Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

juya hagu, amma
bai ga yarinyar nan da take kwance kusa gare shi
ba. Sai ya ce a cikin ransa, "Wannan wane irin
wasa da hankali ne mahaifina ke yi mini? Don me
tun kafin na farka daga [ http://fb.com/
waziriaku ] barci za a zo a dauke yarinyar da aka
kawo nan domin ta taya ni barci? Ba a ko bari
gari ya waye in tambayi sunanta, mu yi zance da
juna? Watau so ake yi sai na matsu na furta da
bakina cewa ina sonta. To, wallahi ina sonta, bari
yanzu in aiki bawan nan ya tafi ya sanar da
mahaifina."
Kamaruzzaman ya kwalla wa bawan nan kira da
karfi, "Ya kai wannan rafkananne!" Bawa ya farka
daga barci a firgice yana mutsuttsuke idanunsa
da hannuwansa. Ya yi sauri ya debo ruwa ya
kawo gaban [ http://fb.com/waziriaku ]
Kamaruzzaman, ya durkusa ya mika masa.

Kamaruzzaman ya dauki ruwa ya shiga bandakin
da ke cikin dakinsa. Ya biya bukatarsa, sa'annan
ya yi alwala. Ya fito daga bandaki, ya yi sallar
asuba. Bayan ya sallame sallah ya karanta
sunayen Allah tsarkaka dari ba daya. Ya yi
addu'o'in da zai yi, ya shafa fatiha. Ya dubi inda
bawa yake tsaye a bakin kofa yana gadinsa, ya
ce masa, "Ya Sawab, shin wace [ http://fb.com/
waziriaku ] yarinya ce Sarki ya sa ta kwana
wurina a daren jiya, kuma wa ya zo ya dauke ta
da ina barci?"
"Wace yarinya kake zance, ya shugabana?" Bawa
ya tambaya cikin mamaki.
"Yarinyar da ta kwana bisa shifidata mana. Kada
ka yi mini wasa." Kamaruzzaman ya daka masa
tsawa. [ http://fb.com/waziriaku ]
Bawa ya tsorata, ya ce, "Ya shugabana, na
rantse da Allah babu yarinyar da ta shigo wannan
gida, balle ta shiga nan dakin har ta kwana bisa
shimfidarka. Yaya ma za a yi na bari [ http://
fb.com/waziriaku ] wani mahaluki ya shigo inda
kake idan ba Sarki ne ya aiko shi ba."
+ + +

Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar
labarun DARE DUBU DA DAYA, wanda yanzu haka na kasuwa...

whatsapp only
08032767547(9) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI
SHAHARUZZAMAN

Bawa ya tsorata, ya ce, "Ya shugabana, na
rantse da Allah [ http://fb.com/waziriaku ]babu
yarinyar da ta shigo wannan gida, balle ta shiga
nan dakin har ta kwana bisa shimfidarka. Yaya
ma za a yi na bari wani mahaluki ya shigo inda
kake idan ba Sarki ne ya aiko shi ba?" [ http://
fb.com/waziriaku ]
"Karya kake yi, munafukin banza. Watau har da
kai za a hada baki a yi wasa da hankalina ko?"
Kamaruzzaman ya daka masa tsawa. [ http://
fb.com/waziriaku ] "To, ko dai ka fada mini
gaskiya, ko kuma ka yaba wa aya zakinta!"
Bawa ya rude, ya duka gaban [ http://fb.com/
waziriaku ] Kamaruzzaman yana rantse-rantse,
yana cewa shi bai san da maganar wata yarinya
ba. Maimakon rantse-rantsen nasa su sa
Kamaruzzaman ya sauko, sai suka kara tunzura
shi. Ya ce masa, "Ya kai la'annanen bawa, wato
kai ma an koyar da kai yadda za a yi wasa da
hankalina ko. [ http://fb.com/waziriaku ] Matso
kusa gare ni in fada maka wata magana."
Bawa ya matsa kusa ga Kamaruzzaman, wai ya
ji abin da zai fada masa. To, Allah ya yi
Kamaruzzaman kakkarfa ne, kuma ga shi jarumi.
Sai ya sungumi bawan nan, ya yi koli-koli da shi [
http://fb.com/waziriaku ] ya kantara da kasa.
Saboda tsananin zafin kayen nan sai da bawa ya
saki tusa. Kamaruzzaman kuwa ya haye ruwan
cikinsa ya yi ta bugu, yana cewa, "Fada mini
gaskiya ko in kashe ka, ja'irin banza munafuki!"

Bai daina bugun shi ba har sai da ya suma. [
http://fb.com/waziriaku ]
Yayin da ya ga ya suma, sai ya rika jan shi a
kasa har gindin rijiyar da ke tsakiyar gidan.
Rijiyar irin mai karfen nan ce, wadda idan aka
juya karfen sai gugar sauka kasan rijiyar. [
http://fb.com/waziriaku ] Idan an debo ruwan
kuma sai a yi ta juya karfen gugar tana tahowa
sama. Da [ http://fb.com/waziriaku ]
Kamaruzzaman ya kai bawa bakin rijiya, sai ya
kwance gugar, ya daure bawa tamau da igiya
maimakon guda. Ya yi ta juya karfe bawa yana
yin kasa har sai da ya ji ya shiga cikin ruwa.
Daga nan kuma ya yi ta juya karfen, ya fito da
shi waje, ya jike sharkaf da ruwa. Lokacin kuwa
ana tsakiyar sanyin hunturu. [ http://fb.com/
waziriaku ]
Kamaruzzaman ya ci gaba da jefe bawa cikin
ruwan rijiya yana fitowa da shi har ya farfado
daga sumansa, ya fara kururuwar neman
taimako. Da Kamaruzzaman ya ji kururuwarsa,
sai ya dago shi sama, ya ce, "Wallahi ba na kyale
ka sai ka fada mini wace yarinya ce a ka kawo
ta kwana wurina, kuma wanene ya dauke ta ina
cikin barci?" [ http://fb.com/waziriaku ]
A nan asuba ta riski Shaharuzad, ta katse
zancenta mai dadin saurare.
WANNAN SHI NE KARSHEN JUZU'I NA FARKO.
JUZU'I NA BIYU
Mun fara da sunan Allah mai gamammiyar
kyauta a duniya, mai kebabben jin kai a lahira.
Yabo ya tabbata ga Allah, ubangijin talikkai. Tsira
da aminci su tabbata a kan shugabanmu, Annabi
Muhammadu, shugaban ma'aika, da alayensa da
sahabbansa [ http://fb.com/waziriaku ], da
sauran al'ummar da ta amsa kiransa.
Bayan haka, wannan shi ne farkon juzu'i na biyu
na littafin Dare Dubu Da Daya, wanda aka zanta
shi daga zantuttukan masu hankali, masana,
mabiya hanyar labarun asali. Kun fara wannan
juzu'i daga [ http://fb.com/waziriaku ] dare na
dari daya da tamanin da bakwai wanda
Shaharuzad take labarta wa Sarki Shaharumana
da 'yar uwarta Dunyazad. Ga Allah muke neman
tsari, gare shi muke dogaro ga dukkan
al'amurranmu. [ http://fb.com/waziriaku ]
A dare na dari da tamanin da bakwai,
Shaharuzad ta ce, na sami labari ya kai wannan
hamshakin Sarki, Kamaruzzaman ya ce da bawa,
"Wallahi ba na kyale ka sai ka fada mini wace
yarinya ce ta kwana wurina kuma [ http://
fb.com/waziriaku ] wa ya dauke ta lokacin da
nake barci." Yayin da bawa ya ga Kamaruzzaman
na shirin halaka shi, sai ya ce, "Ya shugana, na
san da maganar, kwance ni. Na rantse da Allah
zan fada maka kome." [ http://fb.com/waziriaku ]

Yayin nan Kamaruzzaman ya fitar da shi daga
cikin rijiya, ya kwance masa dauri. Bawa ya
zama kamar wanda ya fito daga lahira saboda
tsoro da [ http://fb.com/waziriaku ] kuma
wahalar da ya sha ta tsunduma shi cikin rijiya da
Kamaruzzaman ya yi ta yi. Tufafinsa sun yi
sharkaf da ruwa, duk jikinsa sai rawar dari yake
yi, kamar tsohon dan taurin da ya jiyo kidan
farauta. Hakoransa [ http://fb.com/waziriaku ] na
gamuwa, kaf kaf kaf, kamar tsohuwar da aka
zaro daga cikin kankara. Kansa duk ya yi molallai
har jini yana fita saboda bugun bangayen rijiya.
Da Kamaruzzaman ya gan shi cikin wannan hali
sai tausayinsa ya kama shi. [ http://fb.com/
waziriaku ]
Bayan bawa ya dan murmure, sai ya ce wa
Kamaruzzaman, "Ya shugabana, don Allah ka
bari in tube wadannan jikakkin tufafin nawa, in
shanya su ga rana. In canja wasu, kada sanyi [
http://fb.com/waziriaku ] ya halaka ni, sa'annan
in komo nan in ji dadin fada maka abin da ya faru
a cikin daren jiya, domin da ni aka shirya
kome." [ http://fb.com/waziriaku ]
Kamaruzzaman ya ce da shi, "Tafi ka yi yadda
kake so. Ka dai ga 'yar karamar azabar da na yi
maka ko? To, idan ka dawo ba ka fada mini
gaskiya ba, na rantse da Allah sai na lahira [
http://fb.com/waziriaku ] ya fi ka jin dadi."
Bawa ya fita daga wurin Kamaruzzaman, bai
gasgata kubutarsa ba. Yana fita waje sai ya dafe
keya, ya zura a guje, yana faduwa yana tashi, bai
zame ko'ina ba sai gaban karagar [ http://
fb.com/waziriaku ] Sarki Shaharuzzaman. A
lokacin kuwa Sarki na cikin magana da Waziri
yana ce masa, "Ya Waziri, ka sani cewa tsawon
daren jiya ban runtsa ba. Ina cike da tunanin
Kamaruzzaman kada wani mugun abu ya same
shi a cikin gidan gonar nan. Ka san an [ http://
fb.com/waziriaku ] dade ba a yi amfani da shi.
Shin wai ma, menene amfanin tsare shi a can?"
Waziri ya ce, "Kada ka damu, Allah ya ba nasara.

In Sha Allahu babu abin da zai same shi. Ka bar
shi can tsawon wata guda, [ http://fb.com/
waziriaku ] har sai ya bi da kansa, ya koma cikin
hankalinsa."
Suna cikin wannan zance sai ga bawa, mai gadin
Kamaruzzaman, ya fado cikin fadar da gudu,
wujiga-wujiga, kamar wanda kura ta biyo. Yana
zuwa ya fadi gaban karagar [ http://fb.com/
waziriaku ] Sarki yana cewa, "Kaiconmu ya Sarki
mai cikakken iko! Babu makawa danka ba ya da
lafiya, ya haukace! Ya buge ni, ya shure ni, ya yi
mini kaza da kaza, har na zama kamar yadda
kake ganina yanzu." Bawa ya fada wa Sarki
dukkan abin da Kamaruzzaman ya yi masa na
azaba. [ http://fb.com/waziriaku ]
Ya ci gaba da cewa, "Ya matsa mini wai sai na
fada masa wace yarinya ce aka tura ta kwana
wurinsa, kuma wanene ya dauke ta da yana
barci. Na rantse masa, na kuma na rantse masa,
babu yarinyar [ http://fb.com/waziriaku ] da ta
kwana wurinsa, amma bai yarda ba.

Ya shugabana, na rantse da Allah babu wanda ya
kwana tare da shi, domin ban daga zuwa ko'ina
ba, daga bakin kofar dakinsa ina gadinsa."
Yayin da Sarki Shahruzzaman ya ji bayanin bawa,
sai ya mike cikin fushi, ya yi tsawa ga Waziri
yana cewa, "Ga abin da nake gudu nan! Tashi
maza [ http://fb.com/waziriaku ] ka tafi wurin
dana, ka samo mini labarin abin da yake ciki."
Nan take Waziri ya tashi cikin hanzari, buje yana
tade shi, cikin tsoro, ya saka bawa gaba suka
nufi gidan gona wurin Kamaruzzaman. [ http://
fb.com/waziriaku ]
*** *** ***
Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar
labarun DARE DUBU DA DAYA,..

Whatsapp only pls
08032767547(10) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI
SHAHARUZZAMAN

Yayin da Sarki Shahruzzaman ya ji bayanin bawa,
sai ya mike cikin fushi, ya yi tsawa ga Waziri
yana cewa, "Ga abin da nake gudu nan! Tashi
maza ka tafi wurin dana, ka samo mini labarin
abin da yake ciki." Nan [ http://fb.com/
waziriaku ] take Waziri ya tashi cikin hanzari buje
yana tade shi, cikin tsoro, ya saka bawa gaba
suka nufi gidan gona wurin Kamaruzzaman.
Ko da su ka isa gidan hantsi ya yi, suka tarar da
Kamaruzzaman zaune bisa shimfidarsa yana
karanta Alkur'ani mai tsarki. Bawa ya tsaya daga
bakin kofar daki, idan ya ji kyasham sai ya arce.
Waziri ya shiga cikin dakin ya zauna [ http://
fb.com/waziriaku ] gefen Kamaruzzaman. Da
Kamaruzzaman ya gan shi sai ya dakata da
karatu, ya rufe littafin ya ajiye gefe.
"Wannan rudadden bawan ne ya je wa Sarki da
wani rikitaccen labari wanda ya tayar masa da
hankali." In ji Waziri.
"Me ya fada wa Sarki wanda ya tayar masa da
hankali, fiye da abin da Sarkin ya yi mini, wanda
ya [ http://fb.com/waziriaku ] tayar mini da
hankali?" Kamaruzzaman ya tambaya.
Waziri ya gyara zama ya ce, "Ya je mana
afujajan, kamar wanda ya kwaci kansa da kyar
daga sabon mahaukaci, ya ba mu labari na karya
game da kai, wanda bai kyautu in maimaita
wannan karya tasa ba. Domin da ganin halin da
kake ciki yanzu, na tabbatar da labarinsa karya
ne."

"Wai me ya fada muku ne game da ni, ka tsaya
kana ta yi mini 'yan zagaye-zagaye?"
Kamaruzzaman ya tambaya, ransa ya fara baci,
domin ya ga alamar Waziri na [ http://fb.com/
waziriaku ] shirin boye masa maganar yarinyar da
ya gani jiya cikin dare.
Waziri ya ce, "Ce mana ya yi wai ka tabu!
Saboda ka matsa masa sai ya fada maka wace
yarinya ce aka kawo ta kwana wurinka, jiya da
dare. Kuma wai wanene ya dauke ta da kana
barci. Ya ce wai har cikin rijiya ka yi ta
tsunduma shi don ya ce maka bai ga kowa ba?" [
http://fb.com/waziriaku ]
Yayin da Kamaruzzaman ya ji zancen Waziri, sai
ya cika da fushi, fushi mai tsanani. Ya juya ya
dubi Waziri ido da ido, ya ce, "Yanzu na tabbatar
da cewa ku ne kuka kitsa wa wannan munafukin
bawan ya yi abin da kuka shirya masa. Kuka
hane shi da ya fada mini kome a kan yarinyar da
kuka turo ta kwana tare da ni. Na san ka Waziri
da tsananin dabara, wannan ba shawarar kowa
ba ce face kai. Kai ne ka sa aka turo ta wajena [
http://fb.com/waziriaku ] domin ta canja mini
ra'ayi game da maganar aure. Ta kwana tare da
ni, da kuka ga asuba ta kusa sai kuka lallabo
kuka dauke ta. To, dabararka ta ci, na yarda zan
aure ta, amma tana ina yanzu?"

Da Waziri ya ji zancen Kamaruzzaman, sai ya ce,
"Na rantse da Allah, ya shugabana
Kamaruzzaman, ba mu turo kowa ya kwana
wurinka ba a daren jiya. Kai kadai ka kwana a
kan shimfidarka, sai bawan da ke gadinka a [
http://fb.com/waziriaku ] bakin kofa. Babu wata
yarinya da muka turo wurinka. Yi tunani dai ka
gani, ya shugabana."
Kamaruzzaman ya ce cikin tausasa murya, "Na
kamu da son wannan yarinya da na gani a daren
jiya. Ita ce shugabar [ http://fb.com/waziriaku ]
kyawawa, mai fararen idanu da jajayen
kundukuki. Mun kwana kan shimfida guda tare da
ita."
"Shin ka ganta ne kuru-kuru da idonka, ko kuwa
dai cikin mafarki ka gan ta?" Waziri ya tamabaya,
domin lamarin Kamaruzzaman ya fara daure
masa kai.

Kamaruzzaman ya amsa masa cikin fushi, "Da,
da kunnuwana kake sa ran zan gan ta, yau ga
dattijon wofi. Da idona na gan ta, kuma na dade
ina kallon kyakkyawar fuskarta. Har girgiza ta na
yi ta yi da hannuwana domin ta farka mu yi
zance, amma da yake kun umurce ta da [ http://
fb.com/waziriaku ] cewa kome na yi mata kada
ta kula, sai ta yi kamar barci ta ke yi, ta kyale ni.
Da na gaji da tayar da ita, na ga ta ki tashi, sai
na kwanta kusa gare ta har barci ya dauke ni. Ko
da na farka da safe sai na ga har kun sa an
dauke ta.""Babu shakka wannan mafarki ne, ya shugabana
Kamaruzzaman. Ko kuma watakila ka yi wasu
ciye-ciye ko shaye-shaye da suka kawar maka
da hankali kafin ka kwanta. Ko kuma mai yiwuwa
siddabaru ne na miyagun [ http://fb.com/
waziriaku ] aljanu." In ji Waziri.
"Kai tsohon banza! Ni za ka yi wa wasa da
hankali, bayan wannan munafukin bawan ya ce
zai fada mini gaskiya. Ya fada mani da shi kuka
shirya kome. Ni za ka fada wa cewa wai mafarki
ne nake yi, bayan na ga abu kuru-kuru da idona
ina farke?" Kamaruzzaman na fadin haka, sai ya
tasowa Waziri ya kama gemunsa ya ja shi [
http://fb.com/waziriaku ] da karfi. Waziri ya ji
kamar ransa zai fita. Kamaruzzaman ya dunkule
hannu ya yi ta dimar Waziri, hannunsa daya yana
rike da gemunsa.
Waziri ya yi ta ihu yana hargowa, da dai ya ga
babu ko shakka Kamaruzzaman zai halaka shi,
sai ya ce a cikin ransa, "Bari in yi dabarar da
bawan nan ya yi, tabbas wannan yaro ya
haukace."
"Dakata, dakata, na san da zancen, ya [ http://
fb.com/waziriaku ] shugabana." Waziri ya fada
cikin karaji da zafin duka. Daga nan sai
Kamaruzzaman ya daina bugun shi. Waziri ya ci
gaba da cewa, "Ka gafarce ni ya shugabana,
Sarki ne ya ce in boye wannan magana, kada in
sanar da kai. Hakika mu ne muka shirya wannan
dabarar, muka turo wannan yarinya ta kwana
wurinka domin mu gani ko za ka amince da [
http://fb.com/waziriaku ] maganar aure. Amma
yanzu ka ga na wahala ga hannunka, na sha
bugu kamar jaki. Ka sake ni in dan sarara in huta,
na yi alkawari zan fada maka kome game da
wannan kyakkyawar yarinya da ka gani."
Da jin haka sai Kamaruzzaman ya sakar masa
gemu, ya ce, "Ka dai ji kunya, tsohon banza! Don
me ka tsaya yi mini karairayi, bayan ka san da
zancen? Ba ka tashi fada [ http://fb.com/
waziriaku ] mini gaskiya ba sai da ka sha wuya.
Maza ka fada mini labarinta."
"Kana nufin kyakkyawar yarinyar da ta kwana
wurinka jiya da dare?" Waziri ya tambaya yana
daddafa gemunsa.

"I, ita nake nufi. Ka fada mini, ya kai Waziri,
wacece wannan yarinya, wa ya kawo ta wurina
lokacin da nake barci, wanene kuma ya dauke ta
kafin gari ya waye? Ka fada mini tana ina a halin
yanzu, [ http://fb.com/waziriaku ] domin ina so
in kara ganinta. Idan dai har an jarraba ni ne da
kyawunta a kan bukatar mahaifina ta in yi aure,
to, na yarda zan aure ta in huta da wannan matsi
da tsangwama da kuke nuna mani don na ki yin
aure. Yanzu na amince, bari na kara fada, na
amince zan yi aure. Ka tafi ka fada wa
mahaifina, ya kai Waziri, a aura mani wannan
yarinya domin zuciyata [ http://fb.com/
waziriaku ] ta riga ta mace cikin sonta. Babu
wata mace da nake so yanzu idan ba ita ba. Ka
tashi yanzu da hanzari ka tafi wurin mahaifina ka
shaida masa wannan magana, kuma ina so ka
maido mani da jawabi yanzu-yanzun nan."

Waziri ya ce, "Na ji na dauka." Ya tashi da sauri
ya fice daga cikin dakin Kamaruzzaman yana
godiya ga Allah da ya kubutar da shi daga
hannun wannan yaro da bai halaka shi ba. Ya fita
daga gidan gona yana sauri, buje yana tade masa
kafafu, ya fadi ya tashi, har ya isa wurin [ http://
fb.com/waziriaku ] Sarki Shahruzzaman.
.
Yayin da Sarki ya gan shi cikin wannan hali sai
ya tambaye shi, "Ya Waziri, wane mutum ne ya
aikata maka wannan abu haka? Yaya nake ganin
fuskarka duk ta kumbura haka kamar wanda ya
fito daga filin daga?"
Waziri ya ce, "Ya shugabana, na zo maka da
albishir." [ http://fb.com/waziriaku ]
"Wane irin albishir ne ka kawo mani?" Sarki
Shahruzzaman ya tambaya.

Waziri ya ce, "Babu shakka danka
Kamaruzzaman ya haukace, mummunan hauka."
Yayin da Sarki ya ji haka sai ransa ya baci,
hasken da ke fuskarsa ya koma duhu. [ http://
fb.com/waziriaku ] Ya dubi Waziri ya ce, "Ya kai
Waziri, wane irin hauka ne ya samu dana?" Waziri
ya kwashe labarin dukkan abin da ya faru
tsakaninsa da Kamaruzzaman ya fada wa Sarki."

Da Sarki ya ji haka sai ya ce cikin fushi, "Ka sani
cewa, ya kai Waziri, zan ba ka goron wannan
albishir da ka kawo mani na haukacewar dana.
Goron [ http://fb.com/waziriaku ] da zan ba ka
kuwa shi ne datse kanka da takobi, ya kai karen
wazirai. Domin kuwa kai ne wanda ka ba ni
shawarar in tsare shi cikin wannan gidan gona.
Na rantse da Allah idan dai har dana ya haukace
da gaske, babu makawa sai na tsire ka a gaban
fada kowa na kallo, ka yi mutuwar wulakanci." [
http://fb.com/waziriaku ]
Daga nan Sarki ya mike tsaye cikin hanzari ya
nufi gidan gonar da aka tsare Kamaruzzaman,
Waziri ya bi shi a baya jikinsa na rawa don tsoro.

Suna isa, Sarki ya wuce cikin gidan kai tsaye
tare da Waziri. Kamaruzzaman na ganin
mahaifinsa, sai ya tashi tsaye daga kan abin
zama. Ya zo gaban mahaifin nasa ya durkusa ya
gaishe shi cikin ladabi sa'annan ya mike tsaye ya
mayar da hannuwansa [ http://fb.com/waziriaku ]
ga bayansa ya harde su, ya sunkuyar da kansa
kasa.
Sarki da Waziri da Kamaruzzaman suka yi tsaye
cirko-cirko, tsawon sa'a guda babu wanda ya ce
uffan. Daga nan sai Kamaruzzaman ya dago
kansa, ya dubi mahaifinsa, idanunsa cike da
hawaye har yana gudana kan kundukukinsa. Ya
waka wadannan baitoci:

"Yafe mani laifukana, kafafuna na kakkarwa
domin laifukan da na yi. Bawa na neman afuwar
ubangijinsa. Na aikata laifi, ina neman yafuwarka
da gaggawa. Shin har zuwa yaushe ne wannan
yafuwar za ta kasance?"
Yayin da [ http://fb.com/waziriaku ] Sarki ya ji
wannan waka daga bakin dansa, sai ya cika da
farin ciki. Ya rungume shi, ya sumbaci goshinsa.

Suka zauna kan shimfida, Sarki ya zaunar da
Kamaruzzaman kusa gare shi, ya harari Waziri ya
ce, "Ya karen wazirai! Me ya sa ka fada mini
karya game da dana? Ka ce ya aikata kaza da
kaza, har ma ka ce ya haukace. Ka jefa raina
cikin damuwa." [ http://fb.com/waziriaku ]
*** Waziri Aku ***

Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar
labarun DARE DUBU DA DAYA, Wanda yanzu haka na kasuwa

(11) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI
SHAHARUZZAMAN

Yayin da Sarki Shaharuzzaman ya ji wannan
waka daga bakin dansa, sai ya cika da farin ciki.
Ya rungume shi, ya sumbaci goshinsa. Suka
zauna kan shimfida, Sarki ya zaunar da
Kamaruzzaman kusa gare shi, ya harari Waziri ya
ce, "Ya karen wazirai! Me ya sa ka fada mini
karya game da dana? Ka ce ya aikata kaza da
kaza, har ma ka ce ya haukace. Ka jefa raina
cikin damuwa."
Sarki bai ko jira jin ta bakin Waziri ba, sai ya juya
wurin Kamaruzzaman ya ce, "Dana, wace rana
muke ciki yau?"
"Yau Assabar, karshen mako. Gobe Lahadi, sai
Litinin, Talata, Laraba, Alhamis sai Juma'a."
Kamaruzzaman ya amsa wa Sarki.
Sarki ya ce cikin murna, "Ya dana,
Kamaruzzaman, farin cikin raina, Wallahi
zancenka haka yake, ban ga alamun tunaninka ya
jirkita ba. To, amma wannan wane wata ne?"
Kamaruzzaman ya ce, "Yanzu muna cikin watan
Zulkida ne, yau kwanansa goma sha shida. Daga
shi sai Zulhijja, sai Muharram, sai Safar, sai
Rabiu Awwal da Rabiu Sani, sai Jimada Ula da
Jimada Ahir, sai Rajab, sai Sha'aban, sai
Ramadan, sai Shawwal."

Sarki Shaharuzzaman ya raurawa da farin ciki, ya
dubi Waziri ya tofa masa yawu a fuska ya ce,
"Tsohon banza, makaryaci! Don me kake ce wa
dana mahaukaci? Lalle ba kowa ne mahaukaci ba
face kai, ya kamata a daure ka a turu." Waziri ya
goge fuskarsa da hannun rigarsa, ya so ya yi
magana sai wata zuciyar ta ce masa, "Kara jira
dai ka ga abin da zai faru." Sai ya yi shiru bai ce
kome ba.

Sarki ya juya wurin Kamaruzzaman, ya dafa
kafadarsa ya ce, "Ya dana, shin mecece gaskiyar
maganar da bawan nan mai gadinka da Waziri
suka je mini da ita? Sun ce, wai ka matsa musu
sai sun fada maka labarin wata yarinya da ta
kwana wurinka. Wace yarinya ce wannan kake
magana a kanta?"
Yayin da Kamaruzzaman ya ji wannan tambaya
daga mahaifinsa sai ya yi dariya, ya dubi
mahaifin nasa ya ce, "Ya mahaifina, Wallahi na
gaji da irin wannan wasan da kuke yi mini haka
nan. Na riga na fada wa Waziri, ya shaida maka
cewa na amince zan yi aure, kamar yadda ka
bukata. Amma fa ba zan auri kowa ba face
yarinyar da kuka turo ta kwana wurina jiya.
Saboda na tabbata kai ne ka turo ta wurina
domin ta canja mini ra'ayi. Ka sani ya kai
mahaifina, wannan tarko naka ya kama ni. Ka
gaggauta aura mini ita ko na sami nutsuwa."
Nan take fuskar Sarki ta canja da jin wannan
jawabi na dansa, ya ce, "Don girman Allah wanda
ya halicce ka, ka bar kokarin saka kanka cikin
zancen shirme. Wace irin yarinya ce wannan
wadda kake ta zancen wai na turo ta, ta kwana
wurinka, kuma na sa an dauke ta kafin safiya?
Na rantse da Allah, ya dana, ban san kome ba
game da wannan zance naka, babu shakka ba
kome ba ne wannan face mafarki. Domin lokacin
da ka bar wurina jiya, ka yi ta tsine wa mata,
kuma kana cewa, 'Allah ya tsine wa duk wanda
ya ba da shawarar a yi mani aure.' Ka sani cewa
duk abin da mutum ya kwanta da shi a cikin
ransa, to, babu makawa mafarkin wannan abu zai
yi. Ka kwanta ne da maganar aure a cikin ranka,
shi ya sa ka yi mafarki da wannan yarinya da ka
ce ta kwana kusa gare ka. Amma in bayan kai da
bawa mai gadin ka, babu wanda ya kwana a cikin
wannan gida."
Idanun Kamaruzzaman suka yi ja, suka cika da
hawaye, ya ce wa mahaifinsa, "Ya mahaifina, ina
so ka rantse mini da Allah, wanda ya halicce ka,
ya sanya maka rayuwa, wanda kuma zai shake
rayuwarka, idan kwananka ya kare, cewa ba kai
ne ka turo wannan yarinyar wurina ba, ba ka san
daga inda ta fito ba, kuma ba ka san wanda ya
turo ta ba."

Sarki ya ce, "Na rantse da Allah madaukakin
Sarki, Ubangijin Musa da Ibrahim, ban san kome
ba game da wannan yarinya da kake zance. Ni
ina ganin ba kome ba ne wannan, face yaye-
yayen mafarki."
Kamaruzzaman ya ce, "Yanzu kuwa zan nuna
maka shaidar cewa, wannan yarinya da na gani,
ba yaye-yayen mafarki ba ne. Na gan ta da idona
kuru-kuru, yayin da nake farke cikin hankalina.
Amma bari in tambaye ka wani abu."
Sarki ya ce, "Menene wannan abu?"
Kamaruzzaman ya ce, "Shin ka taba ganin wanda
ya kwanta barci, ya yi mafarki yana yaki, yaki
mai tsanani. Da ya farka sai ya gan shi da
zararren takobi rike ga hannunsa har takobin na
digar da jini?"

Sarki ya ce, "Ban taba gani ba, ban kuma taba jin
haka ba. Ai wannan ba abu ne mai yiwuwa ba"
Fuskar Kamaruzzaman ta washe da wannan
amsa da Sarki ya ba shi, har ya yi murmushi
hakoransa suka bayyana. Sannan ya gyara zama,
ya nutsu, ya dubi mahaifinsa ya ce, "Ya
mahaifina, Wallahi kwatankwacin wannan abu ne
ya faru gare ni. Ka sani cewa, ina cikin barci jiya
da dare, sai wani kwaro ya cije ni na farka. Ko da
na farka sai na ga wata kyakkyawar yarinya,
wadda ban taba ganin mace mai kyau kamarta
ba, tana kwance kusa gare ni tana barci. Na
girgiza ta domin ta tashi in ji ko wace ce ita,
amma ba ta farka ba. Na yi niyyar in sumbace ta,
sai na ji kunya watakila kana nan labe kana
kallonmu, domin a zatona tarko ne ka dana mini
da ita, ka ga me zan aikata gare ta, tun da na
bijirewa bukatarka ta yin aure. Da na tuna da
wannan a cikin raina, sai na sa hannu na cire
zobenta, na saka shi a dan yatsana na kwanta,
barci kuwa ya dauke ni. Yayin da na farka da
asuba, na duba ko'ina babu yarinya babu
dalilinta, na dubi hannuna domin na ga ko
mafarki ne na yi, amma sai na ga zobenta a
hannuna, kuma sai na lura da ta cire nawa zoben
ta tafi da shi."
Kamaruzzaman ya ci gaba da cewa, "Ya
mahaifina, Wallahi ba domin wannan zobe nata
ba, da ban tayar da maganar ba, sai in dauka
mafarki ne kawai na yi. To, amma ga zobenta
nan a hannuna." Ya cire zobe ya mika wa Sarki.
Sarki ya karbi zobe ya jujjuya shi ga hannunsa,
ya gan shi zobe ne mai tsada, mai daraja, ya
girgiza kansa cikin mamaki, ya ce, "Hakika
wannan abu da ya faru gare ka, ya dana,
rikitaccen al'amari ne mai wuyar kan gado.
Amma ba laifin kowa ba ne wannan face Waziri,
wanda shi ne sanadin tsare ka a cikin wannan
gida." Sarki ya shafa kan Kamaruzzaman ya ce,
"Ya dana, ka kwantar da hankalinka, da yardar
Allah madaukakin Sarki, za mu sami hanyar
warware wannan rikitaccen al'amari cikin sauki
ya zuwa ga cikar burinka. Kamar yadda wani
mawaki yake cewa:
"Da sannu al'amari kan juye,
Farin ciki ya kan komawa.
Sa'ar zamani takan lauye,
Mai kuka ya zan darawa."

Sarki ya ci gaba da cewa, "Ya dana, yanzu
hankalina

1 Comments On HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHRUZZAMAN
avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Wanne darasi kuka ?aru da shi daga cikin wannan hikayar,

Please Login or Register in order to submit comment