Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a kayi mata, ai kom Sadiq yaga rauganci gun Nana, dan tayi kuka kamar ranta zai fita, wai ita bata son allura,(TEAM NANA, kunji wata sabuwa kuma, wai Nana bata son allura😜)....

Aiko Sadiq mai zai yi in ba dariya ba, yana cewa aiko yarinya, ya kama ta ki saba da ita ko, dan ko nan gaba kadan gidan allurar zaki dawo, Ita Nana bata fahimci maganar yayan nata ba tana cikin yin kukan shagwabarta.....

Sun iso gida suka tadda malan a gida yana zaune yana jiran dawowarsu....








Share and comment pls




Vote pls on my wattapad 😍




*Meeeeeeelatu πŸ€“*

πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•
*NANA JAWAHEER*
πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•



*STORY AND WRITING*
*BY*
*Jameelah A Belloh*
*(Jameey)*


*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–Š*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.πŸ€™πŸ»```

----------------------------------------








*Wannan page din saudaukarwa ne ga duk wata mai suna _SAKINA_ ,ina son wanann sunan, kuma ina mutunta mai wannan sunan, a duk inda take a fadin duniyaπŸ€—πŸ’”*




*BISSIILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*




Page0⃣9⃣







Zaune suka taida Malan a kofar gida, yana ta fada,Talatu ta gayamai karya da gaskiya, shi kuma ya kama ya zauna, kawai jiran dawowar su Nana kawai yake yi domin yayi rashin mutunci....


"Abba barka da hutawa,"yauwa Sadiq, ashe kai ne Sadiq din da Talatu keman magana, ka bugeta ita da Khadija dan kawai ka tad'da tana yi ma Mamana wa'azi?...



"Eh Abba, amman ba haka aka yi ba,"to gaya man ya abun yake Sadiq...


Nan sadiq ya gayama Malan yanda ya faru da kuma hukunci da ya yi ma Khadija, har yanda yakai ita Nana a chemist....


"Allah sarki, Sadiq Allah yayi maka albarka, Allah na gode maka da ban saurin daukar hukunci ba, na tsaya naji daga bakin ka, haki'ka Sadiq yarinyar nan nasan tana shan walaha a wajen Talatu, to amman ba yanda zanyi da ita, in ba hakuri ba, kuma na mata idanu, nasan Allah zai zaka ma.....


"To amman Sadiq ya a kayi Mamana ta ganeka?!



"Aah Abba na lura Nana bata ganeni ba, kawai dai ta bini chemist din, dan ba yanda xatayi..



"Eh gaskiya baza ta gane ka ba, saboda ai tun tana yar shekara biyar,ba ka sake zuwa wajena ba..



"Ai Abba ina makaranta, duka duka banyi wata biyu da dawowa ba, yanzun haka ma yau zan tafi India domin cigaba da karatu..



"Ikon Allah, Sadiq wannan wani kalar karatune akeyi har yanzun ba'a gama ba?


"Abba ai karatun likita nike, kaga ai dole matum yayi karatu mai zurfi in dai yana son ya zama babban likita..



"Eh tabbas hakane, nidai kyauta ta itace nayi maka adu'a,Allah yasa aje a sa'a kuma a dawawo cikin nasara..



"Amin Abba," daman Abba ina son na nemi wata alfarma a wajenka..


"Wace alfarma ce haka Sadiq?,fadi ko wace alfarma ce,Allah ya bani ikon yi maka ita..


"Amin ya Allah, daman Abba inason,kabani Nana na tafi da ita gida,ta zauna gun Hajiya..


"Tabbas Sadiq ka rokeni abu mai girma," Abba Dan Allah kar kace man ba zaka yi Mani wannan alfarmar ba...



"Sadiq a gaskiya ina jin nauyin ka,sannan kuma tabbas ina tausayin Mamana,zanfi ka jin dadin komawar Mamana a gurin Hajiya,sai dai maganar gaskiya Sadiq ba zan mayar da ita gidanku ba...


"Saboda mai Abba?," saboda ba zan iya bada Mamana wani gida ba da sunan yar riko ba,duk da gidan dan'uwa na ne mafi soyuwa a cikin zuciya ta..


"Tabbas banga laifin su Sulaiman ba shida Hajiya dan suna fushi da ni ba,Amman ka sani ina mai bakin cikin yanke alakar da mukayi a tsakaninmu,Amman duk da haka Ina son kanina,kuma ina kara yi mashi adu'ar bude...


"Amman Abba,baka ganin halin da Nana take ciki?,tabbas barin Nana a hannun Talatu yana cikin barazanar rugujewar rayuwarta..


"Kayi magana mai kyau,kuma tuni na da dai da daukar wannan alkwarin,Mamana na gama makaranta zan yi mata aure...


"Aure kuma Abba?,Sadiq ya tambaya cikin ta shin hakali yana mamakin Abban nashi..


"Eh aure abunda kaji kenan,duka duka yanzun saura shekara biyu ta gama makaranta,ni kuma tana gamawa zan yi mata aure insha Allah..



"Amman Abba,duka duka nawa Nana take da za'ayi mata aure,yanzun fa take shekara sha biyar..


"Eh aure xan yi mata,kuma na gama magana Sadiq,,ka tashi ka tafi kafin ka makara, tunda naji kace yau zaka tafi India..



"To Abba shikenan,Abba ni zan tafi,amman dan Allah Abba kayi tunani akan maganar da mu kayi da kai..


"To shikenan,Amman Sadiq zaka yi shekara nawa a India?.


"Zan yi shekara biyu insha Allah Abba,"to shikenan Sadiq Allah ya yi maka albarka," Amin Abba...



"Abba ga wannan ka rike," to nadoge Sadiq,Aah ka tsaya mana na kira Nana,, na gaya mata waye kai!..



"Aah Abba ba sai ka kirata ba," ai watarana zata sanni, nan gaba insha Allah, "to Allah yasa Sadiq," Amin Abba..
"Allah ya kiyaye kaji yaron albarka," amin ya Allah....


A haka Sadiq ya tafi jikinshi duk a sanyaye,yana tunanin maganar Abba,wai Abba zai yi ma Nana aure tana gama secondary, " *no it* *possible* , ba zai yuyu ba gaskiya,ina zai bari Abba ya yi wannan aika aikar ba..


Yana wannan maganar,har ya isa wani dan shago a cikin unguwarsu nan yayi ma Abban nashi sayarya abinci,yasa aka kai masu a gida ya tafi dan Dady yana jiranshi su tafi Kano....


"Wai Allah Dad,wallahi yau duk na gaji," to Son ina kaje ne har haka kake ciwon jiki?,"gidan Abba naje, muka gaisa...


"Son dan kaje gidan Yaya shine har kaji?," to yanzun ya ka tadda shi dan uwan nawa shida iyalinshi,"duk suna lafiya lau Dad, Amman banda mutun daya a cikin su...


"Wake nan Son?," Nana mana Dad, Nana na cikin wahala,Amman ba yanda zamuyi in ba hakuri ba,shima Abba yace yana gaidaku baki daya...


"Allah sarki dan uwana ina ansawa,ai nima insha Allah zani shiga wajen shi na gaidashi insha Allah," Allah yasa Dad, aiko da na fi kowa farin cikin haka...



Sun gama yin magana da Dad din shi,sunyi shawarar yanda Dad zai shawo kan Abba ya anshi rikon Nana,dan Dad, bai yarda ba Abba yayi ma Nana aure ba, tana yar shekara 17 a duniya ba...


A haka Sadiq yaje yayi ban kwana dasu Momy da Anni sannan ya tafi yana mai kewar gida,sannan tunanin halin da ya Nana take ciki wajen matar ubanta...


A haka suka dauki hanyar birnin kano, Dady yana yi ma Sadiq wa'azi a kan yaji tsoron Allah, duk abunda zai yi ya tuna Allah yana kallon shi, in su basu kallonshi, yana yi mashi wa'azin har suka isa *AMINU KANO INTERNATIONAL* *AIRPORT* , suna jiran lokaci ya ida su tashi zuwa *NEW DELHI* da ke India....






```Sorry pls my fans,wallahi aiki yayi man yawane,shiyasa bani yi maku typing da yawa ,kuyi managed da wannan pls😁


```


Share and comments pls


πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•
*NANA JAWAHEER*
πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•



*STORY* *AND* *WRITING* *BY*
*Jameelah A Belloh*
*(Jameey)*


*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–Š*

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.πŸ€™πŸ»```
----------------------------------------



*BISSIILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*



Page1⃣0⃣



"To Son,is time, dan Allah Abubakar Sadiq, kaji tsoron Allah kayi abunda muka turaka kayi, ka tuna da in mu bamu ganinka Allah yana nan yana ganinka,kasan dai *LATAKUZUHU SUNNATUN-WALANAU* (shi Allah baya gyangyadi, bare bacci) dan haka ka ki yaye kaji dan albarka.....


"Toh Insha Allah Dad, nayi maka alkhawarin zan bi duk dokokin da addini ya dingaya mana, da yarda mai sama..


"To Son, Allah ya yi maka albarka, "Amin Dad...


Nan yaji ana kiran sunan shi, ya kara yin sallama da Dady ya shiga cikin flight ya zauna yana mai jin kamar yace ya fasa tafiya, Sadiq yana zaune ya ji wata yarinya tana ce mashi hey handsome...


"Hey,how are you, handsome? Am talk to you fa, but naga ka kyaleni haba sugar, tayi maganar kamar zatayi mashi kuka...


"Sugar pls mana talk to me, dan Allah kayi man magana mana..


"Hlo can you keep quite? You are disturbing me fa, pls don't disturb me I beg you pls!!!



Ok sorry but I love u more that's why,"what do you mean? I say live me along....


Ok don't worry but, am Salmah from kano state,and you?I dont know, pls dear,"am Sadiq from katsina state that's all, pls don't disturb me okay,"ok shikenan....



Yaci gaba da hidimar gaban sa a flight, amman still salmah dik hankalinta na kanshi itadai kawai taji tana kyaunarsa so na hakika..
Alhmdulillah, jirgin su Sadiq ya sauka a cikin kasar India lafiya, Sadiq yayi dropping din *TAXI* ta kai shi gida, gidan da ya kama a new delhi kafin gobe ya shiga cikin makaranta....



*******************
*NIGERIA*



"Dan ubanki sai yanzun kika dawo ko?, wato kun gama iskancin naku ko, sai yanzun zaki dawo man to baki shigan ma cikin daki har sai kin wanke kazantar dake jikin ki dan ubanki...


"Innalillahi, Inna wallahi ban ma san shi ba, banson waye shi ba, kuma wallahi kawai taimaka man yayi...



"Shin, zakiyi man shiru, ko sai na tashi nazo na ci ubanki, yar iska marar mutunci, tashi kije ki ida yin aikin tunda bani zan ida maki ba, yar iska marar mutunci...



Nana ta ida yin aikin gida, sannan ta shirya ta tafi isilamiya, bayan tataso daga isilamiyar tana sauri ta koma gida ta daura ma inna tuwan dare...



"An mata, haba baiwar Allah, ai ya ka mata ki tsaya kiji mai zan ce maki, tun dazun nike ta binki nike yi maki magana, haba ai kin tsaya kiji koh.
"Da Kata bawan Allah, bani da bukatar tsayawa naji wata magana daga bakin ka, kuma ni baba na bai bani izinin tsaya wa da wani ba, dan haka ka fita a harka ta tun wuri domin ban shirya bata lokaci ba..


"Haba Jawaheer, karki man haka, shin kinsan ko tun yaushe nike bibiyar ki? Ko kin san ko tun yaushe nike dakon son ki a cikin zuciya ta? Shin bazaki tausayaman ba, ki tsaya ki ansa kokon barana ba? Wallahi mudin narasa ki, uhmm komai zai iya faruwa dani...


"Dan Allah, Jawaheer ki tausaya man, wallahi jawaheer ban zo maki da shigar yaudara ba, *ina* *sonki* ! *Ina sonki* !! *Ina sonki* !!! Ina yi maki So na haki'ka, So na gaskiya ki bani izini nanu na maki kalan *Son* da nike yi maki pls Jawaheer..


"Da kata dan Allah,haba malan ya kake so nayi maka, to tsaya kaji daga yau karka sake ka kata tsai dani a kan hanya, kaji dai na gaya maka, sannan kaje kasamu mai sonka, amman ba dai ni ba, kawai mutane su kama tsada ka hanya, kamar wata taxi , sallan kaja man masifa a gida ko..


Allah sarki, Nana na cikin yi magana, aiko sai ga Khadija tazo shiga gida ta ga Nana tsaye da wani a cikin unguwa, nan tabi ta gefen su ta wuce tana cema ta..


"Wallahi sai na gaya ma Inna, daman duk karya ce ba makaranta kike zuwa ba, wajen samari kike zuwa...


"Na boni,ni Nana, yanzun ya xanyi, bawan Allah ai yanzun hankalinka ya kwanta ko? Tunda ka jam'in bala'i, ai zaka iya kama gabanka ko?,Nana ta fada cikin fada da tsoron abunda yau Inna Zata yi mata, dan tasan ita yau mai rabata da Inna sai Allah..


"Dan Allah kiyi hakuri, wallahi banson abun haka yake ba..


"Kaga dakata dan Allah, ai yanzun kasan yanda abun yake ko? Dan haka kaga tafiya ta...


"Aah Jawaheer, dan Allah ki tsaya kiji abinda ke cikkn baki na, wallahi komai kikaga nayi, to duk sonki ne sila, kuma yanzun na fara binki Jawaheer har sai kin ansa soyayyata sannan..


Hmmm Khalid kenan, matashin saurayine mai takama da kudi ga kuma kyau, Khalid ba fari bane, sai dai yafi Nana haske, ana iya kiranshi da chocolate colour, Khalid shi daya mahaifiyarshi ta haifa a duniya, Allah ya jarabeta ta ciwon mahaifa wato *CANCER* wanda hausawan mu suke kiranta da suna *CIWON DAJI* , wannan ciwo shi yayi sanadin rasa mahaifarta, domin likitoci sun ce in dai tana son ran ta to dole sai anfidda mata mahaifar, Tayi kuka, sannan ta barma Allah lamarin ta....


Khalid ya nada shekara 3 a duniya aka fidda ma Fulani mahaifa, shiyasa ya taso cikin soyayya gun uwa da uba, domin Baffan shi yace ba zai kara aure ba dan matarshi ta samu Matsala ba, wanan shine yasa hankalin Fulani ya kwanta da taji Alhaji Abdulrahman yace ba zai kara aure ba...


Tunda Khalid yake bai taba neman abu ya rasa ba, duk abunda yace ma iyayen nashi ya na so dole ayi mashi, kasan cewar Baffan shin shine water board din katsina state baki daya, kuma ya sa hannun jari shida wani babban dan kasuwa, suna bussiness tare..


Yanzun haka Khalid lecturer ne a *UMARU MUSA YAR'ADUA UNIVERSITY KATSINA* *(UMYU)* , Yana department of biology..


Khalid mutun ne mai class, magana ma bata cika damunshi ba ko Kadan, Khalid shima yanada tsawonshi ba laifi, Amman duk tsawonshi bai kai Sadiq ba harta kyau domin Sadiq shi daban yake...


Khalid ya hadu da Nana a hanya zata kai ma Inna adashe a gidan Lami mai adashe anan ya ganta, kuma take sonta ya shiga cikin zuciyarshi, shine yake binta har ya kai da ya kasa hakuri sai da yayi mata magana a yau.....


"Assalama Alaikum,"Amin wa'alikumus sallam,"au wato kinzo kin wani kama yi mana doguwar sallama sai kace wata mutunin niyar kirki....


Nan fa inna ta kama yi ma Nana fadan da tasa saba yi mata har tana cewa in dan Malan ya dawo zata fadi mashi Nana dai aure take so, tunda ta fara bin maza, ta inda take shiga bata nan take fita ba, ita ko Nana sai kuka take tana bata hakuri, amman duk a banza domin Inna tayi nisa bata jin kira, a na haka Malan shigo...

"Wai lafiya ake ta masifa har haka?


"Ina fa lafiya, Nana ta fara kaso mana gardin Allah a kofar gida..


"Gardi fa kika ce Talatu? "Eh gardi mana tunda da idona na gan su suna tsaye a kofar gida, har yana rike mata hannu...



"Aa Baba Allah ko ba haka bane, "ke yi man shiru Mamana, yanzun abunda zaki yi kenan a cikin unguwarnan, to tsaya kiji kar in kuma ji makamanci kalar wannan maganar, kinajina ko?

"Eh Baba Insha Allah zan kiyaye, Nana ta fadi tana kuka mai ban tausayi... ..




**********************
NEW DELHI INDIA........





*NOTE:-* πŸ‘‡


*Tuni nike yin mistake wajen gun sunan ANNI, ashe sunan ba haka yake ba amman ba wanda ya fada man sai yau wata baiwar Allah mai kaunata ta gyara man sunan AMMI yake ba ANNI..*

*Don haka yanzun sunan ya tashi daga ANNI ya koma AMMI, dan Allah duk wanda ya sake gani wani mistake dan Allah agaya man ni kuma zan gyara ngd.*




*Share and comment pls*



_Sannan har yanzun banga an fara view NANA JAWAHEER a whattpad ba pls VIEW and VOTE_



πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•
*NANA JAWAHEER*
πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•

*STORY AND* *WRITING BY*
*Jameelah A Belloh*
*(Jameey)*



*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–Š*
*MWA*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.πŸ€™πŸ»```

----------------------------------------



*DEDICATED TO* *AMINATU* *(HAKIBAπŸ€ͺ)*


*BISSIILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*



Page0⃣1⃣1⃣



UNIVERSITY OF DELHI INDIA, tunda sadiq ya shiga school dinsu yaga kalar tsarin ta...


makaranta ce tsararriya hadadda iya haduwa tinda ga bakin gate din school din zaka taradda da security, za suyi checking dinka, sannan abar mutun ya wuce idan kuma a mota ka ke xa'ayi checking din boot din motarka....

Sannan a baka wani card, sai ka wuce, wanda ake cema *checking point* *card*....

Tunda Sadiq ya shigo taxi ba inda ya tsaya sai faculty of medication sciences...

Sannan ya shiga *department of medicine* *and* *surgery* ,yane mi *lecture hall(theatre) ,* ya shiga theater ya samu sit ya zauna.

"Hello students, am Prof Rajbir Kokureja, Today we should discuss to you a surgery from part of it, we are talking about theatre(CS)..


So class who can give a little definition of theater?any one.....

gabaki daya class din yayi shiru daman ba wani yawane da suba, Sadiq ya daga hannu yace Sir , "Ok stand up, ur name...


"Am Sadiq Musa "Nice name,from where re u....


"From *KATSINA STATE,* *NIGERIA* , "you are welcome, what is theater ?

" ```theater is a medical treatment in which a doctor cuts into someone's body in order to repair or remove damage or diseased Inside part of the body.```


"Wow very nice my
Brilliant student,Sadiq my friend.

Haka dai lecture din taka sance ya gama lecturer din ya fita, amman yana mamakin sadiq din, ba abin mamaki ba ne dan degree folder Ya bada ansa akan area of specialization dinshi...


Amman ba kowa bane zai iya tashi ya bada ansa ba acikin tarin jama'a ba...


Balle wajen daya kasance bako a wajen ka ga launin fata da yare kala-kala....


"Class din sai mamakin confidence irin na Sadiq suke yi...


Dan da yawansu sun sama ransu ta hanyar da za subi domin suyi kawance dashi, haka suma matan....


Tun da Prof Rajbir ya fita Sadiq ya kama harkan gabansa ba matan class dinsu ba harta mazan ma basu da meshi ba...


Saboda ya sama ransa ba da kowa zai hudda ba...


Yana zaune saboda ance masu mai masu lecture din Chemical Substances zai shigo...


Shiyasa basu fita ba, sai dai masu bukatar hakan...


Sadiq bai da niyar fita, yana zaune sai yaji ance mashi,

"Hlo friend, ya daga kai, sai yaga wani kyakkyawan saurayi ne tsaye a gefenshi, yace"am Lukman Yusuf from Katsina State Nigeria, I like to be ur friend, I hope my request has been accepted, da dai Sadiq kamar ba zai magana ba kuma sai yaga from the same state daman yana tunanin shi kadai ne sai yace masa...


"Nice to meet u friend God bless our friendship...


take Lukman yaji wani irin dadi a ranshi marar misaltuwa...

"Lukman yace yanzun tunda Dr Rahul khan bai zoba sai mutafi daman inajin yunwa tunda nasamu aboki...


Yau ina cikin farin ciki, ji nike kamar wani dan uwana...

Sai dai Sadiq yayi murmushi take kyawunsa yakara bayyana har saida Lukman yace *barikallahu* *fihi* a ranshi, ba tare da Sadiq yayi gardama ba ya tashi ya bishi, tinda suka Fito daga hall din yake ganin tsaruwar wajen ba sai na fada muku kalan kyawun wajen ba amman ya kayatu da flowers ga wani irin liftas da zata kai ka upstairs wajen office din lecturers, haka dai suka tafi Restaurant inda Lukman yasa a kawo masu abinci ya tambayi Sadiq me yake son a kawo mashi yace Coffee is Ok, nan Lukman yace ai mashi ordering din shawarma and bottle of water....

Nan suka gama cin abinci sai suka fito inda Lukman, ke cema Sadiq ina ne ma saukinka broth....

sai Sadiq yace yana" *KURANA ESTATES* , wow wonderful place , and you?


"Am lived in Mahendra coters "naji dadin yanda ka bani kulawa Lukman, thanks, "Never mind, it's pleasure.....


Nan sadiq yace zan wuce friend sai mun sake haduwa, okay amman ina son muyi exchanged din contents, da kamar Sadiq ba zai bashi number shi ba, sai kuma ya bashi, yayi godiya kowa ya kama gaban shi,


Tunda sadiq yafita yayi dropping din *TAXI* , takai shi har kofar gida yana shiga ya wuce toilet yayi wanka ya fito yayi sallah, sannan ya kwanta dan ya huta, Sadiq kenan......


*************************
*NIGERIA*


"Zulai, na'am Aunty zoki kawo man wannan mango juice din ban san Daddyn Sadiq ya dawo ba'agama hada kayan abincin nan ba,"Toh aunty gani nan...


Nan Zulai ta kawo mata mango juice din ta saka shi a cikin freezer....


Sannnan suka cigaba da yin jollof cus-cus...


Yanda ake yin jollof din cus-cus..


```Idan kika dora frying pan dinki a gas sai kidan zuba man-gyadanki kadan ko butter dinki, idan yayi Zafi sai ki zuba Cus-Cus dinki, ki so yashi sama- sama sannan sai ki sauki idan ya danyi brown nish kadan, sannan zaki daura tukunyarki ki saka manki da albasa ki soya su, sai ki zuba kayan miyarki, idan suka soyu sai ki zuba ruwanki dai-dai yanda zai isheki ma'ana yawan Cus-Cus dinki, daman kin tanaji kayan dandanonki sai ki zuba magiggiga,daman a gefe kinyanka su, Albasa, carrot peace dinki sai ki wankesu ki zuba cikin tukunyarki,sai ki dauki curry da time dink, ki zuba,To yar uwa da ganan ruwanki zaita tafasa yana dahuwa, daman kin ta fasa namanki ko kinsoya kifinki, sai ki gyara shi ke debe kaya, in kuma nama ne sai ki yanka shi maki-manta sai ki zuba, idan yakara tafasa sai kizuba wannan Cus-Cus din naki da kika soya, sai ki motsashi komai ya hade jikinshi sai ki bashi some times idan yayi taushi saiki sauke , idan kuma da sauranshi saiki dan kara ruwa kadan amman fa ruwan zafi, zaki dan kara sai ki sauke, ki samu cooler ki zuba sai a kaima mai gida akan dining table, ki gyara komai...```


Toh a haka dai su, zulai suka ida aikinsu suka shirya komai, nan Momy ta koma daki ta shirya, ta koma side din Hajiya suka taho ita da Ammie suka zauna sunata fira...



"Wlh Ammi tunda Sadiq ya tafi duk na shiga damuwa ina ta missing dinshi, ai dole daman kice haka tunda kece kika shagwaba shi daman zakiyi missing dinshi...

Suna cikin magana sai ga Dady ya shigo nan ya shiga ya danyi wanka ya fito suka ci abinci sannan kuma suka cigaba da yin fira....


A kwana a tashi su Nana suna ta yin terminal examination din su, yanzun zasu shiga SS2 sauran sati biyu su gama exams...


A bangaren Khalid kuwa.....





*Share and* *comment*


πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•
*NANA JAWAHEER*
πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•

*STORY AND WRITING BY*
*Jameelah A Belloh*
*(Jameey)*


*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–Š*
*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.πŸ€™πŸ»```

----------------------------------------


*BISSIILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*


Page 1⃣2⃣



Khalid tafiya yake amman baki daya hankalin shi da tunanin shi yana gun Nana, ya rasa yanda zai yi ya shawo kanta, Khalid yana magana kamar haka...
"Tabbas ina sonki Nana jawaheer, kuma ke ma sai kin soni, sai kin man son da ba ki taba yi ma wani da' namiji shi ba a rayuwarki,ni kuma zan nuna maki so na gaskiya, zan saki farin ciki na har karshen rayuwarki....


Haka dai Khalid ya kama maganganun shi har ya iso gida, ya dan na ma gate man horn, ya zo ya bude mashi gate yana yi mashi

Please Login or Register in order to submit comment