nayi murmushi.

Da dare wajen 7:30 muna zaune wansu, Muhseen ya dawi daga Abuja, dayake acan yake aiki duk ranar jumma'a yake dawowa.


Da gudu suka isa gareshi har da Faiza suke tare shi da oyoyo. Ni kam ina zaune ina aikin nawa na dannan waya.



Zama yayi suma duk suka zauna, suna gaishe shi, nima na dago nace, "ina yini?"

Muryata mai dadi da sanyi yasa ya kallo inda nake, nikam har na dauke kai na.
"Lafiya," ya amsa


Fari ne dogo kyakyawa ne na karshe. Mikewa yayi dan zuwa dakin sa amman idon sa na kai na.
sai da yaje ya gaishe da Momy sa sanan ya wuce dakin sa.


Wanka yaje yayo ya dawo sanye da 3 quarter da riga, nan yasa aka kawo masa abincin sa, sai kallo na yake ni kam ban san yana yi ba da ina can chatting da Ya Haidar.


Su Gaiza da yan biyu duk sun lura da shi, Faiza ta so hakan ta faru to amman ta san halin kawar ta gashi yanzu Ya Haidar ya hau layi.



Su Yan Biyu ma suna ta murna dan su suna son Hafsa sunga kuma a alamun yayan su ya yaba.

Dagowa tayi taga idon sa akan ta.




MS INDABAWA
08062882472
MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY




BY MARYAM S INDABAWA
MANS





page 23





Duk dagowar da zanyi idonsa na kaina, wannan yasa na mike nayi dakin su yan biyu. Da ido ya bini hae na bace wa ganin sa.



Muhseen mutum ne mai sakar wa kannen sa dan in sun zauna hira ke kyace abokai ne, dan haka bayan tafiyar ta, ya dubesu, yace, "wa ce ta kawon matar aure har gida?," ya fada yana murmushi.

"Yaya Faiza ce ta kawo maka ita."
Daga haka suka cigaba da hira kuma duk akan hafsa ne.


Hafsa na shiga daki mai turo ma sakon ya turo mata kamar haka.



"Tsananin sonki da kaunar kullim ya kan hanani bacci, Hafsa yaushe zaki ban dama na bayyana a gare ki, na matau na aureki, naji ni manne a kirjin ki ina bacci ko naji sauki da radadin sonki."



Innalillahi wai waye wannan ne, anya ba dan iska na fara so ba, uhmm wai tin bamuyi aure ba yake fadan wannan maganganun.

Ban daki na shiga nayi wanka, na zauna daure dan kalin kayan da na cire dan ban iya bacci da kaya masu nauyi ba.

Ina zaune Ya Haidar ya kira hira muka fara, can sai ga Faiza da Hussaina nan, Faiza ta karaso tace,
"Sis har kinyi wanka,"
"Eh."

Hassana ta shigo rike da leda, ta mikowa Hafsat wai tsa kayan bacci karba tayi ta zabi wata riga da dogon wando. Faiza tace, "Ta so muje musha ice cream a falo,"
To nace kawai na saka hijab din yan biyu wanda yake har kasa, roba daya aka bani na fara sha cikin nutsuwa.

Mushenn kuwa sai kallon ta yake dan yana son mace, mai nutsuwa da yanga dan shi gani yake wai yanga rake ita kuwa ajinin ta ne.


Karfe goma na mike nace musu sai da safe dan su naga sai kallon wani series film suke, (king of heart).

"Tin yanzu," cewar Hassana,
"Wallahi na gaji ne gara na kwanta," na fada ina yin gaba, Faiza ce ta biyo bayana, sai da muka dan taba hira sannan muka kwanata

Ya Haidar ne ya tashen tin karfe hudu wai nayi nafila, alwala nayo na hau yin nafila sai da na iddar na dauki kurani na fa karantawa. Sai da naji ana kiran sallah sannan na tashi na tashi su Faiza, nayi raka'atanil fijir. sannan nayi sallah.

Bacci dukka suka koma nikan ina zaune ina lazimi sai da naga gari yayi sha sannan na mike na nufi kitchen masi aiki sai aiki ake masu shara wanke wanke da sauran su. A kitchen kuma ana ta fera dankali doya gyara kaza na karasa na gaidasu.

Nace, "me za'a a dafa zan girka," dankyar suka barni na hada abincun karin sai karfe takwas na gama. Alhj nasa da ban haka na yan biyu sannan na Muhseen ma haka. duk ni na hada na jere su. Na shige daki su Faiza sai bacci suke.


Wanka nayo na fito lokacin karde tara sai a lokacin suka mike shima dan sun ji motsi na ne,
"Lah Sis har kin tashi,"
faiza tace,
"Ai wannan bata koma baccin bama,"


Gaisawa mukayi suka shiga bandaki na gyara dakin sannan na zauna shiryawa, ina cikin shafa mai Faiza ta mikon wata doguwar riga baka mai adon ruwan gold duwarsu tayi kyau sosai. Ita na saka, na feshe jikina da turarn cikin jaka ta.


Ummu na kira! Na gaishe ta, sai na kira khadija. Ina kashe wayar sai ga kiran Ya Haidar nan.
"Baby kin tashi kenan,"
"Ai tinda ka tashen ban koma ba,"

"Gaskiya ne Baby na jaruma ce, ai hakan yafi,"
"Eh, ina kwana,"

"Lafiya gamu a office muna ta fama,"
"Ayyah sannu,"

"Yauwah, kinco dai abinci ko,"
"Shiryawa nake, yanzu zan ci,"

"Ok zan kira ki anjima bye,"
Ya katse wayar sai da na gama gama shiryawa. Sai ga sako nan ya shigo.




"Aslm yake kyakyawar kyawawa mai kyaun hali ina fatan kin tashi lafiya, ina kewar fuskar ki hafsa, dan ma ina ragewa da kallon hotun nan ki. Ina kewar ki ina kaunar ki."


Da turanci ya turo mata sakon kamar yadda duk lokacin da zai turo mata da shi yakw turo mata. Murmushi Hafsa tayi a rai na nace, "ko waye oho," na tabe baki na ajiye wayar.

Cikin mintina kada su Faiza sun gama shirin su, falo suka nufa dukkan su har Hafsa. Daining suka nufa acan suka hango su Dady da Momy da Ya Muhseen.

Har kasa na durkisa na gaidasu suka amsa da fara'a akan fuskar su. Momy na min fadan aikin da nasha dan masi aiki sunce ni nayi girki.


Ni dai shiru nayi, ruwan tea kadai na zuba make sha. Kowa na cin abinci yana santi amman Ya Muhseen hhankalin sa na kaina, dan ya lura ba abinda na zuba. Sai da su Momy suka bar wajen sannan, yace,
"Hafsa ya naga bakya cin abincin,"
kai na sunkuyar nace, "tea kadai nake sha da safe,"

"Ah haba daure kici oo dankali ne,
" ya fada yana daukar faranti yan zuban dankali da farfesun kaza. Faiza tace, "ai wallahi haka Hafsa take da rashin cin abincu."

Hassana tace, "dan Allah ki daure kici," ni kam ban son ana hadani da Allah dan ban son musu naga akan kai na ne wannan yasa naja na fara ludawa cikina. Kadan naci nace na koshi, duk kan su mamaki suke wai har na koshi.

Dakin su Yan biyu na tafi nayi kwanciyata, can sai gasu sun shigi, wai in tashi zamu fita zaga gari. Sosai ya zaga garin damu dan har cikin KUT ya kaimu muka ga makarantar bamu dawo ba sai karfe biyu muna dawowa mukai sallah, sannan muka ci abinci.


Muka shirya dan Ya Mushenn shi zai kaimu gida. Sallama mukai wa Momy inda ta hada mana kayan kwalliya da wasu jakinkina na yan mata sannan ta bamu 5kgodiya mukai mata sannan muka fito. duk suka shige bayan mota dayake da su yan biyu za'a kaimu. Nima bayan na nufa amman Ya Muhseen har ya buden gidan gaba. Yace,
"Bismillah,"
Wannan yasa na shiga ba musu.


Mun dau hanya wayata ta fara kara Ya Haidar ne, hira muke yi sama sama mukai sallama, Ummu na kira nace mata muna hanya tai mana addua dawowa lafiya

Ina jin Faiza na waya da Ya Kamal can sai Saki ya shion ko da na duba wannan number ce dai.





MS INDABAWA
08062882472
MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY




BY MARYAM S INDABAWA
MANS



page 24





Ga abinda ke cikin sakon


"Kaunar ki takai makura cikin zuciyata dab nake da narasa rayuwa ta saboda zugin son ki. Wai yaushe mafarki na zai zamu gaske ne? Naganni a gefenki, ina miki hira na fada miki irin son da nake miki."



Uhmm nace kadai tare da lumshe ido na, "shin wanene wannan, tabbas kalaman sa na ratsa min zuciyata, Allah yasa ba cutar dani zai ba,"


Ina jin su Faiza da Ya Muhseen na ta hira, nikam ina online muna hira da Hauwa.



Hudu saura muka isa gida, sallah muka fara yi sannan aka kawo mana lemo da kayan motsa baki lemon kadai nasha.

Momy tace, driver yazo ya kaini gida, Ya Mushenn yace bari sukai ni.

Tare dasu yan biyu duk muka tafi har vmcikin babban falo na kai su, Khadija ta kawo musu lemo da ruwa. Ummu ta zauna ana ta hira da ita, na nuna mata abinda Momy su ta bani tayi ta godiya. Karfe biyar suka mike zasu tafi, har bakin mota na rakasu bayan su yan biyu sun amshi number ta.

Cikin gida na koma na wuce wajwn su Baba Lami, muka gaisa tace, kwana daya duk tayi keawat daga nan dakin mu na shige.

Wajen karfe 6:30 Hassan ta kirani wai ta sun sauka lafiya, nace, masha Allah ki gaida Momy, Faiza kuwa kirana tayi tai min ban gajiya.

Khairat da ta dawo sai murna take Taty ta dawo. Karfe 9:30 na gama duk abinda zanyi sai ga kiran Ya Haidar nan.
"Baby ya kike yasu Ummu?"
"Suna lafiya, ya mamana,"

"Suna lafiya. Ya naji muryar ki tayi kasa sosai ne."
"Uhmm wallahi bacci nake ji ne."

"Ok kiyi bacci lafiya. Sai da safe."
"Allah ya tashe mu lafiya."

"Ameen. Kar ki manta kiyi alwala da adduar bacci."
"Insha Allahu."
Na kashe wayar.

Sako ne. Ya shigo waya ta lakacin da nake kokarin mikewa dan sake yin alwala.
"Na damu dake, ina begen ki da kaunarki. Na dade cikin sonki. Ki daure ki so ni. Shin yaushe zaki aminta dani na bayyana a gareki har na zama mijin ki.
Yanzu da nake ni kadai ba abinda nake muradin ji in ba ke ba. Ins son naji ki a kirjina ina rikata da soyayyata."

Ya salam! Wai waye wannan Ya Allah ka shige cikin al'amurana. Alwala naje nayo sannann na yi addua na kwanta bacci. Na dade a kwance sannan bacci ya dauke ni da tunanin me turin sakon nan.


Da safe ma sakon ne ya kara shigiwa. Na buda.
"Aslm yake ma'abociyar kyau da nutsuwa. Gimboyyar cikin xuciyata, da fatab kin tashi lafiya. Ina fatan kuma kin tashi dani a cikin zuviyar ki."

"Uhmm lallai tabbas na tashi da kai duk da ban san ko kai waye na." Ta fada a cikin ranta.

"Bari naji ko waye wannan." Ta fada a fili. Sako ta tura masa kamara haka:-
"Dan Allah waye kai? Me kake nufi ga rayuea ta. Don me zaka boyw min kanka, nifa marainiya ce. Dan Allah ka rabu dani kar ka cutar min da rayuwa ta."

Can sai ga reply nan.
"Haba Hafsat! Kar kimin mumminar fahimta. Ni mai sonki ne na har abada wanda zai iya sadaikar da rayuwar sa akan ki, ni mai burin gina miki rayuwa ingantaciya ne. tayaya zaki tunanin zan cutar da ke.
ki aminta da soyayya ta ko na samu sauki a zuciya ta."

"Toh fah!" Ta fada a fili tana kwanciyya akan kujerar da take zaune.

"Naji, to waye kai? A ina kake? Ya sunan ka? Saboda me baka bayyana min kan ka ba, ka tsaya turon sakonni?"

Minti Uku a tsakani sai ga reply.

"Hafsa Kenan zaki san ko waye ni. Kuma zaki san daga ina nake da sunana.
Ina turo miki sakonnin ne saboda nasan halin ki. In da nazo kai tsaye zaki iya kin karbar soyayyata. Da ko magana ma ina jin ba zaki amsa bar. Bare ki dauka wayata."

Murmushi Hafsat kawai tayi ta ajiye wayar. "Lallai wannan yasanni"


Can sai ga wani sakin nan.

"Dan Allah kiban dama naji muryar ki mai samin nishadi a cikin zuciyata."

"To ba damuwa."


Kamar jiran ganin amsar ta yake sai ga kira nan.
"Assalamu alaikum."
taji Muryar sa mai taushi da dadi ga sanyi tai mata sallama. Bata san lokacin da ta rufe idon ta ba, ta saki murmushi. A hankali ta amsa da.
"Wa'aikum salam."


Ajiyar zuviya tajinya sauke, sannan ya ce,
"Hafsat dan Allah ki aminta dani, nasan zaki yi alfaharin samu na a matsayin mijin ki. Ba yaban kai ba, amman nasan zan rike ki amana."
Shiru tayi.

"Hafsat dan Allah ki daure kiyi magana kin aminta dani." Shiru ta kara yi.

"Hafsa kenan to dan Allah ki dauke kimin magana naji muryaki mai sani nutsuwa da nishadi."
"Uhmm to me zan ce."
Ta fada muryar ta a kasa kasa dan ita bata taba tsintar kan ta a irin wannan yanayin ba.

"Abinda zai sani cikin farin ciki."
"Ni fa bansan abinda zai saka ba."

"To cene kina sona."
Ido ta zaro ita sai abin ma ya bata Kunya. Ido ta rufe kamar yana gaban ta dan kunya.
"wayyo Allah kunya nake ji."

"Kunya Hafsat?"
"Eh wallahi."

Murmushi yayi, yace, "toh bari na barki sai anjima amman gaskiya kicewa da kunyar nan ta bamu waje."
"Uhmm" kadai tace.

"Na barki lafiya sahibata." Ya kashe wayar dan yasan ba abinda zatace. Murna yayi tayi na ganin da alamun nassara a alamarin nasa. Tin dagashi har kunyar sa takeji. duk inda kunya take kusa ai da alamun soyayya.

Suna gama wayar murmushi ya sauka akan fuskar ta. Duk da sosai take mamakin kanta, dan sai take jin wani sanyi na shigar ta kuma ita ta tsaya ta iya magana da wani haka. Sosai abin ke bata mamaki.

Wani barin na zuviyar ta na cewa ta aminci wani kuma na mata gargadi na soma naje a yaudare ni.


Ni nasan in masoya ne, ina dasu masu kudi, mulki, ilimi, nasaba da kyau amman banji yadda nake ji idan naga sakon wannan bawan Allah, sam yanayin da nake shiga daban ne.

Ranarvyini nayi tunanin sa duk da bansan ko sjmhi waye ba. Dan har Ya Haidar da ya kira ni. sai da ya tambayen lafiya dan duk yaji nayi sanyi sosai. Haka ma Ummu dasu Hauwa sai dai nace lafiya nake.

Amman ni kam ai duk tunani na ya tafi ga son sanin waye wannan.
Da rana ma bai fasa turon sakon ba na fatan alheri da fatan zan aminta dashi.


Daga baya na yanke shawarar fadawa Hauwa, shawara ta bani akan nayi istihara na neman zabin Allah, "kinsan annabi yace idan wani al'amari ya taso muku kuyi istihara!" Nace mata, " nima abinda na yanke zanyi kenan."

Take cewa, "Amman fa Hafsa mijin da nai miki nasan yafi wannan dake son janye miki hankali komai." Ni dai dariya kawai nayi mukai sallama

Da dare bayan nasa kayan bacci ruwan omo fa ratsin ja, alwala nayo na dau hijab, sallah nayi raka'a biyu sannan nayi addau'a istihara ta cikin hisunu muslim wacce ake yi a cikin tahiyar karshe kafin sallama.

Gado na haye, na kwanta. Kira ne ya shigo na duba ga Numbern nan ce, dagawa nayi m.

Da sallama ya tare ni, na amsa masa, inajin saukar ajiyar zuciyar sa.
"Hafsa kin yini lafiya?"
"Uhmm ina yini?"

Murmushi yayi, yace, "Eh toh, gani nan dai?
"Ya salam! Me yake damun ka?"

"Na yini cikin zulumi, ko

Please Login or Register in order to submit comment