Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jirgi da shi, ba tare da ya
ce masa uffan ba. Ya tura keyarsa zuwa cikin
jirgi. Madugu ya kwance jirgi, ya tuka suka tafi.
Mamaki ya ishi Kamaruzzaman har ya kasa
hakuri ya tambayi Madugun jirgi dalilin
dawowarsa ya dauke shi. Madugu ya harare shi,
ya ce, "Ashe kyawun nan naka kyawun banza ne?
Sarkin Labunus ya fada mana cewa kai barawo
ne, ka taba sace masa wasu kaya lokacin da ka
taba kai 'ya'yan zaitun a kasarsa. Shi ne ya ba ni
umurnin in komo in tafi da kai wurinsa."
Yayin da Kamaruzzaman ya ji wannan jawabi na
Madugu sai ya ce, "Na rantse da Allah, ban ko
san hanyar birnin Labunus ba, balle har in shiga
cikinsa." Madugu dai ya kyale shi bai tanka masa
ba, domin yana cike da hushin wannan tafiya.
Haka suka ci gaba da keta ruwa, kwana da
kwanaki har Allah ya nufe su da shiga birnin
Labunus. Da zuwansu sai Madugu ya ja
Kamaruzzaman zuwa fada wurin Badura. Ya
kuwa sami ana fadanci, Badura na kan karagar
mulki, ta sha rawani fuskarta a rufe, kamar yadda
takan yi idan za ta fita a cikin mutane. Ta dubi
Kamaruzzaman tare da Madugu, nan take ta
shaida Kamaruzzaman, kodayake ya rame, kuma
ya yi baki. Ta kawo dinari dubu goma ta ba
Madugun jirgi ta sallame shi, ya tafi yana godiya.
Ta juya ga bayi ta ce su kai Kamaruzzaman
gidan wanka, idan ya gama wanka su dawo mata
da shi.
Daga nan ta tashi ta shiga gida wurin
Hayatunnufusi, ta fada mata cewa an dawo da
Kamaruzzaman, sa'annan kuma ta ce, "Ina so ki
kame bakinki, har sai na aikata wani abin
mamaki, wanda za a rubuta shi a takarda ana
karanta shi ga Sarakuna da talakawa masu zuwa
bayanmu, tsawon zamani."
Suna cikin wannan magana sai ga bayi sun zo,
suka shaida wa Badura cewa, Kamaruzzaman ya
fito daga wanka. Ta umurce su da su tufatar da
shi tufafi masu kyau na alfarma, irin tufafin
Sarakuna. Bayi suka tafi suka aikata tamkar
yadda aka umurce su.
Yayin nan Badura ta koma fada, ta tarar da bayi
tare da Kamaruzzaman suna jiran zuwanta.
Bayan ta zauna kan karagar mulki, ta dubi
Kamaruzzaman ta ga ya komo cikin hayyacinsa,
yana haske yana kyalli tamkar wata dan daren
goma sha hudu. Sha'awarta game da shi ta
motsa, amma sai ta danne zuciyarta, ta kudiri
aikata abin da ta yi nufi. A wannan rana ta nada
shi daya daga cikin manyan 'yan majalisarta, ta
ba shi kyuatar bayi da kuyangi da dawaki da
rakuma, da alfadarai, da kudi tsaba, masu yawa
ta kuma ba shi gida.

Sai ya kasance kullum Kamaruzzaman yakan fita
fada ya zauna cikin 'yan majalisa ana fadanci,
amma bai taba gane cewa Badura mace ce ba,
balle har ya shaida ta. Ita kuwa kullum ya zo sai
ta yi masa kyauta ta dukiya mai dimbin yawa,
kuma tana girmama shi fiye da sauran 'yan
majalisarta. Har fadawa dai suka gane cewa
Kamaruzzaman dan gaban goshin Sarki ne, sai
suka shiga girmama shi.
Badura ta ci gaba da yi masa kyauta kullum ya
zo fada, har ta kusa ba shi dukkan dukiyar birnin
Labunus. Wannan abu sai ya daure wa
Kamaruzzaman kai, ya ce a cikin ransa, "Kai!
Ruwa fa ba ya tsami banza, wannan kyauta da
Sarki ke yi mini kullum akwai alamun lauje cikin
nadi. Babu makawa akwai wani abu da Sarkin
nan yake nufi game da ni. Babu abin da ya fi
zama alheri a gare ni face in bar masa kasarsa."

Ran nan bayan an tashi daga fada sai
Kamaruzzaman ya tari Badura kafin ta shiga
gida. Ya durkusa a gabanta ya ce, "Allah ya ba
ka nasara, ni dai har yanzu hankalina bai kwanta
ba da irin wadannan kyaututtuka da kake yi mini
kullum. Idan ka yarda, Allah ya ba ka nasara, ina
so ka karbe dukan abin da ka ba ni, ba na son ko
allura, sa'annan ka bar ni in wuce gaba."

Badura ta yi murmushi, ta ce, "Don me kake so
ka bar mu, ka wuce zuwa wani birni? Bayan a
nan kana cikin jin dadi da wadata, da kuma
daukakar daraja?"
"Ya Sarki, lalle wannan jin dadi da wadata da
nake ciki, idan babu wani kwakkwaran dalilin da
ya sa ake yi mini su, to, wannan abu shi ne abin
mamaki, mafi zama mamaki." In ji
Kamaruzzaman, ya ci gaba da cewa, "Ka daukaka
darajata fiye da ta sauran 'yan masalisarka
wadanda na iske tare da kai, wadanda kuma
suke dattijai masu hankali, amma ni ba kowa ba
ne face yaro a cikinsu, amma duk da haka, ka
daukaka ni fiye da su."

Badura ta yi wani boyayyen murmushi, fuskarta
na sunke a cikin rawani, sa'annan ta dubi
Kamaruzzaman ta ce, "Lalle kana da gaskiya, dan
samari. Ba kome ya sa na daukaka darajarka ba,
kuma nake ta yi maka kyaututtuka, face saboda
kyawunka, da kuma fuskarka mai hasken da ke
kunyatar da hasken wata. Tun lokacin da na dora
idona a kanka, na ji sha'awarka ta soki zuciyata.
Idan za ka yarda in gusar da sha'awata a kanka,
to, da kuwa na ba ka dukkan abin da kake so na
dukiya, kuma in daukaka darajarka zuwa
Wazirina, duk da karancin shekarunka. Kodayake
ni ma, ba girme maka na yi a shekaru ba, amma
duk da haka jama'a suka amince mini na zama
Sarkinsu. Don haka ba abin mamaki ba ne a cikin
wannan zamani idan yara sun karbe ragamar
mulki daga hannun tsofaffi. Wallahi ya cika mai
hikima, wannan mawakin da yake cewa:..

"Kai ka ce zamaninmu muna daga mutanen
Ludu, suna da begen juna a cikin kirazansu
musamman na kananan yara."
Yayin da Kamaruzzaman ya ji zancen Badura, shi
yana dauka a cikin ransa Sarki ne namiji mai
auren 'yar Sarki Armanus. Sai ya dukar da kansa
kasa don kunya da takaici, nan take kuma
kumatunsa suka yi ja, kamar wuta mai huruwa,
don fushi. Ya dago kansa ya ce, "Allah ya ba ka
nasara, ni kam ba na bukatar duk wani matsayi
da za ka nada ni domin dai in yarda da wannan
bukata taka ta saba wa Allah. Na fi son in mutu
cikin talauci da bautar Ubangiji da in mutu cikin
dukiya da sabon Ubangiji."
............
Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar
labarun DARE DUBU DA DAYA, wanda littafin nanan akasuwa
26 HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHARUZZAMAN

Da Kamaruzzaman ya ji haka, sai hankalinsa ya
tashi, fuskarsa ta yi duhu. Ya ce, "Allah ya ba ka
nasara, ka tuna fa kana da kyakkyawar mata a
gida, bayan ita kuma kana da kyawawan kuyangi
masu yawa, wadanda babu tamkarsu a fagen
kyau. To, don me za ka hadiye mini miyau, ka ce
dole sai ni? Ka karkata zuwa gare su mana, ka
sami biyan bukatarka."
Badura ta ce, "wannan gaskiya ne, amma babu
daya daga cikinsu da za ta iya kawar mini da
sha'awarka, ni kai nake sha'awa. Ko ba ka ji abin
da aka fada ba ne? Abin da zuciya ke so ai shi
ake ba ta. Don haka, ka daina wani muku-muku,
ka saki jikinka kawai ka biya mini da bukata."
Da dai Kamaruzzaman ya ga cewa, idanun Sarkin
nan sun rufe bisa aikata abin da ya yi nufi, kuma
babu makawa sai ya aikata haka, sai ya ce, "ya
Sarki, ina rokonka alfarma daya."
"Wace alfarma ce?" Badura ta tambaya.
Kamaruzzaman ya amsa mata, "Allah ya ba ka
nasara, tun da har idonka ya rufe bisa aikata
wannan laifi mai girma tare da ni, to, ka yi mini
alkawarin cewa idan ka aikata shi sau daya a
gare ni, ba za ka kara nema na da wannan zance
ba. Domin ni, ina jin tsoron fushin Ubangiji,
wanda yake yi ga duk masu aikata irin wannan
aiki."
"Af, in don wannan, to, na yi alkawari ba zan kara
tonar ka da wannan magana ba idan ka ba ni
hadin kai har na biya bukatata yanzu. Daga nan
sai mu roki Allah gafara, domin shi, mai yawan
gafara ne kuma mai yawan jin kai. Yakan sa
bayinsa Aljanna ne ba domin yawan ibadarsu ba,
sai don rahamarsa kadai."
Bayan ya sa ta rantse da Ubangijin talikai, wanda
babu wani ubangiji bayan shi, a kan cewa za ta
aikata wannan abu a gare shi sau daya tak,
bayan shi ba za ta kara neman sa da maganar
ba. Sai ya bi ta zuwa wani daki a cikin gidan. Ita
kuma tana cewa, "babu tsimi babu dabara face
daga Allah madaukakin Sarki, hakika wannan abu
kadararren al'amari ne, daga mai ikon kaddara
kome."
Bayan sun shiga cikin daki, ta sa Kamaruzzaman
ya cire wandonsa, duk kunya ta rufe shi, sai
hawaye ke zuba daga idanunsa saboda tsoron
irin girman laifin da suke shirin aikatawa. Ita
kuwa Badura babu abin da take yi a cikin ranta
sai dariya, amma ta kanne ta ki bayyanar da
dariyar tata. Ta umurce shi da kwantawa bisa
shimfida, tana cewa, "daga wannan dare ba zan
kara nemanka da aikata wannan aiki ba sai idan
kai ne ka nema. Amma ina tabbatar maka cewa
za ka ji dadin wannan abu da za mu yi yanzu,
har ba za ka taba mantawa da shi ba, tsawon
rayuwarka." Daga nan ta rungume shi ta
bayansa, tana shafa kirjinsa da hannayenta. Ta
juyo da shi, suka yi gaba da gaba. Ta ce masa,
"ka sanya hannunka karkashin cinyoyina ka tashi
liman da almajiransa biyu da ke barci, su farka
su soma ibada."
Kamaruzzaman ya ce, "ya Sarki, ni ban saba da
aikata wannan aiki ba."
Badura ta ce, "babu makawa ka yi abin da na
umurce ka, domin zai amfanar da kai matuka."
Kamaruzzaman ya fito da hannunsa ya tura a
cikin wandonta, hannun yana rawa kamar wanda
zai taba garwashin wuta, ya fara shafa tsakanin
cinyoyinta. Ya ji su da sanyi kamar raba, ga
kuma taushi da laushi kamar audugar rimi, sai ya
ji dadi a cikin ransa. Ya ci gaba da shafawa daga
wajen cinyoyinta har ya tura hannunsa kurya.

Maimakon ya ji ya taba sandar namiji sai ya ji ya
shafi kogon mace. Ya ce a cikin ransa, "A'aha,
wannan Sarki ko maza-mata ne?" Sa'annan sai
ya ce da Badura, "Allah ya ba ka nasara, ban ji
liman da almajiransa biyu ba." A wannan karon
sai Badura ta kasa gintse dariyar da ke cin ta, ta
fashe da dariya har ta fadi bisa keyarta.
Bayan ta gama kwasar dariya sai ta ce, "ya
masoyina, ba dai har ka manta da abin da ya
faru a darenmu na farko ba, daren tarewa?" Daga
nan ta kware rawaninta, nan take Kamaruzzaman
ya shaida ta a matsayin matarsa, Badura 'yar
Sarki Gayur, Sarkin kasar Sin. Suka rungume juna
cikin murna da farin ciki marar misaltuwa, suka
rika rera wakokin rabuwa da juna. Suka labarta
wa juna labarin bayan rabuwa. Kamaruzzaman
ya tambaye ta dalilin da ya sa ta tarye shi da
wannan irin wasa. Ta ce da shi, "ya masoyina, na
yi haka ne domin in yi maka dariya, kuma
wannan haduwa ta kasance abar tunawa tsawon
rayuwarmu."
A wannan dare Kamaruzzaman da Badura suka
kwana rungume da juna suka kashe kishirwar
begen juna. Da gari ya waye, bayan rana ta fito
ta baje haskenta, Badura ta tafi wurin Sarki
Armanus, ta fada masa gaskiyar labarinta. Ta ce
masa ita matar Kamaruzzaman dan Sarki
Shahruzzaman ce. Ta labarta masa yadda suka
fara ganin juna, da abin da ya same su bayan
rabuwa. Ta kuma fada masa yadda
Kamaruzzaman ya bi ta har kasarsu, da yadda ya
aure ta. Ta fada masa yadda suka yi niyyar tafiya
kasar mahaifin Kamaruzzaman, da yadda shi
Kamaruzzaman din ya bace musu, suka ci gaba
da tafiya har suka iso wannan birni nasa. Badura
ta kwashe kome ta fada wa Sarki Armanus, daga
karshe kuma ta ce masa, har yanzu 'yarsa
Hayatunnufusi budurwa ce.
Sarki Armanus ya mamaki da wannan labari
nasu, matukar mamaki. Ya yi umurni da a rubuta
wannan labari da ruwan zinariya bisa takard a
dakin ajiye kayan tarihi domin 'yan baya su
karanta ko za su karu da darussan da ke cikin
labarin. Sarki ya sa aka kira masa
Kamaruzzaman, ya tambaye shi ko zai amince
ya auri 'yarsa, Hayatunnufusi? Kamaruzzaman ya
sunkuyar da kansa kasa ya ce, "Allah ya ja
zamanin Sarki, a yi mini uzuri har in tamabayi
matata Badura, domin kuwa ina da bashinta mai
nauyi a kaina."

Kamaruzzaman ya tuntubi Badura da maganar.
Ta ce masa, "ya masoyina, wannan ai shi ne
daidai, domin duk abin da muka yi mata ba mu
biya ta ba, bisa ga diyaucin da ta yi mana,
hakika ta cika 'yar halas. Ga shi kuma mahaifinta
ya wadata mu da alherinsa." Yayin da
Kamaruzzaman ya ga cewa Badura ta aminta da
zancen auren Hayatunnufusi, kuma ya tabbata ta
fadi haka ne da zuciya daya, babu kishi a cikin
ranta.sai ya je
ya shaida wa Sarki Armanus abin da matarsa ta
ce, ya fada masa cewa ya yarda zai auri
Hayatunnufusi. Sarki ya yi matukar farin ciki da
jin wannan jawabi na Kamaruzzaman. Nan da
nan ya sa aka tara masa dukan 'yan majalisarsa,
da hakimansa, da alkalai. Ya kwashe labari duka
ya fada musu, sa'annan ya ce, "ku sani cewa, ni,
na yi niyyar in aurar da 'yata ga Kamaruzzaman,
sa'annan in nada shi Sarki a maimakon matarsa
Badura. Ko me kuka gani a cikin wannan
sha'ani?"

Suka amsa gaba daya, "tun da dai shi ne mijin
shugabarmu Badura, wadda muka dauka a
matsayin Sarkinmu har zuwa wannan lokaci,
kuma sirikin mai girma Sarki Armunus, mun
amince a nada shi a matsayin Sarkinmu, kai da
kaya ai duka mallakar wuya ne. Wallahi mun so,
mun so." Sarki ya kume don farin ciki, ya umurci
alkalai su rubuta takardar auren Kamaruzzaman
da 'yarsa Badura, daga nan kuma aka shiga
shirye-shiryen bikin aure da nadin sarauta gaba
daya.
Kafin ranar biki aka kawata birnin Labunus,
kwararo-kwararoda lungu-lungu, da kayan
kwalliya iri daban-daban. Da ranar biki ta zo aka
goce da shagali, aka yi kamar wata guda ana
shagali, sa'annan kowa ya kama gabansa yana
addu'a ga sabon Sarki. Shi kuwa tsohon Sarki ya
ba da kyaututtukan tufafi ga hakimansa da kuma
fadawa, ya rarraba sadaka ga mabukata, ya sa
aka sallami dukan 'yan sarkan garin.....27 HIKAYAR SARKI KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHARUZZAMAN

Kafin ranar biki aka kawata birnin Labunus,
kwararo-kwararoda lungu-lungu, da kayan
kwalliya iri daban-daban. Da ranar biki ta zo aka
goce da shagali, aka yi kamar wata guda ana
shagali, sa'annan kowa ya kama gabansa yana
addu'a ga sabon Sarki. Shi kuwa tsohon Sarki ya
ba da kyaututtukan tufafi ga hakimansa da kuma
fadawa, ya rarraba sadaka ga mabukata, ya sa
aka sallami dukan 'yan sarkan garin.
Kamaruzzaman kuwa ya shimfida mulkinsa cikin
adalci da tausayin talakawa, ya sa aka rage kudin
haraji da na jangali, ya zama mai yawan kyauta
ga talakawansa. Ya zauna tare da matansa biyu,
idan yau ya kwana dakin wannan, gobe sai ya
kwana dakin waccan. Dukan bakin cikinsa ya
yaye, zuciyarsa ta koma fari fat, kamar takarda.
Ya manta da kasarsu, ya manta da mahaifinsa Shahruzzaman.

A kwana a tashi, Allah ya arzuta shi da 'ya'ya
biyu daga matansa, dukansu maza, kyawawa,
suna haske kamar watanni. Babban sunansa
Amjadu, wanda Badura ta haifa masa, sai kuma
Asadu, wanda Hayatunnufusi ta haifa masa. Suka
tashi kamar 'yan tagwaye, sai dai Asadu ya dan fi
Amjadu kyau kadan. Suka tashi cikin kulawa ta
musamman, suka nakalci ilimin addini da na
mulki, suka san dukan ilimi na taurari da na
yanayin kasa, har suka fi dukan mutanen
zamaninsu. A fagen yaki kuwa, an horar da su
hawan doki, sun iya sara da takobi, sun
gwanance wajen iya suka da mashi da kuma jefa
shi, sun san dukan dabaru na harba kibiya. Sun
iya kokawa da zamiya. Amjadu da Asadu suka
zama tamkar Antaru a fagen jarunta.
Suna ci gaba da girma kyawunsu da kwarjininsu
na kara fitowa. Mutane duka, maza da mata,
suna kaunarsu, har suka cika shekaru goma sha
bakwai. Yaran nan fa suka tashi cikin kaunar
juna, tare suke wasa, tare suke cin abinci, a
wurin barci ma bisa shimfida daya suke kwana.
Mutane suka rika mamakin hadin kai na
wadannan yara, sai ka ce ba 'yan uba ba.

Yayin da Amjadu da Asadu suka kai munzalin
mutane, sai mahaifinsu Kamaruzzaman ya fara
koya musu sha'anin mulki. Duk lokacin da zai tafi
farauta ko rangadi, ya kan bar su a gida ne, su yi
mulki har zuwa lokacin da zai dawo. Su kuwa
sukan rika raba mulkin a tsakaninsu, idan wannan
ya hau karaga yau, gobe sai wannan ya hau, har
zuwa lokacin da mahaifin nasu zai dawo. Ba a
kuwa taba kawo wa Kamaruzzaman koken
'ya'yan nan nasa, a kan yadda suke gudanar da
mulkinsu ba.
Bisa ga kaddara da kuma rudin shaidan jefaffe,
da kuma raunin tunani irin na mata, sai gimbiya
Badura ta auku a cikin son Asadu. Ta kasance
idan ya zo wurinta, takan ja shi da wasanni da
hira, wani lokaci har takan rungume shi ta
sumbace shi. Shi kuwa Asadu bai dauki wannan
abu a matsayin wani abu ba, a tunaninsa duk
tana yin haka ne kamar yadda mahaifiya kan yi
wa danta. Amma ita abin ba haka yake ba a cikin
zuciyarta, shaidan ya rigaya ya yi mata huduba,
babu abin da take so irin ta kwanta shimfida
daya ita da Asadu, su ji dadin juna
Abin kamar hadin baki, ashe ita kuma gimbiya
Hayatunnufusi shaidan ya rigaya ya gama
kawata mata Amjadu, babban burinta kullum shi
ne ta kwana tare da shi. Kullum sai alamomi
take nuna masa na soyayya, amma shi ko a
mafarki tunaninsa bai yi daidai da abin da take
nufi ba. Ya dauka tana nuna masa soyayya ne a
matsayinta na mahaifiyarsa.
Soyayyar 'ya'yan nan nasu fa ta tsananta a cikin
zukatansu matuka, har barci ya fara kauracewa
daga idanunsu, suka daina jin dadin abinci da
abin sha. Ana nan wata rana sai Kamaruzzaman
ya shirya ya fita zuwa ga farauta, ya bar ragamar
mulki ga 'ya'yan bisa ga al'ada.

A ranar farko sai Amjadu ya hau karagar mulki,
yana umurni yana hani, yana hukunci a tsakanin talakawa da adalci.

Da Hayatunnufusi ta ga Amjadu ya kasa gane manufarta, duk da irin
alamomin da take nuna masa, sai ta yanke
shawarar ta fito fili ta amaye masa abin da ke
cikin zuciyarta. Ta dauko takarda da alkalami ta
fara rubuta wasika kamar haka:
Daga wadda soyayya ta tarwatsa birnin zuciyarta,
wadda ta zama abin tausayi a cikin son wanda
bai san ana son shi ba, ita ce wadda take
azabtuwa a kodayaushe domin begenka. Ya
zama wajibi a gare ni, a cikin wannan sa'a, in
bayyana maka irin sarkakiyar soyayyarka da ta
dabaibaye mini zuciya wadda har ta kai ga ba na
iya cin abinci balle barci, idanuna kullum ba su
rabo da zubar da hawaye domin begenka. Raina
yakan yi zafi, kirjina yakan kuntata domin
rashinka. Na kasance mai bakin ciki da kuncin
rayuwa domin begenka. A takaice dai, wannan
takarda ba za ta isa in bayyana maka irin
soyayyar da nake yi maka ba, da kuma irin bakin
cikin da nake ciki domin rashin fahimtata da ba
ka yi ba. Burina mu kwana shimfida daya, mu
wadatu da ni'imar juna. Wassalam, daga
Hayatunnufusi...

Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ ke muku barka da shan'ruwa28 HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHARUZZAMAN

Ta rubuta wasu baitocin waka na soyayya daga
kasan takardar, ta yanki wani sashi na gashin
kanta mai santsin gaske, kamar siliki, wanda da
za a sayar da shi a kasuwa, da kudinsa ya lashe
baitulmalin wata kasa, saboda kyawunsa. Ta
shafa masa turaren miski, ta nannde takardar da
shi. Ta kira wani bakin bawanta, ta aike shi da
takardar zuwa ga Amjadu.
Bawa ya riki takarda ya tafi yana
gaggawa, ba tare da ya san kaddarar da ke
jiransa ba tattare da wannan takarda, domin
kuwa mai kaddarawa - Allah - yakan kaddara
kome kamar yadda ya so.
Da zuwan bawa, sai ya fadi ya yi gaisuwa a
gaban Amjadu, ya fito da takarda ya mika masa.
Ya karba ya bude, ya karanta sakon da ke ciki,
nan take ya fahimci abin da Hayatunnufusi ke
nufin aikatawa tare da shi na zina da cin amanar
mahaifinsa. Nan take annurin fuskarsa ya gushe,
idanunsa suka hau suka yi ja don fushi. Ya shiga
la'antar mata da ayyukansu na cin amana. Ya ce,
"Allah ya wadan mata bisa ga ayyukansu na cin
amana. Marasa tunani, marasa imani!" Ya dubi
bawan nan, sai kuma duk fushin takarda ya koma
kansa, dama an ce zomo ba ya fushi da
makashinsa sai maratayinsa, ya zare takobi, ya
daka masa tsawa, "Allah ya wadaran ka, bakin
bawa, mai baki kamar gawayi. Don me za ka
dauko sakon zina da cin amanar shugabanka ka
kawo mini?" Bawan nan bai sami ta cewa ba, sai
Amjadu ya dauke kansa da takobi.
Ya nade takarda, tare da gashin nan ya tura a
cikin aljihun rigarsa. Ya shiga gida wurin
mahaifiyarsa, ya fada mata abin da ya faru, ya
kara da cewa, "wallahi ba don gudun bacin ran
mahaifina da dan uwana Asadu ba, da na tafi
yanzu na sare kan ta, kamar yadda na sare kan
bakin bawanta." Ya shura takalminsa ya fita yana
la'antar halayen mata. A wannan dare ya kasa
cin wani abin kirki, ya kuma kasa barci saboda
takaici. Ita kuwa Hayatunnufusi da ta ji labarin
abin da Amjadu ya aikata ga bawanta, sai ta yi
fushi da shi, ta zazzage shi, ta kuduri aniyar
hada masa wani tarko na sharri idan mahaifinsa
Kamaruzzaman ya dawo.
Washe gari kuma sai Asadu ya hau karagar
mulki, ya yi umurni ya yi hani, ya tube ya nada,
ya yi hukunci bisa adalci ga talakawa. Can bayan rana ta yi zawwali, lokacin sallar azahar ya yi.

Sai ga wata tsohuwar kuyanga ta kawo masa
sakon takarda daga gimbiya Badura. Ashe ita
kuma soyayyar Asadu ta ci ta, har ta kasa hakuri
ta rubuto masa takarda, ta yanki gashin kanta
mai santsin gaske, wanda da za a saye shi da
kudi, da ya yi barazana ga tattalin arzikin wata
kasa, saboda darajarsa. Bayan ta shafe gashin
da turaren miski, sai ta nannade takardar da shi.
Asadu ya karbi takarda ya bude, sai ya ga an
rubuta:
Daga wadda ta dulmiye a cikin kogin soyayya,
zuwa ga shugaban kyawawa na zamaninsa. Shi
ne wanda yake kunyatar da farin wata don
haskensa, yake dusashe zinariya don kyawunsa.
Shi ne wanda ya juya baya ga masoyiya mai
tsananin begensa, ya rufe idanunsa kamar da dai
bai san da zamanta ba. Wannan sako ne daga
zuciyar mai bege, wadda son ka ya raunana
jikinta, begenka ya kakkarya kasusuwanta,
tunaninka ya zama abincinta, zuwa ga Yarima
Asadu, farin cikin zuciyata. Ka sani hakurina ya
kare, babu sauran zagaye-zagaye, sonka ya riga
ya mamaye dukan jijiyoyin jikina, ba kuwa zan
samu nutsuwa ba sai ranar da na gan mu
kwance bisa shimfida daya, muna shayar da
junanmu ruwan soyayya. Na sadaukar maka da
dukan kaina, sai abin da ka ga dama da ni. Daga
zuciyar mai bege. Badura.
Daga kasan takardar kuma ya ga ta rubuta wasu
baitoci na wakar soyayya. Yayin da ya karanta
takarda ya fahimci sakon da ke ciki, sai ya nade
ta kamar yadda aka kawo masa ita, ya saka a
cikin aljihun rigarsa. Zuciyarsa ta cika fal da
fushi. Ya la'anci mata, ya la'anci halayensu na
cin amana da yawan sha'awa. Saboda tsananin
fushi sai ya rika ganin tsohuwar kuyangar nan da
ta kawo masa takarda kamar ita ce Badura, nan
take ya sa takobi ya cire kan ta. Ya zauna yana
ciccika shi kadai kamar kwado.
Ya tashi ya shiga gida wurin mahaifiyarsa
Hayatunnufusi. Ya same ta kwance kamar wadda
babu laka a jikinta, saboda zulumin abin da ya
faru tsakaninta da Amjadu. Ya kwashe abin da ya
faru ya fada mata, daga nan ya yi tir da halin
mata, ya fita ya nufi wurin dan uwansa Amjadu.

Ya fada masa abin da ya faru tsakaninsa da
mahaifiyarsa Badura, ya kara da cewa, "Wallahi
ba don gudun bacin ranka ba, da na je na sare
kanta bisa wannan laifi da ta aikata." Amjadu ya
amsa masa, "ya dan uwana, na rantse da Allah
abin da ya faru gare ka, shi ne ya faru gare ni
tare da mahaifiyarka Hayatunnufusi. Wallahi ba
don kai ba, da tun jiya na sare kan ta." Ya
kwashe labarin abin da ta rubuta masa duka, ya fada wa Asadu.
Suka kwana a cikin wannan dare cikin damuwa
da bakin cikin abin da iyayensu suka aikata, suka
kasance suna Allah wadai da halin mata. Suka
yanke shawarar su bar maganar a tsakanin su,
su rufa wa matan nan asiri. Domin idan
mahaifinsu ya dawo ya sami labarin abin da suka
aikata zai iya kashe su don fushi.

Washe gari Sarki ya dawo daga farauta, bayan ya
zauna fada na dan wani lokaci, ya sallami
askarawa da suka tafi farauta tare. Ya tashi ya
shiga cikin gida wurin matansa. Ya tarar da su a
kwance, kowace kamar kazar da kwai ya mace
wa a ciki. Sun riga sun kiste makircin da za su yi
wa yaran nan gun Sarki, domin suna jin tsoron
kada yaran su riga su ga Sarki, asirinsu ya tonu.
Yayin da Kamaruzzaman ya gan su haka sakaka,
sai ya tambaye su abin da ke damun su. Suka
tashi da hanzari suka riki hannunsa suna
sumbata, suka ce, "ya Sarki, ka sani cewa albasa
ba ta yi halin ruwa ba. Domin kuwa 'ya'yan da ka
rena da hannunka, suka kuma tashi a cikin
arzikinka, su ne suka karya wa matanka irli."

Da Kamaruzzaman ya ji haka sai annurin fuskarsa ya gushe, nan take ya cika da fushi ba
tare da ya tsaya yin tunani ba. Ya dubi matansa
ya ce, "ku fada mini dukan abin da ya faru bayan
tafiya ta." Badura ta tausasa murya, ta langabe
kai ta ce, "ya Sarki mai adalci, ka sani cewa
danka Asadu ya ci zarafina fiye da kima, ya keta
mini mutunci. Tun kwanakin baya yake ta aiko
mini da wasiku da kuma sakonni wai yana so na.
Wai shi duk duniya babu macen da yake so ya
kwana tare da ita sai ni. Ni kuwa na hane shi da
haka, na yi masa fada, amma bai bari ba. Rannan
da ya ga ka fita farauta, sai ya je ya sha giya ya
yi tatil, ya dauko takobi ya zo wurina. Ya ce lalle
yau sai ya biya bukatarsa gare ni, ko dai in yarda
da lalama ko kuma ya yi mini da karfi. Da
bawana ya ji haka sai ya taso domin ya kare ni
daga gare shi, amma sai ya sa takobin nan ya
dauke kansa. Ni kuwa da na ga babu dama, tilas
na yarda ya aikata dukan abin da yake so gare
ni." Tana gama fadin haka sai ta fashe da kuka,
ta ci gaba da cewa, "ya zama wajibi a gare ka,
ya Sarki mai adalci, ka kwato mini hakkina a
kansa, a yi masa hukunci mai tsanani bisa
wannan mummunan laifi da ya aikata gare ni.
Kuma Wallahi idan ba a hukunta shi ba, to, ni zan
kashe kaina in

1 Comments On HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHRUZZAMAN
avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Wanne darasi kuka ?aru da shi daga cikin wannan hikayar,

Please Login or Register in order to submit comment