Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

_one hundred thousand._ Yayi kyau Yaya Allah ya bar zumunci ya taimake mu, Allah ya taimaki Abban."

"Amiin ya Allah. Inji Dr. Sannan ya kuma kallon Ukhashatu.




A ina ka sami yarinyar ne."?
Ukhasha yayi saurin bude baki, "Am ai bamu gama daidaitawa da ita bama."
"Hmm, koh.."? Baka sanarwa da su Abba ba kenan."?
Ukhashatu ya daga kai alamar, "Eh."
Cikin nutsuwa doctor yake nusar dashi. "Kayi kokari dai, kayi abinda zai farantawa su Abba."
Ukhashatu ya gyada kai, In sha Allah, bamu dad'e da sanin juna bane shiyasa."
Okey, nagane Allah ya tabbatar da alkhairi.!
"Amin Yaya. Sannan ya duba agogon hannunshi, "Bari na tafi dare yayi yaya.
Okey, ba zaka shiga cikin ku gaisa ba."?
To bari na shiga naga 'yar rigima.

Sukayi dariya sannan suka mik'e a tare.




Suka shiga da sallama. Fadeel na jin muryar auncle ya taho da gudu yana murna "uncle!! uncle!! Ukhashatu ya d`auke shi, ya daga shi sama suna dariya.
"Kaii Kaii Kaii." kai fa ka girma yanzu, kayi nauyi "Ya Fadeel zan daina d'aukarka kai da "Γƒrif. Na'eemah kawai zan dinga d'auka.!! Ukhashatu ya fad'a sanda yake sauke shi.
Suka zauna a Kujera yaron ya zauna kusa da shi."
"Uncle su sunyi bacci."
"Kai meyasa bakayi bacci ba toh."?
"Assignment nake yi, nima yanzu zanyi bacci, aunty dinmu tace ina da k'ok'ari!!
Allah, ai na sani dama _my boy is a gifted.!!_
Suka tafa shida Fadeel d`in suna dariya.

"Au uncle ina yini."?
Inji Fadeel harda d'an rank'wafawa. Doctor da Ukhashatu suka sheke da dariya, doctor yace, "Au sai yanzu aka tuna da gaisuwar."?
"Mantawa nayi Abba.!! Inji Fadeel.
To Lafiya lau, Fadeel d`ina kana lafiya."? Inji ukhashatu.
Lafiya lau uncle.

Suna cikin haka, maman yaran ta fito daga d'aki.
Au Engr. Sai yanzu kenan ka shigo koh."?
Afwan auntie ina yini."?
Lafiya lau, yasu Hajiya da Abba."?
Lafiya lau suke."?
Ta dan sami guri ta zauna.
"To yasu Fadwa M aryam, kwana biyu basu lek'oni ba."
"Suna nan kalau, bari na wuce ma kada dare yayi min."
Daga shigowa kuma."? Inji aunty Jamila.
"Dare ne zaiyi min shiyasa"
Eh, kuma kazo kawar taka na bacci koh."?
Eh fa, ai gobe ma zan dawo in sha Allah."
"Tom sai kazo d`in.
Ya mik'e Fadeel ma ya mik'e ya rik'e hannunshi.
Ya kalli, yayanshi. Sai da safe yaya."
Tom ka gaida gida ukhashatu sai goben, ka gaida su Abba da hajiya.
Zasuji, yace, sannan ya juya ga aunty Jamila, Tom aunty sai da safe, Allah ya tashe mu lafiya, agaida Hajiya da mama."
"Zasuji sosai, yace.
Ta kamo hannun Fadeel, oh baby zo kaje ka kwanta kaji.
Ya noke k'afada "A,a ni uncle zan bi."
Ukhashatu yayi dariya, Aa aboki ka bari gobe zan dawo sai muje gidan Abba amma yanzu kaga dare yayi koh."
Ya daga kai, a sanyaye da alama bai so ba."
Ukhashatu ya sake shi, sannan ya laluba aljihun shi babu, ya zaro 500. "Ungo Aboki."
Ya damk'awa yaron.
Asai chocolate yau na manta ban taho dashi ba.
Yaron yasa hannu biyu ya k'arba yana murna.
Thank you auncle, ka gaida gida.
Aunty Jamila tace, Allah dama ukhasha shiyasa yaran nan suke makale maka, ka daina basu kudi don Allah idan babu alawa a hak'ura.
Yayi murmushi kawai, yana dagawa yaron hannu "Bye bye.
Shima yaron ya daga mishi "Bye bye uncle gud night.!!
Ukhasha ya fita yana murmushi.





__________________
Daya koma gida, 11 na dare ta wuce, kafin yayi wasu al,adu da ya saba kafin kwanciya bacci har sha biyu tayi. Dole ya hakura da kiranta da yayi niyya. Gashi ya gaji likis, yana kwanciya babu jimawa bacci ya d`auke shi mai cike da mafarkanta..



_________________
Tana ta sak'awa da kwancewa akan neman dalilin rashin jin shi gaba-d`aya yau, amma tunanin ta yafi fad'awa kan cewa ya gaji ne, ya yanke hukunci. Hankalinta ya dugunzuma, meyasa bata mishi koda SMS bane bayan wayar da sukayi. Ta shiga yiwa kanta fad'a, tabbatas da gaskiya r shi, su fa ba yara bane 'yan secondary da zata dinga yi mishi abubuwa irin haka.
Dole ne, ta sami hanyoyin fahimtar dashi abinda take ji game dashi.
Ta lalubi wayarta, akan wayar taga dare yayi har k'arfe 11:30pm, taji kamar ta mishi text da _I love you.!_ har ta shiga wajen yin typing message, sai kuma taja dan siririn tsaki, ta fasa.

Sai ta bige da kunna Data, kai tsaye ta shiga wajen sunanshi. Taga rabon da suyi hira, tun randa ya roketa zaizo wajenta, asama taga _last seen_ dinshi k'arfe tun 9:30 na dare.
Nan ma zatayi mishi magana sai kuma ta fasa.

Ta duba profile d'inshi babu komai ma akai ya cire, takaici ya kamata dama bata taba ganin yasa photonshi ba kamar yadda itama bata sawa kodan mutane.

Ganin tana bata lokutan ta, akan bibiyarshi da tunaninshi yasa ta matse wayar tata ta kashe ta, gaba-d`aya. Sannan ta nutse kanta cikin bargo wai ita dole sai tayi bacci. Dama kuma tana da fita gobe tana da wani aiki da sassafe.
Data rufe idon sai taji tana son tunano kamannin shi, ji tayi ta kasa, amma abin mamaki sai ta shiga yiwa kanta dole, da haka tayi bacci.



______________
Kwance take ta nutsa kanta cikin pillow tana risgar kuka, ji take duk duniya babu wanda ya kaita bak'in ciki. Gashi a yau d`in dai gaba-d`aya wayoyinta abbanta ya karb'e, ta rasa wanne irin abun bakin ciki ya same ta haka, duk wani da zatayi _sharing_ damuwarta yau ita dashi babu hanya, banda takunkumin hana fita da abbanta ya saka mata, sannan ya dad'a da kwace wayoyinta.?
Duk bayan minti sai ta tuno da wasu bakaken kalamai da sukafi komai muni a xuciyarta wato.
_"Basma yau dai Allah yayi ikonshi na bada ke, in sha Allah aurenki saura wata biyu, kiyi hak'uri kiyi min biyayya, ina kyautata zaton banyi miki zaben tumun dare ba.!!_
Ya had'e rai sannan ya mik'a mata hannu.
"Bani wayoyinki duka.!!
"Zan baki amma sai lokacin da aka d'aura miki aure.!!"



Tuno wad'annan kalamai da suke muna na, a kunnenta yasa ta bude baki ta kwalla wata muguwar k'ara, wacce lokaci guda kuma tayi saurin toshe bakinta, tuno cewa abbanta na iya jiyo ta, kuma babu abinda zai hanashi hukuntata, koda kuwa da duka ne, don ta kaishi bango.
A hankali take zubar da hawaye tana wani marayan kuka, tana kiran mamanta. Har muryata ta dashe, amma bata daina ba, sai da ta raba dare, sannan dakyar bacci ya sace ta..


_______________

Yau da wuri, ya tashi, bayan ya dawo daga masallaci, ya wuce d'akin abbansu don ya gaida shi.

_Khaady_ Yana zaune yana jan doguwar tasbaharashi, gefe kuma ga wasu manyan litattafai kusa dashi, sai kuma al'Qurani mai girma. Yau shima yana da wata shari,a da yake saka ran yanke hukunci a yau.

Ukhasha yayi sallama, _khadi_ ya amsa.
Sannan ya shiga gaida shi.
"Abba barka da asuba." Cikin sakin fuska ya amsa.
Barka dai malam, ( _kamar yadda yake kiranshi wani lokacin._) an tashi lafiya?
"Lafiya lau, Akaramakallahu."
"To Masha Allah.




Ukhasha ya k'ara duk'ar da kai sannan yayi magana cikin nutsuwa.

"Abba!! yaya ne yayi min magana akan wani d'an company da zasu bud'e shida abokan shi."
Khady ya bada hankalin yana sauraron shi.
Ukhasha ya cigaba.

"To yace idan ina so nima zan iya saka nawa kud'in."

Khady ya nunfasa sannan ya fara magana, "Eh nasan da zancen, ya fad'a min zasu bud'e companyn sarrafa shinkafa ne koh."?
Ukhashatu ya gyad'a kai, "Eh shine."
"Yayi kyau hakan, nawa zaka saka aciki kai."? Cewar Khady yana kallon Ukhashatu.
Cikin ladabi Ukhasha yace, "Shine nake so a bani shawara Abba."

Khady yayi yar dariya, sannan yace, _malam_ kenan, "To ai shawara na wajenka, kai kasan nawa zaka iya sawa."

Ukhasha ya d'anyi murmushi, ya sosa kai.

Cikin Hikima Khady yace, "To komai dai za,ayi ayi daidai misali dai, yadda ba za,a takura ba, idan Allah ya sawa abin albarka sai kuga yana ta hab'aka."

Ukhashatu ya jinjina kai.
"Shi nawa yace ka kawo."? Khady ya tambaya.
"Bai kayyade min ba, amma ya bani shawara.
Yace ka saka nawa.
"Million hud'u." Ukhasha ya fad'a yana sunkuyar dakai.
Khady yayi dariya me d'an tsaho.

"Kana da million hud'u Ukhashatu."?
Ukhashatu ya hau shafa kai.
Khady ya cigaba da magana.
"Amma baka fara ginin ka ba koh."?

Ukhasha yayi tsit, saboda anzo wajen.

Khady ya takaita zancen da cewa, "Ka saka million uku kaga babu takura koh, tunda shima million shidda ya bada."

"Nagode, Abba Allah ya k'ara girma."
Ya shiga godiya kamar wanda akayi wa kyauta.

Sannan cikin nutsuwa Khady ya kira sunanshi. "Ukhashatu!!
Ya amsa a sanyaye.
"Na,am Abba."
Khady bai jira komai ba ya fara maganar da zaiyi.
"Basai an fad'amin ba, nasan kana da isassun kud'in da zaka fara gini, idan aure ya zo maka ma kuma kayi shi, hakane koh."?

_Yana sane ya maida zancen salon tambaya._

Cikin sanyi Ukhasha ya hau gyad'a kai.

"To ka samu ka fara gininka cikin watan nan. Abba ya fad'a yana d`auke murmushin fuskar shi don Ukhasha ya san bada wasa yake mishi ba.

Cikin ladabi ya shiga d'aga kai, zanyi Abba in sha Allah, a taya mu da addu,a."

"Addu,a ai kullum cikin yi muku ita ake Ukhasha kuma in sha Allah, Allah yana amsawa."

Ukhasha, ya motsa kamar zai mik'e don yin sallama da Abba ya tafi, yaji Abban na wata magana.

"Kaji yau in sha Allah, masu kawo lefen maryam zasu zo koh, kuma za,ayi bikin cikin sati uku"

"Allah ya sanya alkhairi Abba. Inji Ukhashatu.

Amiin ya allah, Khady ya fad'a yana k'ara kallon Ukhasha kamar zai mishi magana, sai kuma bai ce komai ba. Shi kanshi Ukhasha a tsarge yake, Allah-Allah kawai yake a sallame shi ya tafi.

Sai kuma ya tsinkayi abban nacewa, "Yau baka je daukar karatun ba ne."? ( _yana nufin makarantar manya da Ukhasha yake zuwa da asuba, a wani masallaci kusa da su_)
Yayi murmushin jin dad'i, don bai zaci haka abban zaice mishi ba.
Eh Abba, yau ana idar da sallah gida na yo, saboda inason zan fita da wuri.
"Khady ya gyada kai, amma gashi ka b'ata lokaci anan.

Ukhashatu yayi yar dariya, "Aa, Abba, dama inason ganawa da kai d`in.
To yayi kyau tashi maza kada a makara.
Ukhasha ya mik'e.
Nagode Abba a huta lafiya.
Khady yayi murmushi yana bin shi da kallo.



_____________
Fitowar ta daga wanka, kenan tana goge jikinta da towel, wayarta ta shiga yin d'an kida.
Batayi mamaki ba don tayi zaton abokan aiki ke neman ta.

Tayi saurin k'arasawa inda wayar take don dubawa ta d'aga.

Wata iriyar faduwa gaba taji, wacce sai da ta d'an had'a da da fe k'irjinta.
Cikin mamaki tayi saurin d'agawa zuciyarta tana cewa, lafiya kuma kiranshi da sassafe."?
Cikin sanyin murya tayi sallama, sai kuma taji shi muryarshi ras ya amsa mata.
Hakan yasa taji babu wata ragowar damuwa a tattare da ita.
Ranki ya dad'e Barka da safiya, Allah yasa dai bani na tasheki ba da safenan.
Ya fada da nutsuwar murya kamar ko yaushe, wanda tunda ya fara magana take murmushin boye, na jin dad`in muryarshi.
Uhum."?
Taji yace, ta kalli kanta, daga ita sai towel, sai taji tana jin kunya gani takeyi kamar zai gano ta.

Tayi murmushi mai sauti, dayaji shi sosai har cikin jininshi.

Ga mamakinshi sai yaji tace, ka tashi lafiya."?
Ta gano farinciki tsababa cikin muryarshi sanda yake amsa mata.
"Lafiya lau _my queen,_ ai da tunaninki na tashi.
Tayi murmushi itama.
Jiya bamuyi waya ba, ji nake kamar mun shekara."
Itama a zuciyarta haka ne amma bata furta komai ba sai murmushi.

Cikin rage sauti yace mata, I miss you dear, you do miss me too."?
Ya fad'a kamar rad'a.
Babu wani tunani ko bata lokaci taji bakinta ya furta _"yeah!!."_
Ukhasha tsaye yake, amma babu shiri ya zauna, a gefen gado.

Really."? Yace mata cikin taushin murya.
Ta toshe bakinta, tana yar dariya, tuno abinda bakinta ya fad'a.

"I have to go to work earlier today, ina son in shirya."
Ta fa ke da fadar haka.
"Dariya, yayi mata shima, yasan dalilinta na fad'ar haka, "me too."
Yace mata, kinga nima shiri nake, amma ina son inji ki..
"bazan iya aiki ba idan banji muryarki ki da safen nan ba."
Tayi murmushin jin dad`in kalaman shi.
Lokaci d'aya kuma taji yace, kada na tsaida ke koh, bye."

Itama "OK bye" tace mishi.
Ya k'ara mata da "I love you."
To fa anzo wajen sai tayi tsit kamar babu ita.
A hankali taji yace mata, "Kinji."?
"Um." tace mishi.
Cikin marairaice murya ya ce, to ni me zaki ce min."?
Tayi shuru tana tunanowa, wato yau dai k'ure ta zaiyi.
Uhum."?
Ya k'ara tambayar ta.
"Thank you!! tace mishi.
Yayi kamar baiji ta ba, ya d'ora da.
"please Say you love me too, please Hafsah.!!
Ta nemi guri itama babu shiri ta zauna jin yanayin muryarshi.
"Please!! taji ya k'ara fad'a.

Nan ma shuru tayi,
please Hafsah ki taimake ni!! Ya fad'a murya can k'asa sosai.
(Kiran sunanta da yake ba k'aramin tasiri yake ba.)

"Nan ta shiga tunani akan ta fad'a ko kada ta fad'a."?

Cikin sanyi ta juyo shi, yana cewa "Okey can't you."?
Bata son su kuma maimaita irin na rannan, don haka da sauri wanda shima babu zatonshi yaji tace, _"me too."!!_

a k'age yace, "You too what.."?
Hmm, tace.
"Ki daina min rowa don Allah wallah kina wahalar dani.!!

Tayi jim na wasu muntuna tana hasashe.

ta jiyo shi yana cewa, idan nine bazan kasa fad'a miki ina sonki ba, wallah I love you with all my heart Hafsah.

Da alama zancen zuci yake, ta fahimci wasu abubuwan suna zuwa bikinshi ne batare da niyyar shi tayin hakan ba, haka kuwa na nuni da zallar soyayyarta ne cikin zuciyarshi.

murya na d'an karkarwa tace don ta huta itama, _ilove you too.!!_


Zo ki ga farin ciki gurin ukhasha, har sai da ya zame ya kwanta.
Yana rik'e da wayar amma yayi shuru.
Itama wani iri take ji, har wani zif-zif take ji a jikinta.
_Anya kuwa tayi wa kanta daidai.?_

Sai da ya gama saita kanshi sannan ya sauke wata ajiyar zuciya a hankali yace, "Nagode, "Nagode Hafsah, in sha Allah by time zaki fahimci irin son da nake miki, kuma in sha Allah bazan taba baki kunya ba, zakiyi farin ciki dani.
Thank you.!!
Ita dai bata da bakin magana, ya san ba zatayi d`in ba, don haka yace..
"Hafsah.! A hankali.
Ta kasa amsawa don bata son ya k'ara jin muryarta a lokacin saboda kunyarshi.

"Ina sonki." taji yace mata, maganar da ta k'ara kashe mata jiki.

Ki shirya kinji, kada na saki kiyi late.. nagode, Allah ya tsare min ke."

Babu sauti amma ta motsa bakinta wajen cewa, "AMIIN."
Don taji dad`in kalaman shi.

Tanajin karar katse kiran shi amma bata motsa ba, ji take kamar ta sauke wani nauyi daga kanta, haka kawai ta yardarwa zuciyar ta, ukhashatu ba k'aramin sonta yake ba, daga jin muryar shi zaka tabbatar da haka.

A hankali ta motsa ta d`auki mai da niyyar shafawa, gaba-d`aya ji take kamar an kwashe mata duk wani _energy_ da ke jikin ta.

A sanyaye ta dinga yin komai, gefe kuma na zuciyarta tana mamakin kanta, da kuma tuhumar kanta kan kalmar da ta furta da sanyin safiyar nan.

Azuciyar ta take fata, _"Allah yasa takai Soyayyar ta inda zata sami kulawa, ba inda za,a cutar da ita ba."_

Bata sami nutsuwa ba, har sai da raunin da jiki da zuciyarta yayi ya kaita da fitar da wata 'yar kwalla, sai da ta goge a hankali, sannan taji ta sami k'wari.


Tun bakwai take shiri, amma saida nawa ta kaita har k'arfe takwas, hakan yasa mama biyota.

Ta ganta zaune ta gama saka kaya, tana d'aura d'ankwali.

Yaya, me kikeyi hakane, keda kika ce da wuri zaki fita kinga takwas har tayi fa.

Ita kanta ba zatace ga abinda ya tsaida ta d`in ba.
"Na gama mama."
"Kiyi sauri kizo kiyi break dai."
Ta gyada kai.
Gani nan mama."

Maman ta juya itama ta fita.




Ukhashatu, tsahon ranar yinin farin ciki yayi, jiyake babu wanda ya kaishi farin ciki a yau. Godiya yake kawai ga Allah don shi ya mallaka mishi ita. Zuciyar shi cike take fal da tsare tsaren yadda rayuwar su zata kasance shida ita.

Bai iya jurewa ba, har sai da kira wayarta da azahar amma Hafsah taki d'agawa, ji take bazata iya mishi magana a yau ba.

Yayi murmushi lokacin da kiran ya yanke.
Kawai sai ya zana mata _text messages_
_"Hmm, dole kik'i daga waya mana dama, kin rikita bawan Allah, kin barshi a rikice kuma.!!_

Text d`in dariya ya bata, ta dinga yinta, har abokiyar aikinta na tambayarta "meke faruwa."?
Sai kuma ta dinga jin kamar da ita yake, domin itace a rikice ai, tun safiyar yau."

Don ta kare kanta ta aika mishi da, _lots of work dear, let's phone to night.!!_

Sanda ya ida karantawa, sai da ya maimaita kalmar _Dear_ a fili.
Ya dinga murmushi shi kad'ai shima, yana fatan daren yayi da sauri.
Amma murnarshi ta koma ciki, daya tuna yana da meeting da daddaren..



πŸ“
*HAJEEEYAH KHAREEMERH*
[17/03, 2:48 p.m.] UMAIMA BASHEER: β™₯️β™₯️β™₯️β™₯️
*ZAZZAFAN SO*
(Masoyin k'warai)
*Cigaban littafin Zazzafan so (Guba ne)*
πŸ’”πŸ’”

*By*
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah Khareemerh)*
*Dedicated to unique in your love heart*




πŸ“„ *57*



____________________
Bai samu ya kuma kiranta ba a ranar, itama kuma sai taji tana da jiran kiranshi, amma bai kirata ba, haka ta hakura har zuwan lokacin baccinta.

Tana mamakin dalilin daya tare shi ga barin kiran nata.



Ranar data biyo baya, sukayi waya, dole ta saki jiki da shi, saboda salon shi, gareta. Duk wani abu da ukhasha zaiyi ya tabbatar mata da son da yake mata yayi shi, wani ta mayar mishi wani kuma ta bishi da murmushi ko tayi shuru, don yanzu ta gama fahimtar dawa take tare. _Wato shi mutum ne daya k'ware a ko ina, yana matuk'ar son yaga ya sakata farinciki kuma._
Daga k'arshe yake rok'onta akan ta barshi ya k'ara zuwa ya ganta.
Da take tambayar shi, yaushe yake so ce mata yayi.
Ko yaushe kika ce nazo zaki ganni."

Tayi dariya Kawai sannan tace, Aa dai mu bari sai k'arshen sati."
"Babu musu ya amince.
Allah ya kaimu lokacin."
Amiin tace mishi.


___________________

Shiri sosai Hafsah ta dinga yi ranar da ya kama zai zo d`in.

Har tunani ta shiga yi, me ya dace tayi mishi na tarbarshi."


Ta kasa tunana komai, k'arshe ta yanke shawarar bashi lemo da snacks kawai tunda suna da shi.

Shiri tayi alwashin yi sosai akan zuwan na shi. Ba su kara yin waya ba tun bayan wayar da sukayi, da rana.



Wani abu da ya da ya wargazawa Hafsah shiri, wanda badon zuwan Ukhasha ba babu abinda zatayi farinciki dashi kamar shi, amma sai zuciyarta ta kasu biyu gefe na jin dad`in hakan gefe kuma naga tunanin gudun samun matsala. Wato abin ba komai bane fa ce zuwan _Jamila_ a ranar.


Misalin k'arfe uku da rabi daidai na yamma, lokacin Hafsah na cikin toilet, don tayi alwashin shiryawa da wuri, ba zata b'ata mishi lokaci ba, sannan tayi alwashin zata nuna mishi soyayya daidai gwargwado yadda zai fahimci tana son shi itama.


Tana cikin band'akin taji sallama daga palourn mama kamar anyi bak'uwa. Bata damu ba take wankan ta a tsanake.

A falon kuma, mama ce zaune ita da mufida, tana mata tausa a k'afa, sukaji anyi sallama da wata iriyar muryar da ta sakasu juyawa duka, don basu gane wanene mai muryar ba.

Mama wata hamshak'iyar babbar mace ta gani, a cikin falonta, wacce ita a ganinta tafi mata kama da irin mata 'yan siyasa.


Mufida kuwa idonta ne yayi wani harr, sai da mai sallamar ta k'aras Shigowa sannan ta gane ta, don sun ganta Kwanaki ita da su yaya Hafsah.

Mama ce tace mata, "sannu da zuwa, zauna mana."
Ta tsuguna ta gaida maman kafin ta zauna a kujerar da aka bata.
Abun ya bawa mama mamaki matuk'a, kafin ta kai ga tambayarta wacece, ita taji tanacewa.
Mama, Hafsah na nan."?
Eh tana nan inji mama, tana k'ara kallon Jamila.

Sannan ta kalli mufida, "Jeki ki kira Hafsan."

Maman taga alamun kamar mufida tasan bak'uwar, amma babu damar ta tambaye ta, sannan da taji wajen Hafsah tazo, sai tafi alak'antata da abokan aikin Hafsah. Amma kuma taji kamar tasan muryar, amma ta manta a ina."?

Sanda mufida ta shigo d'akin hafsah na shirin fitowa daga toilet d`in, don haka ta d'an jirata ta fito.
"Yaya kinyi bak'uwa.
Hafsah na tsane ruwan jikinta da wani towel d`in banda wanda ta d'aura, ta kalli mufida. "Bak'uwa kuma."?
"Eh, Wannan da muka gani a park dinnan ce.!
Gaban Hafsah yayi wata iriyar bugawa.
"Toh, jamila!!
Ta fad'a a hankali.
Sannan ta goge fuskarta kafin ta kuma cewa, "Kice ina zuwa bari na shirya."

Tunda aka, fad'a mata zuwan bak'uwar taji jikinta yayi sanyi.

Da kyar ta tattaro nutsuwa, ta shafa mai sannan ta dakko kayan da tayi niyyar sakawa tasa.

Bata tsaya shafa ko da powder ba, shima kafin ta k'arasa sai da mama ta leko ta.
"Hafsah kiyi sauri mana kin barta tana jiranki."?

"Mama gani nan, yanzu zan fito." Ta bada amsa da haka.
Maman ta k'ara kallonta sannan ta juya ta fita.


Leshin ya amshe ta sosai, tayi kyau duk da bata shafa komai ba, d'an kunne da agogo kawai ta saka, sannan ta fito palourn bayan tayi amfani da turarukan ta.

A palourn sunyi shuru, duka, sai Jamila da jefi jefi take kallon wasu shashi na palourn.
Gidan ya chanja sosai ba kamar yadda tasan shi da ba, an sami cigaba a tsarin gidan da komai ma.


Mama ce ta gaji da hasashen son gano wacece, don haka ta kalli Jamila tana murmushi tace, "Um kema wajen aikin naku d'aya da Hafasan ne."?

Jamila tayi yar dariya sannan tace, Aa, mama baki ganeni ba koh."?
Mama ta jinjina kai, naga kamar na san fuskar koh kina zuwa gidan ne.
Babu jiran komai Jamila tace, "Mama Jamila ce fah."
Tana murmushi.




Mama kallonta ta tsayi sosai, kallon mamaki da tambayoyi, da k'yar ta d`auke ido, tace tana 'yar dariya.

Laa, ai ban ganeki ba sam, ashe kece."
Daga nan ta rufe bakinta.

A Kofar shigowa daga waje ta palourn, Basheer ne ya shigo da sallama.
Mama ta amsa mishi, ya k'araso ciki, daidai lokacin kuma Hafsah itama ta fito daga d'akinta tana takowa zuwa cikin palourn.

Sai da Basheer yazo Tsakiyar palourn sannan yaga fuskar bak'uwar don kujerar da take kai cikin falon take kallowa, sai kuma yaga Hafsah ta fito tana fara,a cikin shigar da tafi kama data fita, badon bata saka mayafi ba, sannan yaji cikin fara,a tana ambaton sunan Jamila.

"Ah, Jamila Sannu da zuwa ashe kece.!!

Maganar data saka Basheer, juyawa ya kalli Jamila sosai.


Ta ganshi itama. Amma basu yiwa juna magana ba, ya nemi guri a kujera 1 _seater_ ya zauna.

Yana bin Hafsah da wani kallo na tuhuma lokacin da take cewaJamila, "shigo ciki mana."
Jamila ta mik'e ta bita. Mama bata ce musu komai ba sai kallo da tabi Jamila da shi, sannan ta k'ara sauke kallon akan Basheer.

Suna nesa dasu, bakin Basheer ya bude rai a b'ace yace, "Mama wai meyasa Yaya zata dinga yin irin haka ne."

Mama ta gane akan me yake magana, amma sai ta cigaba da kallonshi don neman k'arin bayani.


Meyasa dole tace sai ta kula waccan, bata ganin yanzu ba da bace, kinga ta gayyato mana ita gida koh."?

Mama ta danyi murmushi sannan tace, "Haba Basheer ai ba,a gudun mutum a duk halin da yake ciki, kuma ni yarinyar shekarunta nawa rabon da ka ganta a nan gidan, tun sanda akace _tabar gidansu fah._ Ba yawo sukayi da yayarka ba bare kace janta take suna fita."

Basheer ya sake bata rai, "Nidai mama bana son tana kulata bare har ta dinga zuwar mana gida, dama na sani tun ranar da muka ganta a park, Yaya ta wani rikice data ganta, saida taje sukayi magana sannan taji dad`i, shine fa sukayi exchange numbers"

Mama ta d'anyi shuru kafin tace, "Ba fad'a ya dace kayi ba, bayani zakayi mata yadda zata fahimta, amma ka fara zuba ido kaga tunda ai yau ka fara ganin tazo gidan koh."? Kuma ko babu komai Hafsah fa yayarka ce dole ka bi ta a hankali."

Basheer yayi shuru yana had'e rai, _shidai sam bai gamsu da zuwan Jamila ba, kuma har su shige daki ita da yayarshi._


A cikin d'akin kuma, suna shiga Hafsah cikin farin ciki, ta nunawa Jamila gefen gado, "Zauna mana."

Jamila tayi murmushi sannan ta nemi guri ta zauna.

Hafsah cikin rawar jiki ta fito don nemawa Jamila ruwa.

Tana fitowa palourn kai tsaye hanyar kitchen tayi. Basheer ya bita da kallon Takaici, ta zubo mata snacks da dambun nama da basa rabo dashi a, ta had'o da lemo da ruwa. Sai da tazo zata wuce su Bashir yayi mata magana murya a dak'ile.
"Yaya.!
Bata amsa ba ta juyo.
"Yanzu sai da kika gayyato wannan gidannan koh..."?

Jin abinda yake fitowa daga bakin shi ya sata yin gaba, don bata son ma ta saurare shi.


Basheer ya cije leb'e don matuk'a ta bata mishi rai, ya zabura zai mik'e ya bi bayanta amma mama ta hana shi.

Ta daga mishi hannu, "Bari Basheer kada ka bita."

Ranshi ya k'ara b'aci ya zauna shuru ya jingina sosai jikin kujera, bai fi minti d'aya ba, ya mik'e yayi waje mama ta bishi da kallo.


Niyyar ficewa yayi daga gidan gaba d'aya don haka ya nufi hanyar waje kai tsaye.

Yana bud'e k'ofar gate d`in wani Napep na tsayawa a k'ofar gidan nasu.
Bashir na k'arasa fita yaga kamar ana d'ago mishi hannu

Please Login or Register in order to submit comment