Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata. Idan kuwa zalunci ne a kaina,
to, ka gaggauta yi mini sakayya a kan duk wanda
ya zalunce ni. Kai ne mai iko a kan kome da
kowa."
Yayin da kuyanga ta ji haka, sai ta saukar masa
da bugu mai tsanani sai da ya suma. Ta kawo
'yar gurasa da dan tarfen ruwa ta ajiye masa. Ta
sa kai ta fita, ta bar shi nan kwance cikin sarka, a some cikin jini. Ya nesanta da masoyansa da
dan uwansa..
Bayan ya farka, ya yi kuka, kuka
mai tsanani. Ya wake wadannan baitoci:Ya zamani ka saukaka, ka jinkirta.

Domin kwa mun tanadi jin dadi a cikina
Muna maraita, muna jijjibi da masoya.
Tsawonka bai tabbatar mu bisa haka
Ka zam azurta mai dufunnan zuciya
Domin kewar rabuwa da masoya cikinka
Magabta dukansu da ayyukansu bata ne
Mai hakuri sannu zuciyarsa za ta samu waraka.
Bege da kadaici ne ya wanzar da wani abu
Ban samu jin dadi ba ko kadan da waraka
Daga bakin cikin rabuwa da abin ganina ba.
An jarrabe ni da shiga kurkuku da halaka
Bai kasance a gare ni mai debe kewa ba.
Face ruhina da idona na korar makiyanka
Wanda yake mataimakin al'amarina.
Zurfin begena, wuta tasa ba ta bicewa haka.
Da bakin ciki da tunani suna hura ta kwarai
Tana haskaka da hurawarsu ga cutuka
Ni na tabbata cikin bakin ciki na dulmiya
Tsawon darena a cikin azaba na habaka.
Cewa ni, ana kona ni da wutar bakin ciki
Mai huruwa, ga kwarkwata sun samu cimaka
Dangin shan giya a hannun mai begenta
Ya yiwo jijjibi jiki ya rame a dalilin cutuka.
Maraya ba shi da wani mai taimakonsa
Ga ni a cikin kurkuku a cikin wuya uku
In wayi gari a cikin daurewar hannu da kafa
Bakin ciki yana ramar da ni yana son halaka
Yayin da ya gama wannan waka, ya ci gaba da
kuka yana shekar da hawaye. Ya kasance a cikin
wannan gida, kuwwarka banza. Al'amarinsa ke
nan.
Amma Amjadu kuwa, ya yi jiran Asadu a bayan
gari har rana ta take ta sunkuya bai dawo ba.
Gabansa ya fadi, idanunsa suka yi kwal kwal
suka cika da kwalla.

Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ ke tare daku32 HIKAYAR SARKI KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHARUZZAMAN

Amjadu kuwa ya yi ta jiran Asadu a bayan gari
har rana ta take ta sunkuya bai dawo ba.
Gabansa ya fadi, idanunsa suka yi kwal kwal
suka cika da kwalla. Ya ce, "kaico dan uwana,
kaico abokin tafiyata. Ya bakin cikina, ya bakin
cikin rabuwarmu." Daga nan ya gangaro daga
kan tsauni, hawaye na zuba daga idanunsa, ya
shiga cikin birni ya yi nufin zuwa kasuwa. Ya
tambayi mutane sunan wannan birni. Suka gaya
masa cewa, sunansa Birnin Matsafa, mafi
yawancin jama'arsa suna bautar wuta ne, amma
akwai Musulmi 'yan kadan. Ya tambaye su
labarin Birnin Labunus. Suka ce masa, Birnin
Labunus na Sarki Armanus ko? Ai daga nan zuwa
can tafiyar shekara wata uku ce a kasa, ba
magama ba cin zango. Ko kuma tafiyar wata a
jirgin ruwa. Amma yanzu mun ji an ce wani
surukinsa ne, mai suna Kamaruzzaman, wanda
yake auren 'yarsa Hayatunnufusi, ke mulkin birnin
bisa adalci da tausayin talakawa.
Yayin da Amjadu ya ji an ambaci sunan
mahaifinsa, sai ya yi ajiyar zuciya, bakin cikinsa
ya karu. Ya rasa inda zai nufa, ya sayi abinci ya
dauka ya nufi wani sako inda ya lura babu
mutane da yawa a wurin. Ya zauna domin ya ci
abinci, amma da ya tuna da dan uwansa Asadu
sai ya kasa ci. Haka dai ya daure ya yanki loma
daya ya ci, ya sha ruwa domin ya dan ji nauyi-
nauyi ga cikinsa. Ya tashi ya fara zagaya birnin
yana neman dan uwansa, har ya iso ga rumfar
wani madinki. Da Amjadu ya lura da madinkin
nan, kuma ya ga hasken musulci a fuskarsa, sai
ya yi masa sallama. Madinki ya mayar masa da
sallama. Ya shiga ya zauna a cikin rumfa, ya
kwashe labarinsa duka ya fada wa madinki.
Madinki ya ce, "ayya dan samari, ai kuwa idan
dan uwan nan naka ya fada hannun wani matsafi,
to, kai da ka kara ganinsa sai a darussalam.
Amma kuma Allah buwayi ne gagara misali, ko
da ya fada a hannun matsafi ne, sai ya kubutar
da shi ku sake haduwa da juna." Suka yi jim na
dan wani lokaci. Madinki ya tambaye shi, "ko za
ka yarda ka zauna a wurina?" Amjadu ya amsa,
"na'am." Madinki ya yi farin ciki da haka.
Amjadu ya zauna a wurin madinki tsawon
kwanaki. Madinki ya rika kwantar masa da
hankali yana koya masa dinki har ya gwanance.
Wata rana Amjadu ya tafi bakin teku ya yi wanka,
ya wanke tufafinsa suka yi fes. Da ya gama sai ya shiga cikin birni domin ya bude ido, ya kuma
duba ko Allah ya sa ya ga dan uwansa. Ya rika
bi kwararo-kwararo, sako-sako yana yawo. Yana
cikin zagaya birni, ya karya wata kwana sai ya yi kicibis wata mace kyakkyawar gaske, mai
kwarjini da haiba. Yayin da suka hadu kusa da
kusa, sai matar nan ta yaye mayafin da ya rufe fuskarta, ta kyabci Amjadu da idanunta ta
kwararo masa wani murmushi mai dauke hankali.

Sai kuma ta rera wannan waka:
Da na gane ka, ka gabato sai ganina ya rufe
Ka ce kai ka rufu da idon rana.
Cewa kai, kai ne mafi kyawo a cikin kyawawa.
Kai ne namiji mafi kyawo daga cikin mazan
wannan zamani.
Da a ce a wannan zamani namu.
An raba kyawo gida biyar ne
Da kai ne ka kwashe kashi hudu
Sauran halittu kashi daya. Raina fansa ne a gare ka.
Yayin da ya ga wannan mata da irin kyawonta, ya kuma ji wakarta, nan take sai ya ji zuciyarsa ta tafi gare ta. Son ta ya damki ruhinsa, bai san lokacin da ya kyabce ta da ido ba, sa'annan ya rera wannan waka:
Maganar kundukuki ta baci da kayar tsidau ga
wannan abin zantawa.
Ransa manesanci ne ga haka, kada ki mika
hannuwa zuwa gare shi.
Ya tsawaita da aikata wannan al'amari.
Gamuwarmu ta tsaya ga idanuwa.
Gaya wa wannan da ta zalunce ni
Wadda ta kasance fitina a gare ni.
Da dai ta yi adalci, ta saukaka ga fusaka wadda
ta duhunta.
Hakarkarinsa ya konu da wutar bege.
Da ta ji wakarsa sai ta yi ajiyar zuciya. Ta kuma
rera wadannan baitoci:
Kai ne wanda ya shiga tafarki ba ni ce ba.
Kai ne ka samar da saduwa, ko da cikawa ta
kasance gare ni.
Ya wanda asubahinta ke kecewa daga lu'ulu'un
kyawonsa
Mai saka dare yana kawaita yayin tashinka.
Ya kasance babu makawa ga saye na, ka karbi
biya.
Bayan ta gama waka sai Amjadu ya tambaye ta,
"zan bi ki ne na ga gidanki, ko za ki tare da ni kind
ga gidana?" Ta langabe kanta gefe guda, ta amsa
masa da fadar Ubangiji madaukaki, "maza sune
tsaye a kan mata. Allah ya daukaka sashensu
fiye da sashe." Da Amjadu ya ji haka, sai ya
fahimci jawabinta.
ya fahimci tana so ta bi
shi ne. Sai ya fara tunanin inda zai kai ta, domin
yana jin kunyar mai gidansa, madinki. Ba zai yiwu
ba ya dauki mace ya je masa da ita. Don haka
sai ya ci gaba da tafiya hanyar da ya dosa, ita
kuwa ta bi shi a baya. Suka yi ta ragaita, daga
wannan kwararo zuwa wancan, daga wannan
lungu zuwa wancan, har dai ta gaji ta tambaye
shi, "ya masoyina, shin ina gidan naka yake?" Ya
amsa mata, "kara hakuri dai, mun kusa isa."
Daga nan sai ya karya kwana ya shiga wani
lungu wanda gidajensa duka masu kyau ne,
matar nan kuwa ta take masa baya suka ci gaba
da tafiya. To, ashe wannan lungu ba shi bullewa
ko'ina sai a gaban wani gida. Da suka iso
karshen lungun, Amjadu ya gan su a gaban
wannan gida, sai ya ce a cikin ransa, "babu tsimi
babu dabara, face daga Allah madaukakin Sarki."
Ya ga gidan yana da babbar kofa ta karfe, wadda
take kulle. Akwai kuma dakali guda biyu na
zama, wadanda aka gina da duwatsu, daya a
kowane gefe na kofar gidan.
Ya zauna bisa dakali daya, ita ma ta zauna bisa
daya dakalin suna fuskantar juna. "Ya masoyina,
to, me muke jira?" Ta tambaye shi. "Ka bude
gidan mu shiga daga ciki mana." Amjadu ya
sunkuyar da kansa kasa yana tunanin karyar da
zai yi mata. Can sai ya dago kansa ya ce, "ina
jiran yarona ne, wanda na ba makullin gidan,
domin ya zo ya shirya mini abinci da abin sha,
kafin in komo daga bakin teku, wajen shan iska."
Sa'annan ya ce a cikin ransa, "idan ta gaji da jira
ai dole ta kama gaban ta."

Da suka kara jimawa a zaune sai matar ta ce,
"ya masoyina, wannan yaro naka ya dade bai zo
ba. Bai kamata mu yi ta zama a nan bisa hanya
ba." Ta dauki dutse ta nufi wurin kofa. Amjadu
ya ce, "ki kara hakuri, yana nan tafe yanzu."
Kafin ya rufe bakinsa tuni ta balle makulllin kofar
da dutse, ta bude ta shiga. Amjadu ya tsorata ya
ce da ita, don me za ki aikata haka? Ta ce masa,
ina laifi don mutum ya balle kofar gidansa. Ba ta
ko jira ta ji amsarsa ba, sai ta kutsa kai cikin
gidan. Amjadu ya tsaya a bakin kofa yana
shawarwarin abin da zai yi. Shin ya gudu ne ya
bar ta, ko kuwa ya bi ta cikin gidan, kome ta
fanjama, fanjam.
Bai san lokacin da ta zo ta kama hannunsa ba,
ta ja shi suka shiga cikin gidan tana cewa, "haba
hasken idona, farin cikin zuciyata, me kake
tunani ne ka ki shigowa?" Ya amsa mata, "zan
shigo. Ina tunani ne, ko yaron nan ya shirya
gidan kamar yadda na umurce shi, ko kuwa yana
can wajen shiriritar sa?" Ya bi ta suka shiga ciki,
zuciyarsa cike da tsoron abin da zai faru idan
mai gidan nan ya iske su.
Da suka wuce zaure, suka shiga cikin gidan, sai
Amjadu ya ga an shirya shi tsaf, an kawata shi
kwarai da kayan alatu iri-iri. Tsakiyar gidan yana
da fadi da yalwa. Akwai wani dan tabki da aka
gina a tsakiyar gidan cike da ruwa. A tsakiyar
tabkin ga wani dan siririn bututu na karfe yana ta
feso ruwa daga bakinsa, idan ruwa ya fita ya yi
sama, sai ya baje ya dawo cikin dan tabkin
kamar ruwan sama. Kewayen dan tabkin kuma
duk ciyawa ce tsanwa shar, ta yi furanni masu
launi kala-kala, gwanin ban sha'awa. Sauran filin
gidan kuma duk an dabe shi da farin dutse. Daga
can gefe kuma an yi wata rumfa, an shimfide
kasanta da wadansu kilisai na alfarma. A cikin
rumfar an jera abubuwan zama da gadaje. Ga
kuma wani dan gado na alfarma mai kama da
teburi, bisa gare shi an shirya tasoshi na zinariya
da azurfa, da kuma akussa, dukkansu rufe da
mayani. Ga kuma battoci na giya an jera. A
tsakiyar gadon mai kama da teburi an saka wani
fure mai daukar hankali a cikin wani dan kasko,
an kuma ajiye fitila daga gefe daya.
Yayin da Amjadu ya ga wannan irin tsari da aka
yi wa cikin gidan nan, sai hankalinsa ya tashi, ya
tabbata wannan gida na wani mai sukuni ne, ko
kuma mai sarauta. Ya ce a cikin ransa, "daga
Allah muka fito kuma gare shi za mu koma."
Amma ita kuwa matar nan da ta ga yadda aka
tsara gidan sai ta cika da farin ciki, ta ce,
"wallahi ya kai masoyina, yaronka ya cika
umurninka. Dubi yadda ya share gidan tas, ya
dafa abinci ya shirya bisa teburi." Ta matsa cikin
rumfar nan, ta bude mayanin akushi daya, sai ta
ga naman dakwalen kaji soyayye sai wani nash,
sh yake yi a cikin mai. Ta jawo abin zama ta
zauna tana cewa, wallahi na zo a cikin lokacin da
ya dace.
Amjadu dai yana tsaye bai kula ta ba, yana ta
tunanin abin da zai faru idan mai gidan nan ya
same su. Da matar ta ga ya yi tsaye, sai ta taso
ta zo wurinsa, ta ce, "m yake damunka, ya
masoyina?" Ta yi ajiyar zuciya, ta rungume shi ta
sumbace shi. Sa'annan ta ce, "ko dai akwai wata
wadda ka shirya wa wannan liyafa, na zo na bata
muku shiri? A shirye nake in sha damara, idan ta
zo, in yi muku dukan aikace-
aikacen da za ku sa ni. " Amjadu ya yi dariya,
wadda ba ta kai ciki ba, ya je ya zauna bisa abin
zama, gabansa na dar-dar, yana tunani, "ya ya
zan kubuta daga mai gidan nan idan ya riske
mu?" Ita ma ta zauna tana cike da fara'a da
annashuwa, babu abin da yake damunta. Amjadu
kuwa ya tsunduma cikin tunani barkatai.
Ta jawo akushin nan wanda yake cike da
soyayyen naman kaji ta ajiye shi a tsakaninsu, ta
bude shi ta fara ci. Ta dubi Amjadu ta ce, "ka ci
abinci ya masoyina." Ya sa hannunsa ya yagi
naman ya kai bakinsa, maimakon ya ji dadi sai
ya ji shi da daci saboda tashin hankali. Ya mayar
da hankalinsa ga kofar shigowa gidan, matar
kuwa ba ta kula ba. Ta yi ta hadiyar gara sai da
ta ji ta kai masabar gatari. Daga nan ta jawo
wani akushi cike da 'ya'yan itace, ta ci har ya
ishe ta. Ta koma wajen giya, ta balle bakin batta
daya, ta bulbula giya har ta cika kasko, ta mika
wa Amjadu ita. Ta ce masa, "karbi wannan ka
sha, za ta gusar maka da duk wata damuwa da
kake ciki." Ya karbi kasko ya kurba, yana cewa a
cikin ransa, "ko yaya zan kwashe da maigidan
nan, babu makawa zai kashe ni ne." Ya ci gaba
da kurbar giya ba tare da ya dauke idanunsa
daga kallon kofar gidan ba.
Suna cikin haka sai Amjadu ya ji tafiyar mutum,
taf, taf, taf, a cikin zaure zai shigo cikin gidan.
Nan da nan ya mike da hanzari ya nufi zaure
domin ya tari mai shigowa.

Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ ke muku barka da shan ruwa33 HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHARUZZAMAN

Suna cikin haka sai Amjadu ya ji tafiyar mutum,
taf, taf, taf, a cikin zaure zai shigo cikin gidan.
Nan da nan ya mike da hanzari ya nufi zaure
domin ya tari mai shigowa. Matar ta tambaye shi
ina za shi? Ya ce mata ya ji ana sallama ne a
waje zai je ya dubo. Ya tafi babu ko takalmi a
kafarsa. Ashe mai gidan ne tafe, shi ne kuwa
Sarkin Fadan garin. Ya gina wannan gida ne
domin shan iska a duk lokacin da ya bukata.
Yanzu ma ya sa an shirya masa kayan liyafa ne,
domin zai zo shan iska da maraice, shi ne ya zo
ya duba ya ga ko an shirya kome yadda yake so.
Ga mamakinsa sai ya ga kofar gidan a balle.
Allah kuwa ya yi Sarkin Fadan nan mutumin kirki
ne mai son kyautatawa talakawa, ga shi da saukin kai kamar ruwa.

Amjadu ya hadu da
Sarkin Fada a cikin zaure, ya yi sauri ya durkusa
ya gaishe shi. Sa'annan ya ce, "kafin ka hukunta
ni bisa laifin da na aikata maka bari in ba ka
labarina tukuna." Ya kwashe labarinsa, tun daga
fitowarsu daga birninsu, shi da dan uwansa
Asadu, har zuwa haduwarsa da matar da ke cikin
gidan da yadda ta balle kofar suka shiga ciki, duk
ya fada wa Sarkin Fada.
Yayin da Sarkin Fada ya ji labarinsa, ya ji cewa
ashe ma dan Sarki ne, sai tausayinsa ya kama
shi. Ya riki hannunsa ya ce, "Ya Amjadu, saurari
abin da zan umurce ka da shi. Idan ka aikata shi,
ka tsira daga abin da kake tsoro. Idan kuwa ka
bijire masa, babu makawa in halaka ka."
Amjadu ya ce, "umartan ni, Allah ya ba ka
nasara."
Sarkin Fada ya ce, "da farko dai sunana
Bahadaru. Yanzu ka koma wurin matar nan ku ci
gaba da liyafarku, kuma ka kwantar da
hankalinka. Zan shigo muku a matsayin yaronka,
mai yi maka aikace-aikace. Da zarar na shigo ina
so ka rufe ni da fada, kana tambaya ta ina na tafi
na bar ku kuna jiran makullin gida. Ka sami
bulala ka buge ni da ita, sa'annan ka rika saka ni
'yan aikace-aikace. Idan ba ka aikata haka gare
ni ba, babu makawa in kashe ka. Kuma na yi
maka wannan kyautatawar ne domin
kasancewarka bako, ni kuwa ina matukar
karrama baki. Ku yi dukan abin da kuke so a cikin wannan gida har gari ya waye, daga nan
kowa ya kama gabansa."
Sarkin Fada ya umurci Amjadu ya koma cikin
gida. Amjadu ya sumbaci hannunsa, ya yi masa
godiya sa'annan ya koma wurin matar nan,
fuskarsa tana haske, ya jefe ta da murmushi ya
ce, "ya masoyiyita, hakika wannan gida ya
haskaka da zuwanki. Madalla da wannan ziyara
taki mai albarka."
Matar ta cika da mamaki, ta ce, "hakika, yanzu
ne ka yi maraba da zuwa na, amma da farko ai
kamar ba ka yi farin ciki da zuwana ba, duk ka bi
ka bata fuska. Amma menene dalilin
canzawarka?"
Amjadu ya ce, "na rantse da Allah, na yi zaton
yarona Bahadaru ya sace mini wasu sarkoki ne,
wadanda kudinsu ya kai dinari dubu goma, ya
gudu. Amma da na duba da kyau sai na gan su a
wurin da na ajiye su. Ko’ina ya tafi ne, ya dade
haka bai dawo ba? Ga shi ya sa mun balle kofar
gida. Babu makawa in hukunta shi bisa wannan
laifi da ya yi."
Ta yarda da uzurinsa. Suka ci gaba da ci da sha,
suna annashuwa har rana ta kusa faduwa. Daga
nan sai ga Sarkin Fada ya shigo musu, ya canza
tufafinsa ya sanyo irin na yaran gida. Ya yi
damara da wani kyalle, ya sa wasu tsofaffin
takalmi. Da zuwansa sai ya fadi kasa ya yi
gaisuwa, sa'annan ya mike tsaye ya harde
hannuwansa a bayansa, ya sunkuyar da kansa
kasa, alamar ya yi laifi. Amjadu ya dube shi ya
watsar. Can ya kara duban sa, fuskarsa a
turbune, ya daka masa tsawa, "me ya dakatar da kai zuwa wannan lokaci,
sakaran yaro!"
Sarkin Fada ya fara yan kame-kame, ya ce, "ya
shugabana, wallahi na tafi bakin teku ne domin in
wanke tufafina. Ban san da rana za ka zo nan
ba, na aza sai cikin dare."
"Ka yi karya!" Amjadu ya daka masa tsawa.
"babu makawa in hukunta ka bisa wannan laifi da
ka yi." Ya dauko bulala, ya umurci Sarkin Fada
ya kwanta. Ya yi ta tsala masa bulala. Matar nan
ta tashi da fushi ta karbe bulalar daga hannun
Amjadu, ta yi ta dukan Sarkin Fada da bulalar
nan iyakar karfinta. Sarkin Fada ya yi ta hargowa
yana cije hakori don zafin bulala, har sai da ya
fitar da hawaye.
Da Amjadu ya ga abin nata na nema ya wuce
minsharri, sai ya kwace bulalar daga hannunta
yana cewa, rabu da shi haka nan. Ita kuma tana
cewa, ka bari a kara masa, don kada gobe ya
sake aikata kuskure irin wannan. Amjadu bai
saurare ta ba. Shi kuwa Sarkin Fada, Bahadaru,
sai ya mike yana matse hawaye daga idanunsa,
ya koma gefe guda ya takure yana jiran ya ji
umurnin da za a ba shi. Ya tashi ya share dukan
gidan, ya kunna shama'u, ya shirya musu
shimfidar da za su kwanta. Duk kai-da-kawon da
Bahadaru ke yi, babu abin da matar nan ke yi sai
faman yi masa tsawa da zagi, ta uwa ta uba.
Amjadu ya kufula, ya yi mata tsawa ya ce, "ki
rabu da shi haka mana, bai saba da irin wannan fada da kike yi masa ba."

Haka dai su Amjadu suka ci gaba da kwasar
liyafa har dare ya tsala, Bahadaru kuma ya koma
gefe ya makure, nan da nan barci ya kwashe shi
saboda dawainiyar da ya sha, ga kuma zafin
bulala. Bai jima ba cikin barcin sai ya fara jan
rago. Da matar nan ta ji ya fara jan rago, ga shi
kuma ta bugu da giya, sai ta ce da Amjadu lalle
sai ya dauki takobi ya sare kan Bahadaru, ko
kuma ita tashi ta kashe shi da hannunta, domin
ita dai ta tsane shi.
Amjadu ya tambaye ta don me za ta kashe masa
yaro? Ta ce, muddin yana cikin gidan nan ba za
ta iya kwana cikinsa ba. Ta tashi ta dauki takobi
tana cewa, "idan kai ba za ka iya kashe shi ba,
bari ni in kashe shi." Da Amjadu ya ga dai da
gaske take yi, ya tuna irin halascin da Bahadaru
ya yi masa, sai ya karbe takobin daga hannunta,
ya ce, "babu wanda ya kamata ya kashe mini
yaro face ni."
Da ya amshi takobin daga hannunta, kafin ta
farga sai ya dauke kan ta da shi. Kan ya yi tsalle
sama ya fada ga jikin Bahadaru da ke barci,
gangar jikin kuma ta fadi can gefe guda. Nan
take Bahadaru ya farka, ya tashi zaune. Ya ga
Amjadu tsaye kusa gare shi, yana rike da takobi,
wadda jini ke diga daga jikin sa. Ya duba haka,
sai ya ga gawar mace. Ya tambayi Amjadu abin
da ya faru. Ya fada masa kome, ya kara da
cewa, "babu abin da ta so kamar ta kashe ka,
wannan shi ne sakamakonta."
Bahadaru ya mike tsaye ya sumbaci hannun
Amjadu ya ce, "kash, ai da ka yi mata afuwa.
Amma tunda abin ya zamo haka, sai mu yi kokari
mu rabu da gawarta kafin gari ya waye." Ya
shiga wani daki ya dauko tabarma ya nade
gawar, ya samo katon kwando mai murfi ya saka
ta ciki, ya mayar da murfin ya rufe. Ya ce da
Amjadu, "ka ga kai bako ne, ba ka san ko'ina ba
a cikin wannan birni. Ka zauna cikin wannan gida
ka jira dawowa ta, zan tafi da wannan gawa in
jefa ta cikin teku. Idan na dawo zan kyautata
maka matukar kyautatawa, zan taimake ka wajen
bidar dan uwanka da ya bace. Idan kuma rana ta
yi ban dawo ba, to, watakila ni tawa ta kare. Ka
zauni wannan gida da dukan abin da ke cikinsa
na dukiya, na mallaka maka su." Yana gama
fadin haka sai ya saba kwandon nan bisa
kafadarsa ya fita, ya dauki hanyar zuwa bakin teku.

Yayin da ya isa bakin teku sai ya gamu da 'yan
doka suna sintiri. Da shugabansu ya gan shi sai
ya shaida shi, ya yi mamakin abin da ya kawo
shi bakin ruwa, cikin wannan tsohon dare, dauke
da kaya niki-niki. Shugaban 'yan doka ya bukaci
ya ga abin da ya dauko, sai Bahadaru ya fara
'yan noke-noke. Da suka ga dai alamar ba ya da
gaskiya sai suka kwace kwando daga hannunsa,
suna budewa sai suka ga matacciyar mace
nannade a cikin tabarma. Nan take suka buga masa sarka ga hannunuwa suka tafi da shi suka kulle. Da gari ya waye suka yi kwashe shi tare da kwandonsa sai gidan Sarki, suka fada wa Sarki abin da ya faru.
Sarki ya husata da jin wannan abu, ya dubi Bahadaru ya daka masa tsawa, "Allah
wadaranka, ashe dai kai barawo ne, mai kashe
mutane yana kwashe musu dukiya. Mutum nawa
ka kashe a cikin wannan birni?"

Bahadaru ya dukar da kansa kasa bai ce kome
ba. Sarki ya kara daka masa tsawa, "wa ya
kashe wannan mace?"

Ya amsa, "ni na kashe ta, Allah ya ba ka nasara.
Babu tsimi babu dabara face daga Allah madaukakin Sarki." Sarki ya kara husata don jin wannan amsa tasa, nan take ya ba da umurni a
tsire shi. Dogarawa suka cafe shi, suka yi waje
da shi domin zagayawa da shi a cikin gari kafin a
kai shi wurin da za a tsire shi kamar yadda Sarki
ya yi umurni. Mai shela ya tafi tare da su cikin
birni, kwararo-kwararo, lungu-lungu, yana sanar
da jama'a cewa duk mai son ganin yadda za a
tsire Bahadaru Sarkin Fada, to, ya hallara kofar
fada.
Amjadu kuwa ya zauna a cikin gida yana jiran
dawowar Bahadaru, har gari ya waye rana ta fito,
bai dawo ba. Ganin haka sai Amjadu ya ce, "babu
tsimi babu dabara face daga Allah mai girma da
daukaka. Yalla ko wani abu ya faru gare shi."
Yana nan yana jimamin abin a cikin ransa, sai ya
ji mai shela yana shelar za a tsire shi a kofar
gidan Sarki da tsakiyar wannan rana. Yana jin
wannan shela sai hankalinsa ya tashi tausayin sa
ya kama shi har ya zubar da hawaye. Ya ce a
cikin ransa, "wannan mutum da tawakkali yake,
shi ya yarda ya amsa laifin da ba shi ne ya
aikata ba domin kawai ya kubutar da ni daga
halaka. Na rantse da Allah ba zan bari a kashe
shi ba bisa laifin da ba shi ne ya aikata ba."
Nan take ya zabura ya rufe gida, ya bi bayan mai
shela har ya cim masu. Yayin da ya same su sai
ya ce da Sarkin Dogarai, "ranka ya dade kada ku
kashe wannan mutum, domin ba shi ne ya kashe
matar ba. Ni ya kamata ku kashe'.

Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ ke tare daku a awannan lokaci34 HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHARUZZAMAN

Amjadu kuwa ya zauna a cikin gida yana jiran
dawowar Bahadaru, har gari ya waye rana ta fito,
bai dawo ba. Ganin haka sai Amjadu ya ce, "babu
tsimi babu dabara face daga Allah mai girma da
daukaka. Yalla ko wani abu ya faru gare shi."
Yana nan yana jimamin abin a cikin ransa, sai ya
ji mai shela yana shelar za a tsire shi a kofar
gidan Sarki da tsakiyar wannan rana. Yana jin
wannan shela sai hankalinsa ya tashi tausayin sa
ya kama shi har ya zubar da hawaye. Ya ce a
cikin ransa, "wannan mutum da tawakkali yake,
shi ya yarda ya amsa laifin da ba shi ne ya
aikata ba domin kawai ya kubutar da ni daga
halaka. Na rantse da Allah ba zan bari a kashe
shi ba bisa laifin da ba shi ne ya aikata ba."
Nan take ya zabura ya rufe gida, ya bi bayan mai
shela har ya cim masu. Yayin da ya same su sai
ya ce da Sarkin Dogarai, "ranka ya dade kada ku
kashe wannan mutum, domin ba shi ne ya kashe
matar ba. Ni ya kamata ku kashe,

domin kuwa na rantse da
Allah ni ne wanda ya kashe ta." Da Sarkin
Dogarai ya ji haka sai mamaki ya kama shi, ya
kwashe su gaba daya suka koma wurin Sarki. Ya
fada wa Sarki abin da Amjadu ya ce.
Sarki ya juya wurin Amjadu ya tambaye shi, "kai
ne ka kashe yarinya?"
Amjadu ya amsa, "na'am, ya Sarki."
Sarki ya kuma tambayarsa, "me ya sa ka kashe
ta? Maza gaya mini, kuma kada ka zanta mini
face gaskiya."
Amjadu ya ce, "Allah ya ba ka nasara, hakika
labarina abin mamaki ne, wanda da za a rubuta
shi da tsinin

1 Comments On HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHRUZZAMAN
avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Wanne darasi kuka ?aru da shi daga cikin wannan hikayar,

Please Login or Register in order to submit comment