Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ya Haidar ya iso. Ran talata aka zo i akai mana lalle ja da baki. Sosai sukai karan kyau dan ya zanu. Gashi ya hau kan farar fatata.


Gidan da Dadyn Ya Haidar ya bashi ya hadu dan wadan da suka kai kaya naji suna ta zuzuta gidan.

Wasu na cewa aljannar duniya.
Kanin abbu na ya shiryammin daki daya da falo.

Gyaran gashi da komai anyi. Ranan laraba akai children day. Mai kwalliya aka dauko tazo tai mana kwalliya.

White gown ta amare na saka Ya Haidar yasa suit baka. Yara akai musu orange din riga da bakin wando.

Su Faiza da Hauwa, ma sunyi kyau haka su Ya kamal da Ya Nura.

Khadija da bishira ba sun yi kyau anyi barin kudi an sha rawa.
Sai sha daya suka tashi.


Ranar Alhamis akai kamu, wani yadi ta saka wanda duk jikin sa stones ne. Mutli colour. nai adon ja. head takalmi da mayafi.

Tana shiga ganin taron jama'a yasa ta fashe da kuka. Ummu ma kukan ta fashe dashi ganin ga ranar auren ta amman Abbun su baya nan.

Kowa yazo yan uwan Abbu na ma duk sun zo.

Ranar ansha kuka kamar me.
Ranar an yi kamun gargajiya in da aka raba mufici da kaski da turarukan ruwa.

Ranar juma'a akai yinin Ummu. amarya tai kyau cikin purpke din material me kyau. Ranar ma idanun ta jawur.

Inda Mutane suka halarta sosai amarya tayi kyau kamar ka sace ta ka gudu.


Amman ita kadai tasan ciwon da take ji.


Asabar akai dinner. Har Abokan Ya Haidar sun zo inda amarya ta saka pink din kaya da adon milk. Ango ya sha milk din shadda.

Fadar irin kyau da kudin da aka kashe bata lokaci ne.

Ya Haidar duk ya zuba mata ido dan ya kasa dauke idon sa. Sannan daga ganin ta yasan akwai abinda ke damun ta dan yaga yadda take dafe kirji ko dan cije baki.


Kasa yin shiru yayi,
"Baby na lafiya kuwa?"
Dagowa tayi ta kalle shi.

Murmushi ta saki,
"Ba komai."

"Anya kuwa Baby. Kinga idanun ki sun fada."
"kar ks damu kirji ne ka ciwo kawai."

"Muje asibiti kenan."
"A'ah! Zai daina ne."

"To kinsha Maganin kine."
"A'ah in an tashi zan sha."

"Allah sauwake.!"
"Ameen!"

"Gobe fa za'a kai min ke ko."
Murmushi kawai tayi.

"Baby na gobe kin zama mallakina."
"Ya Haidar ka bari man."


"Shikenan nayi shiru."
Hannun ta ya kamo yana taba zanen lallen ta.

"Abin nan yayi kyau."
"Ya Haidar ka bari."

"Dan na yaba da kyan lallen."
"A'ah rike hannun nawa da kayi."

"To na saki shikenan."
Kai kadai na daga.






*INDABAWA*
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY




By *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*





🌐HAJOWπŸ“πŸŒ

πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§ HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾








page *47*






Ranar Lahadi daurin aure tin Asuba Hafsat ta tashi da wani matsanaicin zazzabi ga ciwon kai.

Daurewa take har akai mata kwalliya.

Shigowar Abbi ita ta kara ruda ta. Dan tana falon Ummu a zaune, ya shiga.

Cikin bedroom ya shige Ummu ta bi bayan sa.

Ina daga falo na jiyo har gagin sa.
"Kin jini ko. Wallahi yanzu zan je kuma sai na sa an daura da Shehun da ba kwaso. Dan haka ki kira ma ki fada musu."

Daina ji komai tayi. Ji tayi ta daina gane komai sai ta fara kokawa da numfashi ta fadowa tayi daga kan kujera ta kife a kasa. Numfashin ta ya dauke.

A fusace ya fito a dakin ya fice a gidan ya sa Shehu ya shirta ya biyo shi dan agundin.


Karfe sha daya dai dai aka daura auren *Hafsat da Ya Haidar*


Dai dai isowar Abbi da Shehu, da abokan sa yan ganye.

Wajen kanin mahaifin Hafsat yaje,
"Ya dai ko an daura auren ne?"

"Eh! An daura ana ta jiran ka shiru."

Ido ya ware sannan ya hade rai.
"Dan me aja daura ba ajira ni ba."

Kanin mahaifin Hafsat ya zata kara zai musu sai yaga abin nasa kamar da gadara.
"Saboda ba kaine ma daurin auren ta ba."

"Haka kace?"
"Eh haka nace."


"Ai kam sai an warware auren nan,"
"Au Haba in kuwa kaga *Hafsat da Haidar* sun rabu sai dai mutuwa. Mutumin banza mutun hofi."

"Ni kake zaga."
"An zage kan."


Shehu na ya motsi dan jin me yake faruwa.
"Baba Umaru Lafiya?"
"Wai an daura aure. Nace a raba zai kawon zancen banza."

"Kut.... ya lailayo ashar ya an taya. Wallahi sai an kunce an maida dani."

Yayan Ummu ne ya karaso wajen jin hayaniya. Duk da wajen a cike yake ana farin ciki da murna.

"Ah Sagir! Lafiya?"
Ya tambayi Kawun Hafsat.

"Wannan mutumin ne yazo zai kawon zancen banza. Ni bangane shirmen da suke bama."

"Eh! Ai baza ka gane ba."
cewar Abbi.

Shehu ne yace,
"Eh! dani za'a daura auren ba da Wancan ba."

"Wa kenann?"
"Hafsat mana!"

"To ai Hafsat an riga an daura kuma kunsan an dade da bada ita sannan yanzu lokaci yayi."

"Wai Baba Ado mene na musu bayani. haka ake auren."
"A'ah bari a rabu lafiya."

Ya juya garesu.
"Kuyi hakuri Hafsat, Haidar ta kawo mana a matsayin mijin ta. Dan gaka kuyi hakuri."

Ya ja hannun Kawun Hafsat ya bar wajen.

Suna tsaye jigun jigun har suka bar wajen.

Reception suka tafi. A Mena Event center.

Inda ya samu halar tar manya manya mutane, da masu kudi.

Abokan Ya Haidar ba wanda basu zo ba. Hotuna aka dinga dauka.

Bayan anci ansha.

Bakin ya Haidar yaki rufuwa sai washe su yake. Su Ya Kamal sai tsokanar sa suke.

Shi dai hankalin sa na can wajen Hafsat. Ita kawai yaji yana son ya gani yaga a halin da take.

Har Dadyn Ya Haidar sai da ya fahimci farin cikin da Ya Haidar yake ciki.




Suna tsaye a wajen ya rage daga Baba Umar sai Shehu da abokan sa da suka ci wata waganbarin shadda.

"Gaskiya ka kwafsa mana daman kai bakai wani abu akai bane?"
"Kamar ya banyi wani abu akai ba."

"To gashi nan abu yaki yin dai dai."
"Rufe min baki kar ka bata min rai. Kasan duk abinda nayi ne."

"A'ah kar ka kara batan rai Malam."
"Ni kake cewa malam!"

"Eh an fada me zaka iya yi."
Mari ya kai masa ya rike hannun.

"Ah haba wallahi karya ne ka maren ina zaune lafiya lou!"
Hannun ya saukar kasa.

"Kasan da wa kake Shehu nake vana daukar raini ko na iyaye na."

Fuu ya juya ya tafi abokan sa suka bi bayan sa.

Zak kuwa farin ciki yake da Allah ya kubutar da rayuwar Hafsat daga tarkon su Shehu da *Mijin Ummun tah*










*INDABAWA*


For comment and correction
*08062882472*
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY






By *Maryam S Indabawa*
*MANS*




🌐HAJOWπŸ“πŸŒ

πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§ HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾





Page *48*







*Maman nur* tnc for ur love and supporting.
Really love u.
ur are not only a sister to me.

Allah raya miki su *Mufida, shahid! Nur and Hidaya*








Daga Nan Abbi ba inda ya nufa sai Kaduna. Zuciyar sa kamar ta buga.

To me yake faru me ya faru har Ummu ta kasa yin wani abu.

Ya dade yana ta tunanin mafita da abinda ke shirin faru.



Shi kuwa shehu dabar su suka tafi aka bude dabar shaye shaye dan ji yake kamar ya kashe kan sa.

Dan ya gama shirya abibda zasuyi da kudin sannan ya daura wa kan sa son Hafsat.

Dan yasan Hafsat ba kwanwar lasa bace.




Gidan Biki ana can ana ta kazar kazar amman ba Amarya dan tana dakin Ummu.

Ummu kuwa tin da Abbi ya fita bata fito ba tana daki tana ta kukan takaici da kadarar da Allah ya saukar mata.

Tafi awa biyu a daki tana sakawa da warwara wa. Har yayan ta ya kira yace an daura auren.

"Da wa?"
Tambayar da ta jefa masa kenan.

"Da Haidar mana."
"Toh Allah sanya Alheri ya bada zaman lafita."

"Ameen!"
Ta kashe wayar.

Sai a lokacin ta ji sanyi a ranta.
Falo ta fito bata hango Hafsat ba. Ta fice.


Dakin su Hafsat ta nufa. Su Hauwa kadai ta gani zaune.

Gefen su ta zauna.
"Ina Hafsat din."
"Tana dakin ki ai tin dazu."

"To kuma daga can na fito ban hange ta ba. Bari naje na duba ta."

Ta fita tayi dakin ta.



Karfe biyu bayan sunyi Sallah azahar. Angwaye sukayo gidan su Hafsat.


Ango ya ci wata ruwan omon shadda sai kyali take. Ta sha aiki sai bakar hula da takalmi da ya saka.

Tin a bakin gate suke gaisawa da mutane. Kowa sai Allah sanya alheri yake musu.




Ummu na shiga, ta hange ta a kife a kasa.
"Lafiya Hafsat!" Ta fada tana karasawa wajen.

Dago ta tayi, taga ba numfashi.
"Innlillahi wa'ina ilahir rajiun!"

Abinda tai ta nanatawa kenan.
firij ta nufa ta debo ruwa ta shafa mata.

Amman ko motsi ba tai ba. Wayarta ta dauki ta fara neman layin Kamal.

Dagawa yayi.
"Ummu gamu nan shigowa ma."
"Kayi sauri Hafsat ce!"
bata karasa ba ya kashe wayar yaja hannun Ya Haidar.

"Menene?"
"Muje ka gani."

Dakin Ummu suka shiga kai tsaye. Rumgume suka hango ta rike da Hafsat.

Da gudu Ya Haidar ya karasa wajen. Daga ta yayi daga jikin Ummu.

Ruwa yasa Ya Kamal ya bashi. Shafa mata yayi. Amman ko motsi.

Bakin su Ya hade waje daya ya dinga bata taimakon gagawa amman ko gezau.

Daukar ta yayi kamar jaririya ya fice da ita.

Ya Kamal bayan sa ya bi haka ma Ummu. Mayafi ta dauka ta bisu.

Su Hauwa na ganin Ya Haidar ya fito da Hafsat a hannu suka rufa masa baya.

*INDABAWA SPECIALIST CLINIC* Su ka nufa da kenan Zoo road.

Suka isa aka karbeta. Dr Nusaiba Suleiman ce ta amshe ta nan da nan aka rufa akan ta wajen likito ci bakwai.

Sun dau a kalla awa Biyu akan ta amman sam numfashin ta bai dawo ba.

Su Ummu kuwa suna waje hankalin su a tashe.

Kowa yaje sallah amman Ya Haidar ya kasa tashi.

Sai da Ummu ta lallaba sa sannan Ya Haidar yaje sallah. Ya dade yana rokar Allah ya tashi kafadun Hafsat.

yafi minti talatin sannan ya mike ya fito jikin sa a sanyaye.

Har likito ci sun fitar da rai da ita.

Dan har Dr Yasmeen ta fito, ita da dr Sabir.

Dr Nusaiba kuwa da Dr Fauwaz suna kan ta a tsaye.

Suna ganin su suka mike Ya Haidar ya tare Dr Sabir.
"Dr lafiya ya take,"

Kai ya girgiza. Yace
"Am sorry....

Bai karasa ba yayi baya zai zuben

Ya Kamal ne ya taro shi. Dakin kusa da nata aka shige dashi.

Khadija da su Hauwa sai kuka suke kamar ran su zai fita dan tunanin su Hafsat ta rasu.

Ummu kam dauriya kawai take dan ta kasa kukan ma. Mama Fati ce ke rarashin ta.

Har Dr Fauwaz ya ja zanin gefen ta ya rufe fuskar ta.

Juyawa yai zai fita. Dr Nusaiba tace,
"Dr lafiya?"
"Ina jin fa ta rasu."

"Innalilahi wainna illahir rajiun."

Ta fada tana dafe kai. hawaye ne suka zubo daga idon ta.

Ficewa yayi ya bar ta. Kan ta ta daura akan gadon tana sharar hawaye.








*INDABAWA*




For comment an correction.
08062882472
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY





BY *Maryam S Indabawa*
*MANS*




🌐HAJOWπŸ“πŸŒ

πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§ HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾






Page *49*



Huh never forget wit u *Aisha* Dis page is ur love u irrin da yawan nan

Ana tare🀝



Karar computer gefen gadon ce ta motsa.

Da sauri Dr Nusaiba ta dago da kanta. numfashin ta taga ya dawo tana ta kokawa dashi.

Da sauri ta sauri tai mata connection din oxygen.

"Alhamdulillah!" Ta fada a fili tana kiran Nurse din bayan ta.




Shima likito ne suka rufa akan sa. Cikin kan kanin lokaci ya dawo hayyacin sa.

Ba wanda ya farka da ita a bakin sa sai Hafsat!

"Dan Allah kar kuce min ta mutu. Ku taimaka ku kaini wajen ta naganta."

Ummu ce tayi karfin halin cewa,
"Aliyu dan Allah kayi hakuri ka kwantar da hankalin ka. In ma Hafsat ta mutu to haka Allah ya tsara."

"Insha Allahu ma baza ta mutu ba. Sai munyi rayuwa da ita."

"Kayi hakuri, insha Allah baza ta mutum ba."

Kuka yake sosai shi sai an kai shi wajen Hafsat






Ko da Dr Nusaiba ta fito a dakin Ya Kamal ne sai Khadija kawai.

Ya Kamal tai kira shi da Khadija suka bi bayan ta.

Bayan sun zauna ta kalle shi.
"Kai ne yayan ta ko?"
"Eh nine."

"Toh Alhamdulilah Hafsat dai numfashin ta ya dawo kuma ba komai yaja mata wannan abun ba sai razana da tai. Amman Alhamdulilah mun shawo kan abun. Amman gaskiya zuciyar ta na gab da ta buga."

"Innalilahi wainna illahir rajiun!" Shine kadai abinda Ya Kamal da Khadija suke fada.

"Ku kwantar da hankalin ku. Abu daya ya kamata ayi yanzu shine ku fitar da ita waje dan a can akwai inda zasu duba ta su sosai dan abun ya kai karshe."

"To Dr yanzu kinsan wani acan ne?"
"Eh akwai wata yayata acan take aure ita ma likitace zan sa ta shige muku gaba."

"To madallah nagode. Allah saka da alheri."
"Ba komai yanzu ya kamata ku fara cuku cukun tafiyar ya kamata nan da jibi a tafi."

"Insha Allahu zan yi bakin kokari na."
"Shikenan! Nima zan maka maganar."

Fita sukai suna mata godiya. Dakin da take ciki suka shiga. Kallon ta suka zauna yi.

Sannan suka tafi dakin Ya Haidar. Yana yai musu mitar shi Hafsat.

Suna shiga ya fada musu Hafsat numfashin ta ya dawo.

Alhamdulilah! Suka furta.

Zumbur ya mike. Ummu ce tace.
"Kayi a hankali."
"To!" kawai yace, ya fice.

Dakin ya shiga ya zuba mata ido, lokaci daya ta fada ta rame.

Hawaye ya zubo mishi, lokacin su Ummu suka shigo kallon ta suka tsaya yi suna mata addu'a.

Duk wanda ya shigo sai ya zubar mata da hawaye.

A daren dai kwanan asibiti sukai da Ummu da Mama Fati da gogan dan yace ba inda zai je.

Su Khadija da su Hauwa kuma suka tafi gida kamar zasuyi kuka dan suma Da kyar suka tafi.


A darren Ya Kamal ya sanar da Ya Haidar abinda Dr yace, a lokacin yai wa wani abokin sa waya ya samar musu jirgi.

Ya kira Dadyn sa yace shima ya samar musu.


Yan biki kowa ya watse, da tausayin Hafsat tare da mata addu'a samun lafiyaa.

Gidan daga Hauwa da. Faiza sai su Khadija da Su Baba Lami yan aikin Ummu.


Tin safe suka tashi suka gyara gidan suka hada abin kari.

Shiryawa sukai suka tafi asibiti. Har lokacin Hafsat bata farfado ba.

Da Kyar aka samu Ya Haidar ya sha ruwan tea. Duk ya rame a lokaci kan kani.

Gida su Mama Fati da Ummu suka tafi yin wanka.

Amman Ya Haudar a asibitin yai wanka ya canja kaya.
Yana zaune a gefen ta ba abinda ke motsi a jikin ta sai numfashi da yake fita.

Ruwa ake kara mata. kowa da ka kalle shi zaka san a cikin firgice yake.

Idanun su duk sun kude alamar an sha kuka kenan.

Sai wajen azahar abokin Ya Haidar yace an samu amman sai dai mutum biyu da mara lafiyar.







*INDABAWA*
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY





By *Maryam S Indabawa*
*MANS*





🌐HAJOWπŸ“πŸŒ

πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§ HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾






Page *50*


*Summy. Nusy* dis page are us my daugther love




Ummu ya fadawa, Ummu tace,
"Toh kuje kai da Kamal. Shi kamal ya taho daga baya. Kai kuma mijin tane zaka iya mata komai."

"To Ummu! Ke fa?"
"Kar ka damu Aliyu. Ina son Hafsat amman zan zauna anan ina mata addu'a in ta kama muje zan zo."

"Shikenan Ummu Allah bata lafiya."
"Ameen! Nagode da Allah ya bawa Hafsat miji na gari me son ta. Ga Amanar Hafsat na a wajen ka. Nasan ko ba aure a tsakanin ku kai me rike Hafsat ne. To gata nan Alah taya ka riko."

Ta fada tana sharar hawaye.
"Insha Allahu Ummu zan kula miki da Hafsat ba abinda zai faru da ita. Zan kula da ita fiye da yadda zan kula da kai na. Nagode Ummu."

Mama Fati ce ta taso tana gogewa Ummu hawaye.
"Zamu zo tare dasu da Khadija. Ka kula da ita."
"Insha Allahu Momy!"

Khadija ce ta hada wa Hafsat kayan ta. Da duk abinda zata bukata.

Da Yamma zasu tashi. Filin jirgin cika yayi dan su Ya Muktar da Anty Bilki da dangin Abbu na duk sun zo banda su Hauwa da masu aikin mu. Har su maman Hauwa da Faiza duk sai da suka zo.

Kowa hawaye yake share wa. Ummu ce ta matso kusa da gadon da nake kai.

Kallo na ta tsaya yi sannan ta tofan addu'a a kirji na.
khadija da Khairat da Hauwa sai kuka suke.

Haka aka daga dani da su Ya Haidar da Ya Kamal.

Ya Haidar yana gefena. Ya zuvan ido. Addu'a kawai yake yi. Har aka zo aka gyara ni.

Akace kowa yasa belt.









*Ina Ya'yan Abbi ne.*

Tin rabuwar Abbi da Matar sa bai kara tuntubar ya'yan sa ba wanna yasa bai san dadi ya'ya ba.

Bayan sun rabu aure tayi inda ta auri wani dan siyasa.

Ba abinda bai dauke mata ita da ya'yan ta ba.

Sai dai kash Mijin mahaifiyar su ba mutumin kirki bane dan daga baya yar yake bi har ya samu galaba akan ta suke aikata masha.

Inda babar kuma tai aure amman sam mijin ba ilimi bare addini dokan dare da ban na rana da ba.

Mahaifiyar su bata san a halin da Autar ta Salima take ciki ba sai da taga yar tana ta rama gashi tayi.wani fari ta dauke ta takai ta asibiti.

Gwajin farko ya nuna tana da ciki wata uku. Uwar kuka ta fashe dashii.

Ko da ta tsire yarinaya tace Mijinn babar tane uban dan.

Uwar tayi.kuka kamar ranta zai fita.

Mijin mahaifiyar sune ya matasawa Salima kan cewa lallai lallai sai sun zubar da cikin da ke jikin ta.

Da karfi ya kai ta dan a cire mata. sun je an cire ciki lafiya sai da zubar da jini da ya tsinke mata.

Wanda shi yai ajalin ta.
Mahaifiyar su tasha kuka.

Ita kuwa Baraka bayan mijin ta ya yi shaye shaye. Sa ne ya mata dukan tsiya. Washe gari da safe yai mata saki uku,

Da kuka tayo gida inda ta tarar da mutuwar yar uwar ta.

Bayan an gama zaman makoki ta tatara Baraka tace ta koma hannun mahaifin ta.

Baraka yarinya ce wacce take a nutse can gidan kakan nin ta taje sukai mata kwatancen gidan Ummu.

Koda taje gidan Ummu bata gane ta.ba sai da tai mata bayami.

Abinci aka kawo.mata taci ta koshi sannan Ummu tace Dady su yau kwanan sa 5 bata kara sa shi a ido ba


Baraka taso ta koma Ummu tace ta zauna har Allah ya kawo shi.

Khadija kememe tace yarinyar baza ta zauna a gidan ba. Sai da Umku tahi da gaske ta bar ta amman tace sam ba a dakin su ba.

Daki Ummu ta saka mata katifa ta kwaso mata kayan Hafsat ta bata.





Shehu kuwa sunje shaye shayen su yan Hisbah suka zo kame ta ritsa da su aka yi gaba dasu.


Abbi kuwa da ya tafi kaduna wata damfarar ya tara inda aka kama shi aka tafi gidan yari dashi.

Zaman Baraka a gudan Ummy ta gane sam ita bata dauko halin Mahaifin ta ba.






*INDABAWA*
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY





BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*



🌐HAJOWπŸ“πŸŒ

πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§ HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾





page *51*






Dis page is ur *Anty Ummi.* maman Al amin da Abdulsamad.

Ina yin ki sosai. Ana tare🀝









Suna isa motar asibiti ta karaso aka dauke su a ciki. Sai da aka gama settling komai sannan Ya Kamal yaje gidan da zasu sauka.

Shikam Ya Haidar a asibitin ya zauna. Yana gefen ta rike da hannun ta.

Ko da Ya Kamal ya tashi dawowa. Abinci ya taho masa dashi, sai sim.

Sim din ya karba yasa ka ya kira Ummu ya fada mata sun sauka lafiya.

"Toh Allah bada nasara."
"Ameen Ummu."

Ta kashe wayar zuciyar ta a raunane. Momy sa ya kira ita adduar samun lafiya tai musu.

Sai da sukai sati sannan Hafsat ta farfado.

Dan likito cin ma basa son tashin ta so suke sai razanar ta sake ta tukunna. sai dai sam bata magana sai dai zata. bi mutum ido.

Tayi mamakin ganin ta a wani waje na daban kuma daga ita sai Ya Haidar suke kwana.

Sai da Safe taga Ya Kamal ma. Farfadowar ta ya kara bawa likito ci kara bunciken ta.

Ya Haidar kuwa baku ga yadda yake murna ba ganin ta farka.


Satin Kamal biyu ya juya ya rage daga Ya Haidar sai Hafsat.

Komai shi ke mata. Wanka ne kadai take hanashi yi mata.

Amman shafa mai da saka kaya duk shi yake mata.

Tana kwance Ya Haidar na gefen ta, hannu ya saka a cikin rigar ta yana mata tafiyar tsutsa.

Ido ta lumshe, jin ya gan gara da hannun sa saman kirjin ta yasa tace,

"Ya Haidar!"
Da sauri ya dago dan ganin wanda ya kira sunan sa.

Hasfat ce, murmushi ya saka me hade da hawayen farin ciki.

"Mai maita naji dan Allah!" "Ya Haidar! Ina Ummu na da Khadija."

Rumgume ta yayi yana kukan farin ciki. Hawayen fuskar sa take goge masa.

"Haba Ya Haidar Kuka kuma"
"Hafsat kukan farin ciki ne."

Murmushi tayi, tace,
"To ka daina dan Allah."
"Na daina!" Ya fada yana goge fuskar sa.

Kara rumgume ta yayi a jikin sa. Ido ta lumshe tana shakar kamshin turaren sa.

Dagota yayi, ya ga idon ta a lumshe.

Sumbatar idanun ta yayi. Bude su tayi a hankali.

Ido ya zuba mata. Ganin kalar idon ta ta canaja kala zuwa ja.
"Baby na lafiya."
"Ba komai!" ta fada tana maida hawayen ta.

Wayar sa ya zaro ya kira Ummu. Bai magana ba ya hada su da Hafsat.

"Assalamu Alaikum!" Tai musu sallama cikin sanyin murya.

Ummu rudewa tayi, ta kasa amsa sallamar sai cewa take,
"Hafsat kece baki ya dawo kenan. Allahamdulilah!"

Murmushi Hasat tayi,
"Ummu na kuna lafiya ina su Khadija da Khairat?"

"Suna Lafiya Hafsat ya jikin."
"Alhamdulilah!"

"Toh! Masha Allah. Allah dada afuwa. Ga Khadija."

Khadija ma da murna ta karba taiwa yayar tata ya jiki.

Sai Khairat da ta dinga shirme ina Tatyn ta ta tafi.

Daga Karshe Ya Haidar ya Karbi wayar ya kashe.

"Ya Haidar dan Allah kira min su Hauwa,"
"Sai anjima yanzu kin gaji."

"Allah ban gaji ba."
"Eh! Ni nake son na karasa gajiyar dake din ai yanzu."

Shiru kawai tayi,
"Hafsat ya kike ji yanzu."
"Wallahi Ya Haidar Alahmdulilah sai dai nan da ke min ciwo."

Ta nuna masa kahon zuciyar ta.
"Sannu Baby na. Allah baki lafiya."

Gefen ta koma ya kwanta. Hannun sa akan fuskar ta yana shafawa.

Ido ta lumshe. Kwanciya ya gyara mata sannan ya dinga bubuga bayan ta a hankali kamar yadda ake lalashin baby in zasu yi bacci.

Itama kam bata san lokacin da Bacci ya dauke ta ba.

Ganin tayi bacci yasa ya mike zaune. Ya dade yana kallon ta. Daga karshe alwala yayo yana ta sallah da addua Allah vawa Hafsat lafiya.

Kulawa yake bata sosai dan komai shi yake ma. Abinci ma a baki yake bata.

Washe gari da safe da kanta ta mike tana ta kawa.

Wanka ta mike zata yi. Kamo hannun ta yayi.


"Zaki iya?"
Kallon sa ta tsaya yi. Sannan tace,
"Zan iya."

"Baby na ina son kimin alfarama ma."
"Wacce irin alfarma."

"Ki ban dama nai miki wanka sannan na shirya ki."
"Ya Haidar!"

"Pls Baby na!"
"Naji amman nima kai min affuwa."

"Affuwa tame kennan."
"Kayi hakuri nai wankan da kaina ka Shirya ni."

"Shikenan ya kama hannun ta ya shigar da ita ban dakin."

Da ta fito ma shi ya kamo ta ya daura ta akan kujerar dakin.

Sai da ya tsane mata jiki sannan, ya dauko ya mullka a hannun sa. Kafar ta ya janyo.

Baya tayi da kanta ta kwantar akan kujera.

Shafa mata ya dinga yi a hankali. Haduwar lumshin hannun sa da laushen fatar ta shi ya haifar masa da kasala.

Hafsat kuwa ido kawai ta lumshe. Amman wani abu taji na mata yawo a jiki.

Cinyar ta ya gangaro ya fara shafa mata. Wata ajiyar zuviya ta sauke mai karfi lokacin da ya sauke hannun sa a kan cinyar ta.

Dago kansa yai ya kalle ta idan ta arufe yake.


Murmushi yai ya cigaba da shafa mata man. Duk wani waje da zai taba sai ta saukar da ajiyar zuciya.





*Indabawa*
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY








BY *Maryam S Indabawa*
*MANS*





🌐HAJOWπŸ“πŸŒ

πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§ HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾






Page *52*




*Amal* tawa ga shafin ki. 😜






Duk inda zai shafa mata mai sai ta saukar da ajiyar zuciya

A haka ya gangaro saman ta. Bayan ya lukata ya murza ne, ta rike hannun sa.

Kallon ta yayi kai ta langwabar. Ya gane me take nufi amman yace.
"Lafiya?"
"Barshi zan karasa."

Kallon ta ya tsaya yi. Kai ta kara langwabar wa.

Murmushi kawai yayi ya mike dan dauko mata kaya.

Juyawar da yayi shi ya bata damar shafawa da sauri. Kafin ya juyo har ta gama.

Under wear nata ya miko mata. Hijab din gefen ta ta dauka ta zumbula a jikin ta.


Sannan ta saka kayan yana gefe yana kallon ya yana dariya.

Sai da yaga ta gama shiryawa sannan ya dauke ta kamar Baby ya daura ta akan gado.

Wanka shima ya shiga. Wayar sa ta dauka ta kira Ummu bayan sun gaisa ta kira su Hauwa duk murna suke na dawowar maganar ta.

Suna cikin waya da Hauwa ya fito daure da rigar wanka. Duk kirjin sa a waje.

Ido ta lumshe, saboda bata son ganin sa a haka.

Yana kallon ta,, ta gefen ido. Murmushi ya kuma saki sannan ya juya ya fara shiryawa.

Bata san gamawar sa ba sai jin sa kawai tai ajikin ta.

Da sauri ta bude idon ta. Kallon juna suka tsaya yi.

Knocking ake amman sam basu ji ba. Jin shiru yai yawa yasa aka kara bugawa.

Ina basu san anayi ba. Wannan yasa Nurse din turo kofar kawai.

Ganin sa tayi a saman ta sun zubawa juna ido juyawa tayi da sauri wannan yasa silbar hannun ta faduwa.

Da sauri suka maida hankalin su kan abinda ya fadi.
"Am Sorry Sir!"
"Ba komai!" yace ya sauko a gadon.

Taya ta kwashe

Please Login or Register in order to submit comment