Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bacci ya dauke ta.

Har aka isa gidan bata san sun isa ba. Ganin tana bacci yasa ya dauko ta.

Kamar Baby haka ya dauke ta, yan aikin gidan sai sannu da zuwa suke masa amman sai dai ya daga kai dan kar ta farka.

Shigar su Falon kenan Momy na sauko wa abene, dai dai lokacin kuma Hafsat ta bude ido.


Ganin ta a hannun sa yasa ta fara kokarin sauka. Kam ya kara riketa. Kan Kujera ya zaunar da ita.


Momy kuwa kamewa tayi ganin su tare da Hafsat.
"Lallai Mariya kenan bata ji maganata ba tabar yaron nan tahowa da yarinyar da bata da lafiya. Zanyi magani sa."

Ta fada a. Ranta. Sakowa ta fara yi ta karaso dakin.

Kai Hafsat tayi kasa dashi. Sannan ta mike zaune,
"Momy na barka da fitowa."
"Yauwah Hafsat sannun ku."

Ta zauna a gefen ta.
Kasa ta zame tana gaisar da ita."
"Ina yini Momy!"

"Lafiya lou. Ya hanya?."
Ta fada tana Dagota Momy ta zaunar da ita.


"Lafiya Alhamdulilah. Mun same ku lafiya?"
"Lafiya Hafsat ya jiki?"

"Jiki Alahmdulilah."
"Allah kara afuwa."

"Ameen!"
"Taso muje ki watsa ruwa kici abinci." Ta fada tana kama hannun Hafsat.

"Momy ina yini?"
"Lafiya!" Kawai ta amsa tayi sama da Hafsat.

Dakin ta ta kai ta. Ta hada mata ruwa. Tana fitowa Momy ta bata wata abaya me kyau ta saka.

Sallah tayi sannan suka sauko kasa.
Ba kowa akasan. Abinci taci sannan Momy ta kara komawa da ita sama.

Laptop din ta ta baya dan ko zatai kallo ko game, sai wayar ta da ta bata.

Ummu ta fara kira tace sun sauka sai Faiza da Hauwa.

Hauwa sai murna take. Tace anjima tana tafe.

Da yamma tazo suka sha hira dan sai dare suka tafi.

"Hafsy kinga yadda kika kara kyau kuwa gaskiya ko an karu ne?"
"Wane irin karuwa."

Cikin ta ta nuna wanda a kalla zaiyi wata biyar ya dan turo kai.

Ido Hafsat ta zaro, tace.
"Tayaya ake yin ciki?"
"Ban sani ba."

Dariya Hafsat tayi tace,
"Ban da abinki na tare ne."
"Ban sani ba."

Murmushi tayi tace,
"Ayi zancen gaskiya man."
"Ina jinki."

"Tayaya zan samu ciki ban tare ba."
"Wai ke duk zaman da kukai tare shine vaki tare ba. Ai tinda an daura aure komai ya wuce"

Murmushi ta karayi tace,
"Kin manta banda lafiya ne,"
"Hhhhhh wai ni zaki maida yarinya."

"Wallahi da gaske ba abinda ya faru,"
"Ah lallai Ya Haidar jarumi ne, yana da hakuri da juriya da tausayi."

"Haba! Shi bawan Allah ne ba ruwan sa ai."
"Zaki ga ba ruwan sa in ya kamaki,"

"Kinga bar maganar nan. Wata nawa ne?"
"Mefa?"

Nuni tai mata da cikin ta.
"Oh wata shida ne,"
"Masha Allah.ashe dashi aka sha biki. Faiza kuma wata biyu. Bayan biki."

"Allah shirya ki wallahi."
"Ameen!"

"Ke kuma nan da gobe,"
"Wane gobe ban da lafiya."

"Au har yanzu baki warke ba."
"Lallai Yayan mu zai sha fama da rowa."

"Allah sarki ba wata rowa shima ya sani ai."
"Hmmm Hafsy kenan zaki shiga hannun manya fa."

"Hannun Yaya nane ai zai tausayawa kanwar sa."
"Daga baya ba. Amman in ana kan abin ai baji bare gani."

"Naji shi daban ne ai."
"Gaskiya ne, in da ya dade ba mace ai sai ya huce duk bukatar sa."

"Me?" Ta fada taba xaro ido.
"Eh! Abinda kika ji na fada."

"Ni bar ni da maganar nan."
Daga haka suka canja hirar kuma.

A daki sukai sallah magariba nan Momy ta kawo musu abincu suka ce.

Sai isha'i Ya Nura yazo ya dauke ta







*INDABAWA*
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY






BY *Maryam S Indabawa*
*MANS*








🌐HAJOWπŸ“πŸŒ

πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§ HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾










Page *59*








Ina rakasu na shige daki nai wanka na canja kaya na kwanta.


Sai karfe tara sannan Ya Haidar ya shigo gidan, Momy ya gaisar ta amsa masa tana basarwa.

"Momy lafiya kuwa?"
"Lafiya lou. Me ka gani."

"Naga kin canja min."
"Ba baka jin magana ba."

"Me nayi?"
"Me nace maka?"

"Name fa?"
"Oh wai ka manta ko? Ta na game da Hafsa."

"Momy kiyi hakuri wallahi Ummu ce tace in taho da ita."

"Eh! Kun kyauta yarinya bata gama warware wa ba kuka taho da ita. To zanyi maganin ku."

"Kiyi hakuri. Kuma Hafsat wallahi ta warke."
"Naji."

"Toh! Momy tana ina zamu tafi."
"Ina?"


"Gida!"
"To baza ta tafi ba. Sai nan da naga yadda jikin nata yake."

"Momy wallahi ta warke."
"Naji amman bazan baka ita ba."

"Momy dan Allah!"
kallo. Sa ta tsaya yi.
"Tashi ka ban waje. Fitsarare."

Sama ya nufa
"Kar ka shigar min daki kaji ni ko?"
"Toh!"

Ya wuce dakin sa. Bai kara saukowa ba.
Wajen Karfe biyun dare ya fito kofar dakin ya taba yajita a rufe.

Kai ya girgiza yana murmushi dan yasan Momy ce ta rufe
"Wai mutum da matar sa. Amman ake min rowar ta"


Sallah yaje yayi, sannan ya koma baccin sa.

Da safe yana tashi ya shirya sannan ya tafi dakin Momy. Dakin a bude a hankali ya shiga.

Tana kwance cikin bargo. Kan gadon ya hau ya kwanta gefen ta fuskar ta ya bude baccin ta take hankali kwance.

Sumbatar goshin ta yayi sannan ya sumbaci bakin ta da idanun ta.

Yana bukatar matar. Sa amman Momy ta hanashi abar shi.

Rumgumar ta yayi. Motsawa tayi yai saurin sakin ta dan bai son ya tashe ta.

Saukowa yayi daga gadon ya tsaya kallon ta. Gyara mata rufar yayi sannan ya fita.

A bakin kofa suka hadu da Momy kai ya sosa. Ya duka ya gaida ta. Amsawa tayi kamar bata san daga inda yake ba.

Cikin dakin ta shiga. Yadda ta fita ta bar ta haka ta same ta.
"Haidar ko kunya ta ma baya ji."

daki yana dube dube akan kamfanin da zasu bude anan Abuja.

Sai karfe 9 ta tashi. Dakin ta gyara sannan ta shiga ban daki tai wanka ta fito ta shirya cikin riga da zani na leshi ruwan goro da ruwan madara.

Sosai suka kara gaska ta, zani ya zauna a kugunta sai kace siket ta saka.

Rigar ta kara fito mata da albarkatun kirjin ta. Hijabi ta daukar ruwan madara ta feshe jikin ta da turare sannan ta sauko kasa.

Ba kowa a falo. Daga kitchen ta jiyo motsin can ta nufa, momy ce ke gyara kayan miya.

Da sallama ta shiga kitchen din Momy ta jiyo.

Durkusawa ta tace,
"Momy ina kwana?"
"Lafiya ya kika tashi da jiki."

"Jiki Alhamdulilah."
"To jeki kici abincin ki."

"A'ah bari na fara taya ki."
"Ni na gama jeki kici kinji."

"Toh!" Tace, Ta fita.

Tea kadai ta hada sai dan potatoe ball da yaci guda uku. ta mike ta tafi kitchen.


Ita ta karbi kayan miyar ta blanding sannan ta daura ta tafasa ta soye shi. Ta miya. Sai farar shinkafa da ta dafa da kayan lambu a ciki, Karfe 12 har sun gama abincin rana.

Falo suka koma. Momy ta zauna akan kujera ita kuma a kasa.
"Haba Hafsat dawo sama mana."
"Momy nan ma yayi."

"Hafsat nifa ban dauke ki a matsayin sirika ba. 'Yar tace ke kuma a haka na dauke ki. Ki dai na jin kunya ta ni mahaifiyar kice."
Kai ta dukar.

Sanye yake cikin ruwan madarar shadda yayi kyau dashi, dakin Momy ya shiga bata nan. Van daki ya bude nan ma bata nan.

Kasa ya sakko. Tun daga kan bene ya hanye ta. Tayi kyau sosai, yana son Hafsat kullum kara son ta yake.

Idon sa akan ta ya karasa sakkowa.
"Momy barka da hutawa!"
"Yauwah Haidar!"


Kanta a kasa, tace,
"Ina kwana Ya Haidar!"
"Lafiya Hafsat! ya jikin?"



"Jiki Alahamdulilah."
"Allah kara afuwa."

"Ameen!"
"Momy yaunwah!"

"Ai ga abincin can."
"Ki hadan to!"

Kallon sa tai ta mike tayi sama. Wani sanyi yaji.
"Baby hada min abinci."

Mikewa tayi ta fara tafiya cikin sanyi. Kugunta sai juyawa yake, ido ya zuba mata.

Kallon ta kawai yake ya kasa dauke idon sa.

Mikewa yayi yaje ya rumgume ta ta baya.
"Baby kina rikita ni da yawa. Wallahi. Kar fa na zauce."








*Indabawa*
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY







BY *Maryam S Indabawa*
*MANS*




🌐HAJOWπŸ“πŸŒ

πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§ HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾







Page 60





"Ya Haidar Momy fa."
"Ina ruwana ta bani Matata."

"Nidai dan ka bari kar ta fito ta ganmu a haka."


Juyo da ita yayi. Ya zare mata hijab din jikin ta. Kara matse ta yayi a jikin sa. Sannan ya fara. sinsinar wutan ta.

"Ya Haidar!" ta fada murya na rawa.

"Uhmm!" Kawai yace.
"Ya Haidar!" Ta kuma fada jin ya zira hannun sa cikin rigar ta.

"Baby na ya dai!' Ya fada yana zare hannun sa.
ido ta ya kawo kwalla.

"Yi hakuri kinji."
Hannun ta yaja suka karasa daining din.

Tea ta hada masa ta zuba masa soyayyan dankali da farfesun da Momy tayi.


Zama yayi ya jawo ta ya zaunar akan cinyar ta. Matse ta yayi duk yadda taso ta mike ya hanata.

Abincin sa yake ci hankali kwance. nama ya dauka yasa mata a baki. Kawar da kai tayi,
"Allah in baki ci ba ko..."

Bai karasa ba ta saurin bude baki ya saka mata. A hankali da wayo sai da ya bata taci abincin.

Duk ya bata mata baki da romo. Hannu tasa zata goge yai saurin rige hannun nata.

Bakin sa yakai ya lashe mata, shi tas. Wani yar taji a jikin ta.


Sannan ya komo hannun ta sukai sama. Dakin sa ya isa da ita.

Komai tsaf sai kace ba mutum a ciki sai tashin kamshi yake.

Zaunar da ita yayi, sannan ya zari wayar sa ya dinga daukar ta hoto ita dai kan ta na kasa.

Ummu ya kira bayan sun gaisa, ya bawa hafsat. Gaisawa sukai sannan. Ya amsa yakira Faiza, hira suka sha abinsu yana gefe yana kallon ta.

Komai nata a nutse da tsari. Komai tayi burgeshi taje yi.

Hannun ta ya kamo sukai cikin dakin sa. Kwanciya yayi akan gado ya janyo ya jikin sa.

"Bacci nake ji muyi tare kinji. Wajen satin mu daya bama kwana tare Baby na."


"Ya Haidar nidai bazan iya ba."
"Me din?"

"Ya Haidar, Momy fa."
"Shine me."


Hararar sa tayi. Tace,
"Komai ma!" Dan taga alamar so yake yaja musu abin jin kunya.

Mikewa tayi ta fito. Kallo ya bita dashi. Yadda kugunta ke juyawa shi ya kara jan hankalin sa.

Ido Ya lumshe yana ta tunane tunane, har bacci ya dauke shi.

Dakin Momy ta wuce taje ta kwanata. Itama nan da nan bacci yai gaba da ita da tunanin sa. Lallai Ya Haidar.

Mamaki yake bata in yana wasu abubuwan. Sai taga kamar bashi ba.


Sai biyu ta tashi. Wanka tayi tai alwala tai sallah. Sannan ta sauya kaya.

Tana fitowa shima yana fitowa. Kallon sa tayi tai kasa da kai. Ta tsaya ta kasa cigaba da tafiya.

Ido ya zuba mata sannan ya karaso gun ta.

"Baby kin tashi,"
Kai kadai ta daga masa. Alamar "Eh!'


Hannun ta ya kama suka sauka kasa. Kallo suka fara yi.

Sai yamma ya fita. Ita ta taya Momy girkin dare dan sam Momy tace ita bata da lafiya.

Bai dawo ba sai bayan isha'i lokacin Hafsat na dakin Momy tana game a laptop din Momy.

Falon ba kowa, dan haka sama ya nufa kai tsaye ya wuce dakin Momy.

Fitowar Momy a bamdaki kenan ya turo kofar.Gefen Hafsa ya zauna. Yana wa Momy sannu da gida.

Sannu da zuwa Hafsat tai masa ta cigana da kallo.

Momy na zaune a gefe tana amsa waya. Fita tayi kafin ta dawo ya mike ya dauki makullin dakin guda daya. Sannan ya ajiye saura.


Hafsat bata san abin da yake ba.ita dai kawai kallo take.

Wajen karfe Tara da rabi sai ga Momy nan wai ya tafi ya kwanta.

Haka yana ji yana gani ya tafi dakin sa.



Saida yai wanka sannan ya kwanta.

Hafsat kuwa sai wajen karfe goma ta kwanta bayan tayi wanka tai sallah.

Kasa baccin tayi, dan duk ta tafi tunanin Ya Haidar.

Bata taba zaton zaso wani kamar yadda take jin Ya Haidar a zuciyar sa ba.

Shima a daidai lokacin yana can yana tunanin ta.

Tunawa yai da wayar Momy na gunta. Da sauri ya janyo wayar sa tafara neman layin wayar.

Game take bugawa a wayar sai ga kira nan ya shigo.

*Son* taga an rubuta.
Kindauka tayi dan tayi zaton ko Momy zai nema.

Ganin bata dauka ba sai yace ko bacci take. anya ba bacci take ba Wata zuciyar tace ya tura mata sakon ita yake son magana da ita.

Tura mata yayi. Bude sakon tayi.

Murmushi tayi lokacinda taga kiran sa na kara shigowa.






*Indabawa*
*MIJIN UMMU NAH*
true life story





By *Maryam S Indabawa*
*MANS*






🌐HAJOWπŸ“πŸŒ

πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§ HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾





Page *61*








Dagawa tayi, da sallama.
"Baby na!"
"Na'am"

"Me kike baki kwanta ba."
"Na kasa bacci ne."

"Nazo ne."
"A'ah!"

"Oh bakya nema na."
"A'ah ai kaga Momy."

"Gaskiya ni na gaji. Wallahi matata nake bukata."
Shiru tayi.

"Kinyi shiru."
"Eh! Toh me zance."

"Ke bakta bukatar mijin ki."
Shiru ta kara.

"Baby na! Wai ke bakya bukata ta."
"A'ah!"


"To ki fadawa Momy kin warke,"
"In nace na warke shine me?"


"Sai ta bani matata."
"Au dan ban warke bane taki baka ni."

"Eh"
"Ni kuma sai nace na warke Ya Haidar."

"Eh!"
"Wayyo Allah bazan iya ba."


"Saboda me?"
"Haba Ya Haidar, Momyn zan fadawa haka."


"To shikenan zan ce kin warke in ta tambaye ki kice! Eh "
"Toh!"

Kawai tace dan ya rabu da ita. Hira yake son ya ja ta da ita. Amman ita kuma bacci take ji. Tin tana amsa masa har tayi duf.

Bacci ya dauke ta. Saukar numfashin ta yaji, yai murmushi. Barin wayar yai a haka har shima baccin ya dauke shi.

Sai asuba suka ga lokacin da suka dauka wayar nayi ita kadai.

"Ya Haidar kenan."
ta fada tana shiga ban daki.

yau ma sai wajen goma ta tashi. komai tayi ta shirya cikin doguwar rigar material sai ta dauki mayafin kayan ta yafa.

Kanta yasha gyara sai kyalli yake .dakin ya shigo a gaban muduni ya hange ta tana fesa turare.

Karasawa yayi wajen ta. Kallon juna suke ta jikin madubin. Rumgumar ta yayi. Ido ta lumshe.

Sabuda wani kamshi da ya doku hancin ta,

Kan sa ya daura a kafadar ta. janye jikin ta tayi, ido ta juyawa masa tare da kanne daya.




Kallon ta ya tsaya yi, har ta gotashi tai wajen bedside drower. Bayan ta yabi ta dauki dan kunne ta makala sannan ta juyo tana kallon sa.

Kallon ta ya tsaya yi, ita ma haka. Kai ya dan sosa, A hankali ya dinga takowa yana biyo ta. Ja da baya takeyi.


Murmushi yayi, itama murmushin take yi tana ja da baya. Batai aune ba sai ji taji ya kamota ya hade da kirjin sa.

Kan sa ya matso da yana shin shinar wuyan ta, ido ta lumshe, ganin ya fara lugwigwita ta. Yasa ta tura shi kan gado Fadawa yayi.

Ya mike zaune yana murmushi. Itama murmushin tayi. Ta juya. hannun ta ya kamo.


Kallon sa tai da mamaki. Murmushi yayi ya kada kai ya kanne mata ido daya.

Kai ta gizgiza kawai. Hannun ta ya jawo ta fada kansa. Ido ta rufe, bakin ta yake laluba.

Gefe ta yi ta kwanta, suna fuskantar junan su, ido ta lumshe, murmushi ya kara sakar mata.

Kai ta kawar, daya barin. Shi ma juyar wa yayi yana murmushi. Sai numfarfashi take yi.

Shikam dagowa yayi. Yayi wajen fuskar ta yana shinshinar kamshin jikin ta, hannu ya saka a saman cikin ta.

Wata ajiyar zuciya ta sauke. Idon ta a lumshe. Daukewa yayi ya kamo hannun ta ya hade ya dan haye kan ta.

Iska ya dinga, hura mata cikin kunnen ta. Ido ta rufe da karfi Bakin ta yake son laluba a hankali, da sauri ta dago daga kwancen da take.

Haki take kai kace tasha gudu ne.
mikewa shima yayi Yana dariya jingina da jikin ta. ya daura kan sa a kafadar ta.

Da sauri ta mike tsaye dan Ya Haidar duk ya wani canja mata. Mikewa shima yayi.

Jawota yayi. Ya hadata da bango, bakin su yahade gudaya yana lotsa.
Sandarewa tayi ta kasa hanashi.

Sai da yayi me isar sa sannan ya jawo ta ya rumgume ta. Sunfi minti goma sannan ya saketa.

Hannun ta ya kama suka fita falo. Ba kowa a falon dan Momy na can gyara dakin Dady dan wani satin zai dawo.


Shi ya dinga bata abincin abaki, har ta koshi.







Momy na lura da yadda yake takurawa Hafsat dan haka tace kada ta kuma ganin sa a dakin ta. Ko kofar dakin bata yadda ta ganshi ba.

Zuciya yayi yaki koda zaman gidan duk da kewar da yakeji ta Hafsat









*INDABAWA*
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY










BY *Maryam S Indabawa*
*MANS*





🌐HAJOWπŸ“πŸŒ

πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§ HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾




Page. *62*









Kusan kwanan sa hudi basu hadu ba. Aiki ya koma kullum acab yaje yini sai dare zai dawo.

Da ya dawo zai dibi abinci yai dakin sa. Yana gamawa zai hau aiki da ya gama ya kwanta.

Ya maida kanshi too busy duk dan kar yana damuwa da rashin ta. Amman wani abun kamar kara masa kewar sa ake da son kusantar ta yake.

Ita ma Hafsat sam bata jin dadin rashin ganin sa amman sai ta danne hakan a zuciyar ta dan tasan Momy bazata cutar da ita ba.

Yau Momy ta fita danyo siyayyar abubuwan da take shiryawa bada sanin komai ba.

Kamar ya sani shi kuma ya dawo gida. A lokacin kuma sai yaji yana son ya ganta.

Dakin Momy ya nufa kai tsaye dan yasan bata dakun dai ita.

Da sallama ya shiga amman ba kowa a dakin.

Wajen bandakin dakin ya karasa, jin ana amfani da ruwa yasan Hafsat ce dan yasan ba inda Hafsat take zuwa kullun tana daki.

Kofar ya bude a hankali. Sandarewa yayi ganin ta ciki ruwan kumfa.

Idon ta a rufe ta jingina shi da bango. A hankali ya karasa wajen da take.

Zama yayi a gefen ta ya zura hannun sa cikin ruwan.

Tunani take me zurfi.shiyasa ba taji shigowar sa ba.

Cinyarta ya shafa. Ji tayi wani abu ya bi jikin ta. Wannan yasa ta bude idon ta da sauri.

"Ya Salam!" Ta fada ta rasa me zatayi, dungulewa tayi waje daya.

Kallon ta ya tsaya yi kamar shasha dan duk ta sukurkuta masa tunanin sa.

Ganin ta nade waje daya ne yasa ya daga ta tsaye.

Kuka ta saka mishi dan tasan Momy bata nan yau kashin ta ya bushe.

Kuka take sosai wanna yasa ya sake ta. Ya mike.

Murya a dashe, yace,
"Bari nai miki wanka."

Tana kuka tace,
!A'ah dan Allah nagode."

Murmushi yayi. Ya juya ya fita.
"Ina jiran ki to."
Ya fada mata.

Tafi awa daya a bandakin ta kasa yin komai sai da kyar ta cuda jikin ta ta fito.

Da towel kadai ta shigo ban dakin dan batai tsammanin ganin sa ba.

Da kadan ya wuce cinyar ta.

"Ya Haidar!"
Ta fada tana daha cikin ban dakin.

Yana jin ta yai mata shiru.
"Ya Haidar!"
Ta kuma kiran sa.

Shiru ya karayi.
"Ya Haidar!"
Jin ta kira sa sau uku yasa tace baya dakin.

Fitowa tayi, ta wuce gaban madubi. Zama tai tana shafa mai.

Sai da ta shafa kafafunta sannan ta dage towel din tana shafe jikin ta.

Kamar daga sama akace ta juyo, ta ganshi kwance akan gadon ya zuba mata ido.

Ihu ta saki ta dunkule waje daya,
"Ya Haidar! Dan Allah ka fita."

Kallon ta yayi, kawai . Shifa komai ya tsaya masa.

"Dan Allah!"
Mikewa yayi yana murmushi. Ya fice. Dakin sa ya shige ya fada saman gado.

juyi yake kawai idon sa jawur. Azaba kawai yake sha.

Yayi dana sanin shigarsa ban daki.

Yana fita taje bta rufe kofar ta dawo ta saka kaya.



Daga ranar bata kuma sa shi a idon ta ba.



Momy Ta hana Haidar tafiya da Hafsat ne saboda, dinner da zasu yi in Dady ya dawo.

Dan ranar da ya dawo a washe gari za'ayi ta a mika masa matar sa.

Su Ummu da su Abbi duk zasu zo haka su Faiza.

Taro dai xa tayi sosai.

Dilka ta kira wo aka karayiwa Hafsat sannan ranar da Dady zai dawo da safe akazo akai musu jan lallai. Hafsat har da baki a kai mata.

A ranar kuma yan Kano zasu taho. Ana game wa Hafsat lalle. Ta sa Idi driver ya kai ta saloon ai mata gyaran kai. Jamila mai aiki tasa ta raka ta.

Tafiyar ta ke da wuya Su Ummu suka sauka ta wagar su guda.

Shikam gogan bai san komai ake shirya wa ba yasan dai Yau Dadyn sa zai dawo.

Tin ranar da Hafst ta daga masa hankali be kara bari sun hadu dan zai iya aika aika.

Da Yamma Dady ya dawo.

Da Murnar sa ya shigo gidan dan yasan Dady zai sa Momy ta bashi matar sa.

Abinda ya gani shi ya bashi mamaki sau Ummu ya gani zazaune.

Baki ya bude yana kara murnar ganin ta.

Da sauri ya karasa gefen Momy yana mata sannu da zuwa.

Kamal yaje ya rumguma.
"saukar yaushe." "Dazu nan."

"Taso muje gun Dady yaja hannun sa sukai sama."

Bayan sun gaisa dasu Faiza da Khadija.










*INDABAWA*
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY







BY *Maryam S Indabawa*
*MANS*








🌐HAJOWπŸ“πŸŒ

πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§ *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* ✍🏾✍🏾✍🏾










Page *63*




Sai kusan magariba suka dawo saboda wasu kananun kitso da akai mata.

A gajiye ta shigo dakin, da sallama a bakin ta.

Jin hayaniya yasa tace yau Momy baki tayi,

Tana shiga ta hangi su Ummu da gudu ta fada jikin ta tana kukan farin ciki.

Faiza tace,
"Au wai ke baza ki girma ba."

Da sauri ta juyo, ta fada jikin Faiza tana murna.

Khadija ce ta sauko a bene tace.
"Anty!"

Ya salam ai Hafsat mikewa tayi ta rasa gun wanda zataje dan murna.

Ya Kamal yace,
"Hafsy mu."

Gefen sa taje ta zauna. Sai a lokaci, ta lura da Ya Haidar da ya saki baki hanci da ido yana kallon ta.

Kasa tai da ido, tuna haduwar su ta karashe.

"Sannun ku da zuwa."
Ta fada tana komawa jikin Ummu.

"Kai Anty kinga yadda kika kara gaske da kyau. Ga lallan ya kara gaska ki."

"Muga Gyaran kan naki."

"A'ah! Bari"
"Kai Anty."

"Ke gani a daki "
"Toh!"

Sallamar su Hauwa muka jiyo.

Ita da Ya Nura ne. Cikin ta ya kara fitowa.

Ni dai ina jikin *Ummu nah*
bayan an gaigaisa ne sai ga Momy na.

"A'ah Hafst yau gaki ga Ummun ki ko."

Kasa tai da kai tana murmushi.

Dady da Abbi ne suka sauko.

Duk kasa muka zame, kai na na saman cinyar Ummu.

Dady ne yai addu'a sannan kuma yake fada cewar gobe za'ai dinner bikin mu jibi na tare.

Wani sanyi ne ya ratsa Ya Haidar.

Bai san sanda ya Sauke ajiyar zuciya ba. Su Ya Kamal dake gefen sa suka kalle shi.

Ido ya kanne musu. Murmushi sukai.

Dga nan kuma suka wuce daining dan cin abincin dare.

Bayan an gama suka koma falo aka ci gaba da hira.

Abbi daki aka basa a kasan bene.

Sai Ummu da aka bata wani dakin Kusa da na Momy.

Sai mu dasu Faiza da Hauwa da tare itama anan zata zauna duk a dakin Momy muka kwana.

Sai su Ya Haidar da suka tafi boys quater.


Ranar kwana sukai ana hira daga baya kowa mijin sa ya kira sa.

Ganin haka yasa na mike na bar musu dakin.

Wajen Ummu naje muna hira har tai bacci.

Kwanciya tayi sai ga karar wayar Momy dake Wajen.

Ya Haidar ne. Dauka tayi, sallama yayi. Ta amsa.

Shiru sukai.
"Baby nah" ya katse shiru."
"Na'am!"


"Baby na jibi tare zamu kwana."
Ya Haidar."

"Na'am!"
"Ka bari."

"Me?"
"Zumudi."

"Saboda me." "kawai."

"Shikenan haka waccan karon ma kika ce. Allah yasa lafiya."

"Ameen!"
"Baby na jeki bacci to."



Ciwon mara ne ya tada ita. Daga baccin da take.

Cikin kayan ta taje ta dauko magani tasha. Shine yasa ta samu sauki.

Da asuba ta tashi tai wanka ta gyara jikin ta.








*INDABAWA*
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY









BY *Maryam S Indabawa*
*MANS*







🌐HAJOWπŸ“πŸŒ

πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§ *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* ✍🏾✍🏾✍🏾








Page *64*








Da safe lafiya na tashi sai dai dan ciwon da baza a rasa ba.

Kwata kwata ban ga Ya Haidar ba.
Karfe Hudu bayan nai sallah aka zo akai min kwalliya.


Ba a cikin fuska da tarkace ba sai dai an min jagira da su foundation jan baki sai massacara da aka saka min ta raka fiton da tsayin gashin ido na.

Sosai nai kyau, maroon jan bakin da na saka ya kara fiton da kyan lebe na yayi kyau dashi kamar an dasa.

Kitso nasa akai min kanana wanda ya zubo min har gadon baya. Ribon nasaka masa

Wani dankararen Leshi Momy ta kawon. Golden colour ne adon ruwan hoda a jikin sa. Takalmi da jaka duk golden ne. Sai dankunnen gold da sarka da abin hannu da duk ta kawon.

Dikin doguwar riga ce. Wacce ta zaune a jikina. Yayi min kyau sosai.

Su Faiza kallona suka tsaya yi dan ba karamin kyau nayi ba. Ga wasu turaruka da ta bani masu kamshi da sanyi. Sai tashin kamshi nake.

Mangariba nayi aka fara dibar su Faiza da Khadija da Hauwa.

Gidan ya rage daga ni sai su Ummu. Ina daki a zaune. naji an bude kofa.

Shine ya shigo kallo na ya tsaya yi.
Sanye yake da golden din shadda dinkin yar ciki da babbar riga. Sai hula da takalmi suma duk haka. Sai agogon golden color shima.

Dakin tuni ya dumame da kamshin turaren sa. Yafi minti biyar tsaye yakasa dauke idon sa akai na.

A hankali ya karaso inds nake, hannuna ya kamo, ya mikar dani.

"Ina yini Ya Haidar!"
Bai amsa ba sai kallo na da yake. Kaina na dukar kasa.

"Baby na kinga yadda kika koma kuwa. Kinyi kyau wallahi. Ke kullum ma dada kyau kike karayi."
Murmushi kawai Hafsat tayi.

Jikin sa ya jawo ta ya rumgume ta tsam. Dan rumgumar tata shi zai dan sa ya samu sasauci.

Momy ce ta bude dakin. Da sallama ta shigo da sauri na janye jikina daga nashi.

Kai ta girgiza kawai tace,
"Ku fito ana jiranku fa."

Shi ya amsa da toh muka fita. Hannun sa rike da nawa.

A wata sabuwar mota aka kai mu. Motar golding colour ce sai kwalli take.

Wajen ya hadu sosai. Manyan mutane sun halarta.
anyi mana nasiha sosai sannan aka ci aka koshi.

Kyaututuka dayawa na samu daga wajen abokan Ya Haidar dana Dady banda

Please Login or Register in order to submit comment