Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zakiji dadin zama da Sadiq a rayuwarki, sai kinyi mana godiya kice mun hada da miji mai sonki, na san zaki samu duk wani gata na rayuwa"



"Sadiq yana son ya ganki cikin farinciki, baisan yaga bacin ranki ko kadan ki daure ki koyama zuciyarki son Sadiq kinji Nana?



"Eh naji Insha Allah, Nagode da zab'in da kuka yi man, Allah yasa yaya Sadiq shine alkhari a cikin rayuwata Momy"



"Allah ya yi maki albarka Nana, insha Allah ba zaki yi kukan auren Sadiq ba, sai dai ku dauwama cikin farinciki "



"Ammi baki ce komai ba!!


"Ai ba abunda zance Momy, domin kin fadi duk abunda yake cikin zuciyata, sai dai nace Allah yayi masu albarka, ya albarkaci rayuwarsu damu dasu..



"Amin ya Allah.

________________________________



"Sadiq wai lafiya? Kazo ka kwanta kayi shiru baka ceman komai ba, maike faruwa?


"Man ba lafiya, ya kamata ace nayi farinciki amman ina tausayin Nana da Khalid..


"Bangane ka tausayin Nana da Khalid ba?


"Eh Man, jiya ai Marin Nana nayi, "Marin Nana garin ya haka ta faru Sadiq? dan ban sanka da saurin hannu ba..



"Raina ne ya baci, wallahi bansan na mareta ba, sai dai kawai naji tana cewa Marina kayi fa yaya Sadiq, sannan na gane ashe marinta nayi..



"Ka san ai na gaya maka tunda Nana ta dawo daga kar'karku bata sake yin walwala ba, har ina cewa da na sani ban kaita ba..



"Eh tabbas ka gaya man Sadiq..


"To naga tana exams bani son matsa mata da questions, sai kawai naje kar'karkun da kaina na tambayi Mama mai tayi ma Nana dan tunda ta dawo gida bata sake walwalaba tana cikin damuwa ni kuma bani san ganinta cikin damuwa..



"Shine take gaya man, ce mata tayi ta rabu da Khalid dan ita anyi mata miji, shine nace wannan shine abunda suka yi kenan aiko in hakane Nana na cikin damuwa ga ta fara jarabawa da mai zataji da karatu ko da tunani?


"Shine take ce man tun randa aka haifi Nana, Abba yace shi baida kudin da zai yi man hidima na matsayina na maraya wanda baida uba amman indan Allah ya raya Nana jawaheer to ya bani ita na aura, haka suka yi da Mama daga shi sai Mama suka yi wannan maganar ba wanda ya sani sai ni data gayaman nine mijin da Abba yayi ma Nana, ko ita Nana bata gaya mata ba ta dai ce mata inda lokaci yayi zata ganni...



"Man nayi farinciki sosai, haka na dawo katsina cikin farinciki da an'nashuwa, Amman Man Nana kullun cikin damuwa, bayan ta gama exams shekaran jiya nike tambayarta matsalart shine take gaya man wai Mama tace ta rabu da Khalid ita gashi tana bala'in son Khalid karka so kaji maganganu mararsa dadi haka na hakura na koreta ta bani waje..



"Wai da safe ta isheni nayi hakuri akan maganar da mukayi jiya, amman bata fasa gaya man wani Khalid ba, niko na wanka mata mari..



"Shine ita kuma Ammi ta rama mata marin da nayi mata, ni kuma na gaya masu abunda ya hada masu da yanda nike sonta, shine yau da safe Momy ke ceman Hajiya tace yau zata sa ranar bikin mu nida ita Nana kaji yanda aka yi..



"to gaskiya Sadiq kayi hakuri sosai ma, amman kuma gaskiya kayi kuskure da ka mari Nana, amman komai ya wuce angon Nana, ai yanzun hankali sai ya kwanta ko?


"Aiko Man sai dai ya Khalid zaiyi, dan naga yana son Nana sosai?


"Hakuri zai'yi kuma ai kafi shi son Nana da kuma kai ta dace..

"To shikenan Allah ya bashi hakurin...


_____________________________

'Hajiya ina wuni?

"Lafiya Adamu, sai yanzun nike ganinka ko?


"Aa Hajiya ba haka bane, amman dan Allah kiyi man hakuri, insha Allah ba zan sake ba..


"Shikenan ya wuce"

"Da man Nana jawaheer Sadiq yace ya so ya aura, Amman ita Mamar Nana tace randa ta haifeta kayi mata miji, amman bata gaya mana waye mijin ba, shine nace aka kiraka muje waye mijin..


"Eh hakane tun randa Aminatu ta haifi Mamana nayi mata miji..


"Munji mukace waye mijin? shi muke bukatar ji ai ba wani bayani ba adamu..


"Hajiya Sadiq ne mijin ai, tun da aka haifi Nana nace ga matar Sadiq tazo duniya insha Allah..


"Ka san kayi ma Nana miji mai yasa ka barta ta fara kula saurayi?


"Saboda naga Talatu ta matsama Mamana da yawa, bata da abokin da zai ringa rage mata kuncin da take ciki shiyasa na yarda da ta kula samari, amman bance mata wani abu bayan nan ba..



"To shikenan, na gane abunda kake nufi, dan haka inason asa bikin Nana jawaheer da Sadiq yanzun cikin dakin nan..



"To Hajiya, amman yanzun Nana karatu take..


"Karatu fa kace sulaiman? Wai kai sulaiman har sai yaushe zaka ajiye wanann dibi'a ta ya hudanci? Yarinya tana da miji a hannu mai ake jira inba ayi mata aure ba, Aa kafi so taita zama cikin gida ko?



"Aa bahaka nike nufi ba, amman saura shekara biyu ta gama, dan haka zamu daura masu aure amman ba yanzun zata tare ba har sai ta gama karatu, amman ya kuka gani?



"Ni ban yarda ba, ban yarda da kalar wanann daurin aurenba, kai nacan kana hidimar gabanka yaran da suke zaune gida daya taya za'ayi kallar wannan aikin a gabana ai kafin ta gama sai dai ku ganta da tsohon ciki ko kuma tana goyo cikin biyu dole ayi daya...



"Dan nayi hakuri nan da shekara biyu nike son ayi auren Nana jawaheer da Abubakar Sadiq ko da bani rai..




"To shikenan Allah ya kaimu lokacin, kuma insha Allah kina da ranki Hajiya...



Nan dai suka kara tautaunawa yanda lamarin zai sakance sanann Malan Adamu ya tafi gida , yana farinciki burin shi zai cika..

_____________________________


"Man ni zani tafi gida kaga har mangarib tayi, "to mu shiga mosque muyi sallah sai mu wuce tare dan yau da man zanzo zance, "to tashi mu tafi...



Bayan an gama sallah sanann Sadiq da Lukman suka taho gida tare, bayan sun dawo gida suka shiga part din Hajiya suka zauna nan Hajiya ke gaya masu hukuncin da aka yanke kansu kuma sunyi naam da batun..



''Sadiq gobe insha Allah, zanyi ma khalid bayanin yanda komai ya kasance kuma na san zai fahimta..


"To Allah ya kaimu Man.

Nan Lukman ya tafi gida, shi kuma Sadiq yayi shirin kwanciya, bayan ya gama shan coffee...


Washe gari bayan Lukman ya gama abunda yake ya shirya ya wuce gidan su Khalid...


Bayan ya isa gidan su Khalid, yayi sallama ya shiga ya gaisa da Fulani da Baffah sannan ya wuce part din Khalid..



"Khalid ikon Allah, ana nan ana hutawa kenan?

"Hmmm wani hutun Man, daman yanzun nike shirin zuwa wajenka sai kaga kama zo..

"Lafiya dai ko?


"Ina fa lafiya, duk jiya Nana bata dauki waya taba ko daya nayi mata message amman ba reply duk hankalina ya tashi Man sosai..



"Kwantar da hankalinka muyi magana to, "kana jina?


"Eh ina jinka Man..

"Yauwa Khalid, kana san dai Nana tana sonka ko?

"Eh sosai ma Nana tana sona nima haka..


"To jiya Abban ta ya fidda mata miji, ina jin shiyasa bata dauki wayarka ba..

" *INNALILLAHI WA'INNA'ALAIHIRAJIUN* "


"Man kana nufin yanzun sai dai nayi hakuri My jawaheer?


"Haba Khalid karka bani kunya mana, tabbas nasan da ciwo rabuwa da masoyi, to amman ya za'ayi hakuri zamuyi da kai har ita Nana jawaheer..


"Wallahi Khalid Nana jawaheer tana cikin wani hali na rabuwa da kai amman ba yanda zatayi inba hakuri ba..



"Kuma kasan duk mai san ya gama da duniya lafiya, to dole yabi umirnin iyayenshi..


"Da ka tada hankalinka gwara kayi hakuri kaje har gida ka kwantarma da Nana hankali, amman kai kana cikin wannan situations din to ita Nana tayi hauka kenan?



"Man! Dan Allah kace wasa kake man, dan Allah da gaske kake anba Nana miji?

"Khalid kasan bamu kalar wanann wasan dakai balle nasan yanda kuke san junanku kaida Nana taya zanyi maka kalar wannan wasa?



"Haka ne Man, shikenan Allah yasa haka shine mafi alkhari a wajenmu, amman waye mijin?


"Sadiq ne mijin.

"Sadiq! Sadiq!! Bakomai ai wata kusar tafi kusar, kace ma shi Sadiq din ina tayashi murna sannan Ina fatan zamu cigaba da zumincinmu yanda muke.


"To shikenan Khalid, da man shi Sadiq bai da matsala shi yace ban san da wani ido zai kalleka, dan ba dan san ranshi haka ta kasance ba iyayensu ne sukayi wannan hadi..


Hahaha kunji Man yana yar-karamar karya wai bada san ran Sadiq komai ya faru ba🥺


"Hakane gaskiya, "yanzun Khalid tashi mu tafi gidan tare kai mana..



"Aa Man kayi gaba yanzun zan gaya ma fulani komai, ka ga ya kamata tasan halin da ake ciki ko?

"Eh hakane ni na wuce sai kazo, "ok byee..




Bayan tafiyar Man, sai da Khalid yayi kuka sanann ya samu saukin abun yane ji cikin zuciyar shi da man kallar wannan ranar yake gudu, kuma gata ta sa mai shi, bayan ya sake yin wanka ya tafi wajen Fulani..


"Fulani na rasata"wa ka rasa Noor?


"Wallahi Fulani zan iya mutuwa in har basu bani ita ba, na boni ni Khalid, Fulani banda anfani a duniya tunda na ra sata..


"Subuhanilillah, haba Noor, ya zaka sani gaba kana kuka kana ka rasata, duk ka tadda man hankali ka daure ka gaya man wacece ka rasata haba Noor..



"Fulani MY JAWAHEER.


"Mai yasa mu Jawaheer din? Mutuwa tayi ne?


"Ko daya Fulani, sai dai ni suka kashe da raina Fulani..


"Fulani sunyi ma Jawaheer miji, bani ba bayan sun san kalar son da nike yi mata..


"Allah sarki, yi shiru Noor daina kuka..


"Haka Allah ya kaddara kaji Noor, da man Allah yasa NANA JAWAHEER ba matarka bace..


"Ina san ka zamo jarumin namiji mana, jarumin namiji ba komai yake yi ma kuka ba, duk rintsin abu kuwa, dan haka ka sama zuviyarka salama Noor dan Allah kar wannan abun ya shafa rayuwarka ka daina walwala ko wani abu..


"Na san itama Jawaheer din tana can cikin wani hali, a wannan yanayin Jawaheer take bukatar lailashi daga gareka, indan kayi mata haka zata ji sanyi a zuciyarta, Allah yasa haka shine alkhari a gareki, yi shiru please Noor..


"To Fulani, insha Allah zanyi shawarar da kika bani dan irinta ce Man ya gaya man, dan haka ni zan tafi gidan su Jawaheer na bata hakuri dan Allah SWT yace :-Mutum baya zama cikankan Muslimi har sai yayi Imani da kaddara mai-kyau da marar-kyau, dan haka Fulani kinga ai yarda da kaddara ya zama dole ga duk wani Muslimi..


"Haka ne Noor, Allah hada ka da mafi alkhari, "Amin Fulani, byee ni na wuce gidan su Jawaheer...

_________________________

Bayan Khalid ya shiga gidan su Nana, direct part din Sadiq ya wuce..


"Sallama Alaikum "


"Amin walaikumus salam, Khalid sannu da zuwa..


"Yauwa Sannu Sadiq ya gida? "Lafiya lau Khalid..


"Ina taya ka murna, sannan Allah yasa ayi damu...


"Amin ya Allah, am dan Allah Khalid..


"Shssss🤫 Sadiq ba sai kace man komai ba, na yarda da kaddara ta, haka Allah ya kaddara soyayya kawai zamuyi da Jawaheer Amman banda aure..


"Allah ya kaddara kaine mijin NANA JAWAHEER wallahi komai za'ayi sai ka aureta, baka san rabo yana kashe mutun ba?


"To idan nayi jayaiya da hukuncin Allah wani kalar sakamoko zan tadda a gobe kiyama?



"Dan haka wallahi na yarda da kaddara na barma Allah lamarina, tabbas abun yana da ciwo rabuwa da masoyi, amman kalar wannan rabuwar ya zama dole a rabu dan haka bakomai, ni nazo nayi magana da Nana amman inka bani izini..



"Tabbas naji dadin jin haka da gareka Khalid, kai din mutun ne harda rabin mutun, Allah ya saka maka da alkhari Khalid..


"Amin ya Allah..

"Yanzun kuwa zakuyi magana da Nana bari na aika a kirata..


"To shikenan, nagode Sadiq...



"Nan Sadiq ya aiki Aiman yace yaje yace ma Nana taje garden yanzun zasuyi magana, nan ya ba Khalid juice ya sha sannan ya tashi ta tafi garden...



Bayan Aiman ya gaya ma Nana Sadiq na san ganinta a garden, ta tashi ta samu ta shirya poder kawai ta shafa ta sa hijab ta tafi garden..



"Jawaheer, waigowar da Nana zata yi sai taga Khalid..


"Jawaheer!! Ba kuka zaki yi ba, hakuri zaki yi..


"Jawaheer, yanzun zaki nuna man kalar Son da kake man indai na gaskiya ne, "taya haka zata kasance Khalid?



"Zata kasance mana!! Kin san yanda zata kasance? "Aah bansaniba..


"Yauwa ina san kiyi biyaiya ga iyayenki, su suka haifeki kinga ko sunfi kowa sonki..



"Sannan sunyi maki zabi'in ransu, sai ki ansa zabinsu hannu biyubiyu, kinga zaki ce ribar biyaiya ga iyaye a rayuwa..



"Balle na tarbata Sadiq ba zai barki kiyi kuka da dana sanin bin iyayenki, saboda naga zallar sonki cikin gangar jikin Sadiq, sai yanzun na fahimci Sadiq yana sonki shima, kinga ko shi yafi dacewa da ya aureki, tunda gida bai koshi ba ai ba'anba na waje ba, dan haka kiyi hakuri kinji?


"Eh naji, nagode sosai Khalid, kaima Allah ya baka wanda ta fini Khalid..



"Uhmm Nana, sannan ina san ki zamo mai yarda da kaddara, ina san mutun mai yarda da kaddara mai-kyau da marar-kyau, Allah yayi maki albarka,Allah ya kaimu lokacin bikin lafiya, ni zan wuce Nana sai watarana..



Haka Khalid ya samu ya lailashi Nana sanann ya kama wajen Sadiq suka cigaba da labari shine bai bar gidan ba har da akayi lunch da shi sannan ya dawo ya kwanta yana kara godema Allah...



_By jameelah jameey_ 🖋





Share and comment pls


🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕
*NANA JAWAHEER*
🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕

*STORY And WRITING* *By*
*Jameelah A Belloh*
*(Jameey)*



*🌎MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M. W. A*


```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻
```

__________________________________



*BISSIILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*




Page_4️⃣5️⃣➖5️⃣0️⃣





Washe gari bayan su Nana sun tashi, suka gama hada masu breakfast, sannan suka zauna suka yi bayan sun gama suka yi aikin gida sannan suka shirya ita da Salma yau zata je ta gaisa Baba..




"Momy mun shirya mu zamu wuce, "to Nana dan Allah karda ki biye ma Talatu in kunje, ki barta da aniyarta kinji? ", eh naji insha Allah"..



Nan suka dauki hanyar kofar kwaya zasu su gaida Baba...


"Nana wai yaushe hutun ku zai kare ne? "This Monday ake resuming, amman ni sai next week monday zanyi resume"..


"Ok shikenan Allah ya kaimu lafiya,"Amin ya Allah, nan suka ida isowa gida, tun daga kofar gida suke jin hayaniyar Talatu da Lami mai adashe"...



"Wallahi Talatu yau ko kina yawo da bakar jaba cikin garin nan sai kin bani kudin adashena ko kuma hukuma ta rabamu da ke"..



"Ni kuma Lami banda kudi dan haka bani badawa in kin tashi ba hukuma ba ki daukoman barikin sojoji cikin gidan nan, ehyeeh"..


"Haka kika ce ko? "ga zahiri nan kin gani, tunda banda su ai ba yanda za'ayi dani, "aiko da yanda zanyi dake matsiyaciya, in ba ma tsaya ba baki da komai balle na dauka na fidda kudina"..


"Wallahi kece babbar matsiyaciya, dan ni ban gaji tsiya ba, ke da kika gaji tsiya ai ga kinan kinzo kinyi man tsaye tun safe saboda da dubu goma"..




"To na gani a kasa in baki gaji tsiyarba, ki ban kudina yanzun-yanzun nan ba sai anjima ba, matsiyaciya kawai dake"..



"Haba Inna taya zaki biye mata ku kama fadi saboda da dubu goma? "


"Bala'i ke Nana dan uwarki ni zaki zo kina gaya ma magana matsiyaciya munafika mai mugun hali irin na uwarta"..



"Yi hakuri Inna ban san ranki zai baci ba da banyi maki magana ba"..


"Wannan matsalarki ce, wato angama yawon karuwanci a dawo mana gida da masifa ko?


"To wallahi ba dai gidan nan, dan bani zama da ke cikin gidan nan, yanzun idonki ya bude abunda kika sani ni tsohuwar mace ma bansan shi ba"..


"Haba baiwar Allah, ya zaki ringa yin kallar wanann maganar marar dadin ji".



"Ke kuma yi man shiru tunda ban sako kiba ban kasa dake ba dan haka bance ki kausa ba"..



"Salma yi shiru ki gyale ta kin manta Momy tace karda mu biyeta ma? "Eh hakane fa Nana, dan ni banga hankali a nan ba"..


"Ni zaki ce ma banda hankali, wallahi yau gidan za'ayi bala'i"..


"Ba dai damu za'ayi ba sai dai ku cigaba da inda kika tsaya keda wannan matar"..

Salma tace ma Talatu haka tana nuna Ba'ba Lami da yatsa..

"Salma kiyi shiru dan Allah, Inna dan Allah kiyi hakuri..


''Banyi! Da hakuri ya mutu sarakar nawa kika bada marar mutunci?"..



Nan Talatu tai ta masifa ita daya cikin gida, dan su Nana basu kara ce mata ci kanki ba..


"Ba'ba Lami ga kudin adashin kinan dan Allah ki ringa hakuri, nasan Inna bata da kudi da ta baki kudin ki tuni"..


"To bakomai Nana nagode, da man kudin mutane ne nima sun matsa man shiyasa kika ga har haka ta faru, "to Allah ya kiyaye gaba"..



Bayan Lami ta tafi Baba ya dawo, nan suka zauna suka fara gaisawa..


"Baba ina wuni? "Lafiya lau Mamana, "Baba ina wuni, "lafiya lau yarinya".


"Duk ya gida? "Lafiya lau Baba, ya muka sa maika?".

"Lafiya lau Alhmdulh, Mamana ya karatun? ".

"Alhmdulh Baba, wannan satin ai aka koma, amman ni sai na sama zan koma"..


"To Allah ya taimaka, Allah yayi maku albarka, "Amin Baba, Baba mu zamu shiga mu gaida Ummin su Zee"..

"To sai kun dawo"..


Bayan su Nana sun je gidan su Zee ta gaida Ummi sannan suka shiga daki..



"Nana gobe ne z'a koma school fa, "eh Zee amman ni sai next week insha Allah, "Allah ya kaimu"..


"Baiwar Allah sannu ya hanya? "Lafiya lau, amman sunana Salma"..


"Oyoyo yau dai naga Salma da idona, ai kullun muna shan labarinki wajen Nana a school''..


"Hahaha nima yau naga Zee dan nima kullun Ina shan labarinki wajen kawarki, "Allah sarki, yau dai gamu mun hadu, "aikuwa".



"Zee ban gaya maki ba, "to Nana gaya man inajinki".


''Mun rabu da Khalid"..

"Saboda mai ya hadaku? "..

'Bakomai, kawai dai Baba ya fidda man miji"..


"To wai Nana waye wannan mijin da aka fidda maki? "..


"Yaya Sadiq ne"wow gaskiya Nana ina taya ki murna kinyi dacen miji, shikuma Khalid Allah ya hadashi da alkhari"..



"Amin ya Allah Zee, nan dai Nana ta gaya ma Zee yanda komai ya faru, ita kuma Zee suka bata shawara sosai, sune basu bar gidan su Zee ba sai da la'asar sannan suka koma gida, sai da dare yayi sannan suka dawo gida"..



Bayan sun dawo gida suka shiga suka shirya suka fito suka ci abinci, bayan sun gama cin abincin Nana ta hada ma Sadiq nashi abincin da coffee ta wuce ta kai mashi..



"Yaya Sadiq ga fa abinci naga baka shigo akayi dinner tare ba"..

"Wallahi Nana tunaninki ne ya hanani sukuni shiyasa"..


"Laa yaya Sadiq harka bani kunya wallahi, "kunya ko Nana? To kizo ki cire wannan kunyar nadai fadi maki gaskiya"..


"Nidai ga abincin ka nan na kawo maka,"to ni zan zuba da kaine kenan myluv? "Aah ni na isa na barka ka zuba da kanka ai ina san nasamu lada tun yanzun, nan ta tashi ta zuba mashi". .


"To sai ki sauko muci tare, "Wayyo Yaya Sadiq kana san cikina ya fashe ko? "..



"Aah bani so complainer"..


Nan Sadiq yaci abincin shi Nana na zaune gefanshi ta na hada mashi coffee, bayan ya gama shan coffee ya fara magana..


" *NANA JAWAHEER* !!


"Naam yaya Sadiq!!

"Kina jina? Ki bude kunnanki da kyau ki saurareni sosai, "to Yaya"..


"Nana nasan ni mai laifine a wajenki, ina mai kara neman ya fiyarki ga duk wani abu da nayi maki, wanda nasa ni da wanda ban sani ba"..



"Yaya Sadiq ni baka yi man komai ba, inma kayi man to na yafe maka har abada"..


"Nagode Nana, sai magana ta biyu, dan Allah Nana ki daure ki anshi kaddaraki hannu biyu, ki sauya soyayyar Khalid daga zuciyarki ta dawo gareni domin nafi kowa cencenta da kiyi man ita harma kiyi man wanda tafi wanda kike yi mashi"..



"Nana! Sadiq yana Sonki sosai, dan Allah kema ki soni ko rabin yanda nike sonki ne, wallahi ba zan yarda naga hawayenki sun zuba kasa ba inda ba na farin ciki bane"..




"Ki manta da duk wani abu da nayi maki, wallahi Nana komai nayi maki a rayuwata duk sonki ne ya ja nayi maki haka, dan ina bala'in sonki dan Allah Nana karki juya man baya duk rintsi duk wahala, ki bani hadin kai na nuna maki nima irin nawa salon so Nana Jawaheer"..



"Yaya Sadiq insha Allah, ni da man yanzun na manta da munyi soyayya da Khalid yanzun na maidashi a matsayin Yayana, insha Allah zanyi iya bakin kokarina wajen naga nasaka farinciki kamar yanda nima kake son nawa farincikin a koda yaushe"..



"Yaya Sadiq kai Yayana ne kuma masoyina na gaskiya, wanda yake sona tun bankai mace ba, kaine ka fiddo ni daga hukubar gidanmu sannan baka da burin da ka nayi karatu nima nazama wata a duniya"...


"shin ni mai zai hana da ba zan nuna maka ko wani kalar so ba a duniyarnan, Yaya Sadiq kaine rayuwata a yanzun tunda nan gaba zaka zama miji a gareni kaga dole ka zama rayuwata dan haka kabar neman yafeya a guna ko kuma neman alfarma wajen zama a cikin zuciya ta"...


"To Nana, Allah yayi maki albarka,"amin".


"Magana ta uku kuma"..

"Uhmmm! Ina jinka Yayana..


"Gaskiya bani san wannan Yayan fa"..

"Uhmm to gaya man wani suna kake so"..


"Ina san daga yau na koma da suna *MYLUV* , kema haka zan ringa kiranki da shi"..



"Insha Allah daga yau ka tashi daga Yaya Sadiq ka koma *MY LUV* "..


"Tom, thank you my luv".


"Na san idanuwanan suna jin bacci ga dukan alamu? "..


"Eh suna jin bacci, amman basu gaji da gani abincinsu ba, Amman in anbasu izinin kwanciya ai shikenan".



"Eh na basu izini, amman ba dan nawa idanun sun gaji da kallar kyaukyawar fuskar zinariyar da ke gabana ba, sunyi hakuri kawai dan suna bukatar hutawar sauraniya Gimbiyar mata, autar mata".



"Hakane masoyina na har abada, zan tafi na kwanta, amman ka sani gangar jikina ce kawai ta tafi ta kwanta amman ruhina da zuciya suna tare da maisona sai da safe"..



"Sai da safe myluv "Ilove uh too, "love uh more"..



Bayan Nana ta tafi ta kwanta, ta bar Sadiq da tunanin maganganun da suka yi yana jin dadi yana gode ma Allah dan shi ko yayi sa'ar mace a rayuwa.


```LOL!! TEAM KHALID KUJI SADIQ DA WATA RASHIN KUNYA☹️😎```



Yau Monday, yau Nana zata yi resume a school dan haka tunda safe ta tashi ta shirya nan sukayi breakfast suka tafi..



"Myluv! "Naam myluv"..


"Yau karfe nawa kuke tashi lectures?"..


"Four insha Allah, "ok in dan an tashi zaki rakani wani waje, "ok shikenan myluv". .


Haka Sadiq ya aje Nana wajen lecture sai da suka gama soyayyar su sannan ta fito shi kuma ya wuce wajen aikinshi..



"Zee, "Sannu uwar yan-soyayya sai yau kika yi niyar dawowa ana can ana ta zuba soyayya an manta da boko"..



"To mai hafi raina Zee ai gyara nayi soyayya, balle soyayya da masoyinka kuma Yayanka ke ko ya zaki hango wani soyayya?"..


"Gaskiya ne Allah ya baku Sa'a Nana, "Amin ya Allah Zee, ya gida Yasu Ummi? "Wallahi duk lafiya lau suke, ya Salma kawata? "Ta nan, itama ta tafi wajen aiki, kin san NYSC take a nan FMC shiyasa, "ok Allah ya maidamu adanshensu, "Amin ya Allah"...




Nan dai lecturer ya shigo yayi masu lecture yayi tambayoyi ya kama gabanshi, bayan sun fita sunje sunci abinci suka wuce office din Khalid suka gaisa ya tambayesu ya karatu suka ce Alhmdulh sannan suka shiga lecture din 2-4 bayan sun fito, Khalid ya dauki Zee zai kaita gida ita kuma Nana ta tafi wajen Sadiq su tafi..


______________________________


"Zainab ya karatu? "Alhmdulh, "Allah ya bada sa'a, "Amin ya Allah"..



"Da

Please Login or Register in order to submit comment