Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaki kaini makaranta," hade rai Hafsat tayi, tace, "Baki iya gaisuwa ba,"
Ido Khairat ta zaro sannan ta marauraice tace, "yi Hkri Taty, Ina kwana," "Lpy, kinci abinci ne," "Eh nasha cornflask," "toh maza jekiyiwa Ummu sallama na kai ki tinda yau ina gida,"

Da gudu ta fita tana cewa, "Ummu! Ummu! Yau Taty ce zata kaini makaranta," Ummu tace, "to maza dauko jakar ki," daki ta shige ta dauko jakarta, ta fito da sauri tayo dakin su Hafsat.

Da sallama ta shiga, tace, "Taty na shirya, mikewa tayi rike da wayar ta, tace, "muke toh," a kichen ta hango Ummun su, ta karasa ta durkusa ta gaishe ta. Ta amsa mata, tace, "yau khairat ta tashe ki ko," Hafsat tace, "ai daman na tashi kuma ba abinda nakeyi," Ummu cebta mikowa Khairat fulas wanda ta zubo mata soyayen dankali sai naman kaza, lemo ta bata da biskit tace, tasa a jakar ta. Hafsat ce ta amshi fulas din nata, snn sukai wa Ummu sai sun dawo,


Har bakin gate ta kai ta, Khairat tana daga mata hannu, sai da taga shigewar ta sannan ta juyo, gida ta dawo ta samu Khadija hai ta tashi,
Khadija tace, "Anty ina kwana," "lpy kin tashi lpy," "lpy lou," ta shige dakin su tayi kwanciyar ta, saboda wani ciwon kai da take ji bacci ne ya dauke ta ba ita ta tashi ba sai karfe biyu saura kwata, bandaki tashige ta dauro alwala tayi sallah, kan gadon ta ta koma ta kwanta,

Can sai ga kiran Hauwa, Hauwa mata sallama ta amsa mata, Hauwa tace, "Sis ya naji murya ki haka," murmushin karfin hali tayi tace, kai na ke dan min ciwo ne," "Ayyah Allah sauwake, kinsha magani," "Ameen," Hauwa tace, maganin fa kinsha," "Eh," tace, dan tasan halin Hauwa da naci yanxu zata takura mata sai ta sha. Tace, "to bari na barki ki huta sai anjima na kira ki," "Toh nagode Sis," sukai sallama ta kashe wayar ta kwanta,

Tana kwance bayan minti 30 sai ga kiran Faiza nan, ta dauka da sallama, Faiza tace, "Sis ashe baki ji dadi ba," "Uhm wallahi," "toh sannu Allah sauwake," "Ameen," ta kashe wayar, bacci ta koma sai karfe 4 ta tashi, sallah tayi sannan tayo falon su.


A kan kujera ta kwanta ta lumshe idon ta, Khadija ce ta shigo, tace, "Anty yau baki da lpy ko," ido Hafsat ta bude tayi murmushin karfin hali sannan tace, "A'ah baccin dai nake yi," ok to me zaki ci, samomin chocolate cake dan Allah," kitchen ta nufa ta dauko mata, shi taci da lemo sannan ta kishingida,

Sallamar Faiza tajiyo, sai da ta jiyo sun gaisawa da Ummu, take ce mata ina ciki ai, da sallam ta shigo dakin ta karaso guna, zaune na mike, ina mata murmushi, nace, "Sis kece," "wallahi Sis H bata karaso ba," "zuwa zatayi," "Eh, ita tace muzo mu duba Bestyn mu," murmushi Hafsat ta kuma tace, "sai kace jinya nake," "au sai jinya kike zamu zo duba ki," "A'ah yi hkei kinji,"

Sallamr Hauwa.mjka jiyo, Khadija ta sama a tsakar gida, suka gaisa, falon Ummu taje nan ma suka gaisa sannan tayo dakin mu, ta shigo, gefena ta samu ta zauna, ta fan harari Faiza tace, 'Shine kika riganj zuwa ko," "Kai Sis H, amman kinsan ke kika ce na fito kema kin fito ko," dauke kai Hauwa tayi, ta dubi Hafsat tace, "Sis nah, ya jikin," "jiki da sauki fa, daga nace jna ciwon kai shine duk kuka fito," "ba dole ba, Bestyn mu ba lpy," hawaye ne ya zo min nace, "Nagode yan uwa," Hauwa ta rumgume ni, tana cewa, "to mene abin kukan," Faiza ma tayo kanmu, "tana dan Allah ki bar kukan," Hafsat ce ta dago tana musu murmushi, tace, "ina kaunar ku," tare suka hada baki, sukace, "muma muna kaunar ki,"


Khadija ce ta shigo rike da faranti a hannun ta dauke da snack da lemo, ta same mu a haka, tace, "yau kuma, soyayyar ce ta tashi," dariya sukayi sukace, "Antyn ki yar rigima ce, Khady," Khadija tace, 'in rigimar ta tashi ba,"
Nan muka zauna muna ta hira, har magariba sai da sukai sallah sannan suka tafi gida duk kan mu kamar kar mu rabu, tun kan su je gida suka hau whatsapp suna chat cikin nishadi da kaunar juna, har sukaje gida sai akai sallah isha'i sannan suka rabu,


Karfe 10 Hafsat ta nufi daki zata kwanta, Hauwa ta kira tai mata godiya da ban gajiya, sannan tai mata sai da safe, haka ma Faiza,


Wanka ta shiga tayi, sannan ta feshe jikin ta da turare ta saka kayan baccin ta, kan gado ta kwanta tayi addu'a sannan tayi baccin ta,




Muje zuwa

MS INDABAWA
MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY
6


Writting by MARYAM S INDABAWA
MANS



Dis page dedicated to Zainab Umar Kunya, Allah baki zuri'a ta gari Allah ba baku zaman lafiya ke da mijin. U are my Best friend and Sis love Kunya.




***ASALIN LABARIN***
**********
Alhaji Muhammad haifaffen garin Kano ne, Dan agundi iyayen sa ke zaune amman mahaifin sa haifaffen cikin karamar kumar Rimin Gado.

Yayi auren soyayya da matat sa Hajiya Mariya, inda Allah ya azurtasu da ya'yan mata 2, Hafsat ita ce babba sai mai bimata Khadija.


Alhaji Muhammad ba a kasar nan yayi karatun sa ba, kuma ya karanci harkar kasuwanci, inda yana gama karatun sa ya samu aiki, Allah kuma ya rufa masa asiri ya buda masa, inda har shima ya mallaki kamfanin sa guda 2, daya na kayan masarufi ne, dayan kuma kayan sawa ake masa order daga waje,


Alhaji Muhammad mutumin kirki ne, ga taimakon ma bukata, dan duk asabar da lahadi gidan sa cike yake da mabukata, sannan kk a hanya ya ganka yaga kana bukatar taimako zai taimaka maka.


Hajiya Mariya itama yar nan Kano ce, a nan Gwangwazo, tayi karatun NCE din ta, amman sam Alhaji Muhammad yace bazarayi aiki ba, hakura tayi dan dole, tinda ba abinda ta rasa kawai tana son yin aikin ne dan ta bada tata gudumawar, amman tace, ta koyar wa da ya'yan ta. Alhaji Muhammad yace, duk matsayin karatun da take son yi ya mata alkwari zai taaya mata amman yace aiki dai A'ah, wannan yasa ta koma degree din ta anan (FCE) inda take karantar English language,


Hajiya Mariya macece mai mutum da girmama na gaba, ga tausayi ga fara'a baka taba ganin bacin ran ta,


A yadda gidan Alhaji Muhammad yake, Alhaji Muhammad bai rahe iyalin sa da komai na rayuwa, dan duk karshen wata zai debe ya'yan sa da Matar duk da alokacin babbar shekarar ta 6 kamar 4, zai kaisu suyi shopping duk abjnda suke bukata zai ce su dauka, haka in karshen sati ne in yana da lkkaci zai dibe su suje wajen wasan yara da washen shakata wa, wani lokacin kuma sukai ziyara wajen yan uwan sa.

Yana son ya'yan sa sosai, Hafsat ita ce yar gidan mahaifin ta wato ABBUn ta haka suke kiran shi, inda ita kuma Khadija yar gida UMMUn suce.


Yaran sun tashi cikin gata da kulawa, gashi mahaifansu na daura su akan tarbiyya ta gari, Makaranta mai kyau yasa su daga Arabi har boko, kuma in sun dawo akwai mai musu bitar karatun nasu, yaran badai kokari ba.



Alhaji Muhammad shine babba a wajen mahaifin sa, sai kannen sa 3, maza 2, Sagir, da Salisu, macen kuma Binta,

Hajiya Mariya ita ce Auta a wajen mahaifan ta, Yayan ta 4, Aisha ce babba sai Ado, Tijjani, sai Fatima,
Tin tana karama a hannun yayar ta Aisha ta tashi, dan ita ta aurar da ita, Alhaji Mahmud sunan mijin Aisha, da ya'yan ta maza 3 Ya Muktar shine Babba sai Ya Kamal sai autan su Ya Sani, duk da sa'an Hafsat ne amman ya girme ta kada.
Aisha na da kishiya, Jamila ya'yan ta 2 Aliyu, sai Usman, zaman lpy ake a cikin gidan bamai banbance tsakanin Ya'yan Aisha da Jamika,


Hajiya Mariya zaman lpy suke mai cike da tsafta da girmama juna tsakanin ta da mijin ta, ga ya'yan su da kullum suke kauna da kula dasu.


Shekarar Hafsat 9 mahaifinta Alhaji Muhammad ya rasu sakamakon wani ciwon ciki da ya tasar masa cikin dare kan suje asibiti Allah ya karbi Abun sa,


Gaskiya anyi rashi sosai, dan jama'a ma kuka suka dinga yi bare kuma ya'yan uwan sa da matan sa da ya'yansa, Hafsat kuwa duk da karamcin shekarun ta tayi kuka sosai dan ta shaku da mahaifin su sosai.


Hajiya Mariya kam sosai ta kwanta jinya dan sai da aka hada da taimakon Allah sannan Allah ya yaye mata ciwon, da dakuwar dake ranta.
Hafsat kuwa in tana zaune sai dai kawai tasa kuka, in an tambaye ta tace, Abbun tah, sosai ake tausaya mata, ayi ta lallashin ta har tayi shiru. Duk lokacin da tayi tunanin sa sai ta sa musu kuka, ranar kuwa ko abincu da kyar take ci sai an ta lallashin ta, kuma sai da taci kayan zaki.*******



Muje Zuwa


MS INDABAWA
MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY
7


writting by MARYAM S INDABAWA



Dis page is for you, Khadijat Taiyeb Na'abba, khady en mata.
Allah ta kawo miji na hakri Sis Khady, kawata ina sonki.






Hajiya Mariya na cikin takaba aka gane tana da ciki dan wata 4, dan haka watan ta biyar ta haifi dan ta namiji, ta sha kuka inda tace a mayar mata da sunan marigayi, haka kuwa akayi, ibda aka sawa yaron sunan Alhaji Muhammad suke kiran sa da Sabeer,


Satin yaron 2 ya rasu saboda fama da yake da ciwon ciki, Hajiya Mariya ta sha kuka sosai, dan sai alokacin take kara kukan rashin mijin ta da ua rasu.

Dan tana tuna lokacin da take masa zance haihuwa, take cewa ko ta gama haihuwa ne tinda lokacin Khadija na da shekara 7, yakan ce mata kika sani kk ya'yan da zan haifa kenan.


Ko da aka raba gadon Alhj Muhammad, mahaifan sa duk ya'yan suka barwa kamfanonin, kuma suka bukaci da a cire Hajiya Mariya daga ciki ya zama malakin su Hafsat da Khadija kawai.


Wai a zancin su anan shine, kar tayi aure ta haihu, ya'yan ta su shiga cikin gadon dansu, saboda suna son jikokin su, su samu ingantaciyar rayuwa kar su tagaiyara a rayuwar su. Wannan yasa suka sa a fitar da ita.



*********
Manema dayawa sun fitowa Hajiya Mariya amman sam ko kula su batayi, da yake gidan Yayar ta ta koma ita da ya'yan ta Hafsat da Khadija.


Alhaji Mahmud wanda yake a mazainin mahaifinta, wato mijin yayar tane, yace, dole fa tayi aure tinda bata wuce auren ba dan a lokacin shekarun ta 30 a duniya.
anan take ce masa tana son a nema mata aiki, tinda Alhj Mahmud a ma'aikatar ilimi yake aiki.

Shekarar Alhaji Muhammad daya da rasuwa, Alhaji Mahmud Mijin yayar Ummu, ko ince mariqin ta shima Allah yayi masa rasuwa, Hajiya Mariya har tafi matan sa da Ya'yan sa kukan rashin sa, dan da shi ta bude ido ta gani a matsyin mahaifinta.

yana rasuwa takardar daukar Ummu nah aiki ta fito, Ummuna tayi farin ciki sosai, haka ma Ummi yayar ta,


Anan Gwangwazo aka samar mata makaranta, bayan an share zaman makoki ta fara zuwa aikin ta da nasariri masu yawan gaske, haka suka cigaba da rufawa kan su asiri, duk wata ita da Ya Muktar zasu siyo kayan abincu da kayan bukatar gida.


Shekarar Alhj Mahmud daya da rasuwa Ummi yayar Ummun mu ta rasu, innallillahi wainna illahor rajiun, mutuwar nan ta daki Ummu nah, dan jinya ta kwanta sosai, wannan yasa Mahaifiyar Ummu nah dauke ta daga nan gdn yayar tata, ta maidata gaban ta da zama,



Sai da Hjy Mariya ta dade tana jina sannan ta samu sauki ta koma bakin aikin ta, ko da tace, zata koma gidan marigayiya yayarvta sai aka hanata, wai tinda wadanda take gunsu sun rasu tai zaman ta hannun mahaifiyar ta.

Haka ta hakura amman duk wata in anyi albashi tana siyan kayan abinci da kudi ta kai musu.

Hafsat sunan kakarta ta wajen Ummun ta aka saka mata.


Ya'yan Ummi da yake duk sun girma kuma ana zaman lpy yasa suka zauna a hannun kishiyar Ummi, wato Umma.

Sai da Alhaji Muhammad yayi shekara 5, amman Ummu bata kula kowa.



Ana haka ne wani Alhj Umar ya fito yana son Ummu nah,
Alhj Umar yace shi dan kasuwa ne, sannan yana da mata daya amman ta rasu da marayun ya'yan sa mata 2, wanda yace suna hannun dangin mahaifiyar sune.


Hajiya Mariya tayi na'am dashi in da aka daura auren su, na family house din su ya kai ta, amman ita a bene take, bangaren ta daban, katon falo ne sai dakin bacci guda 2 da kitchen da bandaki.

Farkon auren komai na rayuwar ta ya dauke mata, kama daga ci da sha, kaya ne dai bai taba dinka mata ba, Kudin albashin ta in tayi wa su Hafsat bukatun su sai ta kai banki ta ajiye sauran, dan duk wata ba abimmnda bata ajiye wa su Hafsat kamar yadda Mahaifin su ke musu, haka take yi musu, aje shopping ko aje wayon shakatawa.




A wanje mahaifiyar ta tabar sun Hafsat da Khadija, dan bata son taje damu ana wulakanta mu.


Zaman su Hafsat a hannun kakar su Baba Zulai, sam ba sa ji dadin sa, ko dan mai matan ya rasu ne, dan Abbu duk wata sai ya loda mata kayan abinci da kudi, in azumi yazo har kayan rabo yake bata tayi, sannan yayi mata dinki, to a lokacjn ba kamar su Hafsat duk jikokin ta tafi son su.


Amman yanzu sam, ko dinkin da ta sabayi musu duk shekara ta daina, sai dai tayi wa wadanda suke da uba, abin duniya ya rufe mata ido.

wannan yasa Ummu ke kashe musu kudi sosai tai musu kaya masu kyau da tsada, dan kwata kwata dangin Abbun su ko waiwayen su basa yi, bare su musu wani abun.


Ummu ita ta zame mana Uwa da Uban mu, ita take hana su kukan komai, dan komai na rayuwar jin dadi tana ajiye musu.

Wani abun wai Baba Zulai sai tana jin haushi dan Ummu ta mana abu, Ummu kance mata inban musu ba wa zai musu, kuma dan me nake nema.

Baba Zulai ganin ba yadda zatayi ta hana Ummi yi mana abu yasa ta fara hadamu da yan uwan Ummun mu, yau tace mun mata kaza gobe mun mata kaza.
Kullun ati tayi mana fada.

In mun fadawa Ummu sai dai tayi ta bamu hkri, takan ce zaman tare haka ya gada, amman mai hakuri na tare da Allah, Allah na sane da ku, kuci gaba da hakuri kullum nasihar Ummu kenan ga ya'yan ta.

Haka in sun zauna zatayi ta jan hankalin su akan kula da addinin su, da kame kansu, shi yasa suke so zama da Ummun su dan in dai suna tare tana yawan jan hankalin su da abjbda yake dai dai da wanda ba dai dai naba.


Uncle Tijjani ya dade da rasuwa, inda Uncle Ado yake da ya'ya 4, Anty Fatima kuma tana lagos tana Abuja tana aure da dan ta Haidar.

Hajiya Mariya a hankali ta dinga fuskantar halaiyar Alhj Umar.



Muje zuwa




MS INDABAWA
MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY
8


By MARYAM S INDABAWA
MANS



Wannan shafin naki ne Rabi'at Shuaibu Idiris, (Rabra) Allah raya mana ya'yan mu Ameen



Hjy Mariya a hankali ta fara fuskantar halin mijinta, ashe auri saki ne dashi, dan matan sa 3 duk ya aura ya saka ba wacce ta taba mutuwa.


Ta faron ya'yan 2, ta biyun yar ta daya, sai ta ukun da bata haihu ba suka rabu, kuma ashe buga bugar sa kawai yake yi ba wani kasuwanci sai kuma yar malamta da yake tabawa.

Halin kunci ya samu Ummu dan wani lokacin ko abinci basu dashi, wannan yasa, Ummu duk wata sai ta ajiye kayan abinci. Abinda bata sababa wai yanzu ita ke ajiye kayan abincin da zata ci.


Kullum ta tuna rayuwar ta, ta baya ta kanyi kuka, sannan ta godewa Allah dan ta san wannan jarraba ce sai dai tana fatan Allah bata ikon cinye ta.


Duk da haka MIJIN UMMU in ta siyo kayan abincun, in ta fita aiki sai ya auna yaje ya siyar ya samu na sawa a wayar sa, dan kiran yan.matan sa.

Ita dai Ummu hakuri kawai take da halin mijin ta, ga dangin sa ba son ta suke ba.

Ganin halin da ya'yan ta Hafsat da Khadija ke ciki yasa take son debe ya'yan ta, toh amman ba debewar ba ina zata ajiye su, dan ita gaskiya bazara iya kwaso ya'yan ta ta kawo gidan mijin ta ba, dan tasan yaran ta baza su sake ba.

Ummu ce zaune, ita da ya'yan ta Hafsat da Khadija, Ummu tace, "Hafsat so nake na dauke ku, ku dawo hannuna da zama," murna sosai Hafsar ta dinga yi, dan gaskiya tana son Ummun ta, dan ko da zata tare baku ga yadda Hafsat tasha kuka ba.


Dan wani lokacin ko unguwa Ummu zata Hafsat ta dinga fushi kenan, ita tafi son kullum ta ganta gefen Ummun su.

Ummu ce ta fara magana cikin nutsuwa, tace, "Hafsat bazan iya kai ku wani gidan kuyi zaman agolanci ba, dan nasan baza kuji dadi ba, ni da shawarar da na yanke a tashe dan hayar gidan ku dake sharada sai mu koma da zama,"
"Hakan yayi Ummu, ai sai a fadawa alkali ya basu notices ko,"

Daga nan wajen Alkali muka je, tayi masa bayami kuma ya gamsu, yace "ai gidan ya'yan ki ne ba wata matsala, daman kudin su ya kusa karewa dan haka zan sanar musu tun kan ya kare," muka taho muna tafarin ciki.


Wata 3 a tsakani, Alkali ya nemi Ummu ya shaida mata yan haya sun tashi, Ummu Baba Zulai, mahaifiyar ta ta sama ta fadawa, Baba Zulai sai cewa tayi, "ai gwara dan ta gaji damu," sati daya a tsakani Ummu tasa aka gyara mana gidan aka share aka zuba kaya tsaf, sannan muka nemi gafarar Baba Zulai muka tafi muna kewar juna.

Shi kuwa Abbi MIJIN UMMUn mu, ranar da Ummun mu ta bar gidan a ranar aka jera masa kayan amaryar da ya aura ba da sanin Ummu ba, saj daga baya yazo yana bawa Ummu hakuri tace, Bakomau Allah basu zaman lafiya.

Auren kamar jaraba ya zame masa, dan tun da yayi bai da wanj kwanciyar hankali, Ummu dai sai hakuticda take bashi, tare dayi masa addu'a Allah ya yaye masa.

Gidan mu Babban gida ne, dan yana da katon haranar gida da zataci mota a kalla guda 6, sai bangaren yan aiki, dakin bacci, falo da kitchen da bandaki, sai dan tsakar gudan su, sai ciki bangaren mu, mai dauke babban tsakar gida, wanda yake dauke da dakuna guda 3 ciki da rufa guda 2 duk kuma akwai bandaki a ciki, sai wanmta rumfar babba, akwai katon kithen da bandaki, gidan mainkyau ne sosai.

Ciki da rumfan su Hafsat na da suka dauka suka cigaba da amfami da shi, haka ma Ummu, sai bababn falon baki in sun zo.

Tinda muka dawo Ummu ke nan nan da mu, komai mu, a lokacin tana da cikin wata 4, murna muka dinga yi kamar me dan muna son yara.

Abinda yafi damun mu shine, sam Abbi MIJIN UMMU, baya sakar mana fuska, kullym fuskar sa a hade kamar wanda akayiwa mutuwa, gashi ko gaishe shi mukayi sai dai da amsa da kyar, wannan yasa muke zama a dakin mu,

**************
A lokacin shekarun Hafsat 16, Hafsat fara ce doguwa, tana da manyan idanu wanda suke dauke da gashin ido masu tsayi, sannan tana da hanci mai dan tsaho, da bakin ta dan karami, wanda yake kamar ta shafa masa jan baki, girar ta a kwance kamar wacce take gyara ta, sai dimple dake lotsawa ko yaya ta motsa bakin ta, sannan akwai wani a kana habar ta, dan daya mutane kan ce suna son na kasan habarta, gefen fuskar ta gashine kwance yayi luf, kan ta ma gashine sosai dan in ta sake shi yana kai wa har gadon bayan ta, jikin ta ma gashime kwance luf luf, tana da diri, dan duk namiji ko macen da ya kalle ta sai ya kuma kallon ta. Hafsat sai dai a ce Masha Allah.

Hafsat miskila ce ta karshe, bata sob hayaniya ko surutu, sannan bata da daukar raini, duk wanda yayi mata abu zata fito ta fada masa, saj dai yaji haushi, wannan yasa ake cewa bata iya magana ba, dan in dai taga abinda bai dace ba, to ko waye sai ta mishi magana.


Hafsat bata da tarkacen kawaye, duk da akwai masu son ta, amman ita sam bata kula su, ko a makaranta irin yan sashen su, bata fiya shiga shirgin su ba, suna dai tare amman sai taje makaranta a tasji bai fi sau 3 tayi musu magana ba, in ta shiga suka gaisa, sai kuwa in wani abu take bukata, ko in sun cika mata kunne da surutu.

Wannan yasa ake cewa wai bata son mutane, in kaji maganar Hafsat toh sai dai in tana tare da Ummun ta ko Khadija kanwarta, anan ne zakaji bakin ta, baya gasu bada wanda zakaji tana hira.

Hafat nada kokari sosai, dan a makaranta ma, ita ke daukar ta daya, yanzu haka tana SS2 3rd term anan day Science, Burin Hafsat bai wuce ta ganta tana aikin asibiti ba.


********
Khadija, bakace, tana da manyan idanu, masu dauke da gashi mai tsaho, amman Hafsat ta fita idanu, Khadija tafi Hafsat hanci, sannan tafi Hafsat jiki dan Hafsat bata da kiba, ita kuwa Khadija na da kiba, khadija ma akwai gashi sosai.

Da kagan su zaka san yan uwa ne, dan da dama ma akan kira su da yan biyu, duk da dai Hafsat ta fi Khadija kyau sosai.


Khadija na da surutu, sannan akwai ta da tarkacen kawaye, gata da son a zauna ai ta hira. Itama tana da kokari, dan yanzu tana SS1 anan first Lady makarantar kwana ce,


Hafaat kullum na zaune a gida ba inda take zuwa dan tin tana Aji 3 ta sauke Alqurani, banda Khadija da kullun sai ta fita ta zaga gari ko ba inda zataje, dan kafar ta har cizon ta take yi.






MS INDABAWA
MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY
9

By MARYAM S INDABAWA
MANS

Dis page is for you Khadija Muhammad Mahmud (Nene).love you sis


jikin gidan mu, gidan matar kanin Abbun mu ce, amman sun rabu, to kullum Khadija na gidan, saboda gidan cika yake da yan mmata da samari, ayi ta hira da shewa, ita kuma Khadija nason harkar nan. Wannan yasa take son gidan kullum tana can.

Ita kuwa Hafsat bata son hayaniya dan yanzu kan ta zai fara ciwo shiyasa kullum tana gida in ba karatu ba, to tana amfani da waya.
Dan na kan rasa me take yi a cikin wayar, kullum taana rike a hannun ta, tana faman dane dane.


Abinda yasa Hafsat bata son MIJIN UMMUn su shine, duk wata kadara ta Ummun su ya amshe ya siyar, filayen ta guda 4, ban da golds dinta guda 4 dana Khadija guda 1 sai na Hafsat guda 2 duk ya amshe ya siyar, wai ta ranta masa kudi.


Kuma ko da wasa baya tasar mata da maganar ya amshi kudin ta, kamar yaadda itama tayi shiru da batun.

Gashi Ummu kullum cikin baccin ran sa take, bata da wata kwanciyar hankali game dashi. Dan suna tare ya auri mata wajen 4, duk da yanxu duk basa tare,


Sannan in yasa kafa ya tafi wani garin, karin a ganshi yayi wata 3 bai xo yaga matar sa ba, waya ma sai ya ga dama zai kirata su gaisa, wani lokacin ma bazai dauka ba, ita kuwa Ummu tayi ta ramewa, saboda rashin kwanciyar hankali da rashin mai debe mata kewa.



Abinda Ummu ta tsira dashi, shine aikin da take yi sai dan kasuwancin da take yi, da anyi albashi ta karbi kudin sannan ta kara juyasu ba tare da taje da kudin gida ba, duk abinda mutum yake so zata dauko masa bashi sannan ta daura masa riba yar kadan, wannan yasa ake karbar kayan ta, kuma Allah yake kara buda mata, dan in taga mutum bai da hali ma bata dada masa riba, duk da wasu ba biyanta suke ba. Amman haka in sun bukata zata kuma dauko musu, Allah ya sa mata albarka a kasuwan cin ta.


Toh hakan ma shima zai sa ta debar masa kaya, masu yawan gaske yace zai siyar, amman bazata kara ganin idon kayan ko kudin ba, ya sha karba kayan amman sisi baya kawo mata, ko yasa ta karbo masa a wajen abokan kasuwan cin

Please Login or Register in order to submit comment