Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cike da kunya, sai lokacin ya lura da su wa ke zaune a wajen.
Ciken da rudu, ya fara magana, "Ba Basma..!!??

Mamanshi ta daga mishi hannu.
Dakata.!!
Kasanta ne."?
"Ba bas, Basma ma cehh ma mama.!
Ya fada cikin in'ina.
Uwar ta jinjina kai, sannan ta mike tsaye shima ya mike, gabadaya ya rud'e.

Uwar ta nuna shi da yatsa sannan ta nuno Basma.
"Tabbatar mata ka fasa aurenta kaima."
Cike da rud'ewa ya hau rarraba ido kamar baya gani, tsakanin mamanshi da su Basma.

Uwar ta k'ara daga murya, sannan ta nuna Hajiya Halima da yatsa, Me kikace game da 'yarki. "?

Hajiya Halima ta mike tsaye. "Basai kin nuna ni da yatsa ba, cewa nayi ni da 'yata bama son auren nan idan akayi shi za,ayi b'atacciya.!!
Ta kalli, Basma ta k'ara cewa, ko kina so."?
Basma ta girgiza kai kamar d'azu.

Hajiya rabi ta kalli danta, cikin daga murya tace, zaka aureta ko ka fasa kaima"?
Nour ya zubowa Basma idanu, itama shi take kallo, yana k'ara kallonta, tanajin wani rauni yana shigar ta a hankali.

Ahankali shima ya bude baki yace, "Nima na janye, na fasa auren ki.!!
Yana fadar haka ya dauke idonshi daga kan Basma ya juya ya kalli mahaifiyar shi, kwalla fal idanun shi.
Hajiya Halima ta bude baki, "Ahto gaskiya kunyiwa kanku....

Dakata ke!!
Hajiya rabi ta fad'a da daga sauti sai da ta razana Basma, sannan tasa Hajiya Halima dakatawar babu shiri.


Hajiya rabi ta nuna su duka tare da cewa, tunda abinda ya kawo ku ya wuce, to ku bace daga gidannn kafin na gwada muku kalar nawa ikon, don ba ahaifi yar da akanta, za, ayi min dibar albarka ba. Idan kuma kuka k'ara koda minti cikin gidan nan to tabbas zaku gane inda kuka zo.!!!

Ta juya ga d'anta tana mishi wani kallo.
Jeka karasa shirinka kaji dana.
Nasan baka da damuwa koh.'?

Cike da dakiya ya kirkiro murmushi ya jinjina kai.

Abinda ya bawa Basma madaukakin mamaki kenan.

Ina tarin naci, da dumbin son da Nour ke mata.??


Har suka koma gida jikinta a sanyaye, ta kasa nutsuwa da abinda suka aikata ita da mamanta.

"Anya kuwa batayi abinda zai zame mata nadama ba."?
Wata zuciyar tace, _wacce iriyar nadama bayan kin rabu da alakakai."??_

_________________

Agidansu Nour kuwa, bayan fitar su Basma, Nour ya fada kan kujera, ya dafe kai, kuka yake shirin yi amma kukan ma yaki zuwa, yana mamakin abinda ya faru kamar a mafarki yanzun nan.
Ya sani bazai iya bawa mahaifiyar shi kunya ba, a yadda ta hak'ik'ance zai goyi bayanta, a lokacin da ake nuna mata iyakarta akanshi.

Itama Hajiya Rabi zama tayi kusa dashi, tana son ta bashi baki. "Kayi hakuri kaji Nour, ka d'auka komai kaddara ne, kada kaga agabansu nace ka fasa aurenta. Bani da iko akan aurenku haka suma, Allah shike kaddara komai Idan ya nufa sai Anyi ko basa so. Amma hakan bazai sa na bada damar su ci mana zarafi ba har cikin gida, saboda kana son 'yarta, kaima kayi taka tsantsan kaji, ka nemi zabin ubangiji, amma ka girmama kanka, kada ka wulakanta kanka inda baza,a taba ganinka da daraja ba, bayan Allah ya girmama ka ( _amatsayinka na dan adam._)

Zanyi maka addu,a kada ka damu kaji.. "? Zamuyi magana da abbanka, tashi kaje, kayi fitarka kaji, Allah ya zaba maka abinda yafi alkhairi.

"Da kyar ya ambata Amiin mama."
Ya tashi babu k'wari ya nufi d'akinshi, fitar da tasha ruwa kenan, don ya samu rauni matuka ajiki da kuma zuciyarshi.


Da daddare Abbansu Nour, na dawowa, Hajiya Rabi tayi mishi bayanin komai, sannan ta dora da nata ra,ayin.

_"Alhaji ina ganin tun da har abin ya zama haka, to gaskiya a hak'ura, tunda har suka magantu, kuma abin yakai ga anzo har gida to ina ganin Nour ya hak'ura Allah ya bashi wacce tafita, don idan har yarinya ta furta bata so to za,a sami rashin jituwa._

Alhaji ya jinjina kai jin duk bayananta, sannan ya bude baki, baya son ya nuna mata ra,ayinshi, a lokacin don haka yace, "Tom duk naji abinda kikace kiyi addu,a Allah yayi zab'in alkhairi, zan tuntubi shi Nour din da kuma mahaifin yarinyar."

Daga nan bai sake bata damar k'ara yin magana ba.


______________

Abban Basma yayi mama kin yadda ya dawo yaga Basma bata gidan. Aikuwa ya sauke fushin kan ya ya yayar Basma da ita kanta Hajiya salman, inda ya dora musu laifi duka. Sai da ya sassauto sannan ya fara binciken inda zai samo ta, sai ya fara da Halima.

Ya kirata a waya a fusace, itama tana ganin kiran ta share. Ya kara kira karo na biyu sai taga ma gwara ta daga suyi ta ta k'are.

"Hello ya akayi ne." Ta fada a fad'ace.
Halima ki dawo da Basma, don ba muyi dake zata zo wajenki ba."
Hmm, bazan dawo da ita ba da yake jaririya ce ita da zakace na dawo da ita.!!

Nace ki dawo da itan da waye yace ki zo ki dauke ta.
Tayi dariya au ni na d'auke ta ma koh."?
"Hmm, Alhaji Yunus yarinya fa ta girma sannan ba a kauye muke ba bare kayi mata auren dole tunda tace bata so to fa bazan zuba ido ayi ba. Sannan dawowa ba zata dawo ba.
Haka kika ce koh. "?
"Eh, haka nace.!!
Cikin fusata ya kira sunanta.
"Halima.!!
Ki shiga hankaliki dani wallahi ke kin isa ki hana ni iko akan 'yata."?
To bari kiji ko kinki ko kin so aure sai na aurar da Basma, sannan koma komawarta wajenki bazai sa na fasa daura mata aure ba, sai dai in bata numfashi.."!!
Hajiya Halima ta sheke da dariyar data bashi takaici. Take ya katse kiran tunaninshi ya kira Basma, sai ya tuna cewa ya kwace wayoyinta. Yayi jigum yana tunani tabbas akwai aiki gabanshi.



Wani abu daya bashi mamaki shine kiran Abbah Nour daya gani da daddare.
Da sauri ya daga yana fatan Allah yasa lafiya.
Suka gaisa cike da girmama juna. Kafin Abban Nour ya fara magana.

Am Alhaji dama inaso ne ka bani dama ko zuwa gobe ne ina so nazo na ganka.
Fargaba ta kama Abban Basma. Ya bude baki da sauri yana tambaya "lafiya dai Alhaji."?
Cikin murmurshi yake magana, "lafiya lau, ina so ne mu tattauna wata magana ne.
Da kyar Abban Basma ya kwantar da hankali sannan ya bawa abban Nour dama daya zo gobe su tattauna din.



Yammaci nayi Abban yayi sallama, a gidan su Basma. Abban Basma ya mishi iso a falon bak'in shi.

Ya tarbe shi da ruwa da abin sha. Sun gaisa sosai. Abban Basma yayi jugum cikin fargaba, yana fatan Allah yasa zancen kawo lefe ne ya kawo shi.


Alhaji mukhtar ya muskuta, sannan ya fara jawabi. Yayin da alhaji Alhaji Yunus ya bashi duka hankalin shi.

"Am Alhaji dama wata magana ce nazo da ita saboda maslaha, kuma naga ya dace muyi magana daga ni sai kai.

Ya danyi shuru, ya lura da dan tashin hankalin dake kan fuskar Alhaji Yunus. Sai kawai ya kauda kai ya cigaba da magana.

Wato wani al,amari ne ya faru jiya da maraice. Ita mai mai da dakinka da ita yarinyar da ake nema sun zo har gida sunyi magana kan cewa basa buk'atar wannan aure.!!

Sannan an tambayi yarinyar agaban ita mai dakinka shin tana bukatar auren tace bata so, sannan ta jaddada hakan agaban shi Nuran bayan mahaifiyar shi ta kira shi."
"Innalallahi wa in inna ilaihi raji,un."
Shi Alhaji Yunus yake ta maimaitawa, ji yake kamar yayi hawaye, wannan wane irin wulak'anci ne halima tayi wa yasan iya abinda taje tayi musu a gidan mutane."? Halima ta zubar masa da k'ima.

Ganin yanayin da ya shiga na tashin hankali yasa abban kokarin kwantar mishi da hankali,

To shine nace Alhaji kada azo ayi abu da son zuciya, ya dace a tsahirta a samu amincewar tasu tunda ita yarinya dai da ita za,a zauna, kuma auren nan fata muke ayi ya d'ore. Saboda haka shima yaron zan bashi dama idan ya iya shawo kanta toh, Allah ya tabbatar da alkhairi, zamu gani zuwa wasu lukuta ko ya kace alhaji."?


Abban Basma yasa Handkerchief din sa, ya goge gumin daya tsatstsafo masa.
Rauni sosai cikin muryarshi wanda zai yake nuna tsananin tashin hankalin da yake ciki.
"Don Allah Alhaji kayi hakuri don manzon Allah wallahi ban san abin nan ya faru ba...!!

Alhaji Mukhtar ya dakatar dashi yana fad'in, "ashsha.. ashsha Alhaji ya da magiya haka."?
Wallahi maganar nan saboda maslahar yaran yasa nazo maka da ita ko kadan ni ban bata raina ba akai, don bana nan ma suka zo dake da safe ne. Kayi hakuri ka dauki komai a sannu, su sha'anin mata sai a hankali. Kada ka dawo Alhaji.

Abban Basma ya kara gyara zama..
Dole na roki afuwarka Alhaji. Domin wannan cin mutunci ne, ya za,ayi azo har gida saboda rashin hankali haba ai abin babu mutunci. Don Allah kayi hakuri wallahi bani da masaniyar hakan. Kuma ita matar ba ma tare da ita shiyasa take kokarin hana auren. Amma kayi hakuri don Allah a bawa mutanan gidan hakuri suma don Allah."!!

Cike da kunya alhaji mukhtar yake magana domin bai so yasa abban Basma cikin wannan halin ba.
Babu shiri ya mike da shirin tafiya. Kayi hakuri kaima don Allah sannan kabi komai a sannu. Wallahi babu komai a wajena wannan abin ba komai bane illa neman samun maslaha, kuma mu cigaba da addua Allah yasa alkhairi dama harkar aure dole ana samun kalubale. Amma wannan abin ba komai bane balle kuma kasan sha,anin mata sai su. Ayi hakuri dai Allah ya tabbatar mana da alkhairi."
Ya mik'a mishi hannu jikin abban Basma a sanyaye sukayi musabiha.

Ya mike da kyar ya raka Alhaji Mukhtar cike da kunyar shi. Don abin da Halima tayi yaja mishi kunyar manyan mutane irin su Alhaji mukhtar. Kuma yasan ta gama zubar mishi da k'ima.

Tafiyar abban Nour kenan Alhaji Yunus ya shigo gida.
Yanayin sa ya tada hankalin Hajiya Salma ta bishi dakin shi da sauri..

Ta tarar ya yaye babbar rigar shi, ya cillar a tsakar dakin yana shirin juyawa zai fita. Alhaji lafiya ta tambaye shi.
Sai da ya juya zai fice sannan yayi mata magana a fusace yana huci.

Billahil-aziim sai Halima ta gane wanene ni.!! Ya cigaba da tafiya bai kara magana ba.
Hajiya Salma ta bishi da sauri kiranshi ta tsorata da yanayin nashi amma ina tuni ya fice. Ta biyo shi har Harabar gidan tana kira amma ya fice ko mota bai dauka ba.

Ta dawo gida cike da rudu tana tambaye tambayen da babu amsarsu. Fatima meya faru da Abban ku. Ina tunanin gidan halima zaije fa. Ina tsohon abinda zai faru ko me tayi masa oho."
"Kinga dakko hijabin ki muje wallahi ban aminta da fitar Alhaji zuwa gidan ta ba. Fatima ta taso babu shiri. Itama hankalinta duk ya tashi.



________________
Mamaki da razani ne suka tarar tararwa Hajiya Halima ganin Alhaji Yunus a gidan ta kuma babu neman izini daga sallama ya shigo cikin falon.
Ta mike tsaye a dan tsorace, ya nunata da yatsa. Sannan ya rigata fara maganar da take shirin yi cikin fushi.
"Halima kinyi abinda kikayi kinji dadi kuma yayi kyau bazan ce kinfi karfi naba, don idan nayi niyyar daukar matakin zakiyi mamaki amma zan nuna iko a inda nafi ikon sosai, don wallahi baki isa kin iko akan yata ba kuma aure babu fashi.!!
Kan tayi wani yunkuri ya wuce ta ya nufi bedroom dinta.
Aikuwa sukaci karo da Basman daya shigo nema don tajiyo muryarshi tana shirin fitowa taga me zaiwa mahaifiyar tata.

Ai kuwa ya kife ta da mari kafin ya jata fii ya zubar da ita a kasa.
Cikin tsananin fushi yake maganar.

Kinje kinyi abinda kukayi ke da uwarki yayi muku kyau wallahi idan hakan ya zama silar fasuwar auren ki Basma hakkina sai ya biki don nayi iya kokari na kuma bazan sake saka hannu akan al'amarinki ba. Don na sauke hakki na a kanki.


Meye haka me kake ji dashi ne zaka shigo min gida kana min hayaniya kuma don wulak'anci har uwar daka me kake nufi.

Ya juyo a fusace komai ma ina nufi.. Don baki isa kin hanani iko akan yata ba.
"To wallahi ka fita kafin na tara maka jama'a."
Ya daga muryarshi ya fuskanto ta shima.
Ki tara mini jama,ar Halima sai me aini kin gama zubda min da k'ima kuma sai Allah ya saka min abinda kikemin ina yiwa yata tarbiyya kina rusawa."

Hankalin Basma ya tashi har taji ta dan fara nadamar abinda tayi. Don bata san abin zai zama haka ba. Yau abban ta har cikin uwar daka saboda ita."? Shida da wuya ma ya shigo cikin gidan tun da can ma idan yazo ganinta."?

"Hmm, kada ka manta ba kai kayi min nakudar ta ba ehe kuma wallahi ka kara tabata sai sharia ta rabamu don baka isa ba ka nuna mini iko."

Bai tsaya komai ba saboda xuciya.. ya rufe Basma da duka tana ihu. Yana fad'in idan na karya ta sai naga naki matakin..wallahi Halima nayi nadamar haihuwa tare dake da kika haifa min abinda zai bujure min.

Basma cike da nadama take bashi hakuri tana kuma yayin da hajiya Halima ta kasa kwa kwatarta duk kurinta.. Don abban mahuci yasaka da ya gani a gefe sai da ya kakkarye sannan ya kyele ta. Lokacin Hajiya Halima ta fita waje neman dauki inda ta hadu da hajiya Salma suka ranks rankaya babu tsayawa ce-ce-ku-ce.

Huci yake yana ta sababi. _"Saboda baki dauke ni mahaifi ba kinfi son ki ta garari kina wayo a gari kina son ki lalace ko." Kina biye mata tana doraki kan hanyar banza. Wai har ke kinsan ki je gidan mutane kuyi musu cin mutunci don kawai dansu na sonki.? Cewa nayi miki Alhaji mukhtar sa,a nane ko itah matar tashi sa'ar uwarki ce."? Idan daraja da mutunci ne kin isa ku nuna musu."? Saboda ki nuna baki da tarbiyya yar mace ce ke koh"?_

_To Allah ya gani bada yawuna kuka je ba kuma mutunci na da kuka zubar na barku da Allah kuma illa kanki kikayi wa..._


Hajiya Salma ta dakatar dashi. Don Allah Alhaji kayi hakuri kada ka aibatata. Kayi hakuri kazo mu tafi tun farko bai dace kazo bama. Basma yarka ce ka dinga mata adduar shiriya ba fada ko aibatata ba.

Ya goge gumi ya juyo ya kallesu. Mataki daya zan dauka ko ta bini ko kuma idan bata bini gida yau ba to na rantse bazata kara taka min cikin gidana ba.

Aikuwa bazata bika ba. In yaso ka cireta cikin yayan naka sai me."?
Cewar Hajiya Halima kenan cikin fushi.

Zai tanka mata, matar shi ta tsaida shi. Sannan ta bige da rokon sa kan ya fito sun zo da mota. Don ita damuwar ta shine ya fito daga cikin gidan.

"Don Allah Alhaji kayi hakuri kajira mu a waje yanzu zamu fito da ita din."
Dakyar ya juya zai tafi yana hararar Hajiya Halima.

Itama hararar ta jefa masa kafin tace, "kasani baka daki banza ba don wallahi sai na dauki matakin sharia kan ci muni mutunci da kayi har gida.!!
Cikin kaushin murya shima ya maida mata martani.

Ki kaini kotun koli!! Kuma indai baki barta ta biyo ni ba kada ta kara kirana ubanta."
Fatima ce ta hau mishi magiya.
Don Allah Abba ka fito kayi hakuri.

Ya juya ya fita a dakin.
Ya bar Halima tana ihun sababi.

Hajiya Salma ta sunkuya tana wa Basma nasiha duk da har yanzu bata san abinda tayi ba.

Hajiya Halima ta janye ta tana magana cikin gadara. "Malama zoki bar gidan nan munafuka asirin da kikayi yayi saura ki jira nawa martanin.."
Hajiya Salma tayi murmurshi, "Hmm Halima kenan ke kika san asiri da kike ambatarsa amma kiyi wa kanki fada yarki macece.!!

Bata jira cewar ta ba itama ta juya saboda bata son tashin hankali. Tana cewa Basma, Kibi mahaifinki dai Basma don da uba ake ado sannan aure shine darajar mace.!!

Tanajiyo Halima tana zaginta amma sai tayi murmurshi kawai don bata da lokacin ta.


"Bayan fitar su Halima ta koma gun yarta tana rarrashi tare da kara hure mata kunne tana kara nuna mata ubanta ya tsane ta ne kawai don an rabasu da ita."


Basma taji nadamar abinda tayi amma tana tsoron bin mahaifinta. Don ta daku a wajen shi.


Amma dukan da yayi mata yayi tasiri matuka wajen shigar da ita hayyaci har ta fahimci tayi kuskure sannan kalaman shi sun tsorata ta.



Su hajiya Salma kuwa, sunje gida cike da hikima take shawo kan mijinta har ya dan sakko sannan ta nuna mishi illar zuwa gidan Halima sannan ta taushe shi kan ya dinga yiwa 'yartashi addua.

Sai daga baya ya sakko har ya sanar da ita a binda Halima ta aikata.
Hajiya Salma ta dade da mamakin abin daga karshe ta nuna mishi kada ya damu.


___________________________


Hajiya Rukayya ta zaunar da Nour sosai take tausar shi..ta karanta mishi abubuwan da take guje mishi akan auren macen da bata yi dashi da kuma illar auren mace mara tarbiyya da kuma yar mace. Ta bashi misalai da dalilai kala-kala sannan ta shiga nusar she shi abinda take gudu.

_Nour ni mahaifiyar ka ce, ko kana son ka auri mace n da zata rabani da kai.."? Ya kalleta ta jinjina kai. Tabbas bakasan son mace yana rufe idanu ba har a dinga hango laifin uwa imma ta hanyar kissa ko kuma ta asiri."? Mata da yawa sun rabamu maza da iyayen su. Ko kana son a dinga wulak'anta min kai ko yaushe ka zama baka da kwanciyar hankali."? Wallahi na tabbatar idan ka auri yarinyar nan sai kaji dama baka aure ta ba tunda har abin ya fara da haka._ "Ka tuna fa yadda babu kunyar ido na ko naka amma ta bude baki tace bata sonka haba nour ai so ba hauka bane.. nidai ina rokonka kuma ina baka hakuri don Allah ka cireta a zuciyarka badon bana sonta ba ko don na hana sunna, sai dai don a zauna lafiya kuma in sha Allah, zaka sami wacce ta fita kaji. Allah yayi maka albarka ya baka mace ta gari.

Amin mama inji Nour.

Don bata barshi ba sai da ya yaji ya cire kaso mafi yawa na son Basma daga zuciyar sa. Don yana matuk'ar son mahaifiyar shi idan ya tuno d'awainiyar da ta sha dashi yana k'arami. Don yasha jinya typhoid data sarke shi yana d'an shekara sha uku. Sai da yayi shekara daya yana fama. Babu wanda ya zaci zaiyi rai ma.
Ya saki jiki sosai kuma ya tabbatar wa da mahaifiyar tashi cewa ya bar abin.

Don haka lokacin Abban ya tuntubeshi da zancen yana fada mishi sunyi magana da mahaifin yarinyar yayi hakuri ya cigaba da shirye-shirye kada wannan abin ya dame shi.

Nour ya gyara zama yana zayyanowa mahaifin shi jawabi.

_"Abba dama bansa damuwa ba.. kuma abbah ni nama hak'ura na janye._ ya fada yana sosa kai.

Alhaji Mukhtar ya tareshi da fad'a. "Menene haka Nour."? Ita hajiya rukayyan ce tace maka ka yanje."?
Nour yayi saurin girgiza kai.
"A,a Abba kawai na hakura ne, zan nemi wata kawai."

Haba Noura so kake ka kunyata ni."?

Bayan munyi magana da mahaifin yarinyar nan ma kana so ka maidani karamin mutum kaima koh."?
Nour ya girgiza kai. A a Abba wallahi dama na hakura ne kawai bana so ayi mata dole."

Cikin fada Alhaji Mukhtar yace, "to a wanne dalilin zaka hakura da tunda kuke tare ka taba cewa baka so sai yanzu. To ma ai saika saka hankali a zancen. Ita yarinyar anya ba tilas ta ta akayi ko kuma zuga ba."? Don da bata ce bata so ba sai yanzu."?
Nour ya gyara zama ya zayyanowa mahaifin shi abinda ke faruwa tun asali kuma ya fada mishi cewa dama bata aminta dashi ba mahaifinta ne ya yanke mata hanzari yace ya turo amma dama bata son shi."


Alhaji Mukhtar ya yi jimm kafin ya samo abin cewa.
"Eh duk da haka dai kayi hakuri za'a san abinyi sannan ya dace kaje dai ku sasanta kai da ita don fasa aure fa ba karamin al'amari bane."

Nour yasan mahaifinshi don haka ya amince zai je. Kuma dama yana son yaje yaga Basma face-to-face don ya tabbatar mata shima dan halak ne.



Washe garin da yaje gidan su Basma yadda Abbanta ya tare shi yasa sai da yaji tausayin mutumin sannan Abban Basma da kanshi ya dinga bashi hakuri har Nour yaji kunya. Yana fad'in babu komai Abba.
A take Abban ya fad'a mishi cewa tana gidan mamanta.
Sannan ya roke shi. Don Allah kaje kaji Nour ka dinga hakuri da Basma.
Sannan yace ya jirashi.
Ya shiga ciki ya fito ya mik'a mishi wayoyin Basma gashi ka bata kaji. Amma da sharadi idan har ta yarda dakai kuma ta baka hakuri.
Nour ya karba da hannu biyu yana wa Abba bank wana. Abban sai albarka yake sa mishi yana ta kara bashi hakuri, tare da gode masa sosai. Nour ya nufi gidan cike da kwarin guiwa.

"Babu musu Basma ta fito da kace ana kiranta don bata zaci Nour bane tunaninta yafi bata Yusuf.

Sai da gabanta ya fadi da ta taganshi. Kuma yayi mata wani kwarjini na musamman.

Ta tsaya tana fuskantarshi. Ya k'are mata kallo duk zantukan mahaifiyar shi suka dawo mishi kunne, _babu abinda Basma zata nunawa sauran mata._
Zuciyar shi ta raya mishi wai ace wannan ce zata wulak'anta mishi mahaifiya, take yaji takaicinta ya kama shi.

Ita kuma wani tunani ne ya tsarga mata a zuciya.

_Tabbas Nour mai tsada ne kawai son xuciyarta da kuma yusuf yasa ta kasa fahimtar hakan, bayan haka ma gidan su da ta gani ta sha mamaki bata zaci sunkai haka ba._

A hankali ta fara lura da kallon kaskancin daya fara yi mata.

Ta bude baki zatayi mishi magana. Niyyar ta ta kira sunan shi. Amma ga mamakinta sai ya dakatar da ita.

Cike da izza yace.
Bana buk'atar magana Basma ina maman ku."?
Tayi mamakin maganar amma taji sanyi aranta zatonta wani abin ya kawo Nour.
Ta nuna mishi ciki.
Sannan ta mishi nuni da su shiga. Babu musu ya bita yana murmurshi.

Hajiya Halima bata gane Nour ba ita dai Idonta ya hango mata Basma da wani yaro wanda da alama yana cikin jin dadi kayan jikin shi sun bayyana haka, haka fatarshi.

Ya nemi kujera shima ya zauna. Amma hajiya Halima tayi mamakin yadda baiyi yunkurin gaida ta ba sam.

Basma kallon shi take sosai tana mamakin shi.

Hajiya Halima ta saki murmurshi ganin ya bude baki zaiyi magana, don tana mamakin yadda take mishi kallon sani. To kodai Yusuf ne.!!

Ya kalli Basma sannan ya kalli maman ya fara magana.

Am yadda kuka je gida kuma kuka sanar so nima nazo na sanar.
Ya kalli Basma ido cikin ido.
"Da ina sonki tabbas amma ni ma yanzu sam bana kaunar ki, don haka kamar yadda kikace idan na aureki xaayi Batacciya so bama zan aureki ba bare ayi haka.
Ina nufin na fasa aurenki but kudin na bar miki. Sannan ya ciro wayoyin a aljihun shi. Ya dire su ak'asa.

Wannan sakon abbanki ne yace na baki idan kin aminta da aure na amma ni babu buk'atar ki amince a gareni. Saboda haka gasunan."

Ya mik'e bai kara koda Kalma daya ba ya nemi hanyar fita.

Hajiya Halima ta kasa motsi.

Sai da ya iya fita sannan ta miko hannu kamar me neman abu. Bakinta kuma ya bude.
"Am dama wannan ne Nour din."

Basma bata iya bata amsa ba ta mike ta bishi cike da rashin sanin dalilinta ma na binshi, kawai dai taji ta babu nutsuwa. Bata taddashi ba sai ihu da kurar motar shi.


Kamar ta rusa ihu haka ta dawo gida. Hajiya Halima taji jugum babu bakin magana. Bata taba zaton yaron da gidan su sunkai haka ba. Bata jin Yusuf zai nuna mishi wani abu. Sai taji wani iri a jikinta itama amma sai ta nuna bata babu komai a ranta, tayi murmurshi ta

Please Login or Register in order to submit comment