Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nata, idon Fadwa akansu, zatayi magana irin ta zolayar data saba ya kafe ta da ido. "
Zoki mana photo, sai kiji dad`in kallon mu sosai."
"Kai Yaya ni baku nake kallo ba.!
Ta matso ta amshi wayar, tayi musu, sannan ta mik'a mishi kayarshi.
_Ya karb'a sannan yaja hannun Mahseem, suka fita, tana mishi hira.._



📝
*HAJEEYAH KHAREEMERH*


♥️♥️♥️♥️
*ZAZZAFAN SO*
(masoyin k'warai)
*Cigaban littafin Zazzafan so*
*(Guba ne)*
💔💔
*By:*
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah khareemerh )*
*Dedicated to Unique in your love heart group members.*
📄 *48- 49*
*Yaune,* suke yinin, Fateemah, sun kacame, a wajen biki, ana ta rawa...
Bikin na matuk'ar dad'i a gurinsu, sun had'u duka 'yan matan, har da matar Nazeer ma, anata rawa, da yake, yinin iya mata ne babu mazaa, ko ango bai halarci wajen ba.
Adaidai wannan lokacin kuma Ukhasha nata kiran number Hafsah tana ringing amma ba,a d'aga ba. Da ya kira karo na uku, sai ya hak'ura kawai.
Yayi shuru ya zuba wa _number_ ido, tunani yake kodai, ya hak'ura ne."? Sai kuma yayi wani tunani. _"A yadda take, kuma tana irin wannan aiki a media, dole baza,a rasa, masu damunta da kiraye-kiraye haka ba. Saboda haka zai jinkirta zuwa wani lokaci kawai._
Zai cigaba da addu,a idan da alkhairi akan abin, Allah ya sauk'ak'a mishi samunta. Wani tunani mara dad'i ya d'arsu aranshi. _Yanzu idan an riga an bada ita fah?_
_"a,uzubillah_
Ya fada a fili, bai ma san ya zai kwatanta halin damuwar da zai shiga ba idan haka ta faru..
Da Wannan tunanin kuma ya shiga wani tunani, na daban, wata zuciyar ta karanta mishi.
_To ita yarinyar mutane da kabar ta da damuwa akanka, ya zakayi da ita.. Ko kana ganin zaka samu yadda kake so, alhanin kana da alhakin wata akanka."?_
A hankali ya furta, _"Allah ya gani bana sonta, bazan iya zama da ita ba._
_To ka sama mata mafita, tunda kana kokarin kulla taka soyayyar a wani waje._
Wata zuciyar ta fad'a mishi haka.
To wacce irin mafita, menene mafitar."?
Ya tambayi kanshi.
Kamar an tsikare shi ya jawo wayarshi, ya danna kiranta.
Cike da farin ciki ta d'auka.
Tayi mishi sallama, ya amsa cikin sakin fuska. Tana mamakin sauyawar shi, cikin kwanakin nan.
"Bahijja!!
Ya kira sunanta.
Na,am.
Ta amsa ad`an sanyaye don tana tsoron abinda zai fito daga bakin shi.
_Sau dayawa indai zaiyi mata magana mara dad'i yafi bata hankalin shi, da kuma jawo hankalinta._
Yaushene ma kika ce min zaki cika _twenty years.?_
Farin-ciki ya mamaye ta. _Kodai party zai had'a mata ne."? Sai kuma ta tuna irin gidansu, sannan ta tuna data gayyace shi partyn graduation, yace mata baya zuwa party._
Tana son jin abinda zai fad'a mata don haka tace, "Nan da _three months._
"Okey.." yace mata kawai.
Tayi shuru tana son taji k'arin bayani.
_Wato ma ko 20yrs yarinyar bata cika ba. Ya fada a zuciyarshi. Baya son ta shiga damuwa a k'ananun shekarunta. Tabbas ma yaga tsaurin ido da k'ok'arin yarinyar, da har ta iya furta mishi tana sonshi, ashekarun haihuwa fa zai iya bata goma sha uku fa. Sai kuma ya tuna _shekaru ba sune abun dubawa ba indai da so._
"Meya faru neh Dear."?
Tambayeshi, jin yayi shuru babu k'arin bayani.
Babu komai, kawai na tambayeki ne.
Ta danyi jim, kafin tace, _"Okey"_
"Yaushe zaku fara lecture, a makaranta."?
Ya tambayeta.
Nan da _2weeks_ fah. Tana jin dad`i a ranta, yana janta da hira.
"Ina mamanki."?
"Tana nata room."
Ta fada da mamakin tambayar kodai wani abu ya k'ara faruwa neh. Kafin ta samu damar magana,
ya saita muryar shi, cikin nutsuwa ya fara magana yace.
"In tambayeki Bahijja ."?
Ta danyi shuru kafin tace, "Um."
"Please ki fahimci tambayata kada ki _getting dina wrong."_
Cikin sanyin jiki tace, "Toh inaji."
Kasan zuciyarta na tsoron abinda zai fito daga bakinshi.
Meyasa, da maman ki ta nuna bata son mu,amularki dani baki d`auki mataki ba.??
Tayi d'if don bata da amsa.
"Uhum."? Ya sake ce da ita.
"Me ta k'ara yi maka ne,?_was something wrong happened again.?_
Ta tambayeshi da damuwa.
"No, no no, kawai naga ta damu akan abin ne, kuma nima nayi tunani to this time ya dace ace muyi mata biyayya, mamanki ce tana da hak'k'i akanki, kuma zata fiki sanin what's right for you."
Ya fad'o maganar kai tsaye.
Ai kawai sai ya fara jiyo shashshek'ar kukanta. "Why all this dear, kawai kace abinda mama ta maka ne, ba zaka iya d'auka ba, but since when muke tare da kai and you knew that mama bata so kuma bakayimin wannan tuhumar ba sai yanzu."
Ahankali yace, _"Calm down plz, ki daina kuka mana._
Sukayi shuru kafin yace, _ Bahijja Kinsan girman iyaye kuwa.."?_ _Kinsan girman da Allah ya basu.? Mamanki nada hak'k'i akanki, duk abinda bata sa mishi albarka ba cikin rayuwarki bazai yi miki amfani ba yadda kike so. Ina son muyi magana da ke, amma ki cire aranki don cewa abinda tayi min ne yake damuna, wallah is not, kawai naga time yayi da za,ace kin mata biyayya, ke ba yarinya bace, please mu hak'ura da wannan alak'ar, mu chanja mata suna, ki dawo k'anwata zaifi mana dad'i kuma mamanki zata fi amsar hakan pleasse!!_
Kamar ya bata sakon mutuwa, haka kalaman nashi suka shige ta fiye da koyaushe da yake fad'a mata irinsu, a muryarshi ta fahimci da gaske yake ya gama shirin tsinke zaren alak'arsu. Sai ta fashe mishi da kuka mai tsuma rai, shi kanshi sai da ya cire wayar daga kunnenshi sannan ya mayar.
Zuciyar shi ce ta karanta mishi, _"Ukhashatu idan fa tausayinta zaka tsaya, sam ba zaku je inda kake son aje ba._
_Cikin dakewa yace, "Ki daina kuka, ke banda abinki mene abin kuka cikin wannan maganar, ni da ke fa bamu muke da ikon kanmu ba, kiyi tunani, akan abinda nake hango mana, alak'ar yaya da k'anwa ita tafi dacewa damu fiye da wacce muke yanzu."_
Ta saki ajiyar zuciya, "Me nayi maka laifin me nayi maka."?
"Ya salam, Bahijja, me kwa kika min, me zaki yi min, me yasa kike tunanin kinyi min wani abu."?
Cikin bacin rai ta tace,
" Eh mana, saboda naga gaba-d`aya ka nuna ka gaji dani, baka son cigaba da kulani koh, wai baka ganin irin son.."
Sai ta k'ara saka kuka, tana tausayin kanta, _wai mene haka ne, wane irin soyayya aka jarabce ta dashi."?_
Kiyi hak'uri kinji, ina sama mana maslaha ne ni da ke, bama son gaba ki zargeni."
A fusace ta cafe zancen, _Idan kayi aure ba."? Saboda ni baka buk'atata cikin rayuwarka, baka sona._
Yayi shuru, yana juya zancen, kuma fa, hakane, zancenta baya son ta zarge shi, ranar da zata wayi gari an d'aura mishi aure. Amma yanayin maganar ta bashi mamaki, hakika bata cikin hayyaci da har ta iya fada' mishi magana da irin wannan sigar, da babu _respect._
"Bansan me zance miki ba Bahijja, amma kin san halin da ake ciki, ina fad'a miki ba ba tun yau ba, Abba na yayi min zab'i!!
Babu shiri ta dawo da kukanta. _Kenan zancenta na kan hanya aure zaiyi._
Don girman Allah, kiyi hak'uri kiyi addu,a, Allah ya had'aki da mafi alkhairin zab'i cikin rayuwarki, ki daina kukan nan, ni ba ce miki nayi mu rabu ba fa, na sama mana mafita ne, kuma na miki alk'awari zan zame miki Yayan da xakiyi alfahri da shi kiyi hak'uri kinji.!!
Abinda ya shiga fada mata kenan, don ya rasa, abin cewar komai daya tanada don ya furta mata ya fad'eshi, yasani rabuwarsu ba zata zo da sauki yadda yake so ba.
"Nagode, Nagode, abinda tace mishi kenan. Ta katse waya.
Yayi jim yana tunani, gwara taje tayi tunani, don bashi da wani abin k'ara mata akai, ya tabbatar idan ta nutsu zata sakko kuma yayi kudirin bazai k'ara nemanta ba, gwara ta fara koyar rayuwar da babu shi. Amma bari ya k'ara da tura mata sakon waya yana so ne ta yarda da abinda yake zuwa mata dashi ta laluma, kafin ya janye jiki, ta k'arfi idan yaga abin ya faskara.
_Wallahi ban tab'a sawa raina zan wulak'anta mai so na ba.. Bahijja ban san ya zanyi ki fahimce ni ba, amma ki d'auka wannan shine maslaha agaremu, kiyi hakuri kiyi tunani akan maganata._
Iya abinda ya iya rubuta mata kenan.
Ta duba sakon, tayi shuru tana tunanin abubuwan daya ce, da kuma abinda zaifi zamar mata mafita..
_______________
Tazarar kwanaki biyu ya bawa Hafsah, bai k'ara kiran number d`in ba sai ranar litinin.
Haka ma, Bahijja tun ranar bata k'ara kiran shi ba, hakan ya masa dad'i, _gwara ta saba,_ amma a k'asan zuciyarshi akwai tausayinta fal.
*HAFSAH*
_______________
Tana kwance, tana hutawa, ta gajiyar bikin da suka sha, a yammacin ranar litinin. Danna wayarta take, tana k'ara kallon photonan da sukayi.
Kira ya shigo cikin wayar da wata number, ta d'aga ta kara a kunnenta.
*UKHASHA*
______________
Ba k'aramin farinciki yaji ba, ganin an d'aga kiran nashi, ga seconds har sun fara tafiya.
"Assalamu alaykum."
Ya fad'a cikin nutsuwar murya.
Muryar ta shiga cikin jikinta sosai.
"Wa alykm salam."
Ta amsa da k'aramin sauti.
"Barkanki da yamma, ina fata kin yini lafiya."
Damuwarta shine taji da wa take magana, amma babu yadda zatayi dole ta amsa gaisuwar shi.
"Lafiya lau Alhamdulillah."
Tayi saurin tambaya. "Am sorry ban gane me magana ba."
"Okey hakane." kai tsaye yace. "Sunana _Ukhashatu Abubakar_
Tayi shuru tana son ta tuno ko tasan me irin sunan.
Bai barta da wannan ba sai ya k'ara mata da, "Ina magana da Hafsah ne koh."?
Ahankali tace "Eh itace. Sai dai banajin ni Hafsan kake nema."
Muryarta tayi mishi dad'i don haka ya kashingid'a, sannan yayi murmushi me sauti.
"Me yasa kika ce haka."?
Mamakon ta amsa, sai tace cikin k'osawa.
"Kafad'a min wanene kai yadda zan gane inaga zaifi koh"?
"Ayi hak'uri toh, amma na fad'a miki sunana.
"Bansanka ba ai."
Ta fad'a kai tsaye.
Ya k'ara tattara nutsuwar shi.
"Naga kin gaji dani bari na miki bayani."
"Hmm.." tace mishi, kuma kamar yasan hakan ne.
(Muryarshi tafi komai jan hankalin ta.)
"Sunana Ukhashatu, kiyi hak'uri na kiraki bada izininki ba."
Yad'an dakata, yayin da ita kuma ta bada dukkan nutsuwar ta gareshi.
Bazan boye miki ba, samun number ki ba abu ne mai sauki ba, _i witnessed that._
"Kiyi hak'uri naga babu hanyar da zan iya miki magana ne idan ba ta wayarki ba."
Tayi shuru don babu abin cewa.
"Na rok'i abani number ki ne sai kuma nayi dace aka bani.
Waye ya baka."?
kiyi hak'uri zanyi miki bayani gaba.
"To ina ka sanni ni.?
Hmm, na ganki a wurare da dama."
ka fad`amin, kawai."
Na ganki a television ne kina _program_ d'inki."
Bata san sanda tayi murmushi ba tare da cewa sai kuma ina."?
Shima murmushin yayi, zan fad'a miki sauran amma ba yanzu ba.
"Hmm, ka fad`amin wanda ya baka number ta.
"Allah ne ya bani."
Ya fad'a da zolaya.
Hmm, _I knew that._
Tace mishi.
Ya k'ara yin murmushi, "Yawwa don shi na rok'a kuma ya bani."
Bata k'ara cewa komai ba.
Suka danyi shuru.
Sannan tace, "Okay toh sai anjima."
"Kiyi hak'uri by time zaki gane wane ni, sannan ki min alfarma guda d'aya."
"Tame fah."?
"Kiyi saving d`in nombar nan don Allah.
"Banyi alkawari ba.!"
"Girmanki ne ai, nagode, ki huta lafiya.
Ya katse wayar lokaci d'aya.
Ya barta da tunani.
Wanene wannan, me nutsuwa, dad`i da kuma sanyin murya."? Me yasa ya kirata ya mata haka."? Babu alamun k'uruciya a Yanayin muryarshi da zantukan shi, bare tayi tunanin rainin hankali ne irin na samari.
Yace, _by time zata gane wanene shi._
To Yaushe yake nufi kenan."?
Yace _Allah ne ya bashi number ta._
Yana nufin ba zai fad'a mata inda ya samu ba kenan.?
Kai akwai alamar tambaya.!!
Ita ko irin mutanen da ke kiranta ne, ba haka ta saba amsa gaisuwar su ba, yawanci ma anfi kulata a chat ko ta email. Idan kuwa aka kirata kai tsaye za,ace _muna jin dadin shirinki, kina burgeni wallahi, abubuwa makamantan haka dai._
_Amma shi fa?_
Sam ba da haka yazo mata ba, sai ma afuwa da yake ta nema akan ya kirata, bada izini ba. Kuma yace a TV ya ganta, ta kasa yarda da hakan.
Duk yanda akayi yayi mata kyakykyawan sani, data gaji da b'ata lokaci wajen tunane tunane sai kawai ta share abin, amma fa takan tuno muryarshi lokaci zuwa lokaci.
Bangaren shi, farin cikin daya shiga bazai misaltu, bisa jin muryar ta da yayi ayau d'innan.
"Alhamdulillah Alhamdulillah yake ta maimaitawa. Azuciyar shi, yana addu,ar Allah ya mallaka mishi ita.
Kowa na gidan ya gane yana cikin farin ciki yau, haka kawai ya fita yayiwa driver ( _wanda ya kaishi gidan baffa_) kyauta, bisa tuno kalaman shi masu hikima.
_Ranka ya dad'e ai aure yana cika darajar mutum ne.. Tunda manya sun nuna suna so sai ayi musu kodan biyayya._
To shi ba auren yayi ba ma, amma farin cikin da
yake ciki Allah ne kad'ai yasan adadinshi.
Bai k'ara kiran ta ba, har washegari, gwara ya barta ta huta, tunda babu sanayya a tsakaninsu, bata sanshi ba sam. Kada ta gaji da shi.
Sai da daddare ya kirata bayan kwana biyu, batayi saving number d`in ba, amma muryarshi ce tasa ta gane shine.
"Assalamu alaykum.
Ta amsa mishi itama.
"I hope ba kiyi bacci ba na tashe ki." Ya fara da haka.
"No." Tafad'a.
"Kingane mai magana."?
Azahiri amsar ita ce "Eh, amma saboda ta ja _class_ sai tace, "Aa."
Yayi murmushi,
_"To Ukhasha d'innan ne dai mai nacin nan."_
Ya bata dariya babu shiri. _"Hmm_ tace mishi kawai.
Yayi k'asa da murya, yana rok'o.
"Please ki taimaka kiyi saving number nan mana."?
"No banyi alkawari ba."
"Meyasa."
"Saboda bansan ka ba."
Cikin marairaice murya, irin ta wanda ake tuhuma yace,
"Wallahi sunana ukhasha, ba karya na miki ba.!!"
Ya bata dariya sosai, wannan wanne irin mutum ne, mai barkwanci haka Allah ya had'ata dashi..?
Gashi sai yayi magana kamar bashi yayi ba, da nutsuwa a muryarshi sosai haka daga jin shi babba ne da saita ce, _irin rainin hankalin samari ne._
"Hmm, inda ka sami number ta shi nakeson in sani."
Ta fad'a bayan ta gimtse dariyarta.
"Oh tun a duniya ne fah na samu.!!
Sai da tayi da gaske sannan ta tsayar da dariyarta wannan karon.
"Hmm, Bazaka fad'amin ba koh."?

Cikin k'asa da murya kuma a nutse yace, "kina burgeni Hafsah.
Muryar da kiran sunanta da yayi sukayi tasiri a zuciyarta..
Ina son sunanki, sunan mamana ne dake, fah.
"Allah sarki. "Haka tace kawai.
"Bari na barki kiyi bacci kada na hanaki bacci, Allah ya bamu alkhairi."
Ya kashe ba tare daya jira tace wani abu ba.
Ta zubawa numbobin shi ido, wane ne shi.. wanne irin mutum ne Allah ya hadata dashi, ya sanyata dariya lokaci d'aya ya barta kuma."?
A take, taji ya shiga ranta, duk da wani bangaren na zuciyarta na kwab'arta akan _kada ta zak'e, daga had'uwa baki sanshi ba.!!
_Funny ukhasha._
Haka taga hannunta ya rubuta wajen saving d`in number shi.
Allah ne ya kawo mata shi, lokacin da tunanin Jamila yayi mata yawa, saboda damuwar tana kiran number bata shiga, gashi 'yar wayar da sukayi har yasa ta manta...
Ta runtse idonta, sai taji tana son ta tuno kamannin shi, Ahankali take imagine ( _ayyana shi_) d`inshi, da wani ustazun mutum, mai cikar kamala...
Kwanaki sun fara tafiya, har ta saba da kiranta da yake, su gaisa, amma yawanshi a tak'aice, sai dai ba sa waya su gama bai sata dariya ba. Sai dai wani lokacin idan ya kirata takan share, idan kuwa ta d'aga kiranshi na gaba sai ya nemi afuwar ta, "Ayi hak'uri a taimaka kada a gaji dani d'indai, in sha Allah kin kusa gane wanene ni, don nasan hakane yakesa kike doubting akaina.!!
Wannan wanene haka, ya kware wajen _reading mind d'inta._ Hakika ta matsu ta ganshi, Gashi kullum sai dai yace, mata ta kusa sanin _wane shi,_ amma har yau bai tab'a neman alfarmar zai ganta ba shi, sai ta fara zargin abubuwa da dama..
Abinda bata sani ba shine, ya matsu sosai ya ganta, amma yana shakkar tambayar ta ne kada taga zak'ewar shi..
Yau ta kuduri niyyar kiran jamila a waya, suyi magana ko na mintuna ne ta haka zata gane idan har zata ci nasara akan jamilar.
Bayan missed calls in da tayi mata har wajen guda biyar, k'arshe dai jamilar ta biyo kiran.
'Sun gaisa sosai, sai kuma Hafsah taji kamar ran Jamila a b'ace yake, saboda yadda taji muryar ta.
Gashi kuma gefe guda ta rasa ta yadda zata cigaba da hirar tasu, domin bayan gaisuwar basu ce komai ba.
Jamila ce tace, "Hafsah H Hamid, kin gama school koh."?
"Eh Jamila mun gama Service ma."
Tayi murmushi, "Gud."!
"Kina aiki kenan."
Eh Inji Hafsah, a takaice ta bata amsa saboda tambayoyin yana tuna mata baya ne, kuma sai take ga kamar tono halin da jamilar ke ciki ne a yanzu.
Can ta jiyo Jamilar ta kuma cewa, tana wani murmushi..
"Hmm Hafsah kenan ai zan kawo miki ziyara, Idan na shigo unguwar namu."
Gaban Hafsah ya fad'i jin hakan, saboda batayi tunanin Jamila zatace zata zo gidan su ba.
Amma sai itama tayi murmushi kawai tace, "Okey thanks sai na ganki."
Okey Inji Jamila, sannan tace "Bye."
Ta kashe wayar.
Hafsah tayi ajiyar zuciya kawai, tayi shiru tana tunani, anya abinda take son yi kuwa zai yiwu..?
Ance,
_"Duk wanda yai nisa baya jin kira.!_
Sai taji tana k'ara godewa Allah bisa, yadda ita rayuwarta bata tab'arbare ba..
Tasani ba dabarar ta bace ko kuma dabarar iyayenta, kawai dai shiriyar Allah ce wacce yake shiryar da wanda yaso.'
"Alhamdulillah alaa kulli haal."!
Ta fad'a ahankali tare da yiwa kanta murmushi.
___________________
Yana kwance kan gadonshi, yana kallon sama, ya dafe kanshi da Hannaye biyu, wani irin Ciwon kai yake fama dashi tun tashinshi daga bacci, azuci yake karanto addu,a sannan ya shafe kan nashi.
Ya duba agogo, karfe shida na yamma magriba ta kusa.
Don haka ya mik'e zaune, saboda yamma ce lik'is.
Koda aka kira sallah ma bai fita ba, adakinshi yayi sallah har zuwa daf da isha'i sannan Fadwa tazo tana buga k'ofarshi.
Abude kofar take Don haka ta jiyo shi yana cewa, "Abude yake k'ofar ki shigo."
Duk da bai san wanene ba, yasan bazai wuce ita bace.
Ta shigo da sallama, ya amsa ahankali, yana kwance a dandaryar k'asa, akan dadduma inda yayi sallah.
Ta sami gefe ta dan zauna sannan ta fara mishi magana.
"Sannu Yaya."
Duk da bai fad'a mata ba tasan bashi da lafiya ne.
"Yawwa."
Yace mata.
"Me yake damunka, ya nuna mata kanshi."
"Oh sannu, Hajiya tace baka ci abinci ba, yanzu me za,a dafa maka."?
"Ki dafa min koma mene."
"A,a dai Yaya ka fad'i me zaka ci."
"To ki bari kawai"
Najwa tayi shiru, abin ya bata mamaki da takaici, amma data tuna halinshi sai kawai ta mike ta fita.
Ta fahimci baya son adameshi idan har yana wannan ciwon kan, amma ita ta tambayeshi ne saboda taji irin abinda yakeso, kada tayi mishi abinda baya so.
Har ta tafi sai kuma ta dawo adan tsorace tace, "Um wai kasha magani."?
Yasan babu wanda ya sata ta tambayeshi tunda babu wanda yasan bashi da lafiyar idan ba yanzu da aka ga bai fito ba tun yamma.
"Zansha."
Yace mata kawai.
Ta juya ta fita..
Fadwa rasa abinda zata kawo mishi tayi, sai kawai ta hada mishi kayan tea, ta dafa mishi Indomie, ta kawo mishi.
Ya mike yana kallon abincin, ko nazarin me yake oho, ita ko tana gefe ta zauna.
Har kusan minti 3, sannan taga dacewar ta ta had'a mishi, nan ta hada mishi komai, sannan ta mik'e zata fita.
"Thank you."
Yace mata ahankali.
Bata juyo ba kuma bata, ce mishi komai ba ta fice, tana murmushi.
_Wato zaman da yayi jira yake tayi serving d'inshi ne, amma kuma yaki mata magana._

Ya samu ya ci abincin da tea d'in sosai, sannan ya mike yayi sallar isha'i, ya dan jima a zaune yana jan tasbaha, sannan ya d'akko maganin shi yasha.
Wayar shi nacan gefe tana chaji amma jin kiwuyar dakkota yake yi. Sau biyu yaji kira na shigowa amma kuma bai son tashi bare ya d'akko.
'Wasa wasa Ciwon ya dauke shi kwana biyu, har sai da Hajiya ta matsa aka rakashi asibiti, an mishi 'yan gwaje- gwaje, babu komai, sunfi ta,allak'a hakan, da yawan ayyuka, da yakeyi babu hutu.'
Yad'an sami sauk'i babu laifi, abokan shi sun zo dubiya, ranar ne ma yaji ya k'ara warwarewa.'
Duk kwanakin nan kusan hud'u sam bai kira Hafsah ba, a ganinshi, gwara ya bari sai ya sami sauk'i sannan ya kirata, duk da cewa yasha kewarta sosai da sosai.'
__________________
Itama nata b'angaren tayi mamaki sosai, tunane-tunane dayawa sunzo, cikin ranta ciki kuwa har da fargabar "Shin mai ya jawo shirun nashi haka.."?
Amma cikin k'arfin hali irin nata take ta kokawar, kawar da tunanin, ita ala tilas, bata son ace, abinda takeji game dashi _'Kewar shi ce.'_
Ganin an d'ebi kwanaki haka, yasa har ta fara wani tunani, 'wai ko ta gwada kiranshi ne."?
Nan da nan tayi saurin kawar da wannan tunanin, _yaushe suka dad'e..? Yaushe sukayi sabon da har zata damu haka."?_ Sai taji takaicin hakan ma.
Ak'ok'arin tayi watsi da tunanin nashi ne, yasa ta d`akko wayarta, ta kunna Data, facebook ta fara dubawa inda taci karo da wani abin mamaki... Sunan Yusuf ta gani wai ya turo mata _'friend request.'_
Taji abin wani iri, meye hadin biri da gada kuma."? Kodai bai san ita bace? Kai ya sani.. Yasan sunanta sarai, kamar tayi delete d'in request d'in sai kuma ta fasa, ta fita daga facebook din gaba-d'aya ma.
Bata wani dami ranta da tunanin shi ba, saboda bata da wani damuwa akanshi sam, ta dai san yanzu baya k'asar, don labari baya b'uya, har labarin Basma tana dashi, duk da cewa ba bibiyar rayuwar su take yi ba, amma hakan baya rasa nasaba da yadda har yanzu suna tare da wasu daga cikin 'yan makarantar su ana zumunci.'
Aisha Daheer tayi aure wata biyar kenan da bikin, dama yawancin zantuka a wajenta Hafsah keji.
Duk da ba d'auka take yi ba, takan watsar da zancen ne a inda tajishi, domin ita a yanzu ta kama wani layi daban na rayuwar ta, _kowa tasa ta fishsheshi._
bata da wani abin buk'ata daga garesu ( _Yusuf da b
Basma_ ) dukansu...
__________________
"Hello.!!
Hello, Barkanka da yamma
Barka dai
" I hope you're fine naji kwana biyu baka picking call."
Ya d'anyi ajiyar zuciya, wato ita dai bata tab'a watsar dashi, duk da yanzu ta k'arfi da yaji ya canja mata ra,ayi akanshi, amma har yanzu sabon nan nata na kiranshi yana nan har yanzu.
"Hmm, Bahijja kenan, bana jin dad'i ne kwana biyu."
"Subhanallah meya sameka.?
"Ciwon kai nake fama dashi amma naji sauk'i sosai ma."
Ta d'anyi ajiyar zuciya ahankali,
"Allah ya k'ara lafiya sannu fa."
"Yawwa thank you."
Suka d'anyi shiru, can tace, "ko inzo dubiya ne."?
"No naji sauki fa nagode ba sai kin zo ba."
"Hmm, kai dai kawai baka son nazo ne."
"No ba haka bane."
"Hmm, tayi murmushi kawai."
"Okey shikenan Allah ya k'ara sauk'i."
"Amiin k'anwata."
Ita abin ma dariya ya bata duk da gefe guda tana tausayawa kanta, amma sai taji tayi dariya kawai, ya ta iya da kaddara."?
Shima dariyar ta danji yayi,
"Sai anjimanka."
"Okey thank you."
Kiran nashi da tayi, ya k'ara sashi jin kewar Hafsah, sosai, ya kalli agogo, yanzu ne daidai lokacin da takeyin program d'innan a television, ya mik'e a hankali ya nufi falon Hajiya, cikin d'an mamaki Hajiya ta kalleshi, ya nemi guri ya zauna, sai dai abin taikaici ba tashar suke kallo ba, ya dai daure ya zauna, har zaman ya gundure shi, ya tashi kawai zai fita sai kuma yaga Hajiyar ta dauki remote ta canja tashar zuwa can d'in.
Sai kawai ya dawo ya zauna, nan ma Hajiya ta bishi da kallo kawai.
"Ya jikin naka?"
"Da sauk'i."
Kasha maganin yau."?
Idon shi kan TV yace "Eh Hajiya."
Allah ya k'ara sauki."
"Amiin."
Ba,a fi minti 15 ba, aka gama shirin, yaji dad'in kallon aranshi sai yaji an sauke mishi wani nauyi daga kanshi.
Ya dan zauna kad'an, sannan ya mik'e ya wuce d'akinshi.
'Sai dare sannan yayi tunanin kiranta.'
Tana falo ita da kowa na gidan kiran nashi ya shigo, mufida ce ta miko mata wayar, ta kalli sunan daya bayyana, sai taji sanyi aranta, gefe kuma ya haddasa mata fad'uwar gaba, ko meye dalili oho.
Tana jin kunyar a kirata ta mike tabar su a parlour ta wuce d'aki, ciki kuwa ga abbansu da Mama, amma tasan ita da kanta tafi samun nutsuwa, idan ta keb'e tana waya, ko da wanene takeyin wayar kuwa.
Ganin wayar zata tsinke ne, yasa ta d'aga tare da mik'ewa tayi hanyar bed room d'inta.


📝
*HAJEEYAH*
*KHAREEMERH.*


♥️♥️♥️♥️
*ZAZZAFAN SO*
(masoyin k'warai)
*Cigaban littafin Zazzafan so*
*(Guba ne)*
💔💔
*By:*
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah khareemerh )*
*Dedicated to Unique in your love heart group members.*



📄 *50*







*"Hello"*
Taji yace.
"Hello"
Ta mayar mishi.
Ta taka da sauri tashige bedroom din ta zauna gefen gado.
"Kina lpia."?
Lpia lau,
Kwana biyu kinjini shiru koh.."?
Bata san amsar da zata bashi ba don haka tayi shiru.
"Uhum."?
Yace da ita.
"Um."
Tace dashi.
"Hhum"
Yayi ajiyar zuciya, ya kwantar da murya.
"Hafsah."
Taji kiran ya ratsata, amma sai bata amsa ba.
Shima badon ta amsa din ya kirata ba don haka yacigaba da magana bayan d'an shiru da yayi, cikin nutsuwar murya yace,
"Baki nemeni ba kuma koh."?
Sai taji 'yar kunya, har ta fara k'ok'arin kama kanta da laifi.
"Um um."
Tace mishi,
"Hmm yayi murmushi mai sauti,
"Um um kikace."?
Sai tayi saurin kama kanta, kada fa yaga zak'ewarta.
Ya cigaba da cewa, "Bani da lafiya ne!"
Sai taji gabanta ya fad'i.
Takuma jiyo shi yana maimaita,
"Rashin lafiya nayi Hafsah, wajen _5days_ ina ciwonkai."
"Ya salam."

Please Login or Register in order to submit comment