Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rashin daraja ka ne ko nuna baka isa ba yasa na fada maka abinda na fada maka ba..kawai dai naga kana fassara ni ne kan ba yadda nake ba kuma kana nuna kamar ina maka_
_boye boye amma kayi hakuri."_

Tare suka sauke ajiyar zuciya.

Ukhashatu yaji dadin batun da tayi shi a takaice amma ya wanke mishi zuciya jira yake kawai yaji matsayin shi a wajenta.
Cike da murmushi yace,
"Na yarda dake.!!
Tayi d'an takaitaccen murmurshi kafin tace..
"Kai zabina nane kuma zabin Abba nah.."
Farinciki mara misaltuwa ya bayyana a fuskar Ukhashatu yayi mata kyautar tsadadden murmurshi.
Nagode mai sunan Hajiyata."
Sai lokacin bakin shi ya bude ya samu damar tambaya. Cikin hadewar rai kamar bashi yayi mata murmurshi yanxu ba.
Waye wancen toh."?
Ta dan zaro ido kafin ta saduda tace "He's my ex!!
Don bata iya k'arya ba.
"Exxx"??
Ya tambaya yana jan kalmar.
Hafsah ta danyi murmurshi.. ina mamakin yadda kake had'uwa da mutanen da suka dade da barin rayuwa.
Ta tausasa murya believe me wallahi duk randa kuke had'uwa nima ranar nake qara ganinsu bayan tsahon lokaci.!!
Ya jinjina kai kafin yace "Zaki bani labari but ina zuwa.!!

Ta kalleshi da mamakin abinda yake shirin yi sanda ya fita.
Shiko gun Yusuf ya fita kai tsaye ya mishi sallama Don bazai iya bashi hannu ba saboda kishi.
_Yusuf wanda nutsuwa ta fara zuwar mai sai abinda ba'a rasa ba wanda ya zamar jiki_
Ya amsa asanyaye.
Babu bata lokaci yace.
Kaine kaxo wajen Hafsah koh."?
Yusuf ya jinjina kai da sauri yana k'ara kallon Ukhasha yana tunani ai kamar dai Hafsah bata da yaya namiji.

_"She was like she's the first born kamar dai haka ya santa ya manta dai."_

*"Kayi hakuri an mata miji kada ka sake zuwa neman ta!!*
Inji Ukhashatu cikin maganar shi mai kama da gargadi wanda ta girgiza Yusuf ya kasa katabus.


Ukhashatu na k'are zancen yabar mishi gurin.

Yana dawowa Hafsah ta zuba mishi ido.
Cikin mamaki ta tambaye shi "me kace mishi."?
Ya dan harare ta "ina ruwanki mai kuka."?

Ta kawar da kai cike da kunya..
Yayi kasa da murya.. me yasa a lokacin baki tambaye ni ba kin ce.
"Malam shin an baka ni ne da kake kafa min dokoki."?
Gaba-d'aya suka sa dariya.
Ukhashatu ya kalli hannunta dake bisa cinyarta babu zobe ko daya ajikin yatsun zai jan kunshi a iya yatsun daya saka sukayi kyau.. baisan sanda yakai hannu ba yayi kamar zai tab'a sai ya fasa ita kuma tayi saurin dauke hannanyen. Ya hada hannaye alamun Afwan ta dan hade rai.
Sannan yace "Ya baki saka zoben a hannunki ba ko baiyi miki ba."
"Ai baka ce nawa bane ta fad'a da zolaya."
Ya nunata da hannu. "Kinganki koh."?
To ki saka... ya rage murya ko sai na sa miki."?
Tayi saurin girgiza kai a kunyace shima yayi dariya sannan ya duba ya juya can sit din baya ya dakko wata leda ya mik'a mata yana fad'in "Ungo amarya.!!

Lokacin ita kam ta nutsa cikin tunani kan abunda suka faru yanxu.. wato attempting (yunkurin ) taba hannunta da yayi sai kuma cewar zai sa mata zobe da yayi.. abin ya tuno mata da da sanda Yusuf yasa mata zoben shi..
Ta tambayi kanta..
_"Me yasa abin yaso maimaita kansa"?_
Bata zargin Ukhashatu da komai tana mishi kyakyawan zato sai ta ta'allaqa hakan kan yadda suka kebe a guri mai irin mota su biyu. Dama addini ya hane mu da haka.
Astagfirullah!!
Ta motsa baki ta fada.
Acikin karamin sauti yace tunanin me kike neh uhum"?
Tayi saurin juyowa tasa hannu biyu ta amshi ledar da abinda ke ciki daya fi kama da ice-cream.

Bai magana ba ya bude motar.
Ya fita sannan ya zagayo ya bude mata itama ta fito suka fuskanci juna..
Bari na tafi kada dare yayi min amma in sha Allah gobe zanzo ki bani labarin kinji."?
Ta gyada kai sannan yasa hannu a aljihun shi ya ciro katina ya bata "Gashi wannan na bikin Qanwata maryam tace na kawo miki in sha Allah gobe zan taho dana Abba."
Shima tasa hannu ta amsa.
Ki shiga gida sai in tafi yace mata.
Ta mishi murmurshi sannan ta juya cike da farinciki ta wuce.
Yayi murmurshi shima komai kan idon Yusuf.
Har kwalla yaji ta zubo mishi.

Har Ukhashatu yabar wajen Yusuf tsaye.
Sai da ya gaji da kanshi yabar wajen.


Bacci mai cike da farinciki Hafsah tayi bayan ta koma cikin gida sun baje ice-cream d'in sannan ta mik'a wa mama katinan.. Amira ce tace "amma dai yaya ba zaki je ba koh"?
Bata ce komai ba saboda mama dake wajen..
___________________________

Yusuf ya koma gida jiki a sanyaye ya rasa me yake mishi dad'i yanxu shikenan ya rasa Hafsah."?

In ko hakane zai jinginar da zancen aure duk da yana buk'atar auren a yanzu.
Wato abinda ya nutsar dashi kan batun aure shine:
Tun lokacin da mahaifinshi ya rasu wata daya baya sanda aka k'are zaman makoki wasu daga cikin dangi suka hadu suke ta mishi nasiha da misalai iri.
Sun nuna mishi yadda mahaifinshi ya rasu ba tare da yaga jikanshi ba. Sun nuna mishi yadda rasuwar taxo bag-tatan wanda shima Yusuf ba karamin kaduwa yayi da batun rasuwar ba gani yake kamar a mafarki.. wai daddyn shi ya rasu.
Sun mishi misali da shi kadai ne wajen iyayenshi haka babanshi shi kadai kakarshi ta haifa."?
Duk da ada hakan baya damunshi amma yanzu ya damun ko dan mahaifiyar shi zata so taga ya'yanshi ita.

Sannan sun nuna mishi girma ya fara kamashi don akallah zaiyi shekaru talatin da abubuwa.

Tunda akayi rasuwar ya rage hulda da yan matan shi kuma indai ba gaisuwa zaki mishi a waya ba baya bari kuyi hira.
A lokacin rasuwar mahaifiyar shi taga tarin yan mata kala-kala wanda ta rasa daga ina suke.
Wai don ma kadan daga ciki kenan masu raguwar tarbiyya da tausayawa da suka zo mishi gaisuwar.
Sai lokacin kuma hankalin ta ya tashi tasan d'anta ya wuce tunaninta a kallah kullum ta kanga bak'in yan mata biyu zuwa uku har akayi bakwai kuma suna zuwa cewa suke "ina Yusuf."?


Yusuf bai k'ara saduda ba sai da yaga sun dawo kwana shida mum d'inshi kadai a gidan sai yan aiki gashi mum din kullum cikin kuka yake.

Babu wacce ke yawo a kwanyar shi kullum kamar Hafsah.. amma yana tsoron tunkarar ta. Ita kadaice yaji zai iya aura ba tare daya sa shakku akanta ba a ranshi.


To yau ga abinda ya tarar. Duk da bai sa ran zai ganta ba amma ganin nata ya haifar mishi da damuwa mara misaltuwa.

Ya raba dare babu bacci yana saka yadda zaiyi ya samu Hafsah amma ya rasa mafita. Gashi zuciyar shi ta kasa hak'ura. Ya zauna sosai ya dinga tariyo rayuwar da sukayi a baya cike da shauk'i da yanda komai ya dinga faruwa kamar Film, zuciyar shi na kara ingiza shi.. _shiya san yarintar ta don haka shiya dace ya aure ta!!_


Da kyar ya rik'i wani abu da yake tunanin shine mafita.

________________________
Yau tunda Hafsah ta tashi take jinta cike da nishadi ji take babu sauran damuwa.

Yau abin mamaki sai taga abban ta har dakin ta bayan ya mata knocking tana jinshine taji wata fargaba lafiya Abba har d'akinta yau.
Shiko cewa yake Yaya bude kinji muyi wata Shawara."

Ak'asa ta zauna ta dukar da kai da fargabar wane muhimmin abu ne yasa abban takowa da kafarsa."?

Abban ya zauna gefen gado.. ya fara da nasiha da rarrashi kafin ya fada wa Hafsah abinda ta k'agu taji.

Aure ba abin wasa bane Hafsah babu lallai mijinki ya yarda ki cigaba da aikin gidan TV saboda haka kiyi hakuri ki ajye in sha Allah Allah zai baki wani.. nima bana goyon bayan ki zauna babu wata sana'a ko wani aiki."
Ta dago a hankali ta kalleshi wato zancen Ukhashatu dai..badon tayi imani bazai iya yiwa Abba wannan zancen ba da sai tace shine ya roki Abba, amma tasan basu hadu ba kuma bazai wa Abba zance a waya ba.

In sha Allah Abba zan ajiye zan rubuta resigning zuwa qarshen satin nan.
Ya fad'ad'a murmurshi Allah yai miki albarka in sha Allah da kaina zan sama miki wani.
Tayi murmurshi nagode Abba. Duk da gefe tanajin babu dad'i saboda sabo da mutane..


Bayan fitowar Abba daga dakin nata cikin mamaki yaji labarin wai yayi bako a waje.

Da fitar Abba yayi mamakin ganin saurayi Abba ya mik'a mishi hannu suka gaisa.
Babu jira Yusuf ya fara bayani.

Abban nazo wajen Hafsah ne shine take cemin wai anyi mata engaged kuma wallahi yanzu da gaske nake aurenta zanyi ina sonta Abba."

Abba ya tsaya sororo yana kallonshi wane irin yaro ne wannan magana babu ladabi babu iyawa haka ake neman auren."? Shida yasan Hafsah bata kula kowa to shi daga ina yake kenan."?

Waye kai."?
Abban ya tambaya.
Nine Yusuf Abbah, I dated Hafsah years back har kace na turo..lokacin ban shirya bane..
Abba ya gane shi wato yaron daya hargitsa masa rayuwar gidanshi ne yaso ya hure wa yarshi kunne. Abin ya bawa Abban dariya har sai da ya dara sosai lallai yaron bashi da ta-ido wato har jawabi yake. Gefe guda kuma Abba ya gode wa Allah daya ga wannan yaro ido da ido.
Take ya tuno komai da sanda yasha gwagwarmaya da Hafsah.
Abba ya dan hade rai saboda ya takaita koma meye yace..
Wato sai yanzu ka shirya koh."? To anyi mata miji kaji.. kuma ka dakata da zuwa wajen ta."
Nan Yusuf ya Shiga magiya Abba ya daga mishi hannu kaje gida Allah ya baka wata kaima. Daga nan Abba ya juya ciki.
Aka bar Yusuf kamar ya fasa ihu.


Abba ya shiga gidan yana dariya, yasa a ranshi ba ma zai fadawa Hafsah ba sai dai kuma zai bawa Amina labari.

Sun kuwa sha dariya sosai shida ita.
_Kinga abu kamar mafarki ko amina."?_
Ta gyada kai.
Yace alhakin kine dana yarki ke ya dinga sawa shakku da kokarin sa miki hawan jini ita kuma tana matuk'ar sanshi shiko yana k'okarin bata ta.
Mama ta d'ora "sannan ya yaudare ta ba ai dama na roki Allah sakayya."!!
Ya kalleta suka sa dariya.


Ukhasha yazo kamar yadda yayi alqawari sun sha soyayyar mu shida Hafsan shi a hankali cikin hikima da wayo yadda bazai zargi wani abu a ranshi ba ta bashi labarin rayuwarta ta baya wacce ta kunshi Yusuf da Basma da Jamila. Daga karshe ta nuna masa yadda Basma tayi mata snatching.
"Kaga ina na d'auke ta aminiya ashe saurayina take so."
Hafsah ta fada mishi hakane don bazata iya fad'a mishi zahirin abinda ya faru ba da yadda Yusuf yake ko don gudun zargi..

To ya akayi kika gane ta kwace miki shi."?
Tayi wani murmurshi kafin tace naje gidansu ne naga yazo zance wajenta."
"Hmm..yace..
Ku fa mata haka kuke waya ce miki zance yaje."?
Ta kalleshi kallo mai kama da harara.
Yayi murmurshi "To ai gashi Allah ya baki ni koh."?
Tayi murmurshi.
Hakane."?
Ta gyada kai.
Ukhashatu yayi k'okari ya nusar da ita yadda rayuwa take. Sannan ya nuna mata ta dauki komai yadda yaxo kada tunanin baya yasa tace zata kusanta kanta da Jamila domin yanzu ba da bace.. _"wasu mutanen zama dazu sai shafa maka bak'in fenti ne kawai.."_
Idan tazo wajenki kada kiki saurarar ta amma kisan irin mu'amalar da xakuyi. Dama irin haka a rayuwa dole a dinga samun shi. Muma suna nan wadanda munyi yarinta tare dasu amma yanzu mu da su sai dai Hi hi tunda kowa akwai layin daya dauka. Kuma kowa da yadda Allah ya tsara mishi rayuwa..


Hafsah ta yarda da duk zantukan shi 100% kuma ta kuma tabbatarwa da kanta lallai Ukhashatu shine ya dace da ita kuma shi _Masoyin k'warai_ ne.

Daga nan suka shiga wata hirar yana tambayarta.. me zamu tsara ne na bikin mu uhum amarya.?
Cike da kunya ta kawar da zancen da cewa.
"Resigning.!!
Ya kalleta yana dariya.
"Ai mun gama maganar ranki ya dade."
Wannan umarnin Abba ne."
Ta fada."?
Cike da zumudi yace Allah."?
Ta jinjina kai.
Kaii Allah ya k'ara nisan kwana gaskiya na gode zanyi wa Abba godiya.
Anjima ma za'a turo kanina ya kawo mishi Invitation Abba yace bazai bani ba wai gwara ya aiko takanas tunda ni na zama dan gida."?
Hafsah ta kalleshi "ka fiya zolaya Allah."
To ba haka bane."?
Hakane.
Tace mishi.
______________________

Yau Hafsah ta k'ara karbar ba k'uncin jamila sai dai cikin wani yanayi na daban wanda Jamila tazo dashi abin tausayi domin da kuka ma ta shigo.


Sai da Hafsah tayi da gaske sannan Jamila tayi shuru ta fara sanar da ita abinda ke faruwa.

"Hafsah na dawo gida yau..Uwar dakina ta rasu yan uwanta sun kwashe komai nata gidan da muke ciki ma sun koro ni dole na dawo gida."
Hafsah ta zaro ido da mamaki "Innalillahi tun yaushe ba kince tafiya xakuyi ba."?
Da ita ne dama kuma ba muyi tafiyar ba ma ta rasu.
Tausayi ya mamaye Hafsah ganin yadda Jamila ke kuka.



D'akin yayi shuru sai da Jamila ta sha kukanta sannan ta bude baki tace fara bawa Hafsah labarin yadda rayuwarta takasance bayan barinta gida.


Hafsah ta bata dukkan hankalinta Jamila kuma ta bude baki ta fara.


"Hafsah nasan kema kina min kallon wacce take zaman kanta koh."?
Duk da hakan ne bani da maraba tunda ba gaban iyaye na nake ba... labarin nada tsaho amma tunda ya riga ya wuce babu amfanin tunawa sai dai zan fada miki wasu abubuwan a takaice ne..

_Bayan barina gida. Nasha gwagwarmaya ta rayuwa ga ciki ajiki na (don nasan kinji labarin komai.)_
Nayi rashin mahalli da tudun dafawa har takai ina na rasa inda zan nufa.

_Tunani na ya gushe na manta da k'awa ta ta makaranta._

_Da kyar na samu abinci a yammacin a wani wajen cin abinci. Wanda na zama tamkar mabaraciya a wajen._

Sai da na ci abinci sannan tunani na ya dawo. A lokacin na tuno da k'awar tawa "Samha"


_Da kyar na ari waya na kirata a rikice. Tayi min kwatancen gidansu. Bani da kudin mota haka na fara takawa a k'afa. Wanda daga karshe dai da kyar na hau abin hawa wanda sai bayan dana sauka ne nake ce mishi ya min taimako bani da ko sisi. Don ba'a barni na fito da ko biyar ba daga gida. Mutumin nan har Allah ya isa yayi min don yace kamata babu yadda zaayi akalleni ace bani da kudi. (Sanda na sami dama na mishi sadakar kudin shi.)_


Ta girgiza kai sannan ta d'ora.

Na tarar da Samha cikin wani irin yanayi a gidan su. Da alama ba mahaifiyarta ce a gidan ba. Kuma na tabbatar da hakan bayan nayi kwanaki a gidan saboda yadda naga suna fada da matar gidan kamar sa'ar ta. Kusan kowa na gidan basa shiri dasu kuma ta raina su.

Ranar dana isa gidan ma suna ce-ce-ku-ce da matar gidan.

Na bata labarin duk abinda ya faru dani a gidanmu da yadda 'sir Garba' ya yaudareni.
Amma sai naga ita hakan bai zama damuwa a wajenta ba.

Ta nuna min babu komai har da bani shawarar "na zubar mana ai ba kaina farau ba.

Ban yarda da hakan ba amma bansan me ya faru ba na wayi gari cikin ciwo kuma bayan munje asibiti aka tabbatar da zubewar ciki na. Nayi jinya sosai ta watanni duk a gidan su Samha. Ni kaina ina mamakin gidansu babu ruwan kowa da rayuwarmu ni da ita shiyasa nake zamana cikin kwanciyar hankali a wajenta.

Na zargi Samha kan zubewar ciki na amma sai nabar abin cikin iya zuciyata saboda itace ci na itace sha na.


Na zauna gidan su tsahon watanni da suka kusa rufa shekara.

Samha kullum sai tace in shirya nasa 'spare' uniform dinta muje makaranta amma sam naki saboda na tsani makarantar ma gaba-d'aya. Sai dai na bata sak'o a wajen Sir kan cin asabar daya min duk da baya makarantar yanxu amma ta isar d'in.


Nabar gidan su Samha bisa dalilai da dama na yau da gobe da kuma halayen Samha wanda na kasa ganewa.
Na fahimci Samha tafini wayewa da budewar idanuwa kafin daga bisani na fahimci ta shallake tunanina tunda har takan iya maida mata maza a wajenta.

Bansan tana da wannan dabi'ar ba sanda muna makaranta sai dai babu tabbaci kan ko batayi ne a lokacin amma sanda gwada min haka take lokacin naji bazan iya cigaba da zama da ita ba.

Rayuwar danayi a unguwar su yasa na saba da wasu makobtansu ciki har da wata mata maiwa yan aiki hanya.

Na je har gidanta na roketa kan ta samamin aiki na gaji da zaman gida.
Bayan dogon kallo daga matar sannan ta min shagub'e kan me zai kaini aikatau bayan ina k'awar Samha."? Duk wayewar mu. Domin babu wanda a unguwar baisan ni ba kawar Samha bace.
Wani abin mamaki shine yadda babu kunya matar ta ke tambaya ta. "Kodai abin ya daina karbar ki ne."? Inada wani malami da zai dawo miki da tauraruwar ki."!!

Banyi fushi ba kuma ban nuna mata ba haka nake ba tunda bani da mafita. Sai dai na nuna mata matuk'ar buk'atar aikin wanda daga k'arshe ta yarda zata kaini sai dai ta yanka min wasu kudade da zan biya ta idan na fara aikin. Ta nuna min tasan inda zata kaini. Bangane nufin ta ba sai dai naji tace..
Na fahimci k'afa kike nema so zan kaiki inda zaki k'ara goge wa dama haka irin ku kuke lumbe-lumbu kuke kuyi kwanton bauna ku goge sannan ku gagari masu gida.."!!

Sai ta sheke da dariya.

Na rok'eta hadi da bata cin hanci kan kada ta fad'awa Samha ina neman aiki. Ta nemi dalili ta rasa. Wanda da kyar na samu ta yarda duk da tana ta mamakin dalilin boyewa ta.

Mun saci jiki sau da dama munje gidanmu nida Samha na kwaso kayana sanda mahaifina bayanan. Mahaifiya ta nuna tsayawar ta duk da sanda baba zai koreni bata nuna wani abu ba domin tasan halin sa zai iya hadamu ya kora.


Nasha gwada in koma gidan mu amma babu damar hakan har mahaifiyata ta gwada min in saduda.


Daga karshe dai matar nan ta samar min aikin kuma nayi mamakin gidan da ta kaini. Gida ne na mata masu zaman kansu.

Takamaimai bansan wa zan dinga yiwa aiki agidan ba sai dai an fada min aikina.
Share-share da wanke-wanke da aike shine aiki na.


Sanda suka ganni sunyi complain kan nayi musu girma harda masu cewa ni uwar mata ce ko suce sumumu-kasau... da kyar suka yarda na fara aiki wanda dole nazama tamkar wata doluwa.

Nasha wuya sosai agidan nan mara dadin tunawa.
Domin mata ne su wajen goma sha amma babu yadda za'ayi wata ta sani aiki wata bata sani ba idan nabar na daya nasha zagi har da duka. Maza ke tururuwa a gidan ba dare ba rana haka kawai ake kyara ta wai mazansu na kallo na ni munafuka ceh..
Sun sha cewa zasu koreni amma ina basu hakuri har da kuka..

Azaman da nake a gidan ne tunanina ya fara sauyawa kan irin rayuwar da suke anya nima bazan fada ba domin neman mafita ta."?
Amma wallahi dana tuno ki sai inji bazan iya ba.


Nayi akallah shekara agidan kafin wani mutumi da yake zuwa wajen wata ya yaudare ni.
Mutumin ya dade yana nuna min wasu abubuwa har saida yasan yadda yayi ya fita dani a motar shi kan zan karbo wa uwar dakina sako a wajen shi.

Mutumin ya kasance mutum na biyu wanda bazan taba mantawa dasu ba a rayuwata. Zan sa shi layin wadanda suka taimaka wajen gurbacewar rayuwata.


Ya huren kunne da hilata kala kala wanda tun bana yarda da shi har na fara sakin jiki.


Naci duka sanda suka gane haka a lokacin ne suka nemi su koreni...
Aunty sadia kawarsu ce don tana yawan zuwa gidan. Allah ne ya kawo ta Aranar ta ceceni itace ta tafi dani gidan ta lokacin ina ga ina da shekaru 18 lokacin tasan yan ajinmu sunyi candy.


Na kasa gane irin rayuwar da take ko irin tasu ce. Nasan dai tana business sai sai yawan bak'i maza a gidan ya zarce misali.

Ta nemi taji tarihi na daga bakina da kuma gaskiyar abinda ya faru dani. Na fada mata komai a lokacin ta gargade ni kuma tayi min fada mai shiga zuciya.


_Ke yarinya ce kinyi kankanta kisa rayuwarki cikin wannan abubuwan kada in kara jin hakan ya faru.. tunda komai daya faru a rayuwar ki ki d'auka kaddara ne mu idan zaki ji namu tarihin zaki ji naki ba komai bane._

Tayi min jan ido wajen cewa duk ranar da taga wani abu shigen wanda nayi acan to zamana ya k'are.
Tayi min wani gargadi da cewa "Ki bar manya suyi ke yarinya ceh."
Na kasa fahimtar me take nufi sai dai na gimtse abun nabita yadda taxo min. Nidai nasan na wuce sahun yara kuma zuwa lokacin nasan abubuwa da dama..


Mun zauna nida ita tana kula dani har yau bazan manta da ita ba.
Jamila ta share hawaye.

Ta yi kokarin maida ni gida sanda tayi wani tunani a kaina amma baba ya koremu. Cewar shi naje na k'ara tambadewa sannan zan kara dawo mishi gida. Har Allah ya isa yayi hadi da tsinuwa idan har na k'ara zuwar mishi gida. Duk abin matan gidan sai da suka bashi hakuri amma yaki hak'ura.

Mun rayu da ita babu tsangwama tayi min komai ban rasa komai ba amma kullum gargadinta dani akan na fita harkar maza ne.

Tana yawan fada min cewa "Maza mayaudara ne badon yaudarar su ba da bata zata tsinci kanta cikin wannan rayuwar ba."

Bata taba ban labarin ta ba har muka rabu amma nasan tasha wuya fiye da tawa.
Mamakina shine yadda yan uwanta ke zuwa gidan ciki harda mahaifiyar ta kuma suyi hira sannan su tafi da kayan arziki.

Na goge da rayuwa a zamana da ita tayi min komai sai dai bata taba min tayin maida ni makaranta ba kuma nima ban zarge ta ba.
Tayi min abinda iyayen a basu min ba ina sa mai kyau inci mai kyau sai dai na fahimci yan uwanta basa k'auna ta.

Na gane ne da irin kallo da kyarar da suke min.

Munyi shekaru a kallah uku kafin dole Aunty ta sallama ni nake tsayawa da samari. Sai lokacin na sake fahimtar yadda mutane suka bata rayuwar su. Yawanci basa zuwa da alak'ar gaskiya Sao dai kowa da manufar shi.

Sanda na lura aunty ta rage tara maza a gidan ta ma'ana sun rage zirga-zirga shine sanda wani mutumi ya nuna yana son zai aureta. Tayi murna sosai nima kuma naji dadi sai dai kash sai da komai yazo daf da daf komai ya ruguje..
Mutumin yasan komai game da ita sai don bazance zaman da take yi ne ita daya bai sani ba. Sai dai lamarin ya tsayawa jama'a da dama aransu musamman k'awayen ta yadda suke ganin zata daga ta barsu.
Ban taba ganin matar nan cikin tashin hankali ba kamar lokacin nan tasha kuka wiwi a gabana. Ta dinga fadamin maganganu kamar ba cikin hayyaci ba kamar ta manta dawa take maganganun.

"Jamila nasan nayi rayuwar da bata dace ba amma na dade da dainawa na tuba yanzu ba da bace halak d'ina nake nema amma meyasa mutane zasuyi min haka."?
Maganganu ta dinga furtawa wasu ma sirrikan ta ne. Nima babu abinda nake sai kuka da bata hakuri.

Anduki lokaci mai dan tsaho kafin aunty ta dawo daidai.

Takan barni nayi mu'amala ta da samari na sam bata hana ni fita da samari. Har mu fita.
Sai dai a kullum zancen ta daya "Kiyi taka tsantsan."

Har kamar ranar da muka hadu dake. Amma nida kaina nake baya baya da mutanen saboda yadda suke nuna min wuce makad'i da rawa.

Aunty da kanta ta sama min hanyar samun kudi a cewarta dogara da abin wani ke jawowa komai ke faruwa.

Na koyi kwalliyar zamani wato makeover da ita nake yiwa kaina abubuwa da dama. Lokacin na k'ara tunowa da gidanmu. Dole na k'ara nemar gida domin bani da wanda inda ya fishi. Ina kaiwa mahaifiya ta alkhairan da wataran har shi mahaifina ake ciki domin komai ya k'are mishi. Kowa a gidan ta kanshi yake.

Da wannan abin nake samun damar zuwa gidanmu kai tsaye.

Sanda nazo wajenki lokacin aunty tayi min alkawarin zuwa dani Dubai domin siye siyan kaya. Nima tace na k'ara gogewa da sanin rayuwa.

Shine tafiyar da na sanar miki zanyi rakiya. sai dai kash mun shirya komai amma Allah bai nufa ba aunty ta rasu bisa wani hats ari da tayi a motar ta bayan ta fita babu jimawa na samu labari kamar a mafarki.

Jamila ta rushe da wani irin kuka mara misaltuwa. Sai da tayi mai isarta kafin tayi shuru wanda har Hafsah itama sai da ta share hawaye.

Hafsah a lokacin na rasa mutane biyu uwar dakina da kawata Samha wacce akace wata iriyar cuta ce ta kashe ta. Duk da ina ganin kamar nayiwa Samha butulci

Please Login or Register in order to submit comment