Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya tare ta.
"Haba Sisi na, kiran ma baza,a amsa min ba."?
"Banji ba ne." ta fad'a murya a dashe.
"Nidai ayi hakuri idan ni na b'ata miki rai, dama abinci za,a taimaka min dashi."
Ya fad'a yana qare mata kallo.
Abin ya bata kunya, taji kunyar kanta, ta dan saki rai sannan tace, "Ciwon kai nakeyi."
"Ayya sannu kinsha magani."?
Ta girgiza kai.
'To kije kisha bari na zuba abincin da kaina."
Ta girgiza mishi kai, bata son ya dinga karantar k'osawar da tayi da shi don haka ta wuce kitchen.
Shi kuma ganin ya sami abinda yake so sai ya wuce d`akin shi.


Ranta ya qara b'aci bata son shiga d`akinshi sam, da yaran suna nan babu abinda zai hana ta basu su kai mishi. Amma babu yadda ta iya.
A bakin kofa ta tsaya. "Ga abincin."
Ta fad'a a qasan mak`oshi.
"Kiyi hakuri ki miqo min ciki."
"Shima yayo magana da ga cikin dakin.
Ta ajye abincin ko kallonshi bata yi ba, zata juya taji yace.
"Don Allah Hafsah, ki zo kiji."
Ta juyo ta tsaya tana kallon shi.
"Ki zauna mana please."
Ta dan d`osanu a Kujera.
Ya juyo gaba-d`aya Ya fuskanto ta.
Cikin marairaice murya ya fara magana.
"Jibi zamu shiga _camp_ Hafsah, gobe zan tafi in barku."
Shuru tayi tana, nazarin zancen, mene alfanun fad'ar kalmar nan."?
Tana tsakiya da mamaki taji yace.
"Zanyi kewar ku Hafsah.!!
Binshi da kallo tayi kawai.
"Baki da waya koh."?
Ta gaji da irin salon nashi me yake nufi, a irin wannan lokacin da take cikin halin k'ila wa k'ala, akan Yusuf, zai dinga zuwa mata da wani zance ?? don haka, ta had'e rai.
Ya lura da hakan, nan ya shiga tunani,
_"Ya dace, ya bar yarinya da wannan batun don da alama hankalinta ba akanshi yake ba kuma, akwai sauran yarinta a tattare da ita."_
_Zai barta zuwa wasu lokuta yaga idan akwai rabon shi._
Ya saki ajiyar zuciya, "Okey thank you, kije ciki na gode."
Ta miqe kamar akan qaya take.
_Ya bi bayanta da kallo yana kissima abubuwa da dama, ko dai ya hakura ne kawai.?_
To, babu yadda Fateema bata yi ba, don "Hafsah ta fada mata dawa tayi waya amma fir taki fad'a.
Don haka ta rabu da ita, sai kawai tayi saving number, da Hafsan ta kira.
Daren Hafsah, cike da mafarke-mafarken Yusuf da Basma mara sa dad`in bada labari, haka ta wayi gari da alwashin sai taje inda Basma ta fad'a mata don a banbance tsaba da tsakuwa tsanin ita da ita.

Da sassafe, Nazeer ya gama shiri tsab, ya fito da jakarshi sab'e zai musu sallama, dakin Mamanshi ya fara shiga ta dad'e tana yi mishi addu,ar samun nasara da tsarin ubangiji..
"Amin mama Nagode." haka yake ta fad'a.
Suka fito shida mama zuwa palour, yaran duk suna nan dake Lahdi ce, mama ta qare musu kallo babu Hafsah aciki, "Fateema jeki kira Hafsah suyi sallama.
Yaji dad`in hakan sosai.
Tare suka dawo da Fateeman.
Ta saki fara,a kuma. "Har da cewa yaya tafiyar ce."?
Shiko abin nema ya samu, murmushi yayi mata. "Eh mun fito sai Allah ya dawo damu, kwana biyu kema ki huta da zubamini-zuba-mini."
Dariya, sukayi musu, mama nacewa, "Ah toh, ashe dai ka sani."
Har habar gidan aka fita raka shi, Hafsah taga bata da zab'i sai illa itama ta bisun. Don haka tabi bayansu.
Kallonta yake sosai, kallon da kowa yaso lura dashi. Kallon da Hafsah ta kasa fassara shi. Daga bi sa-ni ya d`auke idonshi yana da murmushi had`i da daga musu hannu bye-bye."
Yace musu. Driver yaja, suka dawo ciki anata hirar kewa.!
Kusan Yinin ranar Hafsah a d`aki tayi shi, tanata kissima abubuwa da dama a ranta.
_Tabbas sai taje ga Basma. Dole taje ta nuna mata, shuru shuru ba wasa bane, kuma dole ta nuna mata cewa tabbas tayi kafuwar da ita bazata tab'a yi ba har abada a zuciyar Yusuf._
Mama bata takura mata da tambayoyi ba yau, tun bayan da ta tambayi Fateema _"Ko akwai bayani.?_ fateema tace mata babu, amma kuma a bisa dole, ta labarta mata batun wayar da, Hafsah tayi a jiya.
"Ki dinga kaffa-kaffa da wayarki kema, sannan sai kin qara qaimi, kinsa dabara ko in koya miki dabarun."?
Fateema tayi dariya "Aa, ki bari mama, zan iya."
"Yawwa, ko kefa."?
Tun da rana mama ta zubawa duk wani motsin Hafsah ido, tana gani tayi wanka da la,asar ta shirya cikin kaya masu kyau, shirin dai yafi kama da na wanda zai fita.
Bata tanka, mata ba, amma a zuciyar ta ta kissima, _"Kada dai ace yarinyar nan wani ta jawo min gidan nan._
K'arfe 5:30pm, Hafsah nata kallon agogo, ji take kamar akan qaya take, gashi mama ta kasa ta tsare a parlour.
''Oh my God.!! Take ta fad'a a zuciyarta hira kawai ake, amma sam ba fahimta Hafsah take ba, hankalinta na can wani guri, zuciyar ta na raya mata abubuwa da dama bata so, Basma ta ce _tsoro taji_ shiyasa ta qi zuwa.
Ana hada wayar mama tayi qara, ta d'auka ta fara waya, sai kuma tayi d'akinta.
Damar da Hafsah ta samu kenan ta, wuce daki cikin hanzari Fateema na kwance ta ganta, da azama kafin tayi magana ta d`auki jakarta da mayafinta ta fice.
A parlour, sai su Al,ameen da Nour, ta kakkkalle su kawai ta fice.
Yaya Hafsah ina zaki."?
Inji Al,amin.
Abinda mama taji kamar kunnen ta ya jiyo mata take ta yanke wayar. Itako Hafsah, ai jin yaran sunyi magana tuni ta qara da gudu-gudu har ta isa gate ta bude kofa ta fice."
Fitowar mama kenan taci karo da Fateema ita ma.
Maman ta fara magana kenan tana tambayar yaran "Ku Hafsah ce ta...
Kafin ta Ida tambayar su taji fateema na cewa "Mama aiken Hafsah kikayi."?
Cikin rud'ewa mama, ta qarasa tambayar, "Nace muku Hafsah ce ta fita."?
"Har sun dan fara rud'ewa, suna in'ina, "A,eh" fita tayi, muma bamu san ina ta tafi ba."
Mama ta tafa hannaye tana salati, yarinya zata ja mata masifa, ubanta ya amince ya bata ita amma kuma tayi mata haka, du-du-du, ko sati bata cikasa a gidan ba.
Da azama mama ta figi mayafinta, fateema ta bita cike da rud'u.
Me yake faruwa da Hafsah ne, gaskiya bata san halin mamansu ba da bazata dinga, irin haka ba. Da ace ita ce, ai kashinta ya bushe..."
_Har rige-rigen fita suke ita da mama, kuma babu wanda yacewa wani uffan, to ina ma suka ga lokacin magana."??....._


📝
*HAJEEYAH KHAREEMERH*

♥️♥️♥️♥️
*ZAZZAFAN SO*
(masoyin k'warai )
*Cigaban littafin Zazzafan so*
*(Guba ne)*
💔💔

*By:*
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah khareemerh)*
*Dedicated to Unique in your love heart group member*




📄 *42*


*Acan* wajen qarshen layinsu suka hango ta tana qoqarin tsare napep.
"Ki bita da sauri mana."
Mama ta fad'a da fad'a-fad'a.
"Gudu gudu, sauri sauri Fateema keyi tana, kwalawa Hafsah kira.
Ai kuwa ta jiyo kamar ana kiranta sai ta juyo.
"Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un.
Shine abinda Hafsah ta shiga furtawa ganin mama na nufo ta, yau ta kad'e, ina zata kai kunyar mama."?
Allah yaso Nazeer baya nan da yaya zatayi, da kunyar shi."??
Bata bi takan me napep d`in ba ta juyo, suka had'u da Fateema, ta riqe hannun Hafsah jikinta duk yayi sanyi.
Ina zaki je Hafsah."?
Bata da bakin magana sai jikin ta dake yin rawa, tsabar tsoro m, lallai tayi ganganci da rashin tunani.
Suna qarasowa daf da Mama, takaici yaja maman ta daga hannu ta wanke ta da mari.
"Yau na tabbatar da cewa baki da mutunci yarinyar nan, shiyasa Amiina take cewa, kina neman fin qarfinta.!!"
Ta talle qeyar ta, ta tusa su gaba ita da fateema wuce muje gida ki fad'a min gidan uban wa zaki tafi."
Dukkansu sauri suke kamar zasu tashi sama, sai gasu cikin abinda baifi minti d'aya ba har sun iso gidan.
Kiii, mama taja Hafsah sai d'akinta.
"Nema kike ki wulaqanta ni koh, shiyasa zaki fita bada izini na ba koh."?
"Kuka kawai Hafsah keyi kukan nadama, da Kukan rashi.
Ki rufe min baki ko in tattaka ki anan, kuma idan baki fad`amin inda kikayi niyyar zuwa ba, sai naci mutuncinki a gidan nan.
"Idan kuma don in maida ki gida, kikai min haka ina mai tabbatar miki babu inda zaki, idan nace kin dawo nan babu wanda zan hana ni hakan..."
Takaici ya tuqe mama ta dafe kunci tayi shuru.
Tabbas yarinyar ta bata mamaki, ya akayi ta zama haka ne, yarinyar da aka santa da nutsuwa da ladabi da biyayya, amma gaba-d`aya ta chanja.
Kaii idan ka biyewa yaran yanzu sai ka b'ige da hakan jini ko ciwon zuciya.
Shirun Maman, ya tsorata Hafsah, tabbas an kai ta bango, shiyasa ta rasa abin cewa.
Tsanar Basma ta nunku a zuciyar Hafsah ninkin ba ninkin.
_Ba don ita ba babu abinda zai dinga kawo mata sabani da iyayenta haka._
Tayi mata Allah ya isa tafi dubu zuciyarta. Take hawaye suka fara zarya a kuncinta.
Mama ta riqe haba da takaici, kafin ta miqe zumbur, ta kaiwa Hafsah wani mugun bugu da takaici, Allah yaso ta kauce.
"Ni banyi kuka ba sai ke."? Saboda kin raina ni, zaki dinga kuka.? Me nayi miki.."? Tsabar sharri koh, dama haka kike ban sani ba, dama haka kike yiwa Aminan..?
Gaskiya kin cuci kanki kam, baki yiwa kanki adalci ba..
Cikin kuka ta fara bada hak'uri "Don Allah mama kiyi haquri, don Allah.."
Wallahi bazan qara fita ba, kiyi hakuri na daina don Allah kiyi hak'uri.
"Hum, Haquri ai ke ya kama 'yannan, wacce irin rayuwa kike son ki fara,? Duk qoqarin da ake yi akanki bakya gani koh."?
"Wallahi bazan qara ba don Allah Mama kiyi hak'uri."
Ta rage sautin muryar ta, "To ina kika fita zaki je."?
Cikin shashsheqar kuka tace, gidansu qawata."
"Gidan su kawar ki."? Mama ta maimaita da sigar tambaya.
"To me zaki je yi."
Dif wuta ta d'aukewa Hafsah, sai jan majina da take yi.
"Ba tambayar ki nayi ba."
Shuru, ina ne gidan."?
"Gadon k'aya ne.!!
Hmm, ai kin koyi qarya kam, to ki sani ko zaki kwana kina rantsuwa na daina yadda da abinda zaki fad'a kuma dole ne ki fada min inda kika fita zaki je a yau d`innan, idan ba haka ba zan d`auki munanan matakai akanki, ciki harda sanarwa da Abbanki, abinda kikai."
Da sauri, Hafsah ta waro idanuwa, ita dai ta shiga uku, Yusuf da Basma na neman saka ta a bala'in da babu ranar fita daga cikin sa.
Cikin wasu zafafan hawaye ta durqusa bisa guiwowinta, abin gwanin tausayi, ta had'e hannayenta, tana rokon ta, "Don mama kiyi haquri kada ki fad'awa Abba, wallahi na rantse miki bazan sake ba, wallah bazan kuma yin irin haka ba."
Tausayi ta bawa Mama, don haka tace cikin had'e gira, idan haka ne toh ki fad`amin inda kika yi niyyar tafiya."
Wasu sabbin hawayen suka fara bin kuncinta banda nada, _"Indai zata labartawa mama inada tayi niyyar zuwa, yana nufin fa, sai ta fad'a mata tsakaninta da bamsa da yusuf, kuma dole hakan yakai ga sanin mama akan abinda idon Hafsan ya gane mata a gidan su Yusuf."_
Bazata iya ba.. Sam bazata iya fad'awa mama wannan zancen ba a matsayinta na yayar mahaifiyarta.
"Kinga koh.. Inba rashin gaskiya ba, me yake sakaki kuka idan aka kamaki da laifi irin wannan."
Maganar mama kenan wacce ta katsewa Hafsah tunani.
"Gi..gidan su qawata zanje wa walima."
"Walima kuma yaushe aka gayyace ki ban sani ba."?
Mama tayi mata zancen bawai don ta yarda da abinda ta fad'a d`in ba.
"Um.. tun ina gida ta kawo min katin.."
"Hmm.. Koh."? Inji mama tana tab'e baki.
Hafsah ta ja baki ta tsuke, tasan zancen bai karb'u ba sam.
"To ina ne wajen."?
"Gadon k'aya."
Hmm, saboda ban isa ba, ke kike iko da kanki shiyasa kika fice a sace koh."?
Bata da amsa illa shuru.

_"K`al!!_ mama tayi kwafa, ban yarda da wananna qaryar ba.
Ta nuna ta da yatsa, Tabbas sai kin fad`amin dalilin fitarki, kafin na d`auki mataki akanki. Sannan zaman gidan nan yanzu kika fara shi.
Maman ta dakata saboda kiran sallar magriba da aka fara yi, tana tuno yadda kusan kullum sai Amina (Maman Hafsah) ta kirata akan Hafsah, ta lura har yanzu hankalinta ya gaza kwanciya.
"Don Allah yaya ki taimaka ki saita yarinyar nan, wallah mahaifinta ma cikin damuwa yake, don ma kece shiyasa ya kwantar da hankali amma da babu yadda za,a ya barta taje wani waje a halin da ake ciki."
Ire-iren kalaman da take mata kenan kullum idan ta kirata.
"Kije kiyi sallah, sannan ki dawo nan bamu gama magana ba.
Ai kamar an sauke wa Hafsah wani abu mai nauyi daga kanta haka taji, ta gaji da wannan titsiyan na maman ya Nazeer, amma ko ma menene ita ta jawa kanta.
Tana shiga d'akin ta fad'a gado, minti kadan sai ga fateema daga toilet, tayo alwala. Ta d'an tsaya ta qareway Hafsah kallo kafin ta d`auki hijabi tasa ta tayar da sallah.
Hafsah kuwa kunyar Fateemah takeji, bata so tayiwa mahaifiyarta laifi irin wannan ba.
Sai da ta idar sannan ta hawo kan gadon, har lokacin Hafsah na kife, Akan cikin ta tayi rub-da-ciki, ta kwanta akan hannayenta ta rufe idanuwanta dasu, da alama kuka take.
Zama Fateema tayi sosai, akan gadon tana fuskantar Hafsah kafin ta fara magana, babu ruwanta da rashin d`agowar Hafsan don tana da yak'inin tana jinta.
"Hafsah, Allah ya gani badon wai cewa Mama mahaifiyata bace, kuma badon kinzo gidanmu bane zan fad'a miki haka, amma ke 'yar uwata ce, dole na fad'a miki gaskiya.. Tayi shuru, sannan ta cigaba.
_"Ban so kika yiwa Mama irin wannan laifin ba a yadda take daukar ki mai hankali.. Hafsah Ke ba yarinya bace, kuma ba ke kadai kike rayuwa ba, kina da 'yan uwa.. Meyasa idan kin shiga damuwa bazaki iya fad'a ba idan ba zaki iya fad'awa mama ba sai ki fad`amin in baki shawara, amma mene ne amfanin abinda kikayi."?
"Kin d'aukar min waya, kinyi kira, kuma kinki fad`amin wacce kika kira, sannan kina kuka na tambayeki dalili kinki fad`a, gashi yanzu kin yiwa mama laifi.. Ya kike so muyi miki.. Ko mune muke takura miki.."?
Fateema ta qarashe zancen da murya mai bayyana tsakanin damuwa.
Duk zancen da take, Hafsah bata d'ago ba, amma kuma tabbas zancen Fateema ya shige ta. Idan ba gaskiya zata k'i ba, to kuwa tabbas tasan gaskiyar kenan aka fad`ami mata.
Ta tsagaita da kukanta tana tuhumar kanta..
_Tun farkon da aka fara abin nan babu shawarar wanda ta nema, babu wanda ta sanarwa idan ba aysha ba, itama ta bata shawarar da tayi watsi da Yusuf d`in da Basmar duka, amma tak`i jin zancen ta, sai ita da kanta take yanke wa kanta hukunci._

Jin tayi shuru, kuma babu alamun zatayi magana yasa Fateema, ta kuma cewa, _"Na fad'a miki ne a matsayinki na 'yar uwata amma idan kinga magana ta ta b'ata miki rai toh Allah ya baki hak'uri."_ Tana gama fad'ar ta miqe zata tashi tabar kan gadon, a nufinta ma ta bar dakin gaba-d`aya, amma sai taji Hafsah ta riqo ta gam.
Ta miqe ta zauna itama, fuskarta jajir, cikin dashewar murya ta fara magana.
"Nagode, Fateema, nagode, kiyi haquri, da abinda na yiwa mamanki, na sani nayi mata badaidai ba, don Allah ki bata hak'uri... Hawaye suka fara bin kuncinta. Ta cigaba da magana, Fateema, abinda akayi min ne bazai fad'u ba a baki, bazan iya sake labarta shi ba, don, idan zan fad'a ji nake kamar a yanzu abin yake faruwa... Fateema anci amanata, ancuce ni, an yaudare ni, an raina min hankali.. Na amince anci amana ta, anyi min snatchin mafi muni..!!.Kuka yaci K'arfinta ta kifa, kanta akan cinyar fateema, yayin da Fateema tayi shuru, itama zuciyarta tayi rauni, kome akaiwa Hafsah to tabbas bashi da dad`in ji, tun da tayi haka.
Dukan bayanta ta shiga yi tana bata hak'uri, tana rarrashinta akan ta fad'a mata abinda akayi mata, in sha Allah zata bata mafita.
Da kyar, ta samu ta shawo kan Hafsah, har ta fara magana kamar haka: _"Fateemah wacce kika ga na kira qawata ce, tun a makarantar boko, da ita nake shawara akan komai, ita take bani shawara akan saurayi na, na yarda da ita sosai......_

_Nan Hafsah ta bawa fateema labarin komai tun daga farkon had'uwar ta da Yusuf, da irin shawararin da Basma ta dinga bata, da yadda Basman ta fara shigewa yusuf har zuwa birthday d`in Basma, da abinda Aysha D'aheer ta nuna mata a waya, zuwansu gidan su, yusuf, abinda suka gani da idonsu, har zuwa jiya da Hafsah ta kira basma a waya, kawo fitarta ta yau.._
Rashin sanin, abin cewa, da d'aurewar kai, yasa, fateema zubar hawaye, gaskiya abin ya tab'a zuciyarta..
Bubuga bayan Hafsah kawai take yi alamun rarrashi...


Sai kawai, sukaji an turo kofar, mama ce ta shigo, babu mamaki idan aka ce taji duk abinda Hafsah ta fad'awa Fateema, don basu san dad'ewarta ba, ajikin k'ofar ta zo, ne da niyyar kiran Hafsah, don su d'ora daga inda suka tsaya, a tuhumar da maman ke yi mata, sai kuma taji Hafsah nayin magana, nan ta dakata taji komai, ita kanta abun ya shigeta, _Tabbas qawaye suna iya chanjawa 'yarka tarbiyya cikin kankanin lokaci._
Amma sai ta shigo kamar bataji komai ba, tayi wa Hafsah nuni data biyo ta, _Hafsah ta miqe ta fi maman suka wuce, d'akin ta, fatanta Allah yasa, maman bataji koda kalma d'aya cikin abinda ta labartawa Fateema ba..._
📝



*HAJEEYAH*
*KHAREEMERH.*
♥️♥️♥️♥️
*ZAZZAFAN SO*
(Masoyin k'warai)
*Cigaban littafin Zazzafan so (Guba ne)*
💔💔
*By*
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah Khareemerh)*
*Dedicated to unique in your love heart*



📄 *43*




*"Kinyi sallar"?*
Kalmomin da mama ta fara da su kenan, daga isar su d'akinta.
Ahankali Hafsah ta girgiza kai..
"To me kika tsaya yi."?
"Babu komai."
Tayi mata nuni da toilet d'inta dake cikin d'akin, "shiga nan kiyi."
Ta wuce da sauri, babu b'ata lokaci tayo alwalar ta dawo ta tada sallah.
Bayan ta idar, har zuwa lokacin cin abinci, har zuwa lokacin bacci, mama bata k'ara yi mata tambaya mai kama da tuhuma, ko neman k'arin bayani akan fitar da tayi ba.
Ta tsammaci haka, a lokuta da dama, ko kwakwkwaran motsi maman tayi, sai Hafsah ta tsargu.
Amma maman sam ta share zancen. Hafsah kam ta zargi abubuwa da dama acikin zuciyarta, a hankali ta d'an saki jiki daga zaman d`ar-d`ar d`in da take da maman, ga kunyar marin da maman tayi mata ta lullub'eta. Ya akayi tayi kuskuren yi mata laifin da har ta iya kai hannu jikinta.? Tana matuqar nadamar yin laifin, da ta sani tayi mata koda k'aryar zuwa wani waje ce, duk da dai koma menene ya riga da ya faru, gashi tsoron had'a idonta da na maman take ko magana take mata kanta a k'asa, don wani kwarjini na musamman maman ta kara a idon hafsan, tun bayan ta tasha yatsunta biyar.
"Dakina zaki kwana Hafsah."
Maman ta fad'a lokacin da fateema ke shirin barin parlour don zuwa bacci, Hafsah ma ta mik`e da niyyar binta.
A sanyaye ta dawo da alama bataji dadin hakan ba.
"Ki je ki dakko duk wani abinda zaki buk'ata."
Mama ta sake kallonta ta fada mata haka.
Da sauri ta mik`e ta fice.
Tana isa dak'in ta tarar Fateema na kad'e zanin gado, ( _bed sheet_ ) taji shigowar mutum don haka ta ta waigo.
Ta saki murmushi, Aike Hafsah kin zama 'yar dakin mama.)
"Allah Fateema kunyar mama nakeji."
"Hmm, Hafsah kenan Allah baki da matsala fa, rashin sani ne ya sakaki yanke hukunci da kanki, amma mama sam bata da matsala, kinga ko ni da ni da nake matsayin 'yarta wallahi bana boye mata komai akan al,amran samari na."
Hafsah tayi ajiyar zuciya, "Ya zanyi in fara tunkarar mama da irin wannan zantukan shirmen.."? Ta girgiza kai, "Bazan iya ba.!!
"Hmm, shikenan."
Cewar Fateema.
Hafsah ta chanja kayanta zuwa na bacci, sannan ta d`auki blanket, "Sai da safenki!!
Ta fad'awa Fateema, sannan ta fice. Fateema ta bita da kallo tana murmushi, tabbas tana da yak`inin cewa mama ba zata tab'a barin Hafsah ta shiga garari ba, don ta tabbatar maman taji hirar su kaf, daga ganin yanayinta.
"Ki kwanta a kan gado, ni ba kullum nake kwanan gado ba."
Maman tacewa Hafsah, bayan ta shigo, tana kan dardumarta tana jan carbi.
Ta d'ora, "Amma kiyo alwala tukuna, sannan kiyi addu,a."
Hafsah ta daga kai alamar "Toh."
Salin-alin Hafsah tayi baccinta, kuma taji dad`i da ba gefen mama ta kwanta ba, ji tayi ma kamar ba ayi mata chanjin wajen kwana ba.
Da asuba mama ta tashe ta, sannan ta fita tashin sauran yaran.
Bata barta ta koma bacci ba, _"Zauna yau kema kiyi lazimi."_ haka ta fada mata. Sai da rana ta b'ullo lokacin kuma maman ta gama shirinta na fita office, "Tunda ba zaki karya yanzu ba, sai ki kwanta, maybe karfe 2:00pm, ma ni na dawo, sannan asabe ( _tana nufin me aikinta_ ) zata zo, sai kuyi aikin tare kiyi mana abincin rana."
"To, mama me za,a dafa."? Inji Hafsah cikin ladabi.
Cikin murmushi tace, "Kin iya tuwo."?
Hafsa tayi murmushi itama tana d'aga kai.
"To kiyi mana shi, miyar agushi kuma saura naga bai tuk'u ba." Maman tayi maganar da sigar zolaya.
Sannan ta cigaba da cewa, "ki duba akwai komai cikin kitchen d'in, da kwai nama a fridge."
"To mama."
Suka fito palour tare.. Lokacin duk yaran sun Ida shiryawa har da Fateema. "Yawwa kuyi sauri tare duk zamu fita tun da kunga Nazeer baya nan bare ya kaiku." _Mama ta fada musu haka._
Kamar kuma tayi mantuwa sai, tayi sauri, ta koma d'akinta tare da kwalowa Hafsah kira.
Tana shigowa ta durqusa "mama gani, maman na tsaye bata zauna ba, tayi mata nuni, "Tashi tashi sauri nake."
Tana ida mik'ewa ta nuna ta da yatsa.
"Kada ki ga sai ke kad'ai a gida, kiyi tunanin, fita koda bakin gate ne, zan fad'awa mai gadi ma, kuma muddin kikayi attempting fita zaki gamu da fushi na.!!
Babu alamun wasa a fuskar maman tayi mata wannan maganar.
Daga kai kawai Hafsah, ke faman yi alamar, "Toh."
Azuciyarta, tana cewa, ( _"wane Tsautsayin ne zai qara fitar dani.!!_)
Sai na dawo, maman ta fad`a da murmushi kamar ba ita tayi wannan maganar yanzu ba.
"Adawo lafiya."
"Allah yasa, Maza ayi bacci, bye."
Ta fita tana daga mata hannu. Hafsah taji wata 'yar dariya tazo mata, ko ta mecece oho, ta fada kan gadon tayi shuru har bacci ya d`auke ta.
Sai wajen, sha d'aya, ta farka, ta nemi abu mai sauk'i tayi break dashi lokacin kuma, me aikin har, taci rabin wanke-wanke.
Hafsah tayi wanka sannan ta, fara shirin dora girkin, suna yi suna hira ita da me aikin, wacce bazata wuce shekaru 35 ba, tana da 'ya'ya uku da mijinta ya rasu ya bar mata. Duk a hirar su ne take fad'awa Hafsah.
Hafsah ta k'ara godewa Allah, a zuciyarta tana cewa, _"Gaskiya akwai masu buqatar taimako a duniyar nan!_
Sanda mama ta dawo, fara,arta ta zarce ta safiya, musamman da taga an gama komai gidan tsaf, kamar babu abinda ya faru, sai zolayar Hafsah ta take, "Toh zubo min Tuwon naki mana, nayi testing, ice ko babu hannun asabe a girkin."?
Suna dariya asabe tace, "Ita tayi abinta wallah, ai d'iyar taki ba daga nan ba, nima nace 'ko training d`in aure aka kawota ta d'auka.? Mama tayi murmushi kawai, Hafsah tabar gurin da sauri da alama taji kunya."!



Wasa wasa har kwana hud`u, da alama ma mama ta manta Hafsah tayi wani laifi.( _A ganin Hafsan don ganin yadda maman ke janta a jiki fiye da koyaushe_)
Tunda, Nazeer ya tafi taji gidan ya k'ara yi mata dad'i, jiya ne ma daya kira Fateema, suna waya yace ta bawa Hafsan, babu yadda zatayi haka ta karba suka gaisa.
Da yammacin ranar Juma,a tana taya mama gyaran drawer, sai ga ledar da Yusuf ya bata, dam, gabanta ya fadi tare dajin wani farin ciki ya mamaye zuciyarta, gaskiya tana cikin tsananin kewa, in ba don idon maman yakai kai ba, da babu abinda zai hanata da fe abarta ta b'oye.
Maman ta fi ta hanzari wajen sunkuyawa ta dakko ledar, ta lura sosai da yanayin Hafsan."
"In ba don Laifin da kikayi min ba ai da tuni na baki abubuwan ki ai."
'Inji mama, tana so ne ta shigar da Hafsah hayyacin ta, ta dinga gane abubuwan da suke rufe mata ido suna kaita ne kawai suna baro ta babu wani riba.
_Don a kasan zuciyarta ko hafsah batayi mata wanna laifin ba, bata da niyyar bata wayar yanzu, don bata ga amfanin hakan ba._
Hafsah ta langab'ar da kai kawai, tana bawa kanta laifi.
Hakan ya bawa mama damar cigaba da magana, tabar wancen zancen ta kamo wani, don ta samu ta aika sak'oninta ga Hafsah.
"Hafsah.!!
Ta kira sunan Hafsah a hankali,
Cikin sanyi ta amsa itama.
Kuna zuwa islamiyya koh, Hafsah ta jinjina kai,
"Yawwa." inji mama.
Kinsan shikashikan musulinci koh"?
Hafsah ta k'ara jinjina kai, har yanzu da mamakin tambayoyin a fuskar ta.
"To fad'a min su."
Ta d`anyi shuru sai kuma ta tuna kada mama ta zaci ko bata sani bane, yasa ta shuru. Don Allah a hankali ta fara zayyyano su.
Tana gamawa mama tace _"To saura na imami."_
Hafsah ta fad'o su guda shiddan nan, tanayi tana kallon mama, so take taji dalilin tambayoyin.
Yawwa, 'ya ta."
Ashe dai baki manta karatun islamiyyar ba.
( _zuwa yanzu sun kammala gyaran,

Please Login or Register in order to submit comment