Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kanshi mazauni a kujera kafin yace a shagwab`e Mama wai Taraba suka tura ni."
"Taraba"?
Mama ta maimaita,
Kuma kana so."?
Ya girgiza kai, gaskiya A,a Mama nafison koda jigawa neh."
Okay zanyi yiwa sunusi magana, tana nufin qaninta wanda shi maman su Hafsah ke bi."
"Okay mamy na Nagode."
"Mamy yunwa nakeji." ya fada yana dan shafa ciki."
Sannan ya miqe ya nufi, Kofar fita daga palourn domin dakinshi yana daga waje ne.
Mama ta bishi da kallo, sannan ta kalli Hafsah.
"Ikon Allah kinga ya fice, tashi ki zuba mishi abincin kafin ya dawo kinji."?
Toh Mama ta miqe ta nufi kitchen din.
Plask ta samu guda biyu, ta zuba abinci a babban dayan kuma tasa miya, sannan ta shirya komai kan tray, lokacin data fito Maman bata palourn kawai sai ta ajye akan dinning, kusan minti uku bai dawo ba, sai ta jiyo muryar Mama nacewa, "Hafsah ki miqa mishi abincin kinji don da kyar idan zai dawo.
"To, kawai tace, ta kinkimi tray din tayi dakin shi.
Ad`an ka re taga k`ofar don haka tura wa kawai tayi ta shiga da sallama.
Daga cikin wani daki a dan palourn ta jiyo an amsa inda ya fito ya tarar da ita da kayan tray a hannu, aiko yace me zaiyi idan ba dariya ba.
Ya k`ame yana kallonta yana ta qyaqyata dariya yana nuna ta har Hafsah ta tsorata.
Sannan ya gimtse ya fara magana, cike da shaqiyanci,
"La-la-la-la, gaskiya kina so mama ta zane ni kenan.
ta kalleshi ad`an tsorace sannan ta qara kallon tray d`in.
Ya sa Hannu ya amshi tray d`in ya ajye sannan ya cigaba da magana k`asa-k`asa.
"Wa yace miki anan Mama ke zuba min abinci."?
"Ai Matsayina bai wuce wannan ba."
Ya d`auki plate daga kan tray d`in yana nuna mata.
"Anan ake zuba min abinci kin manta bani ne mai gidan ba." Ya Qarashe zancen yana zaro idanunshi.
D`an murmushi tayi a qagauce, saboda gaba d`aya ji take kamar akan qaya take.
"Bata saba ba sam, ace wai gata ga wani namiji, tsaye irin haka daga ita sai shi, idan aka cire Yusuf, da shi kuma ta bashi wani Matsayi na daban.
Bata da yayye maza, sannan ba wasu mazaa ke shigo musu gida ba har su sami damar hira dasu, idan ka d`auke auncle Abdullah, sai shi Nazeer d`in, sai wad`and`a ba,a rasa ba cikin `ya`yan `yan uwa suma kuma jefi-jefi ne. Su a familynsu ma mata sunfi yawa.
Sannan bata son maman ya Nazeer, taga ta dad`e, don haka ta motsa K`afarta da niyyar juyawa ta tafi amma sai ya katse mata hanzari da cewa.
"Ni al,majiri ne a gidan." Ya fad`a da marainiyar murya.
"Please zubamin, a plate sai ki tafi da sauran."
Ranta bai so hakan ba amma bata da zab`i tana bashi girma a matsayinshi na Yayansu.
Ta tsuguna, da sauri sauri, take zubawa, ta cika plate d`in.
"Kaii ai bazan cinye ba rage min."
Ta kwashe wajen kwatar (quarter) abincin.
"Yawwa ko kefa."
bata ce komi ba tasa mishi miya da nama tasa mishi salad.
Sannan ta d`auke ruwan da ke kan tray d`in ta ajye mishi sannan ta d`auki tray d`in.
Tana lura da kafe ta da Ido da yayi.
"Thank you Qanwaty!
Taji ya fad`a
Bata ce komai ba ta juya tana sak`e sak`e a ranta.
_"Anya kuwa zata yarda, tayi koda kwana uku ne agidan nan bare kuma sati, matuqar za,a dinga zata ayyukan hidima irin wad`annan."??_






📝
*HAJEEYA KHAREEMERH*

♥️♥️♥️♥️
*ZAZZAFAN SO*
(Masoyin k'warai)
*Cigaban littafin Zazzafan so (Guba ne)*
💔💔
*By*
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah Khareemerh)*
*Dedicated to unique in your love heart*




📄 *39*




*Tana* komawa palour, fateema ta shigo ita ma da sallama, Hafsah ta amsa cike da farin cikin ganinta.
Itama da gudu ta qaraso ta rungume Hafsah tana murna da ganinta.
"Hafsy yau kece a Gidan namu."?
Hafsah tayi murmushi ita ma, Nice wallah auntie Fateema."
Fateema ta sake ta tana fad`in "Gaskiya naji dadie."
A palourn suka zauna suna hira, Fateema ta miqe taje ta zubo abinci ta dawo tana fad`in.
"Wata irin yunwa nakeji wallah."
"Sannunki.!!"
Hafsah ta fad`a tana qara kallonta.
"Level 3 kike koh auntie."?
( _Da ke ta girmi Hafsah da wajen shekaru uku._)
Eh, wata test mukayi mai zafi wallah."
Ta fad`a tana kai lomar abinci bakinta.
"Ke fa, kinyi candy kema koh."?
"Eh result nake jira."
To Allah ya bada sa,a.
"Amin."
Suna hirar, Ya nazeer ya qara shigowa, kamar tare suka shigo shida ragowar yaran gidan. Wad`anda murnar ganin Hafsah yasa suka cika gidan da hayaniya.
Ya Nazeer, shima da tashi hayaniyar ya fara musu magana, "Haba cai cai cai cai, kun dawo ai."
Mama ce ta fito itama, lokacin Fateema na tambayar Hafsah.
Amma dai kwana zakiyi koh."?
Mama ta cafe, "Ai Hafsah nan da sati biyu ma tana nan."
Wani murmushi Nazeer yayi, "Kice mun qaru a gidan."
Mama, tace sosai ma, ai kasan tayi candy fah."
Ya qara yin murmushi "Allah Mama."?
Sannan ya kalli Hafsah, sam bashi take kallo, ba. "Congratulations sister."
"Thank you."
Tace mishi nan aka barke da hira.
Mama ta kalle su, zan d`an fita.
"Fateema, Hafsah ku kula da gidan."
"To mama a dawo lpia."
"Tare Mama suka fice, ita da Nazeer don shi zai driving dinta.
Fateema taja Hafsah d`akin ta suka kule suna hirar Yaushe gamo."
Har dare mama bata dawo ba, sun gaji da hira sun dawo palour, suna kallo.
Sai can maman tayi sallama ita da Nazeer da kayi niqi niqi irin na amfanin gida.
Mama kenan _mace me kamar mazaa_, a kalla zatayi shekara Arba'in da biyar.



Mijin ta Alhaji Dalhatu ya rasu shekaru uku kenan da suka wuce, ya barta da yara biyar, uku mata biyu mazaa.
To kasancewar a gajiye maman ta dawo bata samu zaman hira sosai da su Hafsah ba, taje ta kwanta babu jimawa bacci ya d`auke ta.




Da daren Hafsah suna kwance a d`akin Fateema, Hafsan tai jugum tana tunanin Basma da Yusuf. Su suna can suna jin dadin rayuwar su ita kuma sun barta nan cikin k`uncin zuciya.
"Aunty Fatee, Don Allah ara min wayarki."
Hafsah ta miqe kamar an tsikare ta tare da fad`in hakan.
"Okey ungo."
Fateema ta miqa mata wayar.
Hafsah ta zana number Yusuf a ciki sannan tayi saving. Kafin tace, "So nake kawai naga mai number d`innan a online."
"Hira zakuyi"?
Cewar Fateema.
Hafsah ta girgiza kai, "Aa dai kawai sa number zanyi, idan lokacin da za,ayi magana yayi zan miki magana.
"Tom."
Inji fateema.
Ai kuwa sai ga photon, shi a profile.
"Aa wannan ne me number."?
Fateema ta tambaya cikin zumud`i.
Hmm kawai Hafsah ta fad`a ta kafe photon da ido zuciyarta fal da bak`in ciki yaya ma za,ayi tayi sakacin da zata barwa Basma Yusuf, ai impossible.
"Gaskiya ya hadu fah."
Cewar Fateema, wacce fad`in hakan ya qara tun zira, Hafsah. Sai kawai ta miqa mata wayar ta kwanta cike da tashin hankali.
Dole ta nemi mafita, kuma ta tashi tsaye, tunda ana nema afi k`arfinta.
Wani abu ya maqale mata a mok`ogoro, zuciyarta ke wassafo mata basma, da irin rainin da tayi mata har yasa ta mata _Snatching_ mafi muni.
A kullum ta tuna bak`in ciki ne ke qara cika mata zuciya had`i da wata qiyayyar basma mara misaltuwa, bata taba jin ta tsani wani ba sai a kanta.
Nunkuwar tsanar kuma yana da alaqa da rashin samun damar daukar fansa _revenge_ ko yaya neh." Shiyasa abin ya tsaya mata arai, data tuna bata da wata dama fa. Kawai sai ta fashe da wani kuka me cin rai."
Fateema ma na cikin qarewa photon kallo kafin tabi Hafsah da kallo cikin mamaki, da damuwa, gaskiya akwai abinda ke damunta.
Cikin in,ina take fad`in "Ha.. Hafsah me menene."? Me akayi miki don Allah kiyi shuru.
Kukan take sosai ko zata sami relief.
Fateema tayi cilli da wayar ta matso kusa da ita tana lallashinta.
"Kiyi hakuri don Allah, me aka miki ko nice."?
Hafsah ta girgiza kai.
Mama ce."?
Nan ma ta girgiza kai.
Ya Nazeer ne."? Shima ta girgiza kai.
Sai da ta tambayeta
kowa na gidan amma tace babu kowa.
To wanene."?
Fateema an cuce ni, anzalince ni.!"
Ta kuma rushe wa da kuka.
Hakan ya qara rud`a
Fateema.
To wanene Hafsah kodai in kira mama ne."? Ta fada tana qoqarin miqewa.
Hafsah ta ruqo ta.
Cikin kuka tace, kada ki fada mata don Allah ki kyaleni kawai nina san abinda aka min."
"To ki daina kuka, ki fad`amin menene, ko kuma in kirata."
Da kyar dai Fateema ta samu Hafsah tayi shuri amma fir tak`i fad`a mata komai sai ajiyar zuciya take. "Ki bari kawai, take iya ce mata.
A haka sukayi bacci, wanda ga Hafsah ba bacci ne kad`ai ba, bacci ne me cike da mafarkai, na Yusuf da Basma, marasa dad`i.



Da safe Fateema, tayi shirin makaranta, dukan su na palour banda Hafsah da take ta bacci.
Fateema taso fad`awa mama as abinda Hafsah tayi da dare amma tana sauri.
Sai da yamma bayan ta dawo suna zaune ana hira kawai mama, ta tashi ta shige d`aki, minti kad`an kuma sai ta k`wallowa Fateema kira.
Fateema ta miqe ta bita d`akin.
"Ina son dama inja miki kunne tun jiya sai kuma na manta."
Maganar da mama ta fara da ita kenan.
Bbu shiri Fateema ta tattara dukkanin nutsuwar ta ga Maman.
Mama ta d`ora, "Koda wasa kada ki sake ki ara wa Hafsah wayarki ta kira wani, saura kuma kiyi sakaci ta d`auka."
Dam! gaban Fateema ya fad`i jin wata doka mai tsauri irin ta mama.


Anya ta sanar da ita gaskiya kuwa, cewa Hafsah ta riga da ta ari waya."?
Bare har ta fad`a mata zancen Kukan da Hafsan tasha jiya.
Idan hakane da akwai alamar tambaya kenan game da zuwan Hafsah gidansu, dama abin ya bata mamaki, don Hafsah bata wuce kwana d`aya a gidansu amma wannan zuwa na bazata, don mama sam bata musu zancen zuwan hafs
Idan haka ne Akwai abinda ya faru.
Don haka ta yanko tambaya tare da d`agowa don yiwa maman amma sai ta d`aga mata hannu.

📝
*HAJEEYAH KHAREEMERH*

♥️♥️♥️♥️
*ZAZZAFAN SO*
(Masoyin kwarai)
*Cigaban littafin Zazzafan so.*
*(Guba ne )*
💔💔

*By:*
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah khareemerh)*
*Dedicated to Unique in your love heart group members.*



📄 *40*




*Kada* ki tambayeni komai."
Kawai ki bi abinda nace.
"To mama."
Fateema ta amsa cikin ladabi.
Tashi kije ki turo min Hafsan.
To mama.
Ta miqe ta fita, ta sanar da Hafsah kiran mama.
Ta shigo cikin nutsuwa, doguwar riga ce a jikinta ta atampha.
Ta durk'usa a gaban maman.
Mama gani.
Hajiya Nafeesa ta fad`ad`a fara,arta sosai.
"Hafsa na. Ya naga duk kin fad`a"?
Bata jira amsarta ba tace, "Ki saki jikinki kinji kuma ki daina sa damuwa a ranki.
Sannan ta qara kallonta, "Ai babu wanda yake takura miki a gidan nan koh."?
Hafsah ta girgiza kai da sauri. "Aa mama babu kowa."
Tayi murmushi, Yawwa idan ma akwai ki fada min duk wanda kika ga yana damunki ko da kuwa Nazeer ne."
Mama ta qarashe zancen tana dariya Hafsah ma dariya tayi.
So Maman take Hafsah ta saki jikinta da ita tana so ne ta saba hira da ita sosai a haka har ta saki jiki ta fada mata damuwar ta."
Tana son ta gano Menene matsalar ta ita da yaron.
"Ki bani labarin makarantar ku kinji Hafsah."?
Hafsah tayi d`an
Murmushin jin kunya.
Ko bazaki bani ba"? "Ba mamanku tace ke kike daukar 1st position ba ko ba haka bane."?
_Duk cikin sigar wasa take mata tambayoyin._
Hafsah ta d`aga kai.
"Gud girl.!!.
baki tab`a zuwa ko ta biyu bane."?
Ta girgiza kai.
"Kin taba zuwa."?
um, sau nawa sau biyu."
Na uku fa."?
Aa.
"To na hudu fah."?
Nan ma Hafsah ta girgiza kai.
Mama tana dariya tace "To sai na biyar."?
_Tana sane tayi mata tambayar don maman Hafsah ta fada mata komai._
Sai Hafsah taji kunya ta shiga boye fuskar ta cikin cinyoyi."
"Ahh, Hafsa kice kin taba zuwa ta biyar d`in."
"To garin yaya."?
Shuru babu amsa.
"Wasa kika tsaya."?
Nan ma shuru.
"Ki d`ago me yasa kike jin kunya."?
Hafsah ta dago tana noqe-noqe.
Kinaji nah."?
Ta d`aga kai.
"Ki daina yin abinda zaki zo kiji kunya, ko kizo kiyi dana sani."
_"Kinga yanzu kin bata record d'inki."_
"Kin ga da tuni, idan kina bawa Yaranki ('ya'yanki) labari, _you claim and proud that_ baki tab'a tsallake na biyu ba koh."? Amma yanzu kin bata abin."
Mama ta fada da muryar nuna damuwa.
Ran Hafsah ya cika da kishin abin, _Tabbas ta tafka asara ba komai bane kuma sai don dalilin biye wa basma da son farin cikin ganin Yusuf._
A hankali idonta ya cika da kwalla ganin sam bata ribaci hakan ba illa bata record dinta da sukayi kamar yadda mama ta fad'a.
Mama ta lura da kwallar, duk da Hafsah taki barin ta ta zuba.
A hankali ta girgiza kai tace, "Me abbanku yace miki a time d`in daya ga result d`in.
A kunyace tace, "Yayi min fad'a yace kada na sake sakacin yin hakan."
"To Ke me yasa kikayi hakan Uhum."?
"Kina tunanin wani abu neh."?
Hafsah ta girgiza kai.
"To menene.. fad`amin me yasa kakai failing a lokacin."
Ta qara yin shuru.
"Wasa kuke koh.? Kin chanja qawaye koh, kuna zaman hira."


Gaban Hafsah ya fad'i, ya akayi Maman ya Nazeer take neman baro jirginta."??
"Kinyi shuru Ko ba haka bane."?
Bata da amsa, sai kawai maman ta bar zancen ta shiga wani.
Me yasa kike batawa mamanki rai."?
A hankali ta girgiza kai, "babu komai.
Babu komai amma kike yin abinda bata so."?
Idan mama ta lura fuskar Hafsah tayi rauni lokacin.
"Me yasa kike fita bada saninta ba."?
Duk Cikin qasa da murya maman take magana.
"To rannan ina kukaje ke da qawarki."?
Gaban Hafsah ya fad'i, wannan fita ta zame mata jaraba. Sam ta tsani a tambaye ta ina taje."
Bayan inda taje d`in ba alkhairi ta ganowa kanta ba.
Ehe."? _Inji mama jin tayi shuru._
"Asibiti mukaje dubiya."
Wanne asibitin."?
Uhum.. A ina yake."?
_Hafsah bata iya qarya ba don haka ta kasa qirqiro amsa._
"Kin sami babu kyau sabawa iyayen koh."?
Tame daga kai.
To ki daina yin abinda zai b'atawa mama da Abba rai kinji.
"Tom."
_Ta fad'ad'a murmushi._
"Yawwa hafsy, gobe zaki raka ni wajen gyaran jiki na."
Ko Bakya son muje."?
Hafsah taji dad`in hakan sosai don haka cikin fara,a tace "Inaso mama."
"Yawwa jeki wajen su fateemah kuyi hira."
_Ta miqe ta fita mama ta bita da kallo._
Da daddare suna zaune suna kallo, Nazeer ya shigo ya zauna cikin su.
Abinda Mama ta lura dashi shine, kwana biyu Nazeer nason ya zauna cikin su ya dad'e musamman da daddare.
_Bata raya komai aranta ba._

A gurin Hafsah kuwa zaman nashi takura ce a wajenta. _Domin indai ya zauna sai ya tsokane ta, ko yayi ta janta da hira. Gashi tunda tazo gidan duk wata hidimar shi ita yake sakawa, Kama daga zuba mishi abincin, d`akkon kaza-da-kaza._

Amma banda haka tanajin dad`in zaman gidan sosai da sosai banda damuwar dake cikin ranta.
Yanzu ba yusuf ne kad'ai damuwarta ba, a,a harda damuwar Basma, so take ta d`auki fansar abinda tayi mata ko dan ta rage damuwar abin aranta.

_Da Wannan alwashin, ta kwana a ranta._

Gefe guda tana jin takaicin ledar kyautar ta da ke wajen maman Ya Nazeer, damuwar ta wayar dake ciki, da tana wajenta tabbas sai ta yi amfani da wayar ko mai zai faru kuwa, sai ta kira Basma ta huce fushinta akan ta.
Ita da zata ganta ma babu abinda zai hana ta illatata.
Ta rasa me ya hanata d'aukar mataki a lokacin. Ko kuma lokacin bata da kwarin guiwar yin hakan. Saboda taga abinda zuciyar ta bata tab`a wassafo mata faruwar abu mai kama da hakan ba.


Tayi kwafa, yayin da Fateema dake karatu, ta bi inda take kwance da kallo, sam ta zaci Hafsah bacci take.



Washegari da safe tun wajen qarfe 11:00 na rana, Hafsah ta shirya ita da Mama suka fice zuwa wajen gyaran jikin Maman.



_Fateema`s touch_
Sunan wajen kenan, ya had`u sosai, ana gyaran jikin amare, gyaran gashi, wankin qafa da sauransu.
Lokacin da suka je, ana ta yiwa wata amarya gyaran jiki, suna kwa shigowa ma,aikatan wajen suka hau gaida Mama, wacce suke kira da Mommy. Cikin fara,a ta dinga amsawa sannan ta wuce ciki.
Akwai wani d`an office madaidaici wanda yafi kama da palour, nan suka shiga maman ta zauna a kujera, Hafsah ma ta nemi waje ta zauna. K`amshi ne kawai ke tashi, gefe ga _show Glass_ turaruka ne aciki da humra duk na siyarwa.
"Baki tab'a zuwa wajen nan ba koh."?
Mama ta tambayi Hafsah dake faman kalle-kalle. Ita dai wajen ya burgeta sosai.
Tayi murmushi, "Mun taba zuwa da Mamanmu sau biyu, cikin nan ne dai ni ban tab`a shigowa ba."
Suna hirar aka k'wank'wasa kofa, mama, ta bada izini a shigo.
Lemo tazo ta ajye musu, sannan ta fita.
"Kisha lemon kinji Hafsah na ko kina son ki fita kiyi kallo."?
Ta d`aga kanta.
"To kisha sai ki je ki kalla.
"Tom."
Anyiwa mutane biyu gyaran k'afa dana gashi, wato _Saloon_ za,ayi wa ta ukun kenan mama ta sa aka kira mata Hafsah.
Ta miqe ta tafi kiran.
Tanajin dad`in zaman har suna ta hira da ma,aikatan wajen.
"Mama gani."
"Zauna kici abinci." Mama ta nuna mata abincin da ta musu order aka kawo.
Ta fara ci kenan, maman ta miqe ta fita, zagayawa don ganin meke gudana.'
Babu dad'ewa kuma maman ta dawo Hafsah nacin abincin tana janta da hira so take tayi mata wasu tambayoyi masu muhimmanci.
" `Yan mata kinga Yenda ake gyaran jiki koh."?
Hafsah tayi murmushi,
"Ko kina so ayi miki."?
Hafsah na murmushi ta d`aga kai alamar Eh."
"To anqi d`in sai dai anzo bikinki ayi miki yanzu sai dai ayi miki a fuska kawai."
Cewar mama cike da zolaya.
Hafsah ta sinne kai alamun jin kunya.
"Ai kina da saurayi koh."?
Hafsah tayi murmushi jin kunya tana girgiza kai alamar a,a.
"Gidanku!! kina da dashi mana."
"Bani da shi.!!
"Au kikayi magana ko toh kina dashi."
"A,a mama" tayi maganar tana 'yar dariya.
"To wanda ya baki ledar nan fah."?
Ehe."? Inji Hafsah, ta ke yanayinta ya chanja, zuwa damuwa.
"Am um, ba saurayi na bane."
"Hmm, koh."?
Hafsah zaton ta mama ta yarda don haka qara d`aga kai alamar tabbatar wa.
Mamanki tasan da ledar."?
"Aa."
"To meyasa baki nuna mata ba..?
Bata da amsa don haka tayi shuru.
"Kiyi magana mana Hafsah."?
"Babu komai."
Kinga irin laifin da kike koh."?
"Daga yau kada in qaraji kin qara yin laifi me kama da wannan."
"Ta d`aga kai alamar, Toh."
Mama ta d`ora, "Kin ce ba saurayin ki bane, amma meya kaiki amsar kyautar shi, kuma meya sa kika karb`a."?
Hafsah tayi shuru tana tuno amsar da zata bayar.
"Um, am wallah.. hi, ba saurayi na bane."
To menene had`in ki dashi.
"Ni..ni bana kulashi yanzu." ta fad'a cikin in`inah..Fatanta kawai mama ta yarda da zancen ta."
_An kusa zuwa inda mama take son azo don haka tace:_ "To me yasa kika daina kulashi meya had'a ku."?
Ai k'iris ne hafsah bata sa kuka ba.
Take muryata tayi rauni, har rawa take yi.
"Babu abinda ya had`a mu."
"Hmm, kina wasa dani koh."?
"Aa Mama."
"To ki fada min gaskiya."
Shuru babu magana har wajen wucewar muntuna wajen biyu. Sai Hafsah dake faman kokawa da qwallar dake son zubo mata."
"Kawai na daina kula shi ne saboda mama bata so."
"Mama bata so, to meyasa."?
Mama ta tambayeta da sigar irin tayi mamakin maman ne."
Tasan ba zata sami amsa ba, don haka tayi amfani da damar wajen cewa, "Shine kuka fita dashi ranar bikin abdallah koh."?
Gaban Hafsah yayi wata mummunar fad`uwa, ta k'osa wannan lokacin ( _Moment_) d`in ya shud`e, ta gaji da tambayoyin, don ana neman qureta.
Mama bata jira amsarta ba ta d'ora.
"Kinga dalilin d`aya sa mamanki ba ta so koh.. Meyasa zaki bishi wani waje."? Ke aganinki ya dace kiyi haka."?
Cikin nadama Hafsah ta girgiza kai.
"Duk mutumin da bazai taya ki yiwa iyayenki biyayya ba, ki rabu da shi kinji."
Hafsah ta d'aga kai alamar Toh."
Sai wajen la,asar suka tafi gida wanda a hanya tunanin Hafsah ya kasu kashi-kashi, wanda yafi tsaya mata a rai shine, nasihar mama, sai kuma jin asarar barin Basma, haka taci bulus. Dole ta bata mata rai ita ma kamar yadda tasa ranta dana iyayenta b'aci.
Sunje gida da daddare, mama ta kira fateema d'akinta, so take ta sa Fateeman wani aiki akan Hafsah.
"Fatee, kun tab'a wata hira ne da Hafsah, wacce tayi kama data samari."?
Fatima ta tsorata da tambayar don haka ta bud'e baki, gwara ta fad'awa Maman gaskiya kada taje tayi laifi don da alama akwai babban case wanda yake faruwa.
"A,a mama, saidai ta ari wayata tasa wata number, ta duba a Whatsapp amma bata kira ba kuma batayi magana ba."
"Me yasa baki fad`amin jiya ba."?
Mama ta tambaya da fad`a-fad`a.
"Kiyi hak`uri mama, bayan ta sa number sai ta tsaya kallon profile d`in kuma sai ta fashe da kuka."?
"Kuka kuma."
"Eh Mama."
"Amma duk kika k`i fad`amin koh."?
"Mama kiyi hak'uri."
Kada ki sake boye min abu makamancin wannan, tashi ki d`akko wayarki ki nuna min photon yaron..
Kafin na fad`a miki abinda zaki min..."
Nan Fateema ta miqe ta nufi d`akinsu don d`akko wayar.



Acan D`akin kuma, Hafsah ganin ita kad`ai ce a d'akin sai tayi alwashin kawai aiwatar da abinda zuciyarta ke raya mata, don ta sami dama, tana gudun kada ta wuce ta.


Cikin zafin nama ta d'akko wayar dake gefenta, ta danna wasu numbobi, ringin d`in har ya katse ba,a d`aga ba, ta qara dannawa karo na biyu.
Wannan karon an d`aga.
"Hello."
Aka fad'a daga can b'angaren.
Cikin kaushin murya, Hafsah ta fara magana.

"Hi Master of snatching H. Habeeb Hamid ke magana.!!
"Hmm, I already know it's you _good for nothing.!!_
Kada ki d'auka abinda kika yi kinci bulus, karuwar gida kawai.".. Bata bari ta sami kalmar mayarwa ba ta d`ora.. _"Ashe ke b'arauniya ce ban sani ba, b`arauniya, mai sace samarin mutane, yar iska mara tarbiyya._
"Haha Haha, dariyar basma ta cika kunnen Hafsan,
_"I already know zaki fadi irin haka tun ba yau ba loser.!!_
"Kiji kawai da rashin Yusuf da bazai kara dawo miki ba, idan kuma kina son ki tabbatar gobe k'arfe shida mu had'u _Garden_ idan kin isah.

"Qarya kike mayaudariya...

Iya zancen da kunnen Fateema yaji kenan anayi a wayar ta sanda ta shigo d'akin da azama ta warce wayar,
"Wacece..wacece mayaudariya.."??
Wa kika kira a wayata.. Me.. me yasa haka Hafsah."???
_Cikin in'ina fateema ke magana.._





📝
*HAJEEYA KHAREEMERH*
♥️♥️♥️♥️
*ZAZZAFAN SO*
(masoyin k'warai )
*Cigaban littafin Zazzafan so*
*(Guba ne)*
💔💔
*By:*
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah khareemerh)*
*Dedicated to Unique in your love heart group members.*


I DEDICATED THIS PAGE TO YOU _(RUKKY NAILA GROUP 1)_ SURELY YOU ARE A TRUE FAN.. 😊





📄 *41*




*Ki kyaleni..* Ni ki kyaleni.. Wallahi bazan rabu da ita ba, bazan bar mata shi ba.!"

Abinda Hafsah ke fad'a kenan cikin kuka, yayin da Fateema ta riqe ta a tsorace.
"Kiyi hak'uri Hafsah don Allah ki fad`amin me ya faru, wa kika kira.?

Cikin kuka tace "Nidai, kiyi hak'uri na daukar miki waya, amma ki kyale kawai.
Fateema taga bada da lokacin b'atawa don mama na jiranta don haka ta wuce zata fita. Ta kai bakin k`ofa kenan ta jiyo Hafsah na magana.
"Don Allah kada ki fad'awa mama, nayi kira a waya."
"To kawai fatima tace ta fita."
"Me Hafsan keyi."?
Mama ta tambayeta tana zama.
Cikin son rufawa Hafsah asiri fatima har zuwa sanda zataji aikin da maman xata sata don haka tace, "Babu komai tana kwance ne."
"Tom, muga yaron."?
Fateema ta budo profile d`in yusuf ta miqawa mama.
Muntuna uku tana qare wa Yusuf kallo, sannan ta miqo mata tare da jan siririn tsaki.
"Daga ganinshi bashi da cikakkiyar tarbiyya.!!"

Ita dai fateema kallo tabi mama dashi ta mayar da kai k'asa.
"Ki bani hakalinki nan.
Cewar mama, tana zubawa Fateema ido, yayin da ita kuma ta gyara zama ta bada hankalin nata ga Maman.
"Inaso ki dinga janta da hirar samari har ki gano min matsalar ta."
Fatima ta jinjina kai, mama ta d'ora.
"Akwai alamu yaron nan yana hure mata kunne, ada, don (Ameenah/maman su Hafsah) har qarar ta ta kawo min. Amma yanzu naga alamun tana da damuwa, kuma naga kamar yaron ya yaudare ta ne, shine nake son ki hilace ta da hira, ki gano min gaskiyar me ya faru."
"Kingane."?
Fateema ta jinjina kai "Eh, Mama."
Yawwa, ku dinga hirar samari da ita, da kuma hirar makaranta.
"Toh mama."
"Yawwa nasan zaki iya koh."?
Fateema ta d'aga kai alamar Eh." Tana murmushi.
"Yawwa Allah ya taimaka yayi albarka."

Da Fateema taso ta fad'awa mama zancen wayar da ta tarar Hafsah nayi, sai kuma ta fasa, gwara ta kawo mata cikakken bayani gaba-d'aya."
"Ta miqe ta zata fita mama ta kirata."
Kada fa ki matsa mata da tambayoyi ki bari a hankali, zaki bi abin, ba sauri nake ba."
"Okay mama.!
"Yawwa."
Wajen Hafsah ta koma, ta tarar da ita tayi tagumi, ga gumi da ta had`a.
Fateema tazo kusa da ita ta dafa kafad`unta.
"Am sorry my sister, kin sani cikin duhu, kiyi hak'uri ki fad`amin me yake faruwa."?
"Ni yar uwarki ce ko ba komai, zan taya ki da shawara da addu,a."
Hawaye suka qara zubowa, Hafsah, "Kada ki damu, wannan abin ni ta shafa kawai."
"A,a wallahi nima ya shafe ni, don Allah ki fad'a min."
Shuru babu alamun, Hafsah zata ce komai, sai ajiyar zuciya da take tayi tana cije leb`e.

"Hafsy..Hafsy,!!
Nazeer ya kwalo-mata kira.
Har aranta bataji dad`in kiran ba, bata son abinda yake mata bare yanzu cikin yanayin da take, da ita kad'ai ce babu abinda zai hanata yin _burus_ dashi, amma kuma ga k'anwarshi gefenta dole ta amsa, ko dan gudun kada ta ji haushin hakan, tunda ance _d`an-uwa rabin-jiki."_
"Hafsah Ya Nazeer fa yana kiranki."
Fateema ta qara qarfafa mata guiwa da haka. Ala dole ta miqe, ta fita, bata da qarfin muryar da zata amsa.
Yana tsaye a parlour ta motsa baki, zatace _"Gani."_

Please Login or Register in order to submit comment