Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

coffee...




"Sallama Alaikum, Yaya Sadiq, "Amin, shigo kinyi wani tsaye sai kace dogari, "Allah ya baka hakuri, ga coffee nan ni na tafi, "ke waya ce ki tafi? "Bakowa, "to tsaya ina son magana dake, dan haka kina iya jira, nan Sadiq ya sanya Nana tsaye, ya cigaba da hidimar gabanshi kamar bai ajiye kowa ba, sai da ya tabbatar ta gaji sosai sanann ya fara magana...



"Uban waye na ganku dazun cikin gidan nan? Ba magana nike yi maki ba? "Yaya Sadiq, Khalid ne fa, "What, uban waye shi da zai shigo mana har cikin gida, ke kuma kin saki baki sai dariya kike yi mashi kamar wani Yayanki? "Shine wanda zan Aura fa, "kin san Allah kika sake yi man maganar wani wanda zaki aura cikin gidan nan sai na bata maki rai, ke har kin kai ace ana sonki balle har a aureki, Nana duka yanzun kike shekara 18, ina lissafi har yanzun baki ida cika 18 ba, amman har kinsan soyayya...



"Shin karatu zaki yi ko kuma soyayya? "Karatu, "Yauwa good girl, daga yau karki kara kula wani saurayi Idan kina son mu shirya dake cikin gidan nan, ina son kiyi karatu sosai kinji kanwata? "Eh naji, "dan haka ba ruwan ki da wani Khalid, ki kyale shi kiji da karatunki, dan karatun umyu sai mai kokari, sakarai baya iya karatun umyu, tunda su duk shekara in baki kai 1.5 ba sai sun kori mutun, kina son a kore ki kine? "Aah bani so, "as you wash, in kinyi karatu ur business , in ma baki yi ba duk business dinki ne, tashi ki ban waje dare nayi, "to sai da safe...


*Kuyi hakuri da wannan wallahi yau banda lokaci shiyyasa☺️*



_By jameelah jameey_ ✍🏻




Share and comment pls



🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕
*NANA JAWAHEER*
🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕

*STORY AND* *WRITING BY*
*Jameelah A Belloh*
*(Jameey)*


*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻```

_________________________________


*BISSIILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*





Page 2️⃣0️⃣➖2️⃣5️⃣





Washe gari, bayan Nana ta gama taya Momy hada breakfast, sai taje ta shirya tsa, sannan ta fito parlour tana zauna suna gaisawa da Hajiya...



"Hajiya wallahi jiya na gaji sosai, "To Takwara ya zaki yi tunda kince dole sai kinyi boko, ai yanzun kika fara shan wahala, dan haka sai ki ta hakuri, "Hajiya ai da mun gama registration wahalar nan ta kare, Uhmm nidai bari na tashi naje na tada Yaya Sadiq kafin su Ammi su fito, dan gaskiya yau bani son jiran nan da nayi mashi irin na jiya...




"Yaya Sadiq, wakeup mana, yanzun fa 9 tayi fa, "to in nine tayi sai ayi yaya Nana? Mai yasa kike san matsa man da safe?



"Yaya Sadiq, wallahi ban san na makara ina son na dawo da wuri yau, dan zanje nayi registration a Isilamiyar su Aiman shiyasa...



"To naji je hada man ruwan wanka, tunda kin kawo kan ki, "Wayyo Allah Yaya Sadiq na shirya fa, "ba ki zuwa ne? "Ni na isa, "ok sai kiyi Sauri...



"Yaya Sadiq tashi ka shiga wanka, ni zan koma nayi kalaci, "ban salamai ki ba, dan haka sai ki fito man kayan kasa da komai ya dace na sa, kuma in kin fito bance ki tafi ba...

_____________________________



"Inna, wai mai kika dafa mana yau da safen nan? "Kai Sabi'u bani san walakancin banza, yau kwana hudu ban saka a idona ba, "yo sai mai in kinyi kwana hudu baki gan ni ba? Dan haka ba damuwarki bace, dan haka daga yau karki sake ki sa man ido nidai na gaya maki gaskiya..



"Sabi'u ni kake cema haka? Inalillahi wa'innalaihirajun, yanzun Sabi'u da mai zanji da rashin kunyar Khadija ko da wannan halin naka daka dauko, kuma mutun ace bai son a tambaye shi ina yake zuwa, dan kawai karda ranka ya baci? To wallahi dole na tambayeka inda kake zuwa...


"To shikenan, sai kici gaba da tambaya watarana zaki yi da na sani, "Sabi'u ni zanyi da na sani? To shikenan Allah ya baka sa'a, "Amin ya Allah...

_____________________________



"Yauwa Momy mu mun wuce, "To Nana Allah ya taimaka, ya baku sa'a, "Amin Momy, sai na dawo, Yaya Sadiq ka taho dan Allah pls...



"To je ki jirani a bakin mota, sai nayi sallama da matata sannan, ya fada yana kallon Hajiya yana dariya...


"Ni ba matarka bace, dan na fasa aurenka, ni Aiman shine mijina dan haka maza ku tafi, karka makaran man da Takwara a boko...



"Yo dan anbar ta ta makara ai sai tayi hakuri, tayi fushi itama tayi ma Dady magana ya siya mata mota itama, "kaga ni wuce ka bani wuri...



"Nan dai Sadiq ya kai Nana National as usual kafin ya sauke ta sai da ya buge mata warning karta kula Samari,, sai dai tace to kawai dan ita dankalinta baki daya na wajen Khalid, dan yau in sun gama registration zata tsaya office din shi...


"Sauka mun iso ko, "to shikenan yaya Sadiq dan Allah yau kawai ka kaini Umyu da kan ka, kaga ba sauran bus fa, ta ida maganar ta dire kafafu, da yarfa hannu, "to naji sai ki shigo na kaiki, kuma wallahi ki sani yau kawai zan kai ki, dan karki sake ki ceman haka...



"To naji, nagode haka ma, nan suka sauki hanyar Umyu, amman tasha warning kala kala kafin su isa Umyu, ba ida ya ajeta sai senate nan ta shiga ta anso form dinta, daga nan ya ajiye ta a Sciences, sannan ya wuce shima ya fara shirin NYNC din shi,saboda anyi posting din shi a UMYU amman cleaning din su zaiyi ma aiki, da man shi bai shiga camping ba, dan shi baida gurin shiga camping, dan rayuwar camping ba burgeshi ta ke....


Ita kuma Nana bata je office din Khalid ba sai ta ta gama yin komai dan harta result dinta na cleaning duk ya fito, Shiyasa tayi murna sosai, dan bata sake shigowa sai in zata fara attendance lectures, bayan taje office din Khalid shima warning ya dan yi mata na karda ta kula ko wani Samari...



(to fah kunji wai Khalid ke ma Nana warning sai kace ance an bashi☺️)


Bayan Khalid ya gama aiki a office sai ya dauketa ya kaita national, dan yau Zee ta riga Nana zuwa makaranta, shiyasa ta riga ta koma wa gida..


Bayan Khalid ya ajiye Nana a National, juya war da Nana zata yi sai suka hada ido da Sadiq..



"Na boni My Khalid, "lafiya kike cewa kin boni? My Jawaheer, "My Khalid, Yaya Sadiq, "waye haka kuma? "Yayana ne mana, kuma ya hanani kula Samari har sai na gama karatu sannan, "to ai ni My Jawaheer naga nine wanda zaki aura, kinga ai ya ka mata ace ya san ni, dan haka bari naje na gaishi, wuce mu tafi....


"Yaya Sadiq, ga Khalid nan ku gaisa, my Khalid, kazo ku gaisa mana..


"Sallama Alaikum,"Amin wa'alaikumus Sallam, "yaya Sadiq sannu, ya na samai ka,"lafiya, ke kuma sai ki shigo mu wuce gida, in kuma shi zai kai ki sai naji? "Aa yaya Sadiq, my Khalid sai munyi waya, bye...


_____________________________


"Khadija, Inalillahi mai zan gani haka? Yanzun Khadija abunda kika daukarma kanki kenan? Duka nawa kike da zaki fara sayeye? ehye Khadija yanzun fa kike da shekara sha hudu fa, amman kike wannan *MUMUNAN DABI'A* ...



"Dall Allah can ni kiyi man shiru, zaki cika mana kunne da haniyarki, sai kace wata sabuwar kamu, "Sabi'u ni kake cema sabuwar kamu? "Eh mana bani ce maki sabuwar kamu, sai yau kika san wannan yarinyar tana harka sayeye? Ai ita ya ka mata ki sama ido ba ni, dan haka ai sai ki tashi daga dogon baccin da kike"..



"Na boni, Sabi'u ! yanzun Sabi'u ka san abunda Khadija take aikatawaa, amman baka gaya man ba? "..


"Kanki ake ji dai, ni kinga tafiya ta, nan Sabi'u ya tafiyarshi ya bar Talatu da cizon yatsan hannu, ga yanzun Malan Adamu ya sa masu ido, yace suyi abunda zasuyi dan shi sun fi karfin shi....


_________________________



"Nana, wai maiyasa baki jin magana ne? Kina son kullun sai nayi maki fada ko? Ke kullun dai kiga kin sa man ciwon kai sannan kike jin dadi"...


"aah Yaya Sadiq, ba haka bane, kuma naga Khalid shine wanda zan aura shiyasa nike kulashi, "dan zaki aureshi shine aka ce ki shiga motarshi ko? "Aah lecturing yake yi a Umyu shiyasa da zan taho ya rageman hanya...



"Lecturing! dan yana lecturing sai aka ce kullun shi zai dauko ki ko? Shikenan tunda ni baki jin magana ta zan gaya ma Dady abunda kike yi, kina shiga motar saurayi"...


"Aah dan Allah kayi hakuri, ba zan sake ba insha Allah, "ai Nana ba class din ki bane shiga motar saurayi, kuma ina baki kudin bus amman baki shiga, sai ki shiga mota daga ke sai shi, kuma shi ba dan uwanki ba kuma ba wani naki ba, dan iya karshi saurayinki ba mijinki ba"...



"Dan Allah kayi hakuri, ba zan sake ba, "Allah yasa Nana, anjima ki shirya zaki raka ni wani waje, "to Allah ya kaimu".


Nan fa Sadiq suka iso gida, shi ya wuce part din shi, itama Nana ta wuce nasu part, tana yin wanka bacci ta kwanta kafin anjima ta tashi ta raka Sadiq wani waje..

______________________________


"Salma wai yaushe zaki tafi katsina wannan services din? , naji Babanki yana fadi man zaki tafi gidan Alhaji Sulaiman nan zakiyi services...


"Ni fa Umma ban san wannan Alhaji Sulaiman ba da Baba ke ta fadi gidan shi zan zauna nayi services dina".....


"Eh hakane ai Aminin Babanki ne, tare suka yi secondary a Makarantar maza ta kwana da ke a malinfashi katsina, sannan kuma suka sake haduwa a nan buk, kuma suna business a tare, iyalinshi na zuwa gidan nan sosai, dan kafin ki dawo yaronshi nan gidan yayi hutu Aiman sunan yaron...


"Allah sarki, ai ni ban sani ba, da man ai gobe ne zani fi katsinar haka yace, amman yace ban ta fiya da motana, "karki damu da maganar mota nan san gidan suna da motoci sosai sai ki hau wanda kike so, ni dai dan Allah Salma banda rashin kunya kinji, dan yana da babban d'a namiji ki bi sannu, "to shikenan, Umma...


______________________________



Nana ta tashi daga bacci ta shirya tayi kyau sosai, kamar ita tayi kanka, da man ga ta black beauty..


Bayan ta gama shiryawa ta fito ta wuce part din Sadiq, shima ya shirya nan suka shiga cikin katsina ya nuna ma wajaje da yawa suka je duk wani gun shakatawa sannan suka dawo gida, bayan sun dawo gida dare nayi ta kai mashi coffee sannan taje ta kwanta bacci..


Washe gari, bayan kowa ya tashi da shirin ansar bakuwar da gidan Alhaji Sulaiman zasuyi, da man ita yau Nana bata shiga School sai tayi Sati lokacin lectures ta kankama sosai da sosai, to lokacin zata fara zuwa lectures...



"Momy, wai ya naga yau kuna ta hidimar sai kace yau sallah ko zakuyi biki ne? "Wai ba kasan yau diyar Alhaji Ahmad zata zo hutu gidan ba Sadiq? ''


"Au wallahi na manta Momy, kice yau kuna da babba bakuwa to Allah ya kawo ta lafiya,ni zan shiga gidan su Lukman, sai na dawo, "ok Son aka gaida Maman Lukman din"...


Nan su Momy suka cigaba da yin hidimar gabansu na tarar Salma..

_______________________________



"Man kasan abunda ya kawo ni wajenka? "Na sani mana Sadiq, ai maganar gizo bata wuce ta koki, ina jinka yau kuma mai Nana tayi"...


"Sau biyu ina ganinta da wannan saurayin nata, ka san jiya har gaisawa nayi dashi yayi dropping dinta National, ni kuma naje daukota"....


"Sadiq kar girman kai ya cuceka, taya ma akayi shi saurayin nata ya ganta har yayi mata wani abu wai shi dropping eyeeh Sadiq? "



"To wai yana yin lecturing a Makarantar su, kamar ma a department dinsu yake, "wai ya sunan shi saurayin? Dan ina da friend a Umyu wanda yake lecturing a can"..


"Sunan shi Khalid, "Sadiq ba dai Khalid Abdulraham bane ke son Nana Jawaheer ba? "Oho nidai tace man sunan shi Khalid, "tabbas shine, bari kaga pics din shi, wanna nan ne? "Eh shine Man, wanann shine yake son Nana, yakake ganin zamu yi dan naga ita Nana tana bala'in Son wanna guy din"...


"Kayi yanda nace maka, ka samu yanzun shakuwa sosai ta shiga tsakaninku, na san yanda zanyi balle abun ya zo mana cikin sauki Khalid ne masoyin nata, na san shi yana da sauki kai, kuma unguwarku daya, amman bazaka san shi ba tunda kai baka zauna kasar sosai ba".


"To shikenan, nagode na gaya maka a Umyu suka yi posting dina? "Eh haka na kace man, Salma ma a nan katsina aka yi posting dinta a FMC suka yi posting dinta, amman tace gidan uncle dinta zata zauna"...




"To Allah ya bamu sa'a, kace ka huta da zuwa kano gun Salma duk sati kenan? "Ai ko dai Sadiq shiyasa nike jin dadi kuma yau zata zo, ta huta kafin nan da Monday ta fara zuwa aiki"..


"Haka ne Allah ya taimaka, yanzun dai tashi mu tafi gida ko? "To da man ina shirin shigowa gidan ku ka riga, amman duk da haka sai naje na gaida Ammi da Momy"..


__________________________

"Sannunku da zuwa Hajiya Jamila, kun sha hanya, sannunku, "yauwa Hajiya Fatima, ya muka samaiku? "Lafiya lau Alhmdulh, ku zauna ga abincin nan, nan su Umma suka zauna suka ci abinci sosai sannan Umma tace ita ta koma kano...


Bayan tafiyar Umma, Salma ta dauki kayan ta ta kai dakin Nana, sunyi introduction din juna, nan Salma ta shiga wanka, ita kuma Nana ta gyara mata wadrop dan ita Nana, Salma tayi mata itama yanzun tayi kawar labari...



"Sannu da zuwa Alhaji karami, "yauwa Baba Isa, sannu da aiki, har bakin sun zo? "Eh harma daya ta koma, ta bar daya, "ok shikenan, Man mun fara zuwa ka gaishe da Momy, sannan mu wuce gun Hajiya ko? "Eh Sadiq haka yayi"..


Nan suka shiga part din Momy suka gaisa, suka wuce gun Hajiya, "Sadiq shine baka tsaya ba kaga bakuwa ba ko? kai da baka san wanda zata zo ba, "ke fa Hajiya kinji matsalarki wallahi tsogumi, yanzun Man ko na tsaya mai zan yi ma bakuwarsu, "nima abunda na gani, amman ai da ka tsaya kun gaisa"..


"Kyale shi Lukman, ai kana hakuri zaman da wannan mutumin, yanzun bari na kira Nana ta kirata ku gaisa, "ita bukuwar ina ne ma saukinta? "Ina ne in ba nan ba dakin Nana, Takwara! "Naam Hajiya gani, ina kwana yaya Lukman? "Lafiya lau Nana, "Hajiya gani, "je ki taho da bakuwa ta gaisa dasu Sadiq, "to shikenan"...



Nan Nana taje ta kira Salma suka fito tare suna labari sai kace wanda suka dad'e da sanin juna.....




"Salma, "Naam Lukman, da man nan ne gidan ku? "Eh mana, tunda gidan su Sadiq ne, sai sannan Salma ta waiga ta kali Sadiq zaune yana ta kallon Nana, "au Malan Sadiq, da man nan ne gidan ku kenan? "Ai ko dai Malama Salma sannu da zuwa, ashe da man kece wanda su Momy suka ce zata zo daga kano kenan? "Aiko dai gani kun gani, "aiko mun gani welcome home, thank you''...



"Au wai da man kun santa ne? "Eh Hajiya mun Santa Makarantarmu daya da ita da naje India yin MSC, "kai ka san wani MSC, ai shikenan Sadiq ga kanwarka nan yanda kake yi ma Nana itama kayi ma Salma haka kaji mijina? "To shikenan naji, Nana ka wo mana abinci muci, Man ko yunwar ta gushe anga😉, "kamar ka sani, ai ni yanzun Sadiq gidan ku zan dawo da zama gaskiya, "hahha ai na sani ko ba ka gaya man ba, tunda Salma ta dawo gidan ba"...



Nan dai su Sadiq suka ci abinci, bayan sun gama cin abincin suka hadu garden su kai ta fira, "yaya Sadiq, "fadi matsalarki uwar yar'matsala, "da man ina san na tambayeka, gobe Khalid zai zo yace man, "ba na ce maki ba, "Aah Sadiq ka barshi yazo mana Nana, "Naam yaya Lukman, "kice mashi yazo kinji, in kun gama gaisawa kice ya shigo ina son ganin shi....


"To shikenan, zan gaya mashi insha Allah, ni zan shiga ciki, "dawo ba inda zaki tafi, muna cin fira zaki tashi kije ku kama waya ko? Aa Sadiq, nan Nana ta zauna suka cigaba da fira, sune basu tashi ba sai da time din sallah yayi..


_____________________________





Abubuwa sai tabarbarewa suke, dan yanzun haka Khadija sai abunda hali yayi gaba, yanzun Inna Talutu duniya tayi mata zafi dan bata jin dadi yara balle taji dadin miji...




Gashi har yanzun bata san wata kallar sana'a Sabi'u yake yi ba, ita dai kullun sai ta ganshi da kudi, in ta tambayeshi sai yace mata baya san sa ido, in bata bi sannu ba watarana sai tayi da na sani..


Sai dai Talatu tayi kuka, ga aiki yayi mata yawa, dan dole ta ajiye sana'ar koko, tace bata iyawa abun yayi mata yawa..



____________________



"Oyoyo, my Khalid, "my Jawaheer nayi missing dinki sosai,"nima nayi missing dinka sosai, nan suka jira suna fira har suka isa garden, bayan ta kawo mashi drink da fruit sannan ta zauna suka fara fira...



"My Jawaheer, "Naam my Khalid, ya na kamar kana cikin damuwa? "Eh ina cikin damuwa, ya kuke da wannan yayan naki wanda yazo daukarki a national? "Yayana ne, Maman shi da Baba uwarsu daya uban su daya damai gidan kuma, wani abu?"..



"Ok kina nufin cousin din kine kenan? "Eh cousin dinane, ka san yaya Sadiq baida matsala ko daya, yana da mutunci da sauki zama, nima kafin nagane halin shi sai da naji na tsineshi, amman ina fahimtarshi naga shi mutun ne mai son jama'a, kuma kuna sabawa zaka gane haka, dan shi yaya Sadiq baida saurin sabo shiyasa kaga yayi maka haka ranan..



"Hakane yanzun na gane, nidai dan Allah Jawaheer ki taimaka man ki aureni karda ki kujeni, "insha Allah Khalid Jawaheer matarka ce, "Allah ya yarda, "yauwa da man abokin yaya Sadiq yace in mun gama yana son ganinka, "ok suna ina? "Suna part din yaya Sadiq, "ok tashi mu tafi...




Nan suka shiga part din Sadiq, Nana ta barshi ta wuce ciki da sunan zasu yi waya...



"Aah Lukman Yusuf, "Naam Khalid Abdulraham, ai ni fushi nike da kai, ace na dawo MSC dina, amman ba waya balle kazo gida?, "tabbas ni mai laifine, amman wallahi kana raina kullun sai na ce zan shiga barhim gidan ku sai na manta, kasan muyi nisa sosai, dan Allah kayi hakuri, "nayi sai da naji Nana tana ba Sadiq labarinka, kullun basu da labari sai naka, shiyasa nace ai kai, Khaild friend din na lokacin kuna barhim kafin ku dawo nan layout, "aiko dai, kuma har yanzun muna tare ba, "Sadiq, "Naam Man, "ya kayi shiru? "Wai ku gama gaisawa sannan, muma sai mu gaisa, nan sukai ta labari, kafin Khalid ya tafi gida sai da su ka saba da Sadiq, dan har da exchange numbers....



"Nana, "Naam Salma, "niko ina san nayi maki wata tambaya, "to shikenan Ina jinki, amman ki bari na kaima yaya Sadiq coffee in na dawo sai ki tambaye ni kinga gobe ina da 8,"to shikenan, sai kin dawo"...


Nan Nana taje ta kaima Sadiq coffee, sai da ya shanye sanann ta dawo part din su..


"Kin dawo kenan, "wallahi sai yanzun ya kyaleni na taho, dan sai da yasa na tsaya ya sha sannan'..


"Gaskiya Nana soyayyar ku da Sadiq tana burgeni, "soyayya kuma? haka ne soyayya kina ganin mutun ya matsa man da yi bari?"..




"Aiko ki kiso ko karki so, da anga idon Sadiq to anga sonki sosai a cikinshi dan saboda da ke Sadiq yake kin Ko wace budurwa in dan tace tana son shi, "to mu ba soyayya muke ba ni my Khalid zan aura, "karya kike, wallahi babu soyayyar Khalid a idonki, sai dai kina kulashi dan baki san maiye so ba, amman idanunki sunfi nuna soyayyar Sadiq, ke tsaya na gaya maki gaskiya kinfi dacewa da Sadiq akan Khalid"..



"Bari kiji wani labari, harta ni Salma sai da na taya Sadiq amman yace man yana da wanda yake so, shiyasa muke soyayya da Lukman, kuma sai da na ganki nasan ban dace da Sadiq ba sai masoyina Lukman, kin san dai na girmeki nafi ki sanin maiye so, nan gaba zaki gane, "Salma kin, "enough Nana, ai ni na gama magana kuma, kawai kwanta kiyi bacci kina da lectures gud night"..










_By jameelah jameey_ 🖋






Share and comment pls
🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕
*NANA JAWAHEER*
🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕

*STORY AND* *WRITING BY*
*Jameelah A Belloh*
*(Jameey)*


*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻```

_________________________________


*BISSIILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*





Page 2️⃣5️⃣➖3️⃣0️⃣




Washe gari, bayan angama breakfast Sadiq ya dauki Nana da Salma suka tafi gun aiki, sai da ya fara kai Salma sannan suka wuce Umyu bakin sciences ya sauke Nana, sannan shi ya wuce cleaning..


Bayan Sadiq ya wuce cleaning, Nan Nana ta wuce sciences theater duk sai taji ba dadi, dan ita inba Zee ba bata san kowa ba, Allah yasa Zee ta iso dan ta san Zee bata da wasa...


"Nana Adam"..


Nan Nana ta juya tana farin cikin taji muryar Zee..


"Zee baki ji yanda naji dadi ba, ai nasa baki zo ba, "waya gaya maki, ai ni kullun sai nazo kinga har nayi ƙawa ma, "Sannu am Rabi'atu bature, "welcome Nana Jawaheer Adam, "Woow nice to meet you, "meet you too, Zee ya maganar changen course din anyi maki?


"Eh anyi na dawo sciences nima, ban san nayi nisa, shi kuma education yana da nisa ga wahalar karatu"..



"Jakane Zee wallahi Yayata tace man zaman education sai mai koƙari sosai, shiyasa nazo sciences,amman ina bala'in san education..


"Ai duk baku san wani abu ba, wallahi ni Yaya Sadiq yaso su bani BSC(ED) CHEMISTRY, yace man education is better than sciences, saboda ɗan education degree biyu yake lokaci guɗa, da sciences da education, indan zai gama kali biyu ake ba dan education dana BSC da na education, sannan kuma indan kana son kayi MSC sai ka zaba wani size zaka yi, BSC ko EDUCATION, amman yanzun sai a kama gudun education wai ya cika wahala saboda karatun shi rabin shi theory kuma dole kayi understand da creaming...


"Hakane gaskiya Nana kin faɗi gaskiya, amman yanzun ba kowa ke san education ba, duk wanda kika ga yana education 99% ɗinsu ba da hannunsu suka cike education ba, makaranta ce ta kaisu, 10% kuma sune suka cike da kansu, cikin ten percent din ma five percent iyayensu suke sa masu su a choice ɗin su saboda kusan iyayen nasu profs ne sun san anfanin education din...


"Haka ne ko An'babi, kin fadi gaskiya, ni dai ina san education, amman hakuri zanyi da sciences din,ga lecturer nan muyi shiru karda ya fidda mu waje kunsan malaman jami'a ba sauki ne da su ba..


"hello class, am Dr Tofik, Depertiment of biology! Nice to meet uh all my student, then today we are discuss to you cell! Class who give me the meaning of biology ?

"Sir, "ok stand up, ur name? "My name is Habib takur, depertiment of chemistry..



(note:kun

Please Login or Register in order to submit comment