Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kayan yayi. Sannan ya tura kayan magungunan gaban gadon.

Hafsat kuwa duk kunya ta cika ta kanta yana kasa.
Nurse din ce ta matso tai mata allura sannan Ta mika mata magani.

Bata fuska Hafsat tayi.
"Haba Baby yayan ta ki daure kisha man. Kinga Yayn ki ya gaji da zaman asibiti."
Ta fada da zaulaya.

Karba tayi da kyar ta iya hadiye su. ya Haidar ya dinga shafa mata baya.

Har taji ya fada. Sannan aka sa mata ruwa dan jikin da har yau ba kwari.

Soyayya iya soyayya Ya Haidar na nuna mata dan har sai da Nurses da Likoci suka lura dasu.

In Hafsat taki shan Magani suce Ango fa ya kosa.

Wannan yake sawa dole take karba dan ita kunyar irin maganar take.

Satin su uku suka nemi sallama dan su koma gidan su tinda sai bayan kwana biyar take ganin likita.

Sallama aka rubuta musu suka koma amman duk safe da dare sai nurse tazo ta kara duba ta har gida.



Gida ne madai daici mai yalwace da shuke shuke. Sai baban falo da dakin bacci guda hudu


Zaune yake akan kujera mai daukar mutun uku. Hafsat ce kwance akan cinyar sa. Idon ta a lumshe, sai wasa yake da gashin kanta.

"Ya Haidar!"
"Na'am me kike so?"

"Kaina nake son a wanke min."
"Ok yanzu ko anjima."

"Ko yaushe?"
Kanta ya ajiye a kan kujera ya mike ya shiga dakin su. Kaya ya canja. Sannan yazo ya dauke ta kamar Baby

A kan kujera ya zaunar da ita.

Kanta ya fara wanke mata da shamfo. Sai da ya gama wasa da gashin ta sanna ya dauraye mata.

Dryer ya dauko ya busar da kanta sanna ya daga ta tsaye. Kayan jikin ta ya cire mata ya rage daga ita sai ves da 3quarter wando.

Kokarin cire mata wando yake. Ta kamo hannun sa ta girgiza masa kai.

Murmushi kawai yayi yaja hannun ta suka fita.

A kujerar gaban mudubi ya zaunar da ita.

Oiling din gashin ya farai mata. Ita dai kallon mamaki ta tsaya yi.
"Sai da ya gama shafe shi da mai sannan ya taje mata shi a hankali a hankali. Ido yasaa ta rufe.

Three babies yai mata ya kame ko wanne da kallar ribon da ban. Gashin ya zubo ta hefen fusar ta.

"Wow!" Ya furta a fili lokacin da ya kalleta ta mudubi.

"Bude idon!" Ya fada jikin madubin ta kalla. Ita ma sosai taga kyan abun da yai mata.

Ta cikin madubin ta zuba masa ido shima ita yake kalla.

Sun jima suna kallon junan su ta mudubin.



*indabawa*
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY





BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*






🌐HAJOWπŸ“πŸŒ

πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§ HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾







Page *53*







Sun jima suna kallon juna sannan ya dagota.

"Baby na kinyi kyau."
Ido ta lumshe tana murmushi.

Jikin sa ya jawota ya rumgume.
"Wash!" Tace.

"Menene Baby nah, ina yake miki ciwo."
"Jikina ne yake ciwo."

"Ayyah sannu."
Ya fada yana jan ta kan gado. Kwantar da ita yayi sannan yace,
"Bari nai miki tausa."

A hankali ya dinga matsa mata jiki. Idon ta a lumshe, daga baya bacci ya dauke ta.

Wayar sa ya dauko ya dinga daukar ta a hoto.





Su Ummu da Mama Fati kam har sunyi visar zuwan su wajen su.

Basu fada musu ba sai ranar da zasu taho. har dasu Hauwa da Ya Nura dasu Faiza.

Koda suka fadawa Ya Haidar bai fadawa Hafsat ba.

Tana kwance a Dakin su da Three babies din da yai mata. Doguwar riga ce a jikin ta.

Bacci take ji. Amman kuma tasa Ya Haidar ya soya mata kwai. Shiyasa taki barin baccin ya dauke ta.


Bata san lokacin da baccin ya dauke ta ba. Kwan ya dauko da yai masa hadin tumatur a ciki.

Ganin tai bacci yasa ya ajiye mata a gefe a cikin fulas.

Gate din gidan yaji an bude. Ta taga ya hude yaga waye.

Mota ce ta shigo. Ya Kamal yaga ya fito a ciki. Da sauri ya fita a dakin.

Shi ya budewa su Ummu da Momyn sa. Wata mota ce ta kuma shigowa su Faiza da Khdaija da Hauwa ne.

Falo sukayi. Bayan an gaisa ne suke tambayar jikin Hafsat.
"Jiki Alhamdulilah Dan ya daura ta akan magani ne da tuni mun dawo."

"Toh Alhamdulilah. Tana ina ne?"
"Bacci take kunsan mara sa lafiya."

Haka ne! Allah sauwake toh!"
"Ameen!"

"Ku shigo ku ganta."
Momy ce ta mike ta kamo Hannun Ummu dan ta lura kunyar yar fari take ji.

Dakin suka shiga.
kallon ta suka tsaya yi. Ta rame amman tayi fari da ita. Bacci take sha hanin an.

Dakin da take suka zauna Ummu da Momy.

Sai mazan suka sauka a daya inda Hauwa, Faiza da Khadija suka dau daya.


A falo suka ci abinci gaba dayan su. Sai da akai sallah la'asar sannan Hafsat ta tashi.

Agogo ta duba taga hudu har da mintina. Ban daki ta shiga tayo wanka tai alwala da sallah.

Fulas din gefen ta ta janyo. Kwan da Ya Haidar ya soya mata. Zama tai ta fara ci.

Tana tunanin ina Ya Haidar yake da bata ganshi yana jiran tashin ta ba.

Sai da ta gama sannan ta koma ta nade a kan gado dan ciwon kai ta tashi dashi.

Ummu ce ta shigo dakin da sallama.

Da sauri ta mike dan ganin wake shigo dakin. Idon ta ta kara gogewa. Ummun dai ta gani tsaye.

Da gudu tayo wajen Ummu. Ta rumgumeta, Tana hawaye.

Falo ta ja ta sukayi. Ganin su duk a zaune Ta kara sa ta fashe da kukan farin ciki.

Da gudu su Hauwa suka zo suka rumgumeta.
"Kuyi mata a hankali dai " Momy ta fada.

Juyowa Hafsat tayi,
"Momy!" Ta fada tana yin wajen ta. Rumgume juna sukai sannan tayi kan kujera da ita.

"Amaryar mu ya jiki." Ya Nura ya fada.

Kasa tai da kai.
"Jiki Alhamdulilah!" Ya Haidar ya fada.

"Ah gaskiya ai ga alama nan. Wa yayi miki abin kan ki."

Sandarewa tayi tuna abinda yake kan ta. Kan ta ta cusa a cikun cinyoyin ta.

"Wa zai mata in ba ni ba."
Dariya suka saka.


"Dago 'ya ta ki rabu da Yayan nan naki."


Dan kwallin kan Khadija ta fizga ta daure kanta. Sai suka kara sa dariya. Jikin Momy ta kara lafewa.

Hira aka zauna anayi.

Sai dare nurse tazo ta bata magani sannan ta tafi.

Dakin da Su Ummu suke can ta nufa.







*indabawa*
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY






BY *Maryam S Indabawa*
*MANS*










🌐HAJOWπŸ“πŸŒ

πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§ HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾







Page *54*









Dakin su Ummu taje ta kwanta dan maganin na sata bacci.


Kwanciya tayi, amman kuma ta kasa baccin dan ta saba da matsar jikin da Ya Haidar ke mata in zata kwanta.

Yana ganin ta shiga dakin yabi bayan ta.

Jin bude kofa tayi a zaton ta su Ummu ne, dan haka sai ta lumshe udon ta.

Gefen ta ya kwanta.
"Baby na nasan baki bacci ba.'

Juyowa tayi.
"Ya Haidar na kasa jikina ke min ciwo."

"Na sani, abinda nazo miki kenan ai."
"Me fa?"

"Matsa miki jiki."
"A'ah nagode kar su Ummu su shigo"

"To mene in sun shigo, ba matata bace."
Shiru tayi dan tana bukata.

Yana fara mata tayi bacci. Murmushi yayi ya gyara mata kwanciyar ta koma falo.

Washe gari muna zaune a falo. Kai na akan cinyar Momy!
Ummu ce ta fara magana.
"Hafsat me ya kawo miki firgici ranar daurin auren ki."

Hawaye ne ya zubo mata.
"Ummu ina zaune a dakin ki. Abbi ya shigo, ina jin maganar da yake miki. Akan sai dai a daura aure da shehu tin daga lokacin ban kara jin abigda ya faru ba."

"Innalillahi! Daman *Mijin Ummu* ne sanadiyar kwanciyar ki. Wallahi sai na sa an kama shi."
Ya Kamal ya fada.

"Ai ko baka fada ba sai an kama shi wannan wane irin mutum ne?"
"A'ah kubar shi kawai ba komai. Allah daman ya riga ya kadarta."

"Baki da hankali ne?"
"Ya Kamal ba haka bane, ai ko dan darajar Ummu ai ma barshi."

"A'ah Hafsat ki bari su ne ma miki hakkin ki."
Ummu ta fada

"Ummu in dai har ni za'a nemawa hakki to na yafe. tayaya zan kalli Khairat duk so da kaunar da Khairat ke nuna min."

Ta fada tana kallon Khairat dake gefen ta a kwance.
"Wallahi na yafe masa. Ta fada tana kuka."

Ya Haidar ne ya taso ya dago ta sukai cikin dakin su.
"Haba Baby mene na kukan kina son kisa damuwa a ranki ko."


Kai ta girgiza masa,
"To ki daina me zan kawo miki kici."
"Ba komai."

"Har cake din ma bakya so."
"A'ah ina so."

Fita yayi ya dawo rike da faranti. Sai lemo.

Shi ya dinga bata har ta koshi. Hira ya zauna yana jan ta da ita. Har ta sake daga baya suka fito falon.


Ummu sosai take jin dadin yadda Ya Haidar ke kula da Hafsat.

Satin su Ummu daya suka juya aka bar su, su kadai. Dan sauran sati biyu ta gama shan maganin ta.

Momy na komawa ta wuce lagos.

Abbi kuwa ganin wahalar da yake sha ya sanya fadar garin su da iyayen su.

Ko da aka fadawa Maman sa cewa tayi Allah kara ba inda zata bare kudin ta yai kuka.

Wani daga cikin yan gidan ne ya fada wa Ummu, hankalin ta tashi yayi dan Ummu akwai tausayi.

Kadunan ta tafi ita ta biya kudin da ake binshi. Sannan tayo bellin sa.

Duk yayi baki ya rame, ko da suka zo gida yaga Baraka sai da ya tsorata.

Dan duk ta rame ita ma. Bayan yai wanka yaci abinci ne, take fada masa abinda ya faru da salima.

Sosai ya tsorata dan bai taba zaton haka ba.

Ashe shi abinda akewa ya'yan sa bai kai wanda yakewa ya'yan matar sa ba,

Lalai Allah abin tsoro ne. Kuma akace in zaka gina ramin mugunta ta gina shi dai dai kai.

Shi yana ganin yana musgunawa ya'yan matar sa ashe ba komai yake musu ba.

Kuka ya fara na nadamar abinda ya aikata. Neman yafiyar Ummu ya fara tace. Ita ba komai Allah yafe mana gaba daya.

Har dakin su Hafsat yaje yana neman yafiyar Khadija. Banza tai dashi tabar dakin ma. Dan tsana iya kar tsana Ya nuna musu ita.

Kuka ya dinga yi dan yasan in ba dan Ummu ba ba wanda zai taimake shi,


Ummu ya tambaya ina Hafsat,
"Hafsat tafi wata bata kasar nan tin ran daurin auren ta ta fadi."
"Innalillahi wainnalilahir rajiiun."

Ya dinga nanatawa.
"Allah sarki baiwar Allah! Allah tashi kafadun ta. Mariya dan Allah ki ya fe mun."

"Wallahi ni na yafe maka."
"Nagode ki rokar min su Hafsat ma dan Allah!"

"Hafsat bata rike ka da komai ba. Dan tin da mukaje tace ita ta yafe maka."
"Allah sarki Hafsat Nagode. Amman duk da haka ki kada nemanin yafiyar ta."

"Insha Allahu."





*Indabawa*
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY





BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*





🌐HAJOWπŸ“πŸŒ

πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§ HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾







Page 55







Kwance take akan gado, bayan an mata allura tasha maganin ta.

Ya Haidar ne ya shigo rike da faranti a hannu,
"Baby na tashi kici abinci."
"Bacci Ya Haidar!"

"Daure kici." Ya fada yana mikar da ita. A jikin sa ya jingina ta, langwabewa tayi tana masa shagwaba.

Wani yanayi yaji yana shigar sa. Wata matsanaiciyyar sha'awa yake fama da ita.

Ya dade yana fama da ita dauriya kawai yake, a haka ya daure yana bata a baki.

Har ya gama. Rumgumeshi tayi tsigar jikin sa ce duk ta mike. Kwantar da ita yayi ya dauko roba da brush din ta. Shi ya wanke mata bakin sannan ya mai da.

Kara janyo ta jikin sa yayi yana shinshinar wuyan ta zuwa kirjin ta. Wata irin ajiyar zuciya ta sauke,ta kara shigewa jikin sa.

Sai da bacci ya dauke ta sannan ya samu ya janye ta a jikin sa.
Kallon ta ya tsaya yi, gashi ga Hafsat amman kuma bai son mata komai dan yasan ba lafiya ce da ita ba.

Wanka yaje yayi yayo alwala ya zo yai sallah. Kan gadon ya hau ya janyo ta jikin sa. Ko zai samu saukin a binda yake ji.

Matse ta yayi har sai da ta saki yar kara. jijigata ya dinga ji a hankali har shima baccin ya dauke shi.

Da asuba shi ya tashe ta tayo alwala tai sallah.

Wanka ya hada mata ruwan. Shi ya rakata har ban dakin. ya rufo ta.

Tana fito wa ya nufe ta da towel yana tsane mata jikin ta. Gefen gado ya zaunar da ita, ya dauko mai yana shafa mata.

Sannun a hankali har ya gangaro cinyar ta. Ido ta lumshe kawai dan wani yanayi taji yana ratsa ta. Towel din da ta daure saman ta dashi ya cire.

Bama tasan ya cire ba. kallon ta ya tsaya yi.

jin saukar hannun sa a saman kirjin ta yasa "ta saukar da ajiyar zuciya mai karfi tare da bude idon ta a tsorace.

Ido ta zuba masa, kai ya kawar ya cingaba da abinda yake yi. Kifawa tayi kan gadon.

Murmushi yayi ya rufa mata baya. Bargon dake kan gadon yaja ya rufe su.

Bakin ta ya laluba ya hade da nasa, sannan ya dinga wasa da albarkatun kirjin ta. Kokarin magana take amman sam ya ki sakar mata bakin ta.

Ya dauki a kalla minti talatin yana jagwalgwala ta sannan ya sake ta. Lokacin jikin ta yayi sanyi lakwas.

Dunkulewa tayi waje daya ta rufe fuskar ta. Dariya yayi ya rufa kan ta ya rada mata.




"Ya Haidar dan Allah ka bari!"
"Me zan bari?"


"Ni dai.." ta fada a shagwabe kamar zatai kuka.

"To shikenan!"
Dago ta yayi, tashi muje nai miki wanka.

"A'ah ni kaje kawai."
Murmushi yayi, yace,
"To bari na hada miki ruwan.

Ban daki ya shige ya gado mata ruwan zafi.

Bari naje nai wankan. Kafin na dawo na shirya ki.

Shiru tayi, yana fita ta mike ta rufe dakin.
Ta dade tana zaune kafin ta shiga bandaki ta tsarkake jikin ta. Mai kade ta shafa, ta zire dguwar riga sai hijab da ta saka.

Kan gadon ta gyara sannan ta hau ta rufe jikin taa. Knocking taji anyi ta bude.


"Nurse ya zo!"
"Ya Haidar walllahi, na gaji da shan maganin nan kuma ni naji sauki."

"Oh haba! Kace daga nan mu zarce honeymoon din mu."
"Nifa ba haka nake nufi ba. naga yanzu ai ban jin ciwon wajen."

Dariya yayi.
"A'ah fa kin warke. Ai naga alama dazu."
"Kai Ya Haidar!" ta fada kirjin sa tana dukan sa.

"Yi hakuri baki warke ba." Ya Fada yana jan ta waje.

Tea ya haada mata mai kauri tasha. sannan aka bata Magani tashi akai mata allura da sai da kyar ta bari akai mata.

Nurse din tace "Hafsat kin fiya shagwaba ko dan kin samu miji me son ki ne."

Hararar ta Hafsat tayi kawai.
"Yi hakuri allura daga gobe an gama. Jibi zaku je ganin dr. in yaga komai normal sai tafiya."

Murmushi Hafsat tayi.
"Oo ji me hararata taji zata gida. taga Momy ta ko."

Ranar waje suka fita suka zaga dan sai yamma suka dawo.


Siyayya sosai ya dinga mata. Tin tana ta isa har ta daina magana.


Sunje wajen likita anyi gwaje gwaje komai ya zama dai dai.

Dan haka nan da kwana biyu zasu koma.

Ranar da suka koma gida, murna ta dinga yi zata koma gida.

"Wai murna nan fa?"
"Zanje naga Ummu na."

"Wa ya fada miki a lagos zamu wuce."
"Haba dai!"

"Ki zuba ido ki gani ma."
Ganin da gaske yake ba alamun wasa yasa ta fashe masa da kuka. Ita sai taje Kano tukunna.

Lallashin ta ya fara yi amman sam taki yin shiru. Gashi har jikin ta ya dau zafi saboda kuka.

"Yi hakuri zamuje Kano kinji."
Kuka take sosai, amman tai shiru tace.
"Da gaske!"

"Eh!"
"Ka min alkawari."

"Eh na miki."
Jikin sa ta fada tana murna. Rumgume ta yayi shima.

Sumbatar wuyan ta ya fara. Da sauri da janye jikin ta. Tana murmushi. Murmushi shima yake.

Kunnen ta ya kamo yai mata rada a ciki.
"Kai Ya Haidar nace ni ka daina ko!"
"Naki!"

"Sai Kayi tayi."
"Au haba!"

Shiru tayi, ya matso kusa da ita kafin tai wani yun kurin har ya hade bakin su.

Ya salam! Wani abu taji ya tsikare ta. Jikin taa ne yai lubus.
Sai da ya gama tsotse bakin ta. Sannan ya sake ta.


Kan ta ta kifa akan kujera. Dariya yake mata. Dago ta yayi Amman ta rufe idon ta.

Daukar ta yayi ya kai ta kan gaado. Bargo taja ta rufe jikin ta.


Baci ne ya dauke ta. Shi ya canja mata kaya sannan ya tofeta da axdu'a,






*Indabawa*
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY





BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*






🌐HAJOWπŸ“πŸŒ

πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§ HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾






Page *56*








Ranar da suka sauka a Nigeria murna kamar me. Jirgi suka kara hawa yai Kano dasu.

Ya Kamal ya kira yazo ya dauke su. har dasu Faiza da Khadija aka zo daukar su.

Gida suka nufa kai tsaye. Su Faiza da Khadija kam sai murna suke dan jiki alhamdulilah.



Ya Kamak nayin packin ta bude da sauri ta fice.

" *Ummu nah!* " ta fara kwada mata kira.

Ummu ce ta fito da sauri ta tari yar ta.

"Hafsat Alhamdulilah jki yayi jyau ko?"
"Eh!"

"Aliyu sannun ku da isowa "
"Yauwah Ummu."

Ciki suka shige, inda aka tare su da. Abinci cika kala kala.

Ya Haidar ne yaci amman ita Hafsat duk hankalin ta na kan Faiza da Khadija.

Gidan Ya Kamal, Ya Haidar yaje, Inda Hafsat kuma ta zauna a gida.

Sai dare taga Baraka. Gaisawa sukai sannan tai mata ya jiki.

Bayan fitar Khadija ke bata labarin komai har da tuban Da Abbi yayi. Sosai Hafsat ta tausaya masu.

Allah sarki Abbi na yafe maka duniya da lahira Allah ya yafe mana baki daya.

Ba abinda Ummu take barin. Hafsat tayi, komai yi mata ake.kowa kulawa yake bata.

Abbi har daki yaje ya duba Hafsat. Sam Hafsat bata nuna masa komai ba amman Khadija sam ko kallo baya isar ta.

Sosai Hafsat tai mata fada.
"Khadija mene abin kin yafewa Abbii. Kar ki manta *Mijin Ummun* mune fa.
Mece rayuwar da har zaki kullace sa. Allah nason mai yafiya haka nan in baki yafe masa ba kika san me zqkiyi wani shima yaki yafe miki.
Mece duniyar Khdija in yau mune gobe bamu bane. Ya kamata ki duba yar sa Khairat yadda Allah ya hade kan mu ya daura mana kaunar junan mu."


"Kiyi hakuri Anty Hafsat in na tuna irin tsanar da hada mun da yake da hada mu da Ummu ne abin yana batan rai.
kiga fa shine silar ciwon zuciyar ki."

"To mene Hafsat wani ma silar mutuwar wani yake, kuma ba da niyyar hakan yai ba. Ki yafe masa kema Allah zai yafe miki."

"Shikenan Anty Allah yafe mana gaba daya."
"Ameen ni nasan zuciyar ki mai yafiya ce."
Suka rumgume juna




Me gyara aka kuma dauko wa dan ta dan kara murje ta. Lokaci guda ta kara canja kala bayan wacce tayo.

Kullum sai Ya Haidar yazo kulawa sosai ya cigaba da bata.

Kwanan ta shida Ummu ta fara hada mata kayan ta.
"Ummu kayan me ake hadawa ne?"
"Kayan tafiyar ki mana."

"Ina zani?"
Kallon mamaki Ummu ta tsaya yi mata. Sai kuma tace,
"Ai kinsan yanzu kina da aure dai to gidn mijin ki."

Idon tane ya kawo ruwa, tace.
"Ummu ni wallahi ban son na tafi na barki."
"Hafsat ai tafiya ta zama dole tinda kowa haka yake tafiya yana barin gidan su. Ki sani aure bautar Allah ne Hafsat. Ki zama mace ta gari a wajen mijin ki."

Kuka Hafsat ta fashe dashi.
"Haba Hafsat mene na kukan. can ma ga Anty Fati nan. Mijin ki na son ki haka itama na son ki,"
"Ummu ni wallahi na fasa aure. Ban son barin ki."

Ganin da gaske Hafsat take yasa Ummu janyo ta jikin ta na lalashi ta,


A haka Ya Haidar ya shigo ya same su. cikin rudewa ya fara tambayar lafiya


"Uhmm! Wallahi shagwabar ce yau ta motsa. Wai ita baza ta tare ba."
Murmushi kawai yayi ya samu waje ya zauna.

Fita Ummu tayi,
"Baby na wai ciwo yasa kika zama rigimammiya ko me?"

Hararar sa tayi,
"Eh man! ai da naga ba haka kike ba. Ba ruwan ki amman' yanzu shagwaba rigima duk ke kadai sai kace autah. Ko da yake kamar autar ce tinda ni na fari ne kuma Auta kinga a can kin zama autah ko?"

Murmushi kawai tayi.
"Baby na kinsan ina son ki to dan me kike kukan tafiyar mu.mu da zamuje mu bude sabuwar rayuwa mai ciki da farin ciki. Ki kwantar da hankalin ki bazan taba bata miki ba insha Allahu."

Murmushi kawai tayi.
"Yauwah ko ke fa. Yanzu me kike bukata."
"Ba komai,"


"Anya?"
"Eh!"

"To shikenan jibi zamu tafi."
Shiru tayi.

Khadija ce ta kawo masa abinci tare suka ci shi da Hafsat.







*INDABAWA*
*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY





BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*





🌐HAJOWπŸ“πŸŒ

πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§ HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾






page *57*









Momyn sa ya fadawa cewa jibi zasu taso.
Momy tace,
"Haidar ai da ka bari ta kara jin sauki ko."
"A'ah ni Momy wallahi na gaji."

"Ka gajin uwaka. Yarinya ba ishashiyar lafiya ba."
"Allah ta warke "

"ba wani warke wa. Ka barta ta kara warware wa. Kai ka taho jibin."

"wa? Ni ai Momy kafata kafar Hafsat."
"Ai kam zan yi maganin ka."

Ta kashe wayar.
"Momy kenan nima fa ina bukatar matata wallahi." Ya fada yana kwanciya duk kewar ta na damun sa.

Inda da hali tare zasu na kwana. Amman ba yadda zai yi. sun dai kusa su koma.

Momy, Ummu tayi wa waya kan cewa kar ta bari ya taho da Hafsat.

Ummu dai Ta amsa mata ne amman ita gara yaro ya tafi da matar sa ya huta.

Da yanzu tayi wata biyu a gidan ta fa. Kayan ta wadan da ba a kai mata ba Ummu ta cigaba da hadawa.

Ana gobe zasu tafi sukaje gidan su Kawun ta sagiru da Baba Ado sukau musu sallama.

Nasiha sosai sukai musu da adduar zama lafiya.

Gidan Ya Muktar suka je, shima nasiha tare da addu'a yai musu.
Anty Bilki taja Hafsat dakin ta. Abubuwan mata ta hada mata sannan tace,

"Hafsat ina matukar taya ki farin ciki da samun miji na gari me sonki kamai Haidar Na dade ina miki adduar samun miji na gari to Alhamdulilah Allah ya amsa mana. Dan haka kiyi masa biyayya kiyi hakuri da zaman tare dan ance zo mu zauna zo mu saba dole wataran zaku samu sabani.
Nasan ki akwai hakuri da juriya da biyayya Allah baku zaman lafiya da zuria ta gari."

kuka Hafsat ta fashe dashi ta rumgumeta.
"A'ah ki daina kuka. Zaman aure da dadi da wuya. Sai an jure ake samun dadin . Nasan ban da matsala dake haka ma Yayan naki insha Allahu."

"Nagode Anty Bilki."
"Ba komai na dauke ki kanwar da muka fito ciki daya da ita."

Hawayen take goge mata.
Suka fito suka tafi gida.

Da dare ma haka Ummu ta sata gaba tana.kara jan kunnen ta.
"Hafsat ki zama mace ta gari wacce mijin ta zai na alfahari da ita.
Ki kyautata masa ki masa biyayya shi da iyayen sa. Kar ki bari yayi fushi dake.
Hafat ki rike bautar ubangiji ki kasan ce me yiwa mijin ki addua akan komai yasa gaba. Kina jan hankalin sa in kinga ya kaucewa hanya.
Girki da tsafta basan ban da Matsala da ke to kar kisa lalaci ki daura daga inda kika tsaya."

Muryar tace ta fara rawa wannan yasa tayi shiru. Mikewa tayi ta fita a dakin.

Kuka Hafsat ta fara dan sai yanzu take jin keewar barin gida da wata kauna da soyayyar iyayen ta. Da yan uwan ta.


Momy vata san bidirin da ake ba dan ita a zaton ta Haidar ne kadai ta taho.






Ranar da zasu tafi kuwa Hafsat duk tayi tsuru tsuru da ita. Dan har ranta ji take baza ta iya bin saba.

Jikin ta yayi sanyi komai cikin sanyi take yin sa.

Bayan kukan da ta kwana ta nayi duk idanun ta sun kumbura sunyi ja dasu.

Da safe ma kasa cin abinci tayi. Sai da Ummu ta lalashe ta.

Khadija ma kuka take haka Faiza da tazo kuka take. Hauwa kuwa tana can tana murnar zuwan yar uwar ta.

Shi da Ya Kamal suka zo. Bayan sun debe kayan ta. Yai wa Ummu sallama.

Tin da ya shigo gidan bai ganta ba.

Ummu ce tace, ta fito su tafi. Faiza tai mata kwalliya cikin wata atamfa fara da ja. Ta saka jan mayafi da takalmi. Sosai tayi kyau sai kamshin turare take.

Idanun ya jajir. Ga kwalla da ta taru.

Gaban Ummu taje ta tsugunna.
"Ummu ki yafe min duk abinda nai miki."
"Baki min komai ba Hafsat. Allah baku zaman lafiya."

"Ammen!" Suka amsa.
kasa tashi tayi sai da Faiza tazo ta daga ta.

Ita ta rike ta har suka fice. Ko kallon sa batai ba shi kuwa duk ya kosa su fitan ya lalashi abar sa.

Motar Ya Kamal aka shiga da ita tare dasu Khadija. da itama idon ta sunyi ja.

Gidan gaba ya shiga amman duk hankalin sa na kan Hafsat.

Suna fitowa aka fara kiran suna. Kayan boot suka fitar. Kuka Hafsat ta kuma fashewa dashi.

Faiza ce ta rumgumsta tana bata hakuri. Har tayi shiru sai ta hangi Khadija. Da gudu ta fada jikin ta tana sakin wani kuka.

Kuka sukai kamar wanda akace bazasu kara haduwa ba.

Sai da aka fara kiran sunan su sannan Ya Haidar ya dawo dan tafiya da ita.



Ganin su suna kuka yasa zuciyar sa kara sanyi.
Rumgume su yayi yana basu hakuri.

Sannan sukai shiru. sallama tai musu hawaye na zuba a idon sa.

Suka juya suka shige.





*INDABAWA*
*MIJIN UMMU NAH*
True life story









By *Maryam S Indabawa*
*MANS*







🌐HAJOWπŸ“πŸŒ

πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§ HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾






Page *58*











Ko a cikin jirgin ba abinda yake sai lallashi. Har suka isa. Da tayi shiru zata kuma fashewa da kuka na tuna gida.

Sai ajiyar zuciya take saukar wa.

Suna isa driver yana jiran su. Motar suka shiga. Shigar su kenan

Please Login or Register in order to submit comment