Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sannu da zuwa, amman Khalid bai ansa mashi ba, saboda da baki daya hankalin shi baya jikin shi, sai gate ma,yace, "Oh ni Abdu yau komai ke samun yallabai Khalid? Nayi mashi magana bai yi man magana ba, bayan kuma ba haka ya ke yi man bah, dan yallabai Khalid shi mutun ne, mai mutunta na gaba da shi, bai damu da talaucinka ba, dan shi mutun ne mai son tallaka da kuma tausayin su...


"A haka Khalid ya shiga cikin parlo ya tadda Fulani zaune ta na Kallon Manara TV, suna shirin manyan gobe," NOOR, lafiya na ganka ka shigo gida kamar wanda wani abu ke damunshi? (Da yake Fulani cema Khalid Noor suke, dan shi daya Allah yabasu)"Fulani ina cikin matsala babba,"matsala kuma Noor? "Eh matsala Fulani, ya fada yana kwanciya bisa AIM dinta, "wace kallar matsalarce wannan? Pls Noor tell me?


"Fulani, naga wadda nike so,"Alhmdulillah, Noor wannan shine matsala? Bayan kasan nafi kowa son na ga kallar wannan ranar da zaka ceman ka samu wadda kake so, kai Alhmdulillah, Allah na gode ma Allah,wacece wanann yarinya haka mai sa'a? Sannan kuma wace kalar matsala ce kake ceman?


"Hmmm bari Fulani, sunan ta *NANA* *JAWAHEER* , tana a kofar kwaya, Fulani ina sonta sosai, amman kinsan matsalar? "Aah Noor sai ka fadi man kuma kai nike ji ina sauraranka, "matsalar daya ce Fulani, matsalar kuma babba ce, Fulani har yanzun bata bani izinin da ya ka mata na bai ya na mata kalar son da nike mata, Fulani taki bani umarnin da ya dace ta bani, Fulani na kai ki karshe ta ceman kar na sake zuwa wajen ta....


"Inalillahi wa'in na alai hi agarin ya haka ta faru dakai? Noor ai nasan ba macen da zaka ce kana so tace ba bata sonka!!!


"Uhmm Fulani kenan, to banda Jawaheer, ita Jawaheer yarinya ce mai aji da sanin ya ka mata, Fulani,, Jawaheer yarinya ce mai natsuwa da kuma tunani da hangen nesa, tana gudun karta tsaya kulani Babanta ya yi mata fada, may be daga karshe ma a buge ta a gida, dan na fahimci Jawaheer tana shan hukuba a wajen kishiryar Mamanta, saboda kafin na tsada Jawaheer sai da nayi dan karamin bincike a kanta, kuma na gani da ido da muka tsaya...


"Fulani har da wannan yasa nike kara bala'in Son Jawaheer, amman zan cigaba da bibiyarta har sai ta bani lokacinta munyi magana kafin naje wurin mahaifinta da maganar inason diyarshi da aure, ko ya ki ka gani Fulani?


"Haka ne Noor kayi tunani mai kyau, ni kuma zan taya ka da addu'a Allah ya baka nasara, "Amin ya Allah,"sannan Noor ina son ka kula da ita sosai, saboda nima Allah ya dauraman sonta da kuma tausayinta tun kafin nasan cikakken labarinta, yanzun tashi kaje kaci abinci, "uhmm Fulani mai kika dafa mana? "Tuwan shinkafane da miyar egusi, nasan kana son tuwo shiyasa na yi shi yau, tunda Abban ka yayi tafiya, "haka ne nagode Fulani na...


"Nana! Nana!! Nana!!!, wai Nana wanann wani kalar tunani ne har haka ina ta yi maki magana amman kin kyalen? haba Nana, "Zee ke dai kawai ki kyaleni ki ganni kawai, "saboda da mai zaki ce haka Nana? Gaya man mai ke damunki? Mai ye matsalarki Nana?


"Zee ina cikin matsala da tashin hankali, Zee ina fama da matsalar su Inna, amman yanzun ga wata tana neman kunno man kai, " gaya man dan Allah Nana, wallahi kin sani cikin rudani fa, "Zee wani mutune, "wani mutun kuma waye shi Nana? "Eh wani mutun Zee, wani mutun ne yace yana sona, "sai kika cemai mai ke kuma? "Zee ya zan ceman in ba nace ya kyaleni bah, "ya kyaleni fa kika ce Nana? "Eh Zee cewa nayi ya kyaleni, kuma ya fita harkata..


"Ikon Allah, Nana yaushe kika fara hauka? Ehyyeh Nana, shin Nana baki son ki huta da wannan bakar wahalar ta Inna? Ko kuma kema baki san ki ganki cikin kwanciyar hankali kamar yanda kowa yake? "Aah duk ina son nagan ni cikin wanann abubuwan da kika lissafo man, Amman sai dai, "Amman sai dai mai Nana, ai Nana baki da wani reason ma korar samari, ko dai har yanzun kina kan bakarki na son cigaba da karatu?


"Eh Zee, inason na cigaba da karatu, amman na san abunda ba zai faru ba ne, nasan aure kawai Baba zai yi man Zee, Nana ta fada tana yi ma Zee kuka...


"Yanzun dai yi shiru Kawata, ba kuka zaki yi ba , kawai ma fita ya ka mata mu nema, "wata kallar mafita Zee? Kin san yanda muka yi Baba jiya? To da ya dawo Inna ce mai tayi ta gan ni da wani kato, wai yana kama man hannu, "To shi ya Baba yace Nana? "Hmm ya fa, ai yarda yayi ya hau yi man fada...

*************************
*NEW DELHI INDIA*


Hello, morning Dad, sadiq ne ki yin waya da Dady,, "Morng too Son,fatan ka tashi lafiya? "Lafiya Lau Dad, Dad wallahi duk nayi missing din ku, ji nike kamar na dawo gida,nace na fasa karatun Dad, "ai Son haka karatu yake, sai anyi hakuri sannan ake ganin ribar shi, "haka ne Dad, Allah dai ya bamu sa'a, "Amin Amin....


"Yauwa Dad, kaje kun gaisa da Abba ne? "Aah ban kai da zuwa ba da yake nayi wata yar tafiya zuwa Abuja nayi kwana biyu, jiya Allah yayi nadawo, "To Dad, fatan dai kadawo lafiya? "Lafiya lau Son, da man Son mun yi magana da Hajiya, a kan dauko Nana ta dawo gida da zama, "yauwa Dad ya kuka yi da Hajiyar? "Eh ta yarda amman tace ba kai tsaye zan yi mashi maganar bah a hankali za'a yi mashi maganar mu gani ko Allah zai sa ya yarda...


"To shikenan Dad, Allah yasa ya yarda, "Amin, Son yau baka zuwa lecturess ne? "Aah Dad yanzun na gama shirin zuwa, "To shikenan bari na barka karka makara, "Dad dan Allah ka gaidaman da su Hajiya, da man jiya ai munyi waya, amman a sake gaida man da su, "To shikenan, dan Allah Sadiq ka dage kayi karatu sosai, "Insha Allah..


Nan Sadiq ya shirya ya dauki hanyar makaranta, yana shiga ya wuce lecture hall, nan ya hadu da Lukman suka gai'gaisa bayan sun gama gaisa wa lecturer din yazo ya yi masu abunda yayi masu, kowa ya fita ya gama gaban shi..


Amman Sadiq da Lukman suka nufi capateria domin su samu abunda zasu sama cikin su, bayan sun gama yin ordering din chips and egg rolls, suna cikin ci suka ji an ce masu hello...


"Hello, haba sugar ya ina maka magana, amman kayi shiru ka kyaleni, a she nan kake yin karatun? "Hy wai ke wata kalar mata ce? Mai ki ke so nayi maki? "Ina son ka bani dama"dakata dan Allah, zaki tashi ki ban guri ko kuwa sai na ba ta maki rai? "Ba inda zani har sai ka bani lokacin ka, na gaya maka kallar son da ni ke yi maka..


"Haba baiwar Allah, ai ya kama ta ki bi a hankali, Lukman ne ya ke cema Salma haka, "Taya zan bi hankali, kasan ko wani kallar so nike yi ma abokinka? Dan Allah bawan Allah ka tai ma ke ni, ka shawo man kanshi, wallahi dagske ina son shi, auren shi nike son nayi...


"To shikenan, zan yi maki iya bakin ko Karina, "nagode sosai, amman ban tambayi sunanka ba, karki damu, suna nan Lukman, kai fa, "Salma, "nice name, "to tnx,zan iya samu contact din ka, nan dai Lukman da Salma su kayi exchange din number sannan Salma ta kama gabanta, da anjima za su yi magana..


"Haba Sadiq , ya yarinya kamar Salma tana yi maka magana amman kayi banza da ita, ko dai bata yi maka ba? Na ga dai kamar yarinya tana da natsuwa da kamun kai..


"Aah Lukman, tabbas Salma yarinya ce wanda za'ace ana so, amman ni Sadiq na sadaukar da soyayya ta ga yar uwata, Lukman ba nida wanda nike So nike jin son aurenta kamar *NANA* *JAWAHEER* , ina son Nana jawaheer, son da ko nima kai na ban son ya zan fasalta maka shi ba, ina son Nana, sannan kuma ina tausayin Nana jawaheer, kaga ko ba yanda za'ayi na iya hada soyayyar Nana da wata ba, domin maganar gaskiya ba zan iya yin adalci a tsakanina su ba..


"To shikenan, Allah yasa haka shi yafi alkhari, amman dan Allah, ka daure ka gaya ma Salma wanann maganar, "Aah Lukman kawai ka gaya mata pls, "to shikenan zan duba..


*************************
*NIGERIA*






Share and comment pls


πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•
*NANA JAWAHEER*
πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•

*STORY AND* *WRITING BY*
*Jameelah A Belloh*
*(Jameey)*


*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–Š*
*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.πŸ€™πŸ»```

----------------------------------------


*BISSIILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*


Page 1⃣3⃣


*NIGERIA*


"Nana yanzun kina nufin Baba ya yarda da maganar Inna? "Eh Zee ya yarda, amman na san yau in na sake bashi hakuri zai hakura, "yauwa yanzun naji batu, har hankalina ya kwanta, ki san yanda zamu yi yanzun? "Aah Zee sai kin fada..


"Yauwa, kawai yanzun kina koma gida kiba hakuri, in dai ya hakura, Insha Allah komai zai zo mana da sauki Insha Allah, "To shikenan Allah yasa sa Kawata, "Amin ya Allah, yanzun dai tashi mu tafi gida, sai gobe mun hadu in za'a bada hutu, sai ki gaya man yanda kuka yi da shi Baba din, "ok ba damuwa Zee...


Nan dai su Nana su tafi gida suna kara tau'tau nawa a kan maganar da su kayi da yanda zasu shawo kan matsalar da take ciki..


Bayan Nana ta shigo gida, ta tadda Inna tana ta masifa wai tayi zaman ta makaranta, ta barta da aiki yana niyar kashe ta, bayan kuma Khadija tana gida ba inda taje, amman bata taya Inna aiki ba..


Da yake Nana ta fara gajiya da abunda Inna keyi mata sai ta cenmata"Haba Inna sai kace ni daya ce a cikin gidan nan, da zaki ce dole sai ni daya zanyi maki aikin gida, naga dai ga Khadija can zaune tana zaman banza, ita baki ce mata, ta barki da aiki gida ba, amman sai ni, daya ke ni bani da gata balle galihu ko Inna? Kuma naga dai ai makaranta naje ba wani waje ba....


"Ehyeeh!!! Nana ni kike gaya ma wannan maganar Nana? Ikon Allah, ai ko dole yau naci ubanki cikin gidan nan, "ban gane zaki ci ubana ba Inna? Daga fadin gaskiya sai bugu? To wallahi ban tsayawa ki kama buguna ba, kamar wata jakka ba a cikin gidan nan (To fa jama'a yau ga fa Nana ta fara rama abunda Inna ke yi mata) "Nana haka kika ce ko? "Eh inna haka nace, haba wallahi na fara gajiya da cin kashin da kike yi man a cikin gidan nan, ni da gidan ubana amman an hanani sa'ida a cikin gida ubana to na gaji...


Nan fa Nana ta gama yin rashin kunyar ta cikin gida,,, da ta ba Inna haushi da yawa, ta ko kama ta tai ta bugu sai da tayi mata jan bugu, dan ma ita Nanar ta samu ta ruga tana kuka, bayan ta huta ta taso ta fara yin aikin gidan bayan ta gama sai ga Malan nan ya dawo, Nana taje ta bashi hakuri..


"Baba dan Allah kayi hakuri akan abunda ya faru jiya Insha Allah ba zan sake ba, "to shikenan Mamana na hakura, nidai bani son tsayawa a bakin hanya, ki ce mai ko ma waye shi, ni nace kuringa shigo wabko da cikin zaurene, ai kinga yafi kan hanya ko Mamana? "Eh Baba haka, kuma Insha Allah zani kiyaye, "To Allah yasa dan Allah Mamana ki kula da kan ki da kuma mutuncin ki kanji, "Insha Allah Baba, "To tashi ki tafi, Allah yayi maki albarka "Amin Baba...


Washe gari da safe Nana ta tashi tayi aikin gida kamar yanda ta saba sannan tayi ma Inna sallama ta tafiyar ta makaranta saboda yau ake yin hutu kuma harda result zasu ansa, saboda hutun third term ne daga shi kuma zasu shiga SS2(aji biyar) , anyi hutu anba kowa result din shi, wannan term din Nana ita tayi na biyu, Zee kuma tayi na hudu, anba kowa result din shi wanda yayi kokari yana murna, wanda kuma yaga sai a slow yana ta bakin ciki, Allah yasa muga da kyau duniya da lahira Amin..


"Nana ya kuka'yi da Baba? "Yayi hakuri, nan dai Nana ta gaya ma Zee yanda sukayi da baba, nan itama Zee din ta fara ba ma Nana shawara kamar haka..


"Ni dai Nana a gani na ya kama ta kiba wanann mutunin dama kije da mai zo, a haka har Allah ya hadi ki da wanda yake sonki tsakani da Allah kema haka kana sonshi, amman nidai a nawa tunani..


"To Zee Insha Allah zan ba shi wannan damar, zanyi kokari naga nayi yanda ya dace, sanann gaskiya Zee na gaji da abunda Talatu ke yi man a cikin gidan dan haka na gama hakuri, in dai tayi man sai na rama, na gaumace in na rama ta bugeni, "ai tuni nike nuna maki ki ringa ramawa inta ga kina ramawa zata fara jin shaikar yi maki wani abun, "ai kuwa zan ringa ramawa..

*************************
*BANGAREN KHALI*


Fulani ina kwana? "Lafiya Lau Noor, ka tashi Lafiya? "Lafiya Lau, yauwa bari nayi breakfast kin san bani bani wasa da cin wanan abincin naki Fulani, "To yi maza ka ci ka tafi karka yi letting, dan na lura duk randa kake da lectures din 8 kana yin letting, "To Fulani ban san mai yasa suka bani lectures din 8 ba, kuma ni na gaji da koya ma level 1&2 gaskiya saboda basu cika hankali ba, amman zan cigaba da hakuri kawai Fulani, "To ai da man Noor hakuri zaka yi ai, Allah dai ya baku ladar Amin...


"Yauwa Fulani, daga umyu zani wuce kofar kwara wajen Jawaheer naga ko zani dace, "To shikenan Noor Allah yasa a dace, "Amin ya Allah byee..


Khalid yana isa umyu ya shiga theater ya fara yin abunda ya kawo shi, yana daukar su BIO 1201(palant, da yake shi Khalid yafi iya plant biology shiyasa yake daukar su plants shida DR WAGINI, su ke daukar PLANT BIOLOGY), bayan ya fito 8-10 ya sake shiga 2-4 yayi ma level 2 BOT 2201(SEEDLESS PLANTS) shi da DR UMAR tare suke daukar level 2 course din, bayan Khalid ya gama ya wuce unguwar su Nana..

*************************

*BANGAREN SU DADY*

Dadyn Aiman, wai ya ku kayi da Yaya Adam da kaje shekaran jiya? "To Alhmdulh za muce abun yazo cikin sauki mun gaisa sosai da sosai dan ji nayi ma kamar kar mu rabu, "Allah ai haka abun yake, balle an kwana biyu ba a hadu, Allah dai ya yakara daukon zuminci, "amin ya Allah, kuma jiya na sake bi yawa mun gaisa, amman yau nike son na sake zuwa muyi maganar dawowar Nana nan gidan, "to Allah yasa dai ya bada ta, "Amin ya Allah, bari ki ga na tashi na gaishe da Hajiya mukara yin wannan maganar ta Nana, "to a dawo lafiya, "Allah yasa, "Amin...


"Assalama Alaikum "Amin wa"alaikumus sallama, "Hajiya ina kwana? "Lafiya Lau Sulaiman, An tashi lafiya? "Lafiya lau, "Yaya Sulaiman ina kwana? "Lafiya Lau Khadija, an tashi lafiya? "Lafiya lau..


"Daman Hajiya nazo na gaya maki yanzun zan tafi gidan Yaya Adam, ya kika gani? "To shikenan Sulaiman lafiya lau, kaje kuyi magana, Allah ya dauraka a kan Yayan naka, "Amin Hajiya ni dai na tafi to shikenan a dawo lafiya, "Allah yasa, Amin..


*************************

*NEW DELHI INDIA*


Yanzun dai tashi mu tafi gida, Lukman ke cema Sadiq haka, "To shikenan, kawai dai ina tunanin Nana, ka san na gaya maka cikin halin da na barta, wallahi Lukman ina tsoron Abba yace zai yi ma Nana aure kuma ba da ni ba, "ai kai Sadiq kana da matsala guda daya, matsalar kuwa ta ka bari har ka taho nan baka gaya ma Nana abunda ke ranka ba, "What! Kana nufin na tsaya a gaban Nana na fada mata ina sonta? Kana son raini ya shiga tsakani na da ita kenan, Allah ya sawaka man wallahi ko, "Yanzun Sadiq kawai fada ma Nana kana sonta shine ya zama raini? "Eh shine, babban raini ma Lukman, gaskiya ban shirya daukar raini ba, kasan su mata da zaran kace kana son su, to sai su ringa raina maka Wayau, ni kuma gaskiya ba zan dauka ba..


"A gaskiya Sadiq in ko kace haka zaka yi, kasa a ranka zaka rasa Nana, saboda in dai ka bari wani ya riga ka shiga cikin zuciyarta to za ka fa samu matsala, "haba Lukman ya kake kallar wannan maganar, ni nasan Nana zata soni, kuma duka duka nawa Nana take da har wasu zasu ce suna sonta bata tafi 17yrs ba fa, "kai dai Sadiq kasan hausawan na cewa raina kama ka ga gaya, dan haka kaje kayi tunani akan wannan shawara da na baka..


"To shikenan Lukman, zan buda, ya kama ta mu tafi, kaga mun kusa fara exams,ina fatan ka fara yin karatu? "Eh Alhmdulh na fara, Wanda bani gane ba na ajiye su zan shigo ka yi man tutorial, "to shikenan sai ka shigo, "Yauwa Sadiq, ni fa wallahi ina son Salma, dan haka zan yi mata bayanin komai, sanann na gaya mata ina sonta, amman ya ka gani? "Eh haka yayi kayi mata bayani, Allah ya taimaka, "Amin Abokina bye..


"Hello, Salma, Lukman ne,"hy Lukman how are you? "Am fine, and you, "fine, Alhmdulh, "Yauwa Salma ina son mu hadu gobe zamu yi magana da ke, "To Allah ya kaimu lafiya, "Amin..


Washa gari Lukman ya shirya ya shiga school, saboda basu da lecture dan su a week sau ukku suke yin lecture, dan maganar da xasuyi da Salma ta fidda shi saboda mahinmancinta, bayan su gaisa su kayi ordering din coffee only, nan fa suka fara magana..


"Da man Salma a kan maganarki ce da Sadiq, munyi magana da Sadiq ya gaya man komai, "Yauwa dan Allah Lukman mai ya ce maka? Nan fa Lukman ya gaya ma Salma yanda Sadiq ya gaya mashi ya kuma bata hakuri, Salma ta fahimta, taji ba dadi amman sai ta barma Allah komai, sai Sadiq ya fara maganar yana cewa..


"Ni fa gaskiya Salma in kin bani dama Ina son na maye gurbin Sadiq a cikin zuciyarki, amman in kin amince man,in kuma baki amince ba, wallahi ko Salma bakomae zan yarda da kaddara na kuma barma Allah lamarinsa...


"To shikenan Lukman, amman dan Allah ina son kabarni nayi tunani na wani dan lokaci Insha Allah zanyi tunani, sannan kace ma abokinka nagode daya fiddo ni a cikin duhu, Allah ya barshi da mai sonshi, "To Salma nagode ina sauraran ansarki, "To Lukman Insha Allah, byeee..


*************************

*NIGERIA*

"Nana dan Allah ya ka mata ki tsaya ki saurareni mana, "To naji, ammann ka shigo daga ciki mana, "na shigo ciki kika ce Nana? "Eh ka shigo, bayan Lukman ya shigo cikin zauren gidan su Nana, Nana ta kawo mashi ruwa ya sha, bayan ya yasha ruwan, ya fara yi ma Nana magana..


"Jawaheer, wallahi ina sonki da gaske, ina yi maki son gaskiya so na Amana, ki bani dama na nuna maki irin son da nike maki..


"Kafin nan ina son na san sunanka, "ok suna na *KHALID ADBULRAHAM,* "Nice Name, Khalid na san kana sona, amman ina son ka bani wani lokaci zanyi tunani Khalid..


"To nagode Jawaheer, Allah yasa naji alkhari,"Amin ya Allah, Khalid to ni zan shiga cikin gida tunda mun gama maganar, "kafin nan Nana, dan Allah ki bani number ki, "sorry banda waya, "amman Nana, "da kata Khalid mubar maganar waya pls, "To shikenan Nana, sai anjima..

*************************
*BANGAREN SU DADY*


Bayan su Dady sun gama gaisawa da malan Adamu, yake yi mashi bayanin abunda ya kawo shi wajen shi,,yana neman alfarman ta biyu kenan...


"To Sulaiman naji abunda yake Tafe da kai, amman dan Allah Sulaiman ina son ka bani dan lokaci zanyi tunani a kan baka Mamana, in na gama yin tunani da kai na zan yi maka magana, "to shikenan Yaya Allah yasa muji alkhari, "Amin...






TO FA JAMA'A KUNJI WATA SABUWA FA WAI INJI AN CACA... .


SHIN WAI SALMA ZATA AMINCE DA BUKATAR LUKMAN..


SHIN AYYA KUWA SADIQ ZAI GAYA MA NANA JAWAHEER YANA SONTA.......


WAI NANA JAWAHEER ZATA AMINCE DA BUKATAR KHALID...


MALAN ADAMU ZAI YARDA DA BUKATAR KANIN NASHI SULAIMAN KUWA... ...


TO GA KUMA WATA SABUWA NAN, NANA JAWAHEER ZATA CIGABA DA HAKURI DA INNA TALATU...


KHADIJA ZATA CIGABA DA YI MA NANA JAWAHEER RASHIN KUNYA...


DUK WANNAN ANSO SIN SUNA NAN GABA A CIKIN LITAFFIN NANA JAWAHEER IN SHA ALLAH NAN DA BAYAN AZUMI ZAN CIGABA DA KAWO MAKU CIGABAN WANAN LATAFFIN..


ALHMDLILLAH, ALLAH ABUN GODIYA, ALLAH YASA KAMAR YANDA MUKA GA WANNAN RAMADAN LAFIYA, ALLAH YA NUNA MANA KAESHENSHI LAFIYA..



ALLAH MUNA ROKANKA KA KAREMU DAGA SHARIN WANNAN ANNOBAR TA CORONA VIRUS, ALLAH KA KAREMU DAGA SHIRIN ZAMANI, ALLAH YASA MU CIKA DA KYAU DA IMANI..



YAU UWA INA YI MANA FATAN ALLAH YASA MUGAMA AZUMIN NAN LAFIYA, YASA KUMA MUYI SALLAH LAFIYA...



ZAKU JINI INSHA ALLAH NAN DA BAYAN SALLAH INSHA ALLAH..



DUK WANDA TASAN NAYI MATA LAIFI KO NA BATA MATA A WAJEN WANNAN LATAFFIN DAN ALLAH INA MAI NEMAN AFUWARKU, NIDAI NA YA FEMA KOWA, NIMA INA NEMAN ALFARMAN A YA FEMAN DAN ALLAH...


ZAKU GA CIGABAN NANA JAWAHEER BAYAN SALLAH INSHA ALLAH






DAN ALLAH KU RINGA YI COMMENT PLS SANNAN KUMA KUYI SHARE PLS...




πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•
*NANA JAWAHEER*
πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•

*STORY AND* *WRITING BY*
*Jameelah A Belloh*
*(Jameey)*


*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–Š*
*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.πŸ€™πŸ»```

__________________________________


*BISSIILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*





```Alhmdulh Allah na godema ka da ka kai mu wannan lokacin, fatan mu dai Allah ya anshi ibadanmu baki dayan mu☺️```

Page 1⃣4⃣







*NEW DELHI INDIA*


"Lukman , "Naam Sadiq, ya kuka yi da Salma? "Uhmm Salma kenan manyan mata, munyi magana ta fahimta, ta fahimceni ni ma kuma na fahimceta, saboda ta gane kana da wanda kake so, kuma ta yarda da kaddarta, "nifa ba wannan nike tambayar ka ba abokina, ina san naji shin Salma ta amince da bukatarka?


"Eh to, ta ce man zata yi tunani, na bata wani lokaci, "kaji matsalar! matsalar mata kenan wallahi sai kazo masu da magana mai anfani amman sai su mai da abun wasa, shiyasa na ce maka bani iya ga yama mace ina sonta, saboda wannan dalilin..


"Yanzun Sadiq mai ye laifin Salma dan tace na bata wani lokaci? Wai Sadiq mai yasa kake haka ne, ban san sai yaushe zaka sauko daga wanann kudirin naka ba, kuma wallahi kaji nace maka wallahi ko sai kace ma mace kana sonta, kai ba ma iya kana sonta kawai ba har kuka sai kayi ma soyayya, kuma zaka ce na gaya maka, In dai

Please Login or Register in order to submit comment