Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kwanta, na tabbata cewa babu abin
da ya same ka na gushewar hankali. Sai dai
wannan al'amari da ya faru gare ka, abu ne da ba
a taba gani ba, ko jin labarin irinsa ba."
Kamaruzzaman ya rungume mahaifinsa, ya rika
magana cikin shagwaba kamar wanda zai yi
kuka, yana cewa, "Ya mahaifina, ina rokonka da
ka gaggauta nemo wannan yarinya duk inda take,
ka nema mini aurenta, na amince zan aure ta.

Wallahi ba zan iya rayuwa ba, ba tare da ita ba.
Idan kuwa ka ki zancena, ina tabbatar maka
cewa, bakin cikin rashinta da tunaninta za su
kashe ni." Daga nan sai idanunsa suka fara zubar
da hawaye shar shar shar. Sannan ya sake cewa
da mahaifinsa, "Na rantse da Allah, ya mahaifina,
ba na jin zan iya kara sa'a daya ba tare da na
saka wannan yarinya a idona ba."
Sarki Shahruzzaman ya rika tafa hannuwansa
cikin takaici da mamaki yana cewa, "Babu tsimi
babu dabara face daga Allah madaukakin Sarki.
Ya Ubangijin talikai, ka gaggauta biya wa wannan
yaro bukatarsa." Daga nan ya riki hannunsa, ya ja
shi suka koma gida, suka bar wannan gidan
gona.
Suna isa gida sai Kamaruzzaman ya fadi kwance
a kan shimfida. Wasa-wasa abu ya zamar masa
ciwo. Sarki kuwa sai ya kasance kullum yana
wurinsa, dare da rana, yana zubar da hawaye. Ya
daina zuwa fada kwata-kwata. Da Waziri ya ga
kwana da kwanaki Sarki bai fita fada ba, sai ya
same shi inda yake jiyyar Kamaruzzaman. Ya
durkusa ya ce masa, "Allah ya ba ka nasara, har
zuwa wane lokaci za ka ci gaba da zama nan
tare da danka, ka daina fita zuwa ga askarawa?
Ina jiye maka tsoron kada askarawa su yi maka
tawaye saboda rashin zamanka kusa gare su,
kana lura da abubuwan da ke faruwa a cikinsu.
Masu hikima sukan ce idan ka na da raunuka da
yawa a jikinka, to ka fara shafa wa rauni mafi
tsanani magani kafin ka shafa wa sauran
raunukan."

Da Waziri ya ji Sarki bai ce masa kome ba, sai ya
kara dukar da kansa kasa, ya ci gaba da cewa,
"Ya shugabana, shawarar da zan ba ka ita ce, ka
dauki danka Kamaruzzaman ka mayar da shi
gidanka, wanda yake a bakin teku, a rika jiyyar
shi a can. Tunda gidan ba ya da nisa da fada, sai
ka rika zuwa fada duk ranar Litinin da Alhamis
kana ganawa da Waziranka, da fadawanka, da
alkalanka, da hakimai da masu unguwa da
dagatai da askarawanka da sauran talakawanka.
Ka yi umurni, ka yi hani a cikinsu, ka tube ka
kuma nada. Ya kasance dai kana gudanar da
lamurran mulki a cikin al'ummarka. Alabashi
sauran ranaku sai ka kasance tare da danka, har
Allah ya kawo mana hanayar da za a warware
wannan matsala tasa. Amma muddin ka ci gaba
da hana jama'arka zuwa gare ka, to ina jiye
maka tsoro wani abu ya faru ga mulkinka."
Wannan shawara ta Waziri ta daki zuciyar Sarki,
ta maido da shi cikin hayyacinsa, domin shi har
ya manta da wata abu wai ita sarauta. Nan take
ya sa aka dauki Kamaruzzaman aka mayar da shi
a wancan gidan na bakin teku. Gidan an gina shi
ne akan dutse, wani bangare na ruwan teku yana
bi ta karkashin dutsen da gidan yake a kai.

Tagogin gidan da kofofinsa, wadanda aka yi da
zinariya, suna kallon ruwan teku. Rufin gidan
kuwa an yi masa fenti da launuka masu ban
sha'awa. Daben gidan kuwa an yi shi ne da farin
dutse. An shimfide gidan da dukkan shimfidu na
alfarma masu tamanin gaske. Da aka zo da
Kamaruzzaman cikin gidan a ka kwantar da shi
bisa shimfida a cikin wani daki da aka kawata da
kayan alatu. Sai ya kasance Sarki yana fita fada
duk ranar Litinin da Alhamis, ya hadu da
jama'arsa, yana hukunci a tsakaninsu. Saura
ranaku kuwa sai ya zauna kusa ga dansa yana
zubar da hawaye saboda abin da ya same shi na
ciwon so. Cikin 'yan kwanaki kadan,
Kamaruzzaman ya rame, ya lalace, ya yi baki har
ta kai ga ba ya iya cin kome sai abu mai ruwa,
shi din ma sai an dura masa. Wannan shi ne abin
da ya faru ga Kamaruzzaman dan Sarki
Shahruzzaman.

Amma abin da ya faru ga Badura 'yar Sarkin
kasar Sin kuwa shi ne, bayan aljanu sun ajiye ta
bisa shimfidarta, sai ta ci gaba da sharar barci
har gari ya waye. Tana farkawa, sai ta duba
dama, ta duba hagu, ba ta ga saurayin da yake
kwance kusa gare ta ba. Daga nan sai ta yi kara,
kara mai tsanani. Nan take kuyanginta, da
tsofaffin matan nan masu kula da ita suka shigo
wurinta a firgice. Daya daga cikin tsofaffin ta
durkusa ta tambaye ta, "Me ya same ki, ya
shugabata?"

Badura ta harari 'yar tsohuwa ta daka mata
tsawa, "Ya ke makirar tsohuwa! Ina kuka kai mini
masoyina abin begena, wannan da ya kwana
wurina?"
*** Waziri Aku ***

Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar
labarun DARE DUBU DA DAYA, wanda nan akasuwa yanzu haka'...,

Yusuf A jibaga' ke muku barka da dare(12) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI
SHAHARUZZAMAN

Badura ta harari 'yar tsohuwar dake durkushe a
gabanta, ta daka mata tsawa, "Yake makirar
tsohuwa! Ina kuka kai mini masoyina, wannan da
ya kwana wurina?" http://facebook.com/
waziriaku
Tsohuwa ta rude, ta ce, "Ya shugabata, wace irin
magana ce wannan kike yi. Wallahi babu wani
namiji da ya matso kusa da kofar dakin nan naki
balle http://facebook.com/waziriaku har ya
kwana cikinsa."
"Karya kike yi, makirar tsohuwa!" Badura ta fada
cikin tsawa, "Ina kuka kai mini abin begena, mai
hasken fuska, mai jajayen kundukuki, mai fararen
idanu da kyawawan girar idanu, mai http://
facebook.com/waziriaku matsakaicin jiki, sanyin
zuciyata, farin cikin rayuwata, wanda muka
kwana ina rungume da shi ga jikina tun da dare
har kusan wayewar gari?"
'Yar tsohuwa ta marairaice tana rantse-rantse,
tana cewa, "Na rantse da Allah, ya shugabata,
mu, ba mu ga wani saurayi ba a cikin http://
facebook.com/waziriaku wannan gida. Kuma
muna rokon ki don Allah ki rufa mana asiri, idan
har wasa kike yi, kada wannan magana ta kai ga
kunnen Sarki. Domin kuwa idan Sarki ya ji labari
cewa wai wani namiji ya kwana a cikin http://
facebook.com/waziriaku wannan gida, wa zai
kubutar da mu daga azabarsa?"
"Ina tabbatar muku cewa wani saurayi ya kwana
a cikin wannan dakin tare da ni a http://
facebook.com/waziriaku daren jiya, saurayin da
ban taba ganin kyakkyawa kamarsa ba." In ji
Badura.
Wata kuyanga ta tsoma bakinta, ta ce, "Ya
shugabata, watakila dai mafarki ne kika yi, amma
babu wani saurayi da ya kwana a http://
facebook.com/waziriaku wannan gida."
Badura ta duba yatsun hannunta, sai ta ga babu
zobenta, sannan kuma ga zoben Kamaruzzaman
da ta cire ta sa a dan yatsanta. Ta dubi kuyanga
ta ce, "Allah ya la'ane ki! Don me za ku yi mini
karya, ku ce http://facebook.com/waziriaku babu
saurayin da ya kwana a dakina. Kina iya
rantsewa a kan abin da kika fada?"
"Na rantse da Allah Madaukakin Sarki, maganar
da na fada miki gaskiya ce. Ba zan http://
facebook.com/waziriaku rantse miki a kan karya
ba." Wannan rantsuwa ta kuyanga ta dugunzuma
ran Gimbiya Badura, ta sake duba yatsun
hannunta. Nan take cikin fushi ta zare wata
takobi da ke kusa gare ta, ta dauke kan wannan
http://facebook.com/waziriaku kuyanga. Sauran
kuyangi da tsofaffin nan na ganin haka, sai suka
yi waje da gudu, wata na ture wata suna faduwa,
suka nufi wurin Sarki.
Da Sarki ya ji wannan http://facebook.com/
waziriaku labari, nan take ya tafi gidan da 'yarsa
taka tsare, ya ce da ita, "Ya 'yata, me ya same
ki?" Ta amsa masa, "Ya mahaifina, ina saurayin
da ya kwana wurina a daren jiya?" Daga nan sai
shaukin begen Kamaruzzaman ya buge ta, ta
juya da idanunta http://facebook.com/waziriaku
dama ta juya da su hagu, kamar mai neman wani
abu a cikin dakin. Ta dage rigar baccinta har
kirjinta ya bayyana, tana tunanin yadda ta
rungume Kamaruzzaman, gaba daya ta manta da
mahaifinta da sauran kuyangi suna cikin dakin.
http://facebook.com/waziriaku
Yayin da mahaifinta ya ga haka, sai ransa ya
baci, ya daka wa kuyangi tsawa da su kama ta
su daure. Cikin kankanin lokaci, kuyangi suka
taushe http://facebook.com/waziriaku Badura
suka buga mata sarka ga wuya da hannuwa da
kafafu, suka daure ta a turken tagar dakinta.
Suka rufe dakin suka tafi suka bar ta. Bakin ciki
a wurin mahaifinta, ba a ko maganarsa saboda
tsananin son da yake yi mata. http://
facebook.com/waziriaku
Sarkin Sin ya ba da sanarwa a cikin fadin
kasarsa gaba daya, duk wani mai maganin da ya
ba 'yarsa magani ta warke, to, zai aura masa ita,
kuma zai raba kasarsa biyu ya ba shi rabi. Amma
kuma duk mai maganin da ya yi http://
facebook.com/waziriaku ido hudu da 'yarsa, ya
kuma kasa ba ta maganin da za ta warke daga
cutar da take ciki, to, za a fille masa kai, a
sargafe kan a gaban gidanta.
Daga nan masu magani suka yi ta barkowa
domin jaraba sa'arsu, amma babu daya daga
cikinsu wanda ya yi nasara. Duk wanda ya
http://facebook.com/waziriaku yi iyakacin
kokarinsa ya kasa, sai Sarki ya sa a fille kansa.
Haka aka yi ta fille kawunan masu magani har
aka kashe mutum arba'in, duka aka sargafe
kawunansu a gaban gidan da Badura take tsare.
Wannan abu ya ba http://facebook.com/
waziriaku mutane tsoro, domin ba a taba ganin
ciwon da ya gagari wadannan bokaye da aka
kashe ba, don haka sai kowa ya hadiye
kwadayinsa, ya shafa wa kansa ruwa.
Ita kuwa Badura kullum begen Kamaruzzaman
sai kara mamaye mata zuciya http://
facebook.com/waziriaku yake yi. Duk ta rame ta
kare, babu abin da take yi kullum sai kuka, idan
ta gaji da kuka kuma sai ta rera wadannan
baitoci:
"Ni mai bege ce a gare ka,
Kai ne wata mai haske idona.
Ambaton sunanka karatu,
Dadinsa nakan ji dare ko rana.
Wutar begenka tana kona ni,
Kamar Jahima cikin kirjina.
Kullum kwancina ba juyi,
Sai hawaye gun sa idona."
Sai kuma ta rera wadannan: http://
facebook.com/waziriaku
"Na dulmiya kogin kauna,
Wa zai cetan ban da masoyi?
Miko hannunka na kama,
Kar ka bar ni ruwa ya masoyi!
Sannu, ba ta warke cuta,
Ido na kuka don ka masoyi.
Garin masoya ba ya nisa,
Ka zo mu gana haba masoyi!"
http://facebook.com/waziriaku Da zarar ta waka
wadannan baitoci kuma, sai ta yi ta kuka, har sai
hawayenta sun kafe idanunta sun kumabura.
Haka ta kasance a cikin wannan hali tsawon
shekara uku.

To, gimbiya Badura tana da wani dan uwan
shayarwa, watau wanda mai shayarwa daya ta
shayar da su lokacin da suna jarirai. Sunan
wannan dan uwan shayarwa nata Marzuwan.
Wadda ta shayar http://facebook.com/waziriaku
da su kuwa ita ce mahaifiyar Marzuwan, domin
aikinta ke nan shayarwa. Lokacin da ta haifi
Marzuwan a lokacin ne kuma aka haifi Badura,
don haka sai Sarki ya damka shayarwar Badura a
http://facebook.com/waziriaku hannunta. Ita
kuma ta ci gaba da shayar da ita tare da danta
Marzuwan.
Badura da Marzuwan sun tashi tare tun suna
yara kamar 'yan uwa, har suka girma suna tare
http://facebook.com/waziriaku kowa yana nuna
wa dan uwansa soyayya da kuma kauna irin ta
'yan uwantaka. Tun kafin Badura ta gama girma
sosai, har manema aurenta sun fara kutso kai,
Marzuwan ya bar garin tare da mahaifinsa zuwa
fatauci. Kwatsam, ana cikin wannan hali sai ga
shi sun dawo tare da mahaifin nasa. http://
facebook.com/waziriaku
Suna sauka, ko hutawa bai yi ba ya tambayi
mahaifiyarsa labarin 'yar uwarsa gimbiya Badura.
Mahaifiyarsa ta yi jim, sa'annan cikin tausayi ta
ce, "Wayyo, ai 'yar uwarka Badura ta http://
facebook.com/waziriaku kamu da ciwon hauka
shekara uku da suka wuce. Yanzu haka tana
cikin sarka a tsare cikin gidanta. Masu magani,
da bokaye da masu bugun taurari, sun yi iyakacin
kokarinsu amma sun kasa gano kan ciwonta."

http://facebook.com/waziriaku
Yayin da Marzuwan ya ji haka, sai fuskarsa ta
canja zuwa launin toka, ya ce da mahaifiyarsa,
"Ina so in gan ta, na ga halin da take ciki, mu yi
zance da juna, watakila ta fada mani ciwon dake
damun ta." http://facebook.com/waziriaku
Mahaifiyarsa ta ce, "Ai an hana kowa shiga
wurinta, amma ka jinkirta mini zuwa gobe, zan
san dabarar da na yi na hada ka da ita." Ya ce,
"Allah ya kai mu goben."
Daga nan sai mahaifiyar Marzuwan ta tashi, ta
nufi gidan da ake tsare da gimbiya http://
facebook.com/waziriaku Badura. Tana isa bakin
kofar gidan, ta fito da wasu 'yan dirhamai ta mika
wa bawan da ke kula da kofar shiga gidan,
wanda yake baba ne. Nan take ya sa hannu ya
kalmashe kudi yana godiya, yana dukar da kai
don http://facebook.com/waziriaku girmamawa
ga mahaifiyar Marzuwan bisa wannan kyauta da
ta yi masa. Da ta ga bakinsa ya ki rufuwa don
murna da wadannan dirhamai da ta ba shi, sai ta
ce, "Da ma na zo ne in nemi wata bukata a
wurinka."
"Fadi bukatarki kowace iri ce, ya http://
facebook.com/waziriaku shugabata." In ji bawa.

Mahaifiyar Marzuwan ta ce, "Ina da wata 'ya ce
da ta yi aure, ita wannan 'ya tawa babbar
aminiyar gimbiya Badura ce. Lokacin da ta ji
halin da gimbiya ta shiga, shi ne ta zo wurina ta
ce tana so ta zo ta http://facebook.com/
waziriaku duba aminiyar tata domin ta ga halin
da take ciki. Ko za ka bar wannan 'ya tawa ta
sadu da gimbiya Badura?"
Yayin da bawa ya ji bukatarta, sai ya yi shiru
zuwa wani lokaci. Can sai ya ce, "Zan yi miki
wannan alfarma, ya shugabata. Amma ki bari sai
gobe da dare, http://facebook.com/waziriaku
bayan Sarki ya fito daga wurinta ya koma
gidansa, sai ki zo da wannan 'ya taki, ta shiga ta
ga gimbiya." Ta yi godiya ga bawa, ta koma gida.
Wanshekare da dare ta yi wa danta Marzuwan
shigar mata, ta riki hannunsa suka nufi gidan da
ake tsare da Badura. Suna zuwa bawan nan ya
shaidata, ya bude musu kofa. Ya yi musu jagora
har zuwa dakin Badura, http://facebook.com/
waziriaku ya ce musu su wuce kai tsaye, amma
kada su dade, ya juya ya koma kofar gida. Da
suka shiga cikin dakin, suka ga Badura a daure
cikin sarka, tun daga wuya har kafa. Marzuwan
ya gaishe ta, bayan ya cire kayan mata da ke
jikinsa. Ya fito da shama'a ya kunna, ya dauko
wani littafi ya fara karantawa. http://
facebook.com/waziriaku
Yana cikin karatun ne, sai hankalin Badura ya
koma kansu, domin tun da suka shigo tana cikin
tunani ne mai zurfi, don haka ba ta san da http://
facebook.com/waziriaku shigowar su ba. Tana
ganin shi ta gane shi. Ta kada baki ta ce, "Ya
dan uwana, ina ka shiga cikin duniyar nan har
labarinka ya yanke daga gare ni?"
Marzuwan ya ce, "Ya 'yar uwata, na tafi fatauci
ne, ni da mahaifina, muka dade a can tsawon
zamani. Ina dawowa na sami labarin http://
facebook.com/waziriaku halin da kike ciki na
cuta, na ce ba zan koma ba face na zo na gan ki,
na jarraba irin nawa maganin da na samo daga
yawon fatauci, ko Allah ya sa warakar cutarki ta
kasance ga hannuna."
Da ta ji jawabinsa, sai ta dan yi murmushin karfin
hali, ta ce, "Ya dan uwana, kai ma ka yarda da
zancensu na cewa ciwon hauka ne ya kama ni?"
http://facebook.com/waziriaku
Marzuwan ya ce, "Na'am."

Ta ce, "To, ba haka ba ne. Ni, ina da hankalina
ras! Sai dai kamar yadda mai waka ke cewa:
"Sun kira ni da hauka don so,
To ina laifin hauka ga masoyi?
Ku kira shi ya zo zan warke,
Silar hauka a gare ni masoyi."
http://facebook.com/waziriaku Ta ci gaba da
cewa, "Idan har akwai cutar dake damu na, to
ciwon so ne."
Marzuwan ya ce, "Ki fada mini http://
facebook.com/waziriaku labarin abin da ya faru
gare ki, watakila zan iya taimaka miki, in fitar da
ke daga cikin wannan hali."
*** Waziri Aku ***

Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar
labarun DARE DUBU DA DAYA, wanda littafin zai
fito nan ba da dadewa ba

.
Za mu ci gaba ranar Assabar gobe kenan insha Allah.(13) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI
SHAHARUZZAMAN

Marzuwan ya ce da Badura, "Ki fada mini labarin
abin da ya faru gare ki, watakila http://fb.com/
waziriaku zan iya taimaka miki, in fitar da ke
daga cikin wannan hali."

Badura ta ce, "Ka sani, ya dan uwana, wata rana
ina cikin barci da dare a cikin dakina, sai na
farka na ga wani kyakkyawan saurayi kwance
yana barci kusa gare ni. Ka ce shi tsumagiyar
turare ne, ko kuma tsumagiyar Hindu, harshe ba
zai iya kwatanta kyawunsa ba. Yayin da http://
fb.com/waziriaku na gan shi sai na zaci ko
mahaifina ne ya turo shi domin ya jaraba ni a kan
maganar da yake ta yi mini ta aure. Saboda
wannan zaton, sai na ki tayar da shi daga barci,
na kuma ki taba shi, don kada gari ya waye ya
fada wa mahaifina abin da ya faru tsakaninmu.
Na kwanta abina, na juya masa baya har http://
fb.com/waziriaku barci ya dauke ni. Yayin da na
farka da safe sai na ga zobensa a dan yatsana,
shi kuma ya cire nawa. Ya dan uwana, tun
lokacin da na ga wannan saurayi zuciyata ta so
shi, ban kara jin dadin barci ko abinci ba. Kullum
son shi da begen shi sai karuwa suke yi a cikin
raina, babu abin da nake yi face tunaninsa da
kuma wakokin begensa, wannan shi ne
sanadiyyar halin da nake ciki har mahaifina yake
ganin kamar na http://fb.com/waziriaku
haukace." Tana gama wannan magana tata, sai
idanunta suka cika da hawaye, ta yi kuka, ta
waka wadannan baitoci:
"Zuciya takan narke don shi ya,
Yaya zan yi in ji dadi ni babu shi?
Begensa ya cikan dukkan zuciya,
Dole idanuwa su zan ba sa barci.
Shi ne jinin jiki wannan mai gudu,
Yaya rayuwa takan zama in babu shi?
Karfi ya tafi, haka kyawo ya gushe,
A gare ni don yawan tunaninsa a zuci."
Da ta gama wannan waka, sai ta ce, "Wannan shi
ne abin da ya faru gare ni, ya http://fb.com/
waziriaku kai dan uwana." Da Marzuwan ya ji
wannan labari nata, ya sunkuyar da kansa kasa
na wani lokaci yana tunani. Zuwa wani lokaci ya
dago da kansa ya ce, "Ni, na gasgata dukkan
abin da kika fada mini. Hakika wannan al'amari
naki abin al'ajabi ne, ya 'yar uwata. Da yardar
http://fb.com/waziriaku Allah kuma na yi miki
alkawari, idan na sake fita zuwa fatauci, zan yi
iyakar kokarina na ga na samo miki wani abu
wanda zai zama tamkar maganin da zai yi
sanadiyyar warakarki daga wannan cuta ta bege.

Amma yanzu ina horon ki da ki zama mai http://
fb.com/waziriaku hakuri ga wannan yanayi da
kika tsinci kanki a ciki."
Suka yi sallama da juna, ya tashi tare da
mahaifiyarsa suka koma gida. http://fb.com/
waziriaku
Bayan 'yan kwanaki kadan, Marzuwan ya yi shirin
fita zuwa fatauci, a wannan karon shi kadai zai
tafi ba tare da mahaifinsa ba. Bayan ya yi
sallama da mahaifansa sai ya kama hanya ya
tafi. Yana ta tafiya, ya shiga wannan birni ya fita,
ya fada wancan tsibir, ya tsallaka wancan, yana
saye yana sayarwa. Duk http://fb.com/waziriaku
birnin da ya shiga kuwa, sai ya tsinci ana labarin
haukan gimbiya Badura. Ya ci gaba da tafiya, ya
yi nisa da kasar Sin da biranenta, har Allah ya
kai shi wani birni mai suna Tayrab. http://
fb.com/waziriaku
Ya yada zango a cikin wannan birni, ya taba
ciniki. Yana cikin kasuwanci a wannan birni wata
rana sai ya ji ana labarin wani dan Sarki da ya
kamu da ciwon hauka. Da ya matsa kusa wurin
masu zancen sai ya ji wai sunan dan Sarkin
Kamaruzzaman dan Sarki Shahruzzaman. Ya
tambayi birnin da wannan dan Sarki yake, aka
shaida masa cewa birnin yana tsakiyar tsibiran
http://fb.com/waziriaku Kalidan ne, kuma daga
nan tafiyar wata daya ce a cikin jirgin ruwa, ko
kuma wata shida a kasa.
Da ya kara kwana biyu a wannan birni, sai ya
shirya hajarsa, ya biya kudin jirgin ruwa wanda
zai nufi tsibiran Kalidan. Da aka gama yi wa jirgi
lodi, ya nausa da su cikin teku, iska ta yi http://
fb.com/waziriaku masa kyau. Bayan tafiyar wata
daya, suka fara hango gine-ginen birnin Sarki
Shahruzzaman. Suna gab da shiga kofar birnin
sai wata mahaukaciyar iska ta taso tare da
rakuman ruwa, suka kifar da jirgin, mutanen da
ke ciki kowa ya yi ta kansa, babu wanda ya san
halin da dan uwansa yake ciki. Shi kuwa
Marzuwan da ya yi ninkaya ya gaji, sai ya yi
sallama da rayuwa. Ya sha ruwa http://fb.com/
waziriaku cikinsa ya cika, idanunsa suka jujjuye,
igiyar ruwa ta ja shi ta nufi karkashin gidan nan
na kan dutse da shi, inda ake jiyyar
Kamaruzzaman.

Allah da ikonsa, wannan rana ta kasance http://
fb.com/waziriaku daya daga cikin ranakun da
Sarki ba ya fita fada, yana nan tare da dansa, da
kuma Wazirinsa a cikin dakin da Kamaruzzaman
yake kwance. A daidai lokacin Kamaruzzaman na
kwance, kansa na bisa cinyar Sarki, kwana biyu
ke nan bai ci kome ba, ko ruwa ya kasa sha.
Wani bawa yana tsaye da mahuci a bayansu yana
yi musu fita, Waziri kuwa http://fb.com/waziriaku
yana tsaye a bakin taga yana kallon ruwan teku,
ya dunkule hannuwansa a baya.
Can sai Waziri ya hango Marzuwan ruwa ya jawo
shi ya nufo karkashin wannan gida da shi. Nan
take tausayinsa ya kama Waziri, sai ya matsa
kusa ga Sarki ya ce masa, "Ya http://fb.com/
waziriaku shugabana, ga wani bawan Allah can
ruwa ya ciwo, ka yi mini izini in tafi in ceto shi
idan yana da rai, watakila sanadiyyar ceton
wannan mutum, Allah ya tausaya mana ya ba
danka lafiya." http://fb.com/waziriaku
Sarki ya ce da Waziri cikin fushi, "Kar ka cika ni
da surutu ya kai karen Wazirai, ka sani duk
wannan rashin lafiyar da dana yake ciki, kai ne
sanadinta. Ka tafi ka ceci wannan mutum, amma
ina shaida maka cewa, idan wannan mutum ya
zo nan ya ga halin da dana yake ciki, kuma
http://fb.com/waziriaku ya fita waje ya tsegunta
wa waninsa, na rantse da Allah sai na sare
kansa tare da kai."

Waziri ya yi sauri ya fita waje, ya nufi inda ya
hangi ruwa na tafiya da Marzuwan. Da ruwa suka
zo da Marzuwan daidai wurin da Waziri ya tsaya,
http://fb.com/waziriaku sai Waziri ya sa
hannunsa ya kamo gashin kan Marzuwan ya fito
da shi waje, ya kwantar da shi bisa yashi. Waziri
ya dube shi da kyau ya ga yana numfashi sama-
sama, ya durkusa a gabansa ya sa hannuwansa
ya http://fb.com/waziriaku rika dannan cikin
Marzuwan ruwa na fita ta bakinsa. Ba a dade ba,
sai Marzuwan ya farfado, ya tashi zaune. Waziri
ya sa ya cire kayansa da suka jike da ruwa, ya
ba shi wata riga ya sanya, ya bashi wani rawani
irin na fadawa ya nada a kansa. http://fb.com/
waziriaku
Da Waziri ya ga hankalin Marzuwan ya dawo ga
jikinsa, sai ya ce masa, "Tashi mu shiga cikin
gida, amma fa ka sani cewa, Allah ya kubutar da
kai daga halaka ta sanadiyyata, don haka ina
rokonka kada ka zama sanadiyyar halakata."

http://fb.com/waziriaku
Marzuwan ya cika da mamaki, ya tambayi Waziri,
"Ta yaya zan zama sanadiyyar halakarka?" http://
fb.com/waziriaku
"Saboda yanzu za mu shiga cikin gida inda Sarki
ke jiyyar dansa Kamaruzzaman." http://fb.com/
waziriaku
Yayin da Marzuwan ya ji an ambaci
Kamaruzzaman sai murna ta kashe shi, domin da
ma shi ne wanda ya zo nema a wannan gari,
amma bai bayyana farin cikinsa a fuska ba.
"Wane ne kuma Kamaruzzaman?" Marzuwan ya
tambayi Waziri. http://fb.com/waziriaku
Waziri ya amsa masa, "Shi ne dan Sarki
Shahruzzaman, yana nan kwance ba shi da
lafiya, rai-kwakwai-mutu-kwakwai, an yi magani
har an gaji amma kullum ciwonsa sai ci gaba
yake yi har http://fb.com/waziriaku an hakura an
zuba wa sarautar Allah ido. Na hore ka, idan
muka shiga wurinsu kada ka yarda ka daga
kanka, balle har ka kalli wannan dan Sarki. Idan
kuwa ka kuskura ka kalle shi, to, Sarki zai sa a
kashe ka, a kuma kashe ni."

Marzuwan http://fb.com/waziriaku ya ce da
Waziri, "Na gama ka da Allah ka fada mini ciwon
da ke damun wannan dan Sarki." Waziri ya
ce,"Mu ma ba mu san ciwon da ke damunsa ba.
Iyakar abin da kowa ya sani shi ne, shekaru uku
da suka wuce, mahaifinsa, Sarki Shahruzzaman
ya yi, ya yi da shi a kan ya yi aure, amma ya
http://fb.com/waziriaku buga kansa ga kasa, ya
ki. Wannan ya fusata Sarki matuka ya nemi
shawarata, na ce da shi a tsare shi a wani gidan
gona, watakila bayan kwana biyu ya ji tsoro ya
amince da bukatar Sarki. To, tun ranar farko da
http://fb.com/waziriaku ya kwana a cikin
wannan gidan gona, sai ya tashi da safe da
maganar wata yarinya wadda ya ce wai ta kwana
tare da shi a kan shimfida daya, har suka yi
musayar zobe da ita. Muka ce masa mu, ba mu
san da zancen ba, wasa-wasa sai abu ya zamar
masa ciwo, Sarki kuwa ya dauki laifin duniyar
nan na sanadiyyar http://fb.com/waziriaku rashin
lafiyar dansa ya dora a kaina. Yanzu shekara uku
ke nan, duk lokacin da yaron nan ya bude baki ba
ya maganar kome sai ta wannan yarinya."
http://fb.com/waziriaku Yayin da Marzuwan ya ji
zancen Waziri, sai ya ce a cikin ransa, "Shakka
babu, wannan dan Sarki shi ne wanda na zo
nema, kuma shi ne wanda zai zama sanadiyyar
warakar 'yar uwata gimbiya Badura." Ya tashi ya
bi Waziri suka shiga cikin gida. Da suka isa cikin
dakin sai Waziri ya sami wuri ya zauna, amma
http://fb.com/waziriaku Marzuwan sai ya tafi
kusa ga Kamaruzzaman ya kura masa ido. Yayin
da Waziri ya ga haka sai ya kusa ya suma don
tsoro, ya tabbata halakarsu ta zo. Ya harari
Marzuwan, ya yi masa ishara da ido, wai don dai
ya daina kallon Kamaruzzaman, amma a banza.
Marzuwan ya ci gaba da kallon Kamaruzzaman,
ya http://fb.com/waziriaku tabbatar a cikin ransa
tabbas wannan shi ne wanda 'yar uwarsa take
tsanin bege.
* * * Waziri Aku * * *

Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar
labarun DARE DUBU DA DAYA, wanda littafin nanan akasuwa.(14) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI
SHAHRUZZAMAN

Marzuwan ya ci gaba da kallon Kamaruzzaman,
kamar bokan da ke nazarin wata sabuwar cuta a
jikin mara lafiya, ya tabbatar a cikin ransa tabbas
wannan shi ne wanda 'yar uwarsa take tsanin
bege, wanda sanadiyyar begensa har ake
tsammani ta zautu.
Bayan wani dogon lokaci Marzuwan yana kallon
Kamaruzzaman, sai ya daga murya ya ce, "Tsarki
ya tabbata ga Allah wanda ya halicce shi
kyakkyawar sura kamar yadda ya halicce ta
kyakkyawar sura, fuskarsa kamar fuskarta,
kundukukinsa tamkar kundukukinta." Ko da
Kamaruzzaman ya ji wannan magana, sai ya
bude idanunsa, ya karkata da kansa inda wannan
magana ke fitowa. Yayin da Marzuwana ya ga
haka sai ya waka wadannan baitoci:

"Ga ka kana murna da fadata,
Bayan da ka zan mai cuta.
Kai ka karkata gun zancena,
Wanda nake yi don kyawunta.
Kai mai bege ne na gan ka,
Ta jefe ka da kyan tsarinta.
Kowa ya gane ka yakan ce,
Wannan ta jefe shi da sonta.
Don haka tashi ka ban gorona,
Ga ni na zo maka labarinta.
Gorona na zuma zan karba,
Don jin dadin labarinta.
Ita ce wannan kyakkyawa,
Mai haske a saman fuskarta.
Ga ta da haiba ga ta da zati,
Kowa na begen muryarta.
Ta fi dukan mata a wurina,
Balle kai mai son tsarinta.
Kasko na madaci ya kan zan,
Zazzakar zumuwa don shan ta.
Ku bar zunden sa da wauta,
Ya fada tarko don son ta.
Yatsun hannunsa na duba,
Sai na ga yatsun tamkar nata.
Idan har ta shafa musu lalle,
Waye zai ce bai sha'awar ta.
Ita ce ta

1 Comments On HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHRUZZAMAN
avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Wanne darasi kuka ?aru da shi daga cikin wannan hikayar,

Please Login or Register in order to submit comment