Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

san ai ana yin sub'pit ɗin course a university ɗan biology yayi chemistry, haka dan chemistry yayi biology, balle a Umyu lavel one to two dis-some course ake yi masu, yan biology da yan chemistry daya ake yi masu har sai sun shiga level 3 suke raba course, amman duk da haka akwai wani course da dan chemistry bai yi sai dan biology dole haka shima dan chemistry dole akwai course din da zaiyi wanda sai only chemistry students zasu yi su, haka others course ma haka abun yake su physics da maths da computer and so on dai👌)


"Ok, give me the meaning of Biology, "biology is the branch of science that deal with the studyof life. Eg plant and animal(cell)..


"Ok very good difination, so class who can give me the meaning of cell?


"Sir, "ok stand up, ur name? "My name is Nana Jawaheer Adam, depertiment of Biology..


"Ok Nana Jawaheer what is cell?

"Cell is the basic structural unit of life;the smaller part of a living things (organisms) that can carry out of life processes by it self...



"Woow, very nice my intelligent students, so who can tell me cell are in divide into what?


"Any one? Ko sai nayi pointing ne? "Sir, "ok ur name? "Abdulraham munnir, "ok cell are divide in to what? "Sir into two, "are you sure? "Yes sir, "ok tell me the names? "Plant cell and animal cell(Eukaryote and Prokaryote)


"Very good, sit down"..


```Dan Allah in nayi mistake a gayaman wajen meangings din harda ma turanci dan ni har yanzun koyo nike🙈```


Nan Dr Tofik ya baje ma su Nana cell sai da ya tabbatar da sun gane sannan time din shi yayi ya fita yana suka tafi lectures din IN-ORGANIC CHEMISTRY a students center theater..


Kafin su shiga theater sai da suka shiga city compus suka ci abinci sannan suka shiga suka samu waje suka zauna, bayan sun dan huta sai ga lecturer din ya shigo...

"All of you sit down my friends, and stop making noises"...


Nan fa aji yayi shiru kowa ya samu waje ya zauna ana sauraren lecturer..


"My name is Khalid haliru"..


(note:-Khalid haliru shima lecturer ne a Umyu amman Depertiment of chemistry shi da gaskiya akwai shi dan duk wani dan Umyu Indai sciences yake ya san Khalid haliru, kuma shi yake daukar level one in-organic chemistry, shiyasa na sashi yanda zan gane sosai)

"Today am discuss to you periodic table part of the chemistry, before class who give me the meaning of chemistry?


"Sir, ok stand up, ur name? "My name is Nana Jawaheer Adam department of Biology, "ok give me the meaning of chemistry..


"Chemistry is the branch of science that deal with the study of matter or component of compound...


"Ok sit down, that class who tell me the name of this latter(Na)?

"Sir, againt uh ok tell me, "SODIUM (Na) "sit down very good student, so class who tell me the Name of this letter(Ca)?


"Sir, stand up, ur name? "Am Aminu Idris by name, "ok tell me the name of that latter (Ca) "...


"calcium (Ca), nan dai malam Khalid ya gama yi masu bayani akan periodic table sannan ya sallamaisu, su Nana sune basu koma gida ba sai six..


Bayan Nana ta huta taci abinci nan suka yi fira a parlour bayan sun gama fira taje ta kaima Sadiq coffee sannan ta dawo daki suka fara fira da Salma.....

"Salma, "uhmm JJC😉, ina jinki naga sai wani kallo na kike, "kawai dai! "kawai dai mai?, talk mana kina ta wani boyeye, "Nidai kawai soyayyarki da yaya Lukman tana burgeni sosai...




"Hmm yarinya kenan, To bari na gaya maki, ba mata kawai ba harda maza, Nana in dan kika samu masoyin gaskiya riƙe shi da kyau da Amana, karki yarda kice sai mai mota ko kuma wanda yayi degree...


"Yanzun abunda mu yan matan zamanin yanzu muke cewa mu bamu son kowa sai mai mota, Ƙaton gida, degree! Ikon Allah duniya Baki duba halin shi, shi wane yace yana sona! Waye shi ya tarbiyarshi take? Ya ilimin shi yake, ba dole sai dan boko ba, Aah wallahi zamanin nan boko baya aiki, kawai dai ya sana'ar shi take, yana da sana'a, sana'ar wanda zai rike ki da ita wanda kema zaki taimakama na kasa dake, shin yana da gida ba dole sai mai katon gida ba, ke dai ki san yana da muhalli kin san Allah kuka yi aure ba mai jinku dan tun farko soyayyar gaskiya kuka gina....




"Su kuma mazan sun sama kansu karya, ka rabu da duk wata karya ka samo mai sonka tsakani da Allah, Maza! Maza!! Maza!!! Nidai gaskiya nike gaya maku, karda ka kuskura ka tarkaci aure baka da gidan kanka, uhmm *GIDA* *HAYA* ```(sunan novel din maizuwa insha``` ```Allah)```


" gidan haya wallahi tonin asiri ne, wajen chanza gida kayan dakin matarka zasu gantale a kan titi, ga biyen kudin haya ga neman na abinci🙆‍♀️ to dan Allah da wani zaka ji🤔? Ai gwara ka ji da daya mana ba biyu ba...




"Yan'uwana mata,Mata! Mata!! Mata!!! Wallahi yar'uwa karki sake ki auri wanda baida gida, in ba kaddararki ce haka ba..


" matso kiji👂🏽ko mai *HILI* ban ce ba a shawarata ya samu ya gina koda sitting room and bedroom ne sai kitchen and toilet....




"Sun ishe ki zaman duniya bana kiyama ba, wannan duniyar fa mutuwa ake ba zama a kazo yi ba balle kace dole gida sai flate house, ko kuma Aa ai a novel na karanta wani gida ni dai the some kallarshi nike so...



"Ji man dan Allah dasa kai shiga uku, shi fa novel labarin kazan kurejeni, dan mai zaki sama zuciyarki abunda baki samu?




(Wallahi serious talking my sisters, watarana ina cikin chatting sai kawai aka yi man SLM, nace was-sallama, bayan mun gama gaisawa da matar take gaya man tana bin novel din Nana Jawaheer nan taga number na shine tayi man magana, ni kuma nace mata nagode, shine take gaya man aure tayi, sun hadu da mijin a media, sun hadu a Instagram sunyi soyayya wanda sukayi na girma dan harda key din mota ya bata, sannan lefenta set hudu ne ko wane set complete ne, ga uban gida da ya gina mata, tace tunda ya nuna kudi basu yi bincike a kanshi ba haka a kayi aure, bayan aure da kamar sati ya Anshe key din mota, ana nan ana nan yazo ya kwashe duka lefenta ajiye, ya duba abunda babu ya sawo, wai bayan wannan kuma sai ya sake mata gida wani banzan gidane, wanda gidan ubanta yafi wanda ya kaita, anyi bakin duka duka da wata daya taji ya sake sabuwar amarya, lefenta shi ya kaima wacce amarya, na kai ku karshe ashe ita ce mace ta biyu da ya aura amman yace mata baida mata, sai wannan amarya itace ta uku, dan haka ku kiyaye kun san wa zakuyi ma'amila da shi kibar hangen dala yar'uwa kar kiyi soyayyar kudi😇😊)




"gaskiya hakane Salma, yanzun ko in kana da mota, to ana sonka ba ruwan yan'matan yanzun da hali mutun wani kallar hali gareka, su dai kawai kudi🤨..



"Aiko suna da aiki, "aiki kuma Salma? "Eh Nana suna da aiki sosai, je ki kaima Sadiq coffee sai ki dawo na gaya maki kallar aikin da ke garesu, "to shikenan, na tafi...



"Yaya Sadiq ga coffenka, "zauna to saurin mai kike? "Bakomai bacci nike ji ne shiyasa, gashi wai eight garemu again mudai ba'ason mu..


"Yarinya kenan, haka zaku dunga eight kenan har sai kun zo second semester sannan I think zaku fara ten kuma zaku samu ku rage eight,"to Allah yasa...



"Yaya Sadiq wallahi na gaji sosai, yau tun eight muke lectures sai four muka gama, muka biya hostel gun An'babi can mukayi sallah muka dan huta sannan mu ka dawo bus'stop muka shiga bus..


"Sannu kin sha wuya, kin dai sha coffee din kema ko? "Eh na sha, "ok tashi ki tafi sai da safe...


"Salma na dawo gaya man pls, "to Nana uwar yar'san labari, ke baki ba kowa labari, amman kina san a baki...



"Kin san mai yasa nace suna da aiki? "Aah, "to saboda da yanzun samarin Aron mota suke, ke harda ma kaya samarin yanzun Aro suke balle mota, sai kiga mutun har mutun amman ya kashe zuciyarshi da karya, sai bayan aure kaga abu ya chanza, sai aka ma fada daga nan sai saki, shiyasa yanzun zawarawa suka yi yawa a hausawa, sobada ba soyayyar gaskiya aka yi ba, ina sonka dan abun hannunka, tom abun hannu babu ba ko daya kinga dole ayi fada, ina sonki saboda wani abu na jikinki, tom abun jikinki ya gama amfani a waje shi shin aure zai zauna? "Aah Salma gaskiya baya zama, "to kinji da dalilin daya sa nace suna da aiki, yanzun dai Nana mu kwanta kinga har 11 tayi bacci ya dace muyi saboda wannan 8 din da muke fita kullun, "to sai da safe.


Washe gari, bayan sun gama breakfast suka shirya suka tafi, Dady ya ba Salma mota dan haka ta hau motarta ta dauki hanyar FMC, su kuma su Nana suka dauki hanyar Umyu..


"Nana, "Naam yaya Sadiq, "cikin weekend zaki rakani wani kauye, kuma kwana biyu zamuyi tun Friday...


"To shikenan, Allah ya kaimu lafiya, amman kwana biyu baiyi yawa ba? "Ban sani ba, Nana wallahi ki koya zuminci, zuminci abu ne mai kyau dan haka ki kiyaye, "to Yaya naji insha Allah zan kiyaye..


Nan suka ida shiga Umyu Sadiq ya ajiye Nana department shi kuma ya wuce cleaning...


"Dr Sadiq Sannu da zuwa, "yauwa Dr Nura, ya aiki? "Alhmdulh aiki ga shinan muna yi sai dai hakuri, "Allah ya kara mana hakuri, "Amin..


Bayan Nana sun shiga lecture din G. S. P(communication in english 1)bayan sun fito lecture din gsp sannan suka shiga lecture din machanise(physics) haka dai Nana ta wuni lecture sai six suka taho, suna zuwa bus stop suka tadda ba bus duk sun dauki students sai sun dawo suna tsaye sai ga Khalid...


"Hello my Jawaheer, ku taho mu tafi gida mana, "Aa my Khalid, kawai ka tafi mun gode sosai, "saboda mai ba zaki hau motana ba? "Nidai haka nan bakomai my Khalid, "to in babu komai ki shigo na kai ki gida, haka Nana ta shiga ba dan taso ba, shi kuma Sadiq yana can yana sauri ya zo ya dauki Nana, amman yana kallon Nana ta shiga motar Khalid ba karamin bakin cikin yayi ba, haka ya taho gida rainshi bace..


"Nana zonan indan kin gama cin abincin ki sa mai ni a garden, "to yaya Sadiq, bayan ta gama cin abinci ta tashi ta tafi garden a can ta iske Salma da Lukman suna soye warsu..


"Yaya Sadiq gani, "ai na ganki, Nana! Wai sai yaushe zaki fara jin magana ne? "Yaya Sadiq mai nayi? "Ban sani ba Nana, yau bisa mai kika dawo gida? "Bus mana yaya Sadiq, "Nana yaushe kika fara yin karya? "Yaya Sadiq yi hakuri ba zan sake ba, "kullun haka kike cewa nayi hakuri baki sake wa amman a banza, dan haka tashi ki ban waje na san maganinki, "dan Allah yaya Sadiq, nan Nana ta fashe da kuka tana ba Sadiq hakuri..


"Sadiq, "Naam Man! "Mai tayi ma haka wai take kuka? Bayan naga zuwanta ba kuka take ba..



"Hmm Man kenan, na gaji da abun da Nana take yi man a cikin gidan, shin zaki tashi ki ban waje ko sai na balballaki, "yaya Sadiq, "Nana tashi ki ban waje nace, yayi mata yawa wata uwar tsawa, ai Nana bata san fitsari ya kunce mata ba nan ta zubai kasa sumaimiya ...


"Man dan Allah help me, Wayyo Allah Nana karki mutu pls, "haba Sadiq ya kake yin haka kaima? Ya kamata ka ringa yin control din kishinka akan Nana, yanzun gashinan ko? ..



"Nidai dan Allah Man kayi wani abu, "sai kace ba doctor ba, baby bani ruwa mai sanyi sosai, nan Salma ta kawo ma Lukman ruwan sanyi ya watsa ma Nana, sai ga su Nana ta bude ido tana kuka tana...


"Yaya Sadiq dan Allah kayi hakuri, wallahi ba zan sake ba, "tashi nayi hakurin, amman karda ki sake maimai haka kinji? "Eh naji, "yauwa gud girl tashi ki shiga cikin gida...



Dare nayi Nana ta kai ma Sadiq coffee, bayan ya gama sha ya sake yi mata fada akan ta kiyaye, baya son ta na hawa motar Khalid, nan tayi mashi promise din ta daina..



Yau Friday Nana sai 10 take da lecture, bayan ta tashi ta gama gyara ko ina ta wuce part din Sadiq shima ta gyara mashi dakin shi harda new bedsheet ta shimfida mashi, sanann ta shiga tayi wanka ta wuce national ta hau bus ta wuce school, bayan sun gama lecture ta biya cleaning suka wuto tare da Sadiq suna zuwa gida suka fara shiryawa zasuyi tafiya, Sadiq yaji dadi sosai da Nana ta gyara mashi dakin shi...


Bayan sun gama shiryawa suka yi ma su Ammi sallama nan suka dauki hanya...



"Yaya Sadiq,"Ina jinki, "yaya Sadiq nifa ban san ina zamu ta fi ba, "saida ki zanyi a bani kudin, "Wayyo Allah dan Allah Yaya ka gaya man ina zamu tafi, "yi man shiru in munje kin gani, "to shikenan, na hakura..

______________________________



"Baby, "Naam Baby, "nifa har yanzun ban gane tsakanin Sadiq da Nana ba, ina san kayi man bayani..


"Ok ba wani abu bane mai wahalar ganewa ba Baby, shi Sadiq son Nana yake tun tana yar karamar ta, amman har yanzun bata san yana sonta ba, wanann dalilin yasa ta fara soyayya da Khalid, dan yanzun ita Nana tana bala'in son Khalid...



"Haba Baby ai harda laifin ka, "laifina kuma? "Eh laifinka, mai zai hana kai ka nuna ma Nana Sadiq yana sonta, tunda kai bakayi haka ba ni Salma zanyi wanann aikin, insha Allah kafin na bar katsina sai soyayya mai karfi ta kullu tsakanin Jawaheer da Sadiq, "Allah yasa Salma mu duka gidan nan abunda muke guri kenan,"Laa Momy she kina nan?


"Eh nazo wucewa naji kuna maganar abunda yake damuna kenan, dashi nike kwana da shi nike tashi, bani ɗaya ba duka mutanan gidan nan, ni tuni na gane Sadiq yana son Nana, saboda wani abubuwan da yake yi mata, kawai sa ido nayi, amman Salma ke ce zaki taimaka mani wajen ki samu ki janyo hankalin Nana wajen Sadiq..


"To insha Allah, Momy zanyi iya bakin kokarina nayi alkwarin haka, "yauwa Salma Allah yayi maki albarka,"Amin Momy...

_________________________

"Talatu ina yarinyar nan take wai? "Wallahi Malan nima kwana na biyu ban sata a ido ba...



"Shikenan Talatu, kiyi hakuri ki bar Khadija tayi abunda take so, tunda ta nuna tafi karfinmu ai bata fi karfin duniya ba...


"Baba ina wuni? "Lafiya lau Sabi'u, daga ina haka nagan duk kasha wuya? "Wallahi Baba daga neman kudi, da man wata kwangilar ce aka ɗauks muna cikin bur'kina,"to Sabi'u Allah ya taimaka, ka kula kaji? "Insha Allah Baba..

____________________


"To kasa uwar bacci, sai ki tashi mun iso ko, "har mun iso yaya Sadiq? "Eh mana gashi tunda idonki ya ga ne maki..



"To fito mu shiga ciki mana, "yaya Sadiq dan Allah nan wani kauye ne haka nike ganin masu kyau da yawa? "In kin shiga wancan gidan zaki gane ko wani kallar gari ne, nan su Nana suka ɗauki hanyar shiga cikin gida tana yin sallama....


"Amin wa'alaikumus sallama, "Aah wai Sadiq ne kenan ku shigo kai da wa nike jin maganar mace?


"Shigo mana Nana, "Yaya Sadiq tsoro nike ji, ji nike kamar zan ga wani abu, "ba abunda zaki gani sai alkhari dan haka bissimilla, nan dai suka shiga jikin Nana duk a sanyaye, bayan sun zauna sai ga wata mata ta fito tana cewa...


"Lale marhabin da Sadiq yaron albarrrka, Sadiq wa nike gani kamar Nana Jawaheer? "Mama nice, nan Nana ta tashi ta rungume Maman ta suna kuka su dukansu....



"Aah Mama, dan Allah ba kuka zakuyi ba, godema Allah zakuyi da ya sake kaddara haduwarku, "haka ne Sadiq nagode Allah yayi maku albarka, "Amin Mama...



Nan fa aka kawo masu fura da nono mai kyau suka sha, Sadiq bai bar garin ƙarƙarku ba sai bayan sallahr la'asar sannan ya wuce gida sai ranar Sunday zai dawo ya dauke ta...


"Nana Sannu, haka kika koma? kin zama budurwa, "Laa Mama, ya na samai ki? "Lafiya lau Nana ya bayan rabuwa, nan fa Nana ta bata labarin wahalar da tasha wajen Talatu har dawowarta gidan su Sadiq....



"Yanzun kina da saurayi Nana? "Eh Mama, "ya sunanshi? "Khalid, "waye haka kuma? "Shine wanda ke sona, "Nana ban yarda ba, "baki yarda ba Mama? "Eh Nana ban yarda ba, dan haka tun wuri ki fidda son shi cikin rainki...



(to fa ga wata sabuwa kuma☺️)



"Mama, "karki ce man komai Nana, tun randa na haifeki nida mahaifinki muka yi maki miji, kuma nayi Naam da mijin da mahaifinki yayi maki ..


"Mama, da man Baba yayi man miji? "Eh yayi maki miji, dan haka ki gyale wannan Khalid din kinji Nana, "to Mama, amman ya sunan mijin? "Nan gaba zaki sanshi Nana, dan haka wuce ki kwanta bacci sai da safe...



_By jameelah jameey_ 🖋




Share and comment pls


08160508316 ```inkina bukatar shiga group din NANA JAWAHEER dan gaskiya na gaji da tambyata da kuke daga farko inkinshiga group kin samu daga farko☺️```


🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕
*NANA JAWAHEER*
🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕

*STORY AND* *WRITING BY*
*Jameelah A Belloh*
*(Jameey)*


*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻```

_________________________________


*BISSIILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*



❌❌❌NO EDITED 😰



Page 3️⃣0️⃣➖3️⃣5️⃣






Washe gari bayan sun gama duk abunda zasu yi suka shirya suka tafi school...


"Yaya Sadiq, "Naam Nana, "gobe ne fa CA test din nan, "to akwai inda baki gane ba? "Eh bani gane configuration ba baki daya yaya Sadiq, "yanzun Nana configuration din ne baki gane ba? "Eh yana bani wahala ina san nagane yanda ake fidda atomic mass ne, da yanda zani ringa gane P block da F block, "ok ki bari yau zan nuna maki, in-organic kawai za kuyi? "Aah duka week din nan test zamuyi kaga saura two week mu fara exams, "ok ki maida hankali, kiyi karatun baki daya tunda ba wani nisa ke akwai ba tsakanin test da exams ba, "to insha Allah...


Haka Nana yau ma suka sha lectures dan har sai da ta kusa kuka, dan ko wani malami so yake yayi covering shiyasa suka kama yin lectures, dan harda fixing duk sai da aka sa masu, itace bata bar makaranta ba sai six sannan suka dawo gida..
_____________________________


"Sabi'u, "Naam Inna, "Sabi'u wai mai nayi maka kake yi man haka cikin gidan nan, bayan ni na haifeka..


"Ni kawai bani son kina matsaman ne, sannan kin sani na matsa ma yar'uwata Nana cikin gidan nan ba abunda bamu yi mata ba, kuma ke kike zugani har bugunta munsha yi ba sau daya ba cikin gidan nan, to Allah ya nuna man gaskiya shiyasa ba ruwana dake dan ni yanzun so nike Nana ta yafeman, Allah yasoni da rahama ya nuna man gaskiya tun yanzun da taimakon Baba kuma, da ba dan Baba yasa man ido cikin lamarina da tuni na zama cikankin dan kidnapped saboda sakakinki, Alhmdulh Baba ya janyoni jiki ya nuna man hanyar gaskiya kema Allah ya ganar dake, kinga tun ba'aje ko ina ba Khadija ta tsallake gida ta shiga duniya...


"Yo sai mai dan kafita daga harka ta, da man nasan shiga tsakanin mu akayi, aka rabani da dana na cikina, Allah ya isa tsakani na dake Nana kin shiga ke da dangin uwarki kun rabani da Sabi'u to ta Allah ba ta kuba...



"Kuma da kake yi man korin Khadija ta shiga duniya, ai kafin Khadija ta shiga duniya ita Nana ta fara shiga tunda ita ubanta da kanshi ya kaita yawon duniya aka fake mana da wani ta koma gidan Sulaiman, in gaskiya ne ai da ko sau daya ta zo gaidashi...



"Hmm Inna kenan, ana gaya maki gaskiya kina rintsa ido, kina yin kishi da baiwar Allah wanda bata san komai ba, kin wahalar da baiwar Allah da bauta kala-kala, kina cucarta kina yi mata hassada bata ji ba bata gani ba, dan yanzun Allah ya fidda ta daga azabarki shine kike bakin ciki ko? To nima daga yau baki sake ganina, nabarki da halinki saduwar alkhari Allah ya ganar da ke gaskiya kafin ki mutu...



"Sabi'u karka tafi ko'ina, amman ina Sabi'u, ya tafiyarshi ya barta dan shi ya gaji halin maihaifiyarsu in baiyi nisa da ita ba watarana zaiyi abun kunya dan Sabi'u, yana da zuciya sosai...


Nan Inna ta duge wajen daya ta kama kuka, sai da tayi mai isarta sannan ta tashi dan kanta ba mai lailashinta....


Tunda Sabi'u ya fita bai zarce ko ina ba sai wajen Babanshi, nan ya gaya mashi yanda sukayi da Inna, sannan ya rokeshi alfarma ya barshi ya tafi logos zai nemi kudi daga nan zai saya jamb ya shiga university dan ya gaji da zaman banzan da yake ba sana'ar yi kuma ba karatu...


Malan Adamu ba dan yaso ba haka ya bar Sabi'u ya tafi logos neman kudi, bayan yayi mashi wa'azi sosai dan sai Sabi'u yayi kuka ji yake kamar yace ya fasa tafiya neman kudin, amman ina neman kudi dole ne a wajenshi tunda shi namiji ne, haka su kayi bankwana da mahaifinshi bayan sunyi exchanging numbers....


______________________________

Bayan Nana ta gama huta sosai ta dauki handout dinta ta wuce wajen Sadiq dan yayi mata tutorials din karatun ta..



Bayan ya gama yi mata tutorials din, ta ga ne sosai da sosai sannan ta koma daki ta cigaba da karatu dan yau ko coffee bata kaima Sadiq ba, yau Salma ta kai coffee da kafafunta saboda Lukman dinta gidan zai kwana..



Washe gari Nana ta tafi school dan yau sadiq baije school ba, bayan ta gama gaisawa dasu Zee suka shiga lecture suna fitowa daga lecture suka wuce CTB HALL dan yi test, Alhmdulh Nana taji dadin test din saboda duk abunda Sadiq yayi mata tutorials duk sun fito dan haka in minute Nana tayi ta fito tana farin cikin saukin da test din tayi masu, bayan sun fito test suka shiga lecture din 2-4 suna cikin lecture result din ya fito, da man abunka da CTB ce sukayi ba writing ba shiyasa suka ga result ranar bayan sun gama yin lecture ta wuce dan ganin nawa ta samu aiko ta samu 35 /40 ta fada 5 tayi murna sosai da man course din three credit unit gareshi haka ta koma gida tana murna, nan ta gaya ma Sadiq yanda ta samu, yace ta sake maida hankali sosai..



Bayan ta gama abunda zata yi ta cigaba da karatun ta dan yanzun Nana karatu take ba kama hannun yaro inda bata gane ba Sadiq ya tadata, haka Nana ta kama yi har suka gama duka C. A TEST din da zasuyi kuma bata cin kasa da 30 sai dai sama da 30 dan tun a C. A Sadiq ya ba ma Nana samun grade mai kyau...


Nana karatu take yi sosai dan ta maida hankalinta baki daya wajen jarabawa, ta ajiye tunanin rabuwarta da Khalid dinta,domin ta barma Allah lamarinta dan tasan dole tayi ma iyayentta biyayya to amman waye shi wanan mijin da Mama taka sa gaya mata sai dai ta jira lokaci...




Yau ta kama Nana zata fara shiga exams dan haka da wuri ta tashi ta shirya tayi wucewarta school dan ko Sadiq bata tsaya jira ba dan bata san tayi lete....



Bayan sun shiga exam lafiya, Nana gu daya suka zauna da Zee dan haka shiysa suka taimakama juna, sun gama exams lafiya sanann

Please Login or Register in order to submit comment