Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

allura bisa ga gefen ido, to, da ya
zama abin lura ga masu hankali." Daga nan ya
tsuguna ya kwance wa Sarki bakin jaka, bai rage
masa kome ba. Sarki ya yi mamaki, gayar
mamaki, ya ce babu shakka samun adalin mutum
mai gaskiya da rikon alkawari kamar Amajadu sai
an tona. Ya neme shi da ya zama daya daga
cikin waziransa. Amjadu ya amince da bukatar
Sarki, aka nada shi Waziri. Sarki ya ba shi gida
da bayi da kuyangi da dawaki da tufafi kala-kala,
na alfarma. Aka yanka masa albashi.

Shi kuwa Bahadaru Sarkin Fada, Sarki ya nemi gafararsa
bisa tozarta shi da ya yi, aka yi masa kyauta mai
yawa, aka kara masa matsayi. Waziri Amjadu ya
kasance yana mulki da adalci a tsakanin
talakawa, ya kasance mai yawan kyauta da
kyautatawa. Kullum sai ya sa mai shela ya shiga
cikin gari yana cigiyar dan uwansa Asadu, amma
a banza. Ko wanda ya taba ganin sa ba a samu
ba.
Amma Asadu kuwa, yana can tsare a dakin
karkashin kasa, a hannun matsafa, kullum ana
gana masa azaba dare da rana har tsawon
shekara guda. Yayin da lokacin zuwa dutsen
wuta, wurin ibadar matsafan nan ya zo.
Sai
tsohon nan da ya kamo Asadu, wanda yake
sunansa Baharamu, kuma shi ne shugaban
matsafan nan gaba daya, ya sa aka shirya jirgin
ruwa da dukan kayan da za su bukata yayin
wannan tafiya.
Da suka gama shiri tsaf, sai aka fito da Asadu
aka saka shi cikin wani katon akwati aka rufe,
aka kinkimi akwatin aka nufi bakin teku domin
saka shi cikin jirgi. To, ashe lokacin da matsafan
nan ke ta kici-kicin sa kayansu cikin jirgin ruwa,
Waziri Amjadu na tsaye a bakin tagar dakinsa
wanda yake saman bene, yana kallon ruwan
teku. Lokacin da ya ga matsafan nan na ta shirin
tafiya, sai ya ji gabansa ya fadi, bai san dalili ba.
Nan take ya yi umurni a daura masa sirdi. Ya hau
tare da wasu askarawa ya nufi bakin teku. Da
suka isa inda jirgin matsafan nan yake, ya sa
askarawa su binciki jirgin nan. Suka shiga cikinsa
suka bincika ko'ina amma ba su ga wani abu da
ya dauki hankalinsu ba, suka dawo suka fada wa
Amjadu.

Waziri Amjadu ya juya da jama'arsa suka koma
gida, yana cike da tunanin dan uwansa. Yayin da
ya shiga dakinsa sai idonsa ya kai ga wani
rubutu da aka yi bisa bangon dakin, ya ga an
rubuta:
Idan masoyanmu sun yi jijjibi don ganinmu, cewa
zukatansu ba su fasa tunaninmu. Sun maishe ni
daddauda, sun hane ni jin dadin ci da na barci.
Da ya gama karanta rubutun, sai hawaye ya
karyo daga idanunsa, ya yi kuka, kuka mai yawa.
Su kuwa matsafa da suka gama shiri, sai suka
fada cikin jirgi. Baharamu ya yi wa masu tuki
tsawa da su yi gaggawa, suka tsunduma cikin
teku suka nufi tsibirin Dutsen Wuta. Bayan sun yi
nisa cikin teku, Baharamu ya sa aka fitar da
Asadu daga cikin akwati, ya kawo 'yar gurasa da
ruwa ya ba shi. Suka ci gaba da tafiya kwana da
kwanaki har suka fara hangen tsibirin Dutsen
Wuta. Yayin nan guguwar teku ta taso, rakuman
ruwa suka motsa, teku ya haukace ta rika juya
jirginsu yadda yake so, suka debe tsammani
daga rayuwa. Iska ta dauki jirgin ta jefa shi wani
teku na daban, wanda ba su sani ba, tafarki ya
saba musu.
Bayan teku ya lafa, da suka duba gabansu, sai
suka hangi wani birni a gabar teku, wanda yake
da wata babbar hasumiya, madaukakiya, a
tsakiyarsa. Wannan hasumiya tana da tagogi
wadanda suke kallon teku, duk jirgin da zai shigo
wannan birni, za a hange shi ta cikin wannan
hasumiya tun daga nesa. Ashe wannan birni na
wata Saruniya ce, wai ita Murjanatu. Wannan
sarauniya kuwa ta kasance musulma, mai
tsananin kishin addinin musulunci.

Da suka hangi wanna birni, sai madugun jirgi ya
ce, "ya shugabana, Baharamu, ka sani cewa mun
bace daga tafarkinmu, mun shigo birnin
Sarauniya Murjanatu, musulma. Idan kuwa ta
gane cewa mu matsafa ne, babu makawa yanka
mu za ta yi, babu daya da zai tsira daga
hannunta. Ga shi kuma dole mu sauka a birninta
mu huta, sa'annan mu sake fita zuwa ga
bukatarmu."
Baharamu ya ce, "sai mu canza tufafinmu, mu yi
shiga irin ta musulmi. Shi kuma wannan (ya nuna
Asadu) sai mu sa masa kayan bayi. Idan aka
tambaye mu sai mu ce, mu dillalai ne na bayi,
bakake da farare Duk mun sayar da na
hannunmu, saura wannan farin bawan kawai,
amma ba za mu sayar da shi ba, za mu rike shi a
hannunmu saboda ya iya karatu da rubutu."
Madugun jirgi ya ce, wannan dabara taka ta yi.
Suka shirya bisa ga haka, suka canza tufafinsu
suka yi shigar musulmi, suka sanya wa Asadu
kayan bayi. Da isar su bakin gaba sai suka tarar
da Sarauniya Murjanatu da askarawanta suna
jiran isowar su, ashe har labarin zuwansu ya isa
gare ta. Suka sauka daga cikin jirgi suka fadi
suka yi gaisuwa. Ta tambaye su daga ina? Kuma
wace haja suka kawo birninta?
Madugun jirgi ya duka ya ce, "Allah ya ba ki
nasara, mu dillalan bayi ne, muna tafe tare da
shugabanmu." Ta tambaya, wane ne shugaban
nasu? Baharamu ya matso kusa gare ta, yana
rike da Asadu a cikin kayan bayi, ya fadi ya
gaishe ta. Ta tambaye shi sana'arsa, ya ce mata
shi mai cinikin bayi ne. Ta dubi Asadu, ta gan shi
cikin shigar bayi, ta tambaye shi, "menene
sunanka?"

"Sunana na asali ko kuwa na yanzu?"
"Suna biyu gare ka?"
Asadu ya amsa mata cikin muryar kuka, "I,
sunana na asali Asadu, mai farin ciki. Amma
yanzu na koma Mutarrul Maisaramus"
Yanayinsa da kalamansa suka sosa mata zuciya,
ta kara tambayarsa, "ka iya rubutu?"
Ya amsa, "I."
Ta kawo tawwada a cikin kaho, da alkalamin
gashin tsuntsu da takarda. Ta ce, "rubuta mini
wani abu da zan iya karantawa." Ya karba ya
rubuta wadannan baitoci:
Yaya bawa zai yi da ransa, idan kaddara ta auka
masa?
Ya Shugaban adilai, ina mafita ga wanda ka
daure ka jefa shi cikin kogi.
Ka gargade shi da kada ya kuskura ruwa ya jika
jikinsa?

Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ SHINE MAI KAWO MUKU WANNAN LABARI35 HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHARUZZAMA

Yayin da Murjanatu ta karanta abin da ya rubuta
sai tausayinsa ya kama ta. Ta juya wurin
Baharamu ta ce, "ina so in sayi wannan bawa.
Nawa ne kudinsa?"

Baharamu ya dukar da kai ya ce, "ya Sarauniya,
mai karfin mulki, wannan bawa ba na sayarwa ba
ne. Na sayar da duka 'yan uwansa, shi kadai ya
rage mini. Na yi niyyar in rike shi ga hannuna."
Sarauniya Murjanatu ta ce, "ga shi kuwa ya
kwanta mini a rai. Lallai ka sayar mini da shi, ko
kuma ka ba ni shi kyauta." Ya ce da ita, "Allah
ya ba ki nasara ki yi hakuri, ba zan iya rabuwa
da shi ba."
Sarauniya ta harzuka, ta daka masa tsawa, "to, je
ka, an karbe shi da karfi daga hannunka. Kuma
ku gaggauta bar mini birni kafin gari ya waye,
idan ba haka ba zan sa a washe ku, kuma a
kakkarya jirginku." Ta juya ta tafi da Asadu Gidanta.

Sarkin tsafi Baharamu ya juya wurin 'yan uwansa
yana cewa, babu makawa mu koma gida mu sake
shiri. Sa'annan ya umurci mutanensa su cika
salkunansu da ruwa, su dan huta zuwa dare su
juya da baya zuwa gida.
Sarauniya Murjanatu kuwa, da ta iso da Asadu
gidanta, sai ta kai shi wani daki wanda tagoginsa
suke kallon teku, ta umurci kuyangi su kawo
abinci da abin sha. Kuyangi suka shiga girke
musu kayan abinci da na sha kala-kala a
gabansu. Sarauniya ta umurci Asadu ya ci abinci,
suka ci tare har suka koshi. Daga nan sai ta
jawo tulun giya har
suka yi tatil. Allah da ikonsa sai ya jefa son
Asadu a cikin zuciyar Murjanatu, so kuwa mai
tsanani. Ba su daina kwankwadar giya ba har sai
da suka kusa fita daga hayyacinsu. Daga nan sai
Asadu ya mike tsaye ya fita daga dakin da nufin
kama ruwa. Da ya fito daga dakin, sai ya ga
kofar gidan a bude. Ya yi sha'awar ya dan yi
tattaki domin ya mike kafafunsa, sai ya fita daga
cikin gidan ya yi ta tafiya har ya iso ga wani
lambu wanda yake kewaye da katanga, da ya
tura kofar sai ya ji ta a bude. Ya shiga ciki ya
mayar da kofa ya rufe, ya ga lambun nan cike da
'ya'yan itace da furanni masu ban sha'awa. Ya
tsuguna a gindin wata bishiya ya biya bukatarsa,
ya tashi ya nufi wani dan tabki da aka kirkira a
cikin lambun domin ya kama ruwa.
Bayan ya kama ruwa sai ya yi alwala, ya wanke
hannuwansa da fuska. Ya tashi domin ya koma
wurin Sarauniya, sai ya ji wata iska mai dadi ta
buge shi, ya ji duk kasala ta rufe shi, babu abin
da yake so kamar ya zauna wurin nan ya kwashi
iskar nan mai ni'ima. Ya tube rigasa, yadda iskar
za ta ratsa shi sosai, ya kishingida a gindin
tabkin nan, sai barci mai nauyi ya dauke shi. Ya
yi ta sharar barci har dare ya yi sosai bai farka
ba.
Su kuwa matsafan nan da dare ya yi sai
Baharamu ya ce musu su yi maza su shirya
kayansu domin tafiya. Suka ce, "mun ji mun
karba." Suka ce ya ba su lokaci su cika
salkunansu da ruwa tukuna. Suka zari salkunan
fata suka shiga gari neman ruwa, suka yi ta
yawo amma ba su ga rijiya ba wadda za su debi
ruwa. Suna cikin yawo sai suka fado inda lambun
nan yake, suka gan shi zagaye da katanga. Suka
ce a cikin ransu, "babu makawa a sami ruwa
cikin wannan wuri." Sai suka tsallaka katanga
suka shiga ciki. Suka yi ta zagayawa har suka
iso wurin dan tabkin nan da Asadu ke barci a
gefensa.
Da zuwan su wurin sai suka ga mutum kwance,
fuskarsa tana kallon sama, yana ta sharbar barci.

Ko da suka dubi fuskarsa da kyau, sai suka
shaida shi. Suka cika da farin ciki, suka cika
salkunansu da ruwa sa'annan suka ciccibi Asadu
suka bude kofar lambu suka fita da shi, suka nufi
wurin shugabansu Baharamu.
Lokacin da suka zo da Asadu wurin Baharamu,
sai suka ce masa, "buga tamburanka, ka kuma
busa kakaki don murna. Domin kuwa mun dawo
da yaron nan da Sarauniya ta kwace daga
hannunmu." Suka ajiye Asadu a gabansa.
Yayin da Baharamu ya kyalla ido ya ga Asadu,
sai zuciyarsa ta yi fari, ya cika da farin ciki. Ya
yi ta yabon abokan tafiyarsa, bisa wannan kokari
da suka yi. Ya yi umurni a kwance jirgi da sauri a
kama hanya. Suka kwance jirgi, suka saka Asadu
cikin akwatin da aka fitar sa shi, suka tsunduma
cikin teku, suka tasar wa tsibirin Dutsen Wuta.
Wannan shi ne al'amarinsu.
Amma Sarauniya Murjanatu da ta ga har dare ya
yi Asadu bai dawo ba, sai ta tashi ta shiga ko'ina
cikin gidan nan ta duba, amma ba ta gan shi ba.
Daga nan ta fita tare da kuyanginta suna rike da
shama'a, suka shiga cikin gari suna neman shi.
Sai suka iske kofar lambu a bude, nan take
Sarauniya ta raya a ranta cewa yana ciki. Suka
shiga cikin lambun har suka zo wurin dan tabkin
nan, sai suka ga rigar Asadu, yashe a kasa. Suka
bincike ko'ina cikin lambun amma ba su ji
duriyarsa ba.
Haka dai suka yi ta neman Asadu har gari ya
waye ba su gan shi ba. Ta tambayi labarin masu
jirgi, aka ce mata ai tun cikin dare suka bar
garin. Daga nan ta gane babu makawa su ne
suka dauke shi. Ranta ya baci, ta yi fushi, fushi
mai

mai tsanani. Nan da nan ta sa aka shirya
mata jirage goma masu sauri, ta kwashi
askarawa cikin shirin yaki, ta shiga jirgi daya
suka bi bayan jirgin matsafa. Ta yi bushara ga
matuka jirage, ta ce musu idan suka tarar da
jirgin matsafa da sauri za ta yi musu kyauta mai
yawa. Amma idan suka kuskura suka kasa
cimma jirgin matsafan har suka kubuta daga
hannunta, duk za ta kashe su. Da jin haka sai
matuka suka mai da himma ga tuki.
Suka yi ta tafiya cikin teku tsawon kwana uku. A
kwana na hudu sai suka fara hango jirgin
Baharamu da mutanensa. Da ganin haka sai
matuka suka kara kaimi, jiragen suka warwatsu
da nufin zagaye jirgin Baharamu. A wannan
lokaci kuma, Baharamu ya fito da Asadu daga
cikin akwati yana gana masa azaba. Ko da ya
daga kansa sai ya hango jirage suna keta ruwa
daga nesa sun nufo jirginsu. Nan da nan ya gane
cewa Sarauniya ce ta biyo su, ya zagi Asadu, ya
zungure shi ya ce, "Allah ya wadan ka, ka dai
zamar mana kadangaren bakin tulu, kafin
Sarauniya ta kashe mu kai za ka fara mutuwa."
Sai ya ingiza Asadu cikin teku, tsundum. Suka ci
gaba da tafiya suna jiran isowar jiragen
Sarauniya.
Allah da ikonsa, da yake kuma Asadu na da
sauran shan ruwa a gaba, sai ya yi ta ninkaya da
hannuwansa da kuma kafafunsa. Iska kuma ta yi
ta tura shi har ya yi nisa daga jirgin matsafa.

Can zuwa rana faduwa sai iska da rakuman ruwa
suka ture shi bakin gaba. Ya tashi ya tube
tufafinsa ya matse su ya shanya bisa rairayi yana
mai godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya
tsirar da shi. Ya zauna tsirara yana jiran tufafinsa
su bushe, nan take ya yi waka a kan abin da ya
auka masa, ya yi kuka. Da tufafinsa suka bushe,
ya dauka ya saka. Ya yi ta tafiya cikin daji, dare
da rana, yana ci daga 'ya'yan itatuwa yana sha
daga ruwan kogi har wata rana da yamma ya
fara hango gari a gabansa. Ya yi farin ciki, ya
kuma kara sauri domin ya isa cikin garin. Ko da
ya isa bakin garin rana ta fadi an rufe
duka kofofin shiga garin. Kwamfa, ashe wannan
gari shi ne birnin da dan uwansa Amjadu ke
Wazirci, shi ne kuma birnin da aka tsare shi a
dakin karkashin kasa aka gana masa azaba,
watau Birnin Matsafa. Amma shi bai gane
kowane birni ba ne. Da ya ga an rufe kofofin
birnin sai ya rika zagaya ganuwar birnin ko zai
sami wani wurin da zai kwana kafin gari ya
waye. Yana cikin zagayawa sai ya tarar da wani
wuri wanda aka zagaye da katanga, ya nufi kofar
wurin ya gan ta a bude, sai ya shige ciki. Ashe
wurin nan makabarta ce. Ya ga wani kabari a
bude, sai ya shige ciki ya kwanta, ya tada kansa
da hannuwansa, a haka barci ya dauke shi.
Al'amarinsa ke nan.
Amma yayin da jiragen Sarauniya Murjanatu suka
tarar da jirgin matsafan nan, sai suka yi masa
zobe. Baharamu ya ga an zagaye su kamar
yadda farin ido ke zagaye da bakin da ke
tsakiyarsa. Sarauniya ta tambaye su labarin
Asadu. Baharamu ya duka ya yi ta rantse-rantse
wai tun da ta kwace shi daga hannunsu, ba su
koma ganin shi ba. Ta sa a binciki jirgin. Aka
shiga aka yi wa kayansu dai dai, amma ba su ga
Asadu ba. Ta sa aka daure su gaba daya, aka
koma da su birninta. Da, ta yi nufin kashe su, sai
suka ce za su fanshi kan su. Suka bayar da
dukan dukiyar da suka zo da ita, ban da jirginsu,
ba a bar su da ko allura ba, sai tufafin jikinsu.

Suka hau jirgi suka nufi birninsu cike da bakin
cikin abin da ya same su.
Ko da suka iso bakin gabar tekun birninsu, suka
daure jirgi, dare ya riga ya yi har an rufe kofofin
birni. Don haka sai suka yanke shawarar su je
hurumi su kwana gudun kuraye da kyarkeci. Sai
dai abin da ba su sani ba shi ne, daidai lokacin
da suke daure jirginsu a bakin teku, a lokacin ne
kuma Asadu ya shige cikin daya daga kaburburan
wannan makabarta ya yi kwanciyarsa. Suka tasar
wa makabarta, suka tarar da kofa a bude. Bayan
sun shiga ciki sai Baharamu ya ga wani kabari a
bude ya ce a ransa, "babu makawa in ga abin da
ya bude wannan kabari." Ya shiga sai ya tarar da
mutum kwance yana barci, ya yi matashin kai da
hannuwansa. Da ya dube shi da kyau sai ya gane
Asadu ne. Nan take ya yi kururuwa, 'yan uwansa
suka zo. Ya nuna musu Asadu da ke barci, ya
kuma ce musu ai tun da ya yi alkawari sai ya ba
Dutsen Wuta jinin Asadu, to, duk inda ya shiga
sai ya dawo. Nan take suka daure shi, suka rufe
masa fuska. Tun da asuba da aka bude kofofin
gari, kafin haske ya bayyana, suka tafi da shi
gidan Baharamu, babu wanda ya gan su. Aka
daure Asadu cikin sarka aka mayar da shi
kurkukun nan na karkashin kasa.
Baharamu ya damka shi ga hannun wata 'yarsa,
wai ita Bustana, domin ta kula da shi. Ya umurce
ta ta rika yi masa azaba dare da rana har zuwa wata shekara da.

Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ KE TARE DAKU
35 HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHARUZZAMAN

Baharamu ya damka shi ga hannun wata 'yarsa,
wai ita Bustana, domin ta kula da shi. Ya umurce
ta ta rika yi masa azaba dare da rana har zuwa
wata shekara dashekara da za su koma Dutsen Wuta. Ita wannan
diya ta Baharamu, budurwa ce kyakkyawar
gaske. Farkon zuwan Asadu gidan ba ta nan, shi
ya sa aka damka shi ga hannun kuyanga, wadda
ta azabtar da shi. Amma Bustana kuwa, tun da
ta dora idanunta a kan Asadu, ta gan shi
kyakkyawan saurayi, da ido dara-dara farare tas
kamar madara, da girar ido kamar ta barewa, sai
son sa ya auku a cikin zuciyarta.
Wata rana da ta shiga wurinsa sai ta tambaye shi
sunan sa.
Shi kuwa ya amsa mata da cewa "Sunana
Asadu."
"Asadu, farin ciki ke nan ko?" Ta tambaye shi,
"hakika za ka yi farin ciki. Za ka yi farin ciki a
cikin sauran kwanakinka." Ta ci gaba da cewa,
"na lura an tsare ka a wannan wuri bisa ga
zalunci, bai kamata ka ci gaba da zama wannan
wuri ba." Ta yi ta ba shi hakuri bisa ga azabar da
aka yi masa a baya, ta kuma kwantar masa da
hankali. Ta kwance masa sarkar da aka daure shi
da ita. Ta tambaye shi a kan addinin Musulunci.
Ya gaya mata cewa, addinin Musulunci shi ne
addinin gaskiya wanda Shugabanmu, Annabi
Muhammadu (S.A.W.) ya zo da koyarwarsa daga
Allah Madaukakin Sarki. Kuma ya tabbatar wa
kafirai cewa shi Manzo ne daga Ubangijin talikai,
ta hanyar kawo musu ayoyi mabayyana. Ya kuma
gaya mata cewa, bautar wuta bata ce mai girma
wadda Shaidan jefaffe yake amfani da ita domin
karkatar da mutane daga bin tafarkin gaskiya. Ya
ci gaba da gaya mata yadda addinin Musulunci
yake har zuciyarta ta karkata gare shi. Ta karbi
kalmar Shahada daga wurinsa.

Ta tashi ta kawo masa abinci mai kyau da nama,
da abin sha. Suka ci tare, suka yi salla. Haka ta
yi ta ba shi abinci mai kyau, hankalinsa ya
kwanta, jikinsa ya murmure.
Wata rana Bustana tana tsaye a bakin kofar gida,
sai ta ji mai shela yana shela da murya
madaukakiya, "wanda duk yake rike da wani
saurayi, mai kama kaza da kaza, to, ya fito da
shi, za a ba shi kyauta mai tsoka. Duk wanda
kuma ya kuskura ya ji wannan sanarwa kuma
yana rike da wannan saurayi bai fito da shi ba,
idan aka kama shi za a tsire shi a kofar gidansa
kuma a washe dukkan dukiyarsa."
Yayin da ta ji wannan sanarwa, da ma kuma
Asadu ya ba ta dukkan labarinsa, sai ta fahimci
cewa shi ake nema. Nan take ta je wurin Asadu
ta gaya masa abin da ta ji, ta fito da shi daga
cikin dakin da yake kulle, ta riki hannunsa, suka
lallaba suka bar gidan, suka nufi fadar Sarki. Da
isar su sai Asadu ya ga Amjadu, ya ce, "na
rantse da Allah wannan dan uwana ne Amjadu."
Lokacin da Amjadu ya gan shi sai ya gane shi
shi ma. Suka rungume juna suna zubar da
hawaye don farin ciki. Bayan sun dawo daga
cikin hayyacinsu, Amjadu ya riki hannun Asadu
ya kai shi gaban Sarki, inda Asadu ya kwashe
dukkan labarinsa ya gaya wa Sarki.
Da Sarki da jama'arsa duk sai da suka zubar da
hawaye don tausayi. Sarki ya umurci Waziri
Amjadu ya tafi da askarawa a washe gidan
Baharamu, a kuma rushe shi.

a kuma kawo masa shi a daure.
Amjadu ya jagoranci tawagar askarawa, suka
rushe gidan Baharamu aka zo da shi gaban Sarki
daure cikin igiya. Amjadu ya girmama Bustana
bisa ga taimakon Asadu da ta yi. Daga nan suka
kara maimaita labarinsu a cikin fada, tun fitowar
su daga gida, da kuma rabuwar su har zuwa
yanzu kuma da suka sake haduwa. Da suka
gama labarinsu, Sarki ya ba da umurni a tafi da
Baharamu a tsire shi. Fadawa suka cakume shi
za su fita da shi, sai ya ce, "Allah ya ba ka
nasara, ina neman sassauci." Sarki ya ce babu
sassauci gare shi sai fa idan zai musulunta.
Baharamu ya yarda, ya karbi kalmar Shahada ga
Sarki, ya tuba da tsafi.
Aka yi murna da musuluntarsa. Baharamu ya
dubi Amjadu da Asadu ya ce, "ya shugabannina,
hakika dole ku yi murna da wannan haduwa taku
bayan rabuwa, domin tamkar yadda Na'imu dan
Rabi'u da kuyangarsa Na'imatu suka yi bayan sun
rabu ne suka kuma sake haduwa. Aka tambaye
shi, su kuma me ya faru gare su? Sai ya kada
baki ya ce da su.

HIKAYAR NA'IMU DA NA'IMATU.

A birnin Kufa, akwai wani attajiri wanda ake kira
Rabi'u dan Hatim. Yana daya daga cikin manyan
fadawan Sarkin Kufa. Yana da da daya mai suna
Na'imu. Wata rana Rabi'u dan Hatim na zaune
bisa wundi a cikin kasuwar bayi, sai ya ga an
kawo wata kuyanga za a sayar. Wannan kuyanga
tana rungume da wata 'yarta karama, kyakkyawa.
Sai ya yafuto dillalin da aka damka wa kuyangar,
ya tambaye shi, "nawa ne kudin waccan
kuyanga?" Dillali ya amsa masa, "dinari hamsin."
Rabi'u ya jawo lalitar kudinsa, ya kidaya dinari
hamsin ya ba dillali, ya kuma kawo la'adarsa ya
ba shi. Ya ja kuyanga tare da 'yarta ya tafi da su
gidansa, ya damka su ga hannun matarsa, wadda
ta kasance 'yar baffansa ce.
Matar ta tambaye shi me zai yi da kuyanga? "Na
sayo ta ne domin 'yarta." Rabi'u ya amsa mata,
"nan gaba idan 'yar nan ta girma, to, ba za a
sami kyakkyawar mace ba kamar ta a duk fadin
kasar Larabawa da kewaye."
Ta dubi diyar kuyanga da kyau, "ka yi gaskiya, ya
kai dan baffana." Ta juya wurin kuyanga ta
tambayi sunanta da sunan 'yarta. Kuyanga ta
dukar da kai cikin ladabi ta ce, sunanta Taufik,
sunan 'yarta kuwa Sa'adatu.
"Sa'adatu sa'ar mata." In ji matar Rabi'u, "Lallai
wanda ya sayo ki ya yi sa'a, ke ma kin yi sa'ar
samun ubangida." Sa'annan ta juya wurin mijinta
ta tambaye shi, "Maigida, yanzu wane suna za
mu ambaci 'yar kuyangar nan da shi?" Rabi'u ya
ce shi ba shi da zabi, duk sunan da ta zaba
daidai ne. Ta ce, "to, za mu kira ta da Na'imatu."
Maigida ya ce, "Allah ya bar mana Na'imatu."
Aka hada Na'imatu da Na'imu wuri guda ana
renon su, da ma kuma sa'o'in juna ne. Yara suka
tashi tare, kamar 'yan tagwaye. Suna kara girma
kyawonsu na kara fitowa har ba za a iya
banbance wanda ya fi wani kyau daga cikinsu
ba. Har suka kai shekaru goma-goma, Na'imu na
kiran Na'imatu da 'yar uwarsa, ita ma tana kiran
sa da dan uwanta.
Da uban ya lura da sun fara wayo, sai ya kira
dansa gefe ya ce masa, "ya dana, Na'imatu ba
'yar uwarka ba ce face kuyangar da na saya
maka. Don haka kada ka kara kiranta da 'yar
uwarka." Na'imu ya ce, "af, to, idan haka ne sai
in rike ta a matsayin matata." Ya je ya gaya wa
mahaifiyarsa abin da mahaifinsa ya ce masa.
Uwar ta ce, "kuyangarka ce, kana da dama ka
sarrafa ta duk yadda kake so."
Bayan shekara biyu, kyawon Na'imatu ya fito fili,
ya kasance duk fadin garin Kufa babu kyakkyawar yarinya kamar ta. Ta
hardace Alkur'ani mai girma, ta karanci wakoki
kala-kala, ta gwanance wurin sarrafa kayan kida
da busa har babu kamarta a birnin Kufa. Wata
rana suna zaune ita da mijinta Na'imu a cikin
daki, bayan sun ci sun koshi sun kuma dauraye
makogwaronsu da abin sha. Sai ta jawo molo, ta
gyara tsarkiyarsa ta wake wadannan baitoci:
Yayin da ka kasance shugaba a gare ni, mai tsare
dukkan bukatuna.
Kai ne takobin da ka kare ni daga makiyana.
Me zai sa in nemi kariya daga Amru ko Zaidu?
Na'imu ya yi farin ciki da jin wannan waka. Ya ce
da ita, "na gama ki da girman rayuwata, ya ke
Na'imatu, ki kida mana tambari tare da yin
waka." Ta dauki tambari, ta kida shi da hannunta
ta wake wadannan baitoci, iska na kwasar
zazzagar muryarta:
Na rantse da mamallakin rayuwata, mai sarrafa
zuciyata.
Ba ni saba wa masoyina bisa son zuciya, balle
magabta su gani.
Ba ni kaurace wa jin dadin barci tare da
masoyina
Makiyana kuwa na sa tsidau bisa shimfidarsu
inda za su aza hakarkarinsu.
Na'imu ya yi kyekkewa da jin wannan waka, ya
ce da ita, "babu shakka Allah ya yi ma ki baiwa
mai yawa wadda ba duka mace take da irin ta
ba."
Haka dai Na'imu da Na'imatu suka ci gaba da
zamansu a cikin farin ciki da kaunar juna har
wata rana labarin Na'imatu ya kai ga kunnen
Sarkin Kufa mai suna Hajjaj. Sarki ya ji cewa wai
duk fadin Kufa babu kyakkyawar mace wadda ta
iya kida da waka kamar Na'imatu kuyangar
Na'imu dan Rabi'u.
Shi kuwa Sarkin nan mutum ne mai son a yabe
shi musamman ga manyan Sarakuna. Don haka
sai ya ce a cikin ransa, "babu shakka wannan
kuyanga ba ta dace da kowa ba face Sarkin
Muminai Abdulmalik dan Marwan, domin na
tabbata babu kamar ta a cikin fadarsa." Da ma
ya san babu abin da Sarkin Muminai ke so kamar
kyawawan 'yan mata wadanda suka iya waka da
kida. Don haka sai ya kira wata tsohuwar
kuyangarsa, gwanar iya makirci, ya umurce ta, ta
tafi gidan Rabi'u dan Hatimu ta san dabarar da ta
yi ta sace masa kuyangar dansa Na'imatu ba
tare da kowa ya san cewa shi ya sa ta ba.
Tsohuwa ta ce, wannan abu ai ya fi shan ruwa
sauki a wurin ta. Washe gari sai wannan tsohuwa
ta saka wasu tsummokaran tufafi na gashi, ta
kawo wata tasbaha mai ‘ya’ya dubu ta rataya a
wuyanta...

Baharamu ya ci gaba da
labarinsa, ya ce, Washe gari sai wannan tsohuwa
ta saka wasu tsummokaran tufafi na gashi, ta
kawo wata tasbaha mai ‘ya’ya dubu ta rataya a
wuyanta. Ta sami butar karfe, ta alwala,

1 Comments On HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHRUZZAMAN
avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Wanne darasi kuka ?aru da shi daga cikin wannan hikayar,

Please Login or Register in order to submit comment