Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaki aminta dani, ko akasin haka, shiyasa duk na yini vikin fargaba duk na kasa sukuni." Ajiyar zuciya na saukar jin yadda ba wani abu ke damun sa ba. Yadda yake bayanin sa ma a tsare muryar sa na kara shiga jikina.

"Ayyah Kayi hakuri na hanaka sukuni. Ban son ta dalili na wani ya shiga cikin wani hali"
"Ba komai Hafsa, kinsan abu mai daraja ba ta sauki ake samun sa ba. Amman in dai bakya son ki ina shiga cikin wani hali akan ki to ki aminta dani da soyayyata."

Ni wallahi tsoro nake ji?"
"Tsoron me? Kisa Allah aranki duk abinda ya faru Allah yarigabda ya tsara miki. Duk da nasan kinsan da hakan. Addu'a kuma zaki nayi Allah kare ki daga sharrin mutum da aljan. Nima ina tayaki yi."

"Uhmm to nagode,"
"Ba komai. Ni na dade da neman zabin Allah. kuma ke nakejin zuciyata na aminta da ita dan sonki kara shigar ta yake."

"haka ne Allah yai mana zanin alkhairi."
"Ameen! nasan lokacin baccin ki yayi bari na barki sai da safe."

'Allah tashe mu lafiya."
"Ameen." Na kashe wayat.

Sakon sa ne ya shigo:- "Gaskiya nasan nayi da mata mai hankali, kyau, nutsuwa, ilimi, sai dai fatan Allah yasa ta aminta dani.
Jin muryar ki kadai kan jefani cikin wani halli, na shauki da begen ki. Hafsa ina kaunar ki. Kuma bazan taba daina kaunar ki.
Ki cire duk wanin tsoro daga zuviyar ki banzo dan in cutar da ke ba, ina fatan Hafsa dina zata aminta dani.
Kiyi Bacci mai dade Allah kare min ke.

Ameen nace na tufa addu'a na kwanta.


MS INDABAWA
08062882472
MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFW STORY



BY MARYAM S INDABAWA
MANS



page 26





Dedicated to My student *FATIMA SALISU,* *ZULAIHAT AUWAL,* *HASSANA & USAINA RABI'U,* *FATIMA ABDULLAHI,* *HALIMA AUWAL SHARIF.* love u soo much. U always make me happy.







Da dare bayan mun kwanta sai ga kiran Aliyu nan. Fita nayi dan nasan halin Faiza yanzu zata fara min cah.

Falo na nufa na zauna.
"Baby nah!"
"Na'am, yaya nah.'

"Ya gidan ya gajiyar biki."
"Lafiya. Gajiya tabi jiki.'

"Masha Allah, gobe I yanzu naga Baby na ko?"
"Eh! Mun dade da haduwa ma."

"In kin ganni zaki gane ni."
"Taya zan gane ka ban san ka ba."

"Haka ne! Bari na baki satar amsa. Dan da kin ganni ki gane ni."
"Toh."

"Gobe zan sa farar sadda da babbar riga xan hula mai adon baki, takalmi da agogo duk bakake. Dan haka da kin ga mai irin wannan shigar to gun ki yazo. Sai dai fa ni baki ne, sannan ban da kyau."
"Haba Ya Aliyu. Ni nace mutum mai kyau nake son aura ne,"


"Alhamdulillah matata ta yadda dani koma a ya nake, nagode miki hafsa sai da safe kije ki huta."
"Allah kaimu nagode."

Nayi daki na kwanta. Da tunanin yaya gobe zata kaya gani ga Aliyu.



Ranar daurin aure saddar da Ummu tai mana muka saka, ruwan goro sai zanen ruwan ganye, dinkin riga da siket sun amshe mu. wani ruwan ganyen mayafi muka saka mai duwatsu a jikin sa. Sosai mukai kyau. Da yamman ranar za ayi walima inda Malama Binta Yahuza xatayi lecture.

Tin safe akai mana kwalliya, wacce nace ni baza ai min shafe shafen nan ba. Hoda da jan baki sai ja gira kadai akai min, amman nayi kyau sosai.

Karfe goma mun shirya dan sai anyi sallah juma'a za'a daura auren.

Tin da na tashi nake jin faduwar gaba. Wanda duk ya sauyan yanayi. Faiza taje ta fadawa Momy. Momy da kan ta tazonta dauke ni.

Dakin Dadyn Faiza ta kai ni. Tace in zauna na huta.

2:30 naji karar wayata wadda tai dai dai da fadiwar gaba na. Dauka nayi na duba Aliyu ne,

Ji nayi dukan da kirjina ya ke ya dado wanda har sai da na dafe shi.
"Hello Princess. Kin tashi lafiya? Gani fa nazo. har an kaini boys quarter's din gidan."
"To gani nan."

Na dade a zaune kafin na iya tashi na fita. Bayan gidan na tafi kai tsaye bayan na fadawa mai aikin su Faiza ina da bako ta kawo masa abinci.

Har lokacin kirjina bai daina dukan uku uku ba.

Da sallama na shiga dakin.
A tsaye na hange shi ya juyan baya. yana amsa waya.

Kallo na kare masa. Gaskiya Aliyu cikaken namiji ne dan tin ta bayan ma hakan ya nuna.
Dogone shi mai cikar haiba, fari ne nagane hakan ta wuyan sa.
tabbas farar shaddar yasa ka da hula mai kyau wacce take da adon baki. Gashi ne kwance akansa mai kyau da sheki.

Kallon sa nake ko kiftawa bana yi, kamar yadda bugun zuciyata bai canja ba. Ga wani sanyi da nake ji sai kace mai zaxxabi.

A hankali ya juyo, ta kafar sa nasan ya juyo tinda kai na a sunkuye yake, wayar ya katse sannan , yace,
"Wow amman fa amaryata tayi kyau. Dama muma yau ne ranar mu da daga nan sai gidan mu."

Shiru nidai nayi, murmushi yayi, ya cigaba da magana.
"Hafsa yau dai ga Aliyu Haidar,a gaban ki, yake kyakyawa, sarauniyar yan matan duniya. Ina son ki dago ki kalli mummunan Aliyun ki, kiga ko zaki iya maneji dashi a matsayin mijin ki."

"Ya salam!" hafsa ta furta a ranta dan muryar sa ma kadai ta isa tasaka cikin nishadi,

"Daure ki dago na kalli idanun ki."
A hankali na dago ka na. Wanda hakan yai dai dai da faduqar gaba na. Na ganin wanda ke gaba na.


Fari ne dogo, yana da idanu manya, sannan hancin sa dogo ne, siriri. Da leben sa mai kyau sai sheki yake.

Murmushi sai tashi yake akan fuskar sa. waye wannan in ba *YA HAIDAR BA.*

Sai da tunanin ta ya dan dauke na mintina. Idon ta na kan sa.

Idona na murza, na kara budewa, amman dai Shi din ne a gabana. Ji nayi jiri na dibata. nayi baya da sauri ya tare ni. Na fado jikin sa.

Wani daddadan kamshi ya bugi hanci na. Bansan lokacin da na lumshe ido na ba. Na kwantar da kai na a kirjin sa ba dan juwa ke ta diba na.

Bayan minti biyar, naji na nutsu da sauri na janye jikina daga nashi.

Murmushi ya sakar min, sannan ya kama hannuna ya zaunar da ni akan kujera.

Sunkuyar da kai na nayi.
"Hafsat, Baby nah. Yau ga Aliyu Haidar din ki. ina fatan na miki zaki aminta dani."




*INDABAWA*
08062882472
*MIJIN UMMU NAH*
True life story



BY MARYAM S INDABAWA
MANS



🌐HAJOWπŸ“πŸŒ

πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§ HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾


Page 27




Dedicated to *Hajara M Bash*




Kai ta kara dukar wa, dan wata kunyar sa da nauyin sa take ji.


Yau gani ga Aliyu, duk dokin ganin san da nake yi sai gashi yau gani gashi amman abin naji shi qani iri.


Muna zaune najiyi sallamar Indo mai aikin su Faiza, shi ya amsa ta shigo hannun ta dauke da faranti kato sai Uwani tafe a bayan ta rike da kwando da kula da lemoka a ciki.


Gaisawa sukai sannan suka fice.
To taso ki zuba min naci. Dan yau ban ci komai ba. Ina dokin zuwa gare ki da sufar ainihi.

Idona ke kawai yake son gani. Sai dai kash gashi nazo, amman sam taki ta dago na kalli fuskar ta.

Hafsat dai shiru tayi bata ce komai ba.

"Wayyo ciki na! Momy nah"
Da sauri na dago kai na.sai naga ya rike ciki yana dariya. Kasa na kuma yi da kai na.

"Wayyi Momy na yunwa zata kashe miki Haidar din ki."
Kallon sa na kuma yi dan yasi ya bani dariya ma.

Ganin da gaske yake sai kace Momyn na wajen yasa na mike da sauri na isa wajen kayan abin cin.

Faranti na dauka ta bude fulas din.wainar shinkafa ce da sinasir. Dayan kuma fried rice sai miyar wainar da taji naman kaza. Lemon da snack a dayan farantin.


Na zuba masa komai a faranti daban daban na ajiye masa. Ni kaina nasan ba duka zai ci ba dan Ya Haidar bai daci.

Ina ajiyewa na mike na nufi kofar fita. Muryar sa najiyo cikin sanyi yana cewa
"Dan Allah Hafsat ki dawo ki zauna."


Ba musu na koma na zauna. Dan ni indai zaka hadani da Allah to in dai abin ba sabon Allah bane zanyi shi.

Abincun yake ci amman idon sa na kai na.
sanyi sanyi na fara ji yana ratsa ni na alamar zazzabi ga ciwon kai dake damuna. Ido na lumshe na jinginar da kai na da kujera.

Muna zaune najiyo karar wayata. Ina duba Hauwa ce.
"Ina kika shiga ne Hafsy ga angawaye sunzo ana hotuna.

zanyi magana naji ya amsha wayar. Sai da ya duba sunan sann ya kara a kunnen sa.
"Ga ta tare da nata angon. Amman gamu nan zuwa."

"Lah Ya Haidar kazo daman! Nifa naga ban ganka anan ba. Ashe kana nan kana tsinkar furenni."
Murmushi kawai yayi. Ya koma kan abincin sa.


"Lallai Hafsy sai mun hadu anjima."
"Me zaki mata."
"A'ah wannan kuma ni da ita ne."

"To shknn sai kun hadun." ya kashe wayar.

"Na shiga uku yanzu Ya Haidar sai da ya nuna wa su Hauwa akwai abu tsakanin mu." Hafsat ta fada a zuciyar ta.

"To mene dan sun san muna soyayya Hafsat. Ai sa tayani inyi nasara akan ki."
Ido na zari dan ko a tunani na yaji me na fada.

Amman sam baiji ba yasan dai zata ayyana hakan a zuciyar ta ne.

Goge hannun sa yayi ya nufo ni.
"Hafsat ki So ni kamar yadda kike son Aliyu dan ni din ne shi. Na miki alkawarin bazan canja daga duk abinda Aliyu ke miki ba kuma duk alkawarin dana dauka ina Aliyu zan cika miki su da izinin Allah."

Shiru tayi.
"Ni mai son ki ne. Bazan taba cutar dake ba. Haka nan bazan bari wani ya cutar min dake ba. Son ki ajini na yake."

Kasa tayi da kanta. Hannun sa yasa mai laushi ya dago kan nata.
Kallon kallo suka dinga yi.

Sam ta kasa dauke idon ta danki take kamar wani mayan karfe ne a cikin idon sa ya makale mata nata. Ba abinda take gani cikin kwayar idon sa sai tsntsar son ta da kaunar ta.

Haka shima sam ya kasa daina kallon idanon ta masu kyau da kyalli. tabbas ya gano son sa acikin idanon ta to amman ya fison ta amince ta yadda dashi itama ta furta masa.

Sai da tayi karfin hali sannan ta janye idon ta da kyar. Idanun ta, ta lumshe kamar yadda shima ya lumshe nasa. A tare suka saukar da ajiyar zuciya.

Mikar da ita yayi. Ya jawi ta jikin sa. Kokarin sumbatar ta take. Gane hakan da tayi, yasa tayi saurin dukar da kanta.

Dariya yayi ya rumgumeta. Sannan ya dago ta ya kamo hannun ta sukayo waje.

A hankali suke tafiya hannun ta makale da nashi duk yadda tasi ta cire ammn sam ha matse hannu.

Suna fitowa harabar gidan aka fara musu hotuna dan sunyi kyau sosai ke kace sune amarya da ango.

"Please Ya Haidar ka sakeni. Baka ganin mutane ne."
"To mene dan na rike hannun kanwata kuma matat."

"Ni dai Please!"
Ta fada kamar zatayi kuka."

Sakar ta yayi. Yace
"Allah kika matsa a gefe na sai na kamo ki."

Wannan yasa ta tsaya daga gefen sa. Duk hoton da za'ayi tana gefen sa.

sunyi dmsu shida. Ango da amarya da Ita da Ya Haidar, sai Hauwa da Ya Nura.
Hoton ba karamin kyau yayi ba

Sann sukai matan kadai.



*INDABAWA*
08062882472
MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY



BY MARYAM S INDABAWA
MANS



Page 25




Dis page is urs *SADNAF* Allah kara basira da daukaka. Allah yasa kifi haka. Allah yasa ki gama lafiya Ameen.




Addu'a na tofa na janyo bargo na rufe jikina, bacci me dadi ya dauke ni cike da mafarke kala kala.

Kuma da Ya Haidar nayi mafarkin abin ya bani mamaki sosai mai ya kawo Ya Haidar cikin mafarki na. Ko da yake mafarki ba gaskiya bane.

Da Asuba ma mamakin mafarkin na ringa yi.



*Lokaci nayi kwanaki na juyewa su zama satitika haka satitikaa kan rike de su zama watanni.*



Yanzu watannin mu 5 da hadu ta da Aliyu, kamar yadda ya fada min sunan sa haka kuma yana zaune a lagos, yana aiki a company mahaifin sa a matsayin manager.


Soyayya muke taba wa ba laifi. Kullum muna waya ko chatting, duk da yanzu na rage kunyar sa amman da akwai kunyar nan bama in yana min maganar aure.


Ya haidar ma kullum sai munyi waya kamar yadda kullun muke tare da su hauwa a waya.


Makaranta kuwa yanzu munyi nisa dan mungama level 2 Yanzu level 3 zamu tafi first semester. A makaranta kuwa ba ruwa na da kowa daga gaisu bana karawa duk da mutane da yawa naso na da mu'amala. Amman ni janye jiki nake.

Karatu kam alhamdulilah in ban gane ba akwai dan kawar Ummu dake koya min karatun shima lecturer ne a BUK.


Khadija ma yanzu tana Level 2 bangaren Anatomy.



Rayuwa tayi gaba, komai lafiya sai dai matsalar Mijin Ummu nah tana nan, dan wata kara tsanar mu yake.

Ga kazafi da yake jafar mu dashi. Yace muna yawo da maza. To Ummu duk abinda Ya fada mata ko menene yadda take dashi wannan yasa zata rufe mu da fada. Duk da tasan Khadija ba kula maza take ba bare kuma ni.


Bikin Faiza sai da aka dada wata 7 saboda ya Kamal zaije wani course a germany. Wannan yasa aka dada wata 7 tinda wata shida zaiyi.



Bayan wata shida

Ya kamal ya dawo cikin nasara inda akai masa karin girma.

Hauwa kuwa ta samu ciki amman ya bare, inda Faiza kuma biki ya kuma gangarowa. Saura wata daya.

Aliyu kuwa ya matsa min kan yazo amman nace sai na kamala karatu tukkunna duk da ina son ganin sa.


Yanzu haka muna shekarar karshe a makaranta a second semester yanzu karatu ya dau zafi.




*****----*****
Zaune nake a harabar gida ina jiran zuwan Faiza dan zamu kai dinki.

Ya Haidar ne ya kira ni, na dauka muka gaisa.
"Amman bro ya kamata ka taho tin yanzu dan ka ragewa kanin naka zirga zirga."
"Wallahi Hafsa nima ina son nazo. To aiki nee ya min yawa amman zan samu na yakice shi."

"Toh Allah kawo mana kai lafiya."
"Ameen."

Mukai sallama.




Bayan kwana goma sai ga Mama Fatima maman Ya Haidar a gidan mu ta sauka. Dan suna son kai laifen Faiza.

Sosai nayi murna da zuwan Anty na. Dan Mama Fatima na sona sosai komai ta kawo ni.


Ana saura sati biyu bikin Faiza aka kai laife. Ranar gidan mu Faiza tayo. Laife sosai Ya Kamal ya hado mata wanda ya kashe kudi masu yawan gaske banda wanda Mama Fatima ta kawo masa daga lagos. Da wanda Ummu take daukar masa in an kawo mata kaya.


Ranar yinin mukai vedio call da Hauwa inda tace, sai sauran kwana biyar xata taho. Saboda in sun zo sai sunyi sati uku zasu koma. Sosai nayi murna.



Ya Haidar kuwa cewa yayi sai sauran sati zai zo. Ai kam sati na yi ya dira gidan mu Ya Kamal ya kawo shi dan shi a lokacin yana da aiki.

Yana direshi ya tafi. Ahinci masu rai da Lafiya na hada masa. Ya Haidar ya kara kyau ya murje. Ya kara fari. fatar sa sai sheki take.

Wata farar atamfa na saka. Wacce akai mata zane da gashin dawisu da take da adon ja. Sai jan mayafi da na yafa. Banyi kwalliya ba amman ni kai na nasan nayi kyau.


Muna zaune daga ni sai shi, dan Ummu tana dakin ta, tayi baki. Ido Ya Haidar ya zuba min. Duk sai naji na kasa sakewa dan wata kunyar sa nake ji.

"Hafsat wallahi kin kara kyau."
"Kai Ya Haidar a hakan. duk makaranta ta kodar da mu."

"Tab amman makarantar nan kyau ta kara miki."
"Ka dai fada ne kawai."

"Yanzu to ya batun aure kuma?"
"Hmm aure sai Allah ya kawo mijin,"

"Allah ya kawo sai da kar kiyi wasa da damar ki," ban gane me yake nufi ba. Sai nace,
"To Allah zaba mana mafi alheri."

"Ameen."
"To kai fa Ya Haidar?"

"Nima na kusa kwanan nan dan bana son na kai wata shekarar."

"Toh Allah sanya alheri."
"Ameen."


Daga haka shiri mukai. Karar wayata yasa nayo cikin daki. Kiran Hauwa ne, nake ce mata Ya Haidar ya diro. Tace eh sun yi waya daga haka tai min maganar kalar abin nake da bukata.
Mukai sallama

Missed call din Aliyu na gani guda 5 sai message nashi. Sakon na bude.
" *Baby ina kika shiganina ta kiran waya amman shiru, daman ce miki zanyi na shigo kano yanzu, kuma ke nake son fara gani sai gashi bakya kusa da wayar. Gashi hobe jigawa zan tafi sai laraba zan dawo.*
*Nasan mu da mu hadu sai laraba ko alhamis. Ki gaida su Ummu da Khadija.*"

" *Ayyah ban ji dadi ba amman. Amman Allah kaimu Larabar nagode.* " Ta tura masa.

Falo tayo, nan ta samu Ya Aliyu na duba waya yana dariya.

Ranar sai karfe goma Ya Kamal yazo ya dauki Ya Haidar


Washe gari gidan su Faiza naje, ta matsam sai naga laife ni kam ban iya wani kallon kayan laife b.

Rabo kuwa mun jima da gama shi.
Tin daga ranar da Ya Aliyu ya zo ban kuma ganin sa ba. Ko da na tambayi Ya Kamal ce min yayi, yayi tafiya sai laraba zai dawo.

Aliyu kuwa safe da rana da dare muna tare dashi a waya.

Ranar Monday Hauwa ta dira a gidan ta. Dan ni da Faiza muka gyara mata mukai musu girki.

Damu Ya Kamal yaje ya dauko ta. Hauwa tayi yar kiba tayi fari ta kara kyau sosai.Bayan anci an koshi ne su Ya Nura suka fita.

A lokacin ta fito da akwatin kayan da tai mana.
code less masu kyau tayo mana ni da ita kala daya na amarya nata daban. Sai jakunkuna da takalma da dan kunnaye da sarka da abin hannu. Kayan masu kyau na yan gayu haka ta kawo mana.

Banda wanda Ummu tayi mana wata sadda da atamfa. Momyn Faiza tayo mana leshi.

Da magaraiba muka tafi, Faiza kuma sai karfe tara Ya Kamal ya maida ta gida.

Tin ranar talata muka tafi gidan su Faiza ni da Hauwa.
Dakin Faiza muka sauka. Anan akai mana lalle da gyaran kai.


Ranar laraba mukai children day, yara suka saka ruwan hodar riga da bakin wando. Nima Ruwan hodar riga nasaka mai bakin dowatsu. Hauwa kuma ta saka Ja da adon baki. Amarya kuma ta saka ruwan omo da duwatso bakake. Ango ma bakar suit yasa ka haka su Ya Nura. Sai a ranar naga Ya Haidar yayi kyau sosai kayan sun amshe shi.

Khadija da Bishira ma sunyi kyau cikin Ruwan hodar riga har gwiwa da bakin wando sai mayafi baki.
Wajeen dai masha Allah yayi kowa yayi kyau sai yan ciye ciye da akai sai gift da amarya ta bawa yaran


Ranar ansha rawa amman ni ina gefe. Ya Kamal da Faiza ma sun cashe. Su Khairat ma yara ba abar su abaya ba.

Su Khadija da Bishira suma sun cashe bama su da suke tashen yam matancin su.

Ranar Alhamis. Aliyu yai min waya ya dawo tin jiya. Yaso mu hadu Alhamis nace sai juma'a tinda yace, Zai je daurin aure.

Ranar akai Mothers even. Wata jar atampa muka sa da adon yello. yan matan amarya suka saka ibo rapper ruwan omo da ruwan dorawa. inda kawayen Momy suka saka tasu. Ibon Ruwan omo da ja.Anyi kyau kuma anvi ansha an bada Kayan rabo.



*INDABAWA*
08062882472
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY


BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*



🌐HAJOWπŸ“πŸŒ

πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§ HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾



page *28*






A hankali ta samu ta zille can bangaren Dady. Zaman tunani tayi tama rasa wanne kalar tunani zatayi.

Ido ta lumshe. tana rufewa taga Ya Haidar. Da sauri ta bude sai dai taga baya wajen.

Da ta kara rufewa sai dai taga Ya Haidar yana mata murmushi.
"Wayyo Allah nah."

Ta fada a fili dan bacci take so ko dan ta samu sauki a zuviyar ta. Amman yaki zuwa.


Sako ne ya shigo wayar ta, na Ya Haidar.
*" ki fito muyi sallama zamu tafi walima."*

"Tab ashe baza kaje ba. Indai sai nazo ne."
Ta fada tana kara mikewa akan kujera.

Karatun kur'ani ta fara cikin zuciyar ta. Wannan ya bawa bacci barawo damar dauke ta.

Momy ce tashigo dakin wajen karfe 3:30 dan ganin Hafsat na nan. A can cikin kujera ta hange ta tana bacci. Ta kane ta cure waje daya kamar mage.

A gefen ta zauna,
"Hafsa! Hafsat"""
"Uhmm."

"Tashi har karfe 3:30 fa."
Da sauri ta mike.
"3:30 wallahi Momy ban san lokaci ya wuce haka ba."

"Ti tashi kiyi sallah."
Ta mike tayi hanyar qaje.

"A'ah! ina zaki? Baga bandakin Baban ku nan ba."
Dawowa tayi ta shige. anan tayi alwala ta fito hijab Momy ta mika mata.

Ina tayarwa ta fice. Lokacin da na idar ta shigo hannun ta rike da basket. A gabana ta dire shi.

"Maza zo kici. Kinsan nawa Ummun ki alkawarin kula dake. Dan haka maza zo kici kar bayan biki kizo ulcer na tashi."

Jawowa nayi na zuba na fara ci. Kadan naci na tsame hannuna.
"Hafsat har me? Ko bakya son masar ne in kawo miki shinkafa."

"A'ah Momy na koshi ne."
"A'ah daure ki dada kadan."

"Toh!"
Nace na fara ci. Turawa kawai nake. har naji zanyi amai. sunkuyat da kai nayi.

Murya a shagawabe nace,
"Momy na koshi."

"To shikenan. Tashi ki tafi gun yan uwanki."
Na mike tara da daukar basket din jiki ba kwari nayi kitchen na dire. Sannan nayi dakin Faiza.

Dakin na shiga. Duk suna zaune ana ta hira. Sun canja shiga zuwa wata super holland blue da maroon kala.

"Sannin ku." Nace dasu.
"Yauwah!" suka amsa.

Hararata Faiza tayi nima na wurga mata.
Hauwa, tace, "yar gatan Momy. A ina Momy ta boye kine."

Murmushi kawai nayi. Na cire kayana na jefa mata. Dan Allah taimaka min da wuce ban daki.

Wanka nayo na fito.
"Yauwah beauty dan Allah ki tsaya nai miki kwalliya man."
Inji wata kawar su zubby da take musu kwalliya.

"A'ah zubby rabu da ita. Dan in ta yadda yanzu to wallahi aniima bazata yadda ba."

Dariya ma suka bani. Na ganin sai lalalabani ake duk dan na bari ai min kwalliya. shiryawa nayi nima cikin irin atamfar da suka saka.

Nace,
"Allah sarki! Yan uwa zanyi kewar ku."

"Kar ki damu muna tare ai."
Sai hawaye sharr. Dukkan su suka rufeta suna tamabayar meke damun ta. "Kuma in kewar mune ai kema nan kusa ne ko."

Ganin dai da abinda ke damuna yasa suka fitar dani can boys quarters mukaje. Sai na kara rushe musu da kuka.

"Wai manene hafsat." Cewar Faiza, itama idon ta ya ciko da hawaye. Hauwa ma haka.

"Allah kuka bar hawayen nan ya zubo, ya bata muku kwaliiyar nan sai munyi fada."

Sai duk suka shaye kukan, Faiza tana goge hawaye.
"To fada mana mene damuwar ki." Hauwa ta fada tana rike hannun su."

"Sisters wallahi ina cikin damuwa."
"To ai shine nace ki fada mana."

"Ina wanda nace yana min text din nan?"
"Eh!"

"Bana ce muku zai zo ba."
"Eh! Bai zo bane?"

"A'ah!"
"Amman ko ki fada mana. Ki hada mu."

"Uhmm ba haka bane."
"To menene?"

"Kunsan waye kuwa." Ta fada hawaye. Na kara zubo mata."
"Haba dan Allah ki daina kuka. Kar ki karya mana zuciya."

"Kunsan waye?"
"Sai kin fada."

"Uhmm Ya Haidar ne."
"Ah dan Allah fa. Alhamdulilah!"

"To menene? Abin kukan da damuwa."
"Haba Hauwa, kukan me ma kike cewa."
"Ah Hafsat! Gaskiya banga abin kuka. Mene da Ya Haidar. Mene na kuka a kanshu." Faiza ta fada.

"To dan me zai tayin yawo da hankali na?"
"Na tabbata, indai yazi kai tsaye baza ki saurare shi ba. Sanan halin ki." Cewar hafsat
"Hafsat!" Fauza ta kira ta.

Ddagoqa tayi ta dubeta.
"Menene yanzu a ranki bakya son sa ne ko me?"
"Eh!"

"Eh!" Auka hada baki suka fada tare da zari ido.

*INDABAWA*
08062882472
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY



BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*




🌐HAJOWπŸ“πŸŒ

πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§ HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾

page *29*



Dedicated to u *Anty Fatima* love u so much.








Faiza ce ta kamo hannun Hafsat tace,
"Ki nutsu dan Allah menene aibun sa, duk kyan nan nasa, duk cikar halittar sa da nutsuwar sa, ga ilimin ta haba Hafsat ki nutsu."

Hauwa tace,
"Wannan kadai ma kika sani faiza, ni da muka zaune da Ya Haidar tare ni zab fada miki kowaye ya Haidar.
Ya Haidar mutum ne mai hankali, nutsuwa, kirki ke komai ga ilimi both, ga tsafta, gayu ke kinga yadda yan mata ke sonsa. Sai kece zaki juya nasa baya.
Wallahi samun namiji kamar Ya Haidar sai an bata lokaci, Allah ya dube ki ya dubi addu'ar da maraicin ki, kuma ki, ki amsa hannu biyu."


Tayi shiru.
"Na tabbata zai kula dake dan mutum ne mai kula akan abinda yake so, In har kin samu Ya Haidar kin gama dace dan ya cika duk wani abu da za'a so namiji."

"Hafsat!"
"Na'am"

"Indai tamune, kiso shi, amman fa kiyi istihara. Neman zavin Allah, amman zanso ki so Ya Haidar."


Shiru Hafsat tayi, tabbas Ya haidar ya gama haduwa, kyakyawa ne. Masha Allah a ktau dai ba baya bane.

Ilimi ma akwai shi arabi da boko, dan ina gani yadda yake gudanar da abubuwan sa cikin tsari, da ilimii.

Dan ko

Please Login or Register in order to submit comment