Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin d'aure fuska.

Ya saki tattausan murmushi, yana girgiza mata kai, don yasan dalilin ta na fad'ar haka.

Nima haka Hafsah, bana son karya kuma in sha Allah ba zaki same ni maiyi miki itaba..

Ya tsura mishi ido, Shikuma ya d'aga mata gira, cikin k'asa da sauti yace, _"sai dai ina da zolaya.!!_

Ba tayi dogon tunani kan abinda ya fad'a mata ba, banda haka da ta d'ora wasu zantukan nashi a ma,aunin zolayar dayake yana dashi.
_Misali auren daya ce mata yana da.._


Hmm, tace mishi kawai. Sai ya kalleta itama ta zuba mishi ido sai ya b'ige da yi mata wasu dogayen zantukanshi masu sanyaya mata jiki.

Kiyi hak'uri idan a zuwan nan da nayi nayi wani abu daya bata miki rai, babu zuciyar da zan so in sata farin ciki kamar taki, sai dai idan ina tare da ke bana iya control d`in kaina, ina iya yin komai ne domin na burge ki, sai dai a samu akasin ke a wajenki ba abin burgewa bane, tunda ban kware wajen karantarki ba tukuna.


Nagode, da irin hidimarki gareni, amma ina son inji amsata ko da a waya ne, don Allah idan banyi miki kalar wanda zaki aura ba ki sanar dani.!!

Ta bi shi da kallo, shima ya k'ura mata ido.

Bari na barki kada na cika ki da surutu, Nagode Allah ya huci zuciyarki..

Lokaci guda ya mik'e itama sai ta mik'e d'in. Ji tayi zuciyarta na tafasa, sam bata tsammaci tafiyar shi yanzu ba,
Ji tayi kamar, hasken wajen ne zai d`auke idan ya tafi..


Bata ankara ba taji yana ce mata kiyi hakuri ki karb'i wannan, ta dawo da kallonta gunshi, kud'i ne sababbin 'yan dariya biyu, _wrapper_

Ta tsaya sororo tana kallon shi, kafin tayi yunkurin yin magana ya rigata.

Bance don kina da buk'atar su ba ko wani abin, sai dai inason na dinga kyautata miki nima da iya abinda nake da iko, kamar yadda kike min.

Ya ajjye su akan table d`in sannan ya daga mata hannu yana murmushi mai tsaya mata a rai.
"Bye bye.!!

Ya juya ya nemi hanyar shi ta fita ya barta daskare a wajen ta zubawa kud'in idanu....




πŸ“
*HAJEEEYAH KHAREEMERH*
[17/03, 2:54 p.m.] UMAIMA BASHEER: β™₯️β™₯️β™₯️β™₯️
*ZAZZAFAN SO*
(Masoyin k'warai)
*Cigaban littafin Zazzafan so (Guba ne)*
πŸ’”πŸ’”

*By*
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah Khareemerh)*
*Dedicated to unique in your love heart*



*IN SHA ALLAH ZAN TAKAITA BOOK D`IN CIKIN 3PAGES. DALILI SHINE MUN KOMA MAKARANTA KUMA KARATU YA KANKAMA..*
_SAI AYI HAKURI DA YADDA LABARIN ZAI ZO ATAKAICE._πŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌ




πŸ“„ *59*



Ukhashatu na fita motar Abban su Hafsah na sako kai, don haka ya dakata aka bud'e mishi ya shigo, lokacin ita kuma Hafsah lokacin ta gaji da tsaiwar ta wuce ciki cikin sanyin jiki..



Abba yaga ukhashatu kuma ya yayi mamakin ganinshi tunda yasan ba abokin Basheer bane.

Sai da yayi parking ya fito, ukhashatu dake rakabe a gefe ya k'arasa wajen shi.

Har k'asa ya tsuguna ya gaida shi, Abba ya amsa cikin sakin fuska yana mishi alamu da hannu 'da ya mik'e.'

Ukhashatu cikin ladabi ya mik'e zai juya. Abba ya buda baki ya mishi magana cikin sakin fuska. "A to ai a shigo mu k'ara gaisawa koh."?

Ukhashatu cikin ladabi ya dawo yana murmushi, Abba yayi gaba, shi kuma yabi bayan shi.

A sit room suka yada zango, bayan dukkansu sun zauna a gurin da shi abba yaiwa kanshi mazauni, da kuma gurin da yayi wa ukhashatu nuni daya zauna tun f
Kafin shi Abban ya zauna, amma sai da ukhashatu ya bari Abba ya zauna sannan ya zauna a k'asan kujerar da aka mishi nuni da ita.


Abba yaji dad`in wannan ladabin. Ya fuskace shi kuma da murmushi a fuskar shi.

"Ya mutanen gidan suna lafiya."
Ukhashatu yayi murmushi, yana dan sunkwi da kai.
Lafiya lau Abba.
Abba ya d'anyi gyaran murya.

"Sai dai ban shaida fuskar ba daga ina ake."

Ukhashatu ya k'ara k'asa da kanshi.
Nassarawa."
"To Masha Allahu." yana murmushi yace, "Za,a fad'a mana sunan mai Gidan ko nafi ganewa."

Ukhashatu yayi murmushi shima, Eh, "Alhaji Abubakar Khady."

Abba ya fad'ad'a fara,arshi.
To Masha Allah, Khady dai da na sani mai sharia na majestry court"?

Ukhashatu ya jinjina kai cikin ladabi.
Abba cikin fara,a Alhamdulillah. "Ai Khady na mu ne, Allah ya k'ara mishi lafiya."
"Amin Abba."
Cewar ukhasha.
Sannan Abba ya d`an shaki numfashi kafin yace, "To wajen Basheer aka zo ne."?
( _baya son ya mishi tambayar gurin wa yazo cikin yayanshi mata kai tsaye._)

Ukhashatu ya sosa k'eya yana gyara zama cikin jin nauyin abba yace, "Eh Abba mun gaisa dashi kuma nazo wajen mun gaisa da Hafsah ma."

Abba jira kawai yake yaji alak'ar Basheer da Hafsah.
Cikin son mishi wayo irin nasu na manya yace, "Wajen aikin ku d'aya kenan."?
Ukhashatu ya girgiza kai, fata yake kawai Abba ya fahimta basai ya fito b'aro-b'aro ba.


"Am um dama ina zuwa ne muna gaisawa."

Abba yayi murmushi, cikin matsanancin farinciki, "Alhamdulillah ya furta a fili."

Yana yiwa Allah godiya, da ya bawa Hafsah miji irin wanda yake mata fata. _(Dan gidan manyan mutane ba girma irin na naira ba, sai dai duka kuma Allah yayi an had'a kudi da sanin yakamata ga kyakykyawan asali)_

Ukhashatu yana iya karantar irin farin cikin daya bayyana kan fuskar Abba.

"Masha Allah, Allah yayi albarka."
Kai tsaye yace, Za,a iya yiwa manyan magana sai a zo agaisa koh."?

ukhashatu ya gane me Abba yake nufi, cikin farin ciki, shima ya ke zuba godiya.
"Nagode Abba Allah ya saka da alkhairi."
"Amin Amin."
Sai a bani number shi Abban naka koh."?
Abba ya ciro wayar shi ya mik'o.
Ukhashatu ya karb'a da hannu biyu ya rubuta number, sannan ya mik'awa Abba.

Abba yayi saving, sannan zana tashi number akan wayarshi, ya k'ara mik'awa ukhashatu.

"To gashi, koh sai a d`auki tawa saboda a sanar idan an shirya zuwan."

Ukhashatu ya karba yasaka, a wayarshi.
Sannan ya mik'awa Abba wayar.
Yana fad`in "Angode Abba."
Abba yayi murmushi sannan ya mik'a mishi hannu sukayi musabiha, yana fad`in agaida mutanen gidan, naga magriba ta k'arato.
Ukhashatu ya mik'a bayan sun saki hannun juna, "Na Barka lafiya Abba."



Ya fita cikin matsanancin farin ciki, ji yake kamar ango ne shi.
Godiya yake ga Allah daya sauk'ak'a mishi komai. Ya sani ba dabarar shi bace Allah ne ya saukaka mishi komai yadda zai sanya mahaufanshi cikin farin ciki.
*______________*
A wani masallaci ya tsaya a hanya yayi sallar magriba inda babu wani jira ya, k'ara tarar napep Kai tsaye ya wuce gidan abokin shi, da k'yar ya lallabashi kan ya taso ya raka shi gadon k'aya gidan Baffa..Babu irin mitar da Mubarak bai mishi ba a mota. _kai ka cika zumudi daga haka sai ayi haka, wa yaga farin shiga."? Banda na matsu kayi aure nima da babu abinda zai hana ni zamana a gada. Kawai ka taso mutane suna hutawarsu._

Shidai ukhashatu kus yayi yana jinshi don yana cikin farin ciki, baya son ya tanka mishi ya ce bazai raka shi ba.

Yanayinsu da Baffa ya gani ya tabbatar mishi da akwai magana, kuma shima ya sakar musu fuska kamar yadda ya gansu cikin farin ciki.
Bayan gaisuwarsu kamar ko yaushe, _ta musabiha._
Baffa cikin fara,a yake tambaya.
Ya akayi ne, ya Abban naku."?
"Yana lafiya lau Baffa."

"To Masha Allah." Suka k'ara yin shuru.
Baffa ya k'ara tambaya.
Komai kalau dai koh."?
"Lafiya lau Abba suka fad'a cikin ladabi, Mubarak ya gyara zama, ganin dare ya farayi ya fara magana.


"Baffa ayi mana afwa munzo da daddare."

Baffa ya gyada kai, yana murmushi, "Ai ku ba bak'i bane, babu komai, ai shi ya sha amsa kiran dare ma a gidan nan." Ya kalli Ukhashatu yana k'arashe zancen.

Ukhashatu shidai kanshi na k'asa.

Sannan baffa ya juya ga Mubarak yana, tambaya. "Me ya faru ne."?

Mubarak ya gyaran zama ya fara bayani.

"Dama Baffa, akwai gurin da Ukhasha yake zuwa amma bai jima ba, to yau d'innan sai mahaifin yarinyar yace a turo magabata."

Tunda ya fara magana Baffa najinshi yana gyada kai, sai da yakai k'arshe sannan suka ga wata fara,a da basu taba gani ba musamman ukhashatu a fuskar Baffa.
Masha Allah Alhamdulillah Allah ya tabbatar da alkhairi, ai wannan abu ne da muke nema."

Sannan ya juya ga ukhasha da kunya ta cika yace, "Har kwananka nawa da fara zuwa zaka ce, baku dad'e ba."

Kai a k'asa yace, wata d'aya zuwa biyu, amma zuwanta na biyu kenan gurinta."


"Baffa ya ca fe, ahaf ai tunda kun daidaita kuma har tana saurarar ka ai zance ya k'are."

Ya juya ga Mubarak, "Abban nashi ya sani."?

Mubarak ya girgiza kai.

"A,a Baffa ai yanzu ne akayi maganar."

"OK tom babu komai."
"Sun bada number ne da zaayi magana."?
Mubarak ya kalli Ukhashatu, shi kuma da sauri ya lalubo wayarshi a aljihu, ya danno number _Abban Hafsah_ ya mik'awa Mubarak.

Cikin ladabi Mubarak da hannu biyu ya mik'awa Baffa.

Baffa ya amsa yana murmushi yana cewa, "Ai kuwa gaka anyi dabara da aka bada number."


"Sai ayi magana yadda ya dace."

A wanne unguwa suke. Mubarak ya amsa, "Sallari."
"To ya sunan shi mahaifin yarinyar da yarinyar."?

"Alhaji Habeeb Hamid."!!
"Ita kuma Hafsah."
Duk Mubarak ne ya bada amsa.

"Masha Allah, "Allah ya tabbatar da alkhairi.
"Amin." Inji Mubarak.


"Zamuyi magana da Yayan." Baffa ya fad'a.
Ukhashatu ya d'an tab'a mubarak alamun ya tashi su tafi.

Mubarak ya mik'e shima ya mik'e, cikin ladabi suka mishi sallama.
"Baffa zamu tafi kada dare yayi." Inji su.
Tom Allah yayi albarka tunda har kun mik'e ku gaida gida, an gode kaji Mubarak."?


Suka fita, kowa fuskar shi da murmushi.

A waje mubarak yake ta tsokanar Ukhashatu, "Aikin banza ka wani zama silent a ciki don gulma koh."

Ya gyada kai Eh mana, ni wuce ka kaini gida malam.

Cab bazai yuwu ba wallahi, sai dai na ajyeka a titi, kawai na baro iyali na salon ka hura min wuta kai kana kokarin gida naka gidan."?

Dukansu sukayi dariya, Ukhasha ya zagayo ta daya barin yana cewa "Eh naji saukeni a titin."

Suna zuwa titin kuwa yayi parking. Ukhashatu ya mishi godiya ya fice ya tari Napep yayi gida.

_______________
D'akin Hajiyarshi ya nufa daga shigowar shi gidan, fara,ar shi ta musamman a lokacin, yana nufo d'akin, Mahseem ta nushi da gudu ta d'ane shi, "Yaaya!!
Ya daga ta da k'yar.
Kin girma fa "Mahseem na daina daukar ki daga yau."
Ya sakko ta ya rik'e hannunta suka k'arasa cikin gidan.

Yayi sallama ya zauna.

Hajiya ta kalleshi.

"Ina kaje ne haka tun yamma."?

Ya sunkuyar da kai, "naje gidan baffa hajiya."
"Acan ka dad'e haka."? Hajiya ta k'ara tambaya.
"A,a naje gidan abokinah..."
Yana cikin fad'a Fadwa ta ca fe, tana dariya "Hajiya zance yaje fah."

Ya aika mata da wata hararar data sa ta saurin to she bakinta da hannu.

Ya jinjina kai sannan ya mik'e, hajiya ta bishi da kallo, to ya Hajiyar ka baro su lafiya."?

"Lafiya lau Hajiya."
Mahseem ta biyo shi ta rik'e hannunshi suka nufi d'akin shi.
"Yaya tasbahar da kace zaka siyo min."

Yayi murmushi, Eh na siyo miki "Mahseem har da chocolates ma."
"Yawwa brother nagode."

Ya bude d'akin suka shiga, mahseem na mishi tambayar da ta saka shi juyo wa.

"Yaya wai da gaske zance kaje."

Ya tsaya ya kalleta har tasha jinin jikinta kafin yayi murmushi.

Museem ki min addu,a kinji Allah ya zaba min abinda yafi alkhairi.

Tayi murmushi, "Tom Yaya inayi."

Ya bude drawer ya dakko mata ledar, ungo kije ki kwanta, kice maryam ko Fadwa su kawo min abinci kinji."
"Tom Yaya sai da safe." "Yawwa Mahseem.
Yace da ita.


Sai da yazo kwanciya bacci ya tuno yadda suka rabu da Mutuniyar tashi, nan ya dinga dariya kamar bazai daina ba, Yanajin kewarta a zuciyar shi daga k'arshe, ya lalubi number ta amma tak`i d'auka.
Yayi murmushi a fili yace, "Hmm yarinya na kusa mallakar ki na huta.!!

_____________________________

Khady yayi mamakin jin batun da, k'aninshi yazo mishi dashi, _wai ukhashatu da neman aure.!!_ Bayan cikin kwanakin nan ma ya mishi maganar amma ya nuna ba wani shiri da yake.

Badon bikin maryam sati biyu kawai sukayi saura ba, da babu abinda zai hana yace a had'e.

Ya nuna jin dad`in shi ga kanin nashi, sannan suka shawarta yadda abubuwan zasu kankama, sun tsara zasuyi bincike kafin suyi magana da mahaifin yarinyar.


Sukayi sallama kowa cikin farin ciki da mamakin Ukhashatu.


___________________________


Maman su Hafsah ta lura da kalar farincikin da Abban Hafsah ya shigo dashi d`auke a fuskar shi, itama sai ta tare shi da hakan.


Sai da ya nutsu yake mata jawabi yadda zata fahimta.
Amina, naga wani yaro yazo wajen Hafsanki, kuma na yaba dashi har na nemi daya turo iyayenshi."

Mama ta waro ido, "Abba da wuri haka."?
Ya gyd'a kai to me za,a jira tunda Allah ya kawo."?

Kuma yaron dan gidan sanannun mutane ne, amma duk da haka zanyi d'an takaitaccen bincike, kedai ki taya ta da Addu,a Allah ya mata zabin alkhairi.
"Amin."

Inji mama, taji dad`in hakan amma kuma tana tsoron gaggawar da akayi kan al,amarin."


"Kada Ki sanar mata har sai sunzo, sannan zan sanar mata da kaina."

Mama ta gyada kai alamar "Toh."


Sanda Basheer ya shigo ya shiga d'akin Abban don tsaigun ta mishi bak'on Hafsah.

Shima Abba a k'age yake yana son jin zancen daga bakin Bashir d`in tunda bakon ya tabbatar mishi sun san juna shida Basheer.

Akwai magana ne malam Bashari."?
Basheer ya sosa kai sannan yace,

Am Eh Abba dama naga wani yazo wajen aunty Hafsah ne yau kuma naga kamar tana sauraren shi itama."
Abba yayi murmushi.
"Nasan zancen, na gamu dashi kuma har nace ya turo iyayenshi ma."

Bashir ya d'ago da sauri yana mamaki, Abba yayi murmushi.

Ba yace min yasan ka ba."?

Bashir ya labartawa Abba had'uwar su da Ukhashatu sannan ya dora da cewa, amma sun dad'e da aunty sunfi wata d'aya zasuyi biyu ma, kuma yace min zuwan shi na biyu kenan."

"To masha Allah Allah yayi jagora."

Bashir yace Amiiin, shima yaji dad`in abinda mahaifin nashi ya yanke.


____________________

Hafsah cikin tunani, barkatai da takaicin Ukhashatu ta kwanta, shiyasa tana ganin kiranshi amma ta share, takaicin ta d'aya matar daya boye mata yana dashi.


Har kwalla ta zubar, meyasa sai da ta fara sonshi sannan zaiyi mata wannan tozarcin, gaskiya maza basu da amana.




Share shin da take ya fara azabtar dashi, don haka ya shirya kalaman ban hakuri masu sanyaya zuciya da taushi ya turo mata.


_Kiyi hak'uri Queen idan nayi laifi, ni mai matuk'ar son ganin farincikinki ne, joking with you inpresses me ina son wasa dake amma wallah bani da mata bare 'ya na nuna miki k'anwata ne da 'yar yayana, am sorry dear na zabtu bzn kuma ba, kiyi picking call kiji wani abu kinji gimbiya.!!_




Sanda text d`in ya iso wayarta, da daddare ne, amma tana dubawa bazan san sanda ta saki wani dan ihu ba, da saida Zainab ta ankarar da ita _dare ne,_ sannan ta nade tabarmar kunya da hararar Zainab.
Zainab itama ta harare ta a wasa ta juya tana kus kus.

Ta jira kiranshi amma bai shigo ba, ita kuma tanajin kunyar kiranshi da kanta.



β™₯β™₯β™₯β™₯
*ZAZZAFAN SO*
(Masoyin k'warai)
*Cigaban littafin Zazzafan so*
*(Guba ne)*
πŸ’”πŸ’”
*By:*
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah khareemerh)*

*Dedicated to Unique in your love heart group members.*




πŸ“„ *60*



#Not edited
*Kuyi hakuri da typing error.*


______________________________


*Farar* Safiya ce misalin k'arfe takwas na dare, gidan yayi shuru kasancewar _*Mazauna Gidan* (Haermebaererh novels_)
basa nan, Abba anyi mishi wata rasuwa ta Babban abokin sa, a daren jiya daya saka shi fitar sassafe don ya sami Jana'iza.

Ita kanta matar gidan ta fita, wani uzuri nata, yayin da sauran 'ya'yan gidan suka fita nasu harkokin. Sai su biyu da suka rage a gidan kamar idanu.


Ita kadaice a d'akin ta, jin shurun gidan ya k'aru ya tabbatar mata da cewa mutanen gidan basa nan.



Gani tayi wannan wata dama ce ta samu na gabatar da abinda take ganin maslaha ne gareta. Wanda kuma take ganin zai dakatar da abinda ake shirin yanke mata.

_Bata shirya amsar aure yanzu ba don haka bata jin zata yarda da katsalondon irin wannan._


Doguwar riga ce ajikin ta, ba tare da bata lokaci ba ta d'ora wani mayafi da taga yafi kusa da ita, kawai ta kwashi takalma a hannu cikin sand'a ta fara takowa tana waige waige kamar _barauniyar data shigo sata._

Cikin sa,a babu wanda taci karo da shi. Har zuwa kofar fita, shima a sa,a babu mai gadi a wajen, da Alama ya zagaya wani wajen.

Da gudu ta k'arasa ficewa sai lokacin taji ta sami sukunin watsar da takalman hannunta a k'asa sannan ta saka, jikin ta na rawa ta fara tafiya.

Cikin layin ta hango napep ta tsare amma ya girgiza kai alamun Aa, cikin k'osawa ta kara sauri tana mita, a zuci..
Ta d'anyi yar tafiya kafin ta hango wani, kamar ta kifa take tsayar dashi.. Aikuwa ya tsaya.

Ta kara sauri sannan ta afka ciki cike da jindadi, har da ajiyar zuciya.

Sannan ta sami sukunin sanar da shi inda zai kaita.
Tarauni zaka kaini.!!

Me Napep ya juyo ya kalleta, sanye yake cikin wata riga wacce ta dan dame shi, mara hannu, (sleeveless) blue color, sai farin wandon jeans iya gwiwa, (three-quater). Kanshi ya tara gashi. Yafi kama da matasa wadanda ake kira _'yan swagger._

Ta yatsina fuska ganin ya k'ura mata ido har da daga gira.


"Okey, yanmata."
Yace da ita, sannan ya juya ga tuk'insa.


Ta kuma yatsina ffuska, da takaicin kiranta da yanmata da yayi, sai kuma taji fargaba tuno cewa bata sami damar dakko kudi ba bare _purse._

Me Napep gudu dinga yi da ita, yanayi yana bin wakar daya kunna musu.

Da sauri suna isa, unguwar sannan tayi mishi nuni daya kaita cikin wani layi, babu musu ya kaita har k'ofar gida.

Sannan ta bude baki, cikin yauki' saboda taga ta dawo cikin nutsuwarta tace, "Am na manta kudi na a gida, so zan dan shiga ciki na amso maka kud'in."

Ya bita da kallo kafin ya jinjina kai babu magana.

Ta juya ta shiga gidan, shiko ya bita da kallo.



Kai tsaye dakin maman ta nufa, tana kala mata kira, Mama!! Mama!! Maman ta yi saurin fitowa suna had'u a palour, da sauri cikin faraa, ta rungumeta "Yawwa my daughter.!!

Cikin jin dadi itama ta k'ara rungume matar kafin tayi saurin sakinta tace, "Oh mum nabar Napep a waje so bani 500 na bashi."


Okey, inji matar, ta duba gefenta kan kujera, ta dauki Jakarta ta dakko ta bata. Da sauri ta fita, ta tarar da shi ta mik'a mishi, ya amsa yana lalubo chanji, yaga tana kokarin juyawa, "Wallahi kin burgeni fah."

Ta zaro ido lokaci guda tare da jan tsaki. Sannan ta juya da sauri, tana fad'in Nonsense.!!



Ta dawo cikin gida, abinda ya kawo ta ya fi karfin ta tsaya tuna abinda mai Napep din yayi mata.

Tana zama maman ta tare ta da tambaya.

Ya akayi kika fito."?
Sun fita ne duka, anyiwa Abba rasuwa.
Okey good.
Sannan ta saita murya itama ta yar ta bata hankali.

"Shawara daya na yanke wacce nake ganin itace matakin k'arshe.!!
Indai mukayi haka to dole a fasa auren nan, kuma zamu aiwatar da komai ne a yau, don bamu da wani lokacin daya dace idan ba yau ba."

'Yar ta jinjina kai, maman ta d'ora, "Ai kinsan gidansu koh."?
Ta jinjina kai.
Eh, ya taba kwatantamin.
"Can zamuje.!!
Ta fada kai tsaye.

Yar ta zaro ido, uwar ma ta kafe ta da nata idanuna, tare da nuna ta da yatsa.

_matukar baki yadda mun dauki wannan matakin ba, to sai dai ki zauna ki aure shi kuma kada ki sake, mini complain akan bakya sonshi._
Ta dire zancen cikin daga murya tace, ko kin fara sonshi ne, kin yadda zaki aure shi."?

Tayi saurin girgiza kai.
Uwar ta mike tare da sab'ar jakarta, sannan ta mik'o mata hannu.
"Taso muje."
Babu musu ta mike ta bita, suka shiga motar uwar suka dauki hanya.
Jikin yar duk a sanyaye ko menene dalili oho.

Lura da hakan da uwar tayi yasa ta shiga yi mata wasu jawabai.
_ina raye bazan zuba ido ayi miki auren dole ba, tunda shi ya rantse bazai janye kudurinsa ba, ni ina da yadda zanyi.
Idan su gidan su yaron suka ce basayi ko shi yaron su ai ba zai musu dole ba koh."?

Ki kwantar da hankalin ki, ayau zuwa gobe zakiji batun auren ki babu shi kinga sai ki auri duk wanda kike so koh."?

Sukayi murmushi a tare, sannan sukayi shuru kowa da nashi tunanin.


Sub iso unguwar, sai da suka had'a da tambaya sannan aka nuna musu gidan.

_"Babban gida kalar gidan manyan mutane.",_


Matar wacce zatayi kimanin shekaru Hamsin
ko da d'oriya, na zaune a palournta, tayi shuru a zuciyarta tana lissafin wani abu.
Wato batun auren babban d'anta dake k'aratowa.

Ita ba tunanin hidindumu ne ya dame ta ba, Aa sai dai wani rad'e-rad'i daya ke ta isowa ga kunnenta a kullum, Wato _wai kalar yarinyar da d'anta ya dakko._

Bataji wanda ya yabi yarinyar ba sam, Sai dai kushe, amma ta daure abun, tunda ta tambayi mijinta kuma ya bata yak'inin tabbas mahaifin yarinyar mutuminki kirki ne kuma ya bawa 'ya'yanshi tarbiyya. Don haka ta yanke wani hukunci cikin tunanin da take na, _zata tuntubi dan nata sannan zata sa itama ayi mata binciken sirri._
Tunda indai kaji anfiya batu kan abu guda toh akwai magana.


Tana tunanin ne ta sami sakon cewa, wai tayi bak'i, abinda, ta fara yi shine duba agogo.

K'arfe 11:00am, don haka sai tayi tambaya "Su wane"?
Dan aiken yace, Hajiya dana tambaye su cewa sukayi, su ba baki bane, surukaine don haka in barsu su shigo.

Kamar zata sake magana sai kuma k'aguwa ( _eager_ ) taga su waye, yasa tayi saurin cewa shigo dasu kawai.

Suka shigo da sallama kamar, gaske, hajiya ta dago ido tana kallonsu da murnushi.

Duk abinda Hajiya Halima ta had'iyo sai taji tana shayin matar kuma tayi mata kwarjini, _mutum a gidansa kenan_

Sukayi shuru, bayan ta basu gurin zama, tare da musu tarbar da murmushi had'e da musu _sannu da zuwa._
Itama cikin son tuno ko ta sansu yasa take ta bin karamar da kallo, don ita tafi yi mata kama da _idon, sani._

Ta gaji da hasashen da kuma shurun da bak'in sukayi tace, cikin murmushi, _"Naso na shaidaku kuma na kasa, ko zaku min bayani."?_

Sai lokacin bakin Hajiya Halima ya bude, ta sami kwarin gwiwar yin abinda take ganin shiya dace, kuma zai jawo fasuwar al, amran."

Yes babu lallai ki sanmu, especially ma ni..

Hajiya ta zubo musu ido, don taji maganar kamar babu _salama_ cikin ta.

Kafin tace wani abu hajiya Halima ta nuna 'yarta,
Wannan 'yata ce Basma, itace danki yake shirin aure, to shine nazo na sanar muku gaskiya, _ni da ita bama son auren nan ubanta ne ke shirin kullawa,_ kinga kuwa gwara a hak'ura kada anayin batacciya don yata ba so take ba.

Ta kalli Basma, "Basma ko kina so."?
Duk rashin kunyar Basma sai taji tana shayin matar itama, kuma tayi mata wani irin kwarjini, amma don kada ta kunyata uwarta sai ta girgiza kai.
Hajiya Halima cike da k'warin guiwa ta dora, to kinji dai daga bakinta, yarinya bata so don, haka sai azan abinyi gaskiya, idan da zaki tambayi yaron ma, shi kanshi yasan...

Hajiya Rabi , bata bar Hajiya Halima ta k'arasa, zancen ta ba, ta daga mata hannu, sannan ta kafe ta da ido, da yanayin fuskarta da ta ke ta sauya zuwa kalar matsanancin fushi.

Ya isa, kin fad'i magana, kuma, sako yazo, saboda haka zancen ya yasheni haka."

Abin mamaki kuma sai ga Hajiya Halima ta kasa, mayar da martani sai shuru da tayi kawai tana jiran taga mai Hajiya rabi zatayi, don taga ta dauki wayarta.

Cikin tunanin t tsinkayeta tana cewa cikin wayar, "Kazo palour ko me kake yi."
Bayan d'an shuru kuma taji, tace, cikin fada nace kazo koh, babu ruwana da me kake, ko aya kake idan ba zaka zo ba tom... "
Sai ta katse kiran.
Minti baifi daya ba, sai sukaji sallama, ta bayansu, basu waiga ba, shikuma shigowarshi kai tsaye gun mahaifiyar shi ya nufa, cike da jin kunya.
_Dama mama tasan da baki tasa ya fito a haka babu wata cikakkiyar riga."?_

_Ya fito daga wanka ne, yana shirin fita, yana sa kaya ta kira shi, yasa wando, baisa riga ba sai singlet._ Abinda yake fada mata a waya kenan Cewar, _kaya yake sawa._ amma sai ta nuna fushi.

_Ashe bak'i tayi take son su gaisa.??_ Shidai yayi mamakin dalilin mama na azalzala haka, ya dan dosanu gefen ta,

Please Login or Register in order to submit comment