Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Na mayar da ke ga
shugabanki." Daga nan ya juya wurin Na'imu, ya
ce, "ya saurayi, shin wanene ya sanar da kai inda
kuyangarka ta ke? Kuma wa ya shirya maka
dabarar da ka shigo nan?"
"Ya Shugaban Muminai, " Na'imu ya amsa masa,
"saurari labarina, na rantse da darajar kakanninka
ba zan gaya maka karya ba."

Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ42 HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHARUZZAMA

Na'imu ya amsa masa,
"saurari labarina, na rantse da darajar kakanninka
ba zan gaya maka karya ba." Ya gaya masa
yadda suka tashi tare da Na'imatu, da yadda aka
shirya dabara aka sace ta daga hannunsa, wanda
sanadiyyar

wannan rabuwa ce ya kwanta rashin lafiya. Ya
fadi yadda mai magani Bafarishe ya gano abin da
ke damunsa, da yadda ya taho da shi nan
Damashka neman Na'imatu. Ya kuma gaya wa
Halifa yadda tsohuwa ta zo wurin su nema wa
Na'imatu magani, wanda hakan ya sa suka san
tana cikin gidan Halifa. Ya fadi yadda tsohuwa ta
taimake shi har ya shigo gidan Halifa, da yadda
ya rude har ya shiga dakin 'yar uwar Halifa.
Na'imu ya kwashe labari kaf, bai rage kome ba,
ya gaya wa Halifa.
Yayin da Halifa ya ji wannan labari, sai ya cika
da mamaki, matukar mamaki. Ya ce a kirawo
masa wannan Bafarishen Boka mai tsananin
hikima. Da aka kira shi, ya nada shi daya daga
cikin 'yan majalisarsa, yana cewa, "wanda duk ya
nuna irin wannan basira da fasaha, to, ya kyautu
mu rike shi kusa gare mu." Ya yi masa kyauta
mai yawa, kuma ya yanka masa albashi.
Haka kuma ya ba Na'imu da Na'imatu kyautar
dukiya mai yawan gaske, tsohuwa ma ba a
manta da ita ba. Suka zauna wurin Halifa cikin
farin ciki da jin dadi. Bayan kwana bakwai, suka
nemi izinin komawa gida, Kufa, domin hankalin
mahaifansu ya kwanta. Halifa ya hada su da 'yan
rakiya, suka ka kai su har cikin gida. Na'imu ya
sadu da mahaifinsa da mahaifiyarsa. Suka yi
zamansu cikin kwanciyar hankali da farin ciki har
lokacin da mai katse jin dadi, mai raba tsakani ta
riske su.

KARSHEN HIKAYAR NA'IMUH DA NA'IMAHTU

Yayin da Baharamu ya gama wannan labari nasa,
Amjadu da Asadu suka yi mamaki, suka ce, "lalle
wannan labari akwai tausayi da ban al'ajabi a
cikin sa." Suka raba dare
suna hira. Da gari ya waye, Amjadu da Asadu
suka hau, suka nufi fada. Da aka yi musu iso,
suka shiga suka yi gaisuwa ga Sarki, suka zauna
suna zance da shi. Can sai suka ji kururuwa da
hargowar mutane, a cikin gari, suna neman
gudummawa. Ko kafin a yi haka, sai ga wani
dogari ya shigo fadar a guje, rawaninsa ga
hannu. Ya fadi gaban Sarki yana haki, ya ce,
"Allah ya ba ka nasara, yaki bisa kan mu."
Sarki ya dube shi ya ce, "wane irin yaki bayan
muna zaune da makwabtanmu cikin aminci?"
Dogari ya ce, "Allah ya ba ka nasara, ni ma dai
abin ya ba ni mamaki. Ba mu san ko wane Sarki
ba ne, yana nan bayan gari ya yi sansani da
rundurarsa bila adadin. Babu abin da mutum zai
gani sai walkiyar masu da takubba."
Sarki ya juya wurin Waziri Amjadu ya ce masa ya
je ya samo labarin da ke tafe da wannan Sarki.
Amjadu ya hau doki ya sukwane shi, ya nufi
bayan gari. Da ya isa wurin rundunar, sai jama'ar
da ke ciki suka gane cewa jakada ne. Amjadu ya
ce su kai shi ga Sarkinsu, suka kai shi har gaban
Sarki. Ya fadi ya yi gaisuwa, da ya dago kansa
sai ya ga ashe Sarkin ma, mace ce, watau
Sarauniya ce.
Ta dubi Amjadu ta ce, "ba kyawon birninku ne ya
kawo ni ba, na zo ne neman wani dan saurayi,
bawana. Idan yana wurin ku, ku ba ni shi. Idan
kuma kuka ki, zan mayar da wannan gari toka."
"Allah ya taimake ki, menene sunan wannan
bawa naki? Kuma yaya kamanninsa suke?"
Ta ce, sunansa Asadu. Yana da siffa kaza da
kaza, ta siffanta yadda Asadu yake. Ta ci gaba
da cewa, "sunana Sarauniya Murjanatu, na hadu
ne da wannan bawa yayin da wasu matsafa suka
je da shi birnina. Na kwace shi daga hannunsu,
amma da dare ya yi sai suka lallaba suka sace
shi suka gudu."

Yayin da Amjadu ya ji zancenta, sai ya gane
cewa dan uwansa ne take nema. Sai ya ce,
"godiya ta tabbata ga Allah, mai yayewar dukan
bakin ciki. Ki sani cewa wanda kike nema dan
uwana ne." Ya kwashe labarinsu duka, tun daga
fitowar su daga birnin Labunus, da yadda suka
rabu, da kuma yadda suka sake haduwa, ya gaya
mata. Saruniya ta cika da mamaki, ta kuma yi
farin ciki da ta gane Asadu. Ta kawo riguna na
musamman ta ba Amjadu, ya karba ya hau
dokinsa ya juya zuwa cikin gari domin sanar da
Sarki abin da ake ciki.
Lokacin da Amjadu ya gaya wa Sarki labarin
Sarauniya, sai suka yi farin ciki. Sarki ya hau
tare da fadawansa da Waziri Amjadu da Asadu
suka nufi bayan gari wurin Sarauniya Murjanatu.
Yayin da suka isa wurin ta, suka zauna suna
mayar da zance. Can sai suka hangi kura ta
tokare sararin samaniya har ta rufe hasken rana,
suka rika jiyo karar kofatan dawaki da kururuwar
askarawa, kamar kasa za ta tsage. Yayin da kura
ta yaye, sai suka hangi rundunar mayaka masu
yawan gaske, tamkar kumfar teku, sai takubba
da masu ke walkiya cikin hasken rana. Wannan
runduna ta taso wa birnin da nufin zagaye shi,
tamkar yadda zobe kan zagaye yatsan hannu.
Lokacin da Amjadu da Asadu suka ga haka, sai
suka buga salati, "daga Allah muka fito, kuma
gare shi za mu koma. Wannan wace irin rundunar
mayaka ce mai yawan gaske. Babu shakka mu
nemi gudummawa daga wannan Sarauniya, idan
ba haka ba kuwa za su lakume mu, kamar yadda
wuta ke lakume karmami." Sarki ya umurci
Waziri Amjadu ya tafi ya jiyo labarin wannan
runduna.

Amjadu ya zaburi dokinsa, ya nufi wurin wannan
runduna. Da zuwan sa aka kai shi wurin Sarki, ya
fadi ya yi gaisuwa, ya tambayi Sarki dalilin
zuwan sa da rundunar yaki.
Sarki ya amsa masa, "ni ne Sarki Gayur, mai
fadoji bakwai, Sarkin tekuna da tsibiran kasar
Sin. Na fito neman 'yata Badura, wadda kaddara
ta raba tsakaninmu, bayan na aurar da ita ga
Kamaruzzaman dan Sarki Shaharuzzaman.
Tsawon shekaru da yawa, har yanzu ban ji
duriyarsu ba. Ko kuna da labarinsu a wannan
kasa taku?"

Ko da Amjadu ya ji haka sai ya fahimci cewa,
wannan tsoho kakansa ne, watau mahaifin
uwarsa, Badura. Sai ya kara durkusawa
a gabansa ya ce, "ai ni ne dan 'yarka, Badura. Ita
mahaifiyata ce, Kamaruzzaman kuwa mahaifina
ne." Yayin da Sarki Gayur ya ji haka, sai ya
sauko daga kan dokinsa, ya rungume Amjadu,
hawaye na zuba daga idanunsa.
Amjadu ya gaya masa cewa, Badura da
Kamaruzzaman suna nan cikin koshin lafiya, suna
zaune a wani birni da ake kira Labunus, shi ne
ma Sarkin garin. Ya kwashe labarin abin da ya
faru tsakaninsa da mahaifinsa da kuma dan
uwansa Asadu, da yadda mahaifin nasu ya yi
fushi da su har ya umurci hauni ya sare musu
kawuna, inda shi kuma haunin ya ji tausayin su, ya kyale
su suka gudu, duk ya fada wa Sarki Gayur.

Sarki Gayur ya ce, "in Allah ya so, zan koma tare
da ku zuwa birnin Labunus, in yi sulhu tsakaninku
da mahaifinku." Ya kawo kyautar tufafi na
alfarma ya ba Amjadu, wanda shi kuma ya hau
dokinsa ya koma wurin Sarkinsa, fuskarsa cike
da farin ciki. Ya gaya wa Sarki da Asadu labarin
Sarki Gayur. Sarki ya yi farin ciki, ya sa aka aika
wa Sarki Gayur da shanu da rakuma da tumaki
masu yawa, da kuma buhuhuwan hatsi. Haka
kuma ya sa aka ba Sarauniya Murjanatu irin
wannan kyauta, ya kuma gaya mata labarin Sarki
Gayur da abin da ke tafe da shi. Ita ma ta ce, za
ta tafi tare da Amjadu da Asadu zuwa birnin
Labunus domin ta lallashi Kamaruzzaman ya
yafe wa 'ya'yansa.
Ana cikin haka kuma sai aka hangi wata kura
daga nesa, ta tokare sararin samaniya, har wuri
ya duhunta, ya koma tamkar cikin dare.

Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ GOBE ZAMU GAMA DUKA INSHA ALLAH43 HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHARUZZAMAN

Ya kawo kyautar tufafi na
alfarma ya ba Amjadu, wanda shi kuma ya hau
dokinsa ya koma wurin Sarkinsa, fuskarsa cike
da farin ciki. Ya gaya wa Sarki da Asadu labarin
Sarki Gayur. Sarki ya yi farin ciki, ya sa aka aika
wa Sarki Gayur da shanu da rakuma da tumaki
masu yawa, da kuma buhuhuwan hatsi. Haka
kuma ya sa aka ba Sarauniya Murjanatu irin
wannan kyauta, ya kuma gaya mata labarin Sarki
Gayur da abin da ke tafe da shi. Ita ma ta ce, za
ta tafi tare da Amjadu da Asadu zuwa birnin
Labunus domin ta lallashi Kamaruzzaman ya
yafe wa 'ya'yansa.
Ana cikin haka kuma sai aka hangi wata kura
daga nesa, ta tokare sararin samaniya, har wuri
ya duhunta, ya koma tamkar cikin dare. Da kurar
ta fara yayewa sai suka ga askarawa bisa
dawaki dauke da zararrun takubba da masu, suna
kururuwa da hargowa. Yayin da wannan runduna
ta matso kusa, suka hangi rundunar Sarauniya
Murjanatu da rundunar Sarki Gayur a bayan gari,
sai suka fara buga ganguna. Sarkin birnin
Matsafa ya ce, "hakika, wannan rana tana cike
da albarka, mun gode wa Allah da ya hada mu
da wadannan rundunoni biyu."
Ya juya wurin Amjadu da Asadu ya ce musu, su
tafi su samo masa labarin wannan runduna mai
yawa kamar farin dango. Amjadu da Asadu suka
hau dawaki suka nufi wurin wannan runduna.
Ko da da suka isa wurin rundunar nan sai suka
ga ashe mayakan birnin Labunus ne, wadda
mahaifinsu, Kamaruzzaman, da kansa ya fito tare
da su. Yayin da suka yi arba da mahaifinsu, sai
suka fadi suka yi gaisuwa. Lokacin da
Kamaruzzaman ya ga 'ya'yansa, sai ya yi kamar
ya some don farin ciki, ya rungume su cikin
kirjinsa, dukkansu suna kuka. Ya ba su labarin
yadda ya gane gaskiyar lamari, tsakaninsu da
iyayensu mata, da kuma yadda hauni ya fada
masa cewa bai kashe su ba har ya fito neman
su. Ya nemi gafarar su, suka gafarta masa.
Sa'annan suka fada masa labarin zuwan Sarki
Gayur, suka nuna masa inda rundunarsa take.
Kamaruzzaman ya hau tare da 'ya'yansa, da
wasu mukarrabansa, suka nufi wurin surukinsa,
Sarki Gayur. Da suka kusa isa wurin, sai Amjadu
ya zaburi dokinsa ya yi gaba, ya riga su isa
wurin sansanin Sarki Gayur. Ya gaya masa
labarin zuwan Kamaruzzaman. Nan da nan Sarki
Gayur da wasu na kusa gare shi suka hau dawaki
suka tari Kamaruzzaman. Bayan sun gamu, suka
ba juna labarin bayan rabuwa. Suka yi mamakin
wannan haduwa tasu, matukar mamaki.
Mutanen cikin birni kuwa da suka ji labarin abin
da ake ciki sai suka fara tunanin me ake ciki,
kowa ciki ya duri ruwa, suna zaton yaki ne. Suka
yi ta fitowa da kabukkan abinci da nama, da
tulunan ruwa da abin sha, suna kawo wa baki.
Wasu kuma suka rika debo harawa da ciyawa
suna kai wa dawakin askarawa. Wasu kuma suka
fito da kayan kida da na busa aka fara kade-kade
da raye-raye ana shewa.
Mutane na cikin wannan bidiri, sai kuma aka
hango wata kurar ta rufe ko'ina na sararin
samaniya. Aka rika jin kasa na girgiza kamar za
ta tsage. Gunjin dawaki da bugun ganguna suka
hadu tamkar aradu na sauka. Mutane duk aka
tsaya cik ana sauraren isowar wannan runduna.
Da kura ta yaye sai aka ga dukkan askarawan
wannan runduna suna sanye da bakaken tufafi,
don yawansu sai suka zama kamar tururuwa
daga nesa.
Sarkin birnin Matsafa ya ce, "babu tsimi babu
dabara face daga Allah Madaukakin Sarki.
Wannan kuma rundunar wane sarki ce?" Sauran
Sarakunan nan suka ce masa, kada ya ji tsoro,
idan ma har makiyi ne, to, za su taimake shi
wurin yakarsa. Suna cikin wannan zance sai ga
'yan sako sun zo daga cikin rundunar. Suka fadi
gaban Sarakunan nan hudu suka yi gaisuwa.
Daga nan sai suka ce, "Sarkinmu ya ce a sanar
da ku, ya fito daga kasarsa da ke yankin Farisa
domin neman dansa da ya fito daga gida,
shekara da shekaru. Idan yana wurin ku ku fito
da shi, idan kuwa kuka ki, to, zai darkake wannan
gari naku, ya mayar da shi turbaya, kamar yadda
ya yi wa biranen da biyo ta cikin su."
"Haka ba zai faru ba," in ji Kamaruzzaman,
"mene sunan wannan Sarki naku?" "Sunansa
Shaharuzzaman, mai mulkin tsibirai da tekunan
Kalidan."
Lokacin da Kamaruzzaman ya ji an ambaci sunan
mahaifinsa, sai ya yi wata kara mai tsanani, ya
fadi kasa somamme. Aka shafa masa ruwa ya
farfado. Da hankalinsa ya dawo, sai ya dubi
'ya'yansa Amjadu da Asadu, idanunsa cike da
hawaye, ya ce musu, "ku tafi tare da wadannan
manzanni wurin kakanku, Sarki Shaharuzzaman.
Ku yi masa bushara da kasancewa ta a wannan
wuri." Sai kuma ya ce a cikin ransa, "Allah Sarki,
har yanzu mahaifina yana sanye da bakaken
tufafi domin nuna bakin cikin rabuwa da ni." Da
ya tuna irin tsananin son da mahaifinsa ke yi
masa, sai ya sake fashewa da kuka.
Kamaruzzaman ya fada wa sauran Sarakunan
labarin kuruciyarsa, da yadda mahaifinsa ke son
sa, da yadda aka yi ta fama da shi a kan ya yi
aure, da kuma abin da ya raba shi da gida, da
wahalhalun da ya sha duka, ya fada musu. Suka yi al'ajabi matukar
al'ajabi. Suka tashi gaba daya suka nufi sansanin
Sarki Shaharuzzaman. Yayin da Kamaruzzaman
da mahaifinsa suka ga juna, sai suka sauka daga
kan dawakansu, suka rungume juna, don tsananin
farin ciki sai da suka suma.
Bayan sun farfado, hankalinsu ya kwanta, sai
Kamaruzzaman ya kwashe labarinsa kaf ya fada
wa mahaifinsa. Ya nemi gafararsa a kan rashin
komawar sa gida. Haka dai kowa ya bayar da
labarinsa, da irin wahalar da ya sha. Sarkin birnin
Matsafa ya sa aka shirya gagarumin biki domin
murnar haduwar wadannan Sarakuna. Aka kwana
bakwai ana shagali, babu dare babu rana, daga
nan kowane Sarki ya yi haramar komawa
kasarsa.
Aka daura auren Asadu da Sarauniya Murjanatu.
Amjadu kuwa ya auri Bustana, diyar Baharamu,
sarkin tsafi na da. Daga nan Sarki Gayur da Sarki
Sharuzzaman da Sarki Kamaruzzaman da
'ya'yansa, da Sarauniya Murjanatu, suka yi
sallama da Sarkin birnin Matsafa, tare da
alkawarin za su rika ziyartarsa a kai a kai, suka
dunguma suka nufi birnin Labunus.
Yayin da suka isa, Kamaruzzaman ya tafi wurin
surukinsa, Sarki Armanus, ya kwashe labarin
tafiyarsa ya gaya masa. Ya kuma gaya masa
yadda ya sadu da 'ya'yansa da mahaifinsa da
kuma surukinsa, uban Badura. Sarki Armanus ya
yi mamaki. Badura ta ga mahaifinta, suka
rungume juna suna kuka don farin ciki. A nan ma
aka shirya wani kasaitaccen buki. Bayan wata
guda, sai Sarki Gayur ya dauki 'yarsa Badura tare
da jikansa Amjadu zuwa birnin Sin.
Yayin nan ya yi murabus ya nada Amjadu a
matsayinsa. Shi kuwa Kamaruzzaman sai ya
nada Asadu, wanda yake jika ne ga Sarki
Armanus, a matsayin Sarkin Labunus, ya bi
mahaifinsa, Shaharuzzaman, zuwa kasarsu ta
Kalidan.
. Lokacin da suka kusa isa, sai suka dakata a
bayan gari suka tayar da 'yan bushara su kai
labari. Ba a dade ba kuwa, sai ga 'yan tariya sun
zo da kade-kade da bushe-bushe. Aka dunguma
aka shiga cikin birni. Aka kawata birnin Kalidan
da kayan kwalliya, tamkar yadda aka yi a ranar
bikin haihuwar Kamaruzzaman. Aka share wata
guda ana biki. Daga nan sai Shaharuzzaman ya
yi murabus, ya nada Kamaruzzaman a
matsayinsa. Sai ya kasance daga lokaci zuwa
lokaci, wani daga cikin Sarakunan nan zai kai wa
wani Sarkin ziyara har kasarsa. Suka zauna cikin
jin dadi da kwanciyar hankali, har mai katse jin
dadi, mai raba da da mahaifi, mai raba masoya ta
zo musu.

Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ KARSHE KENAM INSHA ALLAH' SAIKUMA INMUN HADU AWATA HIKAYAN,

WhatsApp 08032767547

This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


1 Comments On HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHRUZZAMAN
avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Wanne darasi kuka ?aru da shi daga cikin wannan hikayar,

Please Login or Register in order to submit comment