Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka fito suna shirin komawa gida suka gamu da Khalid...


"My jawaheer, ya exam? "Alhmdulh my Khalid, exam sai dai godia, "Ai na ganki dana shigo hall dinku, "nima ai na ganka kana korar wasu, haba my Khalid dan Allah ku ringa yin sauki mana...


"My jawaheer maiye abun wahala ga exam din CBT, objective ne fa, ba essay ba amman duk da haka sai ansamu wanda suka yi magana, shiyasa ni duk wanda na kama a CBT tana magana fidda ta kawai nike yi waje, "to Allah yasa mudace amin...


"Yanzun ai na san gida zaki ko? "Eh gida zani mana, "shigo na ajiyeki to, "Aah ka san yaya Sadiq ke tafiya dani, Dady yace haka kayi hakuri my Khalid yanzun zaka ga yazo ma..


"Bakomai My jawaheer, amman yau fa zan shigo da marece bayan kin huta, "to shikenan Allah ya kawo ka lafiya, nan Khalid ya wuce gida bayan tafiyar Khalid da two munite sai ga Sadiq nan ya taho..


"Ya exams din? "Alhmdulh, "tayi sauki sosai ko? "Eh Alhmdulh, "yauwa Nana haka nike san ji kullun kice man tayi sauki kinji? "Eh naji, "yanzun kafin mu tafi gida zamu biya umarstore muyi shopping naga kwana biyu kamar kayan kwaliyarki sun kare,,ko exam ce ta hanaki yin kwaliya Nana? "Aah kawai dai babu kayan makeup din,''to shikenan mu wuce daga nan sai mu biya greenhouse kiyi new hijabs ko? "Yay Sadiq harda gyale pls,"ke dai Nana kina son sa gyale, to shikenan amman daya zamu saya shima babba irin na su Ammi, "wayyo Indai kallar nasu Ammi ne na hakura,"baki san babban gyale ko? "Ehmna, "ok sai dai a hakura ko, dan ni bani sayan karamin gyale gaskiya...


Bayan sun isa umarstore suka fara yin abunda ya kawo su, daga nan suka wuce greenhouse suka yi dakin hajib har guda goma, sai taga wata rich masu bala'in kyau tace dole sai Sadiq ya sayarmata ita tunda bai sayan gyale, haka ko akayi sai da ya sayar mata, sannan suka wuce gida, bayan sun dawo Nana ke cemai anjima Khalid zai zo su gaisa, nan take mood din Sadiq ya chanza amman daya ke yana bin shawarar Lukman sai yace Allah ya kawo shi lafiya......



Bayan Nana ta nuna ma su Momy kayan da Sadiq ya saya mata, sannan ta shiga wanka ta shirya cikin wata dakakar shadda maroon color tana jiran zuwan Khalid...



Bayan Khalid ya sanar da ita zuwan shi, nan Nana ta fita gun masoyin nata, nan tayi mashi jagora zuwa garden...



"My Khalid sannu da zuwa, "yauwa my jawaheer, kiyi kyau Sosai, "kaima kayi kyau dan ko kafafunka ban kamo ba wajen kyau, "uhmmm my jawaheer shikenan tunda kince haka, "haka ma ne my Khalid, ya naga duk ka rame haka? "Bakomai my jawaheer kawai dai ina tunaninki ne, sai naga kamar zasaki zanyi! Shiyasa kullun nike cikin tunani da fargaba, da zaki yarda da munyi aure kin ida karatun cikin dakinki..


"Aah my Khalid, kabar wannan tunani! Kuma komai yafaru da mutun kaddara ce daga Allah, inka ga ban aurenka to kasa ma ranka haka Allah ya kaddara domin ba mai auren matar wani! Haka ba mai auren mijin wani, kasa wannan a ranka my Khalid, "to shikenan my jawaheer..



Bayan sun gama gaisawa yaje ya gaisa da Momy ya wuce part din Sadiq nan suka yi fira sosai shine bai bar gidan ba sai bayan sallahr insha'i sannan ya wuce gida...


Bayan tafiyar Khalid Nana taje ta kaima Sadiq coffee, sannan taje ta kwanta bacci..


Washe gari, bayan Nana ta tashi daga bacci ta shirya ta wuce school dan yau tana da exam...



Alhmdulh exams din yau ma tayi ma su Nana dadi, daga ctb hostel suka wuce dakin su Anbabi, nan suka dafa abinci suka ci, bayan sun gama cin abinci suka hau labarin duniya, sune basu bar hostel ba sai bayan sallahr la'asar sannan suka hau bus suka wuto gida...



"Nana wai ban ji kince man komai ba tun bayan maganar da mu kayi da ke akan Sadiq....


"Uhmm Salma kenan wallahi ni abun ya daure man kai, ko jiya sai da my Khalid ya kusa yi man kuka, ban san ya zanyi ba, ni yanzun na ajiye wannan maganar ma kawai, ta karatuna nike..



"To shikenan Allah ya baki sa'a, ai gobe ma zaki yi ko? "Eh mufa bamu da wani intable wallahi, duka duka intable din kwana hudu muke da ita,"Allah ya bada sa'a, "Amin


Nan Nana ta tura ma khalid text sannan ta cigaba da karatu...



Khalid yana zaune yana tunanin maganar da suka yi da Nana, matar mutun, ba mai auren matar wani, bayan shi bata ce mai haka sai kawai ya ga text nan ya fara karanta..


_Love is something beautiful, and a feeling that one will like to carch. Love is the feeling that makes you feel alive._

```(so wani abu ne mai kyawu, kuma wani yanayi ne da mutum zai so ya damke. 'So. shi ne yanayin da kan sa ka ji ka a raye.)```

_I hope you understand that I will ove you untill the end, because .you are notjust my boy. But you are also my best friend._

```(Ina _fatan kin fahimci cewa zan so ki har karshe, saboda ba ka kasance saurayina kadai ba, kai ne Aminina.)```


Nan shima ya maida mata da..



_Ki san ina fatan kasancewa tare da ke a ko yaushe tsawon kwana bakwai a sati bana taba_


```gajiya da ganinki masoyiyata, ina sonki.

(You showed 'me how it is to be loved, and you showed me how it is to be care of you, I love you forever,
```)

_Kin nuna 1min yadda 'ake 'soyayya, haka kurna kin nuna min yadda zan‘ kula da ke. Ina sonki har abada_


```(Every message,'is a smile, every word is like rose, but when you are with me” .don’t run away)```

_Dukken sako murmushi ne, dukkan kalma tamkar fure ‘ce,_


Wana ta karanta message din da Khalid ya turo mata, bata san lokacin da fara kuka ba sai da tayi kukan ta sannan ta hada handouts dinta ta koma daki tayi sallah suka tafi cin abinci, bayan sun gama cin abincin, ta kai ma Sadiq coffee sannan taje ta kwanta tana tunanin yanda zata yi rayuwa da wani bada Khalid ba, dan ita Khalid take da burin rayuwa da shi amman dole tabi umarnin iyayenta....



Haka Nana ta kwanta bacci haka kawai take baccin ba dan yayi mata dadi ba, sai dai kawai ita dai ta kwanta bacci...





```Wai yau na gaji sosai gaskiya🙍‍♀️, wallahi typing da wahala sosai ga aikin gida 🙆‍♀️, sai dai hakuri kawai zamuyi muduka😉```





_By jameelah jameey_ 🖋






Share and comment pls


🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕
*NANA JAWAHEER*
🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕

*STORY AND* *WRITING BY*
*Jameelah A Belloh*
*(Jameey)*


*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻```

_________________________________


*BISSIILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*






Page 3️⃣5️⃣➖4️⃣0️⃣






Washe gari,haka Nana ta ta shi jikin duk a sake dan ita tana hangen yanda za'ayi rabuwar ta da Khalid tana hango wahalar DA zuciyarta zata sha rabuwa da masoyin ta mai sonta,Khalid shi ya fara gaya mata kalmar So a rayuwata lokacin tana cikin halin wahala ita ba kowa ba,Amman Khalid shine yazo tana a haka yace yana sonta,bai duba yanayin da take ciki ba na tallauci Amman haka yace yana so ,ita gaskiya Khalid shine yafi dacewa da rayuwarta....


"Nana ki ta shi ki shirya kafin Sadiq ya shigo ya tadda baki shirya ba....


"To Ammi,yanzun zan tashi da man,"yauwa yar-albarka ta shi kinji,ki shirya ban san Sadiq ya shi go ya ganki haka,kin san shi Sadiq baya san jira....


Haka Nana ta ta shi ta shiga wanka,ta samu ta shirya ta Kara sake duba handout din BIO1210 dan yau exams dinta zasuyi bayan ta gama dubawa ta ta shi ta fita...



"Yaya Sadiq,Ina kwana?"lafiya lau Nana,kin tashi lafiya?"lafiya lau Alhmdulh,"ok tashi mu tafi,Ammi sai mun dawo,"ok Sadiq a dawo lafiya...


"Nana dan Allah ki daure ki gaya man matsalarki in Ina da maganinta zanyi maki ita insha Allah,"yaya Sadiq ki bari na dawo exams munyi magana,"to Nana Allah yasa,dan Allah ki maida hankalinki wajen exams dinnan duk da kin kusan gamawa saura biyu?"eh saura biyu mugama insha Allah,"ok Allah ya kaimu lafiya,"Amin..


Nan suka ida isa school ya ajiyeta bakin cbt tana zuwa ta iske har anfara shiga nan ta dauki student ID card din ta ta shiga layi,nan suka shiga suka fara exams,bayan ta fito tayi ma Sadiq waya tace ta wuce gida ita...


Bayan ta koma gida wanka tayi ta dauki handout din machanise ta wuce garden ta fara karatu sallah kawai take ta data,da tayi sallah zata koma karatunta,da Sadiq ya dawo ya tadda Nana a garden ya tambayi Momy taci abinci,nan Momy tace bata ci ba,da kanshi ya dibi abinci ya spoon biyu shi da ita ya wuce garden...


"Nana,"Naam oyoyo ,yaya Sadiq ka dawo kenan,"eh nadawo ,sannu da karatu kanwata,"yauwa sannu da hanya....


"Nana ga abinci na zubo mana muci tare,"ayya Yaya Sadiq ni na koshi,"Allah ban yarda ba ni sai kin ci,"Yaya Sadiq gobe muke second to the last exams fa,kuma course din yana da wahala,"haba Nana dan Allah ki daure kici abinci,karatu ai baya hana cin abinci,dan haka come and enjoying,"to shikenan,nan suka fara cin abinci....



Sai da Sadiq ya tabbarta da Nana taci abinci sosai,sannan ya tashi ya barta ta cigaba da karatunta,Nana itace bata bar garden ba sai sallahr isha'i da tayi sallah ta fito parlour...


"Sannu uwar yar-bokoko sai yanzun ake ganinki?"laa Hajiya wai uwar-bokoko,to indan ba muyi boko ba,mai zamuyi tunda yanzun bokon keci,"aiko dai Nana kin fadi gaskiya,Hajiya wannan zamanin yanzun boko shine gaba,ko kasuwa zakayi in baka da boko sai a cuceka,dan haka dan-dole mutum yake boko yanzun...



"Aiko dai Salma kin fadi gaskiya,"Hajiya ku taso muje muci abinci ko?"To ku tashi mu tafi,haka suka ci abinci bayan sun gama cin abincin suka Kara yin fira,sannan Nana ta tashi ta wuce kitchen dan ta hadda ma Sadiq coffee bayan ta gama hada mashi coffee ta dauka ta tafi part din shi....



"Yaya Sadiq ga coffeen nan ashe lafiya,"to zauna mu sha tare ko?"Uhmmm ai ni na koshi,yanzun nagama cin abinci,"as with wish nidai nace ki zauna ki ki sha,"to shikenan yaya Sadiq, nan ta zauna suka sha coffee din tare ,bayan sun gama sha Nana ta tashi ta wuce ta kwanta.....





Washe gari,da wuri Nana ta shiga makaranta,bayan sun fito daga exams ta wuce gida,bayan ta dawo gida ta cigaba da karatunta itace bata gama karatu ba sai da dare yayi sannan Nana ta tashi daga karatu sannan ta wuce cikin gida,bayan tayi sallah ta wuto parlour suna cin abinci,bayan sun gama cin abinci Nana ta tashi taje ta kaima Sadiq coffee ta wuce ta kwanta....



Yau su Nana ke yin last paper,10 suke shiga exams din shiya Nana sai 9 ta tafi school ,tana zuwa suka shiga cbt suka tayi exams din,bayan ta fito daga cbt direct gida ta wuce,yau farin ciki fayau cikin zuciyar Nana dan yau ta samu hutu na wani lokaci....




"Nana ,Sadiq yace ki sa mai shi a garden yana son magana dake,"to shikenan Salma,bari na ta shi,"Aah Nana haka zaki tafi wajen Sadiq din bako poder?"ikon Allah ,Salma ya kike so naje wurin yaya Sadiq?"ina son kiyi kwaliya dan haka matso ma ki fara yi,"tom naji Amman poder kawai zan shafa,"shafa poder bakomai ai yafi babu"....


Nan Nana ta shafa poder,harda lipstick sai da Salma ta matsa mata ta shafa harda turare,sannan Nana ta wuce wajen Sadiq...


Bayan Nana taje wajen Sadiq, ta zauna..


"Yaya Sadiq gani kana nemana, "eh sannu da zuwa, ya exams? "Alhmdulh gashi yau har mun gama first semester, "Allah ya bada Sa'a Nana, "Amin ya Allah"..


"Da man naki raki ne ki gaya man matsalarki dan ban san naga wannan damuwar a tartare dake".

"Dan haka Nana gaya man matsalarki "..

"Yaya Sadiq, da naje, "da kikaje Ina Nana? "..

"Da ka kai ne wajen Mama, shine tace na rabu da my Khalid, wai bashi bane mijina ba, nan ta fara yi mashi kuka, wani bakin cikine ya kama Sadiq wato yarinyar nan saboda da Khalid ta sa kanta cikin damuwa..


"To sai akayi yaya?''..

"Eh kuma ita Mama bata gaya man waye mijin ba, wai tace lokacine"..


"Nana! Dan ance ki rabu da Khalid shine kika sa kanki cikin damuwa? ".


"Yaya Sadiq, Ina son Khalid Sosai"..

"Ke! Yi man shiru kona bata maki rai, tashi ki ban waje ko na bata maki rai mutunniyar banza"Sadiq ya fada cikin ɓacin rai da bakin kishi.


"Yaya Sadiq, intashi fa kace? Ina ganin zaka bani shawara"..


"Eh Nana tashi ki ban waje, wanann ya nuna ba zaki bi umarnin iyayenki ba, saboda soyayya"..


"Dan haka tashi ki tafi ni gobe zanje gidan Abba da kaina"..


"Wayyo dan Allah ka rufa man asiri, wallahi Sharin sha'den ne"..


"Zaki tashi ko sai na bugeki a nan wajen?"..


Haka Nana ta tashi jiki duk a sake tana da ta sannin abunda tayi, dan sai taji tana jin haushin kanta dan haka ya zama dole taba Sadiq hakuri gobe...



"Nana har kin dawo? "Eh Salma yaya Sadiq kusan buguna yayi, "bangane kusan bugunki yayi ba, mai kika yi mashi? ''..



Nan ta gaya ma Salma, yanda suka yi da Sadiq daga farko har karshe...



"Gaskiya ni Nana kin fara bani haushi, ke ba yarinya ba, amman kina abu irin na yara! Yanzun ai ko Sadiq ba sonki yake ba bai kamata ki kira wani a gabanshi ba har kike gaya mashi baki iya rabuwa da shi"..


"Yanzun Nana duk abunda nike gaya maki baki jin shi cikin kunanki kenan? "..


"Aah Salma ba haka bane, amman wallahi inason my Khalid sosai"..


"Karya kike Nana baki san Khalid, kiyi maza ki fidda Khalid cikin zuciyarki tun kafin dare yayi maki nidai Ina gaya maki gaskiya "..


"To Salma insha Allah, zanyi yanda ya dace, yanzun ya zanyi inba yaya Sadiq hakuri?"..


"Yanda kika ga ya dace ni kinga kwanciyata, dan gaskiya kin bani haushi sosai"..


"Ai bake daya ba koni naji haushin kaina baki daya, dan ni yanzun wata kunyar yaya Sadiq nike ji Allah, "ke dai kika sani Nana"..




Bayan Nana ta tafi, Sadiq ya tashi duk ranshi bace yana bala'in bakin ciki yaji koda sunan Khalid ya fito a bakin Nana, amman a gabanshi Nana ke cema wani katon banza MY, wannan kalma tana yi mashi ciwo sosai, dan haka dole ya samu mafita dan ya gaji da halin Nana..


Washe gari koda Nana ta tashi daga bacci, direct kitchen ta shiga dan yau tun 7 ta tashi bacci, dan haka ta wuce kitchen ta fara hada masu breakfast, tana cikin hada breakfast din taji kamar motsin mutun a bayanta tana waigawa taga Sadiq tsaye yana kallonta....


"Laaa yaya Sadiq kai ne?ina kwana"..

"Lafiya! nan Sadiq ya bi gaifenta ya wuce ya hada coffee yayi hanyar fita...


Nan Nana ta kama mashi hannu tace"yaya Sadiq, nan ta duge kai gu guda tana hawaye...



"Lafiya? Zaki wani kama man hannu sai kace abokinki, nan ya buge hannunshi ya wucewarshi ya bar Nana tsaye tana kuka...



Bayan ta gama hada breakfast din, ta wuce daki ta shiga wanka, tayi kwaliya sannan ta tada Salma bayan Salma ta gama shiryawa suka fito parlour tare suka zauna, sai da kowa ya zo amman banda Sadiq wai yace shi bai jin yunwa...


Haka dai Nana ta ci abinci ba dan dadi ba, bayan angama Momy ta hada ma Sadiq nashi ta ba Nana ta kai mashi...


"Assalama Alaikum "


"Amin, lafiya? Mai ya kawo ki guna Nana? ".


"Abinci nazo na kawo maka naga baka yi breakfast ba please dan Allah yaya Sadiq kaci abinci"..


"Haɗa kayanki ki bani waje Nana! In kuma kina so na bal'laki sai ki tsaya yi man wata magana taki marar ma'ana"..



"Ni kuma wallahi Yaya Sadiq bani fita har sai kaci abinci, haba da mai ake son naji cikin zuciyata? Da fushin da kake dani? ko kuma da abunda nike ji na rabuwa da Khalid da zanyi?".



"Tas! Wanann shine farko kuma na karshe da zaki kira sunan wani ƙato a gabana"..

"Yaya Sadiq marina kayi fa"..

"Eh Nana, indai zaki cigaba da kiran sunan wani namiji a gaba, to zan'iya yin komai dan kema kiji zafin da nike ji cikin zuciyata"..


"Nana kin san ko tun yaushe nike sonki? Ko kuma kin san yanda zuciyata keji in na ganki da wani kuma magana? "..


"Duk baki sani ba, hankalinki kwance ni ina can shekara da shekaru ina fama da ciwon sonki, amman ke kina can kina soyayyar karya da wani banza har kina ce mai *MY* a gabana"..


"Ko kuma ki shiga motarshi duk ina kallonki, amman ina hakuri to tunda abun naki bana hankali bane zanyi maganin abun dan haka get out of my room"



"Yaya Sadiq nika mara fa!''..

"Shin zaki fita ki ban waje ko sai na sake wanka maki wani marin? Get out madam kuma ki dauki abincin ki fita dashi bani ci"..



Haka Nana ta fita tana kuka wi-wi har ta isa part din Hajiya..


"Nana lafiya? Mai a kayi maki kike kuka haka? "..

"Momy y
Yaya Sadiq ne"..

"Yaya Sadiq mai, ke gaya man matsalarki lafiya kike kuka mai Sadiq yayi maki? "..


"Yaya Sadiq ya mareni, daga nace dole sai yayi kalaci"..


"Shi Sadiq din ya mareki? Dan kawai ki nuna damuwarki akan sai yaci abinci "..


"Kai Aiman wace ka kira mani Sadiq kace ni *KHADIJA SABI'U* nace yazo ina san ganinshi yanzun nan amman in ni na haifeshi"..



"Haba Ammi bai kamata ki dauki abun da zafi haka ba, kama ta yayi kiyi bincike kiji mai ya haɗasu ''..


"Ba wani binciken da zanyi Momy, da man ai ke kike daure mashi a cikin gidan nan , Sadiq da man Ina sane dashi ya matsama Mamana cikin gidan gidan nan, kai tashi kaje ka kirashi"..


"Yaya Sadiq, kaje inji Ammi, "to gani nan zuwa"..


"Ammi gani".


"Matso nan kusa dani, Tas! Tas!! Tas!!!


"Haba Khadija ya zaki dauki mataki har haka, kenan kin nuna Sadiq bai isa ya hukunta Nana ba? "


"Kai tashi ka ban waje, kuma dan Allah ba mari ba naga ka kawo man gawar Mamana cikin gidan nan, sanann zan san ka tsaneta"..



"Ammi dan Allah, "yi man shiru baka da bakin da zaka yi man magana Sadiq "..



"Kai ne Babba, baki daya zuri'armu kaine muke sa ran ko bayan ranmu zaka kula da yan'uwanka, Amman tunda ranmu kana wulakanta yar'uwarka mari Sadiq? , ai na sa komai Nana tayi maka bata cancanci haka daga gareka ba, yarinya mai hakuri duk daren duniya ita ke kai maka coffee Ina kallo na sa maka ido ai..



"Ina laifin wanda ya damu da kaci abinci? ".


"Ammi duk hakurin da nike da Nana cikin gidan nan baki gani Ammi? ".


"Wani kalar sone bani yi ma Nana? Nabi duk wata hanya da zan bi Nana ta gane ina sonta nabi, amman tana gani tayi kamar bata san ina yi ba"


"Sai ta kai da Nana tana kawo wani banza a cikin gidan nan da sunan saurayi haka nayi hakuri na sa ido cikin gidan nan, ba wai dan ban son ta, duk cikin kuka Sadiq ke bayani..



"Duk abun bai tsaya a nan ba naga Nana cikin damuwa na damu da naji matsalarta, amman ina tambayarta sai tace man wai *MY KHALID,* tsakani da Allah a gabana take nuna ma nuna ma wani *SO* , amman ni bata damu da wani hali zan shiga ba, haba Ammi, ya faɗa yana kuka mai cin rai...




"Sadiq, "Naam Hajiya, "wuce ka kaci abinci, naji matsalarku baki dayanku dan haka zanyi magana da iyayenku baki dayansu"...


"Hajiya,"na gama magana Khadija, ke kuma daga yau bance ki sake daukar hukunci a hannunki ba daga yau, ina fatan kin jini? "..


"Eh! Allah ya baki hakuri Hajiya, Nana bar kukan haka wuce ki kwanta ki huta Mamana"..


"To Ammi, dan Allah nidai kuyi hakuri "..

"Wuce nace ai maganar ta wuce"..


Haka Nana ta shiga daki duk bata jin dadi ba, dan bata son haka abun zai faruba da bata gaya ma Momy yaya Sadiq marenta yayi ba...



"Na boni ni Nana, yanzun yaya Sadiq aka mara a kan idona! Duk yanda ya dade yana sona, haka nai ta soyayya da my Khalid a gabanshi, amman bai ceman komai ba, dan ya mareni har ake rama man, ayya nayi ma kaina adalci kuwa? "..




"Salma dan Allah ki gaya man, nayi ma yaya Sadiq adalci kuwa?"..


"Hmm Nana kenan, tuni abunda nike gudu kenan, shiyasa nike gaya maki tun wuri ki rabu da Khalid amman ke yar soyayya kika ce baki iya rabuwa da masoyin ki ba, to ai yanzun gashina, kinji dadi an mari Sadiq gaban kowa cikin gidan nan ta dalilinki"..



"Wayyo Allah na, Salma dan Allah yanzun ya zanyi na ga yaya Sadiq yanzun?".


"Ki bi ta kofar baya mana sai ki fita ki wuce part din Sadiq ba wanda zai ganki sai ki bashi hakuri"...


Haka Nana tabi ta baya ta dauki hanyar part din Sadiq, gabanta na haduwa tana tunanin yanda zasu hadu da Sadiq...



"Salama Alaikum "



"Nana!


"Yaya Sadiq, dan Allah ka rufa man asiri ka ya feman dan girman Allah"..


"Tashi Nana, ni zance ki ya feman, zafin kishine yasa na mareki kuma banji komai ba dan Ammi ta rama maki marinki ba, ramawar da tayi shine dai dai"...




"Da bata rama maki ba ba zan yafema ma kaina ba, yanzun haka Zuciyata bata yafeman ba Nana"...



"Dan Allah Yaya Sadiq, nidai duk da haka ka yafeman kuma Insha Allah daga yau na rabu da Khalid da yarda Allah"..



"Nana da gaske kike zaki rabu da Khalid?".

"Eh yaya Sadiq nayi wannan alkwarin da yarda Allah"..



"Allah yasa Nana, Nana zo ki rama marinki dan Allah, ko naji saukin abunda nike ji zuciyata"..



"Haba yaya Sadiq nifa kanwarka ce ka isa ka hukantani indan nayi laifi"..



Nan suka zauna suna fira hankali har Nana ta samu Sadiq yaci abinci sosai, Nana ce bata bari part din shi ba sai da dare yayi tare suka tafi suka ci abinci sannan ta rakashi da coffee din shi har part din shi sanann ta dawo ta kwanta tana tunanin halin da Khalid zai shiga indan ya gano ba shine zata aura ba..




_By jameelah jameey_ 🖋






Share and comment pls

🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕
*NANA JAWAHEER*
🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕

*STORY And WRITING* *By*
*Jameelah A Belloh*
*(Jameey)*



*🌎MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M. W. A*


```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻
```

__________________________________



*BISSIILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*

```Gaskiya na gaji jiya da yau inayin mistake din numbers sai nayi posting akeman magana🤒🤒dan haka ga 41-45. Shine farko sannann 45-50 dan haka no Editing☹️😚```


Page_4️⃣1️⃣➖4️⃣5️⃣






Bayan yau sun gama yin breakfast Hajiya ta fara magana..


"Sulaima, "Naam Hajiya,"kana jina? "Eh inaji Hajiya, "yauwa ina san yau ba sai gobe ba kaje kace ma Adamu indai ni na haifeshi to inasan ganinshi yau yau din nan....




"To shikenan Hajiya, da man yana san yazo ya gaidaki sai yaga kamar bazaki yi hakuri ba, amman yanzun zan tashi naje na taho dashi....



"Ni na wuce Hajiya sai mun iso, "to kayi maza ka dawo sulaiman, "to...



"Momy ni zani gidan su Lukman"


"To Sadiq, Amman dan Allah karka jima sosai na sanka inkuka hadu baku san rabuwa"


"Insha Allah Momy, Ammi byee"


"Nana! "Naam Momy"


"Kiyi hakuri Nana, na san kina son Khalid sosai, amman Sadiq shi yafi dacewa da rayuwarki"


''Kinga shi Sadiq dan uwankine ba yanda za'ayi yace zai wulakantaki ko watan watarana, sannan Sadiq yafi Khalid sonki, ni tuni nasan Sadiq yana sonki, sai shi Sadiq yana da zurfin ciki"



"Amman wallahi Nana

Please Login or Register in order to submit comment