Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

man ina san nayi magana dake amman inkin bani damar haka"...

"Tom shikenan ina jinka"..


"Yauwa, Zainab nasan kin san komai ya faru tun daga haduwa ta da Jawaheer har zuwa yanzun ko? "..


"Eh gaskiya, na sani bani daya ba, kowa ke tare da Nana ya san kalar son da take yi maka amman ba yanda zamuyi haka Allah ya kaddara"..


"Haka ne, tabbas koni na gode domin gaskiya Nana ta nuna man soyayyar gaskiya, wanda samunta a wannan zamanin yake da wuya samu"...



"Mai zai hana ki mayai man gurbin kawarki cikin zuciyata? "..



"Malan!!!


"Eh Zee abunda nace kenan, ina sonki, ina san ki mayai man gurbin Nana cikin zuciyata, amman kiyi shawara Zee"..



"Amman karda dan munyi wani relationship da Nana yasa kice baki yarda da bukata taba, Aa ko daya nasan Nana sai tafi kowa farinciki taga muna soyayya dan tasan bazaki cutar dani ba, amman yanda kika gani".



"Tom shikenan insha Allah, zanyi shawara komai kenan zaka ji daga gareni, "to Allah yasa mudace, "Amin ya Allah"..


"To mun iso gida ko? "Aiko dai, sai da safe kuma ina sauraran ansarki Zainab, "tom shikenan Allah ya kaimu nagode byee"..

_____________________________


Daga school ba inda Sadiq ya wuce da Nana sai *NI'IMA MOTORS* ..



"Tom myluv mun iso fito mu shiga ki zabi duk motar da tayi maki wajen nan"...


"Aah myluv nidai ka zabar mani bi ban iya zabai da kai na ba"..


"Ok ai umarnin ki ake jira Gimbiyar Mata , sarauniyar birnin zuciyata"..


Nan Sadiq ya shiga ya zabin ma Nana mota mai suna *TOYOTA X 2019*



Bayan sun gama cinike shida Alhaji yace sun kai mashi motar gida, daga nan suka wuce *PARK* *AND ZOO* nan su kayi kallo suka wuce *SOLI* *CENTER* , nan suka ci abinci sannan suka wuto gida...




"Sadiq gaskiya wannan motar tayi kyau sosai, "aiko dai Momy ta Nana ce na saya mata, dan na gaji da maidani drive da tayi, nan ya fada yana kallon Nana ya kashe mata ido daya..



"Aiko haka ma mun gode, bari na kira Mutanan gida su fito suga abun arziki"..


"Ammi kufito Kuga abun arziki mana, "to Momy bari na tashi wa yaƙi ganin abun arziki? "Sai Wanda bai san arziki ba, "Laa aiko hakane Hajiya..



Nan suka fito su dukansu suka ga mota suka sa alkhari...


A hankali Sadiq ya koya ma Nana mota itama, nan ta fara zuwa da motarta school..




"Zee ku fito Kuga nayi mota, "wow Masha Allah gaskiya kawata ina taya ki murna motar tayi kyau sosai"...



"Nagode kawata, yaya Sadiq ya siya man, "aiko kin gode, Nana ina san yin magana dake in mun fito wannan lecture ɗin, "tom Zee shikenan..



Bayan sun gama lecture suka shiga mota suka tafi hostel dan basu sake shiga wata lecture sai 4-6 shiyasa suka tafiyarsu hostel room din An-babi, bayan sun huta suka fara magana...




"Nana, Malan Khalid yace yana sona, wai na mayai mashi gurbinki cikin zuciyarshi"...



"Alhmdulh, gaskiya niji dadin wanann maganar da man abunda ke ranmu kenan nida Salma ki auri Yaya Khalid amman ba yanda zamuyi, yanzun gashi abu yazo cikin sauki, Allah yasa alkhari..


"Ai ban ce man na Amince ba, "saboda mai Zee?"


"Gani nike kamar naci Amanarki Nana naso wanda kika so"..


Zee tayi maganar cikin damuwa dan gani take kamar ta so zuciyarta sosai..

"Karki damu yar-uwa, baki sani ba sai nafi kowa farinciki idan haka ta kasance, dan haka dan Allah ki amince da Yaya Khalid please, wallahi yana da mutunci sosai kin sani ba sai na gaya maki ba"...



"Hakane Nana Allah yasa haka shine alkhari a garemu baki daya"..


"Amin ya Allah Zee"..



Bayan sun gama suka wuce lecture, suna fitowa suka wuce gida, Nana ta kai Zee gida sanann ta ida isa gida...



Washe gari bayan su Nana sun tashi daga lectures ta biya office din Khalid bayan sun gama gaisawa nan Nana ta fara magana..


"Yaya Khalid ya aiki? ".

"Alhmdulh gashi nan muna yi Jawaheer ya gida? "Lafiya lau"..


"Da man nazone akan maganar ka da Zee, munyi magana da ita komai dai dai, sai dai tace bata iya gaya maka shiyasa nazo na gaya maka...

"Maitace Jawaheer ?, "Ta Amince da soyayyar ka"..

"Alhmdulh!! Allah na gode maka, gaskiya Jawaheer bani da bakin da zani yi maki godiya, Allah ya bar zuminci"..


"Amin Yaya Khalid, yanzun Jawaheer ki bani number Zee ɗin zamuyi waya da ita".



Nan Nana ta ba Khalid number Zee sannan ta tafiyarta ta shiga lecture, bayan sun fito lecture take gaya ma Zee yanda sukayi da Khalid suna cikin magana sai ga Khalid din ya tsaya yace ita Zee ta shigo su tafi tare, nan Zee ta shiga ita kuma Nana ta shiga ta ta motar ta kama gabanta....



"Zeee, "Naam.!!


"Naji sakonki gaskiya naji dadi sosai Allah yayi maki albarka,"amin ya Allah".


"Maiyasa baki iya gaya man ansata da bakin ki sai dai Jawaheer?"..



"Bakomai kawai hakanan nida ita duk daya ne ai shiyasa"..



"Hakane gaskiya, hakan ma naji dadi, Allah ya saka da alkhairi Zee na"...



"Anjima zamuyi waya, "Allah ya kaimu lafiya,"Amin".


Nan Khalid ya kai Zee gida sanann ya wuce gida shima ya fara gayama Fulani..


"Fulani nayi budurwa"..

"Masha Allah, Noor ina ka samu budurwa kuma? "..


"Wallahi ƙawar Nana, ina wata Zainab wanda nike baki labari ita ta hadamu da Nana Jawaheer lokacin da nace ina sonta? ''..



"Eh hakane Noor na tunata,itace kenan? "..


"Eh wallahi itace yanzun nace inaso Fulani, "to Noor Allah yasa alkhari, "Amin Fulani"...



Haka rayuwa ta cigaba da tafiya soyayya ake yi sosai tsakanin mutane uku, Sadiq da Nana Jawaheer, sai Lukman da Salma sannan Khalid da Zee...



yau su Nana suka fara exams din second semester 100 level, bayan sun fito daga exams suka wuce gidan su Zee itace bata dawo ba sai bayan sallahr la'asar sannan ta dawo gida...



"Myluv, sai yanzun Allah ya baki ikon dawowa kenan? "..


"A fuwan myluv wallahi Zee ta dauke ke man hankali ban san rana tayi ba sai dai naji ana kiran sallah, da yake tutorial mukayi shiyasa"...



"To Allah ya bada sa'a, kenan zakuyi gobe? ".

"Eh zamuyi insha Allah,"to Allah ya baku Sa'a,"Amin"..



Bayan nan suka wuce cikin part ɗin Hajiya suka ci abincin dare sannan suka wuce kowa ya kwanta..



Haka dai Nana ta cigaba da karatu sosai ba kama hannun yaro,suna cikin yin exams aka fiddo masu da result ɗin first semester, Alhmdulh result yayi kyau dan Nana 4.00 ta samu ita kuma Zee 3.45 ta samu...




Yau su Nana suka gama exams ɗin second semester sun gama 100 level sun shiga hutun season..





_By jameelah jameey_
✍🏻



Share and comment pls


🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕
*NANA JAWAHEER*
🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕

*STORY And WRITING* *By*
*Jameelah A Belloh*
*(Jameey)*



*🌎MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M. W. A*


```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻
```

__________________________________



*BISSIILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*




Page_5️⃣1️⃣➖5️⃣5️⃣





"Myluv!

"Naam ina jinki"..


"Da man wai ina san muje wani biki nida Salma".


"Biki myluv?"..


"Eh wata course mate dinmu ce za'ayi ma biki, shiyasa"..


"Myluv magana fa nike kayi shiru", ta yi maganar tana dirdira kafafu tana ta zuba mashi shagwabarta wanda ta zamai mata jinin jiki..


"Uhmm, ki bari zan maki magana yanzun ai kinga ina wani aiki ne"..


"Myluv munfa shirya kawai yanzun tafiya zamuyi yau ake dinner".


"What?"..

"Dinner myluv?"..

"Eh dinner ai bani daya zani ba nida Salma ce, kuma na san Zee ma zataje"..


"To in Zee zata ke baki zuwa, gaskiya ba zan laminci wanann yawon ba, yanzun karfe hudu fa myluv"..


"Amman sai yanzun zaki biki, Aah bama gidan yinin biki ba, dinner zaki tafi haba myluv"..



"Tom nidai dan Allah please myluv".



"Gaskiya ba zan boye maki ba Amman sorry to said myluv ba wata dinner da zaki je"..


"Kana nufin bani zuwa bikin baki daya?"..


"Aa zakije yinin biki insha Allah, amman banda zuwa dinner Myluv"..


"Tom Shikenan hakan ma mungode Myluv".


"Sorry Myluv komai kika nayi maki akan Sonki ne, luv uh"...


"I know Myluv"..



"Salma wallahi ya hana, yace bamu zuwa wata dinner".


"Dan Allah? karki fadi man haka Nana".


"Wallahi dagaske ya hana amman yace gobe munje yinin biki".


"Uhmm Sadiq! wallahi Sadiq halin shi sai shi, yanzun duk wannan kwaliyar da muka yi zata tafi a banza kenan?''..


"Hmmm! Haka yake nufi Salma"..


"No impossible! Ba zai Yuyuba, Nana tashi mu tafi garden ko pictures ne munyi na turama Baby"..


"Good idea! Kin kawo mafita wallahi taso mu tafi ma kafin dare yayi"..


Nan suka je garden suka fara dauka pictures kala-kala, shi dai Sadiq yana gefe yana aikin shi amman ya kan kallesu sai dai yayi dariya yana mamakin wai su a dole basu kwaliyar banza..


"Myluv nazo a dauka dani ko?"Yana dage mata gira daya..


"Ni bani hoto da maza, sai mata" ta fadi tana murguɗa baki😚..

"To ai ni mijinki ne, kinga ai dole ayi dani ko?"..


"Aa ba dole, Salma cigaba da dauka picture mana"..


"Wallahi baki isa ba sai kinyi dani, dan na hana fita sai a ce za'a hukuntani ta wanann hanyar, haba Myluv"..


"Uhmm Salma continue please, karda dare yayi fa, dan yau da wuri zanyi bacci".


Nan dai Sadiq ya shiga akai ta yi masu pictures, sunyi kyau sosai sai da time din sallah yayi sannan suka wuce cikin gida, shi kuma Sadiq ya wuce mosque..



"Salma wallahi, Yaya Sadiq baida kunya"..


"Hahhahhaha! Nana Sadiq din ne baida kunya?"...

"Ehmana, kiga fa ya hanamu fita,amman yazo yana wani cewa dole sai anyi hoto da shi, kiji fa?"..



"To ya zamuyi Nana?"..


"Ai ba yanda zamuyi, da man mu mata haka zamu kare a karkashi wani"..


"Kinga muka taso a karkashi ikon iyayenmu, da zaran kuma munyi aure zamu koma a karkashi ikon mazajenmu, dan haka hakuri ya zama dole ya zauna cikin zuciyoyin mata"..


"Amman ai ba'a daura aurenmu ba balle har ya hanani fita, nima da baki ce na tambayeshi ba da yanzun muna can muna shagalinmu".



"To ai ke Nana daura aurenku ne kawai ba'ayi, amman tuni family dinku kowa ya shidda Sadiq zaki aura nan da yan shekaru'..



"A bunda yasa nace ki tambaye shi, so nike ki saba da halinshi tun yanzun".



"Dan na fahimci Sadiq yana da kishi sosai, ba zai barki ki ringa fita anyhow ba"...



"Kuma na lura ke kina da son kiga kin fita, Nana kina da son kiyi harka da kawaye, to bari na baki shawara"..


"Idan kika yi aure, Nana ban baki shawara ki ringa ja-inja keda mijinki ba, kinga yawan ja-inja yana zubda martabar mace a idon mijinta"..



"Sannna indan kika fahimci mijinki yana da kishi, to ki yaye duk abunda zai taso mashi da wannan kishin har yakai da kun samu matsalal"..


"Kinga kenan ya zama dole ki hakura da sa gyale, sannan sai kinyi hakuri da cewa zaki fita anyhow, dole sai kinyi hakuri da duk wani abu da zaki san zai sa mijinki yaji kishi sosai wanda zai kawo matsala"..



"To sadiq yana da kishi, shiyasa baya san saya maki gyale, sannan kuma baya so kina fita, shi fa bai ƙiba ko kofar gida karda ki fita, inba zaki school ba".


"To ba sai ki kiyaye ba Nana!

"Hakane gaskiya Salma, naji shawarki nagode sosai, gobenma na fasa zuwa bikin baki daya"..


"Yauwa nima abunda nagani kenan"..


"Salma wai saura wata nawa ku gama NYSC?"..


"This mouth ne fa Nana"..


"Wai har kinyi shekara a gidan nan?"..

"Aiko dai akwana atashi ba wuya wurin Allah"..


"Gaskiya kam, amman ai zaki danyi hutu kafin ki tafi ko?"..


"Eh upper week zan wuce gida, kin san next week za'akai kayan baikon mu ko?"..


"Eh haka ne fa, Allah yasa alkhari, Salma dai ankusa zama ta yaya Man"..


"Aiko! Kamar yanda kika kusa zama da Sadiq ba"..



_______________________________



"Malan dan Allah ka rufa man asari, karka yi man haka"..


"Talatu wani rufan asiri kike so nayi maki? "..

"Bayan ni kin tona nawa asirin"...


"Wallahi Talatu kin cuceni, ba zan taba yafemaki ba, kinci Amanata"..


"Kin tarwatsaman gida, kinga dai kika rabani da matata, sanann kika watsaman zuri'a baki daya a gidan nan"..



"Dan Allah Malan kayi ma Allah kayi hakuri, na san banyi maku hallaci ba kai da Amina, amman duk da haka kayi man rai Malan"..


"Kinga, shiyasa ba'ason Hassada, kinga kinyi ma Aminatu hassada ita da Nana sai gashi su duka suna cikin kwanciyar hankali''.



"Wa gari ya waya inba ke ba, yanzun haka baki san ina Khadija take ba, sanann baki san idan Sabi'u ya ke ba, baki basu tarbiya mai kyau ba, kin daurasu bisa tubalin karya gashi ya afka dasu rami".


"Dan haka kije keda Allah wallahi Talatu ban ya fe maki ba"..



Hmmm! Rayuwa kenan da man In zaka gina ramin mugunta ka kina shi gajere...


Yanzun dai ga Inna Talatu nan yanzun duniya ta juya mata baya, sai kace ba itace Talatun da tayi mulki gidan Malan Adamu ba...


Shiyasa aka ce kabi duniya a sannu domin ita duniya budurwar wawa ce..


"Malan wallahi nayi nadamar duk abunda nayi a rayuwa, dan Allah ka yafeman ba dan halina ba"..


"Shikenan Talatu na yafemaki, Allah muma ya yafemana, "Amin Malan nagode sosai"..


Haka rayuwa ta cigaba da tafiya yanzun Talatu tayi nadamar halin ta so take taje tanemi yafiyar Nana Jawaheer domin tasan ta cutama yarinyarnan sosai..



______________________________



Yau su Nana suke koma wa hutun season, yanzun Nana anshiga level 2..


''Myluv gobe ne fa ake maki mana interview din nan".


"Myluv, Allah yasa aje a sa'a''.


"Amin ya Allah, Myluv gobe kina da lectures kenan?"..


"Wallahi ko Myluv, ni gani nike kamar second semester tafi first semester sauki"...


"Mai yasa kice haka?"..


"Myluv duka duka yaushe na shiga 200level, amman gashi wai har na shigo second semester, nan da two weeks zamu fara exams mu shiga 300 level"..


"Ai daman haka abu yake wuyarshi ace ba'a shiga ba, amman ana shiga sai kaga har an gama, ni ba gashi ba har FEDERAL MEDICAL CENTER sunyi man text suna nema na interview zasu dauki aiki a matsayin babban likita da jaha ke bukata"..


"Hakane gaskiya Allah dai ya bamu sa'a Myluv, "Amin ya Allah"..



"Bayan mungama exams da sati daya ne bakin su Salma ko?"..

"Eh hakane,"to Allah ya kaimu lokacin, "Amin"..


"Au Myluv ban gaya maki ba! Kin san next week Mama take tarewa gida ko?''..


"Wai da gaske Baba sun maida Aurensu?".

"Ehyyeh! Wai da kina daukar abun kamar wasa kenan?"


"Aa sai naga kamar dai mafarki nike wallahi Myluv"..


"To ba mafarki kike ba idonki biyu, Allah ne ya cika maki gurinki"..


"Allah na gode maka"..



Washe gari bayan su Nana sun tashi, sun gama yin komai suka yi breakfast, ita ta shirya ta wuce school, shi kuma Sadiq ya wuce interview a FMC ...



Bayan ta dawo daga lectures ta wuce gidan su Zee nan suka shirya yanda zasu yi shagalin bikin Salma, sanann Nana ta wuto gida..



"Momy, kinga yanzun aka turoman offer ta email dinna FMC sun daukeni aiki"..


"Alhmdulh, Allah nagode maka, Sadiq yau gashi kaine da aikin government"..


"Aiko dai Momy, Ammi kinji fa!

"Eh Sadiq ni bansan mai zance ba ai, Allah yasa alkhari, dan Allah kayi aiki tsakani da Allah, kaga aikinka na taimakon al-umma ne, dan haka dan Allah ka kiyaye".


"To shikenan insha Allah Ammi, wai ina Jawaheer bata dawo ba? ".

"Ai kasan yau suka gama yin exams din second semester sun gama 200 level kenan itama ko?"..



"Eh yau Nana Jawaheer take gama yin CTB EXAM, sai kuma WRITING an shiga 300 level yanzun saura shekara 1 tagama karatu itama"..



"Ai nidai nagaji da wannnan karatun boko naku, dan haka ko ba saura shekara daya ba nidai Sulaiman, yana dawowa zansa ayi baikon bikinku"..


"To Hajiya Allah ya maido Dady lafiya dai"..


"Amin ya Allah!


"Myluv congrats, yanzun nadawo Hajiya ke bani labarai masu dadi"..


"Congrats too Myluv, yau anfito final exams at 200level"..

"Thank You Myluv, naji Hajiya tace Dady na dawowa za'ayi baikon mu?"..


"Eh hakane insha Allah, kuma Dady bai dawo har sai kingama karatu da one week, tunda karatu yaje karowa kinga bai dawowa yace sai ya gama saboda Aiman shima ya yi J. S. C. E din shi sai su dawo baki dayan su"..


"To Allah ya maidosu lafiya, ni yau gida zani nayi ko da sati biyu ne Myluv"...


"To shikenan, da anjima zaki tafi ko? "Eh da anjima zani insha Allah"...



Da anjima Nana ta shirya taje wajen Mamanta..


"Mama ina wuni? "Lafiya lau Nana, ya gida?".

"Lafiya lau duk suna gaidaku, "muna ansawa"..

"Wai nagaji sosai wallahi Mama, "to tashi kije ki gaida Innarku sai kizo ki kwanta"..


"To Mama, ai nasa bata nan, tunda na shigo banji motsinta ba"..


"Tana ciki, Kin san yanzun bata jin dadin zama da Babanki, baki daya zaman hakuri take cikin gidan nan"..


"To Allah ya sawaka gaba, "Amin''..


"Inna ina wuni? "Lafiya lau Nana, an shigo kenan? "Wallahi nazo nayi maku sati, "to Allah yayi albarka, "Amin Inna"..


Nan Nana ta yi sati daya gidan su sannan ta wuce gida bayan ta dawo gida suka shirya duka gidan suka tafi kano bikin Salma...


"Oyoyo ga Nana'..


"Oyoyo Salma Amarya, kinga yanda kika yi fresh sai kace har anyi komai ma".


"Kinga ban ciki da wannan iskancin naki, ai dole da man kiga Amarya tayi fresh tunda tana shan dalka ko ba haka ba Zee?"..


"Aiko dai hakane Salma, ita ba'ace tayi fresh ba sai ke, kallata fa ki gani yanda Nana ta koma"..


"Kedai gane man hanya Zee, yanzun dai sannunku da zuwa ya hanya? "..


"Lafiya lau Alhmdulh, ya shirin bikin? "..

"Gashi nan muna tayi gobe ne ake bridal-shower"..

"To Allah ya kaimu, yanzun bari to muje ayi mana kunshi ko?"..


"Eh ki taso mu tafi wani Saloon na nan, nan akayi man nawa".

"Wow kinga ko yayi kyau sosai, tunda ma Saloon zamu kawai ayi mana harda gyaran gashi ko Zee?"..


"Eh haka Yafi ma, nan suka je Saloon dake cikin nan unguwar Zooroad dake Kano, nan aka yi masu komai, suka kara shirya komai yanda zai kasance masu gobe sannan suka dawo gida suka kwanta ko wa ya kama waya da masoyin shi...


Washe gari suka shirya suka yi bridal shower Masha Allah Salma tayi kyau sosai, shigar purple color tayi su kuma su Nana su kayi shigar sky blue sunyi kyau Masha Allah...


Bayan sun dawo daga bridal shower suka yi wanka suka kwanta washe gari suka tafi dinner..


Wow Masha Allah, Salma na hango cikin wannan zafaffan material Armygreen ba karamin kyau tayi nan suka dauki hanya zuwa wajen dinner.


Alhmdulh anyi dinner lafiya andawo gida washe gari aka daura Auren LUKMAN YUSUF da UMMA-SALMA AHMAD akan sadaki naira dubu dari, bayan an daura aure angwaye suka wuce reception suka ci abinci wajen karfi hudu na rana aka dauki amarya aka kai ta gidan mijinta dake jahar katsina a unguwar Goriba road..


Bayan ankai amarya su Nana suka je akayi yanda akeyi sanna suka dawo gida shi kuma ango Lukman ya shiga dakin Amaryarshi, mudai sai dai muce Allah ya basu zaman lafiya😎..



Yau su Nana suka koma school sun shiga three hundred level cikin ikon Allah..


Shi kuma Sadiq ya maida hankalinshi a wajen aikin shi, yanzun bai cika zaman gida ba saboda aikin da yake zuwa..



A kwana tashi ba wuya gurin Allah yau su Nana Jawaheer suke gama degree dinsu, yau suke yin final examination @Umaru Musa yar'adua University katsina..



"Alhmdulilah Myluv, kaga yau dai na gama degree sai dai na jira fitowar result kuma"..


"Masha Allah Myluv gaskiya naji dadi sosai, Allah ya fiddo mana result din lafiya"...


"Amin ya Allah, gaskiya ban san ya zanyi ba dan murna"..

"Godema Allah zakiyi Myluv, yanzun shigo mu wuce gida tunda kibar taki motar gida"..


"To ai ina sane na bar motata gida, dan nasan murna bazata barni nayi driving din da kaina ba"..


"Gaskiya kam, naga alama Myluv, kuma next week Dady yake dawowa"..


"Hakane Allah ya maidoshi lafiya, "Amin ya Allah".



Nan bayan sun je gida, yan gida suka taya Nana Jawaheer murna gama degree din ta, sanann Sadiq ya shirya mata surprise party a soli center na taya ta murnar gama karatu..


"Myluv anjima karfe hudu ki shirya zaki rakani wani waje"..


"Tom shikenan Myluv Allah ya kaimu Lafiya"..


Nan Nana ta tashi, tashiga wanka tunda taga lokaci ya fara matsowa zata raka Sadiq wani waje..



"Cikin wata bugaigiyar ar' niyar atamfa red and blue tasa, dakin riga da stiker pies simple style ne aka yi ma dakin ba wani yar'batsar din styles akayi ma atamfar ba..



"Kayan sun anshi jikin Nana da fatarta, abun ka sa black beauter sai abun ya sake fiddo ta tunda atamfar red ce and blue, simple makeup tayi, sannan ta murza daurin dankwalin zamani yayi mata bala'in kyau..


Sannan ta dauki watch dinta itama blue ta daura a hannu, ta dauko gyalenta medium dai-dai dashi, dan Sadiq bai san sa karamin kyale, shima blue ta yafa, sai ta dauko post dinta blue ta rike ta dauki wayarta yar company *IPHONE* , ta rike tana yin dialing din number Sadiq tace ta shirya nan yace ta fito su wuce..



Shima Sadiq wata shadda blue ce yasa zigina da hularshi black takalminshi ma black ne da agogonshi duk black ne nan ya fito suka wuce Shi da Nana da ka gansu kaga masoya..


"Myluv bissimila mun iso, but close your eyes, don't open please Myluv har sai nace ki bude..

"Ok shikenan Myluv!

Nan suka shiga, Sadiq ya kama hannun Nana, saboda har yanzun bata bude idon ba..


Suna shiga yace.

"Ok Myluv open your eyes"..

"Wow! Myluv nagode sosai, gaskiya naji wannan surprise party din"..


Nan fa mutane suka kama yi mata congrats dan harda mutane Sadiq ya gaiyato, ga uban decoration da wajen yasha Masha Allah..


"Congrats Nana Jawaheer, angama karatu lafiya? ".

"Thank You yaya Khalid Lafiya lau Alhmdulh ".

"Congrats Kawata".

"Thank You Zee, congrats to you".


"Congrats Nana Jawaheer angama karatu lafiya"..


"Thank You yaya Man lafiya lau Alhmdulh ".

"Congrats Nana Allah yasa alkhari".

"Thank Salma, da fatan mun kusa zuwa suna? "..

"Bansaniba, ke ko ina sai kinyi shirme? ".


"Myluv kyalesu, in sukayi wasa, sai mun rigasu zama Dady da Momy ko?"..


"Uhmm! Nidai babu ruwana Myluv"..


Nan dai suka ci abinci da kayan lashe baki sannan kowa ya koma gida..


yau Dady ya ke dawowa daga kasar America shida Aiman, yau suka dawo kasa Nigeria..


Dady yayi murnar gama karatun Nana yanzun saura aure kenan.


Bayan ya huta ya tafi gidan Abba nan suka sa bikin Nana Jawaheer da Abubakar Sadiq nan da wata uku mai zuwa insha Allah...


____________________


"INNALILLAHI wa zan gani haka ni Talatu"..



"Khadija kece kika zama haka wannan wani kalar bala'in ne wanann"..


"Talatu wai wace Khadija? "..

"Yaya Khadija ta dawo wanda kika san ta gudu ta barmu shekara da shekaru".


Nan Maman Nana ta fito taga Khadija kwance tsakar gida bata iya yin numfashi sosai..


" *SUBUHANALILLA* "..

"Talatu tashi mu kai ta asibiti, "to Yaya"..

Nan suka dauke ta suka kaita FMC, suna zuwa emagerncy aka kaita direct, nan su doctor Sadiq suka shiga domin ceto rayuwar patient dinshi kuma kanwarshi..


Bayan wasu an awanni suka fito da ita suka kaita resting room..

"Sadiq wai maike damun Khadija? Baka ce mana komai ba"..


"Baba taho muje office sai muyi magana"..


Bayan sun zauna Sadiq ya fara magana..

"Baba gaskiya Khadija tana fama da ciwon hanta (heptatic C)sosai ga kuma AID tana fama da ita, saboda da bata shan magani shiyasa cutar ta tashi daga HIV ta koma AID zamuyi iyakar bakin kokarin mu muga mun shawo da kan matsalar"..


Haka Sadiq ya kama Kwantar ma da Baba hankali sanan suka dawo

Please Login or Register in order to submit comment