Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aure yana sa a dinga ganin k'imar mutum ta musammaman.'
'Ya kalleshi,
"To yanzu idan na fahimta wata tawaya ce kenan saboda bani da aure koh."?
"A,a mai gida, kawai shi aure yana cika darajar mutum ne."
"Yai murmushi, sannan ya gimtse, sannan yace,
"Bana son wulak'anci ne irin na mata."
"Alhaji ai ba kalar ku ake wukak'antawa ba gaskiya.'
"Hmm, haka kace, amma kada in maka shishshigi da sai ince, tsakaninka da Allah matar ka bata maka wulak'anci."?
"Kasan ni shine abinda na tsana a gurin mace."
'Ya fad'a yana yatsina fuska.'
"Eh to, wallahi mai gida batayi gata da sanin yakamata, ga tsafta, sai dai kawai kasan mata ba,a rabasu da jan aji wani lokacin."
"Yai murmushi sannan ya jingina jikin kujerar motar,
'Jin daga an tab'o matar shi ya fara zuba.'
"Ahankali yace Allah sarki, tunda haka ne, in sha Allah nima zanyi k'okari ko dan farin cikin su Abba.'
'Driver ya ce "Toh Allah ya zab'a ta gari, mai gida."
"Ami'n"
'Dai dai lokacin sunzo wajen wani store mai kyau, yayi mishi alamar da yayi parking a wajen.'
'Sai da suka tsaya, sannan ya kalle shi,
"Muje kad'an sama mata kayan gayu, madam d'in taka tunda kace 'yar gayu ce, sai ka had'a harda na jaririn koh? "
'Driver ya hau fara,a "Godiya nake alhaji."
"Tare suka shiga, kantin.'
'Kaya ake siyar wa na madaidaitan kud'i, amma sai kyau."
B'angaren atamfofi ya zab'ar mata uku masu kyau, amma ya mishi alamar daya k'ara, ya dad'a guda biyu saboda kada ya zak'e da yawa, babu abinda bai sashi ya d'aukar mata ba tun daga kan mayafai takalma, sark'oki da turare, da sauransu.'
'Sai kuma kayan Baby, sai takalman yara da yace ya d'aukarwa ya'yan nashi.'
'Shidai Najib har kasa godiya yayi, yasan kawai Allah ne yayi mishi katari, ayau d'in, don yana shirin fitowa ya nufi gida, Ukashan ya kirashi, kira yake kawai,
"Allah ya k'ara arziki, yasa a gama lafiya, Allah ya k'arawa alhaji nisan kwana."
"Ami'n yake cewa shi dai,
'Ya mik'a katinshi aka zara wajen dubu abba'in da wani abin.'
abinka da kud'in yanzu ba wuya kiji sun taru akan k'aramar siyayya bare kuma siyayya irin wannan.'
'Sai da suka fito yace mishi, to adinga taya mu da addu,a muma, Allah ya bamu nagari."
"Ami'n Ami'n, mai gida addu,a dama kullum muna saka ku a cikinta."
"Sun isa gida, ya sauke shi, sannan ya deb'e kayan shi ya nufi gida cike da jin dad'in yadda matarshi zatayi farin ciki da kayan, saboda yana yabonta sosai.'
"Ukasha kuwa, yana shiga cikin gidan yaji wata masifaffiyar yunwa, nan ya tuna rabonshi da abinci tun safe, lokaci guda kuma ya tuno da wannan Yarinyar ta d'azu a wajen biki, take yaji wata mummunar fad'uwar gaba, daya tuna bai ma san yaushe tabar wajen ba."
"A shagwaba irin tashi ne, ya nufi d'akin k'anwarshi yana buga mata k'ofa, saboda sanyi ne duk sunyi bacci, shiyasa ma bai nufi d'akin hajiyar tashi ba.
"Ita kam Fadwa, yasan ba bacci take ba, fadwa please ki fito mana.'
"Ta ajye wayar ta gefe, sannan ta mik'e ta zare key sanan ta fito,
"Kinyi bacci ne?
"No, ta girgiza kai."
Ok plz ki had'amin abinda zan iya ci yanzu yunwa nakeji kinji."
"Ta gyad'a kai kawai, saboda tasan halin yayan nata da rigima bama tasan me zata dafa mishi ba, kuma may be idan ta tambayeshi yace ya fasa, ko ya zaci ya takura mata ne.'
"Ta nufi kitchen, ta duba taga da miya sai kawai ta, d'ora d'an ruwa ta dafa mishi taliya, sannan ta zuba ruwan tea madaidaici tasa mishi kayan k'amshi, ta juye a plask, amma saboda ta tsokane shi sai ta d'auki iya abincin kawai, ta nufi d'akin shi dashi.'
'Ta tarar ya idar da sallah, ta ajye mishi tana cewa bross, gashi toh."
'Ya d'aga mata hannu alamar godiya, sannan bayan ya shafa addu,ar ya kalleta,
"To ina coffee d'in kuma."?
"Tayi murmushi, kamar yace ta mishi da coffee, sai kawai tace,
"Ai bakace min da coffee ba."
"Yazanyi in iya cin abinci babu coffee kin sani, amma shine zaki k'i had'a min"?
"To bari in samo maka."
"No ki barshi ai kinsan ina so, baki had'o min dashi ba, so kije ki huta kawai thank you, kinji."
'Tayi murmushi, wai shi dole sai ya nuna mata baiyi fushi ba kenan, bayan tasan wannan zai iya zama sanadin k'in cin abincin nashi ma gaba d'aya.'
'Zata yabeshi bashi da matsala a komai, amma a b'angaren nan, sai matarshi ta fahimce shi, idan ba haka ba zasu dinga samun matsala, saboda, shi mutum ne dayake son kawai ki fahimci abubuwan da yake so, da wanda baya so, idan ya nuna miki al,adar shice yin abu to ki rik'e ba sai kullum ya maimaita miki ba.' saboda bashi
da son yawan maimaita abu.'
'Shiyasa take mishi fatan ya samu mace, mai lura sosai, saboda banda wannan bashi da wata matsala shi dai.'
"Am yaya na fa had'a maka d'akko maka kawai zanyi.'
'Ya jawo hannunta sannan ya rankwasheta,
"Kin maidani abokin wasanki koh,? saboda muna level da'ya ni da ke koh"?
yana nufin,πŸ‘‡πŸΌ
(Duk basu da aure)
"Ougsh,! Yaya da zafi."
Ya sake ta,
"Maza hurry up ki d'akko min yunwa nakeji"."
"Ok bros, tayi saurin kawo mishi had'e da cup da d'an plate ak'asan cup d'in.'
"Thank you, sai da safe, kuma, gobe ki fad'a ma su Maryam zaku je dinner d'in bikin nan, coz yana min k'orafin baku je yau yau ba.'
"Okey yaya saura kai, dama ku biyu kuka rage"
Ta fad'a tana Mik'ewa zata gudu.'
'Ya jefa mata key d'in shi, ta fita tana mishi dariya.'
'Ahankali yake dan shan tea d'in, sai yaji gaba d'aya ya manta da damuwarshi ta d'azu, sai kuma wata sabuwa tunanin yarinyar nan dake damun zuciyar shi, abin ya fara damunshi dak'yar ya iya cin abincin kad'an, duk kuma fargarbar yadda zasu k'ara had'uwa yake.'..
'Abin ya dinga bashi mamaki, sai yake tunanin kodai yarfa sun da tayi ne, yake jin haushin hakan"?
'To ai kuma shi baiji ko da d'igon haushin ta ba cikin ranshi, hasalima wani abu yake ji na mussamman game da ita, ji yake kamar ya mik'e ya tafi nemanta.'
'Ya dafe kanshi yana tunanin wannan wane sabon abu ne ke shirin samunshi..??
πŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌ



*πŸ‘πŸ»Karima tijjani Mansur*
*Like me on facebook @ karima Tijjani novels*
*Luv u all*😘


β™₯️β™₯️β™₯️β™₯️
*ZAZZAFAN SO*
(Masoyin k'warai)
*Cigaban littafin Zazzafan so (Guba ne)*
πŸ’”πŸ’”
*By*
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah Khareemerh)*
*Dedicated to unique in your love heart*
πŸ“„ *37*
*Sai* bayan magriba HAFSAH ta koma gida.. Mama na kitchen ta wuce parlour inda ta tarar da abin murna..
Basheer neh qaninta ya zo gida hutun makaranta.
Yana ganinta ya taho da murnar shi
"Oyoyo aunty nah.!!"
Ta saki fara,a saukar yaushe Basheer.??
"Da yamman nan."
Ya fada tare da amsar jakar ta suka qarasa shiga cikin parlourn."
Kujera daya suka zauna ta riqe haba tana kallon Basheer.
"Oh ni Basheer sai wani girma kake haka.?
Yayi dariya Yana shafa dan gemun shi daya soma taruwa, Yasan shi ta gani shiyasa tace mishi haka.
"Mene ka wani tara gemu sai kace wani babba."?
Murmurshi yayi yana kallonta qasa- qasa yace "To ai shi dinne yaya."
"Hmm baka da kunya fah.!!
Mama ce ta shigo parlour, "To sarakan hira an hadu koh?? "Nace, an kira sallah"!!
Basheer ne ya fara miqewa "Aunty bari na dawo akwai hira fa."
"Okay Basheer itama ta miqe ta nufi hanyar dakin ta."
Yau wani irin farin ciki takeji, tana son ta ganta ita da Basheer suna hira shiyasa bataji dadin tafiyar shi karatu wani garin ba..
Duhu ya fara yi lokacin daya dawo suna zaune a parlour dukan su, Hafsah, Mufida, Amira, da Zainab mama tana toilet.
Hafsah kallon Basheer kawai take tana mamakin girman shi.
"Even She's just 25 knocking 26 shi kuma 24 yake."
'Ya miqe da wani irin tsaho irin na abban su sai farar fatar mamansu, cika da kyau sun bayyana agareshi ga wani dan gemu daya ajjye dayake qara mishi kyau.
Komai nashi cikin yanga yake dole ya burge yan mata.
"How time fly? ta fada a zuciyarta yaushe tayi candy ma? Lokacin da tayi candy shekarar ta 18 cif.
Ta sami tsaikon shekara daya bata shiga Jami,a ba (Tuna baya wato zamanta gidan Mama)
Yanzu haka ta kammala digirinta a fannin _International relationship_ sabanin burinta na son zama lawyer. tna wata na qarshe ashekarar service dinta wanda takeyi a wani gidan television.
Basheer ya nemi guri kusa da ita ya zauna.
"Aunty nidai hira nakeso muyi sosai."
Ya kalli su mufida.
"Amma Nidai bana son yaran nan suji mana hira."
Amira dake danna wayar ta ta dago ido ta kalleshi, sannan ta kalli mufida suka kwashe da dariya har da tafawa."
Ya miqe yana hararar su, yaja hannun Hafsah suka nufi dakin ta.
Yana matuqar ji da ita.
"Yaya ni nama rasa ta ina zan fara."?
Ya fada bayan sun zauna a dandaryar qasa, kan carpet din dakin.
"Meya faru ne Junior naga kamar a damuwa kake"?
Ya shafa gashin Kanshi daya taru yake ta faman kyalli.
"Hmm, babu komai boko ce kawai tamin yawa."
Suka kwashe da dariya dukan su.
Sannan ya dora cikin qasa da murya.
"Sai wata Christian girl data takura min."
Hafsah ta riqe hab'a. "Uhum? Tace dashi.
"Yes Aunty, yarinyar mayya ce wallah ta takuramin she can even comes to my room fah everytime."
"Even at n night"?
Hafsah ta tambaya tana zaro ido."
Ya jijina mata kai.
Yes sister, she's beyond your expectation fah ko tsakan dare ne zata iya zuwa min, rannan fa cemin tayi dole dakina zata kwana fah."
Hafsah ta riqe haba tace "Uhum??
"Ya kayi kuma.??
"Hum ya sauke ajiyar zuciya sai da na mata jan ido ta fita."
Ya jaro wayar shi ya nuna mata photon ta, "See her, wai blessing sunan ta.
Hafsah ta qare mata kallo sannan ta miqa mishi.
Class dinku daya"? Noo amma dai faculty dinmu daya civil engineering nake, ita kuma electric amma we're in the same level.
Level 3 take nima haka."
"Hmm."
Inji Hafsah.
Yanzu ya zakayi da ita.
Mafita nake nema aunty nah. Ya fada da marainiyar murya, "Allah bazaki gane nacin yarinyar ba, ni da na zaci abin nata wasa ne, wai a haukar ta aure na zatayi."
"Hafsah ta toshe baki tana dariya."
Bashir ya danja siririn tsaki, ya ja kwafa yarinyar class less ce sam ba aji."
Hafsah ta kalleshi "Nidai suggestions dina shine..
Bashir ya bada gaba daya hankalin shi akan ta ya zaci wani abin arziki zata fada.
Fada min aunty mene ne, ya fada a zak'e (cikin zaquwa/ so eagerly)
Hmm Tana yar dariya da siririyar muryarta tace, zan fada a labaran mu, _A level 300 Muslim student proposed to a Christian his level mate)..._
Bai bari ta qarasa ba ya tareta cikin damuwa.
Haba aunty Don Allah ki maida abin serious, wallah am seriously worried, tana hanani karatu fa kuma bana son Abba fa ya sani."
"Hmm ga mafita ma, Kawai mu fada ma abban..
"Oh my God.!! Ya dafe kai.
"Plz Yaya ki bari mana."
Tayi 'yar dariya ta gimtse.
"Okay, me kake ganin zaa yi. Uhum?"
Yawwa ni cewa nayi Kodai na baki number nata ki kirata kici mata mutunci, as wacce aka zaba min agida za,a aura min."?
"Umm.. Bari muga lemme think deeply gaskiya zanyi tunanin wani mafitar.
"Okey yaya ta thank you.
Tayi murmushi.
Hmm Basheer mai 'yan mata.
Shima dariyar yayi "Haha wallah Yaya na rasa what's wrong with 'Yan mata yanzu kowa tana son ka, banda ita akwai wasu fa.. Kawai su gwara Muslim ne kuma basa takuramin as she do."
"Um kace kana sonsu kawai."
"Noo Yaya kadan ne suke burge ni cikin su."
"Hmm kaji ba."
Ta fada, Sannan ta mayar da muryata serious tace, "And plz Basheer don Allah don't ruin any girls life, and not to broke her heart kaji, duk wacce baka so ka rabu da ita Kawai salin-alin bubu wulaqanci ko bata lokaci.
Ya kalle ta a sanyaye yana gyada mana kai, yasan abinda ta tuno, yasan dalilinta na fadar haka, yasan ta dan-dana."
"Kada ki damu Yayata ba haka nake ba."
"Thanks Yayana!!" ta fada tana murmushi.
Shima murmushin yayi jin tabashi girman, duk da yasan tasan yana da son girma.
Kallonta yayi shima, cikin wata nutsuwa, ya gyara zama sannan yace, "Yaya
Kema akwai maganar da na keson muyi dake Don Allah."
Ta tattara dkukan nutsuwarta wajen shi, sannan tace cikin sanyi.
"Wacce magana ce haka Basheer."?
Ya danyi yar ajiyar zuciya, "Um ba wata magana bace fa mai tsaho, Kawai dai tambayar ki nake son inyi.
"Ina jinka toh."
"Don Allah yaushe zakiyi aure.!"?
Ta ke Yanayin ta ya chanja, "Basheer aure kake tambayata koh, ka gaji da gani na agidan koh, ko na tare maka damarmaki (dama) dayawa ne."?
"Calm down, my dear aunty, ya fada cikin qasa da murya. "Ba fa abin zafi bane, I just asked you ne saboda mu fara shirye shirye, ya qarasa fada yana dan murmushi.
A tayi ajiyar zuciya a hankali, "Ai na zaci ka gaji da ganina ne, fah."
"Rufamin asiri ya fada yana zare ido, ya nuna kanshi wane ni in gaji da yayata."
"Dariya yaga tayi ta jin dadi." Duk da hankalinta daya kwanta amma dole ne ya qarasa mata zancen, don yana son ta dauki zancen da muhimmanci, don haka yace.
"Aunty kinsan da na dawo me Abba yace.?
Ta girgiza kai.
"Ya ganni na girma, shine ya cewa Mama wai da mace ne ni tuni na isa aure har da yarana."
Nace, "Haba Abba a village dai, shine yamin dak'uwa, wai a gidan nan ma haka neh."
Aunty kinsan na tarar dashi kafin ki dawo ya fita.
Inaji yana qara wa mama bayani after nabar wajen, "Wai Kema yaga shuru bakya wani sauraron kowa bai san meke damunki ba, Gashi even mufida ita ma ta isa aure fah."
Ya sauke waccen maganar, har yanzu idonta na kashi ko motsa su batayi..ya dora.
"Plz Yaya I don't say that kin gunduri Abba ko mu, infact ma ba zamuji dadie ba ki tafi ki barmu, but ke macece, shiyasa kika ga hakan."
Ya daga hannun shi alamar roko. "Please before Daddy talk to you about it, please kiyi making wani decision akan abin kinji, Allah nasan baki rasa masu sonki bafa kawai baki bada fuska ne."
Kinji my beautiful aunty ki daure ki manta da komai, forget your fast, wani YUSUF and wata Basma, whatever ma yanzu you're beyond their classes, ki manta dasu plz."
Sai da ya ambaci YUSUF sannan yaga tayi murmushi.
"Hmm Basheer kenan, azaton shi YUSUF ne ya hanata kula wasu?? Ita ko wacce irin zuciya ce da ita da zata iya riqe abubuwan shekara wajen bakwai baya, _Broken heart Time_
Haka ta bawa lokacin suna.
Murmushi ta kuma yi sannan tace "Hmm Basheer kenan, naji toh naji don't mind zaka ganni da aure gobe goben nan."
Suka kwashe da dariya, ta fadi hakane don kada ya dauka zancen nashi ya sa mata damuwa wanda a badini ba damuwa kadai ba, har tunanin baya sai da ya dawo mata.
"Wato tunda Abba ya sake ya bayyana haka to Lallai abin yana ranshi."
"Aunty nah, amaryar gobe bari na barki toh.."
Ya miqe yana cewa I think Abba ya dawo lemme go and tell him gobe yana da daurin aure."
Ta kaiwa bsyanshi duka ya fice yana cewa "Amarya- Amarya.
Bata da zabi illa ta bishi parlourn ita ma Don haka ta mike.
Ahankali take tafiya, tun daga nesa take qarewa mazauna palourn kallo, so take ta karanci, halin da suke ciki.'
Abbansu ne, wanda a kujerar farko wacce take facing TV, kana ganinshi shima girma yazo mishi a qallah zaiyi shekaru 55 zuwa 57, cikar kamalar shi na nan sai ma abinda ya qaru. Akwai cigaba sosai cikin al,amran gidan a yanzu fiye da shekarun baya, kama daga kan tsarin gidan daya samu gyara sosai, akwai qaruwar arziki duk da yana dab da retire baifi saura 'yan watanni ba, bayan haka ya shiga Fagen siyasa, kuma babu laifi ana damawa dasu, suna da kyakykyawan zato su sami nasara a zab'e mai zuwa, Wanda idan hakan ta faru, gwamna zai iya bashi matsayin kwamishina (commissioner) ko kuma wani mai bashi shawara wato (Adviser)
Mamansu ta qara, girma da gogewa ta zama wata babbar mace, akwai cigaba sosai akan fannin kasuwancin da take yi.
Kana kallonta zaka gane babbar macece da take cikin kulawa, da kuma tsari mai kyau, kuma a tsaye take kyam kan al,amran Gidan ta.
"Zainab tana level 2 yanzu inda take karanta pharmacy, a qallah zatayi shekaru, 21.
Sai Ameera, me jiran admission, sai mufeeda da take year din qarshe a secondary.
Dukkansu babu wacce baza,a kaita gidan miji taki zama ba, ko waccen su ta girma sosai akwai wayewa tattare dasu, ta fuskar komai, amma waye wa irin ta masu ilimin addini. Suna da class amma sam ba,a taba kwatanta su da masu wulaqanci ko wani girman kai..'
Hakan ya isa abin godiya ga Allah a wajen, iyayensu sun haifi 'ya'ya kusan dukka mata, kuma sun iya da tarbiyyar su, abin alfahrin daddy ne ace cikin yayanshi har da wacce ta hadda ce al,qur,ani (Zainab) yaso hakan ga Hafsah, amma komai nufin Allah ne, domin falalar sa ce, da yake bawa duk wanda yaso."
Itama tana da izufi talatin cif, akanta, wanda ba gazawa ce ko wani abin makamancin ta, ya hanata karasawa ba sai dai abin na Allah neh..'
Sauran suna iya kokarin su don suma suna karatun daidai gwargwado ciki harda Basheer.
Kullum fatan iyayensu shine Allah ya kawo musu miji na gari. Duk da ba su rasa masu sonsu ba sai dai abin komai lokaci ne.
"Yayah, ? Abba ya kirata kamar yadda ya saba karanta ko yaushe.
"Na,am Abba."
Yau Basheer yaxo koh, ana ta hira."
Tayi murmushi.
Kin gaji koh"?
Ta daga kai alamar "Eh"
"To aje aci abinci a kwanta koh tunda ya cika ki da hira ya fice koh."?
Dariya ta danyi, tabbas tana son ta kwanta ta huta.
Kitchen ta wuce, cike da farin ciki tana son wannan kulawar da take samu awajen abban ta, bata jin wani daga cikin su yana samun irinta, dole ta yi abinda zai dinga faranta mishi rai shima indai tana son ta dace da rahmar ubangiji.
Kad'an ta zuba abincin, ta fito ta sami guri akan center carpet kusa da, zainab da take fama da litattafai ta zauna.
Mama ta kalli plate din, "Shikenan dan abincin da zakici Hafsah."?
"Banajin yunwa sosai mama."
Bama ta cinye abincin duka ba, ta tashi ta mayar kitchen, sannan ta musu sallama ta shige dakin ta, wanda mallakinta ne ita da mufeeda har yanzu.
Yayin da Ameera da Zainab suke da d`aki d`aya, sai dakin Basheer shi kad`ai.
Sallar isha ta fara yi sannan ta cire kayan jikinta ta mayar dana bacci.
A gajiye ta haye gadon ta kwanta da tunanin fal cikin zuciyar ta.
"Lallai maganar Basheer, abar dubawa ce, abin yana tsorata ta idan ta tuna wai ita ce me shekara 25, a duniya, lokaci yana matuqar gudu, bata tab'a zaton zata kawo irin wannan lokacin baa gidan mijinta ba, tasan haka ma burin Abbansu yake.
Mates dinta da yawa anyi aurensu, ciki harda Aisha, wasu ma harda yara biyu harda masu uku, amma ba ta taba sawa ranta damuwar hakan ba, tunda tasani kowa da yadda Allah ya tsara mishi tashi rayuwar.'
Bazatace bata da masu sonta ba ko kuma wanda taji yayi mata, amma xata iya cewa zuciyar ta rabu da son wani D`an adam, kwatankwacin irin son da ta yiwa Yusuf, ko da rabin hakan ne.
Sai muka wani abu da ake cewa _"Ko wacce kwarya..._
Ita ba raina arziqi bace ko kuma buri da son abin duniya, amma ya zama wajibi ta duba wanda zasu samu daidaito, Domin shi zaman auren ba wai zamane na wata daya ko shekara ba, zama ne na din-din -din, ta yuwu tun kana iya jure tsanani da hakuri, har azo _level_ din da zakaji bazaka iya jurewa ba."
Saboda haka ita ba sauri take ba sam, abbansu ya hore ta da gudun gaggawa acikin al,amra.
Har tana tuna wata magana da take cewa, _''One day it will just happens, you will meet the one that will love you the way you deserved to be love, and you no longer have to fight for it.._
In ta tuna tana samun nutsuwar zuciya, da hakan, kuma tasan Tabbas wata rana zata iya samu, kasancewar tasha haduwa da wadanda kai tsayen zata iya cewa basu dace da ita d`in ba ta fuskar mu,amala, suna mata kamanceceniya da irin ta Yusuf, ko kuma ta fuskar dabi,u da Yanayin fahimtar rayuwa.
A haka har ta tattara su ta watsar ta mayar da hankalinta gabadaya kan karatun ta wanda dashi take fatan gina feature dinta.
To irin haka ce tayi ta gara rayuwarta da zamaninta, har kawo yanzu, da shekaru suka shud`a ba tare da ta ankare ba, amma yanzu bulaliyar da Basheer yayi mata ta farkar da ita, cewa Tabbas akwai buqatar ta matsa ta bawa 'yan baya waje, suma suci nasu zamanin.
Don da tuni ma Ameerah tayi mata tsallake, sai aka samun akasin tafiya k`aro course da mijin da ta samu yayi wanda zai kai shekara d`aya, zuwa da rabi, da tuni ansa rana, kuma abinka da itama karatu take sai duk ba,a damu ba.
Da ire-iren qananun tunanin nan ta fada kogin tunanin tuno rayuwarta ta baya wato shekarun zaman ta gidan Mama, wanda ta kirasu da shekarun gwagwarmaya....






Muje zuwa.πŸ‘πŸΌ


β™₯️β™₯️β™₯️β™₯️
*ZAZZAFAN SO*
(Masoyin k'warai)
*Cigaban littafin Zazzafan so (Guba ne)*
πŸ’”πŸ’”
*By*
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah Khareemerh)*
*Dedicated to unique in your love heart*
πŸ“„ *38*
*Zaman* ta gidan Maman Ya Nazeer, zama ne da zata iya fassara shi da "Zaman qaruwa da qarin ilimi tare da samun experience akan rayuwa.
Zama ne wanda bata samu takura ba sam a yayinsa, sai ma tattalinta da aka dinga yi sam baa son kukanta.
Idan Hafsah zatayi lissafin mutane muhimmai wad`anda suka taka rawa a rayuwarta to tabbas daga abbanta, sai mamanta sai kuma yayar mahaifiyarta wato maman Ya Nazeer, kamar yadda suke karanta..
Bawai don sun dauki tsahon lokaci tare ba, a,a sai dai taimakon da ta bata na tsahon wata uku kacal, amma shine zatace ya tallafi rayuwarta har kawo yanzu, wanda badon ita ba da tuni ta zama wata abu ta daban ba Hafsar da take ayanzu ba."
To dama hakane, wad`ansu mutanen suna da irin wannan baiwar, wad`anda zama kad`an zakayi amma ka qaru da abinda zai tallafe ka har qarshen rayuwa.
Maman ya Nazeer, ta jata a jiki, ta dawo da ita hayyacinta lokacin da ta fita daga cikin shi, ta nuna mata cewa tana da da ma lokacin da tayi losing duk wai hope nata, _she lost hope and she's completely broke._
Bata taba tunanin zata iya rayuwar da babu Yusuf cikinta ba, sai gashi maman ta nuna mata cewa zata iya kuma ta koyar da ita yadda zata iya d`in, kuma gashi ta iya d`in.
Dole ne ta gode mata bisa wannan d`au ki data kawo mata cikin rayuwa wanda bata da abinda zata saka mata dashi banda addu,a.
Shiyasa wani lokacin Hafsan, ke tuhumar kanta da laifin _butulci_ na bujerewa Soyayyar Gudan jinin matar da ta tallafi rayuwarta.
Amma takanji sassauci idan ta tuna cewar kai tsaye, Maman bata da masaniya bisa hakan sai dai hasashe, kuma baza,a iya cewa tak`i Nazeer kai tsaye bane, sai dai ace tak`i bada fuska gareshi yadda zai shigar da buk`atar sa, har ya gaji ya haqurar wa zuciyarshi.
Ahankali take tuno abinda ya faru.
#TUNANIN #BAYA
Wato bayan isar su gidan ita da Mama a wancan lokacin sun isa gidan babu kowa cikin sa, kasancewar yaran sun tafi makaranta.
Driver ne ya shigo mata da kayanta, inda Maman ta nuna mata wani dak`i mallakin yarta Fatima tace "Kai kayan naki wancan dakin."
Ta miqe a hankali, ta ja trolley din ta nufi d`akin.
Sun yini su biyu ita da maman cikin nishad`i har Maman ta sa ta tayi musu girki, sai wajen qarfe biyu da rabi sannan yaran gidan suka fara dawowa.
Da farko Nazeer ne ya shigo wanda shine babban d`a a gidan, sai fateema mai binshi, sai Al,ameen, sai Nour, sai Siddiqa.
Hafsah ce kadai a palourn ta qurawa TV ido, Ahankali yayi sallama, da takarda a hannunshi ta dago kai ta kalli mai shigowa, ta amsa sallamar, sannan ta kauda kan ta.
Murmushishi ya fad`ad`a, "Hafsy ce yau a gidan namu."?
Tayi murmushi, Nice "Ya Nazeer ina wuni."? Ta gaidashi tana mai dan duk`awa daga kujerar da take.
Ya sakar mata murmushi sosai, yarinyar akwai tarbiyya ga Ladabi, lpia lau, Hafsah, ya mama Ina su zainab"?
"Suna lpia lau."
Ya qara kallon ta.
"Ina Mama nah"?
Ta kalleshi so take ya qara bayani ko zata fahimci zancen, wacce maman yake nufi.
Taji abinne banbarakwai babba dashi yana cewa Mamanshi.
"Ina Mamy nah nace."?
"Uhum. Maman ku."?
Yayi `yar dariya.
"Yes, mamy nah, ai mamie tawa ce ni kad`ai k`wace min akayi aka min rubdugu."
Hafsah bata ankara ba sai jinta tayi tana k`yak`yata dariya, a zuciyarta tana cewa dama haka Ya Naseer din yake da hira.?
Ta sani dai yana zuwa gidansu, amma bai fiya jimawa haka ba, kuma ita bata cika zuwa gidansu ta kwana ba, idan ma tazo yawanci yana school.
Dariyar su Mama ta jiyo ta fito zuwa a palourn. "Oh dama nasani ai sai kai."
Ta fad`a tana kallon Nazeer d`in.
Yayi

Please Login or Register in order to submit comment