Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shud'e a wajen ta."?_


Sai lokacin bakinta ya bude cikin fushi ta fara magana.

Ta nunawa Basma hanyar fita. Cikin k'araji tace, Basma Yunus, fita, fitar mana daga gida, kar na k'ara ganinki a nan, an fad'a miki yanzu da ce"? Saboda kin rainawa kanki hankali kike tunanin har yanzu ke da Yusuf you're part of my business.."? Ke ce kike cikin damuwa, ke kika d`auki Yusuf mutum who worth your wested time, but to me ( _ta nuna kanta._) YUSUF IS WORTHLESS.!!
Ke dashi bani da had`i da ku, don haka matsalarki ce ni ban san wani Yusuf ba bare ke..!!

Fita!! Ta fad'a da sauti me k'ara.



Shigowar mama kenan taga taga abinda ke faruwa.
Ta tsaya ta k'are musu kallo har da bak'uwar fuskar da bata gane ba.

"Ke Hafsah mene haka."?
Cikin haki murya na rawa ta fara magana.
Mama Basma ce fah, Basma Yunus, kuma ta rasa sanda zata zo sai yanzu tazo ta korar min bak'ona!!.. ( _bama tasan sanda ta fadi hakan ba._)
Then tana fad`amin wani rubbish wai Yusuf mene ne had'ina dashi ni ta fita.!!
Zata fara kuka kenan Zainab ta tarota ta d'an rungumo ta, sorry Yaya kada ki bata hawayen ki kinji, bari kiga.

Sai ta saki Hafsah, tayi kan Basma, ta daga hannu zata daketa. Ke banza fice mana daga gida, idan kina da kunya ma zaki iya zuwa gidan nan, nonsense, deceiver, Hypocriter, snatcher.!!
Fita nace kafin musa a fitar mana dake.!!
Zata sauke mata hannu, mama tayi saurin rik'e hannunta. Ke Zainab shiga hankalin ki fah.. Me tayi muku zaku dake ta."?
Ta ruk'o Basma ta zaunar da ita, akan Kujera. Hafsah ma ta zauna.

Wacece ke."?
Mama ta tambaye ta.
idonta cike da k'walla, tace "Basma, kawan Hafsah ce ni."
"K'awar Hafsah, amma ban sanki ba."? Inji mama.
Basma tayi tsuru-tsuru.
"Me kika zo yi gidan nan toh "? Mama ta tambaye ta cikin tsanaki tana son ta gano wani abu itama.
Basma tayi shuru, tana kame-kame, um am.. "Na...na zo ne kawai.."
Hmm, to waye Yusuf da naji kin kirashi."?
Ta waro ido, ana shirin k'ureta.
Ehe.?
Inji mama.
"Sa..saurayin Hafsah ne.!!
"Saurayin Hafsah kuma."?
Inji mama.
Sai kuma ta juya ga Hafsah. Cikin had'e rai tace, "Ke waye Yusuf."?
Hafsah tayi saurin girgiza kai.
"Ban sanshi ba mama.!
Mama ta, juya, ga Basma.
''Ya'yana basa kula saurayi ba tare da sanina ba, saboda haka bamu san wani Yusuf ba a nan gidan.Don haka kada ki k'ara kawo mana zancen wani cikin gidan nan kinji.!!
Basma ta gyad'a kai jiki a sanyaye kuma a kunyace.

"Mene had`in ki ke da Yusuf d`in tunda kince saurayin Hafsah ne da bakinki."?

Basma ta hau zare ido. Bata da amsar bayarwa..
"Mama ma ta san hakan don haka ta cigaba da magana.


"Duk abinda ya faru ma, basai kin fad`amin ba na sani.
"Kinsan cuta babu kyau, k'awarki ta yarda da ke, ki cuce ta ki k'wace mata saurayi..kinsani to alhaki kwikwiyone, saboda haka ki tashi ki tafi gidan ku, kuma kada ki k'ara kawo mana zancen wani Yusuf cikin gidan nan, bamu da alak'a dashi.!!

"Kije, kinji abinda yayi miki ma ya isheki darasi, kije Allah ya baki wani kema, amma Hafsah kam bata san wani yusuf ba sam..

Cikin kuka Basma ta fara magana, Mum Dad d'ina ne yace ya fito ko ya aura min wani, shine yak'i na ya nuna bazai aure ni ba, shine kuma bayan ya dawo na je nemanshi na ganshi tare da k'awata, har mari na sukayi, and he til me bazai taba aure na ba kuma kada na k'ara kula shi.!!

Mama bata da abin cewa da alama kuma taga abin ne yana damun Basman shiyasa har take amaryar dashi, bata damu da korar ta da ake yi ba.

Ta mik'e ta kallesu dukansu, mama thank you, H. Hameed am sorry for give me for what I did to you.!!

Ta juya zata fita sai ta bawa mama tausayi.

Mama ta kirawo ta.
Zo 'yata kinji.!!
Basma ta juyo, ta dawo ta Tsaya.

"Ki bi zabin da mahaifin ki ya baki kinji."
Ta d'aga kai kawai, amma aranta bakin ciki ne fal.
Da alama taji shawarar mama da kunne ne kawai.
"Thank you mama. Tace, sannan
Ta juya ta fice.
Su Hafsah suka bi ta da kallo.



Ta fita tana cije lebe, tabbas yau taga Tashin hankali, wato har gwara abinda sukayi wa Hafsah ita da Yusuf..
Da irin korar da Yusuf yayi mata.

Kai tsaye Gidan mamanta ta nufa, taje ta rushe mata da kuka. Da kyar ta shawo kanta.
Kiyi hak'uri kinji 'yata fad`amin abinda ya faru.

"Mama gidan su Yusuf naje nemanshi na tarar ashe ma ya dawo.."
Sai kuma akayi yaya."?
Inji Hajiya Halima.
Cikin kuka tace, shine naga Hala a gidan suka mini wulaqanci ita da shi.
Hala."? Wace Hala."? Inji maman Basma.
My friend Hala.
Cab!! Me kikayi musu ke toh."?
Inji mama.
Mama, bazan iya dasu ba, baki ga abinda suka mini ba, har sawa yayi servant dinshi suka min wulaqanci, mama Yusuf bashi da mutunci, ban san haka yake ba sai yanzu."

Maman tayi shuru, itama bata da abin cewa, ga shi lokaci ya k'ure musu. Sai kawai ta shiga rarrashin 'yar tata, tana nuna mata tayi hak'uri akwai sauran wata hanyar, dole a koya musu hankali.
Basma ta d'ago ta kalleta, "How mama, can't you see lokaci ya k'ure gobe fah Abba zaice iyayen Nour su zo, kuma fah kinsan bana son shi mama."

"Kiyi hak'uri zanzo zamuyi wannan zancen, yanzu tashi ki tafi gida kinji, nasan abbanki bai san kin fito ba, kada kija matar nan ta zuga shi ya miki wani abin. Oya!! ki kwantar da hankalinki, babu mai aura miki wanda baki so, nina fad'a miki kinji."

Basma tayi ajiyar zuciya, ta gyara zama bata son tafiya tabar gidan.
"Mama ni bazan koma ba."
Ta fad'a a shagwabe.
Maman ta dan had'e rai, Oya tashi tashi mana, kina son ki b'atamin shiri so kike Abban naki yasan kin fito."? Ba nice dai nace kije babu komai ba."?

Ala dole ta mik'e ta nufi hanyar gida, cikin rashin sanin abinyi, gaba-d`aya duhu take gani, ta rasa wacce irin bak'ar rana ce wannan.

Mamanta kuwa ta rasa abinyi, ta sani alhaji Yunus yafi k'arfinta ba zata iya ja dashi ba, tun da tun farko ita ce ta mayar masa da 'yar, da komai bai faru ba. Mataki d'aya take ganin zata iya d'auka wato na shari,a shi kuma tana shakkar yin hakan nan ma. Amma fa dole tasan abinyi. Duk da wani b'angaren ita kanta ta sani Basma ta isa aure kuma, auren Basma hutu ne a wajenta, amma damuwarta shine ba zata bari a aurawa 'yarta wanda bata so ba..



*HAFSAH*
________________


Hafsah duk bayan muntuna tana duba wayarta ko zata ga missed call d`inshi, amma bata gani ba. Haka kawai taji babu dad'i, bataji dad'in zuwan Basma ba, a irin lokacin, gashi ta tsargu da tafiyar da yayi daga ganin Basma, anya kuwa bai santa a wani waje ba.?


Tayi shuru tunani fal a ranta, a zahiri tak`i bayyana damuwarta amna cikin zuciyarta damuwa ce fal, don Zainab ma sai da ta dameta da tambayoyi. "Yaya ya akayi wai bakon naki ya tafi."?
"Ke bansaniba nima, dama ba nace miki bazai dad'eba ba."

Amma naji d'azu kina cewa mama, Basma ta korar miki bak'o."?
Hafsah ta zaro ido, Yaushe tayi wannan maganar.
Sai ta mik'a hannu ta d'an daki Zainab.
''Yaushe nace haka, k'arya kike."
"Hmm, wallahi Yaya na fad'a.
Ta mik'e zata hau ta da duka, Zainab ta gudu.

Sai ga Basheer ya shigo, Zainab tayi bayanshi ta boye, "Yaya, Yaya, auntynka ce zata bige ni."
"Mene haka ke, me kika yiwa Yayata."?
Ya fad'a yana matsawa gefe.
Au bazaka boyeni ba."?
Inji Zainab.
"Sai kin fad`amin me kikayiwa auntie nah."
Hafsah ta koma ta zauna,tana jinsu.
Ai kuwa da labari zo kaji Yaya.

Hafsah ta had'e rai, tana hararar Zainab, "Allah Zainab ki shiga hankalin ki fah."
Zainab tayi dariya.
Au nidin, ba zaki bari a fad`amin ba koh Yaya. Inji Bashir.

Hafsah ta harare shi shima. Yau girman ya motsa. Basheer ya fad'a, azuci.
A fili kuma sai yayi murmushi, "Zainab ki bari zamu hadu ai zamu sa labule.!"
To Yaya. Zainab ta fada cike da tsokana tana kallon Hafsah tana mata dariya..

Bashir yasa Mufeeda ta zubo mishi abinci yana ci suna hira, acikin hirar Basheer yake cewa, "Yaya ni kuwa mun tab'a exchanging numbers da wani, wata rana mun fita har muka danyi clash da wani a mota."?
Gaban Hafsah ya fad'i da sauri tace "Toh menene."?
Basheer ya girgiza kai, "babu komai nasan dai ya kira number ta bai sameni ba kuma na duba number babu akan wayata bata hau kan email ba da nayi saving."

Sai kawai tace Okey, wani abin zakuyi kai da shi."?

Baya son ya fada mata ya nuna yana son wata cikin su don haka yace, A,a kawai babu dad'i ne."

Daga nan ya kawar da hirar. Zuwa wata. Ita kuwa Hafsah jikinta tayi dama ace ya kira Bashir d`in taji mai zai ce.?
___________________


Har washegari, zuwa yammaci bai kirata ba.

Ta d`an damu, don haka ta kira Zainab suyi shawara. Bayan Jan kunne da tayi wa Zainab d`in, kan koda wasa kada ta sake ta bawa Basheer labarin bak'onta..
Zainab d`in tace "Toh.

Sannan Hafsah ta fara maganar da tafi damunta..

"Zainab kinga bai kirani ba, tun sanda ya tafi. Ta fada da 'yar damuwa.

"To Yaya ke ki kirashi mana.!!
"In kirashi."? Inji Hafsah tana d'an hararar Zainab.
Zainab ta jinjina kai, "Eh, may be fa gwadaki yake yaga idan ma kin damu dashi, kuma tunda shi yazo wajenki you supposed to call him, irin kice ya yace gida."?
Hafsah ta tab'e baki. "Ke tafiya fa yayi babu shiri, kuma yak`i kirana, so kuma sai in kirashi, saboda zub da class."?
Yayah.. Wallah babu wani down da class zaiyi, kuma ma ai da dalili, rashin kiranki da baiyi ba, shi zaisa ki kirashi, kuma ba doguwar waya fa zakuyi ba, just irin ki nuna mishi ya yaje gida, and mai isa ya tafi don kinyi bak'uwa kinga inda ma wani abu a k'asa zaki ji ai..

Hafsah tayi shuru, cikin raba tunani, tana son ta kirashin, don gaba-d`aya ji tayi tayi wani sabo da shi, ga kuma tasirin ganinshi da tayi, yayi mata sosai taji ya shige ranta cikin k'ank'anin lokaci, amma kuma bata son yaga zakewar ta..
Nan ta d'anyi jim cikin shawarwari....


_____________________________

Shi kwa bayan ya koma gida, tunani ya zauna yi. Me ya hadata da k'awa irin wannan, menene alak'arsu haka, yana so ya gano. Yarinyar sam kana ganinta Kasan babu tarbiyya, amma me yasa ya ganta tazo kamar Cikin rashin hayyaci, yaji kuma tana ambatar wani, to me ya faru da ita, me wanin yayi mata, ta yuwu fa wani abun ya mata mara dad'i, kuma ta rasa gurin wa zata zo sai wajen Hafsah, in kuwa mafita tazo nema kenan Hafsah aminiyarta ce."? Tunda da amininka kake shawara. Sai yaji baya fatan abin ya zamana haka.
Yayi sauri yayi _Ta,awiziy_ saboda zargi kawai yake, bai tabbatar da ko d'aya daga cikin abubuwan da yake tunani ba, sai yaji ya dace ya sa ido, ko kuma ya d'an yi bincike game da hakan..



_ALHAMDULILLAH naga wad'ansu daga cikin copy da nayi a *clip board*, wasu kuwa sunbi ruwa especially wanda nayi tun daga yau da safe, da kuma na yamma...babu komai وما قدر الله حق قدره... Alhamdulillah alaa kulli haal.!!_👏🏼👏🏼👏🏼

Allah ya kaimu gobe.😊😇
*THNKS*
*FOR*
*YOUR*
*LOVE*
*&*
*SUPPORT.*
👍🏻👍🏻👍🏻👍🏻👍🏻



📝
*HAJEEYAH*
*KHAREEMERH*
[17/03, 2:42 p.m.] UMAIMA BASHEER: ♥️♥️♥️♥️
*ZAZZAFAN SO*
(masoyin k'warai)
*Cigaban littafin Zazzafan so*
*(Guba ne)*
💔💔

*By:*
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah khareemerh )*
*Dedicated to Unique in your love heart group members.*


_~Am sorry readers/fans anyi mana rasuwa ne again, yayar mahaifina ce ta rasu.!!~_👏🏼👏🏼👏🏼👏🏼



📄 *55*





*Yana* cikin tunanin wayarshi tayi k'ara, ai kuwa da sauri ya duba, ganin Itace yasa shi wani murmushin jin dad`i.
Ya d'aga kiran tare da saka ear piece a kunne.

Itama ganin ya d'aga ya sa ta d'an so ta rikice, kada fa yaga zakewar ta. Amma babu yadda zatayi ta riga ta kirashi.

A hankali ta bud'i baki tayi mishi sallama.
Ya amsa muryarshi na bayyanar da farinciki.
"Wa alykm salam."

Sukayi shuru a lokacin, shi cikin jiranta tace mishi wani abu, itama tana jiran taji ya k'ara magana.


Zainab na gefe tana mata alamu da tayi magana mana. Ta aika mata da harara sannan tace,
Ya kake."?
Caraf ya amsa.
"Lafiya lau hope kema kina lafiya."
"Lafiya lau itama tace."
"Naji dad`in ganinki sosai fah."
Ya fad'a yana murmushi.
Tayi murmushi itama.
Ya d'ora duk da nasan ke ba haka bane koh."?
Hmm, tace mishi don bata abin cewa idan ba hakan ba.
"Hakane kenan gashi nan kin fad'a.!!
Cikin son kare kai tace, "Um Um fah.
Hmm, ai na sani bani da kyau ko had'uwar da zan burge ki."

Hafsah tayi shuru, a zahiri. Wannan mutum yana son ya dinga sata fadar abinda batayi niyya ba. A lokacin ya dace tace mishi _kayi min mana."_ Amma kuma tana ganin kamar lokaci baiyi ba da zata fada mishi irin haka. Don haka sai ta raka zancen nashi da murmushi kawai sannan tace, "Ai baka dad'e ba ka tafi."

Yaji dad`in maganar, don wannan wata dama ce da zai gano abinda yake son gano wa.
"Ai naga kinyi bakuwa ne."
No don nayi bakuwa, sai ka tafi, itama ba dadewa tayi ba.
Yayi yar dariya, naga kamar tana son ku tattauna ne, am sorry na kula da yanayinta kamar akwai damuwa koh.. Shiyasa na barku ku tattauna."

Hafsah ta d'an tsargu, kuma har yanzu bata kai ga gano cewa, ko yasan Basma ne, bata son zargi ya shiga tsakanin su, tunda bai san tabbatar ba itama ba gama tantance halinta yayi ba, don haka ba tare da tayi wani dogon tunani ba, tayi saurin cewa. "Noo nifa na dad'e banganta ba for long.!!
"Koh."?
Taji yace,
"Yes zamuyi 2years bamu had'u ba."
Ukhasha ya d'anyi jim, baya son ya k'aryata zancenta tunda bashi da masaniya, kuma baya son yaja zancen da tsaho, amma kuma yana son yasan ainihin dalilin zuwanta toh.
"Oh am sorry naji kamar tana kiran sunan wani koh, wani abun ne ya faru."?




Anyi mata rasuwa ne brother nata shiyasa tazo tana irin haka, banjin ma, tasan tazo."

Take yaji ya yarda da ita, sai ya nuna alhinin shi, "Allah sarki Allah ya jiqanshi. Shine naji tana kiran Yusuf koh."?

Hafsah, ta waro ido, Wannan mutum bashi da mantuwa, dole tayi taka tsantsan.
Cikin k'osawar da ya fahimta a cikin muryar ta tace, "Eh."
"I'm sorry na dameki da zancen koh."?
Sai kuma ta d'anji kunya. "Tayi yar dariya.
Ya katse kiran, tuna cewa ita ta kirashi, sannan ya kirata, lokacin sun tafa ita da zainab zainab nace mata, ai dama na fad'a miki Yaya.

Ta d'aga kiran tasa a kunne, muryarshi da sanyi sosai, kuma tayi can k'asa da kyar ta fara jiyo abinda yake fad'a.

"Hafsah.!! Taji wani iri kamar yadda ta saba ji idan ya kirata da sunan ta.

Wallah ina sonki kin burge ni, sosai tun sanda na fara ganinki, bare jiya da na k'ara ganinki kinyi min sosai."

Jin zancen da yake yi, yasa ta bada hankalinta gabadaya kan abinda yake cewa, tana bukatar nutsuwa, sannan bata saba da dinga yin waya gaban wani ba, bare shi da yanzu yake mata wani irin zance, tana bukatar ta saurare shi sosai. Don Allah tayi Zainab nuni data fita.
Zainab tayi mata dariya, sannan ta noke kafad'a.
Zainab ta aika mata da harara, sannan ta mik'a hannu zata kai mata duka, Zainab ta tashi da gudu tana mata gwalo.


Baiji tace komai ba, don haka ya cigaba da magana..

_Ki yarda dani, ban taba jin ina da niyyar wasa da hankalinki ba, zan fada miki gaskiya, wallahi tunda na ganki naji kinyi min sosai, ina son kulla alak'a dake, ina son ki, kuma zan iya aurenki idan kin amince min..

Ya marairaice murya, "Don Allah idan har banyi miki ba, ki sanar dani, bana son in d'inga bata miki lokaci..

Thanks for your time, gud night."

Ya kashe wayar take.





Wayar na kunnenta, ta kasa motsi bare ta cire ta, jikinta yayi sanyi da kalaman shi.
Kanta ya kulle tamau, ta rasa wanne irin tunani ma zatayi"? Me yasa yake mata haka. laifin waye a cikinsu nata ko nashi."? Ya zaiyi mata magana irin wannan sannan ya kashe mata waya ta ke."? Tunda amsa yake nema daga wajenta to meyasa bazai jira yaji ta bakin nata ba."
Sai kuma ta shiga kasa musu laifukan ita da shi.
Laifinta shine jan aji. Inji wani b'angaren na zuciyarta. _"Hafsah kina ja wa mutumin nan aji sosai, yanzu ak'alla kunyi fiye da wata ke da shi, kuna waya, amma kin kasa sakin jiki da shi, magana ma doguwa bayi mishi kike ba, aganinki zai ta zama dake haka ne."?_

Tayi saurin kare kanta. _Tabbas tana da dalili lokaci baiyi ba da zata fada mishi irin abinda yake bukatar ji. Tana da buk'atar sanin wasu abubuwa muhimmai ga me da shi."_

Me yasa zai k'i sanar da ita abubuwan da ya dace ta sani game dashi."? Wannan shine laifinsa.


Na nutsa tunaninta cikin tunano shi, siffofin shi, da kuma wasu abubuwa da ta lura game dashi a had'uwar su.




_Mutumin ya hadu ba shi da makusa ta bangaren halitta. Yana da kyau matuk'a, ga kwarjini komai nashi zai iya burge ko wacce mace._

Yana da barkonci, kuma ta lura bai fiya daga kai ba ko nuna isa. Ya damu da ita matuk'a, sannan shi mai mata hidima ne ta gani a zuwanshi wajenta. _A yadda ya nuna kenan a zahiri, don bata san ainihin cikin zuciyar shi ba. Tunda sanin gaibu sai Allah.!!_

Wata zuciyar ta tambaye ta. To me kike son ki sani banda wannan kuma."?

A zahiri ma sai da bakinta ya motsa, ta furta babu sauti. _Waye shi."?_

Tabbas akwai buqatar ta san waye shi, dan gidan waye, Matsayin karatun shi, sana,ar shi da sauran abubuwa.



Wani gefe na zuciyarta ya k'alubalenceta da cewa. Yanzu Hafsah don zaki amshi Soyayyar mutum sai kinsan dan gidan waye."? Har da binciken aikin shi."? Anya kuwa son gaskiya kike mishi, ko ma kina son nashin kuwa."? Lokacin da kika amshi Yusuf AI baki kawo wadannan tunanukan ba sam, ko dan shi bakya sonshi shiyasa kika tsaya tantance wadannan abubuwan, Yusuf kuwa idanunki sun rufe saboda Soyayyar shi koh."?
Sai dai idan ba son gaskiya kike shirin yi mishi ba, kina da abinda kike so kawai.


Gabanta ya fad'i, bata so ace abin ya zama haka, bata son zargin ya fad'a akan cewa sonshi ne da batayi shiyasa haka. Don haka ta lalubo hujja.

_"Tabbas lokacin da ta amshi Yusuf batayi bincike ko tunani irin wannan ba, ta kalli Yusuf ne kawai a matsayin cikakke wanda ya hada komai da take buk'ata. Amma yanzu ta mallaki hankali ya dace ta tantance kafin ta zaba ko dan gudun mamaita abinda ya faru._

Abinda kike son sani wannan bincikene na iyaye ba naki ba. Kawai in zaki amshi soyayya ki amsa, da wuri don shima ya nuna ya gaji da baki lokacin shi.

To idan na shirya amsa ta yaya zan nuna mishi.? Yayi magana bai jira cewata ba ya kashe waya.!!
Ta tambayi kanta.

_Akwai sauran dama.!!_ Ai bacewa yayi ya daina kiranki daga yau ba, kuma dole ki nemo hanyar da zaki nuna mishi kin amince da shi yadda zai fahimta.





Wayar da ke kunnenta ta shiga k'arar da tasa ta dawo daga tunanin ta take ta kullawa a zuciyar ta.

Tayi saurin zare wayar, sunan Jamila ta gani.

Ta saki ajiyar zuciya, ta daga kiran.

Hello."
Jamila tace.
Itama ta amsa da Hello
Jamila kina lafiya.
Cikin muryar ta da dama ta dad'e da chanjawa, tace, "I'm fine. "Ya mutanen gidan ya mum."?
Hafsah taji dad`in hakan..
Lafiya lau." tace tana dan murmushi tace, "Bayan kince zaki zo baki zo d`in ba."?
Wallah babu time ne, ina ta son inzo, but zaki ganni, savoda zanje Dubai nan da two weeks so zan shigo unguwar kafin na tafi."

Gaban Hafsah ya fad'i. "Dubai kuma."?
"Kada dai Jamila tayi shaharar zama _International."_

Don haka taga asarar barin Jamila batare da ta nemi k'arin bayani ba. Da sauri tace.
Dubai me zaki je yi Dubai."?
"Zanyi rakiya ne."!! Jamila tayi magana tana wata 'yar siririyar dariya.
Kan Hafsah yayi wata iriyar sarawa.
Tana son ta k'ara tambayar Jamila, _Wa zata raka haka."?_
Amma kuma bata son Jamilar taga kamar tana binciken ta ne. Don haka tayi shuru kawai.
Sai ta juyo Jamila na cewa. "Thank you, ki gaida mama, bari na d'aga wani kira.
"Okay thank you bye bye.
Hafsah tace...






📝
*HAJEEEYAH KHAREEMERH*
[17/03, 2:46 p.m.] UMAIMA BASHEER: ♥️♥️♥️♥️
*ZAZZAFAN SO*
(Masoyin k'warai)
*Cigaban littafin Zazzafan so (Guba ne)*
💔💔

*By*
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah Khareemerh)*
*Dedicated to unique in your love heart*



📄 *56*



_NAILA group 1 ina godia da Soyayyar ku... Espclly #ummita_😊😊
_Sayyada_ kema Inayinki. (NAILA group 2)

*Team Ukhasha
*Team Hafsah.
Inajin dad`in comment d'inku.💃🏼💃🏼💃🏼


*Ranar* da ta biyo baya, bai kirata ba sam tun daga safiya har wata wayewar garin.

Hafsah ta sanya kanta cikin tsarguwa. Amma kuma tanajin ba zata iya kiranshi ba.


___________________
Yau gaba d'aya busy yake, abubuwa sun mishi yawa, bayan dawowar shi daga office, yayanshi Dr. Sunusi yace ya same shi a gida, zasu tattauna.

Yana dawowa abinci kawai yaci, yayi wanka sannan yayiwa Hajiya sallama ya wuce.



Bayan hira da sukayi ta zumunci, Dr. Sunusi ya bujurowa da Ukhasha maganar da yasa ya kirashi.

"Ukhasha."!!
Ukhashatu ya amsa.
"Naam Yaya.!!
Dama wata _share_ ce zan maka talla ko zaka sa kud'inka kaima aciki..

Ukhashatu ya bada gaba d'ayan hankalinshi ga yayan nashi.

Dr. Sunusi ya cigaba da magana.

Wani d'an k'aramin company ne, na had`in guiwa mukeso mu bude ni da abokai na mu shidda, to kuma mun duba munga muna da buk'atar k'arin kud'i shine muke bukatar k'arin mutum d'aya.

Ukhasha ya gyara zama. Okey Yaya, kamar nawa ake buk'atar kowa ya saka."?

Ba wai bukata ake kowa sai yasaka daidai da na kowa ba. Zaka iya saka ko nawa kake dashi kawai, tunda za,a dinga raba ribar ne, daidai da yadda kudin mutum yake aciki.

Ukhashatu ya jinjina kai, Okey na gane Yaya, amma kamar nawa kake ganin ni zansa."?
Um..To." Inji Doctor. Sannan ya kalli ukhashatu.
Zaka iya saka 4million, ko da rabi ma.!!

Ukhasha yayi murmushin gefen kunci.

"Doctor, ansan nauyin aljihun fah.
Na sani.!
Inji Dr Sunusi yana murmushi shima.
"Ka saka 4million d`in dai."
Ukhasha yayi ajiyar zuciya a hankali, Dr. ya kalle shi da alamar tambaya. Ukhasha yace, "da inada wani lissafi da nakeyi ne."

Dr. Sunusi yayi murmushi, wanne tunani kuma."?

Ukhashatu ya sunkuyar da kai, yana shiga matsa k'afar shi, dama a kasa suke dukan su a zaune.
Dariya ya bawa, Dr. ma sai da ya gama dariyar sannan yayi magana.

Aure zakayi."? Bai barshi ya bada amsa ba ya d'ora.
Ka gaji da zaman gwaurontakar kenan...
Ukhasha yayi wani dan murmushi. "A,a fa Yaya."
To mene tunanin naka idan ba shi ba.
Yayi shuru, don bashi da amsa.
Hmm, yanzu dai ka nemo, 4m. kawai kaidai, zamuji dad`in abin fa idan ya kankama.
Okey in sha Allah."
Inji Ukhasha.
Zuwa Yaushe za,a karbi kud'in.
Nan da wata d'aya muke son mu fara shirya komai, amma muna yin meeting akan yadda abin zai kankama, gobe ma muna dashi, da daddare sai ka shigo muje.!!

Okey, in sha Allah.

Am naji Hajiya na cewa zatayi retire koh."?

"Eh haka tace, nan da wata d'aya ne."
Gud, ai gwara ta huta.!! Inji Dr. Sannan ya shiga wata maganar.
"Yaushe ma Abba yace zamuje gidan gonar nan don na manta.
Nan da sati d'aya ne." Cewar ukhasha.
Ai abin ne da yawa abubuwan sunyi yawa.
"Ana kokari ai."
Inji ukhashatu, Naji yace yana so ne, ya k'ara fad'ad'a wajen."
"Yayi kyau hakan ai, kaga ya dad'e bai je duba gurin ba fah.
Ukhasha ya jinjina kai, "Eh amma
"yana tura ni akai-akai ai, kuma naga babu laifi ma,aikatan suna kula da wajen yadda ya dace.!!
So ko zamu bude namu d'an k'aramine haka koda iya kaji ne, da kifi sai mu saka. Cewar Doctor yana dariya.
Ukhasha ya taya shi dariyar shima. "Hmm Doctor kenan.!!
Cikin nutsuwa yake jawo hakalin Ukhashatu kan abin da cewa, "Ina da wani tunanine, kuma dana bujurowa da Abba shi naga ya nuna jin dad'inshi har ya sanyawa abin albarka ma."
Ukhashatu ya kalle shi irin kallon neman k'arin bayani.
Cikin nutsuwa doctor yace, inaso mu bude wani kasuwanci dukanmu har matan ma, kai hatta mahseem sai ansa mata nata kason aciki.!
Ukhashatu ya waro ido.
Doctor ya jinjina kai, Yes, wannan zai kara kawo had`inkai, sannan kuma gaba ake ji ba baya ba."
Ukhashatu ya jinjina kai. "Hakane..abun yayi kyau.
Baka ga yadda Abba ya d`auki abin ba, daga yi mishi zancen ni na zaci ma yayi maka zancen.
Ukhashatu ya girgiza kai.
"A,a" Amma waye zai sawa su yaran tunda kace har Mahseem."?
Doctor yace yana dariya. "Abba ne.!! Kuma ai ba wani abu mai yawa zai maka musu ba, tunda kasuwanci ne irin na kayan amfani irin na kasuwa da kadan zamu fara, kuma za,a saka equal ne babu mace babu namiji kowa

Please Login or Register in order to submit comment