Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hannunsa daga
hannun bawa, ya nufi gidan cikin sauri, ya bar
bawa a baya. Bawa ya cika da mamaki yana
cewa a cikin ransa, "Ban taba ganin mai
gaggawar tura kansa ga halaka ba kamar wannan
saurayi, anya kuwa kansa daya?" Ya daga murya
ya ce, "Kai wannan mai gaggawar kai kansa ga
halaka, dakata tukuna in zo." Kamaruzzaman bai
tsaya ya saurare shi ba, ya ci gaba da sauri har
ya riga bawa isa kofar gidan.
Da suka isa kofar gidan, bawan dake tsaron kofa
ya bude musu kofa, ya yi musu rakiya cikin gidan
har zuwa bakin kofar dakin gimbiya Badura,
wanda kofarsa take a bude sai dai akwai labule
wanda ya rufe bakin kofar. Kamruzzaman ya ce
da bawa, "Shin in warkar da ita daga nan bakin
kofa, ba tare da na shiga wurinta ba? Ko kuwa in
shiga inda take?" Bawa ya yi mamaki da jin
wannan magana, ya ce, "Idan ka warkar da ita
daga nan bakin kofa ba tare da ka gan ta ba,
shakka babu, ka cika boka uban bokaye, kamar
yadda na ji kana ta kankambar yayatawa."
Jin haka sai Kamaruzzaman ya yi murmushi, ya
zauna a bakin kofar. Ya saka hannunsa cikin
jakar da ya zo da ita, ya dauko takarda da
alkalami da tawwada, ya fara rubutu kamar haka:
Wannan rubutu ne daga hannun wanda soyayya
ta raunata, wanda bege ya haukata, wanda ya
gwammace wa mutuwa a kan ya rayu ba tare da
abar begensa ba. Shi ne wanda babu mai
tausayin halin da zuciyarsa ta shiga, wanda a
kodayaushe yake ganin dare kamar yadda ya ga
rana, wanda jikinsa ya rame saboda tunani, da
dai bai koma jin labarin abar begensa ba tun
bayan rabuwarsu.
Daga nan sai ya rubuta wadannan baitoci:

"Na yi rubutu da zuciyar da ta dabaibaye a cikin
sonta. Na yi kukan kadaici har hawayena sun
zama jini, jikina ya zama daurarre a cikin sarkar
begenta. Tufafi sun zama tsumma a jikina domin
rashin wanka da wanki. Ba na zargin kowa a kan
halin da na shiga face ke. Hakuri ya wuyata a
gare ni face na yi tozali da abar begena."
Sai ya ci gaba da rubutun wasikar:
Ciwon zuciyata ya kusa warkewa domin tana gab
da saduwa da wadda take kauna, wadda in ba ita
ba, sai Allah ne kawai zai iya warkar da ita.

Tsakanin ni da ke na san babu yaudara a cikin
soyayyarmu, idan kuwa akwai Allah ya cire ta
daga zukatanmu. Babu amintacce abin amincewa
kamar masoyi mai tsare asirin masoyinsa da
gaskiya.
Sai kuma ya rubuta wadannan layukan a
matsayin kammalawa:
Daga mutumin da soyayya da kauna suka rikita,
daga masoyin da soyayya ta yi wa dabaibayi ta
daure shi a cikin kurkuku. Daga Kamaruzzaman
dan Sarki Shahruzzaman, zuwa ga shugabar
kyawawa ta duniya, daya daga cikin Hurul Aini,
gimbiya Badura 'yar Sarki Gayur. Ki sani cewa
tun lokacin da na farka da dare na gan ki kwance
kusa gare ni, da gari ya waye na neme ki na
rasa, tun lokacin na rasa kaina. Na kasance cikin
ciwo mai hauhawa, na kasance mai zubar da
hawaye babu kakkautawa, na kasance marashin
barci dare da rana, na kasance bawan soyayya
wanda idonsa ba ya rabo da zubar da hawaye.
Na kasance mai kunar zuciya a kodayaushe.
Daga kasan takardar ya rubuta wannan baiti:

"Amincin Allah ya tabbata a gare ta, ita ce
wadda ta mallake zuciyata don kyawunta."
Da kuma wannan baiti:

"Ga zobenta nan da na musaya da nawa, ina
fatar haduwarmu za ta maido mini da zobe
nawa."
Kamaruzzaman ya cire zoben Badura ya nannade
shi tare da takarda, ya like bakin takardar. Ya
mika wa bawa ya ce ya shiga ya kai mata
wannan takarda. Bawa ya riki takarda ya shiga
wurin Badura.
****** ****** ******
Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar
labarun DARE DUBU DA DAYA, wanda littafin nanan akasuwa yanzu haka....

whatsapp only pls
08032767547(17) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI
SHAHRUZZAMAN

Kamaruzzaman ya cire zoben Badura ya nannade
shi tare da takarda, ya like bakin takardar. Ya
mika wa bawa ya ce ya shiga ya kai mata
wannan takarda. Bawa ya riki takarda ya shiga
wurin Badura.
Lokacin da Badura ta karbi takarda ta bude, sai
ta ga zobenta a ciki, nan take ta fara dawowa
cikin hayyacinta. Ta karanta takarda gaba daya,
ta fahimci sakon da ke cikinta gaba daya. Ta
fahimci cewa masoyinta ne, abin begenta, farin
cikin rayuwarta, abin tunaninta, shi ne yake waje
a kofar dakinta wanda labule ne kawai ya raba
su. Sai ta ga abin kamar mafarki ne take yi, ta
waka wadannan baitoci biyu:

"Hakika na yi nadama na yi takaici,
Don rabuwarmu da kai ya masoyi.
Hawaye ya yi kwarara babu iyaka,
Kullum fatana na gane ka masoyi.
Tana gama wannan waka sai ta ji wani irin karfi
ya shige ta. Ta riki sarkar da ta yi mata zobe ga
wuya, ta takura iyakar karfinta, ta bude zoben, ta
cire sarkar daga wuyanta ta watsar. Ta kuma
tsinka ta kafafunta, kamar mai tsinka rubabbiyar
igiya, ta zubar a kasa. Ta hankade labulen kofar
daki, ta yi ido hudu da Kamaruzzaman. Nan take
ta fada ga jikinsa, suka rungume juna suna
hawayen farin ciki. Bakunansu suka hade suna
tsotsar yawun juna, tamkar bakunan uwar
tattabar da 'yarta yayin da take ba ta abinci.
Bayan sun dade a cikin wannan hali, sai suka
saki juna kowa na kallon dan uwansa. Badura ta
ce, "Ya masoyina, shin idona biyu ko kuwa
mafarki nake yi? Allah mai jin tausayin bayinsa
ya kara hada mu bayan rabuwarmu? Tsarki ya
tabbata ga Allah da ya sake hada mu tare."

Yayin da bawa ya ga wannan abu, sai ya
dimauta, ya zura a guje bai garje ko'ina ba sai a
gaban Sarki Gayur. Ya fadi ya yi gaisuwa,
sa'annan ya ce, "Allah ya taimake ka, Wallah ban
taba ganin cikakken mai magani ba kamar
wannan saurayi. Wannan ai shi ne shugaban
dukkan ma su ba da magani na duniya, domin
kuwa ya warkar da 'yarka ba tare da ya shiga
inda take ba, daga bakin kofa ya bayar da
maganin aka kai mata, nan take ta koma cikin
hankalinta."
Nan take Sarki ya mike tsaye, kamar wanda aka
soka da allura, ya dubi bawa ya ce, "Ka tabbata
ba karya kake fada mini ba?" Bawa ya ce, "Wa ni
nan in yi maka karya, Allah ya ba ka nasara?
Idan ba ta warke ba, ta yaya za ta sami karfin da
za ta iya tsinke sarkar da aka daure ta da ita har
ta fito da gudu ta rungume saurayin tana
sumbatarsa? Allah ya ba ka nasara, kamata ya yi
ka tafi da kanka, ka ganar ma idonka, don an ce
gani ya kori ji."
Sarki ya zabura ya nufi gidan da 'yarsa take, bai
ko kula da ya hau doki ba. Yayin da ya isa gidan,
gimbiya Badura ta gan shi, sai ta rufe fuskarta
don kunya, ta waka wadannan baitoci:
"Banin son waninsa idan ba shi ba,
Don me zan ambaci waninsa bayan ga shi?
Kada a aurar da ni ga waninsa face shi,
Ni tasa ce shi kuma nawa ne babu kyashi."

Yayin da Sarki ya ji wakarta, ya tabbatar da ta
sami lafiya, sai ya ji kamar ya tashi sama don
murna, ya sumbaci goshinta saboda tsananin son
da yake yi mata. Ya juya wurin Kamaruzzaman
ya tambaye shi labarinsa, da kuma inda ya fito.
Kamaruzzaman ya fada masa sunansa da sunan
mahaifinsa da kuma kasar da ya fito. Ya kwashe
labarin abin da ya faru tsakaninsa da gimbiya
Badura a daren da suka ga juna, da yadda ya cire
zobenta, duka ya fada wa Sarki Gayur. Sarki ya
yi mamaki, matukar mamaki. Ya ce, "Babu
shakka wannan labari naku bako ne, akwai
abubuwan mamaki a cikinsa. Ya kamata a rubuta
shi cikin littafi a ajiye domin 'yan baya su
karanta sa'annan su karu da darussan dake ciki."
Bayan sun koma fada, Sarki ya kira alkalai ya sa
suka rubuta takardar shaidar auren Badura da
Kamaruzzaman, aka saka ranar daurin aure. Sarki
ya yi umurni da a kawata birni kafin zuwan ranar
daurin aure. Aka kawata birni da kayayyaki na
kawa, masu kyau da daraja. Da ranar daurin aure
ta zo, mutane suka taru daga kowane yanki na
kasar Sin, suka shaidi auren gimbiya Badura da
Kamaruzzaman. Aka yi shagalin da ba a taba yi
ba a duk tsawon tarihin kasar Sin.
Kamaruzzaman ya tare da amaryarsa a daren
farko, suka debe kishirwar begen juna. Kashe
gari Sarki ya shirya kasaitacciyar walima, ya
gayyaci jama'ar jazirorin Jawariyya, da na
jazirorin Basaraniyya. Aka gabatar da abin
nishadi na daga kade-kade da bushe-bushe. Aka
jera kabukkan abin ci, da kasaken abin sha. Aka
tabbata kan haka tsawon wata guda, sa'annan
kowa ya kama gabansa.

Kamaruzzaman na zaune da matarsa cikin farin
ciki da kwanciyar hankali, sai rannan da dare ya
yi mafarki da mahaifinsa, Sarki Shahruzzaman. A
cikin mafarkin ya ji mahaifinsa na cewa, "Don me
za ka guje mini, ya dana? Wane laifi na yi maka
wanda na cancanci irin wannan hukunci daga
gare ka?" Sai ya ji yana waka wadannan baitoci:

"Hakika watan duhu ya gan ni abin tsoro,
Na bude kuben idona ga duban taurarinsa.
Ya zuciya jinkirta mini ko zai juyo gare ni,
Ku ji kaina ga abin da aka jarrabe ni a kansa."
Daga karshen wakar sai ya ji mahaifin nasa ya
ce, "Ya dana, haka da ka yi mini ka kyauta ke
nan?" Nan take Kamaruzzaman ya farka daga
barci, zuciyarsa ta koma gida wurin mahaifinsa.
Da gari ya waye, sai Badura ta lura da cewa
yanayin mijinta ya canja ba kamar yadda ta saba
ganinsa ba. Ta tambaye shi dalili, ya fada mata
mafarkin da ya yi.
............
Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar
labarun DARE DUBU DA DAYA, wanda littafin nanan a kasuwa' kuna iya saye don morewa karanta DADa dan labarai irin wannan...

YUSUF A JIBAGA' KETARE DAKU(19) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI
SHAHRUZZAMAN

Bayan Kamaruzzaman ya huta sosai sai ya tashi
ya nufi kofar shiga wannan birni, wanda bai san
kowane birni ne ba. Ya shiga cikin birni yana
tunanin inda zai nufa. Amma ga mamakinsa, sai
bai ga mutum ko daya ba a cikin wannan birni,
ya ci gaba da tafiya har ya kusa isa daya kofar
birni wadda ake shigowa daga bangaren teku.

Birnin ya kasance yana kan gabar teku ne, don
haka yana da kofofi guda biyu, daya wadda ake
shigowa daga bangaren da babu teku, ita ce
wadda Kamaruzzaman ya shigo ta cikinta, daya
kofar kuma ana shigarta ne daga bangaren teku.
Yayin da Kamaruzzaman ya nufo wajen bangaren
teku na birnin, sai ya iso wani makeken fili inda
mutanen birnin suke yin lambuna. Ya zo ga kofar
wani lambu da aka zagaye da katanga, mai
lambun na ganinsa sai ya yi sauri ya fito, ya yi
wa Kamaruzzaman sallama, ya amsa masa
sallamarsa. Da mai lambu ya ji Kamaruzzaman
ya amsa masa sallama, sai ya ce, "Tsarki ya
tabbata ga Allah madaukakin Sarki. Yi sauri ka
shigo daga ciki kafin wani mutumin wannan birni
ya gan ka." Ya riki hannun Kamaruzzaman ya ja
shi zuwa cikin lambu.

Kamaruzzaman bai yi gardama ba, ya bi mai
lambu suka shiga daga ciki yana mamaki. Da
suka shiga cikin lambu sai Kamaruzzaman ya
tambayi wannan mai lambu, wanda ya kasance
tsoho ne, shekaru sun yawaita a kansa, ya ce da
shi, "Baba, wane birni ne wannan? Kuma don me
kake tsoron wani daga cikin mutanen wannan
birni ya gan ni?"

Mai lambu ya ce, "Ka sani ya kai dana, mutanen
wannan birni matsafa ne. Yaya aka yi ma har ka
zo wannan birni?" Kamaruzzaman ya kwashe
dukkan labarinsa ya fada wa tsoho mai lambu.
Mai lambu ya cika da mamaki, matukar mamaki,
ya dubi Kamaruzzaman ya ce, "Ikon Allah! Lalle
wannan al'amari naka abin mamaki ne. Ka sani
cewa daga wannan birni zuwa birnin musulmin
dake kusa gare mu, tafiyar wata hudu ce a cikin
teku, idan kuma ta kasa ne, to, tafiyar shekara
daya ce cur. Duk shekara akwai jirgin ruwa da
yake kawo kayan masarufi daga tsibiran birnin
Labunus, wanda yake shi ne birnin musulmi mafi
kusa da wannan birni. Idan ya kawo kayan
masarufin yakan debi kayan lambu ya koma da
su, ya ajiye wasu a birnin Labunus ya wuce da
wasu a birni Kalidan, birnin mahaifinka. Daga nan
kuma wannan jirgi ba zai sake dawowa ba sai
wata shekara. Ka kuwa yi sa'a, yau saura wata
uku wannan jirgi ya zo."

Kamaruzzaman ya yi shiru yana jujjuya maganar
mai lambu a cikin ransa, ya ga dai babu abin da
ya fi face ya jira zuwan wannan jirgi nan da
watanni uku. Ya juya wurin mai lambu ya ce
masa, "Ko za ka yarda na zauna nan wurinka, in
rika taimakonka ga aikace-aikacen lambunka?"
"Me zai hana?" In ji mai lambu, "Ko banza na
tsufa ga shi ba ni da wani mai taimako."
Mai lambu ya kawo wata 'yar guntuwar riga, iya
gwiwa mai launin shudi, ya ba Kamaruzzaman ya
saka, ya cire tufafinsa masu kyau ya ajiye. Ya
koya masa yadda ake ban ruwa, da yadda ake
budi, da kuma noma. Kamaruzzaman ya ci gaba
da taimakon mai lambu kullum. Idan yana cikin
aiki ya tuna da mahaifinsa ko Badura, sai ya yi ta
zubar da hawaye yana wake-wake. Al'amarinsa
ke nan.

Amma Badura kuwa, yayin da ta farka daga
barci, ta duba kusa gare ta, ba ta ga
Kamaruzzaman ba, sai kuma ta lura da an
warware mata kubakar wando, ta nemi dan
dutsen da ta nannade a kubakar wandon ta rasa.
Ta ce a cikin ranta, "Babu Sarki sai Allah." Ta
tabbatar da cewa hakika wani bakon al'amari ya
faru gare shi na daga asirin dake jikin wannan
dan dutse. Domin kuwa Kamaruzzaman ba zai
bar ta ba, tsawon wannan lokaci, ba tare da ya
dawo ba. Ta so ta fada wa bayi da kuyangi batan
Kamaruzzaman sai ta ji tsoron kada su ji tsoro
su ce za su koma da baya, ko kuma su yi mata
tawaye. Saboda haka sai ta bude kyankyandin da
Kamaruzzaman yake ajiye tufafinsa, ta dauko
babbar riga da wando da rawani. Ta saka kayan,
ta nada rawani, ta yi amawali, kamar dai yadda
Kamaruzzaman yake yi. Ta fita daga cikin tanti,
ta kirawo wata amintacciyar kuyanga tata, ta
fada mata kome, da kuma nufinta na son su isa
birnin Kalidan, Kasar mahaifin Kamaruzzaman, ba
tare da sauran bayi da kuyangi sun gane
Kamaruzzaman ba ya tare da su ba.
Ta yi wa kuyanga shiri da tufafinta, kamar ita ce
gimbiya Badura. Ta fito cikin bayi, babu wanda
ya gane ta, da ma kamarsu daya da
Kamaruzzaman, a fuska da kuma jiki. Ta bayar
da umurni a aza wa dabbobi kaya a ci gaba da
tafiya. Nan take bayi suka cire tantina, aka dora
wa dabbobi kaya, aka kawo mata dokin
Kamaruzzaman ta taka ta hau, aka jawo wa
kuyangarta dokin Badura, ita ma ta hau, ayari ya
motsa, suka ci gaba da tafiya.
Suka ya ta tafiya kwana da kwanaki ba tare da
sun tsaya ba har suka fara hango gine-ginen
wani birni can nesa da su. Da suka zo gab da
birnin, sai Badura ta ba da umurni a sauka a huta
a bakin kofar wannan birni, ta tura wani bawa da
ya shiga cikin birni ya samo musu labarin sarkin
birnin da yanayin jama'arsa. Aka sauke wa
dabbobi kaya, aka kafa tantina, kafin dan aike ya
dawo.
Bayan wani dan lokaci sai ga bawan nan ya
dawo, ya ce wa Badura, "Allah ya ba ka nasara,
sunan wannan birni Labunus, jama'arsa kuwa
duka musulmi ne. Sunan Sarkinsu Armanus, yana
da wata kyakkyawar 'yarsa da yake tsananin
kauna, sunanta Hayatunnufusi."
............
Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar
labarun DARE DUBU DA DAYA, wanda littafin nanan a kasuwa' kuna iya sayen sabon fassaran dare dubu da daya'....

Whatsapp only pls
08032767547(20) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI
SHAHRUZZAMAN

Dan aike ya dawo ya ce wa Badura, "Sunan
wannan birni Labunus, jama'arsa kuwa duka
musulmi ne. Sunan Sarkinsu Armanus, yana da
wata kyakkyawar 'yarsa da yake tsananin kauna,
sunanta Hayatunnufusi." Badura ta sallami bawa,
ta fada wa sauran bayi da kuyangi cewa, za su
huta a wannan wuri na kwana biyu kafin su shiga
cikin birni su ga Sarki.
To, ashe kuma lokacin da tawagar Badura suka
sauke kayansu labari ya kai ga kunnen Sarki, sai
shi kuma nan da nan ya tashi dan rahoto domin
ya samo masa labarin mutanen da suka sauka a
bayan garinsa. Dan rahoto ya koma ya shaida wa
Sarki cewa, tawagar wani dan Sarki ce wai shi
Kamaruzzaman dan Sarki Shaharuzzaman na
birnin Kalidan, hanya ta biyo da su ta nan suka
ya da zango. Da jin haka, sai Sarki Armanus ya
hawo tare da wasu fadawansa ya nufi bayan gari
domin ganin wannan bakon dan Sarki.
Yayin da Sarki da fadawansa suka iso wurin da
tantinan nan suke, sai Badura ta fito daga cikin
tantinta, tana cikin shigar Kamaruzzaman, ta zo
gaban Sarki ta fadi ta yi gaisuwa, Sarki ya amsa
mata, sa'annan ya ce bai kamata su zauna a
wannan wuri ba, su kwashe kayansu su shiga
cikin gari. Suka bi umurnin Sarki, suka cire
tantina, suka labta wa dabbobi kaya, suka
rankaya cikin birni. Aka saukar da bayi da
kuyangi a gidan baki, ita kuwa Badura Sarki ya
saukar da ita a wani bangare na gidansa.
Bayan kwana uku sai rannan Sarki Armanus ya
shiga bangaren da aka saukar da Badura, ya
kuwa same ta ba ta dade da fitowa daga wanka
ba, fuskar nan tata tana sheki kamar farin wata,
amma tana cikin tufafi na maza ne, wadanda aka
yi wa kwalliya da zinariya da lu'ulu'u. Bayan Sarki
ya zauna sai ya ce, "Ya dana, na zo neman wata
alfarma ne a gare ka." Badura ta ce, "Wace
alfarma kake nema a gare ni, Allah ya ba ka
nasara?"
Sarki ya ce, "Ka sani cewa shekaru sun yawaita
a kaina, na fara tsufa har sha'anin mulki na
neman ya gagare ni, ga shi ba ni da magaji
namiji. Amma ina da 'ya daya, wacce kusan
kamarku daya a wajen kyau. Idan ka yarda, ina
so in aura maka ita, ni kuma in yi murabus in
nada ka a matsayina."
Yayin da Badura ta ji zancen Sarki Armanus, sai
ta sunkuyar da kanta kasa, nan take zufa ta
tsattsafo daga goshinta, kunya kuma ta rufe ta.
Ta ce a cikin zuciyarta, "Kaka-tsara-kaka, yau fa
ana dara ga dare ya yi. Yanzu idan na fada masa
gaskiya cewa ni mace ce ya ya zai ji? Kuma a
wane matsayi zai dauke ni? Kuma ni ba abin na
gudu ba cikin dare, na san zai sa a kamo ni,
watakila idan ya yi fushi da ni ya sa a kashe ni.
Babu abin da ya fi face in amince da bukatarsa,
daga baya na san dabarar da zan yi." Sai ta daga
kanta, ta ce da Sarki, "Allah ya ba ka nasara, na
ji, na amince."
Sarki ya cika da farin ciki, ya tashi ya fita wurin
jama'arsa ya fada musu abin da ake ciki, ya
kuma ce musu a je a fara kawata birnin Labunus
da kewayensa, a shiga shirye-shiryen kasaitaccen
bukin auren 'yarsa da bakon dan Sarki.

Washe gari Sarki ya kira dukkanin hakimansa, da
Waziransa, da alkalai da limamai da fadawansa
da jama'ar gari. Ya sauka daga karagar mulkinsa
ya dora Badura a matsayin sabon Sarkin
Labunus, ya umurci dukkanin mahalarta da su yi
mata mubayi'a. Daga nan dukkanin jama'a suka
rika zuwa daya bayan daya suna yi wa Badura
Mubayi'a, babu daya daga cikinsu da ya gane
cewa mace ce, dukkansu sun dauka cewa dan
Sarki ne, suna masu tsananin mamakin baiwar da
Allah ya yi masa ta kyau da kwarjini da farin jini.

Bayan jama'a sun gama yi wa Badura mubayi'a,
bisa al'adar kasar Labunus, aka buga ganguna
domin tabbatar da nadin sabon Sarki. Daga nan
kuma sai tsohon Sarki Armanus ya shiga shirye-
shiryen auren 'yarsa Hayatunnufusi da sabon
Sarki. Da ranar daurin aure ta zo, mutane suka
hadu daga kowane bangare na tsibiran kasar
Labunus. Ango da amarya suka zauna wuri guda,
fuskokinsu na haske, kai ka ce watanni biyu ne
suka jera. Aka yi dukkan abubuwan da za a yi na
al'ada, aka rubuta takardar auren Kamaruzzaman
da Hayatunnufusi, daga nan kuma sai aka goce
da shagali. Aka yi kwana bakwai ana buki
sa'annan kowa ya kama gabansa.

A daren da amarya za ta tare, mata suka je suka
gyara mata dakinta, aka shimfida shimfidu masu
daraja, aka saka labulayye a kowane bango na
dakin. Ango ya fara shiga ya zauna yana jiran
isowar amarya, zuwa wani dan lokaci, sai ga
tsofaffi sun rako amarya zuwa dakinta. Da suka
iso da ita a bakin kofar dakin, sai suka tura ta
ciki, su kuma suka koma abinsu. Yayin da Badura
ta ga tsofaffi masu kawo amarya sun tafi, an bar
su su biyu kadai a cikin daki, sai ta tuna da
mijinta Kamaruzzaman, hawaye suka zubo daga
idanunta. Ta yi tagumi tana tunani.
Yayin da ta gama tunaninta sai ta riki hannun
Hayatunnufusi, ta zaunar da ita bisa shimfida, ta
sumbaci goshinta. Ta tashi ta dauki buta, ta
shiga bandakin da ke cikin dakin, ta yi alwala. Ta
dawo cikin dakin ta kabbarta salla. Duk lokacin
da ta yi raka'a biyu sai ta sallame, ta tashi ta
kabbarta wata. Ba ta daina salla ba, sai da ta
lura cewa barci ya dauke Hayatunnufusi,
sa'annan ta sallame, ta yi addu'o'in da za ta yi,
ta je ta kwanta kusa ga Hayatunnufusi.

Da gari ya waye Badura ta riga Hayatunnufusi
tashi daga barci, ta shirya ta nufi fada. Tsohon
Sarki da matarsa, mahaifiyar Hayatunnufusi,
kuwa suka shiga wurin 'yarsu. Bayan sun shiga
cikin dakin, sai mahaifiyar Hayatunnufusi ta dubi
shimfidar da 'yarta ta kwana tare da angonta,
amma ba ta ga abin da take son gani ba. Sarki
ya tambayi 'yarsa yadda suka kwana.
Hayatunnufusi ta kwashe labari ta fada musu har
da wakar da ta ji angon nata ya rera. Mahaifanta
suka fahimci dai babu wani abu da ya shiga
tsakaninsu a wannan dare na sha'anin miji da
mata.

A fada kuwa Bdura ta harde bisa karagar mulki,
fadawa sai faduwa suke yi a gabanta suna
kwasar gaisuwa. Ta nada ta tube, ta yi hukunci,
ta sallami 'yan jarun da suka cancanci sallama,
ta daure masu laifi da suka cancanci daurewa.
Ta ba askarawa umurni, ta rarraba taimakon kudi
ga mabukata, ta yi kyautar tufafi ga hakimai da
fadawanta. Jama'a suka yi san barka ga wannan
sabon Sarki nasu mai adalci da yawan alheri,
suka rika yi wa sabon Sarki addu'ar dorewa a
kan karagar mulki, babu daya daga cikinsu da ya
gane mace ce. Haka Badura ta ci gaba da jan
ragamar mulki har dare ya yi, aka tashi daga
zaman fada. Ta shiga gida wurin Hayatunnufusi.
Ta same ta zaune a kan shimfida ta shirya mata
abinci kala-kala. Ta zauna suka ci abinci tare,
suka sha abin sha, da lokacin barci ya yi,
Hayatunnufusi ta saka tufafinta na barci ta
zauna bisa shimfida tana jiran angonta. Badura
ta je ta zauna kusa gare ta, ta sumbaci goshinta,
ta tashi ta shiga bandaki ta yi alwala, ta fito ta
fara salla. Ba ta daina yin salla ba sai da ta ga
barci ya yi awon gaba da Hayatunnufusi,
sa'annan ta sallame salla, ta yi addu'o'in da za
ta yi, ta je ta kwanta kusa gare ta. Da gari ya
waye, ta tashi ta yi salla ta kimtsa ta nufi fada,
ta bar Hayatunnufusi tana barci. Ta je ta kame
bisa karagar mulki, ta yi umurni ta yi hani,
tsawon wannan rana.
Bayan Badura ta fita zuwa fada sai Sarki
Armanus da matarsa suka shiga wurin 'yarsu
domin su ji yadda ta kwana da angonta.

Hayatunnufusi ta kwashe labari ta fada musu
tare da wakar da ta ji Badura ta rera, ta kara da
cewa, "Ya mahaifina, wallahi ni dai ban taba gani
miji mai ibada kamar wannan miji nawa ba, babu
abin da yake yi tsawon dare daga kuka da waka
sai salla." Sarki ya ce, "Zancen banza! An fada
masa cewa an kawo masa ke ne domin ya koya
miki kuka da waka? Ko kuwa salla ce ba ki iya
ba da zai koya miki? Ga shi tsufa ya zo mana
muna so mu ga jikokinmu kafin mu mutu amma
ya tsaya shiririta. To, ki fada masa aure kika zo
yi ba koyon kuka da waka ba. Idan muka dawo
gobe, rana ta uku ke nan, ba tare da wani abu na
tsakanin mata da miji ya wakana a tsakaninku
ba, babu makawa zan tube shi daga matsayin da
na dora shi a kai, in kuma sa a yi masa korar
kare daga wannan birni namu." Sarki da matarsa
suka fita fuu, cikin fushi.
............ .

GOBE ZANCI GABA' INSHA ALLAH
(21) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI
SHAHRUZZAMAN
Sarki Armunus da matarsa, mahaifiyar
Hayatunnufusi, suka fita daga wurin gimbiya
Hayatunnufusi cikin fushi. Bayan dare ya yi, an
tashi daga fada, sai Badura ta shiga gida, ta tarar
da Hayatunnufusi ta shirya mata abinci da abin
sha, tana jiran dawowarta. Bayan ta zauna sun ci
sun sha sun koshi, sai ta tuna da mijinta
Kamaruzzaman, ta tuna daren amarcinta da shi,
ta yi ajiyar azuciya, hawaye suka zubo daga
idonta, ta rera wadannan baitocin waka:
"Rabuwarmu ta kasance hukunci ne na Allah,
tamkar rana mai rabuwa da haskenta zuwa ga
kowace jigawa, tana furata ishara tata, ina
fahimtar rubutunta. A kullum begena ya kan
zama mai daduwa, ba shi karewa. Ni na ki hakuri,
domin kuwa hakuri abin ki ne yayin bege. Zuciya
ta kuntata, ta raunana. Amma an ce duhu yakan
yaye idan asuba ta zo."
Tana gama waka sai ta sumbaci Hayatunnufusi a
kan goshinta, ta mike za ta shiga bandaki domin
ta yi alwala sai Hayatunnufusi ta rike mata riga,
ta ce, "Haba angona, shin kai ba ka jin kunyar
zalunta ta, bayan dimbin alherin da mahaifina ya
yi maka?" Yayin da Badura ta ji haka, sai ta koma
ta zauna, ta ce, "Ya amaryata, me ya yi zafi kike
fadin wannan magana?" Hayatunnufusi ta ce, "Ni
ban taba ganin mutum mai son kai kamarka ba.
Ta yaya za a kawo ni gare ka a matsayin
amarya, amma tsawon kwana biyu ba ka kusance
ni ba? Ko sona ne ba ka yi? To, ni dai ina yi maka
hannunka-mai-sanda, domin kuwa kullum sai
mahaifina tare da mahaifiyata sun tambaye ni
yadda muka kwana, ni kuwa ina fada musu
gaskiya. Mahaifina ya yi matukar fushi da kai da
ya ji cewa ba ka kusance ni ba tsawon kwana
biyu, ya kuma yi alkawri idan ya dawo gobe ya ji
cewa ba ka kusance ni ba, to, zai tube ka daga
sarauta, ya sa a kore ka daga kasarsa. Amma ni
na san mahaifina a kan zafin zuciya, watakila ma
ya sa a kashe ka. Ka ji abin da ake ciki, ya
masoyina, yanzu dabara ta rage ga mai shiga
rijiya."
Yayin da Badura ta ji zancen Hayatunnufusi sai
ta sunkuyar da kanta kasa, kunya ta kamata. Ta
ce a cikin ranta, "Ta faru ta kare, an yi wa mai
dami daya sata. Yau fa ake yin ta, ga bukin zuwa
amma

1 Comments On HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHRUZZAMAN
avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Wanne darasi kuka ?aru da shi daga cikin wannan hikayar,

Please Login or Register in order to submit comment