Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amma har yanzu ledar na hannun mama._ )
Mama ta zauna gefen gadon, Hafsah ta zauna kasa gefenta.
"To me ake nufi kaddarar da naji kin fad`a. aciki"?
Hafsah ta kulle baki da alama bata san yadda zata faro bada amsar ba.
"Uhum."? Inji mama.
"Baki sani ba."
"Ta jinjina kai."
"Hmm.. To marin da na yi miki rannan shi ma ai kaddara sunan shi koh."
Kunya sosai ta lullub'e Hafsah ta sinne kai a cinyoyin ta tana dariya.
"Hmm, bada wasa nake miki ba Hafsah, tunda har an koya miki a makaranta, kuma kin iya kina fad'a to kuwa dole kiyi amfani dashi.
"Kinaji nah.."? Hafsah ta daga kai.
Cikin muryar nutsuwa mama ta fara mata jawabi.
_"Kin sani a makaranta, an koya muku, dole ne mutum ya nemi ilimi kuma dole yayi amfani da ilimin sa Koh?._
Hafsah ta daga kai.
Ta tausasa muryar ta. "Ki fada min gaskiya kinji kada ki boye min ni maman kice. " _Kina son Yusuf_ "?
Hartar cikin Hafsah ta kad`a wani irin tsoro ya mamayeta. _Sunan Yusuf, kuma daga bakin mama."_?
_Kina son shi._"?
Mama ta k'ara maimaita mata tambayar. _"To ko kuma wannan wata dama ce ta samu, wajen dawo da yusuf bisa hanya, tunda har mama ta shigo cikin zancen."_ ?

Ganin maman bata buk'atar b'acin lokaci yasa Hafsah daga kai a hankali, sai kuma ga hawaye na d`iga.
Mama ta tallafo ta da hannunta ta jigina ta da gefen k'afarta, "To menene na kuka kuma."?
Ba tambayar ki kawai nayi ba.?
Aka danyi shuru, kafin mama ta cigaba, "Idan nace ki daina kulashi zaki daina."?
Wannan tambayar daidai take da zubar garwashi a zuciyar Hafsah, don yanayin data shiga da jin maganar bazai misaltuwa ba, wannan karon kuka ta fara harda shashsheqa, _wanne irin zance ne wannan mara dad`in ji a kunnuwa."?_ Ita ta zauna ma ta kissima ('Imagine') rayuwar da babu Yusuf asara take gani saboda tasan, abu ne da bazai tab'a yuwuwa ba a wajenta.
Mama tasan za,ayi haka, don haka ba tare da nuna damuwa ba, akan Kukan da Hafsah keyi ta
cigaba da, zubo maganganunta, wad`anda baza,ace basa shiga kunnen Hafsah ba, tanajine, amma tunanin ta na wata duniyar.
_"Hafsah ita rayuwar nan da kika gani, in bakayi-bani guri ake, nasan bazakiyi mamaki ba naji komai dake tsakanin ku da yaron nan, amma tambayar da zanyi miki shine, ya sunan matsayinki a wajenshi.?_
(zuciyar Hafsah ta raya mata _"wadda zai aura mana"_)
Itama k'awar taki mene nata matsayin."? (gaban Hafsah ya fad`i, _wannan tambayar kam babu amsa, don daidai take da k'ure._ )
"Bazan zarge ki ba don ina miki kyakykyawan zato, amma tsakanin ki da Allah kin tab'a jin labarin soyayya irin taku."?
Shin kin tabajin anyi haka..?
_Bari na fada miki gaskiya, _Duk ranar da kika sake kuka cigaba da alak'a ke da shi, to ki tabbatar kema ranar kin shirya zama irin Basma ne, ko kuma kin zama irin ta.!"_
Hafsah tayi saurin d`ago kanta kamar wacce aka tsikara _ita kuma..??_ Mama ce take mata wannan magana, bata fatan ta zama irin Basma, azuciyar ta ma tana cewa _"Inaa.. sai dai idan ranar ba ni Hafsan bace._
"Hmm, a yanzu dole kiyi mamaki har ki kalleni, amma zan gaya miki wani abu, _Ba,a zama inuwa d'aya idan hali bai zo d'aya ba.!!_
_"Saboda haka, kodai ki rabu da shi, ko kuma ki zama irinshi."_
Kuma kada ki d'auka wak'ar da yake miki na zai aure ki gaske yake.. Duk k'arya ne!!.
"Ni Hafsah banda ma rufewar idanu, ki duba kiga tun sanda kika fara kulashi wacce riba kika ci a rayuwar ki, banda koma baya da kakai ta samu."?
Iyayenki na d'aukar ki mai hankali, amma yanzu kin nuna musu ba haka bane.. Da an sanki da tsoro, da sanin yakamata amma yanzu komai randomly kikeyi, kawai gaban kanki kike, har kina iya fita bada sanin kowa ba.!! Sannan kin san a baki abu ki b'oye k'iki nunawa, idan da gaske sonki yake babu abinda zai hana abbanki ya kirashi yazo, ke inya yi niyya ma, abbanki zai bawa abinda zai baki yace a baki.."
"Da yana son cigaba da kulaki ku cigaba da mu,amala ai zai nemeki duk inda kike.. Amma duk baiyi haka ba, sai ke kike
k'untatawa ziciyarki."?
_Ita dai Hafsah tayi shuru ma da Kukan tana sauraron gaskiyar dake yi mata d'aci, azuciyarta tana ta kokawar dole sai ta kare Yusuf daga abinda ake jingina masa."_
"Ke yanzu ba abin kunya bane, bayan sun kunyata ki agaban mutane an nuna baki da wani matsayi, sannan ki dawo kulashi."?
Wato kin nuna baki da class kenan, kuma babu wanda kike dashi sai shi koh."?
Abin da sukayi kin taba jin wani yaro mai tarbiyya yayi.."?
"Nidai bazan matsa miki ba, amma ina fad'a miki ki fitar da yaron nan daga zuciyar ki, ki d`auki kaddara, ayadda kika yi sati biyun nan ba tare daya nemeki ba, to ki saba a hakan ki cigaba da rayuwarki harki manta dashi. Zaki sami wanda ya fishi alkhairi in sha Allah."
Zuciyar Hafsah ta cika fal da kunci, so ya rufe mata ido, da da sa,arta take mata magana babu abinda zai hanata cewa, _"Ai Yusuf bani da wanda zaifi shi a wajena.!!_
Amma sai ta b'ige da cije leb'e kawai, mama fa tana fad'ar abinda bashi da ranar yuwuwa ne.
Ita ko Yusuf ya nemeta ko kada ya nemeta, ita zata nemoshi kuma tana da yak'inin bazai taba juya mata baya ba.!
Kamar mama ta karanta abinda ke cikin zuciyar Hafsah tace, "Nid'ai ina fad`a miki ne, duk da nasan maganata ba zata taba shiga kunnenki yanzun nan ba, amma kiyi tunani, sannan kuma daga nan zuwa duk ranar da kika sa aranki zaki rabu dashi, to kizo ni kuma zan fad`a miki hanyoyi da matakan da zaki bi in sha Allah, ko wanne irin so kike masa sai kin manta dashi."
Da a halin farin ciki, Hafsah take to da babu abinda zai hanata yin dariya, ji wasu kalmamomi wai _"wai na manta da Yusuf.!!_
Ashe kuwa ranar, zuciyata bata jiki nah.!! Abinda Hafsah ta sawa ranta kenan..
"Zaki iya tafiya, kuma daga yau zaki iya komawa dakin fateema da kwana har zuwa sanda kika ga ya dace ki tuntubeni idan zancen da na fad'a miki ya samu karb'uwa.
Da Wannan mama ta katse mata tunanin ta, wanda akwai hikima a cewar mama, _"Hafsah ta koma dakin fateema da kwana."_

Hikimar kuwa Itace, Hafsah da Fateema shekarunsu kusan d'aya ba kamar ita maman ba, sau dayawa yara sunfi yarda da shawarar sa,anninsu fiye da ta iyayensu ko kuma wanda ya girme su. Tasan Hafsah zata iya nemar shawarar Fateema akan zancenta.
"Nagode.!!
Haka Hafsah ta iya cewa kawai, shima don gudun kada aga rashin kunyarta ne, mama ta d'auka cewa zancenta bai sami shigaba."
Ki dinga addu,a, dai ki nemi zab'in Allah, shine kawai.


Sai yanzu taji sanyi, kuma taji mama ta fad'i maganar da inda addua ce zata iya cewa "amiin."
"Ki turo min fateema.!!
Mama ta rufe da wannan kalmar.
Ita dai Hafsah gaba tayi kawai, don bakinta yayi mata nauyi, mamaki ma take mama da girmanta amma take son sanya kanta cikin al,amran soyayyar yanzu, Hafsah gani take ma anya mama tasan so kuwa da take ambata mata kalmar _rabuwa,_ _rabuwa._!!?
😅
Fateema na zuwa mama ta fara fad'ar sakonta babu b'ata lokaci, "Idan yarinya can ta nemi ki ara mata waya, ki bata, matuk'ar kin tabbatar yaron nan zata kira."
Fateema ta waro idanuwa da mamaki, ya mama da ake zaton zata gyara, kuma da b'atawa."?
"Eh..!! 'Inji mama ganin kallon da fateema ke zubo mata.
_"Ai ko ni bazan goyi bayan Hafsah ta cigaba da mu,amala da wannan mutumin ba.!!_
Fateema ta fada a zuciyarta.
Mama ta katse tunaninta.
"Tashi kije idan hakan ta faru, sai ki zo ki labarta min, dalili ne ma zaisa na hanata wayarta, da tatan zan bata."
Babu fuskar yin tambaya ko nuna rashin gamsuwa, don haka fateema tayi azamar mik'ewa tana fad`in, "To mama Shikenan.!!
Mama ta bi bayanta da kallo, hikimar ta shine "Don Hafsah ta sami damar yin shawara da Fateema, tunda Itace sa,arta zatafi yadda da zancenta fiye dana maman.
Gefe kuma, tana tunanin idan suka jone da yaron, menene mataki na
gaba kuma..."?


Tabbas yarinyar na buk'atar addu,a, tuna cewa babu addu,ar da tafi ta uwa amsuwa yasa, taja waya don kiran Amina, cikin nutsuwa take kwantar mata da hankali, tana nuna mata komai ya kusa zuwa k'arshen addu,ar ta kawai ake da buk'ata."
_"Ki riqa yin addu,a nan da nan zaki ga komai yazo da sauk'i wannan ba wani babban abu bane can.._
Hakan maman ta fad'a mata...




📝
*HAJEEYAH*
*KHAREEMERH*


♥️♥️♥️♥️
*ZAZZAFAN SO*
(masoyin k'warai )
*Cigaban littafin Zazzafan so*
*(Guba ne)*
💔💔


*By:*
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah khareemerh)*
*Dedicated to Unique in your love heart group members.*




📄 *44*




*Tun* bayan da Fateema ta koma d'akin babu wanda yace wa wani komai tsakanin ta da Hafsah, kowa na sak'awa yana kwancewa Hafsah zantukan mama da ta d`auke su marasa yuwuwa ke mata yawo, Fateema ma, su d'inne dai. _"Mene zai sa ace Hafsah ta cigaba da kulashi."?_
Shirun ya d`auke su lokaci mai tsaho, kafin Hafsah ta nemi guri ta kwanta don gani takeyi gwara ta k'irk'iro bacci, da zaman juya kalaman mama arai, masu tada hankali.
Da safe, ta tashi sakayau, babu wani _tension._ don ta sama wa kanta mafita, kawai gwara tayi watsi da abubuwan da mama ta fad'a mata ta manta kawai da ta fad'a mata su ta maida hankali akan dawo da Yusuf cikin rayuwarta, la-allah ko mama ta gane, abinda take fad'an zai faru ba faruwar zaiyi ba.
"Hafsah ta sawa ranta yiwa yusuf uzuri cikin abinda ya faru, da tasirin tuno maganganun shi.. _"Dama na fada miki duk abinda ya faru ke kika jawo.!!_
_Banyi miki cin amanar rabuwa da ke ba.!!_
To in dai kuwa hakane, ashe ita ce ta nisanta kanta dashi kenan,? Tana son dawo dashi cikin rayuwarta ba don ta biye mishi akan abinda yake so ba, sai dai da nufin, nusar dashi ya gane abinda yake nufin suyi, ba shine abinyi yanzu ba a wajenta. Abin mamaki kuma sai take yiwa kanta fatan samin nasara mai kama da yak'ini. Ta manta da cewa wanda yayi nisa baya jin kira, kuma mutum baya sauyawa lokacin d'aya, sannan Yusuf kallon da yake yiwa rayuwa da banbanci da irin nata kallon.
_Akwai aiki a gabana."_
Ta fada a zuciyarta tuno cewa bata san ma ta yaya zata fara jawo yusuf d'inba su dawo ma kamar da. Kafin azo ga batun chanja mishi ra,ayi.
Duk wata hanya an toshe, bata da damar kulashi, an hanata fita, gashi bata da waya, sannan tana kunyar ta k'ara aron wayar Fateema. Amma kuma gefen zuciyarta na bata kwarin gwiwa.
_"Hafsah kunyar Fateema ne zata sa kiyi sakacin da zaki rasa farin ciki."? Baki da isashshen lokaci fah"_
Ta ke taji cewa a zuciyarta, zata iya tambayar Fateema waya, tunda tana da yak'inin ba zata iya hanata ba, toh amma kuma idan ta sanarwa mama fah."?
_"Ki rok'eta akan ta rufa miki asiri.!_
wata zuciyar ta raya mata.
Wannan tunanin shine ya dinga yawo a zuciyarta har tsahon kwana biyu.
Abinda Hafsah bata sani ba shine, Basma har text messages, ta turo a layin Fateema, da taji shuru Hafsah bata zo inda tace su had'u ba.
_"Hmm, dama nasan bazaki iya ba, hmm ke kin isa dama ki ja da Basma Yunus."?_
Sai da _text_ d`in yayi wajen kwana uku, sannan Fateema taga ya dace tayi mata _reply_ ba tare da ta sanarwa da Hafsa zancen _sms_ d`in ba don gani take yin hakan ma kamar iza wuta ne, amma kuma yarinyar bata chanchanci ayi mata shuru ba, don kada ta zaci ana tsoron ta ne.
Saboda haka da zuciya cike da kishi irin na 'yan uwantaka, Fateema ta rubuta _reply_ a zuwan Hafsah ce.
_"Ai idan kika ga mutum na tsintar abinda ke k`asa, to ya rasa mai zai ci ne, daga ke har shi kunyi min kad'an in zauna ina bibiyar k'azamar rayuwarku, ke dai da bakya ramin kanki sai kije kiji ta cusa kai da zubar da mutunci, ni nafi k'arfi d'aga murya akan abinda kika kula, don bansaki a layin mutane ba bare na zauna damuwa da abinda kika damu dashi, ai ke duk abinda zai burge ki to expired neh..masu hankali bazasu shinshina ba.. To kije ku qaraci k'azamar rayuwarku ni na wuce ajin kulaku dukanku._
Kalaman sunyi matuk'ar zafi a zuciyar Basma, ita da taso suyi ta jan zaren, tayi ta k'onawa Hafsah rai, amma ta sakar mata, anya kuwa ba karfin hali H. Hamid tayi ba.. Ya zaayi, ma tace Yusuf ya zama _useless_ a wajenta, bayan basma tafi kowa sanin irin son da Hafsah keyi wa yusuf d`in.
_"Kai k'arya kike kawai kinji ba zaki iya yakin bane saboda anfi karfinki. Dole ki rungumi sorry_
Abinda Basma ta aiko dashi kenan, zuciyar ta cike da zafin kalaman da aka aiko mata, _bansaki a layin mutane ba."_
Wato ana nufin ita dabba ce kenan.
" _Haha..ni fa na fad`amiki yusuf bola ce wacce nayar kika d`auka banda hakanw bazaki tab`a iya winning d`in heart dinshi ba yanzu ma da kike kurin, koda ace tabbas kwatuwa yayi daga wajena, ki tuna da yadda kika kwace shi mana, siya kikayi da mutuncin ki, kika maida kanki qaramar karuwa ko kin manta..."? Kuma n fad'a miki ki jira randa abinda kika tsinta zai tsere miki.!!_
Fateema ce tayi reply da haka. Kan Basma ya kulle, anya kuwa H. Hamid ce zata iya turo wad`annan kalaman, yarinyar da tasan ta da tsoro, wata zuciyar tace, zata iya fin haka ma, tunda kinfi kowa sanin me kikayi mata, kuma ai dama shiru-shuru ce, irinsu kuwa babu mai sanin zurfin cikinsu.
Kalmomin sun mata zafi ta rasa martanin mayarwa, sai kawai tahau turo da zage-zage Fateema ta ga asarar ta barta don haka ta tura mata reply d`in qarshe da nufin tayi block d`inta.
_Kanki ake ji..kuma nasan rashin abinyi ne yasa kike ta zagi haka, kedai kiji da asarar da kikayi, zagi kuma kanki kika zaga, kar ki k'ara turo min da text don bani da wata alaqa dake if not kuma...Hmm._
Tana kokarin yin block kira na shigowa ta katse kiran tare da yin block na number.
Fateema ta lura da yawan kallonta da Hafsah keyi da alama akwai magana a bakinta.
"Meya faru ne Hafsah."
Tayi ajiyar zuciya sannan ta fara 'yan soshe-soshe.. "Um Fateema da.. dama don Allah waya zaki ara min in..kira."
Tayi ta rarraba zancen kamar me tsoron tambaya.
"Wa zaki kira."
Fateema ta tambayeta kai tsaye.
"Don Allah ki ara min so nake na tabbatar da wani abu."
Me zaki tabbatar."?
Nidai ki fad'amin wanda zaki kira."
Cikin matsuwa take, don haka ta muskuta.. "Don Allah kada ki fada wa mama na ari waya."
"A,a ni nace ki fadamin wanda zaki kira mana."?
"Nidai kiyi alk'awari bazaki fada mata ba.
"Hmm, to meye idan ta sani, nidai ki fada kawai."
Hafsah ta k'ara cewa "Don Allah, kinji."
"To naji, ki fad`amin wanene."?
:Da gaske ba zaki fad'awa mama ba."
Hafsah ta tambaya tana murmushi so take ta k'ara tabbatar wa don gudun matsala.
"Kaii wai so kike na rantse neh, Allah bazan fada mata ba, Shikenan?."
Hafsah ta rungumeta "Thank you sister.!!
A kunyace tayi k'asa da murya tace, "Shi zan kira."
"Hmm", inji Fateema.
Don ta yarda Hafsah ta shiga koro jawabin kariya.
"Kinga dai nice ban neme shi ba shiyasa, gashi bashi da hanyar nema na."
"Hmm, gaskiya.!!"
Cewar Fateema kuma da yake itama tana son a kira d`in don taga k'arshen _game_ d`in sai ta bada wayar.
"Ungo, amma with one condition."
Hafsah ta amsa cikin zumudi tana zaro ido. Mene."?
"Zaki sa wayar a hands-free naji."
Ita dai Hafsah _buk'atar maje hajji sallah_ don haka tayi saurin jinjina kai alamar yarda.

Take ta danna kiran waya, tayi ringim mai tsaho, aka d'aga. "Hello, akace daga can.
Taji muryar cikin ko ina na jikinta yaushe rabonta da jin muryar shi, har kwalla ta tarar mata a idonta, Basma tayi mata laifin da baya yafuwa.!
"Hello."
Itama tace da rawar murya.
"Wanene.""?
Aka tambaya, ita kuma ta rasa abin cewa sam, tayi d'if kwakwalwarta ta kunne, baya kawai take tunowa.
"Nace wanene."?
Aka k'ara tambaya daga can.
Cikin raunin murya tace, "Nice Hafsah ce fah."
"Hmm.." akace daga can, sannan ba,a b'ata lokaci ba aka katse kiran.
Mamaki da tsoro suka saka Hafsah daskarewa ta kasa motsi.
Yau..? Ita.."? Kuma yusuf..? Haka ta faru."?
Fatanta kawai komai ma ya juye ya zama mafarki.
Fateema taji tausayinta matuk'a kuma fuskar ta ta nuna hakan, musamman lokacin da Hafsah take mishi bayanin _"Nice fah Hafsah ce.!_
Akan idonta taga Hafsah ta k'ara danna kiran, amma ba,a d'aga ba.
Fateema tasan ko ta rarrashi Hafsah rarrashinta bazaiyi tasiri ba, zata b'ata bakinta ne kawai, kuma gwara ma ta kyaleta ta zubar da hawayen ko dan ta rage rad'adin zuciya.
Bata son sauraron kukan, don haka ta mik'e tabar d`akin sai kuma taga kawai gwara taje ta fad'awa maman.
Maman a parlour take zaune da wani littafi a hannunta, Fateema tayi sallama, ta d'an rakab'e a gefe, tana kallon maman. Mama ta dago ta kalleta don taga alamun bata zauna ba. "Menene kike rab'e -rab'e"? Tana Sosa kai tace,
"Um, da dama Hafsah ce tayi kiran a waya.
"Matso nan ki fad`amin me ya faru."?
Ta ajye littafin a gefe ta bada dukkan hankalinta akan Fateema.
_"Kinga data kira, shine yace mata wa ye.. Tana cewa ita ce, yace hmm.. Sai ya kashe."_
Mama ta jinjina kai.. "Okay okay, shikenan, ba suyi wata magana ba"?
"Eh." inji Fateema.
"Ok jeki nagode."
Har ta dan fara tafiya sai kuma ta juyo cikin k'asa da murya tace, "Um mama don Allah kada kice na fad`amiki."
"Hmm." Mama taji d'an murmushi, tayi mata alama da hannu irin, _jeki kawai."_
Tun daga ranar damuwar Hafsah ta k'ara nunkunwa, har Fateema ta saba da ganinta tana kuka haka siddan. Abin ya fara damunta har take k'ara fad`awa Mama, "Mama Allah kusan kullum sai tayi kuka fa take bacci."
Jinjina kai kawai maman tayi tace mata, "Toh naji."
Aranar ne kuma mama tayi niyyar d'aukar wani mataki akai.
Da dare ta kira Hafsah d'akinta, "Baki yanke shawarar ba koh."?
Hafsah taji jim, tana tunani, _wannan fa wata dama ce, gwara ta bawa mama dama ta fad'i abinda ke ranta ko zai zama mafitar ta, don ita kanta ta sani ta damu da yawa, kuma ta gaji da zama cikin k'uncin zuciya.
"Na takura miki koh.."? To tashi ki tafi."
Tayi daurin girgiza kai. A hankali tace, _"Aa wallahi mama, na kirashi ma bai yakashe."_
Sam Hafsah ta manta ma da mama take magana, abinda ke ranta kawai take son ta fitar.
"Hmm, kingani koh."? "Abinda nake fada miki kenan Hafsah kada ki damu kanki akan mutumin da bai damu dake ba, amma bakya ji."
Abinda mama ta hau fad`a kenan, wad`anda Hafsah taji mamakinsu, azaton ta fada mama zata rufeta dashi, akan kub'utar bakin da tayi.
Mama ta kamo ta, "Tashi ki dawo kusa dani kinji."?
Hafsah ta mik'e mama ta rik'e ta harda jingina ta da jikinta, cikin murya mai nuna alhini, take magana.

_"Hafsah ba laifi bane don kinso yaron nan, tunda so baya zama laifin mutum, abu ne da yake faruwa haka kawai. Sau dayawa mutane suna tsintar kansu akan soyayyar wanda bai dace su so ba, amma babu yadda zasuyi._
"Kinga abubuwan da na fad'a miki sun tabbata koh."?
Hafsah ta jinjina kai. Don tabbas hakan ne.
"Zaki hakura dashi."?
Hafsah taji saurin d'aga kai, don ita kanta ta gaji, gwara maman ta fada mata ta gwada d`in idan zai curu.
Mama tayi murmushi, a zuciyarta tana hamdala.
_"Kiyi hak'uri Hafsah, ki d'auka hakan kaddara neh._
Kinji.
Ta d'aga kai kawai.
"Abubuwan da zaki guda biyu ne, na farko aiki ne da gangar jiki na biyun kuma aiki ne da zuciyarki.



Nafarkon shine:
Addu,a.
_"Addu,a ita ce ta farko kuma ita ce maganin komai. Ki dinga tashi da dare kina fad'awa Allah damuwarki, ki rokeshi ya yaye miki dukkan damuwa._




_Sannan na biyu shine, ki ragewa zuciyar ki yawan tunani, kinajin tunanin shi yazo miki kiyi kokari ki kauda shi da wani abin."_



_"Sannan ki daina bari zuciyarki na k'awata miki shi, ki mishi kallo da idon da kowa yake kallonshi, kada ki sawa ranki yafi kowa, zaki ji kin rage wani kaso daga sonshi."_


_"Kada ki d'auka idan kin rabu dashi bazaki taba samun wanda ya fishi ba, ki tuna mutane, daban daban ne, kuma kowa nada tashi baiwar, zaki iya haduwa da wanda ba kiyi tsammani ba a lokacin kuma zaki gane, ashe wancan ba komai bane kawai son zuciyarki ke kawata miki shi."_


_"Kisa aranki zaki iya rabuwa dashi kuma, ba zaki iya sab'awa Allah saboda shi ba."_


_"Ki bawa, kanki da rayuwarki, maimahimmanci fiye da shi, yadda zaki yardarwa kanki akwai masu buqatar ki aduniya banda shi, akwai masu son farin cikinki, ko shi baya so, akwai wad`anda suka damu dake kuma sun fishi yawa, saboda haka ba zaki wulak'anta rayuwarki akan mutum guda d'aya ba."_


_"Ki kalli alkhairan da ke tattare da sauran mutane, masu nuna suna sonki, kada Ki rufe ido akan mutum d'aya."_


_"Ki d'auka cewa, da zaki bawa wani dama, zai miki son da shi baya miki rabinsa, Hafsah meye amfanin damuwa da wanda ya nuna baya buk'atar ka."?_

_"Ki d'auki lokacinki da muhimmanci kada_
_ki k'arar dashi akan abinda bazai miki amfani ba, ko neman abinda bazai samu ba, kada Ki wayi gari lokacin kuruciyar ki ya shud'e amma baki amfani kanki, da sauran mutane da komai ba."_..


Mama tayi murmushi, _"Idan kika saka haka aranki, ina mai tabbatar miki, by time, zaki nemeshi a ziciyarki ki rasa, a hankali Soyayyar shi zata dusashe.!"_
Bance miki lokaci d'aya ba, don komai yana buk'atar lokaci, amma ki tsananta addu,a... Sannan kisa a ranki cewa zaki iya kinji.
Hafsah ta daga kai zantukan sun shige ta, sosai, indai har zasuyi mata amfani yadda mama ke nuna mata tabbas zata gwad'a.
A lokacin taji zuciyar ta ta cunkushe, da tunani daban-daban ta rasa na d'auka kawai sai ta mik'e a wajen ta kwanta sai kuma bacci.



Bayan ta farka ma hakane, taji zuciyarta tayi mata nauyi, maganganun mama sun tsaya mata a rai, a hankali ta fara hango gaskiya a cikin su.
Yusuf? Shine ya kashe mata waya.."? Jin cewa ita ta kira shi..? To wanne irin mantawa yayi da ita haka.. Lallai tabbas ya nuna mata baya buk'atar ta. Nan take kishin kai ya shiga zuciyar ta, taji aranta tabbas ita ma abu ce mai muhimmanci ba _Banza ba._ don haka ta sawa ranta cewa ba zata k'ara neman sa ba, matuk'ar bashi ne ya neme ta ba. Basma kuwa zata barta da Allah, don tasan komai lokacine, kuma alhakin ta bazai barta ba.
Kwanaki suka shud'e mama ta daina yi wa Hafsah magana mai kama data Yusuf ko makamancin haka. Gashi ita kuma Hafsah a kullum maganganun mama suna mata yawo a zuciyarta, ta rik'i wasu daga ciki, misali addu,a, da kuma daukar kai da muhimmanci, sai kuma muhimmanta lokaci, ahankali kuma da taimakon Allah, da amfani shawarwarin hazik'ar mace, wato _Haj. Nafeesah_ a hankali taji komai yana raguwa daga cikin zuciyar ta, har zuwa yau da zata iya claiming cewa babu d`igon son Yusuf ko ragowar damuwar shi aranta, ya zama tarihi, abin ya na bata dariya idan ta tuno lukutan, babu kamar ma irin musayar kalaman da Basma sukayi a text ita da Fateema a zuwan Hafsah ce, sai bayan ta fara dawowa hayyaci, Fateemah ke bata labari.
Zaman wata 3, tayi gidan mama wanda har Abba ya gaji dashi, tana zuwa gida, amma babu kwana, ita kanta tayi kewar komai, tana ganin tarairaya a wajen mamanta.
Sanda ta cika wata biyu, a iya cewa komai ya saitu, nutsuwar ta ta dawo, to lokacin kuma mama ta nemi da a barta tayi azumi anan, tunda yan kwanaki kawai suka rage.
Daga baya kuma, mama ta dawo da ita gida, godiya kuwa sara wacce, Alhaji Habib Hamid, zaiyi wa mama, yayi sai dai fatan alkhairi, don kud'i ko wani abin duniya, sunyi kad`an.
Duk wani labarin zaman gidan da Hafsah tayi da yar gwagwarmayarta mama ta bawa mamanta labari. Sannan ta mik'a ledar kyautar graduation d`in Hafsah wacce Yusuf ya bayar ga maman tare da cewa, "Ki bata sauran ta amfana kawai ita kuma wayar ki mikata ga Abbanta duk ranar da yayi niyya saiya bata a sanda yaga ya dace ta mallaki waya. _"Ikon Allah wai yaran yanzu sun fi bawa soyayya muhimmanci fiye da komai a rayuwa.!!_
Allah ya shirya mana su." Inji aunty Nafeesa, mama tace "Amin.
Ta karbi ledar duka, da niyyar bada kayan duka
abban da hannunsa ya bawa Hafsah, bayan sun gama hirar _yaushe gamo_ a d'akin sa, ya cire wayar, ya bata sauran. Bata ga amfanin su wajenta ba, tana baro d'akin ta bawa zainab agogon, ta bawa Ameera kuma turaren, tayi cilli da greeting card d`in mufida ta d`auke. Akan idon mama, tana murmushi zuciyarta tana

Please Login or Register in order to submit comment