Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta, yace zai biya, daga karshe sai dai ita ta biya.

Sannan wani abun da ke kara bata wa Hafsat rai shine, sam baya sakar musu fuska, kullum cikin hade rai, dan ko gaishe shi sukayi, a ciki ciki zai amsa musu.

Gashi indai ya kalla ya ga kudi a wajen Ummu, to sai yasan yadda yayi ya amshe mata su,


Abinda ba su sani ba shine, Abbi ba haka ya bar Ummu ba, ya kaya asiri dan ta so shi, bayan wannan kuma ya mata na duk abinda ya bukata ta bashi, ya da gama da ita gaba daya, sai yadda yayi da ita.

Dan ma Ummu da da karfin addu'a ne abin ya tsaya haka,

Abu daya ne ya kasa, wanda a yanzu ma aiki yake akai, shine na ya raba Ummu da ya'yanta, so yake ta daina musu duk abinda take musu, sannan ta daina kula dasu, daga baya ya amshe kadarorin su.


Duk abinda abu keyi yana shakar Hafsat, ba kamar Khadija ba da ya daurawa tsanar duniya.


Halin kuncin da Ummu take fama dashi akan mijin ta, yana damun Hafsat dan waani lokacin daki take shigewa taa shaa kuka, wannan abun yana taba zuciyr Hafsat, bacin rai ne ya hadu da wacce bata son magana bare kuma shiga jama'a ya kuke tunanin abun zai kasance, mutun bai da wanda zai fadawa matsalar sa, sai dai ya ajiye a zuciyar sa tana cin sa.


Wani abun ma shine sam Abbi ba yason yaga Ummu tayi wa su Hafsat Abu, ko ta siya musu, sai ya hau fadan karya.

Ko in yaji zata siyo mana kaya sai yace ta bashi kudin zai je Cotonou, zai taho mana dashi, ai kam baza mu kara jin labarin kayan ba bare kuma kudin, yayi wa Ummu haka yafi sau 3.


Sannan wai ha damar Ummu zata fita tace, muje mu rakata nan zai hau fada, ko yace sam bama za'a fitar ba.

Duk halin kunci shi yake son yaga su Hafsat a ciki. Tabbas yana sa Hafsat a halin sai dai ko a fuska baza ka gane ba sai dai abin na damun ta a cikin zuciyar ta



MS INDABAWA
MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY
10


BY MARYAM S INDABAWA


Dis page is for you Ummu Habiba A Kardam
Allah biya miki bukatun ki na alheri,

Da dukkan musulmai ma Allah biya mana bukatun mu na alheri.






Akwai lokacin da Hafsat take wa Ummu magan kan wayar hannyn ta ba bata matsala, tana son Ummu ta cika mata dubu 20, ta hada da tata ta siyar, bayan Ummu ta amince akan gobe zara bani, ban san ya akayi ba washe gari nace ta bn kudin, tace Abbi ya amsa

Ashe wajen ta yaje yana neman kudi, tace masa, Hafsat zata bawa kudin wajen ta, zata canja waya, sai dai ya bari nan da sati mai zuwa, fada ya hau yi kukwace wani abu akayi masa. Ashe da safe ne, Ya dauke kudin, Ummu ta tashi zata kawo wa Hafsat taga wayam,


Hakuri ta bani da taga bbu, sannan tayiwa wani waya a can kasuwar wayoyi ta sa ya kawon wace banyi tsammanin samun ta ba, godiya nai mata sosai.





Zafin da yayi wa zuciyar Hafsat yawa shi ya jawo mata ciwon zuciya, wanda tasha ciwo a daddafe dan ko Ummu bata fadawa ba, sai da Ummu ta lura da ita ta dauke ta sukaje asibiti, bayan likita ya duba ta ne, yake fadawa Ummu, Hafsat na fama da ciwon zuciya, fada yayiwa Ummu sosai ganin karancin shekarun Hafsat amman take dauke da wannan ciwon.
Magani ya daura Hafsat akai, sannan yace ina rage sa damuwa a rai na,



Ummu ta tausaya min dan tasan ba abinda yake damun Hafsat kamar matsalae mijin ta, nasuha ta dinga yiwa Hafsat kan ta daina barin abu a zuciyar ta, sannan tna sanar da ita damuwar ta.

Ummu har hawaye tayi na ganin halin da Hafst ke ciki, dan sai da suka je asibiti ciwon ya tasar ma hafsat sosai.


Ummu zama tayi tan tuna halin Hafsat na ko in kula, da damuwar da take shiga in taga Ummu a damuwa,
dan wani lokacin ko kuka Hafsat kasawa take saboda tsananin baci da ranta yake duk da tana son ta zubar da hawayen ko taji raguwar zafin da zuciyar ta take mata.


Dan Abbi yana kunta ta mata, dan ma ya hadu da Hafsat din ne, dan ko kallo ba isar ta yake yi ba bare, kuma in ya fara haniyar tasa, nan da nan zata hade rai, ko Ummu tai mgna zata ce, "Ummu ke ba Kya ji dadin sa sannan muma ya zo yana kuntata mana da masifa, badama muyi abu dana fada da bana fada ba yayi ta fama.


Dan ko gaisuwa Hafsat bata yiwa Abbi, in ko har ta gaisar dashi sai dai in Ummu ce tasa ta a gba taje ta gaishe dashi, to gaisuwar ma a wulakance zai amsata.

Ummu tasan lallai Mijin ta ba ya son ya'yanta, to amman ita ta rasa ya zata bullowa abin.


Sai da Hafsat ta sha jinyar wata daya sannan jikin ta y warware, kuma sai miskilancin ta ya dadu, dan ko magana da kyar take yin ta.

Haka suka cigaba da rayuwa, wanda Ummu ta rage fadawa Hafsat damuwar ta dan kada ta shiga wani halin, waccen in Abbi ya dawo Hafsat ji take kamar ta mutu.

Abbi irin mazan nan ne masu wayon tsiya, dan shi komai na Ummu sai ya bincika yasani, amman shi komai nasa kaf Kaf yake dashi, sannan ko ya samu kudi sam baya nunawa sai dai yai tacin na Ummu, shi dai gaba daya baida gaskiya dan baya taba gaya mata gaskiya akan al'amuran sa.



Kullum kuma cikin yiwa Khadija fada yake, dan yanzu yana kara jin tsoran yi min fada, dan yasan Ummu zata fitae Da kudi akaina in ciwo na ya tashi.


Shi sam so yake yaga Ummu ta daina son mu tana ganin laifin mu sannan ta daina kashe mana kudi wajen siya mana abubuwan da muke bukata.


Watan mu 5 da komawa, gidan mu na sharada, Ummu cikin ta yayi wata 9, ko da taje awo a lokacin rike ta sukayi, dan sunce jinin ta ya hau sai dai ai mata (operation) aiki kenan.


Ai ko bakin cikin da Abbi ke saka mata jinin ta ya hau, dan in ya shuda yayi gaba, inajin har mantawa yake da ita.


Dan ko kira baya mata, haka in ta kira sai ya ga damar dauka zai dauka, in kuwa ya dawo toh kudi yake nema a hannun ta, gashi Sim card dinshi sun fi guda 10 saboda rashin gaskiya, dan kullum shine a cikin rikicin kudi, sai Ummu ce zata biya masa.




Hankalin Ummu da su Hafsat yayi mummunan tashi, dan kuka suka dinga yi, itama ta tausaya wa yaran ta, dan bata sani ba ko zata fiti lpy, haka. Aka shiga da ita dakin su Hafsat sai kuka suke, Anty Fatima ce tazo tindaga lagos dan yin jinyar Ummu, ita ce ta dinga kwantar musu da hankali.


An yi mata aiki lpy inda ta haifi yar ta mace yarinyar kyakyauwa fara ga hanci,


Yan uwan Ummu duk sunxo, kowa yana mata sannu,
Kwanan Ummu 5 aka sallame su, sai ana jibi suna sannan ya dawo, Ummu ita tayi komai na suna da na Baby.


Ran suna Baby taci sunan mahaifiyar MIJIN UMMU nah, wato Hauwa, muke kiranta da Khairat.


Khairat ta tashi cikin jin dadi da gata, dan Ummu na sonta haka ma su Hasfsat da Khadija, dan Ummu da jima bata haiguba ba duk da Abbun su ya rasu dan ko lokacin da ya rasu shkarar Khadija 7,

Ba abinda Ummu bata mata, take mata, su Hafsat ne ke rainon ta duk da tana da mai raino, sai in su Hafsat basa nan.


Shekarar Khairat daya Hafsat ta kammala sakandare, ta fiti da sakamako mai kyau, tayi jamb itama tayi kyau, amman tace School of Nursing take so,


Can aka samar mata form, taje tayi jarrabawa, nan ma taci tayi gwaji komai dai ta tsalake ta fara karatu cikin sa'a.


Acaan ta hadu da kawayen ta Hauwa da Faiza...



MS INDABAWA
MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY
11



BY MARYAM S INDABAWA


Manzo Allah (SAW) yace duk wanda ya karanta qulhuwallahu Ahad kafa x10, Allah zai gina masa gida a gidan aljannah...




Khadija kuma da yake makarantar kwana take nan First Lady, sai anyi hutu take dawowa.


Abbi baya yawan zama a Kano, kullum yana Kaduna, sau yayi wata 2 ko 3 bai zo ba,


Kayan abinci kuwa sai dai Ummu ta siya, kullum tana cikin tashin hankali, na rashin kulawar Mijin ta, amman sai dai suyi ta tayatada addu'a.

Hafsat ba inda take zuwa daga makaranta sai gida, in kunga Hafsat awaje to Abbi ne ya dawo, shima gidan Ya Muktar kadai take zuwa dake bayan layin su, da matar sa Anty Bikki mai mutunci, tana son Hafsat, ko dan aikin da take tayata gashi Hafsat na burgeta. Au iowa ma Hafsat burge shi take dan a nutse taje ga hankali,

In ba can sai gidan kakanin ta. In ko an bata mata rai to, tana kebe kan ta ne daga cikin jama'a dan kar zuciya tasa tayi abinda ba daidai ba. Wani lokacin ta kanje tyi karatu ko taje wajen shakatawa ta huta, duk da akwai makranta amman haka take tafiyar ta, su Hauwa kuwa ranar basa jin dadi., haka zasu dameta da waya.




Samari masu ji daa kansu, suke bibiyar Hafsat amman kallo basa isar ta, dan ma wasu naganin kwarjinin ta suna kasa tunkarar ta. Amman duk da haka suna takura ta.


Rashin son cin abincin Hafsat shi ya jawi mata Ulcer, wacce in ta tasar mata kamar zata mutu, amman duk da haka bata iya cin abinci mai yawa, ita dai rabu da ita da kayan zaki da sanyi, dan komai sai ta hada shi da suga take sha wanda kuma in wata yayu lokacin al'adar ta take shan wuya sosai, dan wani lokacin har a asibiti take kwanciya, dan fita take daga hayyacin ta sosai,
Ko tace ta daina da ta warke xata manta da tasha wata wahala, Ummu tayi ta mata fada, sai dai ta bata hakuri.



Ummu ganin Abbu na hanata bawa su Hafsat kudi, wannan yasa ta bude musu ma'ajiyar kudi a bakin duk mai buka yaje ya cira, ita ma duk wata take zuba musu kudi. Sosai su Hafsat suka ji dadi.





***************

Yanzu haka Khadija hutu tazo shima kuma a dai dai lokacin yazo gida shine fa ya addabe su, wanda kullum cikin hayaniyar sa.



Yau Asabar, da safe bayan mun tashi nagama komai, na shige daki dan bana son na hadu da Mijin Ummu nah, wanka nayi na shirya, sannan nayi falo, ina zaune Ummu ta shigo na gaidata,


Kayan kallo na kunna, na dauko wayata.
Ummu tace "har yanzu Khadija bata tashi ba ko," "Eh," kawai tace,

Cikin dakin ta shig, tace, "Khadija wai ke bakya gajiya da bacci ne, har karfe 11 kina fama.
Khadija tace, "Ummu ramuwar baccin makaranta fa nakeyi," ta tashi. Ta diro daga kan gadon, ta fada toilet tayo wanka, ta gyara dakin.





Falo ta shigo ta sami Hafsat, tace, "Anty kin tashi ashe," kai kadai Hafsat ta kada mata,
Tace, "ina kwana," "lpy kin tashi lpy," "lpy Anty nah,"


Tea Ummu ta hado mana, sai gasashen bread da nagasa shi da kwai da kifin gwangwani, tean nasha nace na koshi, Ummu tace sai na cinye dan dole na dinga tusawa har da hawaye na.

Ummu kuwa na ta fada, wai shiyasa kullum nake a rame saboda rashin cin abinci na.

Bayan mun gama sai ga Khairat ta shigo, kai tsaye wajena tayo, tace,
"Taty ina kwana,"
Nace, "lpy lou Baby na,"

Tace, "uhnm Taty Awawa zaki ban nasha, ni bana son ta wajen Ummu taku nake so,"



Murmushi Hafsat tayi tace, "Baby na kin fiya shan zaki ko?"

Ummu tace, "ai ke kika koya mata,"

"Kai Ummu, Khadija shiga daki ki daukon jakar da na fita da ita jiya,"

Khadija ta shige dakin, ta kawo mata jakar, kwalin chocolate guda ta mikawa Khairat tace, "ai tasha gashi nan,"


Hannu biyu tasa ta amsa, tace, Taty a gode," ta fita da gudu, daya kwalin na dauko, na dauki daya na mikawa su Ummu, Ummu tace bata sha, ni da Khadija mukaa hau shan abar mu.


Ina zaune har sha biyun rana tayi zaman ya isheni, mikew nayi na dauki hijab nace, Ummu zanje gidan Ya Muktar, Ummu tace sau kin dawo ki gaidata da jiki.

Nan da na naje nakwankwasa gate tazo ta bude min, "Anty kece a gidan," ta fada tana min murmushi, nima murmushin na skr mata wanda ya kra min kyau, nace, "wallahii,"

Tayi dariya tce, "ki dai Abbi ya dawo," kallon ta nayi dan neman karin bayani tace, "Eh man sau yana nan kike fitowa, in bayana nan daga makaranta shikenan,"

Murmushi kawai nayi, Anty Bilki tace, "wai gidn cizon ki yake yi ne, in yana nan,"

Kaina na kawar gefe nace, "ni in yana gidan wallahi gidan baya min dadi sam,"
"Kina Hakuri, wataran sai labari kinji," nace, "shi muke fama yi ai,"
"Ina Khadija?"
"Kin san tana gidan su ai," na fada ina mai mikewa akan kujera. Ido na lumshe,


Murmushi Anty Bilki tayi, dan tasan dan ta rabu dani da magana ne yasa na rufe ido, badan ina jin bacci ko gajiya ba.



Kitchen ta nuf dan girki take yi, can sai ga sallamar Yaya Muktar nan shida abokin sa Murtala,


Mikewa nayi na amsa, sannan muka gaisa. Ya Muktar yace, "Anty yau kece a gidan namu,"
"Wallahi baban yaya," yace, "ya makaranta," "Alhamdulilah," na bashi amsa.

Dayan dakin na nufa nayi kwanciya ta. Sai daya da rabi na mike. Bandakin dakin na shiga nayo alwala. Na fito nayi Sallah,

Ina sallah Anty Bilki ta shigo ta zauna sai da na iddr na shafa addu'a sannn tace, "taso muci abincu," bayan ta na bi, muka wuce dakin cin abinci.


Acan na samu su Ya Muktar suna cin abinci, kujerar gefen sa na jawo na zauna,


Fried rice na duba cokali daya, sai nama da nasaka da hadin cabeji, Ya Muktar ya kalle ni, yace, "haba Anty dan wannan abincin, sai kace wanda Khairat zata ci





MS Indabawa
MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY
12





BY MARYAM S INDABAWA
MANS



Manzon Allah (SAW) yace duk wanda ya karanta suratul Kahfi, a ranar juma'a Allah zai cika masa hasken sa har zuwa wata juma'ar yana cikin haske da fariin ciki.

(Allah bamu ikon karantawa AMEEN)












Ya Muktar yace, "ai shiyasa kike kullum, bakya gaba,"

Murmusho nayi kawai, dan na saba jin haka kowa sai yace, bana kiba. Ganin zai kara magaba ne, yasa nace, "bafa kyau ana cin abinci ana magana,"
"Haka ne fa," ya fada tare dayin shiru.


To abincin ma da na zuva da kyar na cinye shi, Anty Bilki dake kallo na tace, "ke dai Anty ina jin a duniya abinci ne ba kya son cin sa, da kayan zaki ne da yanzu kin zauna kina dan kara,"

Shiri nayi dan nasan yanzu zata iya sa Ya Muktar ya sa na dada abincin.

Sai da muka gama, mukayo falo, Ya Muktar ya fita.

Robar Ice cream, Anty Bilko ta kawon, tace, "gafa abin,"

Na dago ina Murmush, nace, "Kai! Anty sai da na cika ciki na, amman anjima zan sha,"


"Anty dan Allah taimakan da Cingam mana, in rage ciki na,"

Daki tayi tana fadan sai kace wani abun kirki naci da zan rage cikin.

Kwallin orbit ta mikon, na karba na dauki daya, ci nake cikin yanga, dan ba kowa ne zai san ma ina tauna ba. Dan a duniya na tsani naga ana tauna ana Kas-Kas din nan har ciwon kai yake sani. Shiyasa ni ban fiya cin Cingam na duk da ina so, to ban son naje nayi ban sani ba.

(Yan Uwa dan Allah musan yadda zamu na taunar cingam, wani bai son kararsa, sannan duk wacce aka ganta akan titi tana tauna to yawanci daukar yan tasha ake musu, in dole sai anci, to aci a gida, amma wallahi.maza da yawa basa son ganin ana tauna akan hanya ko kuma ana yin kara dashi. In dan kamshin baki kike so to kiyi amfani da mouth fresh, ko alawa kina tsosa ba wanda ya sani, Allah mu gyara wallahi ba girman mu bane. In dabi'ar wani ce yayi hkri ban fada dan na bata masa ba sai da gyara.)



Anty Bilki ce ta kallen cikin sha'awa, tace, "wallahi Anty kina burge ni, komai naki a tsare, sannan cikin yanga kike yi,"

"Kai Anty ni ina wata yanga da nake yi,"

"Allah komai naki tsav ga tsafta ga iya daukar wanka duk da kwalliya bata dame ki ba, ga bakya son surutu bare wani ya kawo miki gulmar wani, komai naki na birgeni, kalli cin cingam din ma kamar bakya taunar komai,"

Murmushi Hafsat kawai tayi. Anty Bilki ta cigaba da cewa,

"Allah mijin ki ya huta ba ruwan sa, in ilimi ne masha Allah dukka biyun Arabi da boko, gaki kyakyawa ga tsafta, hankal nutsuwa, ga rashin son hayaniyar ki. Allah da ina da kani je zan masa kamu dan nasan duk wanda ya dauke ki ya gama sa'ar mata, kuma ya gama sa'a a duniya sai dai yayi fatan gamawa lpy. dan kin hada komai da ake burin ssamu,"

"Anty kenan, Ai dan adam bai cika 10 ba, 9 yake, muna fatan dai Allah yasa mu gama lpy,"

"Ameen, amman ke kin fi 9 nan, wai wane saurayin ne, naji ya dace da kanwar tawa,"

"Anty! saurayi! Ai tukunna, kina mana addu'a dai Allah kawo nagari,"

"Insha Allahu zan na tayaku yi, sannan in nazo haihuwa ma bazan manta ba Insha Allahu, zan saka ki a addu'a, kin san Allah na amsa addu'ar mara lapiya, ko wanda yake kan nakuda, da mai ciwon ciki, toh Insha Allahu zan roka miki, sai muyi ta fatan Allah ya amsa mana,"


"Ameen Antyna nagode,"

"Ba komai, ina kaunar ki Hafsat,"

Na dubeta nace, "Anty sauran wata nawa ki haihu ne,"

"Wata 3 ya rage,"
"Tog Allah sukeki lpy, Ameen,"

Itama Ameen din ta amsa da ita.


Dadare kuwa Ice cream dina kawai nasha nace na koshi, ai kam nasha fada gun Ya Muktar, dan cewa yayi sai naci abinci, sai da nayi kuka ya hakuri ya bar ni.


Sai karfe 8 na dawi gida, dakin mu na fada, akan kujera na kwanta, bacci ne ya dauke ni, cikin baccin na dinga jiyo hayaniya sama-sama.

Tashi nayi, muryar. abbi najiyo, tsaki nayi, dan shi da abin fada da bana fada ba yinsa yake,


Dan shi ko, magaba yake da hayaniya saka jiyi shi.

Daki na shige, kai na na sara min dan dududu baccin minti 20 ne ya dibeni, bandaki na shige dan bana son jin hayaniyar tashi.

Wanka nayi na sanya kayan bacci na, turare na fesa nayi falo, wayata na dauka,

Ummu ce ta shigo da sallama, na amsa.

Gefe na ta zauna tafe, "ashe kin dawo,"
"Eh Ummu, na leka babban falo naga bakya can ne, Anty Bilki na gaishe ki,"
"Ina amsawa, Khadija bata dawo ba ko?"
"Eh,"

"Toh dan Allah je ki kirata kar Abbi ya fara fadan nasa,"

Tih nace, ina mai jin tausayin mahaifiyar mu.
Katon hijab na saka na fice can gidan Umma,



Sallama nayi, wacce ba kowane ya ji ba, Umma na gaisar, na juya na kalli Khadija, nace, "kizo,"

Na juya duk yan dakin kallo suka bini dashi bansan ko na mene ba. Tare muka shiga gidan.

Ummu tace, "Khadija wai meyesa bakya jine,"
"Ummu kiyi hkri," muka hada baki muka fada tace,"Toh Allah shirya min ku," muka Amsa da "Ameen."


Ummu tace, "jeki rufe gate da kofar tsakiya," ta amsa da toh.
Acan ma hira ta tsaya yi da saurayin ta Khalifa. Ummu kuwa dakin ta ta nufa.


Ina zaune har wajen minti 10.....







MS Indabawa
MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY

13


BY Maryam S Indabawa
MANS




Annabi (SAW) yace duk wanda ya haddace ayoyi guda 10 na farkon suratul khafi Allah zai kareshi daga fitinar dugal

Allah ya kare mu Ameen ya Allah





Wayata na dauka na kira ta amman abin haushi sai naji karar ta a gefena,

Mikewa nayi na nufi gate din, abakin kofa na tsaya na haske ta, da fitilata, a firgece ta juyo, tai saurin rufe kofar.

Daki na shige sai gata ta shigo, na dubeta nace, "ke wai bakya gajiya da neman magana ne? Kin fi son ki ya jawo mana hayaniya da jawi mana bacin rai ko,"

"Yi hkri Anty na, zan rufe ne yaxo,"

Tsaki nayi na mik na shige daki,


Duk duniya daga Mahaifiyata Ummu, da Mahaifina Abbu (Allah masa Raham yasa Allah makomar sa) sai Khadija da Khairat, sai kawayena Hauwa da Faiza su kaidai nake kaunar kamar me, ina son su, dan suma suna sona suna kaunata kuma zan iya yin komai dan samun farin cikin su.


Alwala nayo na shige bargo, wayata na dauka na kunna bakara, addu'a na karanto na lumshe idona ban san lokacin da bacci ya dauke ni ba,


Ita kuwa Khadija sai karfe 2 ta kwanta bayan ta gama kallo a System dina, da asuba na tashe ta mukai sallah.

Gado ta koma, falo na fita na kunna karatun alqurani, na mike akan kujera sai 6 sannan na gyara dakin mu da tsakar gida. na nufi kichen, dankali na kwasa na nufi bangaren su Baba Lami, Dije mai yiwa khairat wanki na bawa nace ta ferayen.
dan Jamila naga tana gyara harabar gidan mu, in ta gama kuma nasan wake wanke zata zo tayi mana. Baba lami ita kyma tana daura musu abin kari.


Ruwan tea na daura wanka yaji kayan kamshi, snn na daura farfesun kifi, ina cikin yi sai ga Dije ta kawon, nan da nan na soya, na gama na shige daki nayi wanka, na waka uniform dina farare kar dasu kamar ba'a sasu, sun sha goga.



Bakin tea kadai na sha, na dauki takalmi na cover shoe ruwan hoda. na saka sai jaka ma ruwan hoda, wayat na dauka na kira Umma, gaida ta nayi, nace na shirya zan tafi makaranta,
"Da kudi a hannun ki," Ummu tace,
"A'ah zan biya na cira yanzu ko in an tashi, sannan yau za'a kafe mana result din mu,"

"Ok toh Allah bada sa'a, da nasara," nace, "Ameen,"


Daki na shiga na fesa turare har lokacin Khadija na aikin nata na bacci, na dade ina kallon yar Uwar tawa sannan na juya na fita.




A makaranta kuwa tin abakin gate muka hadu dasu Hauwa da Faiza, ai kam muka rumgume juna, notice board muka karasa dan duba sakamakon mu, Cikin ikon Allah Faiza ta shige ta dubo mana dukkan mu mun haye, "Alhamdulillah" muka hada baki muka furta tare da murmushi akan fuskokin mu.

Daga can Hall mukayi dan muna da lecture karfe 9, tinda malamin ya shiga sai karfe 12 ya fita, yana fita Malam Najib ya shigo.


Hauwa tace, "Sis kinga cingam dinki ya shigo fa,"
Hafsat tace, "ke rabu dashi,"

Ban dagi na kalle shi ba, dan nasan a hakan ma ni yake kalla,

Faiza tace, "Sis Allah Sir Najin karshe ne, duk Makarantar nan, amman bansan me yasa kike korar sa ba,"

Hafsat dai shiru tayi bata tankaba,
Faiza tacigaba, "Mutumin nan ga ilimi gashi dan gayu, ga Naira to me kuma zaki nema dan Allah, kina gannin yadda yan mata Ke son sa kamar me,"

Hafsat dai shiru tayi batace Ufan ba kuma bata dago kai ba,


Sir Najib ne ya farayi musu murnawadan da suka haye ya kuma kara ja musu kunne dasu dage su fita da sakamako mai kyau sannan, ya daura da musu lecture sai karfe 2. Ya gama musu,
Duk wani motsi na Hafsay akan idon sa take yi. Amman sam yaki dago kai bare yaga idanun ta yaji dadi.



Bayan ya fita suka fiti suka nufi masallaci Sallah sukayi sannan suka wuce cafeteria.


Kujera suka samu suka zauna, Hafsat ta dubi Hauwa tace, "Sis yau jakata ba kudi, sai an tashima zan biya na cira dan haka ki samo mana abu mu taba mu wuce aji please,"

Faiza tace, "ni dai Abinci zanci dan yunwa sai kace ban karya ba na fito,"

Hauwa tace., "Acici, Ni dai daga wacce bata cin Abinci, sai kuma mai ci sai kace gara,"

Dariya mukayi mu dukka,


Hauwa tace, "Sis keme zaki ci,"


Hafsat ta yamutsa fuska tace, "Ziza ma ta isheni,"

"Sis tazo muje," Hauwa ta fada tana kama hannun Faiza.



Bayan tafiyar su na dauki waya ta, Number Khadija na duba kamar yadda tai min saving da Kidney Sis, bugu daya ta dauka,
"Anty," Khadija ta kirata,

"Uhmm" kadai Hafsat tace,

"Kin je makaranta lpy, ya makarantar,"

"Lpy Alhamdulillah,"

"Inasu Anty Hauwa da Anty Faiza,"


"Sunje kawo mana abinci,"

"To ya akayi ne Anty? Wallahi yau

Please Login or Register in order to submit comment