Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

'yan uwan Dady suna kuwa yazo sai da ya bude jakata ya saka min.

Karfe tara su Ummu suka yafi gida ya rage daga mu sai abokan Ya Haidar.

Kida aka saka inda akasha rawa. Ni dai banyi ba inda daga tsaye amman su Khadija an dage sai rawa ake sha.

Anyi liki sosai inda karfe sha daya aka tashi gaba daya.

Motar da muka zo ita muka koma a ita bayan kowa ya bar wajen. Hannuna rike da nashi kamar za'a kwace masa ni.

Muna zuwa gida shi ya rakani har dakin Ummu sannan ya juya. Wanka nayi na zo na kwanta gefen *Ummunah.*

Washe gari Ummu taso su tafi amman Momy tace su bari akai ni mana. Da kyar ta yadda.

Ina kwance a daki Momy ta shigo rike da wani kofi a hannun ta.

Wani hadin ne a cikin kofin. Dan danawa nayi naji akwai saki gashi sai kamshin kayan kamshi yake. Sai dayan kuma hadin wani abune da madara.

Haka tasa na shaye su. Sannan ta dauko wani hadin turaruka ta bani da wani dan karami tace na shafa shi akowacce gaba ya jikina na.

Na karba, nai mata godiya.

Su Hauwa ne suka shigo ita da Faiza.

Gefena suka zauna,
"Amaryan yayan mu."

Murmushi kawai Hafsat tayi,
"Wai ya naga bakin ki ya qara mutuwa ne."

"Nima dai haka nagani." Inji Faiza.

"Dallah ki kwantar da hankalin ba wata wahala fa." Hauwa ta fada da zolaya.

"Ah toh fada mata dai. Wahalar ta dan lokaci ce zata wuce."

"Yau zaki zama cikakiyar mace kamar mu."

"Wai me yasa kuke yan iskane. To ni ba abinda zai faru."
Dariya suka sheke da ita.

"Hafsat kenan."
Hararra su tayi.

"Dan Allah ku rabu dani inji da abindan ke damuna."
"Haba Sis sai mu barki da damuwa. Kinsan dai damuwar mu taki ce."
"Daure ki fada mana. Kinji."

"Uhmm ni kai na bansan takamaimai me yake damuna ba. Amman dai naji sai faduwar gaba nake."

"Ayyah sannu ai wannan normal ne ba wata matsala."
"Gaskiya kam fargaba ce."

"Kina addu'a a ranki."
"Sabuwar rayuwa zaki shiga. Allah yasa ki shiga a sa'a kema nan da wata tara musha suna."

"Faiza kefa muguwa ce. Ai taci amarcin ta dai ko?"
"Amarci banda wanda suka ci."

Tsaki Hafsat tayi ta juya musu baya.
Dariya sukai suka cigaba da hirar su.









*INDABAWA*
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY






BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*








🌐HAJOWπŸ“πŸŒ

πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§ HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾





PAGE *65*







Daga haka bacci ne ya dauke ta. Sai bayan la'asar ta tashi.

Ummu ta gani zaune,
"kin tashi."
"Eh."

Khairat ce ta shigo,
"Taty kin tashi."

Ta fada tana zama a kusa dani.
"Eh Khairat. Ya makaranta."
"Lafiya muna ta karatu."

"Yauwah Baby na a kuma dagewa."
"Me kike so?"

"Ni so nake mu koma makkah garin da dadi."
"To shikenan in anyi hutu kisa Ummu ta kai ki."

"Kefa Taty?"
"Zamu hadu acan insha Allahu."

"Taty wai kin dawo nan da zama."
"Eh!"

"Nima Momy tace, dauke ni zatai."
"Ai kam da naji dadi."

Murmushi Momy tayi dan Hafst da Khairat in suna tare sai ka sha dariya dan Hafsat biye mata take su sha hira.


Ba da wanda Hafsat tafi hira kamar khairat daga ita sai ummu da Khadija sai kuma kawayen ta.


"Taty dazu mukaje gidan ki."
"Haba?"

"Allah dani da Ummu da Momy dasu Khdija. Yaya Khadija ma na can muka barta."

Ummu, Hafsat ta kalla.
Ummu ce tace,
"Eh munje gida yayi kyau sai dai fatan zama lafiya da samun zuri'a ta gari."

Kasa Hafsat tayi da kai.
Momy ce ta shigo,
"au kin tashi."

"Eh! Momy."
Fita tayi sai gata nan da filet kasashen nama ne wanda yaji tumatur a ciki. Sai kunun aya da yasha madara.

Dire mata tayi a gaban ta.
"Sauko kici."

Saukowa tayi ta fara ci. Ita da khairat.

Ban daki ta shige ta hada mata ruwan wanka. Da ya sha hadin turarukan wanka wanda har sun kama jikin Hafsat.

Tana gama ci Momy tace taje tayi wanka.

Kayan ta ta cire ta shiga bandakin ta dade tana cuda jikin ta sannan ta fito.

Mai ta shafa da hadin turarukan da Momy Ta bata.

Momy ce ta shigo tare da wata yarinya.

"Yi mata simple makeup." To tace
Kwalliya tai mata me kyau wacce ta kara fito da kyan ta.

Wata Atampa Momy ta shigo da ita a hannun ta da takalmi da mayafi.

Ruwan goro ce wacce akai mata adon da dark green.

Dinkin riga da zani rapper ne. Rigar an mata dinki me kyau wacce aka bi partern din atamfar akai mata ado da stone dark green.

Sai mayafi da bata wani dark green kai bakace mayafi bane dan ya hadu. Takalmin ta ma kalar mayafin ne.

Sai dankunne da sarka da ta saka mata na azurfa wanda akai musu ado da dark green din stone.


Wani turare tazo ta bade ta dashi. Take ta kara bada wani kamshin me sanyi.

Momy ce ta kama hannun ta,
"Hafsat kibi mijin ki, ki zama mai gaskiya, ki rike addinin ki da muhimmanci, ki baiwa ya'yan ku kula da tarbiyya ta addinin musulunci.
nasan kina da tsafta. Kiji tsoron Allah a kowacce hanya kika tsinci kanki.
kiso Allah da mazan sa fiye da kowa, ki daura ya'yan ki a akan son Annabi,
ki zama mai yiwa mai gidan ki addu'a ta alkhairi."


Kuka Hafsat ta saka. Lallashin ta Momy ta fara.
"Haba Hafsat mene na kukan. Ki daina ke da zakije wajen Yayan ki kuma Mijin ki. Nasan Haidar na son ki kuma zai rike ki amana insha Allahu, kar kisa damuwa aranki. Muna tare duk abinda kije da bukata ki fada min. Ba tin yau ba na fada miki ni Mahaifiyar kice ba Sirikar ki ba dan haka ki sake kina fadan abinda kike bukata.
Ga Khairat nan ma zan dauko mana ita kinga ai baki da matsala kuma zan na sa shi yana kai ki gun *Ummun ki.*
ki daina kuka kinji."

Kai ta daga alamar "toh"

"Kin san dai aure sunnah ce, haka nan. Manxon Allah (SAW) yace, Aure sunnah tace. Duk wanda yayi shi tamkar ya sami cikar rabin addininsa ne!"

Haka kuma Abu Ayyuba ya rawaito cewa, Manxon Allah (SAW) yace, Abubuwa biyar suna cikin sunnonin Manzanni, yawan kunya, da yawan sa turare da goge hakora da kuma yin aure."
a takaice aure hanya ce ta tara zuri'ah ta gari ingantacciyar Alumma. Aure ne kan haifar da sahihiyar rayuwa da samar da tarbiyyar tan cikar alumma.
Aure ne kan samar da dangi da iyali da kabila.
Aure ibada ce babba mai mutukar mahimmanci a rayuwa.


Jikin ta Momy ta jata tana lallashi har ta daina zubar da hawayen.


Su Hauwa ne suka shigo su suka cigaba da lallashin Ta.
"Haba Hafsat bakya ganin in Ummu ta ganki zaki tada mata hankali, kiyi Hakuri ki daina kinji."

Kai ta daga musu.

Kamata Ummu tayi ta kai ta gaban *Ummun ta.*.








*INDABAWA*
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY





BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*






🌐HAJOWπŸ“πŸŒ

πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§ HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾





Page *66*







A gaban Ummu ta zaunar da ita akan karfet. Ummu tace,
"Haba Anty Fati ai kin gama mata kuma."
"A'ah gata nan dai."

Ta juya ta fita. Su Hauwa ya rage a dakin. Mikewa sukai Ummu ta tsaida su.

"Ku dawo ku zauna dukkan ku"
Dawowa sukai suka zauna suka sa Hafsat a tsakiya.

Kallon su tayi gaba daya sannan ta fara magana.

"Duk abinda zan fada muku nasan kun sani sai dai na kara jan hankalin ku akan sa, da kara nuna muku su."

Shiru sukai. Kan Hafsat a kasa tana zubar hawaye,

"Ku kula da ibadar Allah Musaman kula da sallah akan lokaci tare da kula da kaidojin ta,
Ku kiyaye tsarkin jiki dana tufafi da na muhalli tare da cikakkiyar tsfta a ko wanne lokaci.
ku kasan ce kuna yawaita zikirin Allah da Sallati ga Annabi da godiya ga Allah da istigifari.
Ku yawaita karatun Al kurani a duk lokacin da kuka samu sarari. Ku daure kuna karanta abinda ya sauwaka a kullum.
Duk abinda ya dameki ko ya tayar miki da hankali kada ki dimauta kiyi hakuri. Kuna yawan addua ki gayawa Allah.
Ku girmama mijin ku a ko wanne lokaci kuma kubi duk umarnin da suka baku. Matukar basu sabawa Umarnin Allah da Annabin sa.
Ku kula kwarai ku kiyaye da abinda mijin ku suka fi so. Kuyi kokarin musu wannan abun.
Ku kula da abinda basa so ku guje shi
A duk lokacin da kukai wa mijin ku abinda ya bata musu to kuyi saurin basu hakuri da neman afuwar sa
A duk lokacin da mijin ku ya bata muku rai kada kuyi saurin fushi da tayar masa da hanakali. Ku yi hakurin tare da addu'a.
Amman idan ya zama dole ki fahimtar dashi to ki fahimtar dashi ta cikin ladabi da girmamawa tare da kalmomi marasa tayar da hankali."





Shiru tayi sannnan ta dora,
"Ku guji yawan kai karar mijin ki wurin kowa don gudun tona asirin ku sai dai idan har ya zama dole. Shima sai ki tari iyayrnki ko iyayen sa.
Ku guji sauraren 'yan tsegumi masu kawo miki labarin rayuwar gidn wasu.
Kuma ku rike sirrin gidajen ku.
Ku dauki rayuwa da sauki. Ku yawaita tunanin abinda yake me kyau da wanda baida kyau.
Ku guji yawaita kalle kallen fina finai barkatai da karanta littafi marasa amfani. Mai makon haka kuna karanta al qurani.
ki yawaita addu'a ga Allah dan neman Rahama.
In Allah ya albarkace ku da ya'ya ku. Kula da tarbiyar su da ibadar su
Duk abinda zaki nema wajen mijin ki kada ki taba zafafawa. In bai miki ba ki yi hakuri in ya mike ki gode masa.
kada ku nuna musu kwokwanton amarsa da gaskiyar sa.
Ku guji yin gasa da Kawaye ki godewa mijin ki akan duk abinda yai miki."




"Ku zama masu alkinta kayan mijin ku. Banda almubazzaranci.
Ku girmama yan uwan mijin ku da iyayen su
Ku na ziyar tar yan uwan ku da na mijin ku.
Ku san kalaman da zaku na fadawa mazajen ku
Ku tabbatar da tsafar jikinku da muhalli da tufafin ku. Ku kula da gashin kan ku, cikin kunne, baki, hammata, da gaban ku.
Kada mijin ku ya shaki wani wani abu maras dadi daga jikin ku
ku daure kunayin Sallah cikin dare
ku nisanci cudanya da maza
Kuna tambayar miji irin abincin da yake so
Ku kasance masu kyawawan hali
Kuna kamala Girki akan lokaci"



"A duk sanda kike magana da mijin ku kada ki daga murya komai bacin ran ku. Ku guji sa'in sa da shi
In Allah ya hadaku da abokiyar zama ki rumgume ta tsakani da Allah to Allah zai kare ki daga kaidin ta.
In zaku fita kuna shiga ta musulunci
Kada ku taba fita daga gida ba tare da cikaken izinin mijin ki ba.
Domin Manzon Allah (SAW) yacr
"Duk matar da ta fita daga gidan mijin ta ba tare da izinin sa ba to har taje ta dawo tana cikin tsinuwar maka'ikun Allah."
dan haka ku kiyaye."



"A karshe ina yi muku nasiha da ku kiyaye dukkan abubuwan dana lissafa muku da wasunsu ma kyawawa.
Allah yayi muku albarka ya Albarkaci Auren ku. Ameen"

"Mun gode Ummu Allah saka da alheri."
"Ba komai. Allah baku zaman lafiya."



Daga nan Momy ta shigo ta daga ta.

Wajen Dady ta kaita shina yai mata nasiha sosai.
Wacce ta kara kashe mata jiki.

Daga nan wajen Abbi shima nasiha yai mata da kara bata hakuri akan abinda duk ya faru.


Su Hauwa suka fito dan kai amarya dakin ta.

Momy da kan ta tace zata kai amarya dakin ta dan ita sam tace Hafsat ba sirikar ta bace.

Dan kuwa da ba Haidar ta aura ba dole ita zata kai ta dakin ta.

Haka kuwa akayi dan yanzun ma ita ta kama hannun ta dan kai ta dakin ta.

Mota sabuwa fil wacce Ya Haidr ya siyawa Hafsat a ita suka tafi kai ta.

Tinda suka fita take zubar hawaye. Momy sai lallashin ta take dan idanun ta har sun kumbura sunyi jajir.











*INDABAWA*





For comment and correction,
*08062882472*
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY






BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*








🌐HAJOWπŸ“πŸŒ

πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§ HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾







Page *67*







Gida ne madaidaici amman wadatacce, don ko harabar gidan zata ci a kalla manyan motoci guda biyar.

Bangare biyu ne da a gidan, daya dakin bacci biyu da falo sa bandaki da kitchen

Dayan kuma falo ne da daki daya sai kitchen da ban daki. a kasa sai bene dakin bacci biyu da falo da ban daki da kitchen.


Falon kasa an masa ado da Jajayen kujeru da baki inda labulayen ma duka jajaye ne. Sai center karfet ja mai adon baki.

Sai kayan kallo da speakers da aka jera su.

Bed room din kasa ma duk adon ja da baki akai mata. Dan gadom bakine.


Sai gefen kitchen din ta inda aka saka katon daining a wajen.

cikin kitchen kuma komai na ciki ja da baki ne. Hatta firji da deep frizer din ta duk ja ne.

Store din su cike yake da kayan abinci ba abinda babu. Shinkafa, taliya masaroni, cuscus, indomie, kayan tea, biskit kala kala, fulawa, semo, garin alkama. Lemo katan katan da dankali kwai kai hatta kanwa akwai ta lode a store din su. freezer kuwa nama ne da kalolin kifi duk sun kankare.

Jan Karfet a ka shimfida a matatakalar benen.

Falon sama shima kujeru ne irin leather chairs din nan dark ash da ratsin light pink.
Tafka tafkan kujeru ne masu numfashi su kadai

Sai katon karfet (Turkish) da wasu. Labulaye Dark ash da rastin pink.
Sai wani karamin karfet na welcome a kofar dakin shima duk kalar su daya.


Dakin ta na sama, wasu dakankun royal bed ne, kalar dark ash da rashin pink hade da katifa da filo wanda suka sha pink din bed sheet da bargo.
a duk gefen da zaka sakko daga gadon akwai wani dan karfet pink colour.
Labulayen dakin duk dark ash ne da ratsin pink

Sai kayan kallo irin katuwar plasma slim da zungura zunguran speakers da suka kusan kamo rabin bangon dakin sai fiidge a gefe

Kitchen din sama kuma komai na ciki Ash da baki ne.
Sai daining ma cin kujera hudu a gefe inda aka saka pink din labulaye

Sai kuma wani daki a can waje bayan na mai gadi. Gidan ya hadu da fulawowi masu kyau. Lambune a bayan gidan inda akai musu wajen shakawa a gefe.


Daya bedroom din kuma adon purple, colour be da adon silver sai wata kujera da ke gefe Purple colour.


Bangaren can kuwa anyi wa falon jeran dark brown da milk sai abubuwan kallo da na decoration duk milk colour.

Gaskiya gidan ya hadu, fada ma bata baki ne.


Gaba dayan su Hauwa kallon gidan suka tsaya yi, suna taya Yar uwar su murna.

Side dinta Momy ta kai ta mai Ash din kayan dakin.

Hafsat na kuka haka ta fito ta bar ta. Da kyar suka yakice suka fiyo daga gidan Hafsa. tamkar baza ka fito ba saboda tsaruwar sa.

Ita kadai aka bari a gidan.

Tana zaune akan gado, sai matsar kwalla take.




Ya Haidar kuwa sai bayan magriba yaje ya shirya cikin shaddar ruwan madar tasha brown aiki yasa brown takakmi da hula sai kamshi yake zaubawa.

Yayi kyau sosai fuskar sa sai murmushi ke tashi dan farin ciki yake ji sosai yau an kai ma matar sa.

Cikin gida ya shiga dan yin sallama da Momy.

Ita da Ummu ya same su.
"Haidar an kai maka Hafsat kamar yadda ka dade kana fata.
Toh Haidar ga Hafsat can ka kular mana da ita ka cire ta daga maraicin da take ciki.
Yanzu duk duniya kafimu kusanci da Hafsat dan Allah ka rike ta amana ka kula da ita.
Kasan mata in tai maka ba dai dai ba kasan ta yadda zaka sata a hanya tare da mata nasiha."

"Hafsat Amana ce a wajen ka in har kaci amanar Hafsat sai Allah ya tambaye ka. Ka kula."


Kansa akasa, yace,
"Momy insha Allahu zan rike amanar Hafsat kuma bazan taba ci ba. Zan kula da ita fiye da yadda zan kula da kai na insha Allah."

"Allah yai maka Albarka ya baku zaman lafiya mai daure wa."
"Ameen!"

Wajen Ummu ys matsa.
"To Ummu zan tafi."
"To Aliyu! Allah baku zaman lafiya da hakuri da juna. Allah kiyaye hanya."

"Amren Ummu nagode."

Ita ta kamo hannun sa sukaje wajen Dady, dady ma amanar Hafsat ya kara bashi tare da jan hankalin sa na ya kula da ita.



Wajen Abbi sukaje shima dai nasihar ce yai masa.

A waje suka tadda su Kamal. Har mota ta shigar dashi sannan ta juyo tana sanya masa albarka.

Su Kamal da Ya Nura sai tsiya suke masa. Shi dai sai murmushi yake musu.

Sai da sukai musu siyayya sannan suka wuce gida.







*INDABAWA*




Fir comment and correction
*08062882472*
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY







BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*







🌐HAJOWπŸ“πŸŒ

πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§ HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾







Page *68*






Tin daga harabar gidan kamshin turarukan wutan da gidan ya ji yake tashi.

Yana fitowa yaji wata iska da ni'ima na ratsa shi. Ido ya lumshe yana addua a cikin ransa.

Ya Kamal ne ya tabo shi sannan ya bude idon sa.
"Lafiya?"

Murmushi kawai yayi yai gaba,
Suna shiga falon wani sanyi ya doke su, na splite zungura zungura farare kal kal guda biyu daga kusurwar dakin. Sai kamshi da ya kama dakin.

Kai baka ce a kasar kake ba sai kace, a irin kasar waje kake CANADA ko kasar CYPRUS a lokacin SNOW. Ga kamshin da ya dinga dibar su mai taba zuciya.

Tabbas wajen ya burge su duk da sun saba gani da zuwa waje irin wadannan har da wadan da suka fi nan amman nan din ma ya burge su.

Sama suka haye, wani kamshi da sanyi na daban ne ya canja. Zama sukai shima zaman yayi.

"To ai sai ku tafi ko kunga gida."
"Haba Yayan mu ai dai maga kanwar mu.muyi mata nasiha ko."

"Ta gode ai kunsan Su Momy sun mata."
"Ni dai a kira ta nai mata sallama ko."

"Kai fa ka cika naci."
"Eh naji."

Mita Ya mike yanayi. Dakin ya shiga.
"Ya salam."

Wani daddan kamshi ya duki hancin sa kusan faduwa yayi kasa.

Dan rudewar da yayi.
Kallon ta ya tsaya yi. Kanta a kasa amman ba karamin kyau tayi ba.

Da kyar ya daga kafar sa ya karasa wajen da take, kai ta dago tana kallon sa ta cikin mayafi.

Zama yayi a gefen ta.
"Baby, taso muje Yayanki zai miki sallama."

Ya fada yana kamo hannun ta. Mikewa tayi jiki a sanyaye. Falo suka isa.

A threesitter suka zauna. Bayan sun gaisa muryar ta a dashe dan bata ma fitowa sosai.

Addu'a sukai musu sannan suka mike zasu tafi.

Ya Haidar yace.
"ku gaida gida,"
"Au ba rakiya."

"Eh! Au zan rufe kofa muje na raka ku."

Ya fada yana mikewa. Har wajen mota ya raka su sannan ya dawo ya rufe musu kofar.


Yana shigowa ya gannin ina kuka, lallashi na ya fara tare da jijiga ni yana fadi,
"Dan Allah Hafsat ki daina kukan nan bana son ganin hawayen ki dan Allah kiyi shiru. Gaya min me kike so."

Fuskata ya dago. Kallo na ya tsaya yi.
"Kin yi kyau Baby."

Kasa nayi da kai na. goshina ya sumbata sannan ya sumbaci kumatuna.

Kallona ya kuma yi.
"Baby ina sonki."

Kasa na kuma yi da kai na. Dan wata kunyar sa nake ji.

Ta so muje muyi Sallah. Gabana naji ya fadi tinawar da nayi bana sallah.

Hannuna yasa ys dago ni muka shige daki. Ban daki ya shiga dani dan dauro alwala. Shi kadai yayi ni na tsaya ina kallon sa.

Yi Alwalan mana. Alwalar nayi.muka fito. Sallaya ya shimfida mana. Hijab ya mikon. Taso kinji.

Kasa nayi da kai na ina wasa da yatsun hannu na.
"Baby nah!"
"Uhmm!"

"Taso man."
Kasa na karayi da kai na. Wannan yasa ya gane me ke faruwa tina yau nawa ga wata.

Murmushi yayi ya tada sallah sai da ya idar sannan ya jawo ledar da ya shigo da ita.

Kitchen yaje ya dauko filet da kofi.
kahi ne gasasu da nono na kwalaye tare da lemuka masu sanyi.

Shi ya rinqa bani a baki na ki karba na kau da kai, haka ya rungumo ni yana rarrashi na dole na karba na rinka ci da kyar na iya bude baki na nace na koshi.

Ya janyo ni mukaje mukai brush sannan ya hada min ruwan wanka. Ya fito ya bar ni.

sai da nai wanka sannan na fito.

Baya dakin dan haka shiryawa nayi cikin riga da wando masu kauri na bade jikina da turarukan da Momy ta bani.


Ina gama shiri na haye gado naja bargo na rufa, cikin bacci na ji shigowar sa. Cikin kayan baccin sa shima

Ina jin sa ya dinga feshe kusuwar dakin da Air freshner tare da wasu dadasan turaruka masu dadin kamshi.

AC dakin ya dado nan da nan sanyib dadi ya cigaba da tashi. Ya kashe fitilar dakin gaba daya sai Dim light da ya bari.

Ya hawo gadon ya kwanta ya jawo ni.






*INDABAWA*
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY







BY *Maryam S Indabawa*
*MANS*






🌐HAJOWπŸ“πŸŒ

πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§ *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*✍🏾✍🏾✍🏾





Page *69*




Jawo ni yayi ya manna da kirjin sa. Ya zira hrshensa a kunnena ya rinka sumbatar jiki na haka ya gangaro har zuwa kirji na.


Tsigar jikina tuni ta tashi, nan da nan jikina ya ringa karkarwa. Tsoro ya kamani na manta a halin da nake ciki.

Sai da yai mai isar sa sannan ya jawo ni ya makale ni a kirjin sa. Ya jawo bargo ya rufe mu. Muka shiga bacci me dadi.



Da asuba ina jin tashin sa. Yai Sallah sannan ya zauna yana karatun al qurani. Yai addu'a ya hawo gado.

Bacci muka sake komawa sai wajen sha daya Ya Haidar ya tashe ni dan yin break fast.

Ina mikewa na gyara dakin sannan na shige bandaki na fada. Wanka nayi sannan na fito na tsaya a gaban mudubi. Na tsara kwalliya ta wacce daga hoda sai kwalli sai jan baki da nasaka ruwan hoda.

Wata shadda na saka mai taushi ruwan hoda wacce akai min dinkin doguwar riga, an mata aiki da ruwan omon duwatsu.

Dauri nayi me kyau na saki gashi na bayan na saka masa ribon.
wankan turaruka nayi. Nan da nan dakin ya dau kamshi.

Ni kai na da na kalle ni a mudubi nasan nayi kyau. Takalmi na saka ruwan hoda.

Na fito yana falo a zaune, yana hango ni ya mike da sauri ya taro ni.

Shima ya shirya cikin lallausan farin boyel, ya bude min hannun sa a hankali cikin salo na fada jikin sa.

Yasa hannun sa ya rumgume ni kam a jikin sa. Mun fi minti uku a tsaye sannan muka zauna.

"Ina kwana Ya Haidar!"
"Lafiya lou Baby na ya bakunta. Da fatan.kin tashi lafya" kai na daga masa kawai.


Duk na narke a jikin Ya Haidar shi kuma sai wasa yake da kitson kai na yana yaba shi. Tare da wasa da wasu sasan na jikina.

Sai sha biyu dai mukayi break da lafiyayen abinci da Momy ra hado mana shi.

Sai da su Faiza suka zo sukai min sallama na hada musu kaya masu yawan gaske.

Sai Karfe biyu Ya Haidar ya mike dan zuwa gida. Nayi mishi rakiya har bakin kofa. Ya tafi.

Na sauko falon kasa, inda yan aikin gidan suka dinga shigiwa suna gaida ni. Baba Mai gadi ne sai Bala mai sharar harabar gidan da gyara fulawoyi.

Sai Baba Zulai me yin wanke wanke da Dije mai sha sai Kubra mai girki wai.
wai zance man dan ni nasan sai dai ta dafawa masu aiki. Amman zan iya aiyuka na.


Minti talatin nayi a kasa na koma sama nayi kwanciya ta ban dade ba bacci ya dauke ni.

Cikin bacci naji karar waya. wayar Ya Haidar ce, dauka nayi nace
"Hello"
"Hello Baby na barki ke kadai ko. Kiyi hakuri gani nan taho wa."

"To sai ka dawo" Na yi saurin mikewa na fada bandaki na sake wanka. Da sabuwar shiga. Ta wani bulu din boyel mai adon baki.
duk kayan da nayi amfani dasu dazu sai da na canja.

Na feshe jikina da turare na fito falo na kuma juna turaren wuta tare da kara sanyin AC ai kan Nan da nan dakin ya dau kamshi da sanyi.




Kallo na kunna. Na zauna kan dum duma dum dumar leather sit dina. na zurfafa cikin tunanin su Ummu.

Ya Haidar ne ya murda kofar dakin ya shigo kallo na ya tsaya yi, yana me sha'awar kwalliya ta, a kasan zuciyara kuwa zallar kaunata ce take azazzalarsa.

Yana tsaye a bakin kofa yai salma da gyaran murya wajen sau uku sannan na dawo hayyaci na.

Zumbur na mike na isa gareshi na durkusa. Nace,
"Barka da dawowa."

Yasa hannu ya dago ni ya makale ni a barin sa, tare da komawa cikin falon ya zaunar dani a kan cinyar sa.

"Baby na tunanin me kike yi? Ba kin min alkawarin kin daina tunani ba bare kisa ciwon ki ya tashi."
"Yi hakuri, Ya Haidar na kasa durewa ne, gashi sai ni kadai."

Nan da nan kwalla ta kawo mata. Rumgume ni yayi, yana jijiga ni,
"Yi shiru Baby gani na dawo toh. Kinji dadin dawowa ta."

Kai na daga alamar amswa. Harshen sa yana lasar hawayen.

"Haka kawai an min wannan kwalliya ai kuma hawaye kazo zaka bata min ita."

Haka ya dauke ni zuwa wajen cin abinci. A cinyar sa ya zaunar dani ya fara ciyar dani.

Haka muka kasance da Ya Haidar, yana matukar sona yana bani kyakyawar kula wa. Baya yadda yayi nesa dani ko na minti daya.

A zancen auratayya kuwa sam bai ne meni ba

Please Login or Register in order to submit comment