Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nayi kewar ki sosai,"

Murmushi nayi na lumshe ido na, nace, "Mie too Sis,"

"Anty," nace, "Na'am"
tare da bude ido na. Sir Najib na hango yayo cafeteria, ido na kawa, nace,
"Sis result ya fito, kuma dukkan mu mun haye,"
Wani ihu Khadija ta saka na murna, wanda yasa na dauke wayar daga kunnena, sai can naji ta fara magana, wannan yasa na mayar da wayar kunnena, naji tana cewa,
"Anty Congratulation ina taya ki murna ku dawu Anty Faixa, Allah kara basira ya bada nassara, bari na fadawa Ummu, Ummu! Ummu! Ummu!, naji tana kwadawa Ummu kira murmushi nayi na sauke wayat na mayar jaka.


Sir Najib na gano yayo waje na, kai na sunkuyar daya daga cikin kujerun wajen ya samu ya zauna a kusa dani.

"Sir Ina yini,"
"Lpy Hafsat, ya kike ya karatu,"
"Alhamdulillah!" Na fada idona na kallon kasa,
"Wai meyasa bakya son kallona ne, ko tsoro nake baki ne,"
Kai kadai na kada alamar A'ah,
"To indai ba haka bane, dago ki kalleni,"
"Ayyqh Dan Allah Malam kayi hkri, ni wallahi bana iya kallon mutum haka,"
Murmushi yayi sannan yace, "au haba, ai kam ni sai kin kallen yau din nan, in ba hakaba mu kwanan anan wajen,"

Ganin ina son ya tafi yasa, na dagi da kaina, karaf sai a cikin nashi, da sauri na kawar da kaina gefe.

Dariya yayi yace, "Wow idon ki yana da kyau sosai Hafsat,"
Shiru nayi ina wasa da yatsun hannuna, su Hauwa na hango na sauke ajiyar zuciya,

Magana yake amman ni duk hankalina na wajen su Hauwa, suka karaso da sallamar su, Sir Najin suka gaisar sannan suka zauna.

Faiza takeaway tayo, Hauwa kuma Lemo da Snacks ne, leda Hauwa ta ajiye a gabana, Sir Najib ne ya bude ledar, Nama ta siyon gassashe, sai Ziza Milk.

Murmushi yayi yace, "wannan namu ne kenan," Faiza tace, "Eh,"

Budewa yayi, ya ajiye gaban mu, yace, "toh Bismillah mu fara ko,"
"A'ah Sir na koshi,"
"Haba dai daure muci man,"

Kai na girgixa nace "A'ah,"
Murmushi yayi yace, "in kunyata kike ji bari naje sai anjima, in an tashi ki jirani,"

Ya mike yayi gaba.



MS Indabawa
MIJIN UMMUNAH
TRUE LIFE STORY


BY MARYAM S INDABAWA
MANS



Page 14




Deducated to SADNAF Ina son ki wit all ur book Allah kara basira da daukakka, Allah sa kifi haka. Dis page is for u and ur fans.





Yana mikewa, nace, "kunsan dai bazan iya cin abinci anan ba ko,"
"Haka ne," Hauwa ta fada.
Faiza tace, "sai ki bari mu gama mu ai ko,"
"Lah yanzu muka gama waya da Khadija tace in gaida ku," cewar Hauwa ta fada tana danna waya.
"Allah sarki My Khadija ta tana lpy, hutu dai ya kusa karewa,"
Hauwa tace, "Eh, dama ita ce Hafsat ma,"
Faiza tayi murmushi, "ke dai bari da munfi shan.....
"Haba! Ku kuna cin abincin ma surutu, haba dan Allah bakyau fa,"
Shiru suka, sai da suka gama sannan sukace, "munji munyi laifi muna cin abinci muna magana, tashi muje kici naki kar lokaci yayi,"

Ta mikie tana tsakiya Hauwa na gefen dama, Faiza ana hagun, duk wannda ya gansu sai sun birgeshi, kuma indai sun sanka sau sun gaisa damkai banda Hafsat, da abin ya zaman mata biyu, ga rashin son magana ga takuear d Sir Najib ke shirin yi mata.


Sai da mukaje aji, na samu naci na kora da maltina, sannan na dube su ina murmushi nace, "Nagode fa yan uwa,"
Hararata sukayi kawai, mukayo gaban ajin.


Karfe 4:05 muka fito daga dakin daukar karatu, masallaci muka nufa dan yi sallah, muna idar wa muka fito.


Sir Najib na hango zai shiga motar sa da sauri na janye su Hauwa mukai can bayan massallaci nace ina neman wata ne, sai da na bata mana minti wajen 20 sannan muka fito.


Hauwa anan Jan bulo take, Faiza kuma Zoo road. Drivern su Hauwa har yazo dan haka shi ya debe mu mukayo gida, Faiza muka fara saukewa sannan muka dau hanya, anan sharada nasa driver na tsata na ciri kudi sannan mukayi gida. A bakin gate suka direni, ina dafa mata hannu itama haka, duk kamar kar mu rabu.



HAUWA IBRAHIM
Shine sunan Hauwa mahaifinta commissioner ne, su Uku ne wajenn iyayen ta.
Hajiya Halima sunan Maman ta kawar Ummun muce tin daga firanare har yanzu sosai suke kawancen. Amman ni da Hauwa da sai dai mu gaisa in sun zi gidan mu, dan ni ban fiya zuwa gidan su ba, A Ckul of Nursing anan muka hade dan ganin mun san juna yasa muke tare ko yaushe. Wannan yasa muka zama kawaye.

Hauwa sa'a tace dan ma ta banu a kalla wata biyu, Farace tana da dan jiki kadan akwai hanci gata mai fara'a da surutu, akwai kokari.



Ya Jamil sunan yayanta yana malleshiya karatu yanzu haka sai kanwar ta sa'ar Khadijan mu, me suna Bushira itama wannan shekararr zatayu candy.







FAIZA YAHUZA
Faiza kuma mahaifin ta propesor ne a BUK da matar sa Hajiya Aisha, itama ma'aikaciyar ilimi ce malamar makarantar firamare, Su biyar ne, Anty Binta ce babba da ya'yan ta 3, sai Anty Wasila da ya'yan 2, Anty Nasiru dansa 1, sai ya Luknan dake can india yana kartu sai autar su Faiza.


Faiza itana fara ce, bata da iiba kamar ni take, tana da hanci kyakyauwace itama, Faiza ma akwai dan bazan surutu,


A makaranta muna yawan zama kusa da juna, surutun ta da barkwanci yasa Hauwa janyi mana ita,



Zakuyi mamaki na ni da banda son hayaniya gashi ban da surutu amman yan uwana kamar sa saida ka dan surutu, ba komai yasa nake tre da su ba, sai Allah da ya hdamu muke son junan mu, sannan suna da hankalu ga nutsuwa ilimi duk ba baya ba, sannn a duk lokacin da suka ganni a cikin wani halin rashin son magna su da kan su suke kyaleni nayi abin da nake so, Hauwa kan ce, "Wallahi mijin ki ya shiga uku ke kam, kawai kizo kiki magana kuma muna miki kina basar wa sai kace kinga hula akan mu, tabb wannan in hula kika gani yakenan?" Sai dai na harare ta kawai,
"Eh kya harareta man, ai zamu ganine nasan in wanda ya zama sarkin zuciyar tane ai bata masa haka ba, amman mu ta maidamu kamar me, Allah sarki mu,"
Nudai sai dai bayi murmushi kawai.

in kuwa suka ga raina ne a bace to sai sun san ydda suka ciren damuwata. Gaskiya ina son Hauwa da Faiza kamar yadda suma suke sona.





Cikin gida na shiga da sallama, Abbi na gani yana amsa waya a harabar gidan, dan kar in gaida shi yasa nayi cikin guda da sauri, kalli na yayi ya girgiza kai.

Ummu na sama a tsakar gida kan kujera nan na nufeta da fara'a ta na durkusa, dafa ni tayi, nace, "ina yini Ummu ya gida,"
"Lpy lou, Hafsat ya makarantar,"
"Lpy Alhamdulillah!"
"Naji sakamakon ku ya fito, kun haye Allah kra bda sa'a Allah yasa ku gama lpy, Allah bada miji na gari kuma,"
Nayi kasa da kai na amsa da "Ameen,"
Na mike na shige daki.

Khadija na kan kujera a kwance, ta mike ta zo ta rumgumeni, "sannu da zuwa, Anty nah,"
"Yauwah ya gidan,"
"Lpy, ya makaranta, ina taya murna,"
"Nagode,"
Na shige dakin baccin mu, hijab kadai na cire naji sallamr khairat ta dawo daga islamiyyah, murryar ta naji tana cewa, "Ummu taty ta dawo,"
"Eh yanzu ta dawo," da gudu ta fado dakin tana kwadan kira "Taty! Taty,"
"Na'am yar gidan Taty ya akayi," na fada ina fitowa daga dakin mu, sama na dagata nace, "Oyoyo Swt baby na, ya makaranta,"
"Lpy, Taty ina chocolate dina,"
"Oh my Baby! Ki fa rage shan zaki, kinji ko," kai kadai ta daga min alamar toh.

"Muje daki na dauko miki to," tana gaba ina binta a baya, kan gadona ta haye tana jiran in dauko mata, cikin jaka na miko mata, tasa hannu biyu ta amsa tace,
"Jajakallahu bil kairan Taty,"
Ta fice a guje, ina dariya ita a lailai sai ta kwaikwayi yadda muke yin abu, Khairat kenan ina son ki.

Khadija ce ta shigo, ta shige bandaki ta hada min ruwan wanka, "Anty ga ruwan wankan ki can fa,"
"Toh Cwt Sis nagise fa," na shige nayo wanka na fito, mai na shafa kawau sai turare na zira doguwar riga nayo Falo.


Sallamar Sani najiyo a tsakar gida, suna gaisawa da Ummu,



MS INDABAWA
MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY



BY Maryam S Indabawa
MANS



Page 15



Dis page is ur Anty Yasmeen, love u soo much




Sani kanin Ya Kamal ne, dan gidan yar Ummu mu da ta riketa. bayan sun gaisa da Ummu ya shigo dakin mu, "Hajiya Hafsay em mata,"
"Ah Bro ya kake,"
"Lpy, Ya Makaranta?"
"Alhamdulillah,"

"Yaya Sani Oyoyo! Oyoyo!" Khadija ta fada tana fitowa daga cikin dakin mu,
"Oyoyo Sis nah, ashe kina ciki,"
"Wallahi ya kake ya gida yasu Umma?"
"Duk suna lafiya, ya hutu?"
"Hutu yzo gangara, in zubo maka abinci ne?"
"Eh, kamar kinsan yunwah nake ji kuwa,"

Ta mike ta fita, yadubeni yace, "Yau yan miskilancin ne kenan,"
Dagowa nayi na harareshi dayake kusn sa'a nane, dariya kawai yayi, yace, "wannan mijin ki ya shiga uku, ga rashin magana ga harara tab,"

Shiru nayi masa, yayi dariya, "wato na ci kaina....,"
Karar wayata ce ta katse shi, ina dubawa naga Hauwa ce, murmushi nayi na dauka, "Hafsat ya kin shiga gida lpy, yasu Ummu?"
"Wallahi lpy, yasu Ummi da Bishia?" "Lpy, kinsan me kuwa?"
"A'ah sai kin fada!"
"Ya Nura fa ya dawo,"
Nace, "Inye! Ayi masa sanni da zuwa kan mu hadu, kuma kice nice zan kunce jaka,"
"To shikenan an gama, bari naje na kintsa kar yazo ya ganni haka,"
"To a tahon da kayan dadi gobe,"
"Kice dai kayan sa ciwon ciki, dan sune kayan dadin ki kedai,"
"Eh naji,"
Na kashe wayar ina dariya.


Ya Nura, saurayin Hauwa Ne, kuma dan uwansu ne, shi zata aura dan har an bashi ita, muna gamawa za a saka rana.

Yanzu haka saura wata hudu mu fita asibiti daga makaranta, daga nan shikenan kuma sai jarabawar karshe mun gama.



Sani ne ya dubeni, "ke dawa haka kike ta magana ne,"
Nace, "hauwa ce,"
"Eh, ai nasan sai itan, wallahi yaran nan na hakuri da halin ki,"
"Su waye yaran, sannan kuma kada suyi hakurin ma man,"
Dau dai lokacin Khadija ta shigo da tire a hannun ta. Shinkafa da miyar kaji sai hadin salad, sai lemo da snacks a gefe.


can wajen magariba sai ga Ya Kamal ya shigo, shima yayan Sani ne daga Ya Muktar sai ya Kamal,

Ya Kamal shi keson Faiza kawata, dan shima har manya sunje akace sai ta gama karatun,
muna shiri da Ya Kamal sosai, dan shima yana daukar halaiyata, sannan duk abinda nake so shi yake min, shi ke iya xama dani na rashin magana dan sai yaxo mu bata awa daya bamuce kala ba, duk da in magana ce yana da surutu.

Gefena ya nufo, ya zauna, naace, "Sannu,"
Harara ya watso min, sannan yace, "Ciwo nake da zaki ce min Sannu,"
Baki na tabe, nace "dan nace Sannu,"
"Eh din,"

Mukai shiru, matsowa yayi, yace, "Ya ina mutuniyar,"
Kaina na dauke, dan ko kallo bai ishen ba, bare yasa ran zan bashi amsa.
"Haba Sweety nah, yi hakuri kinji, ya kama hannuna yana lallashi na."
Sani yace, "ai daman kai ke kara sangar tata, yanzu mene abin bata hakuri,"
Hararrar sa nayi, Sani yace, "ke dai sai idanun nan sun fadi zaki daina hararar mutane ko,"
"Kai Sani ba ruwan ka da ita," cewar Ya Kamal,
"Allah baku hakuri, Khadija zo, ya ina mutumin?"
"Ya Sani, yana nan wallahi,"
"Ok yana gari kenan,"
"Eh, yazo jiya,"
"Ok in zan tafi ma hadu," ta dau waya tace, "hello," cikin yanga da iyayi sai kace yana gaban ta, banji amsar sa ba, sai ji nayi tace,
"Oh My Khalifa, kayi hakuri, daman bro sani ke neman ka," tayi shiru da alama magana yake,
"Ok gamu nan toh,"
Ya kamo hannun Ya Sani, tace, "taso yana waje ma yana jiran mu," suka fice.


"Ya Kamal!" Na kira sunan sa cikin shagwaba,
"Ya akayi ne,"
"Dan Allah ka kaini nasha Ice cream mana in anyi magariba,"
"Ok, toh ina mutuniyar,"
"Kai Ya Kamal,"
"Eh fadan,"
wayata na dauko, ya bini da ido, dan son sanin abinda zanyi, ni kam lambar faiza na nemo, na kira, tana dagawa na kara a kunnen sa..
Ai kam da ihu ta dauki wayar tana cewa, "kinji Ya Nura ya dawo ko," "Baby nah," taji muryar Ya Kamal, ai tuni ta rage muraya, "Na'am Habibinah,"
"Ya kike ya makaranta,"
"Lpy Alhamdulillah,"
sai hirar soyayya ta balle, kalamai yake ta fada mata masu kwantar da hankali, tsaki na dan ja, na mike nayi cikin daki. Abin na bani mamaki kowa soyayya ji wai Khadijama soyayyar take, Allah ya kyauta.

Kwanciya ta nayi, kiran Sallah najiyo na mike nayi cikin bandaki, alwala na daura sannan na zo na tada Sallah, ko da na iddar ban mike ba ina zaine ina ta tasbihi, har akayi Sallah isha'i sannan nayi na fito falo.


Shima Ya Kamal sai da yaji Sallahar sukai sallama, massallaci ya tafi bai dawo ba sai isha'i, a falo ya tadda ni zaune da waya a hannu,
Ya dubeni yace, "Sis tashi muhe dan ina son zuwa wajen Antyn ki,"
mikewa nayi, na shige cikin daki, After dress na daura na fesa turare, dakin Ummu naje na fada mata zamu fita,
"Allah kiyaye hanya kuma kar ki dade," na amsa mata da "toh."
yaso yaje dani wajen Faiza naki, dole yana siyan abinda nake so ya maidoni gida ya wuce.



Satin Khadija uku suka koma makaranta, kuka sosai muka sha dan mun saba duk tafi sai munyi, kamar kar mu rabu da juna. Rayuwa kenan watarana ma duniyar za mu bari baki daya.



Harkar karatun mu sai cigaba take, tare da nasarori, Wani Farin jini ya kara futon, dan ko a makaranta daga Malamai har dalibai kowa sona yake, dan ma ina da kwarjini, basa iya tarata sai dai su Faiza, suma suna sharar fada min sai dai su bada hakuri.



Satin Khadija biyu da tafiua, nake cewa su Faiza zanje wajen ta, "Ai kam kisa mana rana muje mu gano ta,"
Hauwa tace, "ranar Laraba zamu tinda karfe 2 muke da lecture ranar,"
"Haka ne, Allah kaimu," cewar Faiza.


Ni kam ina gefe duk suka gama tsara yadda za'ayi, "musa kayan makaranta, sai musa After dress tinda daga can makaranta zamu biya ko," duk wannan bayanin na Faiza ne.



Ranar laraba tin karfe 10 Hauwa tazo da drivern su, Wata Bakar Abaya nasaka mai ruwan goran duwatsu, tamin kyau ainun, ruwan goran cover shoe nasaka tare da jakar su, Hauwa sai yaba kyan dani take, Gidan su Faiza mukaje, Momyn Faiza har da bada soyayyun kaji akai mata, sahad muka biya, na siyo mata ice cream da chocalate dan Hauwa tayo mata miya, da snacks, Faiza kuma ta jidi mata biskit da lemo ka, sosai naji dadi nayi musu godiya.

Karfe 11:30 muka isa, har ciki mukaje sannan muka nufi offishin vice, karbar hannu biyu akai mana, daga karshe aka kira mana Khadija, hall din da ake ganin dalibai mukaje jiran ta, tana gano mu ta kwasi a guje, ta rumgumeni tana murna, ta sake ni tayi wajen Hauwa dagan Faiza, hira muka taba dan sai Karfe 1 muka baro ta da kewar juna, tana ta godiya har da hawayen ta.


Rayuwa muke me ciki da kaunar juna da taimakon junan mu, ina son su Hauwa dan ko ya suka gannin ba dai dai ba zaki yadda zasu na nan nan dani.


Watan Khadija biyu, akayo waya gida bata da lafiya, Ummu da kanta taje dauko ta, tana dawiwa ta leka gidan Umma dan dubata ance itama bata da lafiya, lokacin ina Makaranta.

Dawowata kenan na tadda Ogan gidan namu wato MIJIN UMMU NAH, yana ta fada kamar zai ari baki, kuma ba akan komai bane sai akan Khadija tashiga gidan Umma, "Ke ahakan ne baki da lafiya, kinsa an dauko ki, zaki fara yawo nifa bazan dauki wannan abun ba."


Daki kawai na shige abuna, sai ga Khadija ta shigo tana hawaye,
"Ke dan me to kika fita,"
"Gaaida Umma fa naje yi,"
"Ciwon karya dai kike yi, duk kin tda mana hankali baki da lafiya ko, in ba haka ba ai ita ya kamata tazo ta gaidaki,"

na mike nayi cikin daki, halin Abbi, Mijin ummu nah na damu na bazu tab yin magan a hankaki ba sai cikin karaji da daga murya, kai Allah ya ban miji mai tausasa kalaman sa akb iyalan sa, bance kada a tsawatar ba dan nasan dole a dora mu akan hanya to amman ai akwai yadda ya kamata ya yi fadn nashi, kuma nasan yanzu haushi yake ji dan Ummu zata siya mata magani, shi bai son abinda Ummu zata taba kudin ta, sai dai shi yai ta cemata kaza yakeso kuma ta bashi sai kace nauyin sa akan ta yake, mu da nauyin namu ma ke akan ta baya son tai mana amman shi yake daura mata nasa, kai Allah kawo karshen wannan alamuran na mijin Ummu nah."






MS INDABAWA
MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY




BY Maryam S Indabawa
MANS


Page 16



Dedicated to you, Zetty, maman Hanan, Allah ya daukakai Allah ya shige miki gaba ya kareki daga sharrin mahassada, Allah kara basira My Zetty prety.




Satin Khadija daya ta warware ta koma makaranta, in Ummu zata siya mata abu sai ya hana wai ana sangartata karatun zatayi ko cin kayan dadi, dan haka ne ma wani lokacin Ummu bata sanin naje dan zanje nai mata siyayya ne na kai mata, sannan duk bayan sati biyu zan mata siyayyar kayan motsa baki, wanda nasan basa samu na kaimata, wani lokacin su Hauwa in sun sani tare muke tafiya kuma kowa da abunda zai kai mata. Dan haka ita bata damuwa da halin sa ta wannan fanin, dan tasan da Ummu na yi mata komai kafin ta ganni ma aiki ne.




Haka rayuwar mu ta ke kasancewa, yanzu haka Asibiti muka tafi, duk kannin mu Asibitin Murtala muka zaba kuma mukayi dace dan duk sun karbe mu.




Cikin Azumi muka fara jarabawar karshe, in da yanzu saura kadn mu gama, Khadija kam ban fasa zuwa mata ba dan da azumi duk sati nake zuwa dan yanzu itama neci suke yi.

Sallah sauran sati muka gama jarabawa, inda su Khadija ma haka, kuma duk kan mu muna sa rai da sakamako mai kyau. Dan da sakamako ya fito duk munce gaba zamu yi wato BUK Zamu tafi gaba dayan mu.



Ansa ranar Hauwa watan babbar sallah, ni na fitar mana da wani codeless pink and blue wanda ni da Faiza za muyi fitar dinner dashi, sai wani material Ruwan goro da Baki, ni na mana su ni d Faiza har da amarya ma da ba sawa zatayi ba, dan har sautin jaka da takalmi na bayar iri daya mu uku aka kawo mana.

Na kawayen mu kuma ruwan zaiba mukai da maroon head, faiza ita tayi mana na fitar daurin aure wata dakakiyar ruwan kasar shadda ce, inda Ummi da kan ta tayi mana atamafar fitar yinin ta, mu uku, sai Ummu da tasa akayi mana order Kananun kaya na children day.


Tin bayan karamar Sallah muka gama siyayyar mu dan ba ma so lokaci ya kure mana, ko da Sallah duk shirye shiryen yadda abin zai kasance muke, dan bayan babbar sallah da sati uku ne, dan haka ana yin babbar sallah muka hau rabon kati dan biki saura kwana goma mun gama.



Zaune nake a gaban mudubi na fito a wanka kenn sai ga wayar ya Kamal nan wai ina gida, nace masa "eh,"
"To gani nan ni da Ya Haidar,"
"Sai kazo," na fada ina kashe wayar."


Kwance nake akan kujera, sanye nake da doguwar riga ruwan hoda sai hula dake kaina ruwan omo, bnyi kwalliya ba amman nayi kyau sosai saai tashin kamshin turare nake, wayace a hannuna ina buga game,
Sallamar Ya Kamal najiyo, dakin mu ya shigo, wata sallamr na kuma ji cikin sanyin murya wacce in da da hayaniya a inda nake bama xan ji taba, na amsa suka shigo Ya Kamal ne a gaba sai na gano mutum ta bayan sa,
"Sannu,"
"Na fada miki ban son wannan sannun taki ko,' ya fada, yana samun gefe na ya zauna, mikewa nayi, dai dai karasowar na bayan Ya Kamal,
kai na dauke, nace, "to kayi hakuri,"
gefen Ya Kamal ya zauna, kaina a kasa ban dago ba nace, "ina yinin ku,"
Ya kamal ne kadai ya amsa, duk sai naji na kasa sakewa sannan ina jin ido a kai na.

Wayata ce tayi kara na dauka, Hauwa ce, cikin sanyi nayi sallama, "Hafsat gamu nan fa," ta fada bayan ta amsa sallamar,
"Ke dawa?"
"Faiza mana,"
"Sai kunxo, amman fa ni yau ba inda zani,"
"Ai kam sai kinje,"
"Allah Sis wayo kike mana kefa in anyi biki kina da mai yi miki tausa mukuwan fa,"
"Zanzo da kaina nai miki," tsaki nayi dan jin shirmenta, na katse wayar.


Ya Kamal ne, yace, "Ummu bata nan ne," mikewa yayi ya tafi dakin ta, wayata na cigaba da dannawa,


Har lokacin ina jin idon sa akaina, wannan yasa na kasa dagowa, sallamar su Ummu ce yasa ya dauke kansa akaina amman duk da haka ina jin idon sa, Ummu ce, tace, "A'ah Aliyu, saukar yaushe?"
Kasa ya sauka yayi kasa da kansa, sannan ya fara gaishe ta cikin muryar sa mai dadin sauraro da sanyi, yace, "saukar dazu wallahi, na same ku lpy,"
"Yasu Anty Fati, da lagos din,"



dagowa nayi, sai a lokacin na kalle shi, Saurayi wanda bazai wuce shekara talatin da wani abu ba, Sanye yake da wando Jean baki, sai jar t-shirt mai gajeran hannu idon sa sanye da farin glass da alamu medical ne. wato na ciwon ido ko na taimaka maea gani, Fari ne dogo yana da fadin kirjii, dan a bude yake daga sama, idanun sa manya ne duk da a lumshe na gansu, amman ta tsagar su da tudun dasuke kadai zaka san manya ne, hancin sa dogo ne siriri kuma, sai bakin sa dan madai daici, yana da saje a kewayen fuskar sa, sannan gashin kansa a kwance sai kace na indiyawa, hannun sa duk gashi ne a kwance luf luf, ke daga fatar sa zaki san hutu yana wajen sa da sai wani sheki take.
A rai na nace "badai Ya Haidar dan gidan Anty Fati bane," amman sai nayi shiru.

Sai da suka gama gaisawar, sannan Ummu tace, hafsat kin gane kuwa Yayan naki,"
Na dago nace, "A'ah,"
"Toh Aliyu ne, dan gidan Anty Fati ta lagos,"
"Gaskiya Ummu ya girma,"
Baki Ummu ta rike dan mamaki na wai ya girma, shi bai ce na girma ba sai ni, hararata yayi, yace,
"Ummu kina jin ta ko, wai na girma,"
"Ina ji, Hafsat ina zaki kai son girma ne,"
"Kai Ummu da da suke zuwa ai baifi haka ba," na fada ina nuna dan tsayin sa,
Dariya ma ta bawa Ya Haidar, yace, "ke kuma lokacin kina tsumma kenan ko,"
Nima hararar sa nayi, "ina tafiya wallahi ko Ummu?,"
Sallamar su Hauwa da Faiza ce, ta katse maganarvda Ummu tayi niyyar yi.

Suka shigo suka gaida su Ummu dasu Ya Kamal, Ummu fita tayi, Ya Kamal kuwa gefen Faiza ya koma suna magana kasa kasa,

Nace, "Amarya yau kumanina zaku,"
"Ina zamu dai, dinki zami karbo, sai gidan su Khadija da muka manta bamu kai mata kati ba goran dutse da Zainab kurna,"
Ido na zaro kace zamu sha yawo dai, amman dai tare da driver kuke ko,"
"Ina fa da napep muke tafe.



MS Indabawa
MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY


BY MARYAM S INDABAWA
MANS


page 17





Dis page is ur Maryam Yusuf, u are d best, love u babe, d best reader of Mijin Ummu nah, u love like dis novel as u always love my novels tnx u...






Hafsat ta dago ta kalli Ya Kamal, ido suka hada da Ya Haidar da ya zuba mata narkakun idanun sa, sunkuyar da kan ta tayi da sauri, sai can tace, "Sis kinga Ya Haidar, dan gidan Anty Fati fa, yar Ummun mu,"
Hauwa ta dago ta dubeshi da fara'a suka kara gaisawa, tace, "kuma fa Sis kuna kama,"
Nace, "haba jini ne dai,"



Hira suke tabawa da Ya Haidar da Hauwa,
"Amman dai yakama mu tafi kada dare yayi mana ko tinda ba driver a hannun mu," na fada, ina mai shigewa dakin, ruwa na watsa sannan na canja wata doguwar rigar, mai na dan murza sai turare da powder da na shafa kadai. Falo nayo rike da mayafi a hannuna.


Ya Kamal da Faiza sai soyewa suke, hakan yasa Ya Haidar da Hauwa fara hirat jefi jefi, ina fitiwa nace, su tashi mu tafi, wani kallo Ya haidar ya bini dashi, wanda har sai da na tsargu na yafa mayafin hannuna,
Ya Kamal ne yace, "wallahi Hafsy Kin fiya haxari, ki har mu muyi hirar mu mana, ko dan ke baki san dadi abin ba,"
Harararsa Hafsat

Please Login or Register in order to submit comment