Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hira kuma ta balle.
"Zak mun kusa yin kudi fa."
"Ah haba Bahbah."

"Allah wata yarimya Hafsat yar gidan matar Baba Umaru. Wacce in sunzo muke zuwa leken ta."
"Na gane ta. Wannan ajebotar yarinyar ga kyau ga kudi da ilimi."

"Yah ita wallahi. Ita zan aure."
Hhhhh ya bushe da wata mahaukaciyar dariya.

Kallon sa Shehun ya tsaya yi dan ya fuskan ci dariyar rainin wayo ce
Sai da yayi mai isar sannan yace.

"Haba Shehu, Ina kai ina wannan yarinyar ai ruwa ba sa'an kwando bane. Baka ganin wannan yarinyar ko ya'yan masu kudi da ilimi bata kula wa bare kai kana fama da jahilcin ka."

"To naji in za'ayi bikin karka zo ko ka hana. Kuma kason da nai niyyar baka na fasa."

"Ah haba Aboki. Ayi maganr fahimta man."
Nan ya fede masa duk yadda sukai da Baba Umar. Sosai zak ya tausayawa yarinyar.

Sai cewa yayi.
"Allah tabbatar da alheri."
"Ameen dai. Amman naga jikin ka yai sanyi."

"Abar nan ce ta fara aiki." Ya fada yana nuna abinda yake shaka.






Hafsat ce zaine da bokitin ruwa a gabanta sai kur'ani a gefen ta.

Lokacin ta gama musu tofin ayoyin da Ya Haidar ya bata.

Dakin su ta shiga ta ajiye shi. Sannan ta dibi wani a kofi ta kaiwa Ummu ta sha. Sannan ta bata ta gane jikin ta dashi.

Dakin ta koma ta sha tai tsarkake jikin ta dashi.

Sai na Khadija da Khairat.
tana cikin cire kayan ta tajiyo muryar Ummu na kiran ta.

Fitowa tayi tana amsawa.
"Kije shehu ne yaxo wai yana son magana dake.
"Shehu kuma ummu?"

"Eh!"
"Ai ban gane wanne Shehun ba."

"Oh dan gidan yayar Abban Khairat."
"To" ta fada.

Ta koma daki ta sako katon hijab din ta.

A babban Falo ta same shi zaune. yaci wani yadi sai tashin warin wiwi yake.

Murmushi yayi da yaga shigowar ta.
Gefen kujera ta samu ta zauna.

"Ina yini?"
"Lafiya Ya gida."

"Lafiya lou."
"Uhmm daman wata magana nazo da ita."

"Ina jinka."
"Daman ba komai ya kawo ni ba sai nazo na fada miki ina sonki ne. Kuma aure nake son muyi."

"Allah sarki! Sai dai kayi hakuri dan akwai wanda nayiwa alkawari. Sai dai zan maka adduar Allah baka mace ta gari."

Fuska ya hade ya wani sha kunu yana muzurai irin na yan daba.
"Ina bazai yiyu ba. Ni ke nake sso kuma ke zan aura. Kinji na fada miki ko kuma ki tsaya ki zuba ido ki gani."

Ya fice kamar zai tashi sama.

Murmushin takaici tayi dan tasan wanda zai turo shi.

Tasan ba kowa ya saka wa Shehu wannan tunanin ba sai *Mijin Ummun tah*

Dakin Ummu tayi ta fada mata duk abinda ya faru.

Ita ma Ummu murmushi kawai tayi tace,
"Ki kwantar da hankalin ki. Ki dage da addua Allah yana sane dake."

"Kinsan dai Ba wanda zai miki auren dole bayan an riga ma da an gama magana da iyayen Aliyu. Addu'a zaki kara mikewa da ita. Nima zan kara mikewa tsaye."


"Nagode *Ummu nah* " ta fada tana mikewa tayi daki.

Lallai Abbi u.yanzu na kara sanin ba son mu yake ba. In ba haka ba taya ana son auren miji na gari zai turon shehu.

Zuciyar ta taji kamar zata buga dan zagi da bugun da take mata.

Al qur'ani ta dauko ta fara karantawa. Dan tasan shine magani komai a rayuwa.

Tasan shi zai yaye mata duk abinda take ji da bakin cikin zuciyar ta.

Tana fara karantawa ta nemi abunda take ji ta rasa.





*INDABAWA*
08062882472
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY






BY *Maryamm S Indabawa*
*Mans*





??HAJOW????

??‍??‍????‍??‍????‍??‍?? HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍??✍??✍??





Page *42*






Sister tah *Surry Arab* love u.

Ummu sudais. Allah kara mana dangon zumunci Ameen












Ummu ce ta leko, ta hange ta rike da Al qur'ani. Bacci ya dauke ta.

Karba ta yi ta maidashi ma ajiyar sa sannan ta fita.

Sai wajen magariba ta tashi. Alwala tayi ta tada sallah.

Bata tashi akan sallaya ba sai bayan isha'i.

Kitchen taje dan samun abinda zata ci.

Kwai ta tasa ta soya shi. sannan ta hada kunun alkama ta zuba masa madara da sugar.

Daki taje taci sannan ta kunna kallo.
Wayar ta ce tayi kara dubawa tayi,
Ya Haidar ne.

Cikin sanyin murya ta amsa mishi.
"Baby na lafiya kuwa?"

Abinda ya tambaye ta kenan dan jin muryar ta wata iri.

"Lafiya lou. Nayi bacci ne."
"Ok amman muryar ki tayi sanyi sosai fa."

"Kar ka damu."
"Dole na damu man."

"Hmm yasu Mamana."
"Lafiya lou."

"Ya aiki?"
"Alhamdulilah! Ya makaranta."

"Lafiya Alamhamdulilah."
"Baby na sauran kwana nawa ne?"


"Me fa?"
"Ki zama mallakina."

"Ai yanzu ma taka ce ni."
"Haba da gaske?"

"Eh saura wata nawa."
"A'ah ban son zancen wata. Sati nawa zaki ce."

Dariya tayi. tace,
"To saura sati nawa?"
"Sati sha biyu."

"Ya Haidae kenan wata ukun dai kenan."
"Hmm ai ban san a ce watan ne. So nake naji an fara cewa sauran sati ko kwana kaza."

"Rai dai!"
"Haka ne, Allah nuna mana da rai da lafiya Ameen."

Sukai sallama.





Ko da Abbi ya zo Ummu ya rufe da fada dan me Hafsat za tayiwa dan yar sa haka to wallahi shi zata aura.

Ummu dai shiru tayi tana mamakin yaushe Abbi ya koma haka dan duk sai yanzu take ganin wasu dabi'u nasa. Dan duk abinda ya faru bata cikin hayyacin ta.

Jin take kamar a mafarki abun ya faru shiyasa take mamakin in taga yana wasu halaiya na daban.

Har ya karaci fadan sa da nuna isar sa ta sai Hafsat ta auri zabin sa

Kala Ummu bata ce ba sai kallo da ido kawai.

Shi a tunanin da ta dauka kamar yadda in yace abu kaza ne zata ta yadda ko va haka bane.

Gidan ya fice ya bari.

Ummu har gun Hafsat taje ta fada mata yadda Abbi yace.

Hafsat taso ta daga hankalin ta amman Ummu ta kwantar mata dashi tace,

"Hafsat kar ki damu kullum buri na da Addua ta ki samu miji na gari mai hankali wanda zai rike min ke amana to Allah ya amsa addua ta kuma nayi istahara naga da alheri dan haka ba abinda zai biyo baya."

Sai da ta gama lalabata da magan ganu masu dadi sannan ta kawo hiran abubuwan da take bukata na kammala karatun ta da aure.

Lissafa mata tayi suka qirga kudin da zara bukata.

Sannan da yadda biki zai kaya.


Kudi masu yawa suka kirga.
ummu tace,
"Hafsat baza a taba muku kudi ba. Wannan yasa na siyi filaye wanda in bikin ku ya tashi baza a taba kudin ku."

"Haba Ummu wai menen amfanini kudin namu? Shin wai abun mu ba naki bane."

"Ba haka bane Hafsat. Ai nauyin ku akai na yake ni ya kamata nai muku ba kuba. In nai muku da kudin ku kamar ku kukai ne."

"Ummu ni fa na dade da cewa ki amince ki karbi kamfanonin nan mun baki amman kin ki."

"Kul na hane ki da kara tada maganar na. bani da burin da ya wuce na gan ku cikin kwanciyyar hankali da farin ciki. Yanzu in kun bani na mutu fa. Wanda bai cancanta ya shiga cikin dukiyar ku ma shiga zaiyi."

"Kiyi Hakuri Ummu."
"Baki kin komai ba. Allah miki albarka."

"Ameen."
"Aliyu ya fada mike ne. Nan da wata daya zasu je yin order kayan dakin ki. Anty Fatima wai dole sai naje."

"Mama Fati kenan. Sai Kije ai."
"Eh amman sai naga tashin ku tukkuna."

"Tashin mu kuma Ummu."
"Eh na biya muku umra keda Khadija da Khairat zakuje. in kun tafi sai mu hadu mu dawo tare lokacin sauran sati biyu kuyi final exam,"

"Masha Allah! Alhamdulilah! Ummu. Allah saka Miki da alheri yasa ki gama lafiya. Ameen "

"Kar ki damu."
Rumgumeta Hafsat tayi tana mai jin farin ciki a zuciyar ta.




Tin da taji zance tafiyar su ta mai da kai kan karatun ta dan tasan in har sunje can ba lokacin karatu sai na ibada.

Dan bata manta zuwan su da Abbu da yace,
"Hafsat duk lokacin da kika ganki anan kada kiyi wasa da damar ki wajen yin addu'a. Ba ga ke kadai ba ga duk yan uwa musulmai. Nayi duba naga sai dai ban riku abu anan ba amman da na roka Allah ke amsa min. Dan haka ki nemawa kanki rayuwa mai kyau da inganci."

Allah Sarki Uba na gari. Duk da ina da qarantu shekara Abbu ya rasu ina tuna abubuwa masu mahimmanci da yake horata akan su.


Akwai shi da daura mu akan yin ibada. Dan in munce ya kai mu Landon sai yace.
"Hafsat me za kuyi da landon bayan ga kasa mai tsarki wacce za kuje kuji ni'ima da dadi ga ibada."

Akwai shi da so wa yan uwa musulmai abida ya sowa kan sa.
ya kance,
"Ki fara yiwa yan uwa Musulmai addua kafin kiyi wa kanki. Dan da kin musu mala'ikun rahama zasu rokar miki abinda kika roka musu. Ki kasance mai so da tausayin duk wanda bai dashi. Ba ki kyamace shi ba."



Hawaye ne ya zubo mata tuna hirar su da ya kusa mutuwa.







*INDABAWA*
08062882472
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY






BY *Maryamm S Indabawa*
*Mans*





??HAJOW????

??‍??‍????‍??‍????‍??‍?? HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍??✍??✍??





Page *43*






Dedicated to our group *Huh bro nd Sister* love u my bro nd sis.

May Allah bless u all
*Ameen*


Dis group always make me happy if iam wit u.

*Abnah! Ya Baby! Naz! Abbah! Nana! Lovellyy sisto Nusy!*

Love you guy.







Hawaye ne ya zubo mata tuna hirar su kafin ya rasu.
"Hafsat kiyi koyi da halin mahaifiyar ki. In har kika yi koyi to zaki zauna da kowa lafiya. Mijin ki zai ta sa miki albarka. Allah zai buda miki ya yaye miki kunci tunda kina farantawa iyayen ki da mijin ki. Nasan Mahifiyar ku zata kulamin da ku ko da bayan rai na ne. Nasan kina da hankali da nutsuwa."


" Kiji tsoran Allah kiyi wa Allah biyayya kiyi duk abinda ya wajabta ki nisanci wanda yayi hani dasu. Ki kula da mahaifiyar ki da tasha fama daku kuma nasan nan gaba ma zata yi daku."

"In na mutu kuna min addu'a kamar yadda Ummun ku ke sa kuna wa mamata."

Zuben hannuna na shafa. Na goge hawayen ido na.


"Allah Sarki *Abbunah* Allah ya maka rahama."


Uba ya nunawa ya'yan sa so da kulawa shi ke sa ko da ya dade da mutuwa kullum yana ransu har ta kai ga irin zaman da kuke tsakanin ku da hirar da kuke kuna tunawa.

Duk da lokacin ina yarinya *Abbu nah* ya rasu ina tuna wasu lokutan da muke tare kamar yadda yanzu na dinga tina wa sai kace a lokacin yake fada min.

Ko Ummu na kukan mutuwar *Abbu nah* har yazu kullum addua'a take masa.

Yanzu da bai kula da ita ya bata ingantaciyar rayuwa ba zata na masa addu'a.

In da ya zalunce ta ko ya musguna mata in ta tuna dashi sai dai tana cewa.
"Gara da ya mutu."

Ya'ya suna murna babu dodon su. Eh dodon su man dan yadda yake daure fuska da cin magani kamar zai doke ka.

Ta dade tana raya yadda rayuwar jama'a ke ciki da yadda tayi tata rayuwar

Allah kawai take godewa dan tasan ba wanda yai mata hakan sai shi kuma shi keson ganin ta haka.

Aka ce "Allah baya barin wani dan wani yaji dadi."
Haka yake dan da ya bar musu Abbun su mai son su da kaunar su.

Ganin damuwar zata iya tayar mata da matsalar ta yasa ta mike tayo alwala ta kara yin sallah tai tayo wa mahaifin ta addua da yan uwa musulmai. Ta rufe da karantun al qurani.

Tana iddar wa. Wayar ta tai kara.
Ya Haidar ne.

"Assalamu alaikum!"
"Wa'alaikum salam!"

Ta fada muryar ta a sanyaye.
"Baby nah lafiya kuwa."

Kukan da take dannewa ne yaci karfin ta, ta fashe dashi.
"Ya Salam! Kiyi hakuri ki fada min damuwar ki namiki alkawarin zan kawar miki da ita in kuma tafi karfi na zan kiki addu'a Allah ya yaye miki."

Lallashin ta yai tayi har ya samu ta daina kukan.

"To fada kin menene?"
"Uhmm *Abbu nah* na tina."

"Allahu akbar! Kiyi hakuri Hafsat duk mai rai mamaci ne. Allah yafi mu son shi shiyasa ya dauke shi. Abinda zaki taya shi da ita. Shine addu'a. Nima na miki alkawarin duk sallah sai na masa addu'a ki daina kuka. Abinda kin kusa ki haifi takwaran sa shima yana taya shi da addu'a."


Kunya taji. Ta rufe idon ta tayi shiru.

"Kina ji na?."
"Eh!"

"Ko ba kya sone?"
"A'ah!" ta fada a hankali.

Ya gane kunya take ji. Amman yasn ya rage mata damuwar ta.

Hira ya dinga jan ta dashi. sannan yake fada mata tafiyar su waje shi da Ummu da Momyn sa.

"Baby na naso dake zamu to Ummu tace Umra zakuje kuyi. Amman zan mana zaben kayan daki sannan zan turo miki dan ki zaba da kan ki."

"Lah Ya Haidar ni ba sai ka turo ba."
"Oh bakya son ki zava mana gadon da zai daule mu ba gajiyawa."

"Ai kowanne ma zai dauke mu!"
"Na fison zabin ki. Dan kinsan akan shi zamu more amarcin mu."


"Ya Haudar!" Ta fada a shagwabe.
"Na'am ai nasan kina so ko."

Shiru tayi.
murmushi yayi.
"Kinsan me?"
"A'ah!"

"Dady ya siya mana gida a kano wai in munzo. Dan haka ke zaki zava mana kayan cikin sa. Ni zanyi mana xabin na lagos."


"Su Ummu sa zaba. Amman ni ko wanne Allah sanya albarka."
"Wallahi kina burge ni. Ina sonki."

"Dare yayi kije ki kwanta gobe da Makaranta."
"To Ya Haidar Allah tashe mu lafiya."

"Ameen!"



Addua tayi ta kwanta da mafarken sahibinta.









*INDABAWA*


FOR COMMENT AND CORRECTION
08062882472
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY






BY *Maryamm S Indabawa*
*Mans*





??HAJOW????

??‍??‍????‍??‍????‍??‍?? HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍??✍??✍??





Page *44*




Dedicated to u *AINAU* Love u sis.





Abbi bai karawa Ummu maganar ba haka nan ita ma ko a fuska bata nuna masa bacin ran ta ba.

In ban da kudi da yake tasar ta. Ita kuma ta biye masa tana bashi duk dan ta nuna masa ba wata matsala.


Karatun Hafsat ya kara ja dan yanzu har sunyi covering abubuwa da yawa saura wata daya da sati biyu su fara Jarabawa.

Sam Ummu bata kara nuna masa ma an kawo kudi da sa ranar Hafsat ba dan ko tafiyar su so yayi ya hana. Ummu tace ba ita ta biya ba.




A lokacin su Hafsat kuma suka mika kasa mai tsarki. Wanda washe gari Ummu ta dira a lagos dan ta can zasu tashi.


Tinda Hafsat suka isa ba abinda take sai ibada dan Khairat da Khadija kan shiga kasuwa da Zaga garin.


Amman Hafsat kullum tana harami. Addua'a kuwa kowa ya sha ta. Tayiwa al'umma musulmai. Sannan tayiwa *Abbun tah* da *ummun tah* khadija Ya Haidar kawayen ta. Ba wanda bata saka ba.

Su Ummu kuwa suna can suna zabar mata kayan dakuna.

Inda Ya Haidar ya zaba mata masu kyau da tsada. Banda uban kayan lefan da suka hado.



Hafsat ta kara kyau ga fatar ta ta kuma gogewa kai baka ce ba balarabiya bace.

Jikin ta ya murje kwayar idon ta ta kara kyau da haske.


Satin su biyu suka tura kaya gida sannan suka wuce makkah dan su taho tare dasu Hafsat.

Tinda Ya Haidar ya daura ido akan Hafsat ya kasa dauke wa. Dan ta gama tafita da tunanin sa.

Ita kam tana can tana ta murna zuwan su. Tana jikin Momyn sa a kwance.

Gyaran murya yayi. Yace,
"Amarya ta ni ba ai min sannu da zuwa ba."

Rufe fuskar ta tayi a jikin Momyn sa.

Mikewa Ummu tayi ta nufi dakin su, ita ma Momy bayan ta tabi.

Da sauri ta mike dan tabi bayan su amman ina har ya kamo hannun ta.

Bata jiyo ba. Janyo ta ya farayi. Har ta karaso gaban sa. Juyo da ita yayi.

Ido ya kara zuba mata ya kasa dauke wa. Ganin tsaiwar tasu tayi yawa yasa ta daga ido taga me yake yi.

Caraf idanun su, suka hade da na juna. Kasa dauke nata tayi. Dan shima ba karamin canjawa yayi ba.

Sallamr su Khadija tasa suka dawimo hayyacin su.
"Lah Ya Haidar kun iso? Ina su Ummu?"
"Suna daki!" ya fada a sanyaye.

Wucewa sukai. Shi kuma ya.samu kujera ya zauna.

Wacce ke kallon sa itama ta zauna akai.

"Baby na kin kara kyau fa."
"Kai ai kullum haka kake cewa."

"Eh! Naji ai gaskiya na fada."
"A'ah!'

"Au karya nake yi."
Ido ta zaro. Kallon ta yayi sai yaji ta kara burge shi dan in ta zaro ido wani kyau take karawa.

Ji yake kamar yaje ya sumbaci idan.amman kuma yasan ba kyau.

"Taya zan ce kayi karya."
"To baga shinan ba."

"A'ah! Kayi hakuri."
"Wasa nake miki."

Mikewa tayi.
"Ina kuma zaki."
"Harami nake son zuwa."

"Me zakiyi."
"Ibada da addu'a."

"Allah amsa! Amman ki kwantar da hankalin ki. Kar ki tada hankalin ki da addua akan kshiya ke kadai ce ba kari."

Ya fada yana kashe mata ido daya. Juyawa tayi ta tafi dakin su Ummu tai musu sallama.

Tare suka fita. Basu suka dawo ba sai bayan isha'i.



Haka suka cigaba da rayuwa har suka sati daya. Kasuwa suka kara shiga suka siyayya inda Ya Haidar yai ta lodo mata kaya banda English wear da Arabian.

Kai kace lefe zai hada ko ya manta wadan da ya lodo ne oho?



Lagos su Momy suka wuce inda Ummu da su Hafsat sukayo Kano.

Tinda suka dawo aka Momy ta aiko musu da me gyaran amarya.

Gyara ta ake sosai dan in an bata abu kin ci take sai Momy tayo waya ta bata hakuri sannan take ci.

Sosai ta kara kyau kamar ka taba ta jini ya fito jikin ta sai laushi da kamshi kamar an mata wanka a cikin turaren.

Kowa ya ganta sai ya yaba da yadda ta koma wannan yasa take saka nikaf.

Hauwa Kam ana can ana shirin tawowa bikin aminya kamar yadda Faiza take jin kamar ta jawo ranar.

Ana cikin haka suka fara jarabawa. Gyaran da ake mata ta cigaba dayi duk da tace abar ta ta gama jarabawa amman akace aah.


Jarabawar su lafiya suka kammala inda sukai shirye shirye sun hada party da dinner ta ya. department din su.

Lokacin ya kama ana sauran Wata daya biki.



Ana sauran kwana biyu ya dira a Kano dan yana son taya matar sa farin cikin kammala karatun ta.

Duk yadda yaso ya ganta bai samu dama ba sai ranar da za ayi program din.

Da ba dan yasan Hafasat tin tana karama ba da bazai gane ta ba.
Dan hakan ma sai da ya tsaya tantamar itace ko ba ita bace.

Wata make up akai mata wacce ta kara fito da kyan ta. wata pink din doguwar riga tasaka ta yafa bakin mayafi. Tasa bakin takalmi.


Ya Kamal ne yai gaba dasu da su Faiza da Hauwa inda daga baya su Ya Haidar suka iso.

Shi ya rasa saboda me ake masa rowar ganin ta da son kebewa da ita.
Bai san Momy ce ta hana ba. Dan kin yadda ma tayi yazo sai da yasa mata kuka wannan yasa tabarshi.

Hafsat na daya daga cikin daliban da suka samu kyaututuka masu yawa dan kowa na yaba halin ta da kokarin ta.

Sunyi taro tafiya inda washe gari suka gudanar da dinner su.

Ita da Ya Haidar da Su Faiza suka je. Sosai wajen ya kawata inda aka ci aka sha sannan suka yi hoto nan ban kwana.

Shi dai Ya Haidar sai dai yai ta binta da idanu kamar ya tashe ta ya kaji.






*INDABAWA*



For comment and correction 08062882472
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY






BY *Maryamm S Indabawa*
*Mans*





??HAJOW????

??‍??‍????‍??‍????‍??‍?? HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍??✍??✍??





Page *45*







Dedicated din page to u *preety nah* *Maryam Zamfara* love u Sweet


Allah kan hada soyayyar ka ga wanda baka sani ba. Kamar yadda ya hadano da mutane da dama a ciki har da ke namesake dina.

Allah daurar mana da zumuncin mu Ameen.







Ana gama wa Momyn sa ta dinga masa waya kan ya dawo. Dan akwai abubuwan da yake ga rabon kati.


Lokacin da zai tafi yaje mata sallama.


Tana zaune a dakin ta bayan an gama mata shafe shafe tayo wanka. Wani hadin aka bata take sha wanda madara ce rabin hadin.

Babban Falo yaje sukai sallama da Ummu sannan ya wuce falon su.

Da sallama ya shiga. Mikewa tayi da sauri dan dauka hijab. Duk da rigar jikin ta mai dogon hannu ce, kan ta kuma sanye yake da hijab iya kirji.

"Ina kuma zuwa?"
Shiru tayi dan in tace Hijab tasan zai zaci ta masa mumunar fahimta ne.

kuma tayi ta zauna. Tace,
"da lemo zan kawo maka."
"Amman ai kya bari mu gaisa ko?"

Ya fada idon sa a kanta kamar zasu fado kasa.
kai ta sunkuyar.

Kofin gaban ta ya dauka ya sha abinda ke ciki.
"Uhmm Baby nah kina shan dadi fa, mene wannan?"

"Nima ban sani ba."
"Kike sha kuma."

"Eh! Ai ba abin cutar wa bane."
"Eh! Daga dan danon sa ma ya nuna hakan."

Shiru sukai shiru

"To Mene shirye shiryen ki."
"Sai dai ka tambayi su Hauwa da Faiza."

"Shikenan zan masu magana. Baki da matsalar komai dai ko?"
"Eh!"

Ta daga masa kai. Wata jaka ya mika mata.
"Ga wannan zan turo muku da kudin da zaku bukata. Wannan naki ne ko akwai abinda zaki na gyara da dai sauran su."

"Ya Haidar ni ba abinda zanyi da kudi yanzu."
"Hafsat ni na baki kuma dole ki amsa. Kin manta ni yayan kine ko ba wani abu tsakanin mu ai zan miki kyauta bare kuma gashi zan zama mijin ki."

"To nagode Allah kara budi yasa ka gama da iyaten ka lafiya."
"Ameen nagode."

"To ni zan tafi. Sai nan da sati zuwa zan taho."
"Allah kawo ka lafiya."

"Ameen!" Ya fada yana mikewa.

"Allah kiyaye hanya."
"Oh baza ki rakani ko bakin gate ba."

"A'ah!" Ta fada tana mikewa.

Ummu sukaje yayiwa sallama. Sannan suka nufi gate.

"Toh Babyn zan tafi sai kuma lokacin biki daga nan sai gida na."
"Allah kaimu Allah."

"Sai mun hade kenan."
"Ya Haidar ka rage zumudi fa."

"Saboda me?"
"Kar wani abu ya faru, kaga lokacin da ka tsara naje gidan ka banje ba."


"Kamar ya kenan?"
"shikenn dai amman ka rage kaji."

"Shikenan zanyi kamar yadda kika ce."
"Nagode. Allah kiyaye hanya Ameen."


"Love u bye."
"Aha."

Ya fita ya hau motar Kamal suka tafi Airport.

Yana isa ya kira Hafsat.


Sannan sukai gida.
Momy yaje yasawa rigima, wai shi gaskiya a rage lokacin bikin.

Kallon Mamaki ta tsaya yi.
"Haidar me yake damun ka ne? Naga bikin saura sati uku to mene na ragewa."

"Wallahi Momy hankali na ne yai wajen ta gaba daya so nake, kawai naga an daura kar wani abu ya faru."

"Kada ka damu insha Allahu ba abinda zai faru sai alheri."

"Allah yasa!"
"Ameen!"

"Tashi kaje kai wanka kazo kaci abinci."

"To Momy amman zan dan kwanta."
"Toh saika fito."

Dakin shi ya shige. wanka yayi sannan ya haye gadon sa. Bacci ya dauke shi.

Bashi ya tashi ba sai bayan sallah la'asar.

Wanka ya karayi sannan yayo alwala yai sallah. Ya sauko kasa.

Momy ya tarar a zaune.
"Son ka tashi."
"Eh!"

"Tashi muje kaci abinci."
Ta fada tana mikewa. Bayan ta ya bi.

Ita ta zuba masa sannan ta dinga bashi. bashin da take ne yasa yaci sosai.


Daga nan ya fita wajen abokin sa ya kai masa katin daurin aure, dana dinner.

Sannan yaje yasa a gyara gidan su Hauwa dan jibi Ya Kamal zai taho.






*INDABAWA*



For comment and correction
08062882472
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY






BY *Maryamm S Indabawa*
*Mans*





??HAJOW????

??‍??‍????‍??‍????‍??‍?? HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍??✍??✍??





Page *46*





Dedicated to u Rukky yakasai u re among of the people dat we meet on social media.

Love u Rukky. wish u all the best.








Komawar Ya Haidar da kwana biyar aka kawo lefe.

Lefen da kowa ya gani sai ya yaba da dukiyar da aka kashe mata.


Dan akwatin nan ma kansu abun kallo ne bare kayan ciki.
gwala gwalai a ciki wajen guda 6.

Dagin Abbu sosai suka taya yar su murnar.


Lokacin Abbi baya nan dan bai san komai game da auren ba.

Shirye shirye ya dau zafi. Dan har rabo yayi nisa. zasu yi Children day sai kamu da yinin Ummu da dinner shikenan.

sannan Za ayi, dinner a lagos.



Sauram sati biyu biki Abbi ya dawo gida. A ranar ya daga mana hankali dan shi yace dolee sai shehu zan aura.

Wannan abun da yayi ba karamin ta da min hankali yayi.

Dan tin daga ranar na fara jin canjin kirjina yai nauyi ga wata faduwar gaba da nake sai zazzabi.

Ummu sai hakuri take bawa Hafsat amman Da ta bar wajen zata kara koma wa cikin tunani da damuwa.

Ya Haidar Yayi tambayar duniya amma ban fada masa. Har Ummu ya tambaya tace ba komai. Dan bata son ya sa damuwa shima a ransa.


Sauran sati biyu Hauwa ta dawo gidan mu. Dan Ya Nura tare dasu Ya haidar zasu taho.

Mai gyara Momyn Faiza ta kuma kawon ni duk na gaji da murje murje nan da shaye shayen.

Amman sai ai ta matsa min. Dole nake hakura nasha.

In na fadi yadda na koma sai abin ya bada mamaki sosai. Na cuko kirji na ya daga sosai haka hip din sun kara fito wa.


Jiki na yai laushi sai kace ballo, gashin kaina ya kara fito wa. Ido na ya dada haske da kyau. Bakina ya koma ruwan hoda.

Komai na jiki na yayi kyau. sai dai ni kadai nasan me ke damuna a cikin zciya ta

Dan ranan naga wani sako ya shigon ba na kowa bane sai na Shehu yadda ya jadada min yake in naga ba ai bikin nan ba to mutuwa yayi.


Ranar kuwa nasha kuka. Kamar raina zai fita. Dan ina mamakin wannan wane irin abune.



Haka na dinga jure abinda ke damu na. Har Ummu ta fahimta tace muje asibiti amman nace aah.

Duk matsawar da tayi naki.


Ana sauran kwana biyar fara biki

Please Login or Register in order to submit comment