Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

koyamata tunda antafi anbarta da annob, tun malan yana magana akan wahalar da nana keyi har yakai da ya kyaleta yasa mata idanu dan yace basuci kuma basu magana,in yaga abun yawuce masali ya kanyi magana yanuna ya gaji da walahar da talatu keba nana,ammn Talatu sae tasama malam kukun kissa tace yanuna mata bata isa da nana bah dan yaga ba ita ta haifeta bah daman talura baya ganin kyautatawar da dake yima Nana shikuma sai yai ta lailashinta yana bata hakuri ahaka dae har yasamu tayi shiru...


Annin Sadiq yakama muje gidan malan muga wani hali suke shida iyalensa karku biyema zuciyarsu Daddynsu Aiman mubar yin zuminci,saboda zuciyarmu"tabbas malan yayi ma su Hajiya ba dai dai ba amman baikamata ace kun wareshi acikinku bah baku zuwa ganin zuri'arshi"nima abunda nike kwana dashi kenan nike tashi Hajiya Fateemah lamarin Hajiya da Yaya Suleiman naga abun sai gaba yake, dan ita Hajiya batason ko maganar Yaya Adamu a yimata "kuma shima Yaya Adamu yadauki abun da zafi har haka, ae ni banga laifi ba dan Yaya Sulaiman yace yana son ya bashi nana ya rike,ai hakan bayana nufin yaga gazawarshi bah"Aah ko daya shi dae kawae yana tausayin Nana ne a barta wajen matarshi, ai shikenan yanzun mudae yaushe yakamata muje muga halin da wannan yarinyarnan ke ciki? tabbas zamuje amman ba yanzun bah toh shikenan"yauwa daman inason nayi maki wata magana Annin Sadiq wai haka samu sama Sadiq ido tunda yafi yau kimamin shakara hudu kenan da tafiyarshi amman har yanzun bai zo gida ba, yaga lafiyarmu bah sae dae ya damaimu dayin waya,"hmmm nima ai Momynsu ko jiya sae da nayi mashi fada da mukayi waya,amman yaceman shidae baya dawowa har sae yagama wannan karatun nashi tunda yanzun saura shakara uku yagama karatun baki daya"toh shikenan Allah dai yabashi sa'a yasa agama lafiya"ameen ya Allah......


"Inna nagama wanke_ wanke"ooo inkingama wanke_wanke harwata bulla kikayi yar iya, ubanwa kika ajiye yayi maki wannan tuwan"Aah bakowa Inna aman dan Allah Inna inason kibarni na tafi Isilamiya indan nadawo xani tuka tuwan tunda daman nayi miya"wato Nana ke harda zabi ma gareki ko, to babu inda zaki tafi har sai kinyi wanann tuwon mutunniyar banza mai hali irin na uwarta, a haka Nana tayi tukin tuwo sannan ta tafi makaranta...


Nana ta hadu da kawarta Zainab amman ina kiranta da Zee, sun hadune a makaranta itadai Zainab gidansu bawasu masu kudi bane amman sunada na rufin asiri sannan mahaifinta su biyu Allah yabashi itada kaninta Aminu , Zee suna kiran Mamansu da sunan Umma sannan zee yarinyace mai hankali da mutunci"itadai Zee farace amman batada tsawo sosae sannan batakai Nana kyau bah amman itama tanada kyaunta dai dai misali masha Allah...


Allah yahada jinin Nana jawaheer Adam Sabi'u da kawarta Zainab Kabir Musa wanda sun shaku da juna har yakai basu iya boyema junansu sirinsu Zee tana, bakin cikin abunda Inna Talatu take yima kawar tata, amman ita Nana sai dai tace mata ya zasuyi inba hakuri bah ita dai tasan watarana sai labari, tunda malan Adamu ya saki matarshi Aminatu mai sonshi da kaunarshi tsakini da Allah bata sake waiwayar gidan tsohon mijin nata bah dan har yanzun bata huce abunda shi malan yayi mata ba tabbas basai na fada bah kunsan radadi da ciwon da mace keji ayayin da mijinta ya saketa to haka takasance da Aminatu domin tunda mijinta ya saketa ta kwashe kayan ta koma rugarsu karkarku tayi kuka kuma tayi addu'a Allah yakaremata Nanarta daga shirin Talatu, ahaka rayuwa Aminatu takasance watarana tayi kuka watarana kuma tayi addu'a..



A kwana atashi baya wuya agurin Allah yanzun Nana tayi JSSCE suna shirin shiga SS1,malan Adamu ya sayarmata da uniform da duk abunda ake bukata, shikuma sabi'u ya shiga JS2 sai Khadija tana primary 4 yanzun haka sai dai Khadija, da Sabi'u basujin magana sbd ta dauremasu duk abunda suke so shi takeyi masu basu san wani abuba wai shi daina ko kuma kayi duk sun raina Nana, domin Sabi'u har zagin Nana yake indan kuma Nana ta bugeshi, ranar sae ta gwanmace dama ba haifeta bah a duniya,haka dae Nana taita hakuri da Inna Talatu watarana idan abun ya isheta sai taje gidansu Zee takama kuka, Zee na bata hakuri....


Abangaren Sadiq yanacen niger republic a Maryam Abacha yana ta karatunshi acikin kwanciyar hankali, yasa karatunshi gaba dan yanason yacika burinshi nazama cikakan likita wanda duniya xatayi alfahari dashi sae dun abunda yakeyi tunaninshi da zuciyarshi tana wajen kawarshi Nana "yanason Nana tun baison maiyene soba yana kishin *NANA* tun baison maine nene kishi ba Allah yasamashi soyayyar kanwartashi tun bai son wayeshi bah, yanzun Sadiq yana final year dinshi,,, itakuma Nana tashiga SS1 a secondary school....


Cigaban labari.......


Indan kunason nacigaba dayi maku wannan labari mai cike da soyayya da tausayin toh naga comment dinku domin yanxun akafara labarin ๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜....

Shin malan Adamu zaiyi hakuri yaba kaninshi Sulaiman diyarshi Nana jawaheer domin ya rige mashi ita ko kuma tanagama karatu aure zaiyi mata tunda baida kudin da zai barta ta cigaba da karatun gaba? ayya kuwa Inna Talatu zata sauko daga dokin kiyayar da yima Nana? shin Sadiq yana fadama Nana yanason ta?


duk wannan anso shin suna cikin wannan litaffin mai albarka kude kucigaba da share da comment much love my fans๐Ÿ’˜๐Ÿฅฐ


Share and comments๐Ÿ˜
๐Ÿง•๐Ÿง•๐Ÿง•๐Ÿง•๐Ÿง•๐Ÿง•๐Ÿง•
*NANA JAWAHEER*
๐Ÿง•๐Ÿง•๐Ÿง•๐Ÿง•๐Ÿง•๐Ÿง•๐Ÿง•๐Ÿง•

*๐ŸŒMANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION๐Ÿ“š๐Ÿ–Š*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.๐Ÿค™๐Ÿป```

--------------------------------------

*Story and writing by*

*Jameelah A Belloh*
*(Jameey)*

*DEDICATED TO AUNTY BINTA U ABBLE*



*Bissimillahir Rahamanir Raheem*


*Godiya ta tabbata da Allah wanda ya hallincemu kuma ya halinci mutane da duwatsu ya shinfidda sanmai da kaisai, ya Allah yanda kabani damar yin litaffin lafiya Allah kasa nagama shi lafiya amin๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™*


*Tabbas naga masoya makaranta wannan litaffin, "wasu nacewa karayimaku Read more ae uzuri zakuyiman tunda nidae sabon shigace wannan Nana jawaheer shine farkon fara novel dinna kunga koh dole sae ahankali zani ida sabawa da yawan typing dakunga yanda nike yimaki Read more har biyun nan sae kun jinjina man saboda har ciwon baya nike๐Ÿ˜๐Ÿ™ˆ"amman insha Allah i'll try my best Ilove you all my fans๐Ÿ’”inayinku irin over and over dinna!!!*



Page 0โƒฃ4โƒฃ


"Ke Nana wae har yanzun bakigama gyaran kayan miyar bah?.

"Inna na kusan gamawa kinsan idan na taba kayan miya hanuna zafi sukeman, "dan Allah Inna ko Khadija tazo ta tayani gyarawa ko mungama da wuri? "Tunda kayan miyar sunada yawa sosae kuma naga la'asar tana gabatowa,

"Khadija fa Kikace Nana?

"Yanzun Nana kayan miyar ma sae antayaki gyarawa saboda rauganci irin naki nagado koh, to bari kiji ba wanda zai tayaki aiki a cikin gidan nan, inbama rauganci irin naki ba ai ni banga wani aiki da za'a tayaki ba tunda ba wani abun kirki uban naki ya kawo na azo a gani bah wai kuma a haka gobe sallah za'ayi......


"Asalama Alaikum.
Amin "walaikumus salamu....


"Yauwa Khadija dan Allah kizo kifara yin wannan wanke-wanken kafin na dawo daga kai wannan markaden.

"Kan bun nan yo ni baiwarki da zaki sani aiki?

"To wallahi ko bani yin wani wanke-wanke ni nan ma yanzun kitso zani.

"Khadija yanzun ni zansaki aiki kice bakiyi?

"Eh din ance bani yi karma kisake gigin sake sani wani aiki a cikin gidan nan nadai gayamaki, Ke dan ubanki ni kike gayama wannan maganganun? Ni kawarkice dan ubanki? To yau sai nace uwarki acikin gidan nan....


Nan fa Nana ta tashi ta kama dukan Khadija, "La'ilaha illallah mai zangani haka acikin gidan nan?!!

"Nana yazun diyar tawa zaki kasheman ko?

"To wallahi yau sha naci ubanki cikin gidan nan, a haka Inna ta dage tai ta bugun Nana bataji bata gani har sai da ta gaji dan kanta sanann ta kyaleta....


"Zaki tashi ki idda aikin ki ko sanann ta taso?

"Dan Allah Inna kiyi hakuri yanzun xantashi,

A haka Nana tagama yin aikin daren sallah, tasa sauwar miya sannan tace ma Inna, "Inna nagama......

"harda miyar kin daura ne?

"Eh Inna duk nayi komai harta ruwa duk na e'bo shi.

"Inna dan Allah ina son nima natafi ko kitso ne zee tayiman tunda nagama komai.

"Bangane kin gama komai bah?

"To ko da kin gama ba inda zaki tafi, har sai kin sauke miyar nan, ke baki daya ma ba inda zaki tafi sai kace wata tsiya kika tanadarma sallar, ko dan kala dayar da wancen uban naki, shi yaki ma wani kitso to haka zakiyi sallah ba kitso balle kunshi..

"Aah Inna kibar ni nayi koda kitso ne, ko ba komai ai ko a muslunci ana so koya yane mutum yayi kitso Inna, Dan Allah kibarni nayi Inna..

"Oh ni! Talatu yanzun Nana ni zaki zaga a cikin gidan nan ko?

"To bari ubanki yadawo sai yayi mana tsakani dani dake a cikin gidan nan a haka Inna tagama yin balbalin bala'in ta har sai da Malan Adamu ya shigo ya tadda wannan masifa.

Malam Adamu ne ya kalleta yace "Wai lafiya Talatu kike ta fada tunda na shigo cikin gidan nan ko Sallama ma baki ansa man ba?

"Ina fa lafiya malan yau diyarka ta bude baki ta zageni acikin gidan ka, dan kawai na fada mata gaskiya, nan fa Inna tasama malam kuka tana cewa daman tuni nasan Nana bata daukan a matsayin uwaba, duk son da nike yima Nana amman ita bata gani, tunda gashi yau dai ta zageni da bikinta, Ita mamar tawa ta zagi ki?

"Au haka ma zakace kenan malam ai gatanan ka tambayeta kaji ta bakin ta tunda ni nayi maka karya, Aah talatu ba haka nike nufi ba amman Allah yabaki hakuri, yanzun xanyi maganin abun ba sai gobe bah....

"Ke Mamana zonan mai yasa bakai jin magana?

"Tarbiyar dana baki kenan Mamana?

"Duk kokarin da baiwar Allah nan ki maki baki gani?

"Yanzun inba ita Talatu bah wa zai yi hakurin zama dake cikin gidan nan?

"Magana nike yi kinyi shiru kin kyaleni,

"Baba dan Allah kayi hakuri, insha Allah bazan sake koda yima Inna gardama ba balle abun yakai da haka,

"Inna dan Allah kayi hakuri bazan sake ba Inna,

'Keyiman shiru mutunniyar kawai, kina jina daga yau karna sake ji balle nagani kijini koh Mamana?

"Baba insha Allah.

"To tashi kije a gabanta kibata hakuri sosae...

"Inna dan girman Allah kiya feman ba zan sake ba,"to shikenan nayi, tashi kije ki sauke miyar can sannan ki dauramana abun bude baki,

to nagode Inna....

"haka Nana takama yin aiki itace bata hutaba har sai da aka dawo daga shafa'i da wutri sannan ta kwanta dan tayi bacci...

"Zo nan Aiman tasho kaje zulai tayi maka wanka (zalai mai aikin gidan Alhaji sulaiman ce)"to Momy,"Momy yau yaya Sadiq zai dawo ko?

"Eh yau zai dawo katashi kaje zulai tayi maka wanka domin naji Daddynku yana cewa yayan naka yana hanya, saura kuma in yadawo ka matsa mashi da surutunka kabarshi ya huta sannan,"Aah momynsu ai ko ba za'ayi haka ba shida yayanshi sannan ace wai karda ya matsa mashi bayan sun dade basu hadu bah...

"Haba Annin sadiq, ae shi Sadiq din nasan ya gaji sosai yana da bukatar hutu shiyasa, kai tashi kaje zulai na jiranka!!!....


"Yauwa momy,"naji yaya yana maganar walimar da za'ayi ma Sadiq tagamar kammala karatun nan nashi ko?"eh haka ne,"to gaskiya da zakuji shawarata da ba'ayi mashi wannan walimar ba saboda da mai kika ce haka Anni?

"Saboda ina hangen kudin da yaya zai kashe daya kashen kudin wajen wannan bidi'a ai gwara yayi sadaka dasu yace ayi mashi addu' samun nasarar karatun da kuma yin amfani dashi,"eh gaskiya Anni kema kin kawo taki shawarar, kibari idan yadawo zan yi mashi maganar mugani ko za'a dace....

"Aah bake yakamata kiyi mashi magana ba, kinsan ba yarda zaiyi ba,

Eh hakane, "amman ya kikagani Anni?"abunda yadace kawai muje yanzun mufadama Hajiya nasan ita zai ji ta,"eh Anni, kin kawo shawara mai kyau kuwa, yanzun tashi muje kafin ya shigo kinsan yanzun haka yana hanya, dan yau sai zumudin dawowarsu d'a namu yake, dariya sukayi nan Anni ke cewa ae soyayyar Yaya da sadiq gaskiya Momy daga Allah ce,"tabbas Anni, kuma Sadiq yanada shigar rai sosae fatan mu dai Allah angama da sa'a yana gama service dinshi gsky zamuyi mashi aure...

"Assalama Alaikum,

"Amin wa'alekumus salaam,

"Hajiya sannu da hutawa? " yauwa Fateemah sannunki, ina ja'irin yaron nan yake? "yazo nan yagama bataman parlo yana kallon wanann arrnan wanda ko son musunlinci basuyi, ya gama kuma yatafi ya barman gun haka,

"ai hajiya keda Aiman bamai shiga tsakaninku, inma mutun yashiga to ko yaji kunya ko Anni,"tabbas ai ni shiyasa bansa baki ba, "daman hajiya wata magana muke so muyi dake akan walimar da Yaya yace zai yima Sadiq bayan sallarr nan,"kinga dai yanzun haka Sadiq yana hanya, sannan hajiya agani na baidace ace anyi wannan budi'arba Hajiya, saboda yakamata ace an nemi albarka, amman yakika gani hajiyarmu, tabbas Khadija kunyi tunanin da ba kowane mai hannu da suni suke yin shi, yanzun wannan zamani rabin mutane da kawata burinsu shine idan zasuyi wani abu sudai suyi bidi'a wasu basu yin bidi'ar tasu sai da biki wasu kuma suyi na zaga yowar haihuwarsu wasu kuma su na kanmalla karatu, duk basu san albarka suke debewa ba,
su dai indai duniya zata kalla ta yaba ae abun yayi masu, sun manta Allah shi ya azurcesu da wannan dukiya mai makon su kasheta ta hanya mai kyau Aah sun ganmace suyi bushasha dasu, bayan albarka yakamata su nema wajen ubanginmu Allah (STW), ance kudi akashesu ta hanya mai kyau ai sai wasu suce ai daman ta hanya mai kyau muke kashesu tunda bamuyin zina balle caca, ai ba haka ake nufi bah, saboda hanyar lada tanada yawa koda wani almajiri kasamu kana bashi abinci safe da rana da dare xakasamu lada aikwai hanyoyi kala kala ma wanda zakabi kasamu lada, Allah yasa dai mudace mukuma yi kyaukyawan karshe, Ameen hajiya.

"yanzun kubari idan shi Sulaiman din yadawo zamuyi maganar dashi,

"Toh Hajiya Allah yakara girma da tsawanci rai, Amin ya Allah.....

"Assalamu Alaikum,

"Amin wa'alaikumus salaam.

"Hajiya sannu da hutawa,

"Yauwa Sulaiman andawo kenan?

"Eh Allah ya yarda nadawo Hajiya, kinsan yau Sadiq yake dawowa, yana hanya yama bugoman waya yace sun iso cikin katsina...

"Yauwa zauna inason yin magana dakai kafin ya ida shigowar, "daman maganar walima mar da naji kace zakayi mashi, to ban yarda bah,"amman Hajiya ai,"yi man shiru kafin raina yabaci Sulaiman,"ai dama me eyyeh ko gardama zakayiman?

"To bude kunnanka kajini da kyau umarni nabaka ba shawara bah, na hana wannan walima da zakuyi, kaje kayi sadaka da kudin da kayi kashewa kasa amai addu'a Allah yasa yayi amfani da karatun nashi amfani mai kyau,

"to Hajiya insha Allah yanda kika ce haka xa'ayi, kiyi hakuri Hajiya,

"Tashi kaje na yafaimaka,

Nagode Hajiya...

Oyoyo! Oyoyo!! Oyoyo!!!, ga yaya Sadiq nan.......



*Yawan comment dinku* *yawan typing*



*Daga yau zan ringa yimaku posting sau biyu a rana,saboda ina ganin ruwan comment sosai๐Ÿ˜, kafin nan da azumi*
๐Ÿค๐Ÿป


Share and comment ๐Ÿ˜

๐Ÿง•๐Ÿง•๐Ÿง•๐Ÿง•๐Ÿง•๐Ÿง•๐Ÿง•๐Ÿง•
*NANA JAWAHEER*
๐Ÿง•๐Ÿง•๐Ÿง•๐Ÿง•๐Ÿง•๐Ÿง•๐Ÿง•๐Ÿง•




*๐ŸŒMANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION๐Ÿ“š๐Ÿ–Š*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.๐Ÿค™๐Ÿป```

----------------------------------------


*Story and writing*

*Jameelah A Belloh*
*(Jameey)*



*DEDICATED TO 80k*


*BISSIILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*


Page0โƒฃ5โƒฃ



"Momy, ku fito ga Yaya Sadiq nan, duk suka fito da sauri, Momy tace"Son! Wooow masha Allah wani handsome guy ne naga ya juyo yana cewa"Momyna I really miss you Momy, "miss You more Son,"wellcome home Son, Happy to see you my son, am very happy to see this day because My Son has come back to home cikin koshin lafiya,"Ohhh Hajiya kinga Sadiq da Momynshi sunbarmu nan tsaye kamar ma basu ganmu ba, in bakusan muyi maku sannu da hanya mu koma ciki, munsan dai dole azo agaidamu inkun gama dokin ganin juna,Anni ce take fadin haka tana dariyar farin cikin tilon danta yadawo daga karatu,"Aaah! Annina yanzun nike shirin nataho gurinku in nagama" gaisawa da Momy na, Sadiq yace ma Annin tashi yana yima ta shagwaba,"Ooni Khadija,"Sadiq har yanxun dai halinka na nan,wannan shagwabar ko angirma amman har yanzun baka daina bako"Aah Anni ai ni har yanzun yarone a wajen ku, Sadiq yake fadar haka yana rungume uwartashi yana cewa," nayi missing dinki Anni sosae,nayi missing din fadan nan naki yana dariya,"kaga ni dagani karka karyani, kai kayi Aiman yayi, ta fada tana tureshi,"kinga karki karyaman jika,in shi bai karya ki ba ai ke kin karyaman shi,"Hajiya ce ke fadar wannan maganat tana dariyar farin cikin dawowar babban jikan nata kuma abokin fadanta,"kai Saddiku baka zowa nima ka gaidani dan iyayenka,"haba Hajiya wai sau nawa zan gaya maki banison kina fadaman wannan sunan, amman baki dainawa daga shigowa ta har kin fara batamin rai,Sadiq yace ma Hajiyar tasu haka yana, yimata shagwaba shi a dole kuka zaiyi mata, Ni Nana jawaheer yau naga ikon Allah yanzun kai Saddiku kato dakai kake shirin yimamu kuka, dan nace Saddiku,"to bari kaji yanzun nafara kuma ban dainawa,"haba Hajiya yanzun yadawo fa har kunfara dramar taku ko, Alhaji Sulaiman ne yayi maganar fitowarshi kenan daga cikin gida, yana maganar yana kama hannu Sadiq yana cewa,"kyaleta kaji,"taho kaje kayi wanka kafin akira sallah, muyi buda baki,"to dady, haka suka dun guma suka shiga ciki, ita kuma Hajiya tayi apartment dinta itada Anni......

"Nana gobe fa sallah, Amman banga kinyi kitso ba balle kunshi? "Hmmm Zee bangayamki dramar da akayi bah dazun ni da Inna ba, akan kitso ma kawai, nan dai Nana ta kwashe komai tagayama kawarta, "A gaskiya kawata abun yafara isata abunda Inna keyi maki itada yaranta, inbaki iya daukar mataki to ni gaskiya kibar gayaman kayan bakin ciki,"wai Zee har sai yaushe zangaya maki wannan maganar watarana sai labari, kuma ya zameman dole nayi hakuri da Inna, tunda matar uba nace, insha Allah komai zaiyi sauki, nidai Zee ki ringa tayani da addu'a, ko kin manta bature yana cewa *NO CONDITION IS* *PERMANENT* ?, "to haka abun yake kawata,"to shikenan Allah yasa inada rai naga wannan rana Nana,"Amin,"yauwa daman ummanmu ce tace man nazo na taho dake muje ayi mana kitso da kunshi sai ki kwana gidanmu, Zee tace ma Nana haka, "to amman Zee kinaga Inna zata barni naje kuwa? "Haba Nana ai ba ita zamu tambaya ba muje tunda baba yana nan mu tambayeshi mana nasan baya hanaki tunda gidanmu zakije,"To shikenan, tashi muje mu tambayeshi tunda yanzun yana kofar gida, su Nana sukaje suka tambayi malan zataje gidan su Zee, zasuyi kitso da kunshi"Mamana idan kunje ana gamawa washe gari da safe ki da dawo gida da wuri toh insha Allah baba mungode....

Masha Allah Sadiq na hango yana tafiya zayaje suyi buda baki,Sadiq dai farine sosai dan farinshi har *glowing* yakeyi saboda hutu ya zauna a jikinshi da kwanciyar hankali, tafiya yake amman kamar yana tausayin kasa tsabar natsuwa data zauna jikinshi, Sadiq yanada tsawo sosai sannan yanada hanci sosae yanada manya Idanu sosae lulu eyes,da dan bakinshi dai dai dashi, Sadiq baida hayaniya baya shiga abunda ba'a sa shiba, sannan baya daukar raini da sakarci yanason mutum mai Wayoh wanda baya daukar raini, sannan shi Sadiq mutunne mai fara'a da wasa da dariya, amman duk da yanada wannan halin hakan bai sa ya dauki rainin mutane bah, sannan Sadiq yanada saurin fushi da kuma saurin sauka daga fushin kuma, wannan kenan daga cikin habit din Sadiq....

Sadiq har ka fito? "Eh Momy na fito, sannunku da shan ruwa, daddy sannu da shan ruwa,"yauwa sannu Son, ai kai ke da sannu wanda yasha tafiya mai nisa har haka amman sai da kayi azumi,"ai Alhaji daman nace maka Son jarumin d'a Allah yabamu,"hakane ko momyn sadeeq, "yauwa Aiman tashi kaje ka kaima su Anninka kayan buda baki, dan nasan Hajiya ba zuwa zata yiba muci a nan, baki daya bah,"to Dady,"dady gobe sallah damai damai a ka kai gidan Abba Adamu na sallah?"yauwa Son Allah dai yayi maka albarka,"kaga Daddynku tuntunin duniya nike nuna mashi wannan maganar amman baya tsayawa ya saurareni,tunda azumi nan yakama ko daudawa anan gidan bamu kulle munkai mashi bah balle akai da kayan lashe baki,"haba Daddy gaskiya banji dadin wannnan labari ba,"yanzun zakuci abinci ko surutu zaku tsaya yi?"kuma daga yau karna sake jin wannan maganar a bakin ku, tunda tsakanina da dan uwanane, tunda ba fina sonshi kukayi bah,"Amman Alhaji"ya isa haka Momyn Sadiq,banison ai ta maimaita magana nidai nagama yanke hukunci,"to shikenan Allah yahuci zuciyarka, "amin......


a haka dai sukagama yin buda bakin, Dady yace ma Sadiq "katashi kaje ku kara gaisawa dasu Hajiya gobe insha Allah inason nayi magana dakai, "toh shikenan Dady Allah yakaimu goben lafiya, "amin ....


Yar tsohuwa mai ran karfe,"Saddiku anshigo kenan? "Eh na shigo mai zakibani,"aiko kazo nabaka kunun danayi wanda baka bata shan irin shi ba, "ai ni ba komai nake ciba, "kai dai kasani dan nema, "Hajiya ansha ruwa lfy? "Lafiya lau, ya gajiyar hanya kuma? "Alhmdulh, Anni ansha ruwa lfy?"Lafiya lau Sadiq, da fatan dai ansamu abunda akaje nema?"Eh Alhmdulh Anni,na gama karatu lafiya kuma nasamu result din da nike gurin samu saboda da first class nagama yanzun kuma saura services"To Sadiq Allah yakara baka sa'a dakuma nasara a rayuwarka yakareka daga sharin makiya, "Amin ya Allah, "sannan dan Allah Sadiq ka kara rige mutunci kanka dakuma girman ka kaji yaron albarka,"insha Allah Anni, "To Allah yayi maka albarka, "Amin, Ni Anni zani je massalaci lokacin sallah yayi daga can kuma zan wuce apartment dina na kwana inason natashi da wuri saboda sallahr id'i, "Toh shikenan Allah ya tashemu lafiya Amin....
"Assalama Alaikum,"Amin Wa'alekumus salaam"Wacece haka take yimana doguwar Sallama tunda uwar safiya haka? "Inna nice, "au kece koh kingama yawon banzan naki, wanda kika saba, sai yanzun kika gadamar dawowa cikin gidan ko? "Aah Inna wallahi gidan su Zee na kwana kitso da kunshi mukayi shiyasa, Kuma sai da na tambayi baba, "kika tambayi baba, wato ni banida arzikin da zaki tambayeni ko? Saboda ban isa bah, "ba haka bane Inna, lokacin da zamu tafi naga kamar kina bacci shiyasa, "ina bacci ko? Yanzun bani da lokacin surutunki, kije ki aza sanwar tuwo tunda bani zaniyi maki ba, shegiya mai bakin halin tsiya, Kuma kiyi sauri kigama kafin a fito daga massallaci, "To Inna insha Allah, Nana tasa sanwar tuwan sallah tanayin sanwa tana aikin gida bayan tagama Kuma tafara kai abinci gidan tsofaffin unguwarsu,Khadija da Sabi'u kuma sunyi wanka Inna ta basu kayan masu kyau sun tafi sallah subar Nana da aikin walaha...

Sadiq kuwa bayan sun dawo daga sallah yatafi wajen Dady zasuyi magana....




*Zan ringa yin posting sau biyu

Please Login or Register in order to submit comment