Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kirar
kasar Yaman ta rike a hannunta, a daya hannun
kuma ta riki sanda wadda take dogarawa. Ta nufi
gidan Na'imu dan Rabi'u, tana tafe tana zikiri
tana kaskantar da kanta. Tana cewa, "tsarki ya
tabbata ga Allah madaukakin Sarki. Yabo da
godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai.
Mun shaida babu Sarki sai Allah, mun kuma
shaida Annabi Muhammadu Manzon Allah ne,
kuma bawansa ne." Haka dai wannan tsohuwa ta
tafi tana ambaton Allah a baki, dukkan mutumin
da ya hadu da ita sai ya ce wannan baiwar Allah
ce mai yawan ibada. Ita kuwa a cikin zuciyarta
babu kome sai kissa da makirci. Ba ta gushe ba
tana tafiya har ta iso gidan Na'imu dan Rabi'u
daidai lokacin sallar azahar.
Tana isa sai ta kwankwasa kofa, wani bawa ya
leko ya tambaye ta, "me kike so, ya ke
gyatuma?" Ta rauda kai ta amsa masa, "ni
tsohuwa ce talaka, mai bautar Ubangiji, na ga
lokacin sallar azahar ya yi. Ina so in shiga
wannan gida mai albarka domin sauke farali."
Bawa ya ce, "ya ke gyatuma, ki sani cewa
wannan wuri ba masallaci ba ne face gidan
Na'imu dan Rabi'u."
Tsohuwa ta ce, "ya dana, ai babu masallacin da
ya kai gidan Na'imu dan Rabi'u a wuri na. Ka
sani cewa ni ina daga cikin zababbun masu
bautar Ubangiji wadanda Sarkin muminai ya ajiye
a fadarsa domin yi masa addu'a. Na zo wannan
gari ne domin ziyara irin ta addini."
Bawa dai ya yi tsaye bisa ra'ayinsa cewa ba za
ta shiga ba, sai dai ta nemi masallaci ko wanii
gidan na daban. Tsohuwa ta riki hannunsa tana
cewa, "yanzu kamar ni da nake shiga gidan
Shugaban Muminai da sauran Sarakuna, ba tare
da shamaki ba, za a hana ni shiga gidan Na'imu
dan Rabi'u?" Suna cikin wannan gardama sai
Na'imu ya fito daga cikin gidan domin ganin abin
da ke faruwa. Ya nemi bahasin gardamar
tsohuwa da bawa, tsohuwa ta gaya masa
bukatarta. Na'imu ya yi murmushi ya ce wa bawa
ya bar ta ta shigo.
Tsohuwa ta bi Na'imu a baya, tana sa masa
albarka, suka wuce cikin gida inda suka tarar da
Na'imatu tana zaune ta ci kwalliya, tana sheki
kamar wata. Na'imatu ta gaida tsohuwa cikin
ladabi. Tsohuwa ta dube ta, ta tabbatar wa kan
ta cewa lalle Na'imatu yarinya ce kyakkyawa,
wadda babu kamar ta a wannan zamani. Sai ta
ce mata, "ya shugabata, ina horon ki da ki rika
addu'ar neman tsari ga Allah madaukakin Sarki
domin ya kare ku daga miyagun idanu, ke da
mijinki.37 HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHARUZZAMAN

Tsohuwa ta bi Na'imu a baya, tana sa masa
albarka, suka wuce cikin gida inda suka tarar da
Na'imatu tana zaune ta ci kwalliya, tana sheki
kamar wata. Na'imatu ta gaida tsohuwa cikin
ladabi. Tsohuwa ta dube ta, ta tabbatar wa kan
ta cewa lalle Na'imatu yarinya ce kyakkyawa,
wadda babu kamar ta a wannan zamani. Sai ta
ce mata, "ya shugabata, ina horon ki da ki rika
addu'ar neman tsari ga Allah madaukakin Sarki
domin ya kare ku daga miyagun idanu, ke da
mijinki,

miyagun idanu, ke da mijinki, saboda baiwar da
ya yi muku ta kyau." Daga nan ta nemi ruwa ta
yi alwala, aka kawo mata shimfidar salla.
Ta tsayu a kan shimfida, ta kabbara salla. Ba ta
gushe ba tana salla har sai da rana ta fadi, duhu
ya maye gurbin ta. Bayan ta sallame tana shirin
mikewa domin kabbara wata sallar, sai Na'imatu
ta ce mata, "haba inna, ki tsaya ki huta mana ko
kafafunki sa dan sarara." Tshohuwa ta ce, "ya
shugabata, ina maganar hutu ga bawa mai
neman tsira gobe kiyama. Wanda duk bai nemi
lahirarsa ba a lokacin rayuwarsa hakika ya tabe."
Na'imatu ta tashi ta kawo mata abinci da abin
sha. Tsohuwa ta karba ta yi godiya, ta ce,
"madalla da samun abincin bude baki." Na'imatu
ta tambaye ta ta yi azumi ne? Tsohuwa ta amsa
mata cewa, ai ita kullum azumi take yi. Ta jawo
mata aya ta saba'in a cikin Suratul Furkan:
"Sai fa wadanda suka tuba suka ba da gaskiya,
sa'annan suka aikata aiki na kwarai. Wadannan,
Allah zai juyar da miyagun ayyukansu zuwa
ayyuka na kwarai. Domin kuwa Allah mai yawan
gafara ne, mai yawan jin kai ne."
Na'imatu ta zauna suka ci gaba da mayar da
zance, ita da tsohuwa, zuwa wani lokaci. Daga
nan sai ta ce wa mijinta, Na'imu, "ya shugabana,
ka roki wannan tsohuwa ta kwana wurin mu ko
ma sami albarkacinta." Na'imu ya lallashi
tsohuwa, ta amince da kyar cewa za ta kwana
amma da gari ya waye za ta ci gaba. Na'imu ya
sa aka shirya mata wani daki wanda za ta kwana
a ciki, ya ce kada wanda ya je ya dame ta a
yayin da take ibadarta, watakila wannan zuwa
nata ya zama alheri a gare su.
Tsohuwa ta shige daki. Sai ta kasance wani
lokaci ta yi ta salla, wani lokaci kuma ta zauna
ta yi ta karatun Alkur'ani. Haka ta kwana har gari
ya waye. Yayin nan ta je wurin Na'imu da
Na'imatu ta yi musu barka da kwana. Ta ce
musu, "ina rokon Allah ya tsare ku da
tsarewarsa." Suka tambaye ta ba dai tafiya za ta
yi ba tun da sassafe haka? Ta ce musu ita kam
ta yi harama. Suka lallashe ta a kan ta kara
kwana, amma ta ce a'a, sai dai idan ta kuma
dawowa wani lokaci. Haka suka yi sallama, ba
tare da sun so rabuwa da ita ba, har Na'imatu na
fitar da kwalla.

Bayan tsohuwa ta fita daga gidan Na'imu dan
Rabi'u sai ta nufi gidan Hajjaj, Sarkin Kufa. Da
Sarki ya gan ta sai ya tambaye ta, "ina labari?"
Ta amsa masa, "na sadu da kuyangar, hakika
babu wata mace da ta kai ta kyau a wannan
zamani."
"To, za ki iya dabarar da kika sato ta?" Sarki ya
tambaya. "Hakika idan kika yi mini wannan kokari
zan yi miki kyauta mai tsoka."
"Allah ya ba ka nasara." Tsohuwa ta karkace kai.
"Ina so ka ba ni akalla wata daya, zan kawo
maka ita har gida."
Sarki ya ce, "je ki an ba ki."
Daga ranar nan sai tsohuwa ta kasance tana
ziyartar Na'imu da Na'imatu, wani lokaci ta tafi
da safe, wani lokaci kuma ta tafi gidan da
yamma..

Suka rika kyautata mata, suna girmama
ta matuka saboda yawan ibadarta. Wata rana ta
tafi gidan sai ta tarar da Na'imatu kawai a gidan.
Suka zauna suka yi ta hira, da za ta tafi sai ta
ce wa Na'imatu, "shugabata, ni kam kullum na je
dakin ibada nakan rika yi muku addu'a ke da
maigidanki, nakan kuma roki manyan waliyyan da
muke ibada tare su yi muku addu'a. Ina ma wata
rana za ki tafi tare da ni wannan dakin ibada
domin in hada ki da manyan waliyyan Allah ko
kya sami tubarrakinsu."
Na'imatu ta ce, "ai kuwa ina so wata rana mu
tafi tare. Ni dai ba abin da nake so kamar bayin
Allah masu yawan ibada."
Tsohuwa ta ce, "ki nemi izini wurin mijinki, ko
wurin uwar mijinki."
Na'imatu ta tashi ta tafi bangaren mahaifiyar
Na'imu domin ta nemi izini wai ta bar ta wata
rana ta bi wannan tsohuwa. Suna cikin haka sai
ga Na'imu ya shigo, tsohuwa ta gai da shi tana
sa masa albarka. Daga nan ta fita ta nufi gida.
Washe gari tsohuwa ta dawo, ba ta iske Na'imu
ba. Ta ce da Na'imatu, "jiya mun kwana muna yi
muku addu'a har sai da manyan waliyya suka
tambaye ni wai wace ce wannan da kike yawan
yi wa addu'a? Na amsa musu cewa yau zan kawo
ki wurin su su gan ki." Tsohuwa ta ci gaba da
cewa, "tashi maza yanzu ki shirya mu tafi, kafin
mai gidan ki ya dawo mu tafi mun dawo, domin
ba dadewa za mu yi ba."
Na'imatu ta tafi wurin mahaifiyar Na'imu ta
durkusa gabanta, ta ce, "ina rokon ki don Allah,
ya shugabata, ki yi mini izini in tafi tare da
wannan tsohuwa wurin waliyyan Allah. Za mu
dawo da sauri kafin mijina ya dawo."
Uwar Na'imu ta ce, "ni ina ji miki tsoron mijinki
ya dawo bai iske ki ba."
Na'imatu ta ce, "na rantse da Allah ba tsayawa
za mu yi ba. Za mu dawo tun kafin ya dawo."
Tsohuwa ta tsoma bakinta, "ai ko zaunawa ba za
mu yi ba. Daga tsaye za su gaisa sa'annan mu
juyo da sauri."
Mahaifiyar Na'imu ta ce su tafi, amma kada su
bari Na'imu ya riga su dawowa. Tsohuwa ta riki
Na'imatu ta fita da ita, bayan ta dabaibaye ta da
kissa, ta nufi fadar Sarki da ita. Da zuwa ta kai
ta wani daki a cikin fadar ta kulle, ta tafi ta fada
wa Sarki. Sarki ya ga Na'imatu, ya tabbatar wa
kansa lalle ba karya aka yi ba, da aka ce ta fi
dukkan matan zamaninta kyau.
Yayin da Na'imatu ta ga Sarki ya shiga wurin ta,
duk da yake ba ta san ko wane ne shi ba, sai ta
rufe fuskarta da mayafi. Bayan Sarki ya kare
mata kallo, sai ya kira wani bafadensa ya
umurce shi ya hada dawaki hamsin tare da
mahayansu zai aike shi zuwa Damashka wurin
Halifa Abdulmalik dan Marwan domin ya kai
masa kyautar wata kyakkyawar kuyanga. Ya
kuma umurci bafaden da cewa ya aza Na'matu
bisa rakuma ta musamman da aka kawata da
ado. Ya kawo takarda ya ba bafaden, ya ce, "ka
ba Sarkin Muminai wannan takarda, sa'annan ka
komo mini da jawabinta."
Bafade ya tafi ya shirya dukkan abin da Sarki ya
umurta. Aka fito da Na'imatu tana kuka, domin
rabuwa da Na'imu, aka aza ta bisa rakuma, aka
nufi Damashka da ita. Suka yi ta tafiya, dare da
rana, har suka isa birnin Damashka. Bafaden
Sarkin Kufa ya nemi iso wurin Halifa, aka yi
masa. Bayan ya yi gaisuwa, ya kawo sakon
Sarkin Kufa da Na'imatu da takarda, ya ba Halifa.
Bayan Halifa ya karanta takarda, sai ya umurci
bayinsa su shirya wa Na'imatu dakin da za ta
zauna a cikin gidansa. Halifa ya shiga wurin
uwargidansa ya ce mata, "Sarkin Kufa ya aiko
mini da kyautar kyakkyawar kuyanga, daya daga
cikin zuri'ar Sarakunan Kufa na dauri, wadda ya
saya dinari dubu goma." Matar ta ce da shi" "madalla da wannan kokari na
Sarkin Kufa. Ya kamata Halifa ya ba shi tukuici
mai tsoka."
To, ashe wannan magana da Halifa ke yi da
uwargidansa duka a cikin kunnen wata kanwarsa
take shiga. Nan da nan sai wannan kanwa ta
Halifa ta sulale ta nufi dakin da aka shirya wa
Na'imatu domin ta gan ta.Yayin da ta ga Na'imatu da irin
kyawon da Allah ya hore mata, sai ta ce, "hakika
wanda duk ya same ki a gidansa ya yi farin ciki.
Kamata ya yi a saye ki dinari dubu dari
maimakon dinari dubu goma."
Na'imatu ta dube ta ta ce, "ya ke wannan mai
annurin fuska, shin fadar wane Sarki ce wannan?"
"Nan birnin Damashka ne. Kuma kina cikin fadar
dan uwana ne, Halifa Abdulmalik dan Marwan,
Shugaban muminai." In ji kanwar Halifa. "Ke duk
ba ki san da wannan ba?"
"Na rantse da Allah ban san inda nake ba, ya
shugabata."
"To, amma shi wanda ya saye ki bai fada maki
cewa zai turo ki nan ba, wurin Shugaban
Muminai ba?"
Yayin da Na'imatu ta ji haka, sai hawaye suka
zubo daga idanunta, ta ce a cikin ranta, "wallahi
an yaudare ni, idan ma na fada musu gaskiya ba
yarda za su yi ba. Na damka al'amarina ga Allah
Madaukakin Sarki zuwa ranar da gaskiya za ta
bayyana." Sai ta dukar da kan ta kasa cikin
tunani. Kanwar Halifa ta lura da fuskar Na'imatu
ta dan yi duhu saboda tafiya da kuma zafin rana.
Saboda haka sai ta tashi ta fita domin ta ba ta
wuri ta dan sarara.
Washe gari kanwar Halifa ta zo wa Na'imatu da
tufafi masu kyau, na alfarma, da sarka ta
zinariya. Bayan ta sa Na'imatu ta yi wanka, sai
ta ba ta kayan da ta zo mata da su ta sanya.
Kayan kuwa suka yi mata kyau kamar an gwada
da jikinta, ta kawo wani mayafi ta rufe rabin
fuskarta. Yayin nan sai ga Halifa ya shigo wurin
su, ya zauna kusa ga Na'imatu.
Kanwarsa ta dube shi ta ce, "ya dan uwana, ka
yi duba zuwa wannan kuyanga, wadda Allah ya
hore wa dukkan nau'i na kyau."
Halifa ya umurci Na'imatu ta yaye mayafin da ta
rufe fuskarta da shi domin ya ga fuskarta.
Na'imatu ta ki yaye mayafin, maimakon haka ma
sai ta sa hannunta ta dafe shi, gudun kada Halifa
ya ce zai yaye da kansa. A wannan rana dai
Halifa bai ga fuskar Na'imatu ba, sai wuyan
hannunta kawai ya gani, wanda hakan ya rura
wutar begenta a cikin zuciyarsa. Ya ce da 'yar
uwarsa, ta yi kokari ta lallasar masa ita kafin
kwana uku, lokacin da zai dawo dakinta. Ya tashi
ya fita.

Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ38 HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHARUZZAMAN

Halifa ya umurci Na'imatu ta yaye mayafin da ta
rufe fuskarta da shi domin ya ga fuskarta.
Na'imatu ta ki yaye mayafin, maimakon haka ma
sai ta sa hannunta ta dafe shi, gudun kada Halifa
ya ce zai yaye da kansa. A wannan rana dai
Halifa bai ga fuskar Na'imatu ba, sai wuyan
hannunta kawai ya gani, wanda hakan ya rura
wutar begenta a cikin zuciyarsa. Ya ce da 'yar
uwarsa, ta yi kokari ta lallasar masa ita kafin
kwana uku, lokacin da zai dawo dakinta. Ya tashi
ya fita.
Na'imatu kuwa sai ta kasance cikin damuwa da
bakin ciki mai yawa saboda rabuwa da mijinta
Na'imu dan Rabi'u. Wannan abu sai ya zamar
mata ciwo, ta kasance ba ta ci ba ta sha, sai
kuka. Cikin 'yan kwanaki kadan ta rame, fuskarta
ta komade. Da Halifa ya ga haka sai hankalinsa
ya tashi, ya sa aka nemo masa masu magani da
malamai, suka yi ta ba ta sakesaki da sayyu,
malamai kuma suka dukufa kan addu'a, amma
duk a banza, ciwo sai gaba-gaba yake yi, kamar
iska na hura wuta. Wannan shi ne al'amarinta.
Al'amarin Na'imu kuwa, lokacin da ya dawo gida
sai ya zauna bisa shimfida. Ya yi kira, "ina kike
ne Na'imatu." Bai ji an amsa masa ba. Sai ya
mike bisa dugadugansa, ya kara kwala kira da
karfi, amma babu wanda ya amsa masa, hatta
mahaifiyarsa saboda tana jin tsoron abin da zai
faru.
Na'imu ya nufi dakin mahaifiyarsa, ya iske ta
zaune, ta yi tagumi. Ya tambaye ta, "ya
mahaifiyata, ina Na'imatu ta shiga ne?"
"Ya dana, sun fita tare da tsohuwa mai yawan
ibada domin su ziyarci manyan waliyyan Allah
masu bauta."
"Tsawon wane lokaci suka tafi?"
"Tun da sassafe suka tafi, bayan ka fita."
Na'imu ya yi jugum yana tunani, "me ya sa kika
bar ta ta fita tare da wannan tsohuwa?"
Mahaifiyar Na'imu ta amsa masa, "ita ce ta
dame ni da in bar ta su tafi, ta ce mini ba
dadewa za su yi ba."
Na'imu ya ce, "babu tsimi babu dabara face daga
Allah Madaukakin Sarki." Daga nan ya fita daga
wurin mahaifiyarsa, zuciyarsa cike da damuwa,
bai zame ko'ina ba sai gidan Sarkin Dogarai.
Na'imu ya ce masa, "kuna aikin me a cikin garin
nan har aka sace mini kuyanga? Babu makawa in
yi karar ka gun Halifa Shugaban Muminai."
Sarkin Dogarai ya ce, "wa ya sace maka
kuyanga?"
Na'imu ya ce, "wata tsohuwa wadda ta sa tufafin
gashi, ta rataya tasbaha mai ‘ya’ya dubu a
wuyanta. Tana yawo da sanda da kuma butar
karfe a hannunta."
Yayin da Sarkin Dogarai ya ji kamannun wannan
tsohuwa, sai ya shaida ta a matsayin tsohuwar
kuyangar Hajjaj, Sarkin Kufa, domin cikin 'yan
kwanakin da suka wuce a cikin wannan shiga
yake ganin ta. Don haka sai ya tabbatar a cikin
ransa cewa Hajjaj din ne ya sa wannan tsohuwa
ta sace kuyangar. Sai ya ce da Na'imu, "ka kawo
mini wannan tsohuwa a gabana, ni kuwa zan
tursasa ta ta kawo maka kuyangarka."
Na'imu ya ce, "to, yaya za a yi na kawo maka
ita, tunda ban san ta ba, ban kuma san gidanta
ba. Ban da Allah, wa ya san abin da yake boye?"
"Wannan haka yake, Allah kadai ya san abin da
yake boye," in ji Sarkin Dogarai.
"Babu makawa in je wurin Hajjaj in kai kararka
saboda sakacinka na rashin duba gari har a sace
mutum ba ka kama barawon ba."
Sarkin Dogarai, wanda ya fara harzuka, ya ce
masa ya tafi duk inda zai kai kararsa ya kai. To,
dama mahaifin Na'imu yana daya daga cikin 'yan
majalisar Sarkin Kufa, don haka ne Sarki ya san
Na'imu sosai. Da Na'imu ya bar gidan Sarkin
Dogarai sai ya nufi fada. Aka yi masa iso, Sarki
ya tambaye shi abin da ke tafe da shi. Na'imu ya
kwashe abin da ke tafe da shi ya gaya
wa Hajjaj, nan da nan shi kuma ya ce a kira
masa Sarkin Dogarai.
Yayin da Sarkin Dogarai ya zo, sai ya fadi ya yi
gaisuwa, Sarki ya umurce shi ya nemo tsohuwar
da ta sace kuyangar Na'imu dan Rabi'u, amma
sai ya kyabci Sarkin Dogarai da ido, domin ya
san cewa Sarkin Dogarai ya san wannan tsohuwa
kuyangarsa ce.
Sarkin Dogarai ya dukar da kai ya ce, "Allah ya
ba ka nasara, wa ya san abin da ke boye ban da
Allah Madaukakin Sarki?"
Hajjaj ya ce, "ka tashi dogarai masu dawaki su
shiga kowane lungu da sako na wannan birni su
duba ta, har bayan gari, da kauyukan da ke
kewaye da wannan birni duka su tafi su duba ta."

Sarki, Hajjaj Sarkin kufa ya ce da Sarkin Dogarai,
"ka tashi dogarai, masu dawaki, su shiga kowane
lungu da sako na wannan birni su duba ta, har
bayan gari, da kauyukan da ke kewaye da
wannan birni duka su tafi su duba ta." Daga nan
sai ya juya wurin Na'imu ya ce masa, "idan ba a
gane ta ba, zan ba ka kuyangi goma daga
gidana, da kuma wasu kuyangi goma daga gidan
Sarkin Dogarai, maimakon taka kuyangar da aka
sace." Ya yi tsawa ga Sarkin Dogarai, "maza ka
nemo masa kuyangarsa."

Na'imu ya koma gida cike da bakin cikin rabuwa
da Na'imatu. A wannan lokaci kuwa shekarunsa
goma sha hudu, amma babu kwarar gashi ko
daya a habarsa. Da dare mahaifinsa ya shigo
gida, ya ce masa, "babu makawa Hajjaj ne ya
shirya kutungwilar da aka sace maka kuyanga,
amma ka yi hakuri watakila Allah ya sake hada
ka da ita wata rana." Tun daga wannan rana sai
Na'imu ya shige dakinsa ya yi ta kuka, ya daina
zuwa ko'ina. Idan mahaifiyarsa ta kawo masa
abinci sai ya ci kadan ya ture akushin gefe. Nan
take ya kwanta rashin lafiya mai tsanani, har ya
kasance sai dai a kwantar a tayar. Aka yi magani
har aka gaji amma bai warke ba. Ya zauna cikin
wannan hali tswon wata uku har iyayensa sun
fara debe tsammani. Rannan kwaram, sai ga
wani bakon mai magani ya fado garin daga
Farisa.
Yayin da mahaifin Na'imu ya ji labarin zuwan
wannan bakon Boka, kuma ya ji cewa shahararre
ne, babu maganin cutar da ba ya da shi, sai fa ta
ajali. Nan da nan ya tafi da shi zuwa ga Na'imu.
Mai magani ya zauna kusa ga Na'imu, ya riki
hannusa, ya yi duba a cikin tafin hannun Na'imu,
ya dade yana nazarinsa, sa'annan ya dubi fuskar
Na'imu. Daga nan sai ya yi dariya, ya dubi Rabi'u
dan Na'imu ya ce, "cutar danka tana tattare a
cikin zuciyarsa."
Rabi'u ya ce, "Ka yi gaskiya, ya kai wannan mai
magani. Ina so ka yi amfani da saninka da kuma
fasaharka, ka warware mini dukan cutar da ke
damun dana. Kada ka boye mini kome."
Boka ya ce, "danka ya kamu da ciwon son wata
yarinya wadda a halin yanzu ko dai tana Basara
ko kuma tana Damashka. Babu wani magani da
zai warkar da shi daga wannan cuta face haduwa
da wannan yarinya da yake so."
"Idan kuwa ka yi kokarin hada su da juna," in ji
Rabi'u, "zan ba ka dukkan abin da ka nema gare
ni. Zan yalwata ka da dukiya mai yawa tsawon
rayuwarka."
Boka ya ce, "wannan abu ne mai sauki gare ni."
Ya juya wurin Na'imu da ke kwance kamar ruwa,
ya ce masa, "karfafa zuciyarka dan samari, idan
Allah ya so bukatarka za ta biya. Zan hada ka da
wadda kake so." Ya ce wa Rabi'u ya ba shi dinari
dubu hudu domin zai tafi Damashka tare da
Na'imu, kuma ba za su dawo ba sai tare da
kuyanga Na'imatu. Rabi'u ya kawo kudi ya ba
shi.
Mai magani ya tambayi Na'imu sunansa, ya gaya
masa. Sai ya ce, "ya Na'imu, tashi zaune ka ci
abinci ka kuma sha abin sha, ka karfafa
zuciyarka, domin yau din nan za mu tashi zuwa
Damashka wurin masoyiyarka. Ba za mu dawo ba
sai tare da ita."
Suka rika shi ya tashi zaune, aka kawo masa
abinci da abin sha. Ya ci, ya sha ya koshi, karfin
jikinsa ya dan dawo. Rabi'u ya shirya musu
dawaki da rakuma domin tafiya, ya kawo dinari
dubu goma ya ba mai magani. Na'imu ya yi
sallama da mahaifinsa da mahaifiyarsa, Rabi'u ya
yi musu addu'ar samun nasara. Boka da Na'imu
suka hau dabbobinsu suka mika da tafiya, ba su
tsaya ko'ina ba sai garin Aliffo. Suka dan tambayi
labarin Na'imatu, da ba su sami wani abin
kamawa ba sai suka ci gaba da tafiya har suka
isa Damashka.
Da suka kwana uku a cikin Damashka, sai mai
magani ya kama hayar rumfa a cikin kasuwa. Ya
cika ta da kayayyakin magani iri-iri. Ya sayo
tasoshi na azurfa da zinariya, a cikin kowace
tasa ya zuba nau'in magani daban daban. Ya
cika wata tasa da sakesaki, wata kuma saiwowi
ne cikin ta, wata kuma ganyaye ne ciki. Ga kuma
goruna da battoci, kowace dauke da nau'in
magani na shafawa da na turarawa. Ya sa
tufafinsa irin na masu magani, ya rike wani abu a
hannunsa wanda yake auna marasa lafiya da shi.
Ya sayo wa Na'imu tufafi na siliki, irin na bokaye.
Bayan ya sa tufafin, Boka ya yi masa damara da
wani kyalle wanda a tsakiyarsa aka sa masa
wani maballi na zinariya. Ya zaunar da shi kusa
gare shi. Mutane suka yi ta mamakin irin kyawun
da Allah ya hore wa Na'imu.
Mai magani ya ce da Na'imu, "daga yanzu zan
rika kiran ka da dana, kai kuma ka rika amsa
mini da baba." Na'imu ya ce ya ji, ya aminta.
Suka zauna a haka, mai magani yana kiran
Na'imu da dansa, shi kuma yana amsa masa da
mahaifinsa. Kuma duk lokacin da zai yi masa
magana sai ya yi masa da Farisanci, Allah ya sa
shi ma Na'imu ya iya Farisancin, sai ya mayar
masa da jawabi da Farisanci. Mutane suka rika
zuwa suna karbar magani, wasu kuma sukan zo
da fitsari ko bayan garin mara lafiya. Shi kuma
mai magani zai karba ya auna, ya fadi irin cutar
da ke damun mai wannan fitsari ko bayan gari,
sa'annan ya kawo magani ya bayar. Cikin ikon
Allah kuwa, duk wanda ya karbi maganin sai ya
sami sauki. Nan da nan sai labarinsa ya karade
ko'ina a cikin birnin Damashka da kewaye.
Wata rana suna zaune a cikin rumfarsu sai suka
ga wata tsohuwa ta nufo rumfar tana haye bisa
jaki. Da ta zo gaban rumfar sai ta ja ta tsaya, ta
sa hannun ta yafuto mai magani. Ita wannan
tsohuwa da ganin ta za a gane ta fito ne daga
babban gida, domin kuwa tana sanye da tufafi na
alfarma, wadanda aka saka da lu'ulu'u, aka yi
musu kwalliya da zinariya da azurfa.
Mai magani ya tashi ya je kusa gare ta, ita kuma
tana zaune bisa jaki. Ta mika masa hannu ta ce,"taimaka mini in sauko daga kan
jakin nan." Mai magani ya rike hannunta, ta
sauko daga bisa jaki. Tsohuwa ta tambaye shi,
"kai ne Bafarishen mai maganin nan da ya zo
daga Kufa?" Ya amsa mata, "na'am."
Daga nan ta zaro wata 'yar batta karama, cike da
fitsari, ta mika masa, "ina da wata 'ya tawa da
take kwance babu lafiya." Mai magani ya karbi
batta, ya yi nazarinta cikin dan kankanin lokaci.
Ya dubi tsohuwa, "gaya mini sunan wannan diya
taki, domin in buga taurari da sunan nata in ga
lokacin da ya fi dacewa gare ta, ta sha magani."39 HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHARUZZAMAN

mai magani ya karbi batta daga hannun
tsohuwa, ya yi nazarinta cikin dan kankanin
lokaci. Ya dube ta, "gaya mini sunan wannan
diya taki, domin in buga taurari da sunan nata in
ga lokacin da ya fi dacewa gare ta, ta sha
magani."
"Ya kai wannan Mai magani, sunanta Na'imatu."
Tsohuwa ta amsa masa.
Mai magani ya tsuguna, ya share kasa. Ya shiga
yin wadansu zane-zane, idan ya yi sai ya share
ya kara zana wasu. Can sai ya dago kansa ya
ce, "sunanta kadai ba zai wadatar ba, sai kin
gaya mini sunan garinta na ainahi, domin na ga
kamar ba a wannan gari aka haife ta ba.
Sa'annan kuma ki gaya mini yawan shekarunta a
duniya."
Tsohuwa ta ce, "shekarunta goma sha hudu,
kuma an haife ta a garin Kufa."
Mai magani ya kara dukawa ga zane-zanensa,
can kuma sai ya tambayi Tsohuwa, "kin ce a
Kufa aka haife ta, to, yaushe ta zo wannan
birni?"
Tsohuwa ta amsa masa, " 'yan watanni kadan da
suka wuce."
Duk zancen nan da Mai magani ke yi da tsohuwa
Na'imu na sauraren su. Yayin da ya ji an ambaci
sunan kuyangarsa Na'imatu, sai ya yi kamar ya
some don murna.

Daga nan mai magani ya kara dukawa ga zane-
zane bisa kasa yana sharewa. Zuwa wani dan
lokaci ya dago kansa, ya ce wa tsohuwa, abu
kaza da abu kaza shi ne maganin da za a hada
mata, ta ba 'yarta. Tsohuwa ta yi farin ciki, ta
mika masa dinari goma ta ce, "Allah ya yi maka
albarka, ya kai mai magani. Yi sauri ka hada
mini, ko na koma gida da wuri, in kai mata."
Mai magani ya juya wurin Na'imu ya fada masa
kalar maganin da zai hada wa tsohuwa. Tsohuwa
ta dubi Na'imu, wanda tun lokacin da ta shigo
rumfar ba ta lura da yana wurin ba, fuskarta ta
juye zuwa tsananin mamaki. Ta ce, "Wallahi
wannan saurayi ya yi kama da ita, kamar an
tsaga kara." Ta tambayi mai magani, Na'imu
dansa ne ko kuwa bawansa ne? Ya amsa mata
da cewa dansa ne. Na'imu ya shirya wa tsohuwa
magani, ya saka shi a cikin wani dan karamar
batta, girman tafin hannu. Ya dauko takarda da
alkalami ya rubuta wannan sako:
"Idan Na'imatu ta ni'imta ni daga gani na idonta,
babu mai arzurta misalin arzikina. Ba kwa
kamanta kyawonta da kyawona ba, domin sun ce
an bayar a gare ta kyawo ashirin tamkar nata."
Ya nade takarda ya sa ta cikin batta tare da
maganin, ya rufe bakin battar. Bisa murfin batta
kuma ya rubuta sunansa da haruffan Kufa, ni ne
Na'imu dan Rabi'u mutumin Kufa. Ya mika wa
tsohuwa batta, ta karba ta yi sallama da su. Ta
hau jakinta ta koma fadar Halifa. Da ta

1 Comments On HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHRUZZAMAN
avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Wanne darasi kuka ?aru da shi daga cikin wannan hikayar,

Please Login or Register in order to submit comment