Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiga
gidan Halifa, sai ta nufi dakin Na'imatu, ta ba ta
battar magani ta ce, "ya shugabata, hakika yau
Allah ya hada ni da wani bakon mai magani,
Bafarishe, wanda ban taba ganin masanin
magunguna ba kamarsa. Da na ba shi 'yar battar
nan da kika yi fitsari a cikinta, ya dade yana
nazarin fitsarin, ya tambaye ni sunanki, da inda
aka haife ki, da shekarunki, duka na fada masa.
Daga nan sai ya umurci dansa, wani dan saurayi
kyakkyawa, kamarku daya da shi, ya hada mini
wannan magani da na ba ki. Kuma ya tabbatar
mini da cewa wannan magani tamkar yankan
wuka yake."
Na'imatu ta karbi dan akwati, tana dubawa sai ta
ga sunan mijinta rubuce bisa murfinsa. Nan take
yanayinta ya canza, ta ce a cikin ranta, "babu
shakka mai maganin nan ni ya zo nema, kuma
yana tare da shugabana Na'imu." Ta dubi
tsohuwa ta tambaye ta, "yaya kamannin dan mai
maganin nan yake?"
Tsohuwa ta amsa mata, "saurayi ne kyakkyawa,
ya sa tufafi na siliki masu kyau. Shekarunsa
kusan daya ne da naki, yana da wani dan tabo
bisa girar idonsa na dama. Na ji mai maganin na
kiransa da suna Na'imu."

Ko da Na'imatu ta ji haka, sai karfin jikinta ya
dawo, ta dauki maganin ta shanye, jim kadan sai
ta yi dariya ta ce, "hakika wannan magani sahihi
ne." Ta dauki takardar da ta gani a cikin battar ta
warware ta, ta karanta abin da ke ciki. Ta kara
tabbatar wa kan ta cewa shakka babu, wannan
sakon shugabanta ne kuma mijinta abin begenta,
Na'imu dan Rabi'u. Na'imatu ta cika da farin ciki,
zuciyarta ta yi fari.
Yayin da tsohuwa ta ga Na'imatu ta yi dariya, sai
mamaki ya kamata, ta ce, "hakika wannan rana
cike take da albarka." Na'imatu, wadda tun da ta
kwanta ciwo ba ta ko son jin warin abinci balle
ta ci wani abin kirki, sai ta ce da tsohuwa tana
so ta ci abinci. Tsohuwa ta umurci kuyangi su
kawo mata abinci. Nan da nan kuyangi suka
kawo akussan abinci da gorunan abin sha,
suka girke a gaban Na'imatu. Ta jawo akushi
daya ta fara cin abinci.
Tana cikin cin abinci sai ga Halifa ya shigo
dakin. Yayin da ya ga Na'imatu na cin abinci da
hannunta sai ya yi farin ciki.

Tsohuwa ta ce masa, "ya Shugaban Muminai, ina maka bushara
da warakar kuyangarka. Ka sani cewa na hadu da
wani bakon Bafarishe mai magani, wanda ya san
ilimin kowace cuta da maganinta. Shi ne wanda
ya hada mini maganin da na kawo mata, tana
gama shan wannan magani kuwa, nan take ta
sami lafiya." Halifa ya yi murna, ya kawo dinari
dubu ya ba tsohuwa, ya ce, "karbi wannan, ki ci
gaba da karbo mata maganin har sai ta warke
sarai." Daga nan sai ya fita daga dakin.
Tsohuwa ta tashi ta koma wurin mai magani, ta
ba shi dinarin nan dubu da Halifa ya ba ta, ta
kuma kawo wata takarda da Na'imatu ta rubuto
ta ba shi. Wannan lokacin sai ta gaya masa
cewa, kuyangar Halifa ce take nema wa magani
ba 'yarta ba, kamar yadda ta ce farkon zuwanta.
Mai magani ya karbi takarda ya ba Na'imu,
wanda nan take ya shaida rubutun Na'imatu,
hawaye suka zubo masa don farin ciki. Ya
warware takarda, ya ga rubutu kamar haka:

Daga kuyangar da ta rasa farin cikinta, wadda ta
kusa zautuwa domin rabuwa da abin kaunar
zuciyarta. Sakonka ya ishe ni, ya kuma faranta
mini ciki matuka, kamar yadda aka fada a cikin
wannan waka:
Wasikarka bushara ce gare ni, ta kawar da
dukkan ciwo da damuwa.
Kamar yadda damuwar mahaifiyar Annabi Musa
ta kau
Yayin da aka ba ta shayar da shi.
Kamar yadda makantar bakin cikin Annabi
Yakubu ta yaye
Yayin da aka kawo masa rigar Annabi Yusufa daga Misira.

Lokacin da Na'imu ya gama karanta wannan
takarda, gaban rigarsa duk ya jike da hawaye.
Ashe tsohuwa ta lura da halin da yake ciki, ta
tambaye shi, "me ya sa ka kuka, ya dana?
Wallahi bai kamaci kyawawan idanun nan naka
da zubar da hawaye ba."
"Ya shugabata," mai magani ya amsa mata, "me
ya fi sauki ga dana ya yi, in ba kuka ba? Me zai
hana idanunsa zubar da hawaye? Bayan kuwa
yana kusa da kuyangarsa kuma abar begensa,
wadda aka sace daga wurinsa. Ki sani wannan
shi ne Na'imu dan Rabi'u mijin Na'imatu wadda
kika karba wa magani. Babu wani magani da zai
warkar da ita daga cutar da take ciki, face ta
hadu da mijinta, su ga juna." mai magani ya mayar wa da tsohuwa
dinarin dubun da ta ba shi, ya ce, "ya shugabata,
ki rike wannan, na ba ki su duka. Amma ina
neman alfarma wurin ki, ki yi mini kokarin da
wannan saurayi zai sadu da abar begensa. Idan
kika yi mini haka zan kara miki wasu kudin fiye
da wadannan."
Tsohuwa ta dubi Na'imu ta tambaye shi, "da
gaske kuwa kai ne mijinta?"

Na'imu ya amsa mata, "na'am, ya mahaifiyata."
Ta ce, haba, ai biri ya yi kama da mutum. Domin
kuwa babu zancen da take yi kullum sai naka.
Na'imu ya kwashe labarinsu, yadda suka tashi
tare, da yadda wata tsohuwa ta shirya makircin
da ta sace Na'imatu, da yadda suka zo
Damashka neman ta, duk ya gaya wa tsohuwa.
Yayin da tsohuwa ta ji wannan labari nasa, sai
tausayinsu ya kamata, ta ce, "ya kai wannan
saurayi, na rantse da Allah babu wanda ya
kamata ya hada ka da masoyiyarka face ni." Nan
take ta hau jakinta ta koma gidan Halifa.
Ta iske Na'imatu zaune, ta dube ta, ta yi
murmushi ta ce, "Ya 'yata, da ma saboda rabuwa
da mijinki Na'imu dan Rabi'u, mutumin Kufa, ya
sa kike ta yawan kuka har kika kwanta ciwo?"
Yayin da Na'imatu ta ji haka, sai ta ce wa
tsohuwa, "hakika yanzu labulen sirrina ya yaye,
gaskiyar lamarina ta bayyana gare ki." Tsohuwa
ta matsa kusa gare ta, ta dafa ta da hannu ta ce,
"ki yi murna, ya 'yata, ki karfafa ranki. Na lashi
takobin sai na hada ki da abin kaunarki ko da
kuwa zan rasa rayuwata."

Daga nan kuma sai tsohuwa ta koma wurin
Na'imu ta ce masa, "na iske kuyangarka tana ta
begen ganin ka fiye da yadda kake begen ganin
ta. Ka sani cewa saboda son ka da take yi ko
Halifa ba ta bari ya taba jikinta ba har zuwa
wannan lokaci." Tsohuwa ta dubi Na'imu, ta ci
gaba da cewa, "ina so in sani idan ba ka da tsoro
ko fargabar shiga gidan Halifa. Domin kuwa zan
tafi da kai cikin gidan Halifa, in kai ka har dakin
Na'imatu domin ku sadu da juna. Amma ita kam,
ba ni da ikon da zan fito da ita daga gidan
Halifa." Na'imu ya amsa mata cewa, ai ko da za
a bi ta cikin wuta ne, to, zai iya, idan dai har zai
sake ganin Na'imatu. Tsohuwa ta ce to, madalla.

Ta tashi ta koma wurin Na'imatu.
Ta ce mata, "mai gidanki yana matukar son ki, ya
damu kwarai a kan sai ya gan ki. Minene naki
ra'ayi?" Na'imatu ta yi farat ta ce, "wallahi ina
son ganin shi ni ma."
Sai tsohuwa ta je ta samo tufafin mata masu
kyau, ta kuma samo kayan kwalliya na mata,
kamar janbaki da gazar da hoda, ta nade su cikin
wani zane. Ta dauka ta nufi rumfarsu Na'imu. Da
zuwanta sai ta ce masa zo mu tafi. Ta kai shi
gidan wanka, bayan ya fito daga wanka, suka
shiga wani daki wanda babu kowa a ciki, suka
rufe kofar. Yayin nan ta yi masa kwalliya irin ta
mata, ta kitse masa gashin kansa. Ta sa masa
awarwaro ga hannuwansa, ta daura masa sarka
ga wuyansa. Ta fito da tufafin nan, wadanda
suka kasance irin na kuyangi ne, amma masu
tsada, ta ce ya sa.
Da ta gama shirya shi tsaf, kamar yadda take so.
Ta dube shi ta gan shi kamar daya daga cikin
'yan matan Hurul Aini don kyawunsa, babu yadda
za a yi a ce namiji ne. Ta ce, "tsarki ya tabbata
ga Allah Ubangijin talikai. Wallahi har ma ka fi
Na'imatu kyau a cikin wannan shigar." Sa'annan
ta gwada masa yadda zai yi tafiya irin ta mata,
ta ce masa ya rika tura kafadarsa ta hagu gaba
tare da murguda mazaunansa idan yana tafiya.

DAGA Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ40 HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHARUZZAMAN

Da ta gama shirya shi tsaf, kamar yadda take so.
Ta dube shi ta gan shi kamar daya daga cikin
'yan matan Hurul Aini don kyawunsa, babu yadda
za a yi a ce namiji ne. Ta ce, "tsarki ya tabbata
ga Allah Ubangijin talikai. Wallahi har ma ka fi
Na'imatu kyau a cikin wannan shigar." Sa'annan
ta gwada masa yadda zai yi tafiya irin ta mata,
ta ce masa ya rika tura kafadarsa ta hagu gaba
tare da murguda mazaunansa idan yana tafiya.
Kuma ya rika yin taku daidai, kada ya yi sauri.
Na'imu ya yi tafiya kamar yadda ta ce masa. Da
ta ga ya yi tafiya daidai, yana rangwada kamar
mace, sai ta ce masa, "da yardar Allah gobe da
dare zan zo in kai ka wurin masoyiyarka. Idan
muka isa gidan Halifa kada ka ji tsoron kowa, ko
da mun hadu da dogari ko bawa, ka dan rusunar
da kanka kasa kadan, alamun gaisuwa, amma
kada ka yi musu magana Ni zan hane su daga yi maka wata
magana."
Daga nan ta ce masa ya cire tufafin sai zuwa
gobe da dare za ta zo ta tafi da shi gidan Halifa.
Ta sa kai ta fice daga gidan wankan.
Kashe gari da dare sai ga ta ta dawo, ta sake
shirya Na'imu da tufafin mata, ta shiga gaba ya
bi ta a baya har gidan Halifa. Tun a bakin kofar
gidan wani bawa ya so ya hana Na'imu shiga,
amma sai tshohuwa ta ce masa, "kaiconka, don
me za ka hana kuyangar Na'imatu, babbar
masoyiyar Halifa, shiga wannan gida." Yayin da
bawa ya ji haka, sai ya yi sauri ya ba su hanya
suka wuce. Suka ci gaba da tafiya cikin gidan
har suka yi nisa a cikinsa. Daga nan sai tsohuwa
ta ce masa, "kada ka ji tsoron kome, ka shiga
waccan kofar," ta nuna masa kofa da hannu,
"idan ka shiga za ka ga dakuna da yawa a jere,
dama da hagu. To, daga na bangaren hagu, sai
ka kidaya kofa biyar ka shiga ta shida, domin nan
ne dakin Na'imatu. Duk wanda ya yi maka
magana kada ka saurare shi, ka tafi kai tsaye ka
shiga wannan daki."
Tsohuwa ta ja shi ta kai shi bakin kofa, suka
tarar da bawa tsaye yana gadin kofar. Bawa ya
tambayi tsohuwa, "wace ce wannan kuyangar da
kike tare da ita?" " Tsohuwa
ta amsa masa, "shugabarmu ce ta sayo ta."
Bawa ya tare kofa ya ce ba za ta shiga ba,
domin Halifa ya umurce shi kada ya bar kowa ya
shiga ta wannan kofa, sai fa wanda ya sani.
Bawa ya kara da cewa, amma idan ita tsohuwar
ce za ta shiga, to, ta shiga, amma ita kuyanga
bai san ta ba, balle ya bari ta shiga.
Tsohuwa ta ce masa, "ka manta ne shugabarmu
Na'imatu ba ta dade da samun sauki ba daga
ciwon da ya kamata? Ka kuwa san yadda Halifa
yake son ta sarai. To, ita ce ta sayi wannan
kuyanga domin ta rika yi mata hidima tare da
debe mata kewa. Muddin kuwa ka hana kuyangar
nan shiga wurin ta, to, ina ji maka tsoron ciwonta
ya dawo. Idan kuwa Halifa ya san kai ne
sanadiyyar komowar ciwonta, babu shakka zai sa
a sare kan ka. Ka yi tunani ka gani."
Bawa ya yi tsaye sororo, domin kuwa maganar
tsohuwa ta shige shi. Tsohuwa ta juya wurin
Na'imu ta ce masa, "ki shiga wurin shugabarki,
ina rokon ki kuma kada ki gaya mata cewa
wannan bawa ya tsayar da mu a bakin kofa."
Na'imu ya dan rusunar da kansa kasa, ya shige
ta cikin kofar. To, maimakon ya je ga dakunan da
ke bangaren hagu, ya kidaya kofa biyar ya shiga
ta shida, kamar yadda tsohuwa ta gaya masa.
Sai ya nufi dakunan da ke bangaren dama, ya
kidaya kofa shida ya shiga ta bakwai.
Da ya shiga dakin sai ya ga an kawata shi da
labulayyen bango na siliki, wadanda aka yi wa
ado da zinariya da azurfa. An shimfide daben
dakin da kilisai masu taushin gaske. Ya ji gaba
dayan dakin ya gauraye da kamshin turaren
miski. Daga can kuryar dakin ya ga wani gado na
alfarma, an shimfida masa shimfidu masu daraja
da tsada. Ya tafi ya zauna bisa gadon yana
rarraba ido, yana mamakin irin kayan alatun da
aka shirya a cikin wannan daki, cewa shi, bai san
abin da Allah zai kaddara a kan sa ba.
Yana nan zaune yana mamaki, sai ga yarinyar
nan, kanwar Halifa, ta shigo tare da kuyanga tana
take mata baya. Yayin da kanwar Halifa ta gan
shi, sai ta zaci kuyanga ce. Ta ce masa, "wace
ce ke, wa ya sayo ki? Kuma wa ya kawo ki
dakina?" Na'imu ya yi shiru, ya ki mayar mata da
jawabi. Ita kuma sai ta kara cewa, "idan laifi kika
yi wa dan uwana, Halifa, har kika boye kanki a
cikin dakina, to, ki gaya mini irin laifin da kika yi
masa, ni kuwa zan lallashe shi, in ba shi hakuri
ya yafe miki." Na'imu dai bai amsa mata ba.
Da kanwar Halifa ta ga haka, sai ta umurci
kuyangar da suka shigo tare, ta koma waje daga
bakin kofa, kada ta bari kowa ya shigo. Ta je
gaban Na'imu ta dubi fuskarsa, ta yi mamaki da
irin kyawunsa, ta ce masa, "ya ke kuyanga, wace
ce ke? Kuma ya ya aka yi har kika shigo nan?
Domin ban taba ganin ki a cikin wannan fada ba."
Na'imu dai ya yi kurum, bai ce mata kome ba.
Ganin haka sai ta yi fushi, ta riki damutsttsan
hannuwansa domin ta finciko shi daga bisa
gadonta. Garin ya kubce daga rikon da ta yi
masa, sai hannunta daya ya shafi kirjinsa. Sai ta
ji kamar ta shafi kirjin namiji, domin ba ta ji
alamar nonuwa ba. Nan take ta sake shi, ta ja da
baya cikin kaduwa.
Yayin da Na'imu ya ga asirinsa zai tonu, sai ya
tashi daga kan gado, ya zo gabanta ya durkusa,
ya ce, "ya shugabata, ni bawanki ne. Rayuwata
yanzu tana hannunki, ina rokonki, ki yi mini rai."
"Babu abin da zai same ka. Amma gaya mini
wanene kai? Wanene kuma ya kawo ka nan?"
"Ya ke Sarauniya, sunana Na'imu dan Rabi'u
mutumin Kufa. Na sadaukar da rayuwata ne, na
zo wannan wuri domin in sadu da kuyangata,
abar begena Na'imatu, wadda Hajjaj, Sarkin Kufa,
ya sace daga hannuna ya aiko da ita wurin
Halifa."
Kanwar Halifa ta ce, "kada ka ji tsoron kome,
babu abin da zai same ka na cutarwa." Ta kwala
wa kuyangar da ke bakin kofa kira, ta , ta umurce ta da ta je dakin
Na'imatu ta kirawo ta.
Amma tsohuwa kuwa, bayan sun rabu da Na'imu
sai ta nufi nata daki ta zauna, tana ta zullumin
kada a sami kuskure. Can zuwa wani lokaci sai
ta kasa daurewa, ta tashi ta nufi dakin Na'imatu,

ta tambaye ta, "shugabanki ya iso kuwa?" Ta
amsa mata, "na rantse da Allah ban gan shi ba."
Nan take gaban tsohuwa ya fadi, ta ce, "ai kuwa
ina tsammanin ya rude, ya fada wani dakin na
daban." Na'imatu ta ce, "babu tsimi babu dabara
face daga Allah Madaukakin Sarki. Kaicon
halakarmu."
Suna cikin wannan hali na fargabar abin da zai
faru, sai ga kuyanga ta shigo musu. Ta gai da
Na'imatu, ta ce mata shugabarta na neman ta a
dakinta. Na'imatu ta ce ta ji, ta karba. Tsohuwa
ta dube ta ta ce, "watakila dakinta shugabanki ya
shiga, ai kuwa asiri ya tonu."
Na'imatu ta bi bayan kuyanga suka tafi, da shigar
su cikin dakin sai kanwar Halifa ta ce mata, "ya
Na'imatu, ga shugabanki nan zaune kusa gare ni.
Ga alama ya bata hanyar zuwa dakinki. Amma
daga ke har shi, kada wanda ya ji tsoron kome.
Ku kwantar da hankalinku, ni zan taimake ku."
Yayin da Na'imatu ta ji haka, sai zuciyarta ta yi
karfi, ta matsa kusa ga Na'imu. Shi kuma ya
tashi tsaye. suka rungume juna suna
zubar da hawaye don farin ciki...

DAGA~==>Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ
41 HIKAYAR KAMARUZZAMANA DAN SARKI SHARUZZAMAN

Yarinya kanwar Halifa ta ce wa Na'imu da
Na'imatu, "ku kwantar da hankalinku, ni zan
taimake ku." Yayin da Na'imatu ta ji haka, sai
zuciyarta ta yi karfi, ta matsa kusa ga Na'imu.
Shi kuma ya tashi tsaye, suka rungume juna suna
zubar da hawaye don farin ciki. Suka fadi sumammu Yayin da suka dawo cikin hayyacinsu sai kanwar
Halifa ta ce musu su zauna domin su tattauna
yadda za su shawo kan Halifa bisa wannan
al'amari. Suka ce da ita, "wallahi ya shugabarmu,
mu kam ba mu da wata dabara ko shawara sai
fa abin da kika gani." Ta ce musu, "na rantse da
Allah, ba zan bar dan uwana ya cutar da ku ba.
Ku zauna mu dan yi nishadi."
Ta sa aka kawo musu abinci da nama, da kayan
shaye-shaye da tande-tande. Suka ci suka batse,
kaskon sha ya zagaya a tsakaninsu, suka sha har
ya ishe su. Na'imu da Na'imatu suka yi farin ciki
har damuwar su ta soma yayewa. Daga nan sai
Na'imu ya kada baki ya ce, "ya shugabata,
yaushe ne matsalarmu za ta warware?"
Ita kuma sai ta tambaye shi, "ya Na'imu, shin
kana son kuyangarka Na'imatu?"
Ya amsa mata, "ai saboda son ta da nake yi ya
sa na sadaukar da raina na shigo wannan gida."
Sa'annan ta juya wurin Na'imatu, ta tambaye ta,
"ya Na'imatu, shin kina son shugabanki Na'imu?"
Na'imatu ta amsa mata, "ya shugabata, ai son sa
ne ya yi sanadiyar rashin lafiya ta wadda ta
ramar da jikina. Wallahi ina son shi fiye da yadda
kike tunani."
"Na rantse da Allah, tunda dai har kuna son juna,
duk wanda ya shiga tsakaninku, to, Allah ba zai
bar shi haka ba. Kada ku damu, za ku koma
yadda kuke rayuwarku a baya." In ji kanwar
Halifa. Suka raurawa da farin ciki. Na'imatu ta
dauki molo, ta kida shi da yatsunta, kida mai
taushi da kwantar da hankali, ta sirara murya
tata, ta wake wadannan baitoci:
Yayin da makiya suka kitsa rabuwarmu
Wani abu bai kasance a gare ni ba wanda za su
amfana da shi.
Wani abu bai kasance ga masoyina ba, balle su ji
dadi.
Dukkan munafuki yakan yi mugunta bisa ga bata
Kowa ya dogara ga Allah ba ya jin tsoron
makiya.
Bayan ta gama wannan waka, sai ta mika wa
Na'imu molo ta ce, "ya shugabana, nishadantar
da mu da wata waka da ke gare ka." Ya karbi
molo ya gyara tsarkiyarsa, ya zungure shi da
yatsu, ya wake wadannan baitoci:
Wata yana koyi da ke, ba domin yana ramewa ba.
Rana ita ce tamkarki, ba domin tana faduwa ba.
Ni na yi al'ajabi, da yawan al'ajabi a cikin so.
Ina ganin tafarki makusanci, yayin da na shige
shi zuwa ga masoyi.
Yakan yi mini nisa, yayin da na juyo.
Yayin da ya gama wannan waka, sai Na'imatu ta
cika kasko da abin sha ta mika masa, ya karba
ya shanye. Ta cika wani kasko ta ba kanwar
Halifa, ita ma ta karba ta kurbe. Daga nan sai
kanwar Halifa ta karbi molo daga hannun Na'imu,
ta wake wadannan baitoci:
Bakin ciki da bacin zuciya, matabbata ne a cikin
kirjina.
Da yawan tunanin da nake yawan maimaitawa a
cikin raina.
Su suka rame jikina, da ya zama madaukaki.
Jiki ya kasance a gare ni macuci da bege.
Bayan ta gama waka sai ta cika kasko da abin
sha ta ba Na'imatu, ta karba ta shanye, sa'annan
ta karbi molo ta yi waka. Haka suka kasance
cikin sha da wake-wake, suna annashuwa.
Kirazansu suka yalwata, zukatansu suka yi fari
da wakokin da suke yi. Kwamfa, sai ga Halifa ya
fado dakin, kamar wanda aka ingizo.
Lokacin da suka gan shi sai suka tashi gaba
daya, suka fadi suka yi gaisuwa. Yayin da Halifa
ya ga Na'imatu rike da molo, sai ya yi murna ya
ce, "ya Na'imatu, godiya ta tabbata ga Allah
wanda ya warkar da ke daga ciwo." Daga nan sai
ya dubi Na'imu, wanda yake cikin shigar mata, ya
ce wa kanwarsa, "ya 'yar uwata, wace ce
wannan kuyanga?"
Ta amsa masa, "ya Shugaban Muminai,
kuyangarka ce. Ita tana daga cikin kawayen
Na'imatu wadda ko abinci ba ta iya ci sai tare da
ita, kamar yadda aka fada a cikin wannan waka."
Abokai biyu sun taru, ya za a yi su rabu?
Sai fa cikin rashin sani.
Aboki yakan debe wa aboki kewa.
Halifa ya cika da mamaki, ya ce, "wallahi ita ma
kyakkyawa ce kamar Na'imatu. Gobe kuwa zan
sa a shirya mata nata daki kusa ga na Na'imatu,
saboda wannan shakuwa tasu. Zan sa a kawata
mata dakin tamkar yadda aka kawata dakin
Na'imatu."

Daga nan kanwar Halifa ta gyara masa shimfida
ya zauna. Ta sa aka kara kawo kayan abinci.
Aka kuma kawo na kwalama da makulashe, tare
da abin sha iri-iri. Suka ci abinci tare da Halifa.
Bayan sun gama cin abinci sai ya cika kasko da
abin sha, ya yi wa Na'imatu alama da ta dauki
molo ta yi waka. Ta dauki molo, bayan ta sha
kasko biyu, ta wake wadannan baitoci:
Ya mafi daukakar mutane a cikin wannan
zamani.
Wanda babu tamka a gare shi, mai alfarma cikin
al'amari.
Ya makadaici a cikin daukaka da kyauta
cikakkiya.
Ya shugaban Sarakuna ga kowace jiha.
Ya mamallaki ga sarakunan kasa.
Mai ba da mai yawa ba tare da gori ba.
Allah ya wanzar da kai bisa turmuza hancin
makiyanka.
Shi adanta kushewarka fiye da daukakarka.
Yayin da Halifa ya ji wannan waka sai ya cika da
farin ciki. Ya kara cika kasko da abin sha ya ba
Na'imatu, ya umurce ta da kara yin wata waka.
Ta karbi kasko ta shanye, ta tsuke zaren molo, ta
wake wadansu baitocin. Lokacin da Halifa ya ji
wakarta, sai ya dimauta da fasaharta da kuma
zakin muryarata. Ya ce, "na rantse da Allah
wannan waka ta yi dadi. Na rantse da Allah har
ta fi zuma zaki. Wallahi Allah ya yi miki baiwa, ya Na'imatu. Ga
ki da fasahar waka, ga kuma murya mai dadi da
kwantar da hankali." Haka dai suka ci gaba da
nishadi tsawon wani lokaci, har dare ya raba ba
su sani ba. Daga nan sai kanwar Halifa ta ce
masa, "ya Shugaban Muminai, ni kuwa na
karanta wani labari mai dadi, na wani babban
Sarki, a cikin littafi, da kana da sha'awa da na
gaya maka shi."
"Wane labari ne wannan mai dadi? Gaya mana
shi mu ji." In ji Halifa.

Ta ce da shi "ka sani cewa, ya Shugaban
Muminai, a birnin Kufa, an yi wani saurayi wanda
ake kira Na'imu dan Rabi'u. Yana da wata
kuyanga wadda aka rene su tare tun suna yara
har suka girma tare. Bayan sun isa mutane sai
soyayya mai tsanani ta ratsa zukatansu, suka so
junansu matuka. Daga karshe dai har Na'imu ya
riki wannan kuyanga a matsayin matarsa.
Suna nan kan haka, cikin jin dadi da farin ciki, sai
rannan wata kaddara ta raba tsakanin su. Aka
sace wannan kuyanga bisa ga yaudara, aka sayar
da ita ga wani babban Sarki na wata kasa daban.
To, saboda tsananin son da Na'imu ke yi wa
kuyangarsa, sai ya sadaukar da ransa, ya shiga
duniya wajen neman ta. A kwana a tashi har
Allah ya hada shi da ita a cikin gidan Sarkin da
ya saye ta. Sun hadu da juna ke nan ko mayar
da zance ba su gama yi ba, sai ga Sarkin nan ya
fado wurin da suke. Yayin da Sarkin nan ya gan
su tare, sai ya sa aka sare kawunansu, ba tare
da ya yi wani bincike ba."

Kanwar Halifa ta dubi dan uwanta ta ce, "ya
Shugaban Muminai, shin hukuncin da wannan
Sarki ya yanke ya yi daidai kuwa?"
Halifa ya girgiza kansa ya ce, "wallahi wannan
Sarki bai yi aiki da hankali ba. Ya kamata ya yi
la'akari da abubuwa guda uku, kafin ya bi wani
mataki a kan su. Na farko, ya tambaye su, shin
suna son juna? Na biyu, tunda suna cikin gidansa
ne, sai ya rike su a matsayin baki, ya kyautata
musu kamar yadda aka umurce mu da kyautata
wa bako, daga bisani sai ya yanke hukuncin da
ya ga ya kamata gare su. Abu na uku kuwa, ya
kamata ya kwatanta kansa a matsayin mutumin
da zai yanke wa hukuncin, ya gani idan shi ne
aka yanke wa hukuncin an yi masa adalci."
Yayin da kanwar Halifa ta ji haka sai ta ce, "ya
Shugaban Muminai, ka umurci Na'imatu ta rera
mana waka, kuma ka saurari abin da za ta fada a
cikin wakarta." Halifa ya umurci Na'imatu da yin
waka. Ta dauki molo, bayan ta kada shi sai ta
wake wadannan baitoci:
Ha'incin zamani bai gushe ba yana zambatar
mutane.
Yana wautar zukata, yana gadar da tunani
Yana raba masoya bayan haduwa.
Sai ka ga hawaye na zuba bisa kundukuki
Kwatankwacin bakin cikin kashe rai, mani'imci.

Zamani ya hada tsakaninsu bayan rabuwa
Don me za ka shiga tsakanin wadannan masoya?
Yayin da Halifa ya ji wannan waka sai ya cika da
tsananin farin ciki. Kanwarsa ta ce masa, "ya
dan uwana, yana daga cikar kamalar mutum ya
tsaya bisa ga magana guda, ba a san dattijo da
magana biyu ba. Ka riga ka yanke wa kan ka
hukunci bisa ga abin da zan bayyana maka
yanzu." Ta dubi Na'imatu ta ce ta mike tsaye,
haka kuma ta ce da Na'imu shi ma ya tashi
tsaye, suka mike tsaye. Ta dubi Halifa ta ci gaba
da cewa, "ya Shugaban Muminai, wannan da ta
mike tsaye ita ce Na'imatu, kuyangar Na'imu dan
Rabi'u, wadda Hajjaj dan Yusufa, Sarkin Kufa, ya
sace daga gare shi, ya aiko maka da ita, ya yi
maka karyar cewa ya saye ta dinari dubu goma."
Ta nuna Na'imu, ta ce, "wannan kuma ba mace
ce ba. Shi ne Na'imu dan Rabi'u shugaban
Na'imatu." Ta tashi ta zo gaban Halifa ta
durkusa kasa, ta ce, "ina rokon ka, don alfarmar
kakaninmu masu albarka, don Hamza da Akilu da
Abbas, ka yafe wa wadannan masoya biyu. Ka
mayar musu da matsayinsu da suke ciki, domin
neman tsira gobe kiyama. A halin yanzu,
rayuwarsu tana hannunka. Ni dai na shiga
tsakani, ina neman alfarmar ka yafe musu, kuma
ka mayar masa da kuyangarsa."

Halifa ya yi murmushi, ya dubi 'yar uwarsa ya ce,
"wallahi kin fadi gaskiya, dattijo ba ya magana
biyu. Ni ba zan saba abin da na fada ba daga
farko." Ya juya wurin Na'imatu, ya tambaye ta,
"ya Na'imatu, wannan shi ne shugabanki?"
Na'imatu ta amsa masa, "i, Allah ya ba ka
nasara."
Halifa ya ce, "babu abin da zai same ku na
cutuwa daga gare ni.

1 Comments On HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHRUZZAMAN
avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Wanne darasi kuka ?aru da shi daga cikin wannan hikayar,

Please Login or Register in order to submit comment