Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

gaya mini wannan,
Ta afka kaunar mai son ta.
Na bar ta gidansu a kwance,
Ta fada cutar mai son ta.
Har wasu na cewa ta zautu,
An daure ta cikin dakinta.
Ni kuwa na san cutar so ce,
Ba ta da hauka ko daya gun ta.
Sai ga shi na tad da waninta,
Kwance cikin jiyya don son ta.
Tashi ka saurare ni ka ji ni,
Na zo nan domin warakarta.
Ni na zo manzonta gare ka,
Tashi ka warke wannan cuta."
Yayin da Kamaruzzaman ya ji wannan waka, sai
zuciyarsa ta yi karfi, kuzarinsa ya dan dawo
jikinsa, ya bude baki cikin wata shakakkiyar
murya ta marasa lafiya, ya ce, "Ya mahaifina, ku
matso da wannan saurayi ya zauna kusa gare ni."
Lokacin da Sarki ya ji dansa ya iya bude baki ya
yi magana, sai murna ta kama shi. Da farko kuwa
har ya harzuka da Marzuwan yana shirin ba da
umurni a sare masa kai, amma da ya ji dansa ya
yi magana sai fushinsa ya koma farin ciki. Ya
riko Marzuwan da hannunsa ya zaunar da shi
kusa ga Kamaruzzaman, ya ce, "Maraba da kai
bakon farin ciki." Marzuwan ya ce, "Amincin
Allah ya tabbata a gare ka ya Sarki tare da
danka."
Daga nan Sarki ya tambaye shi daga inda ya fito.

Marzuwan ya ce, "Na fito ne daga kasar Sin,
kasar Sarki Gayur mai fadoji bakwai." Sarki ya
ce, "Maraba da kai ya kai wannan bako. Ina fatar
zuwanka wannan kasa tamu ya zama sandiyyar
warakar dana." Marzuwan ya ce, "Da yardar Allah
madaukakin Sarki, zuwana zai zama sanadiyar
tashin danka daga cutar da yake fama da ita,
shekara da shekaru."
Daga nan sai Marzuwan ya dukar da kansa kusa
ga kunnen Kamaruzzaman, ya yi kasa-kasa da
muryarsa, yadda Sarki da Waziri ba za su ji abin
da zai ce ba. Ya ce, "Na zo wannan birni takanas
dominka. Na zo maka da albishir daga kasar Sin,
na yarinyar da ka gani shekaru uku da suka
wuce. Wannan yarinya ba kowa ba ce face
gimbiya Badura, 'yar Sarkin Kasar Sin. Kamar
yadda ka kamu da ciwon sonta, haka ita ma tana
can cikin ciwon sonka, abin nata ma har ya fi
naka ban tausayi, domin ita tana can cikin sarka,
hannuwa da kafafu da wuya, a zatonsu ta kamu
da ciwon hauka. Amma idan Allah ya so,
warakarku duka za ta kasance daga sanadiyyata
ne."
Lokacin da Kamaruzzaman ya ji haka, sai ya ji
wani karfi ya shiga jikinsa, ya yi wa mahaifinsa
alama da ya tayar da shi zaune. Sarki ya yi
kamar ya yi hauka don murna, ya kama
Kamaruzzaman ya tashi zaune, ya sa masa
matasan kai guda biyu, ya jingina ga bango.
Sarki ya sa aka kawo turare kala-kala aka
yayyafa ko'ina cikin dakin. Ya dubi Marzuwan ya
ce, "Hakika lamarinka mai girma ne, ka yi abin da
ya gagari manya-manyan masu magani." Aka
kawo abinci kala-kala, Marzuwan ya dauki akushi
daya, ya ce wa Kamaruzzaman ya sa hannunsa
su ci tare.
Kamaruzzaman bai musa ba, ya sa hannunsa
cikin akushi, yana cin abinci tare da Marzuwan.
Murnar Sarki da farin cikinsa suka karu fiye da
na farko, ya yi ta sa wa Marzuwan albarka yana
yabonsa. Nan take ya tafi ya shaida wa matarsa,
mahaifiyar Kamaruzzaman, halin da dansu yake
ciki. Ya kuma fada wa fadawansa cewa dansa ya
sami sauki, ya yi umurni da a yi shela cikin birni,
a fada wa dukkan jama'ar gari wannan labari na
farin ciki. Ya kuma ba da umurni da a kawata
birni domin yin bukin murnar warkewar
Kamaruzzaman.
Jama'ar gari suka yi ta farin ciki da wannan
labari, aka shiga kawata birni da kayan alatu iri-
iri. Waziri kuwa, ko ba a fada ba, kun san ya fi
kowa murnar warkewar Kamaruzzama. Marzuwan
da Kamaruzzaman da Sarki Shahruzzaman suka
kwana daki daya, da gari ya waye Sarki ya fita
ya ba su wuri. Daga nan Kamaruzzaman ya
kwashe dukkan labarin abin da ya faru ya fada
wa Marzuwan. Shi ma ya kwashe labarin abin da
ya faru ga Badura ya fada wa Kamaruzzaman, ya
kara da cewa, "Na tabbata kai masoyinta ne, ita
ma masoyiyarka ce. Ka kwantar da hankalinka,
ka karfafa zuciyarka. Da yardar Allah kuma sai
na hada ku tare. Kamar yadda aka fada a cikin
wannan waka:
"Ko an tsare wanda ke so, sai,
Ya sadu da wadda ke son sa.
Ni zan hada wagga soyayya,
Ta masoya biyu su zamto kusa.
Ni zan zamto wuya ga jiki,
Mai hada kai har da kirjinsa."
Marzuwan ya ci gaba da karfafa wa
Kamaruzzaman zuciya, ya rika ba shi labaran
yadda suka tashi da gimbiya Badura tun suna
yara, da wasu labarai, ya rika yi masa wakoki.
Hankalin Kamaruzzaman ya kwanta, lafiya ta
dawo masa, ya nadi abinci sosai, ya sha abin sha
mai yawa. Karfin jikinsa ya dawo, ya mike tsaye,
ya ce yana so ya yi wanka ya canja tufafi.
Marzuwan ya riki hannunsa, suka shiga wurin
wanka, zuka zubar da dattin dake jikinsu, suka yi
fes. Lokacin da Sarki Shahruzzaman ya sami
labarin cewa Kamaruzzaman ya mike tsaye har
ya yi tafiya da kafafunsa, ya shiga wurin wanka,
saboda tsananin murna ya sa aka saki duk 'yan
sarkar garin. Ya ciyar da musakai da miskinai, ya
yi kyauta da tufafi masu yawa ga mabukata, ya
sa a ci gaba da kawata birni zuwa kwana bakwai
domin yin gagarumin shagali a kan murnar
warkewar Kamaruzzaman. Bayan Kamaruzzaman
da Marzuwan sun fito daga wurin wanka, suka
sanya tufafi masu kyau da daraja. Marzuwan ya
dubi Kamaruzzaman ya ce, "Ya shugabana, ka
sani cewa na zo wannan birni ne takanas domin
labarinka da na ji. Tun lokacin da na sami
labarinka, da irin ciwon da ke damun ka, na
tabbata cewa kai ne wanda 'yar uwata, gimbiya
Badura, ta kamu da ciwon sonka, sandiyyar haka
aka jefa ta cikin sarka. Kafin na fito gida na yi
mata alkawari ba zan koma ba face na je mata
da maganin da zai warkar da ita daga cutar da
take fama da ita. Kuma ba kome ba ne maganin
wannan cuta face kai. Ban sani ba ko za ka
amince ka bi ni, in kai ka wurinta?"
Kamaruzzaman ya amsa, "Na'am, na amince ka
kai ni wurinta, sai dai na sani cewa mahaifina ba
zai taba yarda in yi nisa da shi ba, balle ya
amince mini in yi tafiya mai nisa haka."

Marzuwan ya ce, "Yadda za a yi shi ne, gobe ka
fada wa mahaifinka cewa, ka sami lafiya, amma
kana so ka tafi farauta domin ka mike kafafunka
daga kwanciyar jiyyar da ka yi. Ka fada masa
cewa, kwana daya kawai za ka yi a can. Idan ya
amince, sai ka kece sirdin dokinka ka cika shi da
dinari ka dinke, ni ma zan yi wa sirdin dokina
haka. Mu daura wa dawakai biyu amalanke,
sanna kuma mu riki wasu dawai biyu mu shiga
cikin daji, amma kada ka bari a hada mu da
kowa, mu biyu kawai za mu tafi. Da zarar mun
fita bayan gari, sai mu sauka daga kan
amalanken mu daura wa dawakan biyu sirdi, mu
yi ta yi har Allah ya kai mu birnin Sin."
******.

Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar
labarun DARE DUBU DA DAYA, wanda littafin nanan a kasuwa'(15) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI
SHAHRUZZAMAN
Marzuwan ya ce, "Yadda za a yi shi ne, gobe ka
fada wa mahaifinka cewa, ka sami lafiya, amma
kana so ka tafi farauta domin ka mike kafafunka
daga kwanciyar jiyyar da ka yi. Ka fada masa
cewa, kwana daya kawai za ka yi a can. Idan ya
amince, sai ka kece sirdin dokinka ka cika shi da
dinari ka dinke, ni ma zan yi wa sirdin dokina
haka. Mu daura wa dawakai biyu amalanke,
sanna kuma mu riki wasu dawai biyu mu shiga
cikin daji, amma kada ka bari a hada mu da
kowa, mu biyu kawai za mu tafi. Da zarar mun
fita bayan gari, sai mu sauka daga kan
amalanken mu daura wa dawakan biyu sirdi, mu
yi ta yi har Allah ya kai mu birnin Sin."
Kamaruzzaman ya yi farin ciki da wannan
shawara ta Marzuwan. Ya shiga wurin
mahaifinsa, ya nemi yardarsa domin fita zuwa ga
farauta, ya fada masa zancen da Marzuwan ya
umurce shi da shi. Mahaifinsa ya yardar masa
fita zuwa ga farauta, ya ce da shi, "Kada ka
wuce dare daya, ka dawo zuwa gare ni gobe. Ka
sani cewa ba ni jin dadin abnici face kana kusa
gare ni, kuma ni har yanzu ban gasgata ka warke
ba gaba daya." Daga nan sai Sarki ya wake
wadannan baitoci uku:
"Na kasnace wagga rana,
A cikin dukkan ni'ima.
Duniya duka ta kasnace,
A gare ni kamar a ce ma.
Fiffiken sauro ya fi ta,
Daraja in babu kai ma."
Sarki ya yi umurni aka daura wa dawaki biyu
amalanke, aka dorawa raguma biyu da wasu
dawaki biyu kayan abinci da ruwa. Sarki ya yi
ban kwana da shi, ya yi musu addu'ar a dawo
lafiya, sannan ya rungume shi ga kirjinsa ya ce,
"Na roke ka, kada ka faku daga gare ni face dare
daya. Ni ba zan iya yin barci ba face ka dawo."
Yayin nan Kamaruzzaman da Marzuwan suka hau
amalanke suka kora sauran dabbobin, doki biyu
dauke da kayan abinci da na kafa tantuna, da
rakuma biyu dauke da ruwan sha suka tafi, ya
hana kowa ya bi su har suka fita daga cikin birni.
Suka ci gaba da tafiya cikin hanzari, tun daga
rana ta farko har zuwa rana ta biyu ba tare da
sun tsaya ba. A daren rana ta biyu suka tsaya
suka huta, dabbobinsu ma suka huta. Daga nan
suka ci gaba da tafiya ba su ja linzami ba sai
bayan kwana uku, yayin nan suka iso wani wuri
inda hanyar ta rarrabu, a gaba kuma daji ne mai
duhun gaske.
Da suka iso wannan wuri, sai Marzuwan ya kama
rakumi daya da doki daya ya yanka. Ya daddatsa
naman dabbobin tare da kashinsu, ta yadda ba
za a iya gane ko mene ne aka kashe ba. Ya cire
rigarsa da rawaninsa, ya yayyaga su tamkar
wanda yayi kurmususu da kura, ya cakuda su da
jinin dabbobin nan da yanka, ya jefar da su bisa
hanya. Ya umurci Kamaruzzaman ya aikata
kamar yadda ya aikata, kamaruzzaman bai yi
masa musu ba, ya aikata haka ga rigarsa da
rawaninsa. Kamaruzzaman ya tambaye shi
hikimar yin hakan.
Marzuwan ya ce, "Ka sani cewa, yayin da muka
wuce ranar farko ba mu koma gida ba, babu
shakka mahaifinka ba zai hakura ba, zai biyo
sawunmu. Na tabbata kuma ba za mu yi nisa ba
zai tarar da mu. Amma yanzu idan ya iso nan ya
ga rigunanmu cikin jini a yayyage, zai zaci cewa
mun hadu da 'yan fashi ne, suka kashe mu suka
kwace mana kaya. Ko kuma ya zaci cewa wata
dabbar daji ce ta kashe mu, ta haka sai ya
hakura ya koma gida, mu kuwa sai mu ci gaba
da tafiyarmu cikin kwanciyar hankali."
Kamaruzzaman ya ce, "Babu shakka wannan
dabara taka akwai hikima a cikinta."
Daga nan suka daura wa dawakai biyu sirdi, suka
debi abin da za su iya diba na guzuri, suka yi wa
jahar da birnin Sin take tsinke. Suka yi ta tafiya
babu dare babu rana har suka fara shiga wani
yanki na Kasar Sin. Duk tsawon wannan lokaci
babu abin da Kamaruzzaman yake yi sai zubar
da hawaye na bakin cikin rabuwa da mahaifinsa,
da kuma farin ciki zai sadu da abar begensa.
Yayin da Marzuwan ya fada masa cewa sun
shiga karkarar kasar Sin, saboda farin ciki sai
Kamaruzzaman ya waka wadannan baitoci:
"Abar so a guna takan zan gudu,
A yayin da ta mallaken zuciya.
Ki san babu hanyar gudu a gare ki,
Ina nan tafe nan da sa'a daya.
Yarda takan kaurace kun jiya,
Idan babu kauna cikin zuciya.
Na bar mahaifi garan can gida,
Yana zub da kwalla kamar maliya.
Ni na yi karya da zan je farauta,
Ka yafen mahaifi ka zan juriya.
Yayin da ya gama wakarsa, sai Marzuwan ya ce
masa, "Ya shugabana, duba can gabanmu, mun
iso tsibiran kasar Sin na Sarki Gayur mai fadoji
bakwai." Da Kamaruzzaman ya ji haka, ya duba
gaba gare su, ya hangi gine-ginen birnin Sin. Ya
cika da farin ciki marar misaltuwa, ya rungume
Marzuwan don murna, ya sumbaci goshinsa. Da
suka shiga cikin gari, sai Marzuwan ya nufi da su
gidan baki, ya biya musu kudin dakuna, suka huta
tsawon kwana uku, gajiyar tafiya ta sake su.
Bayan sun huta, sai Marzuwan ya ja hannun
Kamaruzzaman zuwa gidan wanka, suka yi
wanka suka tsabtace jikinsu. Marzuwan ya tafi
kasuwa ya sayo wa Kamaruzzaman tufafi masu
tsada irin na bokaye, ya kuma sayo masa kayan
aune-aune irin na masu bayar da magani. Ya
kawo masa ya ce, "Ya shugabana, ka saka
wadannan tufafi a jikinka, ka riki wadannan
kayayyaki ga hannunka, ka tafi kusa ga fadar
Sarki Gayur. Ka yi kira da murya madaukakiya
kana cewa kai boka ne mai bayar da magani,
babu cutar da ba ka da maganinta. Idan Sarki ya
ji ka, zai turo a tafi da kai wurinsa, zai fada maka
labarin ciwon 'yarsa da kuma sharadin da ya
gindaya ga dukkan wanda ya warkar da ita ko
akasin haka. Ka ce masa ka amince za ka
warkar da ita, idan aka kai ka wurinta, ka shiga
gare ta. Tana ganin ka za ta warware daga
rashin lafiyarta, sai ka ba ta abinci da abin sha
har karfin jikinta ya dawo. Wassalam, Allah ya ba
ka sa'a."
Kamaruzzaman ya riki hannun Marzuwan ya
sumbace shi, ya yi ta yi masa godiya. Daga nan
ya saka tufafi, ya riki kayan magani ga hannunsa,
ya zama kamar wani bakon boka, ya nufi fadar
Sarki Gayur. Da ya isa kofar fada, sai ya daga
muryarsa ya ce, "Ni ne boka uban bokaye, ni ne
lamiri mai gani har hanji, na auri doguwa ta aure
ni. Ina mai neman sa'a, a ba shi? Ina wanda ya
yi mafarki, a fassara masa? Ina wanda aljani ya
kama, a fitar masa? Wa yake fama da wata cuta
da ta gagari masu magani? Ga boka uban
bokaye." Yayin da mutanen gari suka ji shi, sai
suka kewaye shi, rabon da su ji tallar maganin
wani boka a wannan kasa har sun manta. Suka
ga Kamaruzzaman saurayi ne kyakkyawa, kamar
dan saurayin aljani, wanda babu kamarsa.
Wani dan tsoho tukuf, dan gajere kamar a kife da
kwando, ya dogaro sandarsa ya kutso mutane ya
tsaya a gaban Kamaruzzaman, ya daga kai ya
dube shi, ya ce masa, "Dan samari, kada ka jefa
kanka cikin halaka don kawai kwadayin auren
gimbiya Badura, bokaye da yawa, wadanda suka
fi ka ilimin sanin magunguna da taurari, duk sun
hallaka sanadiyyar wannan yarinya. Kawunansu
na nan makale a gaban gidanta, idan ka gan su,
sun ishe ka ishara. Amma na hore ka, ka kubutar
da wannan kyakkyawar sura taka daga halaka."
Kamaruzzaman bai ko kula wannan dan tsoho ba,
ya kara daga murya, ya yi kira da karfi, "Ni ne
boka uban bokaye, ni ne lamiri mai gani har hanji,
na auri doguwa ta aure ni. Ina mai neman sa'a, a
ba shi? Ina wanda ya yi mafarki, a fassara masa?
Ina wanda aljani ya kama, a fitar masa? Wa yake
fama da wata cuta da ta gagari masu magani?
Ga boka uban bokaye." Mutanen gari suka
tausaya masa saboda kyawunsa, suka hane shi
kada ya jefa kansa cikin halaka, amma ya ki.
Suka ce masa je ka, ai mai rabon shan duka ba
ya jin kwaba sai ya sha. Shi kuwa yana cewa a
cikin ransa, "Babu tsimi babu dabara, face daga
Allah madaukakin Sarki." Ya ci gaba da tallar
magani da murya madaukakiya a gaban fadar
Sarki Gayur.
**** **** ****
Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar
labarun DARE DUBU DA DAYA, wanda littafin
(15) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI

labarun DARE DUBU DA DAYA, wanda littafin(16) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI
SHAHRUZZAMAN

Kamaruzzaman bai kula da gargadin dan tsoho
da sauran jama'ar gari ba, ya ci gaba da tallar
magani, a kofar fadar Sarki Gayur, cikin murya
madaukakiya, "Ni ne boka uban bokaye, ni ne
lamiri mai gani har hanji, na auri doguwa ta aure
ni. Ina mai neman sa'a, a ba shi? Ina wanda ya
yi mafarki, a fassara masa? Ina wanda aljani ya
kama, a fitar masa? Wa yake fama da wata cuta
da ta gagari masu magani? Ga boka uban
bokaye."

Allah da ikonsa sai Sarki Gayur ya jiyo muryarsa,
ya juya ga Wazirinsa ya ce, "Tafi da sauri ka zo
mini da mai tallar maganin can." Waziri ya tashi
da hanzari ya fito waje, ya tarar da jama'a sun
zagaye Kamaruzzaman suna kallonsa. Ya kutsa
ya jawo hannunsa suka nufi wurin Sarki. Da
zuwansu gaban Sarki, sai Kamaruzzaman ya fadi
kasa, ya gayar da Sarki cikin ladabi da
girmamawa, sa'annan ya waka wadannan
baitoci:
"Takwas na cikin girma, na tara dukkansu. Daya
bai gushe ba a cikinsu daga gare ka, tsawon
zamani, domin sakankancewarka da tsoron Allah,
da girmanka, da baiwarka, da lafazinka, da
harshenka, da iliminka, da daukakarka, da nasara
a kan makiyanka. Allah ya dawwamar da
mulkinka tsawon zamani, ya Sarki mai adalci."
Sarki ya yi murna da jin wannan waka, ya yi
mamakin fasahar Kamaruzzaman da kuma
ladabinsa, ya riki hannunsa ya zaunar da shi
kusa gare shi. Ya dube shi da kyau ya ce, "Na
rantse da Allah, ba ka yi kama da bokaye ba. Ina
ba ka shawara da ka tsirar da rayuwarka da
kuma kyawunka daga takobin hauni. Ka sani
cewa na riga na yi alkawari duk wanda ya yi ido
hudu da 'yata kuma ya kasa warkar da ita daga
cutar da take ciki, zan sa a sare kansa a sargafe
shi a gaban gidanta. Amma kuma duk wanda ya
yi nasarar warkar da ita, zan aura masa ita, zan
kuma raba kasata biyu in ba shi rabi." Sarki ya
dafa hannun Kamaruzzaman ya ci gaba da cewa,
"Wallahi, na rantse da Allah, idan ka shiga wurin
'yata, kuma ka kasa warkar da ita, babu makawa
zan sa a sare kanka, kyawunka ba zai amfana
maka kome ba."

Kamaruzzaman ya dan yi murmushi ya ce, "Na
amince da wannan sharadi naka, Allah ya ba ka
nasara. Ai tun kafin na zo nan, na san da
wannan alkawari da ka yi." Sarki ya sa aka kira
alkalai, suka shaida abin da Kamaruzzaman ya
fada. Daga nan Sarki ya hada shi da wani bawa
ya ce, "Tafi da wannan saurayi wurin gimbiya
Badura." Bawa ya riki hannun Kamaruzzaman
suka nufi gidan da Badura take tsare. Da suka
kusa isa gidan, saboda dokin ganin abar begensa,
sai Kamaruzzaman ya kwace

1 Comments On HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHRUZZAMAN
avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Wanne darasi kuka ?aru da shi daga cikin wannan hikayar,

Please Login or Register in order to submit comment