Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

babu zanin daurawa. To, ni ba namiji ba
balle in kawar da budurcin wannan kyakkyawar
yarinya. Kuma idan na bar ta haka har gari ya
waye babu shakka Sarki zai sa a kore ni daga
kasarsa, ga shi kuma ina ji a cikin raina tabbas a
wannan gari zan hadu da mijina Kamaruzzaman.
Babu abin da ya fi sai in fada wa wannan yarinya
gaskiyar labarina, tun da dai na lura da ita tana
da hankali kuma tana da kirki, ba za ta tona mini
asiri ba."
Badura ta dago kanta, bayan ta gama zancen
zuci, ta dubi Hayatunnufusi ta ce, "Ki rantse idan
na fada miki labarina, ba za ki tona mini asiri ba."
Hayatunnufusi ta kwashi rantsuwa. Daga nan sai
Badura ta warware mata kome na game da
labarinta da Kamaruzzaman. Sa'annan ta ce, "Na
gama ki da Allah ki yi shiru da bakinki, kada
kowa ya ji wannan labari, har Allah ya hada ni da
mijina, daga nan sai mu jira abin da Allah zai
kaddara."
Hayatunnufusi ta cika da mamaki da jin wannan
labari, matukar mamaki. Ta tausaya wa Badura
da Kamaruzzaman bisa wahalhalun da suka sha
a kan soyayya har hawayenta suka yi ta zuba
kamar ruwa saboda tausayi. Ta yi musu fatar
sake saduwa da juna, ta ce, "Kar ki ji tsoron
kome, 'yar uwata, ina rokon Allah ya hada ki da
mijinki." Sai ta rera wannan waka:
"Asiri a gare ni ya tabbata cikin daki, wanda yake
kullalle kuma mabudinsa ya bace. Amma daki ko
yana kulle, asiri ba ya boyuwa face ga ma'abucin
aminci. Asiri abin boyewa ne a wurin zababbun
mutane."
Bayan ta gama waka, sai ta ce da Badura, "Ki
sani, ya 'yar uwata, Allah na rufa asirin wanda ya
rufawa dan uwansa asiri. Ni ba zan taba tona
miki asiri ba." Daga nan suka rungume juna,
kowa na zubar da hawaye. Suka kawanta a
shimfida daya, barci ya kwashe su. Can kusan
assalatu suka farka, Hayatunnufusi ta kamo wata
tattabara, a cikin tattabarunta da take kiwo, ta
yanka ta. Ta je bisa shimfidarsu ta diddiga jinin
tattabarar, ta kuma cire wandonta ta diga masa
jinin, ta sargafe shi wurin da duk wanda ya shigo
dakin zai gan shi.
Da gari ya iyar da wayewa tangaram, Badura ta
shirya ta fita fada kamar kullum. Bayan fitar ta
sai ga Sarki da matarsa sun shiga wurin
Hayatunnufusi, suna shiga sai mahaifiyarta ta yi
tozali da wandon 'yarta da jini a jikinsa, ta duba
shimfida, a nan ma ta ga digon jini, ta cika da
farin ciki ganin cewa 'yarta ta kai bantenta. Sarki
ya tambayi 'yarsa yadda ta kwana da mijinta, ta
fada masa cewa a wannan dare dai sun san
junansu a matsayin mata da miji. Sarki ya yi
matukar farin ciki mara misaltuwa. Tun daga
wannan rana Badura ta ci gaba da mulkinta tare
da Hayatunnufusi a birnin Labunus, tana sa kuma
ana nema mata labarin Kamaruzzaman. Wannan
shi ne al'amarinta.
Al'amarin Sarki Shahruzzaman kuwa, bayan
kwana daya da tafiyar Kamaruzzaman tare da
Marzuwan zuwa ga farauta, sai ya yi ta zuba ido
yana jiran dawowarsu. Da rana ta farko ta shige
ba su dawo ba aka shiga rana ta biyu, sai
hankalinsa ya tashi, ya shiga cikin damuwa mara
misaltuwa, a wannan rana ya kasa ci ya kasa
sha, babu abin da yake yi sai tunanin dansa
Kamaruzzaman tare da zubar da hawaye. Ya
hakura dai har zuwa kwana na uku, da ya ga ba
su dawo ba, nan take ya yi umurni da haduwar
askarawan yakinsa. Nan da nan askarawa suka
hadu, suka cika kofar fada, Sarki ya hau da
kansa suka fita bayan gari, suka bi sawun
Kamaruzzaman da Marzuwan.
Da suka fita daga cikin birni, sai Sarki ya raba
askarawan nan kashi shida ya tura kowane
rukuni jiharsa daban, ya ce musu su hadu nan
gobe kamar yanzu. Dukkansu suka bazama cikin
daji suna neman Kamaruzzaman. Allah da ikonsa
sai rukunin da Sarki yake ciki, suka tarar da
wurin da Kamaruzzaman da Marzuwan suka
yanka rakumi suka yayyaga tufafinsu a cikin jinin
rakumin. Nan take Sarki ya shaida rigar
Kamaruzzaman, ya sauka daga kan dokinsa, ya
ga nama faca-faca ko'ina, wanda ba za iya gane
ko na menene ba. Sarki na ganin rigar nan sai ya
kwala kara mai tsanani, ya fadi ya suma.
Askarawa suka sauka daga kan dawakansu, suka
shiga tarairayar Sarki har ya farfado. Da Sarki ya
farfado sai ya shiga rusa kuka, yana marin
fuskarsa, yana tsige gashin gemunsa. Askarawa
ma suka shiga kuka suna marin fuskokinsu, suna
zuba kasa bisa kawunansu. Sarki ya hakikance
da Kamaruzzaman ya mutu, yadda ya ga rigarsa
cikin jini ga kuma namansu, ya tabbata cewa ko
dai wata dabbar daji ce ta yi faca-faca da su, ko
kuma 'yan fashi ne suka kashe su. Bayan Sarki
da askarawansa sun gama alhinin wannan abu da
suka gani, sai suka hau dawakansu suka koma
da baya, suka hadu da sauran rukunonin
askarawa, suka nufi cikin birni.
............
Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar
labarun DARE DUBU DA DAYA, wanda littafin zai
fito nan ba da dadewa ba.(22) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHRUZZAMAN

Bayan Sarki Shahruzzaman da askarawansa sun
gama alhinin wannan abu http://fb.com/
waziriaku da suka gani, sai suka hau dawakansu
suka koma da baya, suka hadu da sauran
rukunonin askarawa, suka nufi cikin birni. Yayin
da suka isa gida, Sarki ya sa aka yi yekuwa aka
ba da sanarwar mutuwar Kamaruzzaman, aka
umurci kowa da ke cikin kasar Kalidan da sanya
bakaken tufafi na kwana uku domin nuna bakin
ciki bisa wannan http://fb.com/waziriaku rashi
da Sarki da jama'arsa suka yi. Sarki ya sa aka
gina masa kubba a wani gida nasa, aka siffanta
wani abu mai kamar kabari a cikinta, ya kira
wannan wuri kubbar bakin ciki. Ya kasance
kodayaushe Sarki na wurin wannan kabari yana
kuka yana bakin ciki tare da rera wakoki, amma
yakan fita fada ranar Alhamis da Litinin. Wannan
shi ne al'amarinsa. http://fb.com/waziriaku
Al'amarin Kamaruzzaman kuwa yana can tare da
mai lambu yana taimakonsa ga aikin lambunsa,
kullum idan ya tuna da abin da ya faru gare shi
sai ya yi ta kuka yana waka. Haka ya kasance a
wurin mai lambu har tsawon wata uku. Wata
http://fb.com/waziriaku rana yana daga cikin
lambu, yana shirin fara ban ruwa, sai ya hangi
mutanen birnin nan suna ta taruwa wani wuri,
kowane daya daga cikinsu ya ci ado ya kure
adaka, kamar dai ana wani gagarumin buki. Daga
nan sai ga mai lambu ya zo wurinsa, shi ma ya
sa kayansa ma su kyau, ya yi http://fb.com/
waziriaku kwalliya. Ya ce da Kamaruzzaman, "Ya
dana, yau ranar hutu ce a wannan birni, domin
kuwa yau ne ranar bukin ibadarsu. Rana ce da
'yan uwa da abokan arziki ke kai wa juna ziyara,
kuma yau ne ake sa ran jirgi zai zo da kayan
masarufi daga kasashen musulmi. Za su kwana
kamar bakwai suna sayar http://fb.com/
waziriaku da hajar da suka zo da ita, daga nan
kuma sai su sayi kayan lambu su koma da su.
Zan shiga cikin gari in duba in gani ko jirgin ya
iso. Ka yi zamanka yau, ka huta, kada ka yi aikin
kome, sai dai ka fara shirye-shiryen tafiya." Mai
lambu na gama fadin haka sai http://fb.com/
waziriaku ya sa kai ya nufi cikin birni.
Bayan mai lambu ya fita, sai Kamaruzzaman ya
cika da farin ciki, har hawayen dadi suka rika
zuba daga idanunsa. Ya tashi yana murna zai
koma cikin dakinsa, sai ya yi tuntube ya fadi,
http://fb.com/waziriaku goshinsa ya bugi wani
kututturen ice ya fashe, jini ya zuba daga
goshinsa har ya garwaya da hawayen idonsa. Ya
tashi zaune, ya sami tsumma ya daure goshinsa,
sa'annan ya tashi ya ci gaba da tafiya.
Yana cikin tafiya, kafin ya kai ga dakinsa, http://
fb.com/waziriaku sai ya ji fakafniyar tsuntsaye a
saman wata bishiya. Ya daga kansa sama, sai ya
ga tsuntsaye biyu ne suke fada da juna, suna ta
cire wa juna gashi. Kamaruzzaman ya yi tsaye
yana kallon tsuntsayen nan, can sai ya ga daya
ya sa bakinsa ya kame makogwaron abokin
http://fb.com/waziriaku fadansa ya matse gam.
Wanda aka matse wa makogwaro, ya yi ya yi ya
kwace, ya kasa har dai ya gaji ya kai takarda. Da
abokin fadansa ya tabbatar da ya mutu, sai ya
sako shi ya fado kasa, ya tashi sama ya nufi na
sa waje.
http://fb.com/waziriaku Mataccen tsuntsun nan
ya fado kasa a gaban Kamaruzzaman, har ya
daga kafarsa zai ci gaba da tafiya, sai ya ga
wasu tsuntsaye biyu sun sauka a kan gawar
wannan dan uwan nasu. Kamaruzzaman ya tsaya
yana kallon su domin ya ga abin da za su yi.
Tsunstu daya http://fb.com/waziriaku ya tsaya
daidai kan gawar, dayan kuma ya tsaya daidai
bindinsa. Suka daga kawunansu sama, suka kada
fuka-fukafukansu suna wani irin kuka mai ban
tausayi. Yayin da Kamaruzzaman ya ga haka, sai
ya tuna abin da ya same shi na bakin ciki,
tausayin tsuntsaye ya hadu da bakin cikinsa, ya
yi kuka tare da wadannan tsuntsaye.
Daga nan sai ya ga sun tona rami, suka dauki
gawar dan uwansu suka binne a cikin ramin nan,
http://fb.com/waziriaku suka tashi sama cikin
hanzari. Kamaruzzaman na tsaye yana mamakin
wannan abu sai ga tsuntsayen nan biyu sun
kamo tsuntsun nan da ya kashe dan uwansu.
Suka sauka da shi bisa kabarin da suka rufe dan
uwansu. Suka yi ta caccakar sa da baki har suka
http://fb.com/waziriaku kashe shi.

Suka ci gaba
da yagarsa, da kafafunsu, suna caccakar sa da
bakunansu har sai da suka bude cikinsa, suka yi
masa kaca-kaca, sa'annan suka bar shi a nan
suka tashi sama.
Wannan abu ya dimauta Kamaruzzaman, ya yi
tsaye yana http://fb.com/waziriaku kallon gawar
wannan tsuntsu wanda tsuntsayen nan biyu suka
yi kaca-kaca da namansa. Yana cikin dubansa
sai yaga wani abu yana kyalli a cikin
bulukotonsa. Ya matsa ya sa hannu ya farke
bulokoton, sai ya ga dan dutsen nan na matarsa
Badura, http://fb.com/waziriaku wanda shi ne
sanadiyyar rabuwarsu, har ya zo wannan birni.

Saboda tsananin farin cikin samun wannan dan
dutse sai ya fadi kasa sumamme. http://fb.com/
waziriaku
Bayan ya farfado, sai ya yi godiya ga Allah
madaukakin Sarki, ya ce, "Godiya ta tabbata ga
Ubangijin talikkai, hakika gane wannan dutse da
na yi, http://fb.com/waziriaku bushara ce ta
cewa nan ba da jimawa ba zan sadu da abar
begena." Daga nan ya sake duban dan dutsen
nan da kyau da rubuce-rubucen da ke jikinsa,
amma bai fahimci kome ba. Ya sami tsumma
masu kyau, ya kulle dutsen a ciki sa'annan ya
http://fb.com/waziriaku daura tsumman a
damtsen hannunsa. Ya shiga dakinsa ya zauna
yana jiran dawowar mai lambu, amma har dare
ya tsala bai dawo ba. Kamaruzzaman ya http://
fb.com/waziriaku kwanta a kan shimfidarsa,
barci ya kwashe shi, bai farka ba sai da gari ya
waye.
Yayin da gari ya waye mai lambu bai dawo ba,
sai Kamaruzzaman ya dauki kwando da fartanya
domin yin aiki kamar yadda ya saba. Ya zo gindin
http://fb.com/waziriaku bishiyar dorawa domin
ya nome ciyawar da ke wurin. Ya fara noma ke
nan sai ya ji fartanyarsa ta karto wani abu a
kasa kamar karfe. Ya kara nomawa, ya kara jin
wannan abu. Daga nan sai ya ci gaba da nome
kasar http://fb.com/waziriaku wurin, sai ya ga
wani rufi na karfe ya bayyana, ya share kasar
gaba daya sai ya ga ashe kofa ce ta bakin karfe.
Ya daga kofar sai ya ga rami ya yi kasa ga kuma
tsani ya sauka kasan ramin. http://fb.com/
waziriaku
............

Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar
labarun DARE DUBU DA DAYA, wanda littafin nanan a kasuwanninku...

Yusuf abdullahi A JIBAGA, Ke tare daku(23) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI
SAHAHRUZZAMAN

( Tare da: Bukar Mada - http://fb.com/
bukarmada )
Kamaruzzaman ya ci gaba da nome kasar wurin,
sai ya ga wani rufi na karfe ya bayyana, ya share
kasar gaba daya http://fb.com/waziriaku sai ya
ga ashe kofa ce ta bakin karfe. Ya daga kofar sai
ya ga rami ya yi kasa ga kuma tsani ya sauka
kasan ramin.

Ya tattaka matakalar tsanin ya sauka cikin ramin,
da farko duhu ya hana shi ganin kome a cikin
ramin. Bayan dan lokaci sai idanunsa suka waye
da duhun rami, sai ya ga ashe wannan rami wata
taska ce irin ta dauri wadda http://fb.com/
waziriaku Adawa da Samudawa ke yi domin ajiye
dukiya. Ramin dai wani babban dutse ne, mai
kamar girman daki, aka rarake cikinsa kamar
yadda ake rarake goran duma, aka yi masa kofa
a sama. Sai kuma aka gina katon rami aka saka
wannan dutse ciki, kofarsa na kallon sama, to,
kofar ce aka yi wa kyaure na bakin karfe. Daga
nan kuma sai http://fb.com/waziriaku
Kamaruzzaman ya ga wasu irin randuna manya-
manya, kowace tana iya boye kato kome
girmansa. Ya matsa kusa ga tukunya daya ya
duba, babu abin da ke ciki sai jan zinari,
gangariya, yana daukar ido. Ya duba sauran
tukanen ya gan su kowace shakare da zinari.
Kamaruzzaman ya ce a cikin ransa, "Ranakun
bakin ciki na gab da shudewa a http://fb.com/
waziriaku gare ni, hakika wannan dukiya tsaraba
ce Allah ya ba ni, wadda zan tafi da ita wurin
mahaifina. Mai lambu ma, daga yau Allah ya
hutar da shi daga wahala, sai dai ya rike
lambunsa domin sha'awa amma ba domin neman
kudi ba." Daga nan ya tattaka tsani ya fito daga
cikin ramin, ya mayar da kofa ya rufe, ya mayar
da kasar. http://fb.com/waziriaku Ya ci gaba da
aikinsa a cikin lambu har rana ta fadi.
Zuwa can da dare sai ga mai lambu ya dawo, ya
ce da Kamaruzzaman, "Ya dana, ina yi maka
albishir da zuwan jirgi tun jiya. Shi ne jirgin da
zai dauke ka zuwa birnin Labunus, daga can
kuma sai ka bi ayarin fatake masu http://fb.com/
waziriaku tafiya birnin Kalidan, inda za ku yi
tafiyar wata shida a kasa. Sai ka fara shiri domin
nan da kwana shida jirgin zai tashi, bayan 'yan
kasuwa sun gama ciniki. Na riga na yi magana
da madugunsu cewa idan sun tashi tafiya zan
hada ka da su." http://fb.com/waziriaku
Da jin haka sai Kamaruzzaman ya cika da farin
ciki, ya sumbaci hannun mai lambu don murna,
ya ce, "Baba, kamar yadda ka zo mini da wannan
albishir mai dadi, ni ma zan yi maka albishir
http://fb.com/waziriaku irinsa."
"Wane albishir ne wannan?" Mai lambu ya
tambaya. Kamaruzzaman ya fada masa taskar da
ya gani a cikin rami. Mai lambu ya yi mamaki
kwarai, ya yi farin ciki. Ya dubi Kamaruzzaman
ya ce, "Ya dana, ka sani cewa http://fb.com/
waziriaku shekarata tamanin ina aiki a cikin
wannan lambu, amma Allah bai nufe ni da ganin
wannan taska ba, sai kai da ka zo kwana-kwanan
nan. Don haka wannan dukiya da ka gani Allah
ne ya ba ka ita domin ka rage radadin kuncin da
ka shiga, ni kam ba ni da hakkin kome a cikinta.
Domin da rabona ce, da Allah ya nuna mini ita
tun tuni, http://fb.com/waziriaku kafin zuwanka."

Kamaruzzaman ya ce, "Kada ka fadi haka, Baba,
tamu ce mu biyu, babu makawa ka dauki rabi
daga cikinta." Daga nan ya dauki shama'a, ya ja
mai lambu suka nufi wurin ramin nan, suka shiga
cikinsa. Ya nuna masa randunan nan wadanda
suke makare da zinariya. Suka kidaya tukane,
suka ga guda ashirin ne, http://fb.com/waziriaku
Kamaruzzaman ya ce, mai lambu ya dauki goma,
shi ma ya dauki goma. Mai lambu ya ce masa,
"Gobe zan shiga gari in sayo tukwane masu
yawa, ka zuba zinariya kasan kowace tukunya,
kamar rabin tukunyar, sauran rabin kuma sai ka
cika ta da 'ya'yan zaitun na wannan lambu. Ka yi
http://fb.com/waziriaku haka ga kowace
tukunya, har ka boye zinariyar duka a cikin
tukwanen, yadda mutane za su dauka cewa duka
'ya'yan zaitun ne a ciki. Idan ka sauka kuma za
ka sayar da zaitun dinka da daraja, domin kalar
wannan zaitun ba a samun shi ko'ina sai a
wannan kasa tamu, don kyawunsa da dadinsa
ake rububinsa a kasuwannin wasu kasashe, ana
kiran kalar wannan zaitun Asafiri."
Kamaruzzaman ya http://fb.com/waziriaku
amince da shawarar mai lambu.

Da gari ya waye mai lambu ya shiga cikin gari ya
sayo tukwane masu yawa, ya samu masu jakai
suka kawo masa a lambunsa. Kamaruzzaman ya
rika dibar zinariya yana cika rabin tunya da ita,
http://fb.com/waziriaku sauran rabin kuma sai
ya tunfaye da 'ya'yan zaitun, ya rufe bakin da
ganye, har ya cika tukwane hamsin daga
randunansa guda goma, ya bar wa mai lambu
sauran goman. Ya cire dan dutsen nan da ya
daure a damtsen hannunsa, ya kwance shi daga
cikin tsumma, ya saka shi kasan daya daga cikin
http://fb.com/waziriaku tukwanen nan, ya yi wa
tukunyar 'yar alama yadda zai yi saurin shaida
ta.
Kamaruzzaman ya zauna tare da mai lambu,
suna zance amma zuciyarsa na can na sake-
sake, yana cewa a cikin ransa, "Da zarar na isa
kasar Labunus, zan bi ayarin fatake zuwa
kasarmu, daga can sai in shiga neman http://
fb.com/waziriaku masoyiyata Badura. Ko a wane
hali take ciki yanzu? Ko sun ci gaba da tafiya ne
zuwa kasar mahaifina, ko kuwa juya suka yi da
baya zuwa wurin mahaifinta? Ko kuwa dai wani
hatsari ya same su a kan hanya?" Haka dai ya yi
ta tunani a cikin ransa. http://fb.com/waziriaku
Da mai lambu ya lura da cewa shi kadai ke ta
zuba hira kamar aku, hankalin Kamaruzzaman ba
ya wurinsa, sai ya kyale shi. Shi ma ya shiga
lissafe-lissafen abin da zai yi da tasa dukiyar.
Bayan Kamaruzzaman ya dawo daga duniyar
tunani, sai ya fada wa mai lambu labarin abin da
ya gani na mamaki game da tsuntsaye. Suka yi
ta kakabin abin har barci ya kwashe su. http://
fb.com/waziriaku
Yayin da gari ya waye, sai mai lambu ya tashi da
masassara. Cikin kwana uku sai masassara ta
zama zazzabi mai zafi, ya zama daga kwance sai
kwnace, wani lokaci kuma sai ya suma,
Kamaruzzaman ya rika kuka saboda ganin halin
da yake ciki. http://fb.com/waziriaku A kwana
na hudu sai ga madugun jirgi ya zo kofar lambun
ya kwankwasa kofa, Kamaruzzaman ya tafi
wurinsa. Madugu ya tambaya, "Ina mutumin da
za mu tafi da shi birnin Labunus?"
Kamaruzzaman ya ce, "Ai ni ne." Madugu ya
tambaye shi, http://fb.com/waziriaku "Kana da
kaya ne?" Kamaruzzaman ya amsa, "Ina da
tukwane hamsin na 'ya'yan zaitun." Madugu ya
ce, "To, ka shirya zan turo bayi yanzu, su dauki
kayan a saka a cikin jirgi. Kai kuma gobe da
alfijir ya keto, ka tabbata kana cikin jirgin, domin
http://fb.com/waziriaku akwai alamun iska mai
kyau wadda za ta dace da yanayin teku."
Daga nan Madugun jirgi ya koma, cikin dan lokaci
kankani sai ga bayi ya turo. Suka kwashi
tukwanen Kamaruzzaman suka tafi da su zuwa
ga jirgi, shi kuwa http://fb.com/waziriaku
Kamaruzzaman ya koma inda yake jinyar mai
lambu. Tun cikin dare rashin lafiyar mai lambu ta
yi kamari, gari bai waye ba sai da ya ce ga
garinku nan. Kamaruzzaman ya yi kuka mai
tsanani a kan mutuwar http://fb.com/waziriaku
mai lambu, ya yi bakin ciki, bakin ciki mai yawa.
Ya dauki magirbi ya haka rami, ya yi wa mai
lambu jana'iza, ya yi masa addu'ar neman gafara
ga Allah madaukakin Sarki. Ko da ya gama rufe
shi har rana ta take. Ya kulle 'yan kayansa, ya
fita daga cikin lambu da hanzari, ya http://
fb.com/waziriaku mayar da kofa ya rufe, ya nufi
gabar teku wurin jirgi. Da isarsa wurin sai ya
hangi jirgi ya nausa cikin teku. Ya yi kira, ya yi
daga hannu, amma duk a banza, jirgi bai tsaya ba
balle http://fb.com/waziriaku ya juyo. Ya yi
tsaye yana kallon jirgi har ya bace a cikin teku.
Kamaruzzaman ya juya ya koma cikin http://
fb.com/waziriaku lambu zuciyarsa cike da bakin
ciki. Ya zauna yana kuka yana marin fuskarsa,
yana zuba kasa bisa kansa don bakin ciki.
............
Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar
labarun DARE DUBU DA DAYA, wanda littafin nanan a kasuwa.

Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ ke tare daku(24) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI
SHAHRUZZAMAN

( Bukar Mada - http://fb.com/bukarmada )
Kamaruzzaman ya juya ya koma cikin lambu
zuciyarsa cike da bakin ciki. Ya zauna yana kuka
yana marin fuskarsa, yana zuba kasa bisa kansa
don bakin ciki. Ya tuna cewa yanzu shi kadai zai
zauna a cikin lambu, ga shi kuma ya sake
rabuwa da dan dutsen nan na Badura. Yanzu shi
da fita wannan kasa sai kuma wata shekara idan
jirgin ya dawo. Ya ci gaba da kuka, yana rera
wakoki. Bayan kwana biyu, ya ci gaba da aikin
lambu kamar yadda ya saba, ya shiga tasakar
nan ya kwashe sauran zinaren nan, rabon mai
lambu, ya zuba shi a cikin wasu tukwane hamsin,
ya zuba 'ya'yan zaitun a sama, ya sa ganye ya
rufe. Ya zauna jiran dawowar jirgi wata shekara.
Wannan shi ne al'amarinsa.
Amma jirgi kuwa ya ci gaba da tafiya cikin teku
dauke da tukwanen Kamaruzzaman, iska kuwa ta
yi masa kyau har ya isa birnin Labanus. Bisa
kaddara, lokacin da jirgi zai tsaya a bakin gaba, a
lokacin kuma gimbiya Badura tana zaune a bakin
taga, bisa benen gidanta, tagar kuma tana kallon
teku. Sai ta ga wannan jirgi na 'yan kasuwa
dauke da kaya niki-niki. Tana ganin wannan jirgi
sai ta ji gabanta ya fadi, amma ba ta san dalili
ba. Nan take ta sauko daga kan bene, ta debi
wasu askarawa suka nufi wurin jirgi.
Yayin da ta isa wurin jirgi har dillalai da 'yan
kasuwa masu sari sun kewaye jirgi suna jira a
fara fitowa da kayan cikinsa. Yayin da jama'a
suka ga sabon Sarki da askarawansa, sai suka ja
da baya, suka fadi suka yi gaisuwa. Badura ta
matsa kusa ga madugun jirgi ta tambaye shi,
"Wace haja kuka zo da ita?"

Madugun jirgi ya amsa da cewa, "Allah ya ba ka
nasara, mun zo da yadiddika, da zannuwa, da
kwayoyin magani, da kayan kwalliya na mata,
irinsu; katambiri, hoda, jagira, janbaki, kwalli,
turare na ruwa da na hayaki. Akwai kuma kayan
lambu irinsu, karas, albasa, tafarnuwa, citta,
gauta, yalo. Da kuma 'ya'yan itatuwa kamarsu,
lemu, mangwaro, gwaba, tuffa, inabi, tsada, da
kuma 'ya'yan zaitun na Asafiri wanda babu irinsa
a wannan kasa. Kadan ke nan daga cikin dimbin
kayayyakin da muka zo da su, Allah ya
taimakeka."
Lokacin da Badura ta ji ya ambaci 'ya'yan zaitun
sai yawunta suka tsinke, domin kuwa babu
abinda ta fi sha'awar ci kamar zaitun. Ta kuma
tambayarsa, "Wane adadi kuka zo da shi na
'ya'yan zaitun?"

Madugu ya dukar da kansa kasa ya ce, "Allah ya
ba ka nasara, tukwane hamsin ne kawai muka zo
da su, ko su ma na wani mai lambu ne, saurayi,
wanda ya yi jinkiri bai zo ba har jirgi ya baro shi
a can."
Badura ta ce, "Babu makawa ku sayar mini da
dukkanin tukanen nan guda hamsin, da akwai
wasu ma, da na saye su duka. Zan biya ku kudin,
duka lokacin da kuka koma sai ku ba shi
kudinsa."

Madugu ya ba da umurni aka sauke tukwanen
Kamaruzzaman. Badura ta matsa kusa ga
tukunya daya ta yaye ganyen da yake samanta.
Ta ga 'ya'yan zaitun masu kyau, ta mayar da
ganyen. Ta juya wurin Madugun jirgi ta ce masa,
"Nawa ne kudin wannan zaitun?"
Madugu ya ce, "A kasar da muka fito ba shi da
wani daraja sosai, dududu kudinsa ba zai wuce
'yan daruruwan dirhamai ba."
Badura ta ce, "To, a nan fa, kudinsa zai kai
nawa?"
Madugu ya ce, "A nan kasar kuma kudinsa zai
kai dirhami dubu, Allah ya ba ka nasara."

Nan take Badura ta jawo lalitarta ta kirga dirhami
dubu ta ba Madugun jirgi, ta umurci askarawa
suka dauki tukwanen 'ya'yan zaitun, suka juya
zuwa gida. Da dare ya yi, bayan Badura da
Hayatunnufusi sun gama cin abinci, sai Badura ta
dauko tukunyar zaitun daya ta zazzage a cikin
akushi domin su ci, sai suka ga jan zinare na
zubowa tare da 'ya'yan zaitun daga cikin
tukanyar. Ta dubi Hayatunnufusi cikin mamaki ta
ce, "Wannan ai zinariya ce!"
Cikin gaggawa suka tashi suka dauko sauran
tukwanen, suka zazzage su a cikin dakin, a cikin
kowace tukunya suka ga tamkar yadda suka gani
ga ta farko. Wannan abu ya yi matukar ba su
mamaki da kuma daure musu kai. Garin tone-
tonensu sai Badura ta tono dan dutsen nan nata
a cikin zinarin, ta dauke shi ta duba sosai, ta
gane dan dutsenta ne wanda Kamaruzzaman ya
kwance a kubakar wandonta, ranar da ta tashi ba
ta gan shi ba. Nan take ta yi wata irin kara don
farin ciki, ta fadi kasa sumammiya.

Bayan ta farfado, ta nuna wa Hayatunnufusi dan
dutse, ta ce, "Wannan dan dutse da kika gani shi
ne sanadin rabuwata da abin begena, babu
shakka kuma yanzu shi zai yi sandin sake
haduwarmu." A cikin wannan dare dai, babu
wadda ta runtsa tsakanin Badura da
Hayatunnufusi don farin ciki. Gari na wayewa,
Badura ta kintsa ta fita fada ta kame bisa
karagar mulki. Ta aika maza-maza a zo mata da
Madugun jirgi.
Yayin da Madugun jirgi ya zo sai ya fadi a
gabanta ya yi gaisuwa, fadawa suka ce, "An
gaisheka!"
Badura ta dubi Madugun jirgi ta murtuke fuska,
ta yi masa magana cikin tsawa, "Ina kuka baro
mai zaitun din nan?"
Madugu ya sunkuyar da kansa kasa ya amsa,
"Allah ya taimake ka, mun baro shi ne a garin
Matsafa, bayan ya sa kayansa a cikin jirgi sai ya
yi jinkiri bai zo ba har jirgi ya tashi."

"Babu makawa ku koma ku dawo mini da shi." In
ji Badura. Ta ci gaba da cewa, "Domin kuwa ya
aikata mana laifi mai girma wata shekara da ya
kawo mana 'ya'yan zaitun, ya yi mana sata ya
gudu. Zan sa a tsare dukkan kayan da kuka zo
da su, idan ba ku kawo mana shi ba kuwa, to,
zan sa a nemo ku duk kasar da kuka shiga a
yanka ku daya bayan daya."
............
Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar
labarun DARE DUBU DA DAYA, wanda littafin nanan a kasuwa'..

DAGA ==>Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ(25) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHRUZZAMAN

( Bukar Mada - http://fb.com/bukarmada )
"Babu makawa ku koma ku dawo mini da mai
kayan nan." In ji Badura. Ta ci gaba da cewa,
"Domin kuwa ya aikata mana laifi mai girma
wata shekara da ya kawo mana 'ya'yan zaitun,
ya yi mana sata ya gudu. Zan sa a tsare dukkan
kayan da kuka zo da su, idan ba ku kawo mana
shi ba kuwa, to, zan sa a nemo ku duk kasar da
kuka shiga a yanka ku daya bayan daya."
Madugu ya koma wurin 'yan uwansa ya kwashe
abin da ya faru tsakaninsa da Sarki ya fada
musu. Ya ce da su, "Babu makawa yanzu in
koma garin matsafa domin dauko yaron mai
lambun nan da muka baro." Aka sauke wa jirgi
kaya, Madugu ya shiga ya tuka shi, ya karkata
fuskarsa ga jihar da suka bar Kamaruzzaman. Ya
yi ta keta ruwa dare da rana, babu tsayawa.
Allah mai iko ya nufe shi da isa birnin matsafa a
cikin dare. Ya daure jirginsa bakin gabar teku, ya
nufi lambun da Kamaruzzaman yake.
A cikin wannan dare kuwa, Kamaruzzaman na
zaune yana tunanin abar begensa, har yana rera
wadannan baitoci:
"Wannan dare ya yi tsawo, har taurari sun ki
gushewa. Daren da saboda tsawo nake ganinsa
tamkar yinin tsayuwar Alkiyama."

Yana cikin rera wannan waka sai ya ji ana
kwankwasa kofar lambu. Ya tashi domin ya ga
mai kwankwasa masa kofa. Yayin da ya bude
kofa Madugun jirgi ya gan shi, sai ya cafki
hannunsa ya nufi wurin

1 Comments On HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHRUZZAMAN
avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Wanne darasi kuka ?aru da shi daga cikin wannan hikayar,

Please Login or Register in order to submit comment