Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Nana take da shekara 18,tana da bukatar Fatima da Khadija su koya Maya garki da dai sauran abubuwan su na mata, to wai da Ni'yata kafin su gama koya mata sai ta fara makaranta, suna gama wa, lokacin itama ta gama makarantar ba sai ayi Mata auren ba, lokacin insha Allah ta samu miji kinga komai ya zo dai dai..


"Wani ta samu miji Sulaiman? Ai Nana tace man tana da wanda take so, kawai dai zaka bashi dama ya cigaba da zuwa neman aurenta, su Fatima na gama koya Mata sai a fito ayi auren, ai nasan Sulaiman kafin su gama ita ma ta gama makarantar ko Sulaiman?


"Eh Hajiya insha Allah ta gama, amman Hajiya wani hanzari ba gudu ba mai zai hana ku dan kara lokaci, kafin ta fara kula samari, "fita idona na kulle Sulaiman, har wani lokaci ake ba dawa a cikin aikin Allah? "Aah Hajiya,"Au ai nasa kai keda lokacin, ka kiyaye cikin gidan Sulaiman..


"Haba Hajiya, ya za'ayi ace kamar wanann yar yarinyar ace ita ke kula samari, kuma keki biye mata, wai har kuke maganar zai ringa zuwa mana cikin gida? "Ka ji man d'an nema, in kai baka da guri ai ita tana da guri, kuma kai kaji na ko Sadiq? ka tabbatar ka fidda matar aure kadai ji, ba biye maku zamu yi ba ku kama wanann bokon naku ba wanda ni banga wani amfaninshi ba tunda saboda dashi ba'ayi ma yaran yanzun Aure wai har sai sun gama sannan sai kace saukar quri'ani..


"Nana, "Naam Dady, "naji Yaya yace kin samu admission ko? "Eh Dady na samu admissions a umyu, "wani course suka baki? " *BSC BIOLOGY,* "Kinyi registration? "Aah banyi ba, "sai yaushe zaki yi? "Duk sanda kace Dady, "ok gobe kai Son ka shirya ka kai Nana umyu tayi registration da komai da komai, "To shikenan Dad, ni zan shiga cikin bacci zanyi, "tun yanzun Son, "Eh Mom kai na ne ke man ciwo sosai kuma ban jin dadin jikina, kai Nana ki kai man coffee a apartment din na yanzun, ni na tafi sai da safen ku...


"Nana, "Naam Momy, "tashi kije ki kai mashi coffeen kinji, "to shikenan Momy,"sai kin yi hakuri da Sadiq yana da dadin zama, sannan yana da sanyin rai, amman sai kin bi abunda yake so, abunda yake so shine baya son raini kinji? "Eh insha Allah Momy, na tafi, "to shikenan, Hajiya nima na tafi ciki, ina san na dan huta, "To shikenan Allah ya tashemu lafiya..


Haka dai Nana ta dauki coffee zata kaima Sadiq, ba dan rainta yaso ba, sai dan ba yanda zata yi, ita dai tana bala'in tsoron shi sosai, bata san ko ido su yawaita hadawa da shi, domin ita dai baki daya jininta da nashi basu hadu ba bata son ko inuwa daya su ringa zama balle har magana ta hada su, ta tazo apartment din shi, amman fargaci da tsoro sun hanata ta shiga, sai da ta'hado jarin'tarta da nutsuwarta sannan ta samu tayi sallama cikin nutsuwa da kuma taushin murya..


"Sallama Alaikum,"Amin, ke sai yanzun kika gadamar kawoman ko?, wato ka sa'anki kin tsada, "Aah wallahi Yaya Sadiq baka bane,"in ba haka bane to yane?, "To dan Allah kayi hakuri, "zo'nan zo ki zauna nan nace, Nana tana tafiya tana hawaye, dan ita tana tsoron shi sosai ji take kamar ta koma gun Talatu indai gida daya zata zauna da wanann mugun mutunan, "Au kuka na saki kenan? wato ke yar karama dake har kinsan soyayya ko?in banda rashi class irin na saurayin naki mai ya gani a jikinki da har yake ce wa yana so, _kwaila_ da ke kawai, daga yau kullun ke zaki dunga kawo man coffee kafin na kwanta bacci,"kina kina? "Ehehhhh ina jinka, Nana ta fada cikin shashakar kuka, kuma tana ta jero mashi Allah ya isa a cikin zuciya, domin taji haushin cin mutuncin da yayi mata, wai ita yake ce ma _kwaila_ ..


"Kuma gobe ba zan kai ki wata school ba wai kiyi registration, tunda ni ba driver ki bane, ko na yi maki kama da drive? "Aah baka yi, "to dan haka gobe in zaki yi registration dinki, zan ringa ajiye ki a *NATIONAL* kina hawan school bus, in kin dawo zan baki number na kiyi man flashing sai nazo na daukike na mai da ki gida, kinji ni dai ko? "Eh naji,"good girl, sauran kuma ki gaya ma wannan tsohuwar kice Mata bani ke'kai ki ba, hmmmm ni kadai nasan abunda zanyi maki, yarinya karama sai rashin kunya, tashi kiban waje kafin na bude idona na ganki anan..



Haka Nana ta samu ta fito daga part din Sadiq ta hamdala da fito bai maketa, tana tunanin yanda zasu kashe gobe kuma in ta kai mashi coffee da zuwa *NATIONAL* dan taga ba mutunci ya isheshi ba, bayan ta koma tayi sallama da su Ammi taje ta kwanta sai da tayi waya da Khalid dinta sannan ta tura mashi Text massage kamar haka..


" *Amincin Allah su Kara tabbata da kai ya kai ma abocin murmurshi da walwala, haki'ka idanuwa sunyi kawar abincinsu, nayi kawarka sosai, da man na manta ban gaya maka ba gobe zamu shigo yin registration a sch dinku, byeee have a nice sleep, sweet dream with me only, ilv uh..*


Bayan ta tura mashi, sannan tayi waya Zee a kan gobe su hadu a national ko kuma a gun *STUDENT CENTER UMYU* , sannan su kayi sallama, nan fa reply din message din Khalid ya shigo wayar Nana .



"To shikenan masoyiyata, Allah ya kaimu goben lafiya, ina kewarki sosai rabin raina, byee iluv you more my happiness..


Washer gari..







```NOTES :-NATIONAL, wajen da student din UMYU suke hawan school bus, duk wani dan katsina yasan NATIONAL, sannan duk wanda tayi UMYU tasan NATIONAL, koda a HOSTEL take zaune.```





_By jameelah jameey_ ✍🏻





Share and comment pls


πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•
*NANA JAWAHEER*
πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•

*STORY AND* *WRITING BY*
*Jameelah A Belloh*
*(Jameey)*


*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–Š*
*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.πŸ€™πŸ»```

________________________________


*BISSIILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*






Page 1⃣7⃣










Washe gari tunda Nana tayi sallar asuba bata koma bacci ba, saboda da zumundin zuwa yin registration a umyu, bayan tayi sallah, tayi wanka ta shirya 7:30am tuni Nana ta shirya ta na parlor suna gaisawa da Hajiya, nan Hajiya ke gaya Mata, sun Ammi suna can kitchen suna yin breakfast, bayan taje sun gaisa da su Ammi, suka cigaba da yin breakfast din tare, Nana ta mai da hankalinta sosai gun sauwar dan Momy ce Mata tayi duk week din duniya a kitchen zasu wuni, sannan inba da lectures ita zata ringa yin abincin gidan, bayan sun gama hada komai suka kai a dinner table sannan Momy ta tafi ta shirya ita da Aiman, domin shi Dady tun 7 yake fita office kunsan dai aiki banking yanda yake, ita kuma Nana ta gyara kitchen din sosai, sannan ta dawo ta gyara a apartment din su sannan kowa yazo ya zauna amman banda Sadiq yana can yanata aikin bacci hankalin shi kwance, dan ya manta da wai zai kai Nana National...


"Nana, tashi kije ki taso Yayanku, "To Ammi, Nana ta tashi ta tafi, amman duk hankalinta baya jikin ta ji take yi ina ma ta taho da Aiman, dan ita dai bata san abunda zai ha data dashi, tana zuwa wajen kofa ta fara yin nocking din kofar har sau uku, amman bai yi magana ba , dan haka sai kawai ta tura ta shiga cikin room din..


"Heeey, Sadiq yace cikin bacin rai, ke daman ba'a koya maki yin sallama ba?, ehyeeh da zaki shigoman dakin, kamar wani dakin ki, "Yaya Sadiq dan Allah kayi hakuri, wallahi sai da nayi maka nocking amman baka ce na shigo ba, nasa ma baka tashi bacci ba shiyasa na shigo na ta daka saboda naga munyi letting, "keee dan Allah can yi man shiru ko na buge wannan kazamin bakin nan, wanda ko brush baki yi mashi, wai Nana jawaheer yaushe zaki hankali? Ina yi maki kallon mai hankali ashe duk ba haka bane..


"Wallahi Yaya ba haka bane, "to yane in ba haka ba? Nana kin shigo man ba sallama dan ma Allah yaso na sa kaya, ni tashi ki bani waje, gani nan fitowa, "to Yaya, am Yaya dan Allah kayi sauri karda muyi leting pls...


Nana na yi ma Sadiq maganar tana yarfamai hannu ita a dole yayi Sauri ya kai ta national, shi ko ogon naku sakin baki da ido yayi yana kallon ta ji yake kamar ta dauwama haka, dan tayi mashi bala'in kyau, tunda ta shigo yaga tayi bala'in kyau, tun da ta fara yin nocking yana jinta kawai yaki yin magana duk da lokacin ya fito wanka ya gama shafa maya mayen shi ya sa kaya, yana cikin gyaren sumarshi ta shigo amman duk da haka sai da ya yi mata masifa..


"Yaya Sadiq pls am talk to you fa, "eeh naji fita kiban waje nima yanzun zan fito, ko dole sai na jera da ke sannan? "Aah Yaya Allah ya baka hakuri..


Bayan Sadiq ya me sunyi breakfast nan yake gaya ma su, "Ammi kunsan jiya akayi posting dina a cross river, "cross river Son? "Eh Momy cross river, amman gaskiya tayi man nisa, dan ban shirya sake basin katsina ba, dan haka yanzun zan wuce naje ayi relocated a mai doni nan katsina, "Eh gaskiya Sadiq ya dace dai ka dawo nan gidan kayi wanann bautar kasar taka, "aiko Ammi ai shiyasa yanzun zanyi relocated, ina ajiye Nana a school zani wuce ayi man komai, in ma ta kama har NYSC office din sai naje tunda ina da right din da zan zabi inda zani yi services dinna, "To shikenan Son Allah ya taimaka, "amin Momy, ke Nana tashi mu tafi ko karda mu makara, daman naga sai doki ke yi new student, Allah yasa karda kije ki kama yi masu JJC,"Toh, kaji man mutun sai wani sakin ma fuska yake daya ke gaban su Momy muke mugu kawai da shi, Nana tace cikin zuciya tana tashi Tana yafe gyalenta..


"What, gyale zaki sa ki fita, bama fita ba university zaki shiga da wannan shigar, "kai Sadiq banson sakarcin banza, yanzun mai ye laifin wannan shigar ? naga dai laces ne tasa, kuma kayan basu matsita ba, to ya kake son ta fita? Karka kurkura kace zaka matsama Mamana cikin gidan nan fa, "haba Ammi gaskiya bai dace ba ace ta je university da gyale, dan haka indai tana son ta bini taje ta Santa hijab, ke in dai zaki shiga umyu daga yau ki ringa sa hajib, kina jina ko? "Eh yaya Sadiq, "wuce ki dauko hijab din ki ni ina jiranki a mota, sai mun dawo Momy, "To Son Allah ya kiyaye, "Amin, kiyi sauri ina jiranki, "ai ma na fito, sai mun dawo, "to Mamana a dawo lfy "Allah yasa Ammi..


Nan Sadiq ya dauki hanyar national yana yima Nana balbalin masifa a kan karta kurkura ta tsaya kula samari dan ba wannan ya kawo ta karatu ya kawo ta, sannan yau zai biya green house ya siya Maya nikaq, kuma banda yin kawaye barkatai duk bai son haka, haka dai Sadiq yai ta ba Nana role sai kace wani mijinta, haka itama Nana ta kama thinking about that, tana mamakin yanda Yaya Sadiq yake yi mata Wannnan mulkin, haka dai suka isa national ta hau macapolo sannan Sadiq ya kama gabanshi

_________________________________


"Hello Man, "Hello Sadiq, ina jinka, yakane? "Lafiya lau Man, Man kana gida ne? "Eh ina gida, "ok on my way fa, "serious? "Yes, am coming, "ok am waiting for you, nan fa Sadiq ya samu ya iso barhim estate nan ne unguwarsu Man, nan yake cema Man ya iso, Man yazo ya shigo dashi,ya gaida su Mamin shi sanann suka wuce dakin Man..



"Sadiq, lafiya dai ko? "Da saiki dai Man, kasan daman banyi services ba na wuce MSC to yanzun sunyi posting dina cikin wanann batch din, sun turani cross river, amman yanzun daga gun relocated nike sunyi man anjima zan sake jin wani posted din, "To Allah ya taimaka, "Amin, "kasha ruwa mana Sadiq, kafin a kawo mana abinci, "To shikenan, Man amman sai matsala ta biyu, "ai Sadiq nasan matsalar, ko ba Nana ba? "Eh ita kasan yanzun ta dawo gidan mu da zama, wallahi Man yarinyar tana son ta rikita man lisafi, Man Nana ta shiga university, kuma gaskiya bani son tana sa gyale, kasan yau sai da muka yi fada saboda sa gyale...



Nan fa Sadiq ya gaya ma Man komai da yanda yake yima Nana..



"Amman gaskiya Sadiq, zan iya cewa baka da hankali, "Man ni'ne bani da hankali? "Eh tabbas Sadiq! Sadiq anya kana son Nana da gaske? "Maiyasa zaka yi man wannan silly questions din, bayan kafi kowa sanin kalar son da nike yi mata, "ai dole nace maka haka Sadiq, to maganar gaskiya ka saki jikin da ita ka jawo ta jikinka, yanda zata yi sabo da kai, kaga wannan saurayin da take fadi, da bakinta zata ce bata sonshi kai take so,amman ni tawa shaware kenan, sannan kuma kabarta taji da hijab din, pls ka kyale wanann maganar nikaq din pls Sadiq, "To shikenan zanyi kokari naga nayi yanda kace, amman wallahi Man wannan saurayin da take kira in bai yi wasa ba duk randa na gansa, sai nayi masa rashin mutunci, "haba Sadiq, ai sai ka zubda class dinka, kadai kayi kokari ka janyota jiki, inta saba da kai, munsan yanda zamu yi da shi guy din, "To shikenan Man, nan fa suka ci abinci suna kara tautaunawa yanda zasu bi komai yayi normal....


_________________________________


Bayan Sadiq ya ajiye Nana a national sun dauki hanyar umyu, gun gidan mangal bus ta tsaya ta dauki Zee, nan fa suka fara firar yaushe gamo, nan Nana ta fara ba Zee labari..



"Zee kin san mai? "Aah Nana sai kin fadi man, "Zee inajin dadi zaman gidan, suna sona sosai, ba su san bacin rai na, amman sai dai mutum daya kin samai? "Aah ina jinki Nana, "sai dai Yaya Sadiq! Zee ya matsaman karki so kiga killar cin kashin da yake yi man, jiya fa har ceman kwaila yayi, kiji fa wanann Wulakanci..



"To, Nana wanann waye shi kuma? "Zee Yaya na ne cousin din na ne sosai da Mama'nshi da Baba da Dady duk uban'nin su da'ya, shi naji ance Babanshi ya rasu tun yana yaro, "To amman Nana baki yi mashi wani abu ba? "Zee mai zanyi mashi, kawai dai na lura jininmu ne bai zo daya ba, dan nima bai yi mani ba, saboda bashi da tausayi, "haba Nana dan mai zaki ce ba shi da tausayin, ke da duka duka yanzun kike da sati da zuwa gidan su? "Eh Zee bashi da imani, kin san abubuwan da yake yi man?"Aah ke nike saurareni,"To bari kiji, yanzun yace kullun kafin ya kwanta bacci ni zan duka kawo mashi wani coffee can nashi, sannan kuma Zee Dady cewa yayi ya dunga kaine school har sai na gama registration, amman ce man yayi national zai dunga ajiye ni ina hawan bus, sai ya bani kudin kashewa, idan nadawo national sai ya daukeni mu koma gida tare dashi, kinji fa Zee, nan har nace yayi man mutunci da adalci? "Aah gaskiya Nana, amman ki yi mashi uzuri pls, "uzuri kuma Zee, wani kallar uzuri kike so nayi mashi, mutunan da yace daga gobe nikaq zan dunga sawa, ni dai kawai zanta hakuri da shi shima, "To Nana kiyi dai hakuri komai ai dan hakuri ne..




Umyu katsina,! bus stop bus na ajiye su Nana, suka wuce container din sciences, cafe din ATB, nan suka yi mashi bayanin su new enters ne, ya zasu yi registration, nan ya tambayesu zasu zauna hostel suka ce Aah, nan ya fiddo masu course form da form01 dinsu da bio data, da cleaning form da labirary form sai kuma guide form, nan fa suka cike yanda ya ce su cike,daman already sunyi payment dinsu ta fadility bank, sai suka fiddo payment slip dinsu, bayan duk sungama fidda abunda ya dace suka biya kudi sannan suka fito, sun gaya ma Khalid sun shigo, idan suka gama submitted din forms din zasu shigo office dinshi, nan fa suka wuce Senate suka kaima registera form zai yi masu sing, sannan suka wuce Faculty of Education gun DIN din su Zee suka kai mashi form din labirary form, sunyi sa'a basu tadda mutane sosai ba, yana yi masu suka he gun level advisor din su shine yace gobe su dawo, daga nan suka wuce faculty of Sciences gun DIN yayi ma Nana sing, itama level advisor dinsu yace su dawo gobe, duk sun gaji, dan haka suka wuce students center, a Barmo restaurant suka yi ordering din rice suka cin, sukayi sallah, sannan suka fito suka je office din Khalid suka huta nan yake tambayarsu sauran me suka cemai basu je cleaning ba, nan fa ya tashi suka tafi tare ya kai su gun wani friend dinshi nan cleaning yake aiki, basu bi layi ba aka ebi jininsu, aka basu number ake su dawo gobe, nan suka koma office din Khalid suka yi sallahr Asr sannan suka gaisa, yake ce mata next week zai shigo fira tace to, nan ya dauko su, da yaso ya kaisu gida ammn Nana tace Aah, ita dai Zee unguwarsu aka ajeta, sannan ya wuce da Nana national ya ajeta yace xasuyi waya anjima, nan ta kira Sadiq tace tana national...


_________________________________

*KANO*


_By jameelah jameey_ πŸ–‹




Share and comment pls


πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•
*NANA JAWAHEER*
πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•

*STORY AND* *WRITING BY*
*Jameelah A Belloh*
*(Jameey)*


*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–Š*
*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.πŸ€™πŸ»```

__________________________________


*BISSIILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*



```Comments dinku shike bani gwarin giwar yi maku readmore mai yawa, dan haka comments dinku na yau naji dadinshi sosai da sosai dan haka ga giftπŸ’ŒπŸ€Ž```


Page 1⃣8⃣








"Umma, gobe ne Lukman zai zo,, "to Salma ai sai ki fara shirin zuwan nashi, nan fa Salma ta fara shirin zuwan Lukman dan tayi shari mai suna shirin...


_____________________________________




"Hello, Baby gani na shigo kano, kawai direct zooroad zan taho? "Eh Baby in dan ka shigo zooroad, zan sa a taho da kai, "ok shikenan..




Nan Lukman, ya iso Zoo road ya kira Salma, yace ya iso nan Salma tasa drive yazo ya taho dashi, wani katafaren gida ne wanda ya ansa sunanshi gida, wani bangareren gate ne aka bude ma Lukman ya shigo ya samu waje a parking space ya aje motarshi kirar vite, sannan ya kira Salma yace ga shinan cikin gida...



_____________________________________



Bayan Sadiq ya taho, bai tsaya ko ina ba sai National nan ya bude glass din motarshi yana yi mata waving da hannu..




"Yaya Sadiq, sannu da hanya, "Yauwa, ya registration din? "Alhmdulh, "kun gama ko? "Aa sunce na dawo gobe, "ok Allah ya kaimu, amman da mai da mai ne baki ida yi ba? "Eh cleaning sun ce Wednesday zamu ansa result, sai gobe zamuje mu ida anso form wajen su registera inda yayi sing zamu kaima basa yayi mana sing mun gama..




"Ok kenan daga Wednesday kin gama registration saura ki fara shiga lectures? "Eh insha Allah, "ok Allah ya kaimu, amman ban iya daukar wannan zaryar taki gaskiya, "to ni Yaya Sadiq yakake son nayi? ta fada tana shirin yin kuka dan ita har gaji da wannan halin na shi, daga dawowarta bai bata ta huta ba ya fara yi mata jaraba, "wannan kuma matsalarki, ke kika san yanda zaki yi, fitan man mota..



________________________________________





Bayan Lukman anzo an shiga da shi dakin baki, nan aka fara jido mai kayan lashe baki, nan aka cika mai gaban shi da abubuwa Kala Kala..





''Baby, wannan abincin duk ni daya? "Eh Baby so nike naga ka cinye komai baki daya, "ok sai dai muci tare dan ni bani cin abincin ni daya, "Aah ka fara ci, sannan sai nace, dan ni bani jin yunwa, "aiko na koshi nima, ba yanda ta iya haka Salma ta sauko kasa suka ci abinci tare, bayan sun gama, Lukman yaje ya gaisa da Umma, sannan ya dauko hanyar katsina..



______________________________________




"Hello, Jawaheer kina jina, "eh ina jinka Khalid, "ga ni nan a parking spaces din gidanku, "oyoyo my Khalid, bari na shigo da kai nama taho, "ok am waiting, "welcome, ka shigo mana kayi tsaye nan sai kace wani bako kai da gidanku, "to my Jawaheer, ai da man umarnin gimbiya nike jira, nan suka shiga dakin baki tare suna ta zuba soyayyarsu,, bayan Khalid ya gama abunda yake ya je ya gaida Hajiya dasu Ammi, sannan suka fito Nana ta rako shi bakin mota tana ta zuba mai shagwaba ita a dole bata son ya tafi, duk abunda suke a kan idon Sadiq, ji yayi kamar ya shake wuyan Khalid wai wani yake soyayya da matarshi...


(hahahaha kunji Sadiq da wata magana wai Matarshi😍) amman ba komai yau zamu hadu da ita anjima in tazo kawo man coffee..






_By jameelah jameey_ ✍🏻





Share and comment
πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•
*NANA JAWAHEER*
πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•

*STORY AND* *WRITING BY*
*Jameelah A Belloh*
*(Jameey)*


*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–Š*
*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.πŸ€™πŸ»```

_________________________________


*BISSIILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*





Page 1⃣9⃣






"Khadija, wai ba zaki fito cikin gidan nan ba? Wallahi na gaji da wannan mugun halin naki wallahi ko, yarinya sai kace kece kika haifi kanki"..


"wai ke Inna mai yasa kike yi man haka, duk abunda nike maki baki gani cikin gidan, to wallahi nima na fara gajiya da wannan halin naki, haba daga kin haifeni sai kawai ki matsa mani a cikin gida nida gidan ubana..



"Eyeeh, Allah sarki Nana, ita tace mai? da take yi maki har wanki ma, kuma ita ke duka aikin gidan nan, amman haka itama take hakuri..


"Ai Nana daban, Khadija daban, dan haka daga yau karki kuskura ki sake gigin sani wani aikin ki can, "Inalillahi, ke Khadija, yanzun Mamar taki kike gaya ma wannan maganar? Wai maiyasa Khadija baki da mutuncine..


"Wallahi Baba, na gaji cikin gidan, duk kunbi kun matsa man, in zaman gidan ne baku so nayi sai na bar maku gidan ku, ai sai ku huta..


"yanzun dan nayi maki fada shine kike maganar barin gida to Allah ya shirya ki, nan Malan Adamu ya fita gida rainshi bace, yana takaicin yanda Talatu ta bata tarbiyar yarinyarta da kanta..



________________________________



Bayan Khalid ya tafi, Nana ta koma cikin gida suka shiga kitchen ita da Momy, nan suka yi abincin dare, suka jera a kan dinning table, sannan ta wuce daki tayi wanka tasa kayan mararsa nauyi, sannan tayi sallah, bayan ta gama sallah ta dauko kur'ani ta fara karatu itace bata gama karatun ba sai da aka kira sallahr isha'i, sannan ta fita dan suyi dinner...



Bayan sun gama cin abincin, suka taro cikin parlourn Hajiya suna labari, nan Sadiq ya mike yace sai da safensu yana jiran Nana ta kawo mashi

Please Login or Register in order to submit comment