Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

huta da takaicin wannan bakin ciki
da ya kunsa mini."
Haka ita ma Hayatunnufusi ta fada masa tamkar
yadda Badura ta habarta masa, ita ma tana kuka,
ta fada masa har da kuyangarta ya kashe.

Ta kara da cewa, muddin ba a hukunta Amjadu ba, to, za
ta fada wa mahaifinta Sarki Armanus domin ya
nema mata hakkinta a kan Amjadu.
Allah ya kiyashe mu da sharrin mata. Haka dai
matan nan, Badura da Hayatunnufusi, suka
kalallame Kamaruzzaman da karya suka dauki
laifin duniyar nan duka suka aza wa 'ya'yan nan
nasu, su dai idan asirinsu zai rufu, to, ko da Sarki
zai sa a kashe 'ya'yan, ba su damu ba. Suka rika
kuka suna marin fuskokinsu.
Yayin da Kamaruzzaman ya ji jawabinsu, kuma
ya ga suna kuka, har suna marin fuskokinsu sai
ya yarda da maganarsu. Nan take ya harzuka, ya
cika da fushi har idanunsa suka rika rufewa. Ya
zari takobi ya fita waje da nufin kashe 'ya'yansa...

Yusuf Æbdullâhi Æ Jibaga ke muku barka da shanruwa'29 HIKAYAN KARUZZAMAN DAN SARKI SHAHARUZZAMAN

Yayin da Kamaruzzaman ya ji jawabinsu, kuma
ya ga suna kuka, har suna marin fuskokinsu sai
ya yarda da maganarsu. Nan take ya harzuka, ya
cika da fushi har idanunsa suka rika rufewa. Ya
zari takobi ya fita waje da nufin kashe 'ya'yansa.
Yana fita sai suka yi kicibis da surukinsa, Sarki
Armanus, shi kuma ya zo domin ya yi masa
barka da dawowa daga wurin farauta. Sai ya ga
Kamaruzzaman rike da takobi tsirara, idanunsa
sun juye sun yi jawur kamar gauta, ga kuma jini
yana diga daga hancinsa saboda bacin rai. Ya
tambaye shi, me yake faruwa. Kamaruzzaman ya
fada masa laifin da matansa suka ce Amjadu da
Asadu sun aikata gare su. Ya kara da cewa, "na
yi niyyar zan kashe su a cikin wannan sa'a,
mummunan kisa, domin hakan ya zama misali ga
masu aikata mummunan laifi irin nasu."
Sarki Armanus, wanda shi ma tuni ya fusata da
jin laifin da yaran suka aikata, ya ce "ya dana,
hukuncin da ka dauka ya yi daidai, muna rokon
Allah ya la'ance su, ya la'anci dukan 'ya'ya masu
hali irin nasu." Ya ci gaba da cewa, "amma abin
da nake so da kai shi ne, su duka dai 'ya'yanka
ne, don haka kada ka kashe su da hannunka,
domin idan ka yi haka, abin zai tsaya a cikin
ranka har abada, watakila ma sai ka yi da-na-
sanin kashe su da hannunka da ka yi wata rana,
lokacin da da-na-sanin ba ta da amfani. Domin
kuwa masu iya magana sun ce, abin da duk ido
ya gani shi zuciya kan rike, amma abin da duk
ido bai gani ba, to, zuciya ba ta tunaninsa. Ka
tura hauni ya daure su, ya tafi da su daji, cikin
rairayin hamada, ya sare kawunansu, ya turbude
gawarwakinsu can cikin rairayi."

Kamaruzzaman ya ga cewa jawabin surukinsa
abin kamawa ne, sai ya mayar da takobinsa
kube. Ya nufi fada ya zauna.

ya sa aka kira masa hauni. Shi wannan hauni
wani tsohon mutum ne mai yawan shekaru,
wanda bai taba saba wa umurnin Sarki ba. Da ya
zo, sai Kamaruzzaman ya ce masa, "ka tafi wurin
'ya'yana, Amjadu da Asadu, ka daure su da igiya.
Ka rufe kowane dayansu a cikin akwati, ka aza
wa alfadara akwatuna. Ka tafi da su tsakiyar
rairayin hamada ka sare kawunansu, ka ciko mini
goruna biyu da jininsu, ka yi sauri ka kawo mini."
Hauni ya dukar da kai cikin ladabi, "na ji, na
amsa, Allah ya ba ka nasara." Ya tashi da
hanzari ya fita, ya nufi wurin Amjadu da Asadu.
Sai ya hadu da su, sun caba ado da kaya masu
daraja, za su gun mahaifinsu domin su yi masa
barka da dawowa. Yayin da hauni ya gan su, sai
ya durkusa a gabansu ya ce, "ya 'ya'yana, ku
sani cewa ni, bawa ne umurtacce. Mahaifinku ya
ba ni umurni a kan ku, ko za ku bi umurninsa?"
Suka amsa, "na'am."
Ya tashi ya kama hannuwan kowane daya daga
cikinsu ya daure da igiya, ya saka kowa a cikin
akwati. Ya aza wa alfadara akwatunan, ya hau
dokinsa ya kora, suka fita daga cikin birni, suka
nufi cikin daji. Can zuwa rana tsaka, suka isa
cikin yashin hamada. Ya sauke akwatuna, ya
fitar da Amjadu da Asadu. Bayan ya fito da su
daga cikin akwati, ya ga irin kyawun yaran nan,
sai tausayinsu ya kama shi, har ya zubar da
hawaye. Daga nan ya zare takobinsa, ya ce,
"wallahi zuciyata ba ta so abin da zan aikata a
gare ku ba. Sai dai ni, bawa ne umurtacce, ku
sani cewa, mahaifinku Sarki Kamaruzzaman ya
umurce ni da in sare kawunanku, sa'annan in
cika masa goruna biyu da jininku, in kai masa.
Amjadu da Asadu suka ce, "cika umurnin
mahaifinmu, za ka same mu masu tawakkali ga
abin da Allah ya kaddara bisa kawunanmu, domin
shi ne masani a kan kome."

Suka rungume junansu suna hawaye, suka yi wa
juna ban kwana. Daga nan sai Asadu ya ce da
hauni, "ya kaka, ka yi wa Allah ka fara kashe ni
da farko. Kada ka fara kashe dan uwana, Amjadu
a gabana, domin wannan zai sa hankalina ya
tashi." Amjadu kuwa ya ce da hauni, allambaran
shi zai fara kashewa, domin ba zai iya juriyar
ganin an kashe Asadu da farko ba. Ya kara da
cewa, "ka ga shi kanena ne, don haka zuciyata
ba za ta iya jimirin ganin an kashe shi a gabana
ba. Suka yi ta jayayya bisa ga haka, suna kuka.
Tausayi ya kama hauni, shi ma ya fashe da kuka.

Amjadu da
Asadu suka ce da junansu, "wannan abu ya faru
saboda makircin mahaifanmu, da kuma rashin
bayyana wa mahaifinmu gaskiyar al'amari,
wannan shi ne sakamakon rufa musu asiri da
muka yi. Amma babu tsimi babu dabara face
daga Allah madaukakin Sarki, gare shi muka
dogara kuma gare shi muke neman taimako."
Asadu ya rungume dan uwansa yana kuka, ya
wake wadannan baitoci:

Ya wanda mafaka da wurin kai kara suke gare
shi,
Kai ne wanda ya isa ga dukan abin da ya abku.
Ba ni da dabara face kwankwankwasa ga kofarka
Idan ka juyar da ni wace kofa zan kwankwasa.
Ya wanda taskokin kyauta tasa suke cikin fadin
Kur'ani
Ka amince da mu, cewa alheri dukansa ya taru
gare ka.
Yayin da Amjadu ya ji wakar dan uwansa, sai ya
rungume shi ga jikinsa, shi ma yana kuka, ya
wake wadannan baitoci:

Ya wanda kyautarsa gare ni ta kasance mai yawa'
Ya wanda kyaututtukansa suka suka fi karfin a
kidaya.
Musiba da dai ba ta same ni ba a cikin zamanina
Face na garzayo gare ka ka riki hannuna.
Bayan ya gama waka sai ya juya wurin hauni ya
ce, "na gama ka da Allah, wanda babu wani abin
bautawa da gaskiya sai shi, ka fara kashe ni
kafin ka kashe dan uwana. Domin kuwa ba zan
iya jure ganin yadda za ka kashe shi ba." Asadu
ya yi kuka, ya ce, "a'a, ni zai fara kashewa,
domin ba zan iya ganin an kashe ka a gabana
ba." Daga nan sai Amjadu ya ce, "to, mu
rungume junanmu, fuskokinmu na kallon juna, sai
ya sare kawunanmu a cikin sara guda."
Suka rungume junansu, fuskokinsu na kallon juna.
Hauni ya daure su da igiya yana kuka. Bayan ya
gama daure su sai ya dauki takobinsa, ya ce, "na
rantse da Allah, ina matukar takaicin abin da zan
aikata muku. Ba ku da wani sako da za a kai wa
mahaifinku?"
Amjadu ya ce, "babu wani sako a gare mu.
Amma ina neman alfarma, ka dawo daga bayana
yadda takobinka za ta fara sauka a kan wuyana,
ya kasance ni na fara mutuwa. Bayan ka kashe
mu, idan ka koma gida mahaifinmu ya tambaye
ka, 'me suka ce kafin ka kashe su?' Ka amsa
masa, 'ya'yanka sun ce suna gaishe ka, sa'annan
sun ce a fada maka, ka yi hukunci ba tare da ka
tabbatar da mai laifi ba, tsakaninsu da wadanda
suka kawo kararsu gare ka. Sa'annan ka wake
masa wadannan baitoci:

Ku sani mata shaidanu ne wadanda aka halicce
su a gare mu.
Muna neman tsarin Allah daga kaidin mata
Su ne asalin musiba wadda ta bayyana a
tsakanin talikkai, duniya da lahira.

Yayin da Amjadu ya gama rera wadannan
baitoci, sai ya kara rungume dan uwansa, ya
kankame shi ga jikinsa har suka zama kamar
mutum daya. Amjadu ya ce da hauni, "ina rokon
ka, ka jinkirta mana har in rera wadannan baitoci
ga dan uwana. Sai ya rera wannan waka, yana
cewa:
A cikin matafiya na farko na daga sarakuna
mafiya hankali daga gare mu.

Da yawa sun wuce cikin wannan tafarki na daga
manya da kanana.
Yayin da hauni ya ji wannan waka, ya yi kuka,
kuka mai yawa har gemunsa ya jike da hawaye.
Shi kuma Asadu sai ya wake wadannan baitoci
yana cewa:
Zamani zai juya daga bayanmu mai bakanta ciki.
Bayan mun nesanta, kuka ba ya amfana ga tsoffi
da yara kamarmu.
Ba darare nake fadi ba su wanzu gare mu na daga daren hira.

Dare maciki wanda aka hade abin hadewa a cikin
zuciya.
Yayin da ya fito zai bata zuciya gida da waje duka.

Bayan ya gama wannan waka ya yi kuka har
hawayensa suka jika gaban rigarsa, sai ya
rungumi dan uwansa, suka manne wuri daya, ka
ce su jiki daya ne. Hauni ya zare takobinsa, ya
daga shi sama da niyyar zai sare su. Daga
takobin nan da ya yi da karfi, sai ya yi wata kara
a cikin iska fauu. Wannan kara sai ta razana
dokinsa da yake kusa, ya katse igiyar da aka yi
masa dabaibayi, ya runtuma da gudu, ya yi cikin
daji. Da hauni ya ga yana shirin yin asarar
dokinsa mai kimar dinari dubu, da kuma
shimfidar dokin, wadda har ma ta fi dokin tsada.
Sai ya yarda takobi, ya bi bayan dokinsa da gudu
domin ya kamo shi.

Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ ZANCI GABA INSHA ALLAH30 HIKAYAN KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHARUZZAMAN

da hauni ya ga yana shirin yin asarar
dokinsa mai tsada, sai ya yar da takobi, ya bi
bayansa da gudu domin ya kamo shi. Ya bar
Amjadu da Asadu a daure, suna tsaye cikin zafin
rairayin hamada. Doki ya ci gaba da gudu cikin
tsoro, yana tayar da kura daga bayansa har ya
fita daga cikin rairayi ya shigi cikin wani surkukin
daji. Da zuwan hauni bai yi wata-wata ba, sai ya
kutsa kai cikin surkukin nan. To, ashe a cikin
surkukin itacen nan akwai wani tsohon zaki
mafadaci, mai idanu kamar garwashin wuta,
fuskarsa abar tsoro ga duk mutumin da ya gan
ta. Yayin da zakin nan ya ji motsi, sai ya fito
daga inda yake kwance. Yana fitowa sai suka yi
arba da hauni. Lokacin da hauni ya ga zaki, ga
shi kuma ya jefar da takobinsa, babu wani
makami a hannunsa da zai kare kansa da shi, sai
ya ce a cikin ransa, "babu tsimi babu dabara,
face daga Allah madaukakin Sarki. Hakika
wannan bala'i ya auka mini ne sanadiyyar
Amjadu da Asadu da na yi niyyar kashewa ba
tare da alhakinsu ba." Suka ci gaba da kallon
juna, shi da zaki. Zaki na nazarin ta inda zai fada
masa, shi kuma yana ta karanta dukan addu'o'in
da suka zo a cikin ransa.
Amjadu da Asadu kuwa suka yi ta jiran dawowar
hauni, zafin rana da kishirwa suka fara koda su,
suka yi ta kiran hauni amma ba su ji ya amsa
musu ba. Suka ce da junansu, "kai, da wannan
azaba da muke ciki ai gwamma a ce ya sare
kawunanmu mun huta." Asadu ya ce, "watakila
dokinsa tausayinmu ya ji, ba ya so a kashe mu,
shi ya sa ya gudu, wannan kuma hukunci ne na
Allah madaukakin sarki, mai adalci." Daga nan
sai suka yi ta mutsu-mutsu da jikinsu har daurin
igiyar ya sassabe, suka kwance junansu. Suka yi
shawarar su gudu, sai kuma suka ce, "wallahi ba
za mu gudu ba sai mun ga abin da ya faru ga
hauni. Suka dauki takobi suka bi sawun hauni da
dokinsa. Suka yi ta bin sawu har suka zo hanyar
da za ta shiga cikin surkukin itacen nan. Suka ce,
lalle hauni da dokinsa na cikin wannan wuri.
Asadu da ke rike da takobi, ya ce wa Amjadu,
"jira ni nan, bari in shiga in ga abin da ke ciki."
Amjadu ya ce, "wallahi ba ni barin ka ka shiga
kai kadai, sai dai mu shiga tare, idan mutuwa ce,
mu mutu tare kamar yadda muka tashi tare."
Suka kutsa kai cikin surkukin nan, suka tarar da
zaki ya bangaje hauni, ya aza kafafunsa na gaba
bisa kirjin hauni. Shi kuwa hauni yana kwance
rigingine, kamar tsuntsun da aka harbe, idanunsa
a rufe. Ya daga hannuwansa sama yana ta salati,
yana neman taimako daga Allah. Yayin da
Amjadu ya ga haka, sai ya fige takobi daga
hannun Asadu. Ya nufi zakin nan, ya tsarga
kansa gida biyu, ta tsakanin idanunsa. Zaki ya
fadi kasa matacce.
Yayin da hauni ya ji zaki ya fadi kasa, sai ya
bude idonsa ya mike tsaye da sauri yana
kaduwa. Yana kokarin cika bujensa da iska sai
ya lura da Amjadu da Asadu tsaye a gabansa.
Amjadu na rike da takobi, jini na diga daga gare Ta, ga kuma zaki yashe a kasa matacce. Nan take
ya fahimci abin da ya faru, ya fadi kasa yana
sumbatar kafafun Amjadu, yana cewa, na gode
wa Allah da ya sa ban kashe ku ba, domin na
tabbata babu alheri a cikin kashe ku. Kuma ina
gode muku a kan kubutar da rayuwata da kuka yi
daga halaka. Zan fansar da raina a wurin Sarki
domin kubutarku.

Daga nan ya mike tsaye ya rungume su. Ya
tambaye su yadda aka yi har suka kwance daga
daurin da ya yi musu da igiya.
Suka fada masa yadda suka yi ta kici-kici har
daurin igiyar ya sassabe, daga nan suka kwance
kan su, suka dauki takobinsa suka biyo sau. Ya yi
ta yi musu godiya har yana hawaye. Suka ce
masa, "dauki takobi ka cika umurnin
mahaifinmu."
Hauni ya ce, "Allah ya tsare ni da in cutar da ku,
ai ko wani na ga zai cuce ku, zan kare ku sai
inda karfina ya kare. Ku ba ni rigunanku in
dulmiya su cikin jinin zakin nan, sa'annan in cika
goruna biyu da jininsa in dauka in kai wa
mahaifinku, in ce masa na cika aikina. Ku kuma
ku nufi naku wuri, domin kasar Allah yawa gare
ta. Idan an ki ka da yini wani wuri, wani wurin
sai a so ka da kwana." Hauni ya ci gaba da
cewa, "wallahi zan yi bakin cikin rabuwa da ku."
Suka yi kuka dukansu. Amjadu da Asadu suka
tube rigunansu suka ba hauni, shi kuma ya tube
wani mayafi nasa babba, ya keta shi biyu, ya ba
kowa daya suka rufe jikinsu. Ya tsoma rigunansu
cikin jinin zaki, ya kuma cika goruna biyu da
jinin. Ya hau dokinsa, ya sukwane shi sai cikin
birni. Ya isa wurin Sarki Kamaruzzaman, ya fadi
kasa ya yi gaisuwa. Kamaruzzaman ya dube shi,
ya ga duk ya fita daga cikin hayyacinsa, sai ya yi
zaton hakan na da alaka da kashe 'ya'yansa. Shi
kuwa hauni yana tunanin fitar kutsu da yi yi ne
daga hannun zaki, yana kuma tausayin Amjadu
da Asadu bisa ga halin da za su shiga.
Kamaruzzaman ya tambaye shi, "ka aiwatar da
umurnina?"
Hauni ya sunkuyar da kansa kasa, "na cika
umurnin Sarki, kamar yadda ya bukata." Ya jawo
riguna duk sun rine da jini, da kuma gorunan da
ya ciko da jini, ya ajiye a gaban Kamaruzzaman.
"Sun yi maka gardama kafin ka kashe su?"
"A'a, Allah ya ba ka nasara. Sun kasance masu
hakuri bisa ga abin da Allah ya kaddara musu."
"Sun ba ka wani sako zuwa gare ni?"
Hauni ya share hawayen da ke kokarin fitowa
daga idanunsa, "sun ce a gaya maka, suna gaishe
ka. Kuma ba su ga laifinka ba a kan hukuncin da
ka yi musu. Sa'annan sun ce in rera maka
wannan waka:
Ku sani mata shaidanu ne wadanda aka halicce
su a gare mu.
Muna neman tsarin Allah daga kaidin mata
Su ne asalin musiba wadda ta bayyana a
tsakanin talikkai, duniya da lahira.
Lokacin da Kamaruzzaman ya ji wannan waka,
sai ya sadda kai kasa, ya yi jugum yana tunani.
Ya tabbatar da cewa babu makawa ya kashe
'ya'yansa cikin kuskure, ba tare da sun aikata
wani laifi ba. Ya tuna da irin makirce-makircen
mata, sai jikinsa ya yi sanyi. Ya dauko rigunan
'ya'yansa, wadanda hauni ya kawo masa, ya rika
jujjuya su ga hannunsa yana hawaye.

Sai ya ji takarda a
cikin aljihun rigar Asadu, ya sa hannu ya dauko
ta, ya gan ta nannade da gashin mace. Da ya
warware ta sai ya ga rubutun Badura, ya karanta
abin da ke ciki. Daga nan ya gane cewa, Asadu
ba shi da laifi. Ya lalubi aljihun rigar Amjadu, nan
ma ya ga takarda nannade da gashin mace. Ya
warware ta ya ga rubutun Hayatunnufusi ne. Ya
karanta abin da ta kunsa, ya tabbata shi ma ba
shi da laifi. Sai ya fara tafa hannuwa yana
sallallami.
Kamaruzzaman ya yi kuka, ya yi da-na-sanin
daukar maganar mata ba tare da bincike ba,
lokacin da da-na-sanin ba ta da wani amfani. Ya
tabbata ya auku cikin makircin mata wanda ya
dade yana taka-tsantsan domin gudun aukuwa
cikinsa. Ya sa aka gina masa wata babbar kubba
a cikin gidansa, aka siffanta kaburbura guda biyu
a cikin kubbar, kabari daya aka rubuta sunan
Amjadu, daya kuma aka rubuta na Asadu. Ya kira
wannan kubba da suna 'Kubbar Bakin Ciki'. Ya
kasance kullum yana cikin wannan kubba yana
kuka. Idan ya rungumi kabarin Amjadu ya yi
waka, sai kuma ya rungumi kabarin Asadu ya yi
waka. Ya kaurace wa matansa da jama'arsa
duka, ya kulle kansa a cikin Kubbar Bakin Ciki' Al'amarinsa ke nan.

Amma Amjadu da Asadu kuwa bayan hauni ya
tafi ya bar su, sai suka ba jihar da birninsu take
baya, suka kutsa kai cikin daji, ba su san inda za
su ba. Suka yi ta tafiya tsawon wata guda, suna
cin 'ya'yan itatuwa suna kuma shan ruwan
tafkuna da koramu har suka fara hango wani
tsauni na bakin dutse, gungurum a gabansu. Da
suka iso gindin tsaunin sai suka ga hanya ta rabu
gida biyu, daya ta zagaya ta gefen tsaunin daya
kuma ta hau ta bisansa. Suka tsaya suna
shawarwarin wadda za su bi, suka yanke
shawarar su bi hanyar da ta bi ta gefen tsaunin,
watakila ta fi saurin kai su ga gari, kuma a nan
za su rika samun ruwan koramu suna sha.
Suka bi wannan hanya tsawon kwana biyar,
amma ba su hango ko alamar gari ba. Sai suka
juyo da baya, suka dawo mararrarbar hanyoyin
nan. Suka dauki hanyar da ta bi ta saman tsauni.

Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ ke muku barka da shan ruwa
31 HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHARUZZAMAN

Amjadu da Asadu suka dauki hanyar da ta
bi ta saman tsaunin suka yi ta tafiya tsawon
wannan rana har dare ya yi. Suka gaji likis domin
ba su saba da tafiyar kasa ba, balle hawan
tsauni. Asadu, wanda ya gaji fiye da Amjadu, ya
ce, "ya dan uwana, wallahi na gaji sosai."
Amjadu ya ce, "yi hakuri dai mu tafi, da sannu
Allah zai taimake mu." Suka tsaya suka huta,
daga nan suka ci gaba da tafiya, suna jan kafafu
saboda gajiya. Da suka kara tafiya, kamar ta kafa
hamsin, sai Asadu ya fadi kasa yana kuka, ya
ce,"ya dan uwana, ni kam karfina ya kare, ba zan
iya kara ko da taku daya ba daga nan." Amjadu
ya tsaya suka dan sarara, sa'annan ya saba
Asadu bisa kafadarsa. Ya ci gaba da tafiya da shi
da kyar, yana nishi. Yana yi yana hutawa. Can
zuwa hudowar alfijir suka kai kololuwar tsaunin,
suka iske wata korama mai gudana da iccen
ruman a gefenta.
Suka yi matukar farin ciki, suka sha ruwa daga
koramar, suka tsinko 'ya'yan ruman suka ci har
suka koshi. Daga nan suka kwanta, barci ya
kwashe. Ba su farka ba sai da rana ta take. Suka
yi wanka, suka kara ci daga 'ya'yan ruman suka
kwanta. Da rana ta yi sanyi suka tashi domin ci
gaba da tafiya, amma sai suka ga duk kafafunsu
sun kumbura saboda tafiya. Don haka sai suka
zauna wannan wuri tsawon kwana uku. Bayan
sun huta sosai, karfin jikinsu ya dawo, sai suka ci
gaba da tafiya, suna gangarawa kasan tsaunin.
Suka yi ta tafiya kwana da kwanaki, har suka
kusa su halaka saboda kishirwa. Can sai suka
fara hango wani babban birni a gabansu, suka
kuwa yi masa tsinke cikin murna da farin ciki.
Da suka yi kusa da wannan birni sai suka fara
godiya ga Allah madaukakin Sarki. Amjadu ya ce
da Asadu ya dakata nan tukuna, ya shiga cikin
birnin ya binciki yanayin mutanensa. Ya kara da
cewa, "ka san duniya da fadi take, kuma kowane
birni da kalar al'adarsa. Bari in shiga in bincika
mana wane birni ne wannan, wanda da a ce mun
zagayo masa ta hanyar da ta bi kasan tsaunin
nan, da mun kwashe shekara cikakkiya ba mu iso
gare shi ba. Mun gode wa Allah da ya kubutar da
mu." Asadu ya ce, a'a, shi tsoro yake ji Amjadu
ya tafi ya bar shi nan shi kadai. Don haka shi zai
shiga cikin birnin ya binciko musu yanayin
jama'arsa.
Amjadu ya ce, "to, tafi. Amma kada ka jima." Ya
laluba aljihun wandonsa ya dauko wasu 'yan
dirhamai ya ba shi, ya ce ya sayo musu abinci da
abin sha idan zai dawo. Asadu ya karbi kudi ya
gangara daga kan tsauni, ya shiga cikin birni, ya
bar Amjadu nan yana jiran dawowarsa.
Da shigarsa cikin birni sai ya hadu da wani
tsoho, mai dogon gemu. Gemun nasa ya kawo
har ga kirji an kuma raba gashin gida biyu. Yana
tafiya yana dogara sanda, ya sa tufafi masu kyau
irin na tajirai. Ya nada wani dimemen rawani, mai
launin ja, bisa kansa. Yayin da Asadu ya gan shi,
sai ya yi mamaki yanayin wannan shiga tasa. Ya
matsa kusa gare shi, ya durkusa ya gaishe shi
cikin ladabi, sa'annan ya tambaye shi hanyar
zuwa kasuwa.
Tsoho ya dubi Asadu ya yi murmushi, ya ce,
"samari, amma kai bako ne ko?"
Asadu ya ce, "I, baffa. Ni bako ne."

Tsoho ya dafa kafadar Asadu ya ce, "hakika
birninmu ya yi maraba da zuwanka dan samari,
birninku kuwa zai yi bakin ciki da tafiyarka." Ya
tambayi Asadu, "me za ka yi a kasuwa?"
Asadu ya amsa masa, "zan sayo abin da za mu
ci ne, ni da dan uwana da na baro a bakin gari.
Mun fito ne daga gari mai nisa, watanninmu uku
muna tafiya kafin mu iso wannan gari."
Tsoho ya ce, "ai kuwa daurinka ya katse a gindin
kaba. Yau nake bikin aurar da 'yata, na shirya
kasaitacciyar walima ta abinci da abin sha kala-
kala masu tsada, domin bakin da za su zo. Mu
tafi gidana ka debi dukkan kalar abincin da kake so

ka je ku ci, kai da dan uwanka. Hakika Allah ya takaita
maka wahala da ka hadu da ni."
Asadu ya ce, "to, na gode. Amma mu hanzarta
dan uwana na can na jira na a bayan gari."
Tsoho ya kama hannun Asadu ya ja shi, suka yi
ta tafiya tinkis tinkis har suka shiga wani kwararo
matsattse, daga karshen kwararon kuma suka iso
ga wani gida mai babbar kofa. Tsoho ya ja Asadu
suka kutsa kai ciki, suka wuce zaure suka shiga
tsakiyar gidan mai yalwa. Suka tarar da wasu
tsofaffi guda arba'in, dukansu sun yi shiga irin ta
wannan tsoho da ya shigo tare da Asadu. Asadu
ya ga sun kunna wuta a tsakiyarsu, suna yi mata
sujuda.
Yayin da Asadu ya ga wadannan mutane, da abin
da suke yi, sai tsigar jikinsa ta tashi. Ya ji tsohon
nan da ya shigo da shi ya kada baki ya ce, "ya
ku jama'ar wuta, hakika wannan babbar rana ce
a gare mu." Daga nan sai ya daga murya da karfi
ya yi kira, "ina kake ne, ya kai Galbanu?" Sai ga
wani bakin bawa, dogo kakkarfa, ya fito, hancinsa
kamar gajeren wando, ya daure fuska kamar
wanda aka ce uwarsa da ubansa sun mutu.
Tsoho ya yi masa wata alama da hannu. Nan
take ya murkushe Asadu ya daure shi tamau da
igiya.
Tsoho ya ce, "tafi da shi dakin karkashin kasa, ka
damka shi ga hannun kuyangata, gwanar azabtar
da mutane. Ta ajiye mini shi kafin lokacin zuwa
ibada a cikin teku, wurin dutsen wuta, domin
jininsa za mu ba dutse a wannan shekara." Ya ci
gaba da cewa, "ka gaya mata cewa, ta rika yi
masa azaba dare da rana, ta ba shi abinci sau
biyu kullum."
Nan take bakin bawa Galbanu ya sungumi Asadu
bisa kafadarsa, ya shiga wani daki da shi. Ya
daga wata kofa ta karkashin kasa, ya tattaka
matakala ashirin ya sauka kasan dakin. Ya ajiye
Asadu, ya buga masa sarka hannuwa da kafafu,
ya kira kuyanga ya damka mata shi, tare da
sakon mai gidansu. Ya juya ya tafi.
.
Ita kuwa wannan kuyanga ba ta da tausayi ko kadan, ba ta san abin da ake kira da imani ba.
Ran mutum da na kiyashi a wurinta duka daya
ne. Bayan bakin bawa ya tafi, sai ta dauko bulala
ta saukar wa Asadu da bugu ba ji ba gani har ya
suma. Ta farfasa masa jiki ko’ina da bulala, sai
jini ke zuba daga jikinsa. Ta dauko kosai guda da
dan ruwa a cikin kasko ta ajiye kusa ga kansa, ta
tafi ta bar shi nan sumamme. Da tsakar dare ya
farka, ya ji jikinsa duk ya yi tsami saboda bugu.
Ya tuna da dan uwansa, ya kuma tuna irin daular da yake ciki a da.
Ya fashe da kuka, ya wake
wadannan baitoci:

Ku tsaya ga kufan gidaje, ku ba da labari a gare
mu.
Kada ku zata mu masu zama a gidajen ne.
Kamar yadda kuka kasance.
Zamani ya raba tarenmu.
Hakika ba mu samun waraka daga cutar zuci
Face mun sake gamuwa.
Azabata ta jibinci jiki da zuciya
Hakika yunwa ta kaura, bacin zuciya ya maye
wurinta.
Ina rokon Allah ya kusata gamuwarmu
Ya ije mana sharrin makiya daga gare mu.
Bayan ya gama waka sai ya ji kamshin kosai
kusa ga hancinsa, ya sa hannu ya laluba kasa,
kusa ga kansa, ya dauki dan kosan nan ya
lakwame, ya hadiya 'yan ruwan da aka ajiye
masa. Ya so ya dan runtsa ya yi barci, amma
kwarkwata da kudin cizo suka ce da kai aka hada
mu, sun sami sabon jini. Da gari ya waye
kuyangar nan ta zo domin ta canza masa tufafi.
Yayin da ta fara cire dan mayafin nan da ke jikin
Asadu, wanda duk ya rine da jini, sai ya fara
tasowa da fatar jikinsa, saboda dukan da ya sha
da bulala.
Asadu ya yi kara saboda zafin cire wannan
mayafi, ya ce, "ya Ubangiji, idan wannan azaba
da nake cikinta alheri ce gare ni, to, ka ba ni
hakurin jure

1 Comments On HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHRUZZAMAN
avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Wanne darasi kuka ?aru da shi daga cikin wannan hikayar,

Please Login or Register in order to submit comment