Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a rana kafin azumi,azumi na zuwa dani daina yin posting insha Allah 🀝🏻*

*Ga mai magana ko tsokaci yayi man magna ta da wannan number 08160508316 banda kira pls*

*Share and* *comment* 😍
πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•
*NANA JAWAHEER*
πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•




*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–Š*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.πŸ€™πŸ»```

--------------------------------------


*Story and writing* *by*

*Jameelah A Belloh*
*(Jameey)*



*DEDICATED TO NANA* *JAWAHEER FANS GROUP* πŸ’”πŸ˜˜



*Inayin ku irin totally din nan domin gaskiya comment dinku yana sani cikin nishadi sosae da sosae, ba abunda zance face Allah yabar kaunaπŸ€“πŸ€—*


*BISSIILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*



Page0⃣6⃣



Sadiq yana zuwa wajen Daddy, ya zauna ya gaishe shi...


sannan yace"barka da hutawa Daddy anyi sallahr lafiya?


"lafiya lau Son! Ya gajiyar jiya kuma?"gajiya tabi jiki Daddy....


"toh alhmdulh"Daddy daman kace kana son kayi magana dani yau indan anfito sallahr i'di?



"eh hakane Son, daman a kan maganar da mukayi ce da kana makaranta akan kana son ayi maka walima inka dawo.....


"eh hakane Daddy, "yauwa Son, an fasa yin walimar......


"Daddy an fasa fa kace?


"Eh dan albarka an fasa yin walimar, saboda Hajiya tace bata yarda ayi walimar ba,saboda haka anjima kasa mai ni wajen *NI'IMA MOTORS* , zaka zabi motar datayi maka na saya maka dan naga wannan motar da kake hawa ta tsufa sosai....


"toh shikenan Daddy nagode,Allah yakara bude da nisan kwana, "Amin Son.......

"Nana! Nana! Nana! "Na'am Inna"au she yanzun kika gadamar ansa kirana ko?


"Aah Inna ba haka bane ba,"in ba haka bane ba to ya ne yar iya?


"Inna wanke-wanke nike shiyasa,yi hakuri Inna dan Allah.....


"ke ni taso in ai keki gidan Lami, tunda ba surutu nasa kiba,kije ki kaima mata wannan kudin, ki ce mata dubu hude ne sauran dubu shidda suma insha Allah na kusa kawosu...

"To Inna amma,
wanke_wanken fa wa zai ida?


"Ke yiman shiru mutunniyar kawai tashi kije aiken dana aike ki kafin naci ubanki kodan kinga ina binki sannu..


"Yi hakuri Inna, ni natafi, "kuma kiyi sauri ki dawo,tunda bani kika ajiye ba nayi maki saura aikin ba, dan ubanki, haka dai Nana ta tafi kaima Lami kudin adashen Inna,tadawo ta cigaba da sauran aikin gida..

Yau take sallah amman Nana ko kofar gida bata fita bah har sai da Inna ta aiketa sannan taga waje..



"Innalillahi, wa'inna'alaihirajiun, Wayyo Allah, na bani, wayyo ni Nana, haka nana takama cewa tana kuka kamar ranta zai fita daga jikinta....


"Ke Nana lafiyarki zaki kama yin man ihu a cikin gida?..

"Dan ubanki sai kace wanda aka aiko ma da sakon mutuwa, shegiyar yar iska wulakantataciya...


"Inna dan Allah kizo ki taimakeni, wallahi na yanke hannu da wuka gun yanka albasa Inna, na bani jinina zai kare...



"Yo yakare mana sai a yi yaya ni daman jinin naki ya kare dan ubanki, uban kowa ma ya huta in kika mutu shegiya yar banza...


"zaki tashi ki cigaba da yin yankar albasar ko sai na ci ubanki sannan, haka Nana ta tashi ta cigaba da yin aiki, da taga jinin ba mai tsayawa bane sai ta sama wajen gishiri, tana kuka tanayin aiki, itace bata zauna ba har sai da dare yayi ta zauna, taje sanya abinci ta tadda abincin yakare, datayi ma Inna magana sai tace,"ai baki da kaso yau, dan ubanki, dan na ba Kawayen Khadija da suka zo dazun, haka Nana tayi hakuri ta kwanta tana jin yunwa gakuma jinin da ta fitar a jikinta gakuma radadin ciwo duk sun hade ma wajen daya...

Hmmm rayuwa kenan Allah sarki Nana😭😒.....


"Good morning Mommy,"Morning Son, how was your are night,"am fine Mom,Mom wai ina Aiman ban ganshi bah tunda na tashi?


"Kasan Aiman yana wajen Hajiya tun safe, kasan a can yake yin breakfast dinshi"to Daddy fa?


"Shima yafita tun safe, saboda yanada meeting yau a office, kuma yace nace maka yana jiranka...


"To shikenan nima bari naje na gaida su Anni,"Aah breakfast din fa, mai yasa baka son cin abinci wai Son?..


" ko kanason raina ya baci ne?....


"Aah Mom ba haka bane sha tea dana tashi ne shiyasa, am very sorry Mom, but am now felling hungry,that is why Mom,sorry pls, love you tooo Momyna...

Hmm Son kenan shikenan dai......


yanzun tashi ka tafi ka gaida su Hajiya ka wuce wajen Daddynku nasan yanzun sun kusa fitowa meeting din, all right Mom byeee Mom,I miss you Mom,"missing you to Son, but Son pls take care about ur self pls,"ok mom insha Allah...

ya shiga ya gaisa da su Anni,"Anni ni na tafi Daddy na jirana...


"To Allah yayi maka albarka...



"Amin Anni, Ilove you too Anni, "love uh more Sadiq, tashi kaje kasan Yaya baya son jira, "to bye Anni....



Sadiq ya isa wajen *NI'IMA MOTORS* yana zuwa, Daddy ma na zuwa suka isa a tare, manajan company ya tarbaisu, tarba ta mutunci domin tunda yaga Daddy yasan kudi sun zo, balle ya ganshi da shalelen yaron nashi, shiyasa yarasa inda zai ajiyesu, bayan sun gama gaisawa Daddy yafara magana kamar haka,"da fatan mun samai ku lafiya Alhaji Bala?"lafiya lau Alhaji Sulaiman, ya gida da mutanen gida?..


"Duk Alhmdulh Suna nan lafiya lau,"to Masha Allah naji dadin haka,"Alhaji ina wuni,"lafiya lau Sadiq yan makaranta, ya makaranta? angama karatu lafiya?"Lafiya lau Alhaji,"to Masha Allah inada niyar zuwa gida nataya ka murnar kammala karatunka, Allah bai bani dama b...


"Laa bakomai Alhaji, hakan ma mungode...


"Daman Alhaji Bala zuwa mukayi mu da Son ya zabi mota zan bashi gift din kammala karatun na daya....


"To! to! aikom kun taka sa'a saboda jiya aka kawo new desingner masu kyau da kuma qualities,"to shikena....



" kai Son shiga ka zabi wanda tayi maka mana, nan Sadiq ya shiga ya zagaya company har yaga motar da datayi mashi mai suna *AMG* *MERCENDIC 2019* "Daddy wannan tayiman!!



"ka tabbata tayi maka?"Eh Daddy,"toh shikenan,"yanxun Alhaji Bala takai nawa wannan moto din?..

"Ai Alhaji duka duka *THIRTY MILLIONS* take bawani tsada ne da ita bah....



"Ok shikenan bashi key din yanzun zan turomaka kudin ta account dinka insha Allah, tunda daman on ready inada account number dinka.....


nan take Alhaji Sulaiman yayi mashi transfer din kudinshi...


"Daddy nagode Allah yakara bude,"Amin ya Allah, sai magana ta biyu.....



"kawai zaka yi joining *MSC(MASTERS* *DEGREE)* din ka a *INDIA* next month flaying dinku zai tashi insha Allah....



"Toh nagode Allah yakara bude,"Amin, in kadawo kayi services dinka baki daya, bayan sun gama yin maganar kowa ya hau matarshi suka kama gabansu, sunbar zasu aiko drive yadauki new moto din ...

A wajen Nana Jawaheer kuwa.....











*Yawan comment dinku* *yawan typing* 😜


πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•
*NANA JAWAHEER*
πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•




*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–Š*
*MWA* πŸ–ŠοΈ

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.πŸ€™πŸ»```

--------------------------------------

*Jameelah A Belloh*
*(Jameey)*



*DEDICATED TO* *MEENA DARMA*



*BISSIILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*




Page0⃣7⃣







Nana ita ce bata ta shi daga bacci ba sai da lokacin sallar asuba tayi,ta tashi tayi raka'atul fijir, sannan tayi sallah,bayan tagama sallah tayi azakar din da tasaba yi kullun dakuma karatun qur'ani mai girma,tana gamawa ta dan kwanta kan yar katifarta,da niyar ta dan kara hutawa kafin gari ya waye, tana cikin bacci barawo da ya saketa taji ana watsa mata ruwan sanyi! Inna, tana cewa,"wato har lokacin koma wa bacci ke gareki ko ke ga zara gwanna wanda tafi kowa ko?.....





"Innalillahi,wallahi Inna yanzun na samu na dan kwanta, kuma naga gari bai waye ba,"eyyeh gaskiya Nana nan gaba kadan buguna zaki fara yi da kanki naga alama, haka Inna takama yin Sababi,Nana kuma nabata hakuri, tana kuma yin aikin gida, shara ta fara yi sannan wanke-wanke sai ta sa sanwa, tana gamawa tace ma Inna,"Inna ni zan tafi chemist din yaro naje ya dubaman wannan hannu don gaskiya jiya bai barni nayi bacci ba sosai,"ba inda zaki je ragguwa kawai yar wannan yankar shine zaki jema wani chemist yar nema kawai da ke ,je ma ki debo wanki kiyi shi tunda naga alama aiki kike so kiyi a cikin gidannan, "Inna wanki fa kika ce?...




"Haba Inna yakamata ki dan tausayaman koda sau daya ne Inna, wallahi bakiji yanda nike jin zafin wajen ba hakuri kawai nike har nasamu nayi wannan wanke-wanken Inna,"yanzun kawai kice bakiyi basai kin ka kawo man wata yar karamar matsalarki bah, kuma ko kiyi shi a cikin girma da arziki ko ki yishi da masifa da bala'i, kinji ni ko baki ji ba,"naji Inna,"yanzun, zan tashi nayi ma, haka dai Nana tagama shan wankin Inna da yaranta, sannan tayi wanka da sallah ta kuma ci abinci......




"Momyna,am back,"Son har an dawo kenan?,"eh Allah ya yarda Momy,Momy close ur eye pls,"but Son,"stop Momy,don't say anything pls, just close ur eye,"ok Son am close,"gud Mom, Mom don't open ur eye until I count THREE,Mom I start, one, two, three,ok mom open and see what's surprise for,"woow,it very look so beautiful,and it's so expensive Son, Son congratulations, gaskiya Daddynku yayi kokari sosai, may Allah blessed you my Son,"thank You very much Mom,"Mom bari naje na kira su Anni suzo su gani susa albarka,"ya dace gaskiya....



"Assalama Alaikum,"Amin wa'alaikumus salaam,"Sadiq har andawo kenan?...


"Eh Anni, I real miss uh Anni, yana fada yana kwantawa a saman cinyarta, wai Anni ina Aiman yake ne duk yau I don't see him fa Anni,"yana nan, kasan shi da son ball to ita yake yi tun dazun,"Hajiya fa?,"tana daki yanzun ta tashi tana son hutawa, aiko dai fitowa za tayi ko,"Aah baka isa ba ka matsama uwata ba, kai wa ya matsa ma taka uwar, eyyeh?, Aah Anni wani abu zan nuna maku fa....



"To shikenan,nan yashiga rest room din Hajiya,"tashi ga mutuwa nan,"gidanku waya ce maka ina tsoron mutuwa?....




"Ai mai tsoron mutuwa shine wanda bai yi abun kirki ba a duniya tunda yazo,"aiko hakane yar tsohuwa, tashi muje dai yanzun, "ina kuma zaka kaini?....




Gidan horon tsofaffi masu hana jin dadi, tunda kin hana Dady yayi mani walima,"eh an hana din, mutun sai yar banzar son bidi'ar tsiya, sun fita parlo, suka tadda Anni da Aiman, nan Aiman yayi murnar ganin yayan nashi suka fita domin gani fantastics new car din,"Masha Allah, sadiq wannan motar fa?...



"Anni tawace Dady ya sayaman ita yau,"Hajiya kingani fa, "eh nagani tayi kyau Sosae, yaushe za'a dana mu muga gari,"yaya Sadiq kawai ka kai mu park and zoo muyi kalloh, daga nan mu biya ta mansho ka saya mana kaza, yana fada yana dariyar murna yaga yayan nashi da sabuwar mota,"ai Aiman ba park da mansho kawai ba zamu ba, harda soli center zamu da kuma jifatu shop mall duk zamu tafi,"ye! ye!! ye!!!.....




Yaya Sadiq dan Allah yaushe zamu tafi?,"Ku shirya gobe insha Allah zamu tafi,"Yauwa Allah ya kaimu,"amin ya Allah, "amman banda wasu zani tafi, dan ban shirya a bata man mota ba, ya fadi yana kallo Hajiya yana dariya,"aiko mune gaba gaba wajen tafiya, kuma in baka tafi dani ba ai ubanka ya kai ni shi tunda ya zamamai mai dolen shi...



Aah yar tsohuwa mai yayi zafi har haka, zan tafi dake, amman a boat zan saki," mai ye haka kuma? Kai dai ka faya wannan yaren na ya hudawa, kuma zani Rama zagin da kayi man,"to ni ba zaginki nayi ba, cewa nayi a bayan mota zani saki ba ciki ba, a haka zamu yi auren baki i ya turanci ba, sai dai fullanci,"ai na fasa aurenka, don nafi karfin ka, ni Aiman zani aura"Aiman ai zaka aure ni ko?"Aah ni bani auren tsohuwa, nan dai suka kama dariya wai Aiman yace baya auren tsohuwa.......




Washe gari, Sadiq ya tara iyayen nashi suka tafi yawo, sunga gari domin sunyi kallo, ba kamar Sadiq da yayi shekaru rabon shi da gida, sai yaga komai ya chanja mashi, ba kamar yanda ya barshi ba, yaso su biya gidan su Nana, dan har ta unguwar suka bi amman ba damar hakan, kuma shi yana son kafin ya wuce India ko sau daya ne yaje yaga Nana, domin hakuri kawai yake da rashin ganinta, sun koma gida kuma ya kwaso hajiya, shiyasa kowa ya tafi apartment din shi yayi wanka.....



Sannan suka hadu a apartment din Hajiya baki daya harda Dady suka ci abinci suka yi first dare sannan kowa ya nemi gurin baccin shi....



Sai dai shi Sadiq bacci ya kaura cemai a cikn idon shi saboda tunanin Nana, gashi duka duka yau saura sati daya ya wuce India, bai dawowa, sai ya gama baki daya kamar yanda yayi a nijer, shine bacci bai sace shi sai gabanin asuba kuma,ya tashi sallahr asuba yayi raka'atul fijir sannan ya wuce massalaci shida Dady da Aiman dan ma massalacin a cikin gidan su yake.....




Da yake irin gidan nan ne mai massalaci a cikin gida, bayan sun dawo sallah kuma ya karanta al-qur'ani sannan yayi azakar din shi ya samu ya kwanta bacci.....




An yi bikin sallah lafiya, ya yin dasu Nana suka koma hutun makaranta don yanzun sun shiga third term....



kuma Nana ta kara girma sosai domin halittun jikinta sun bai yana sosai dan in ka ganta za kayi tsan manin ta kai shekara 18-19,amman lokacin ta cika shekara 15 ma a duniya, amman Allah ya yi mata halitta....

kuma ita ba kiba sosai sai dai tsawon kafafu, ga hips dinta komai dai Masha Allah...



Karatu suke ba kama hannun yaro domin an fara yi masu *C. A TEST,* kuma ga karatun *C. A..*


Ga kuma wahalar Inna don, watarana har hanata zuwa makaranta baki daya takeyi...


Dan taga abun Inna ba mai karewa bane, in ta hanata tafiya sai ta saci hanya ta tafiyarta makaranta ....



Dan tace karatun shine gatan ta nan gaba....


Malan Adamu ko yanzun sai abunda Inna tayi dashi don harda ita ake ciyar da gidan....


Saboda jarinsa yayi kasa sosai, balle shi irin sana'ar tashi...




yanzun wannan zamanin ba ci take ba, saboda yanzun ana yin fanfo a cikin gidaje....





sannan ga kuma mono nan,duk ya wanci unguwanni akwai su, shiyasa yanzun kasuwar guga tayi kasa...




Ita kuma kaba yanzun mutane da tabbarma suke amfani wasu kuma da carpet suke using dashi a cikin gida....




wannan shine reason din daya sa kasuwar malan tayi kasa saboda babu income sosai.....




Yau ta kama Monday, kuma yau ce ranar tafiyar Sadiq amman, flight dinsu bai ta shi sai karfe 8pm insha Allah kuma a kano state flight din nasu zai tashi...




zuwa kasar india, domin cigaban karatun shi na medicine and surgery....



Yayi promise baya tafiya, har sai yaje yaga Nanarshi yaga ya take zama da matar Abban na shi..



Sannan, ko ya ta koma yanzun,tunda yayi , at least ten years rabon shi daya ga Nana jawaheer a cikin idon shi dan tun tana yar shekara biyar a duniya in bai manta ba....


A haka ya shirya ya dauki hanyar unguwar su Nana wato kofar kwaya.....














Share and comment also
vote on my wattpad account





Account Name:-
meeeeeeelatu



*I really love you my fans😍, ina yin ku over and over, naga na safe nayi dan kadan to ga wanna kurayin manage pls, kunsan abun sai a hankali shiyasa, ga kuma aikin gida da dai sauran hidimomin yau da kullin😍😁*

πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•
*NANA JAWAHEER*
πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•




*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–Š*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.πŸ€™πŸ»```

----------------------------------------







*Story and writing by*

*Jameelah A Belloh*
*(Jameey)*




*DEDICATED TO WALIDARH A BELLOH*



*BISSIILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*




page0⃣8⃣






Tafiya yake yana sauraran wakar umar m Sharif, wakar *LOKACI NE* , yana cewa,"tabbas lokacine, shima yana nan yana jiran lokacin auren shi da Nana, a haka har ya kai gun *SAUKI FISH* ya tsaya ya sayarma su Nana drinks sannan ya cigaba ta tafiya har shi cikin hankali kwance.......

"Inna, ni na tafi Isilamiya, lokaci yana kurewa,"To shikenan sauran kuma ki yi zaman ki daga Isilamiyar, wai dan tsaya Nana, ya naga kamar ba kiyi shara ba?......


"Eh Inna, sai nadawo sannan, kinga yanzun karfe 10am tunda Isilamiyar safe ce da wuri zan dawo shiyasa....

"To dawo kiyi sharar sannan ki fita,"Inna gunwa nike sosai fa,Khadija ke cewa Innarta wai yunwa take ji, tashin ta daga bacci kenan, amman har ta iya neman abinciπŸ˜™, ita ba yin komai ta iya ba kuma yanzun ta kai shekara 10 a duniya.......

"Aah Auta, an tashi kenan?,"ni ba wannan na tambayeki ba....

"Ni abincin nace ki bani, zaki tsaya yin man wata magana ta daban...


Khadija ke fadi haka kai tsaye ko kunyar Allah babu, tana yi ma uwarta magana haka kai tsaye, kamar wata kawarta....



Hmmm ni dai jamila nace, Inna yanzun ki ka fara gani, in dai son zuciya kika sa a gaba,Tom yanxun ki ka fara gani dan haka Inna kin boniπŸ˜‚πŸ˜‚......


"Yi hakuri Auta, yanzun mai kike so nice ne?..
"Kafin nan Inna dan tsaya "Ke Nana wai ma mai kika dafa mana a cikin gidan?_ina magana kinyi shiru kin kyale ni bayan kin san sarai da ke nike magana!!!

"Ubanki nike yi, kin ji ni ko?, kin ji man yar iskar yarinya marar mutunci, yar karama da ke, ke har kin san mai a ke kira da rashin kunya....

"Kan bala'in nan,"ke Nana dan uwarki, diyar tawa ki ke yi ma zagin i bar albarka?, kuma a gaba ba ma bayan ido na ba, ki ke yi mata wannan zagin.....



(oooooo ni jameey yau ina ga nin tsaba ban son xuciya a wajen Inna, wai ita har take fadan taji ciwon zagin da Nana tayi ma Khadija, bayan ita ta mai da zagin Nana breakfast din ta😒, kuma ita kan ta Khadijan ba raga mata tayi ba, yarinya yar karama,amman Inna ta sangantar da ita, Allah yasa mudace Amin)...

"Amman Inna tsakani da Allah, yanzun fa kema ta gama gaya maki magana, haka zamu sama Khadija ido ta raina kowa?...

"Yi man shiru dan ubanki, ke ba'ace kin raina mutane ba sai Auta?,ko dai bakin cikin da kike yi matane ya fito fili?, daman na dade da sani kina yi ma yarana bakin ciki, shegiya mai bakin gadon tsiya, wato yan ubancin ne zaki na nuna masu ko?, to sun fi har abada dai dan ubanki....

"Amman ki san, Allah Nana in baki,"Aah yi mana shiru Inna, barni da ita nice dai dai ita.....

Khadija ce ta dakatar da Inna da fadin haka ta na mai gir giza jiki kamar wata cikakar mace, wanda ta isa ta kai a kirata da suna mace☺....

"To da kike ce man yar iska, to bari kiji in fada maki, dan naga alamun kin manta kina tuya baki sa albasa ba, ke Nana har kin isa ki ceman yar iska?, bayan uwata ke ciyar da ke a cikin gidan nan matsiya kawai da ke, wanda bata da wani gata, uwar taki ma ta manta dake tunda ta tafi daga gidan mu bata sake wai wayo ki ba dan taulanci yayi maku katutu cikin dangi....

Kwatsam maganar da Khadija keyi ma Nana ta sauka a cikin kunnen Sadiq zai shigo gidan kenan, ya jiya wannan mumunnan kalamun da Khadija take yima yayar tata, ita kuma Nana ta tsugune gurin tana ta kuka, wai ko zata ji sausaucin a cikin zuciyarta, domin ita Nana tana da hakuri, amman kuma tanada fushi sosai......


"Ke! Ke!! Ke!!!, tas! tas!! tas!!!, take Sadiq ya wanke ma Khadija zafafa maruka, har guda uku, wanda batason sanda tayi wata muguwar karaba ta fadi kasa, ita dai ba numfashi ba, kuma ba suma ba, tunda idanunta bude suke.....


"Wayyo Allah ke Auta, kar dai ace ka kasheman diya wallahi ko, sai nayi kararka, ka zo har gida ka kasheman diyata, Inna ke fadin haka tana kama ma Sadiq kwala din riga..

duk ta fita cikin hankalinta, har ta ka ma mai rigar gizinarshi daya ya anso ta jiya gun telanshi, domin kawai yasa ta don zuwa India, amman gashi Inna ta batamai rigar....

"Ke talatu, ki sake ni tun kafin kema na juyo kanki, Sadiq yace ma Inna haka cikin ba'cin rai idanuwanshi sunyi ja jawar tsa ba'cin rai da konar zuci, take Inna tayi shekarsa ta shige ta amman sai ta dakai, duk da ta sake shi yanzun amman tana cewa.....

"To wallahi ko bari Malan din ya dawo sai ta bi mana hakinmu cikin gidan,tunda na lura baku san mutunci ba, tana mai ko mawa wajen Khadija da take a jikin Nana tana lailashinta, tana kuka sosai...

"ke munafika, yimana shiru, duk bake bace silar komai ba, munafika mai mugun halin tsiya, tana fadin haka tasa hannu ta buge ma Nana baki, nan take jini ya balle yana zuba sosai, nan ko Nana ta karama kukanta volume.....


"Talatu wai mai yasa baki da arziki eyyeh?, Sadiq ya taimbaye ta, yana kama Nana cikin ba'cin rai yana kallon yanda jininta ke fita daga bakinta, ga kuma kukanta da yake taba mai cikin kohon heartbeat din shi, ji yake Kamar ya fasa ihu ko zai samu sausauci da yake ji....

"To wallahi kika sake gigin bugunta, Allah ni kada nasan abunda zanyi maki, kinji nace Allah, sai dai Abba yayi man duk hukunci da zai yi man, kinci darajar Abba a cikin gidan nan, wallahi da sai nayi maki mugun bugu....

"Ke kuma dalla Allah can ki tashi muje chemist a wanki maki bakin, kina yi ma mutane kukan banza marar anfani kawai, shakara da kai kawai marar wayau...


Haka Sadiq ya dauki Nana zuwa chemist, kuma yana yi mata balbalin bala'i, domin gaskiya ta bashi haushi sosai, ji yake Kamar yai ta zaneta ko yaji dadi...

"Au zaki man shiru ko sai naci ubanki cikin motarnan, sakara dake, kin tsaya mata da yaranta suna yi maki abunda ransu ke so, kuma kin kyalesu..

"Ni Yaya Sadiq, ya ka ke so nayi da Inna?, shin kana so na buga su Inna? ko kanason na zagi Inna? ko kuma nayi mata rashin kunya? Ta ida maganar cikin sigar ban tausayi da kuma lailashi...

"Duk ba haka nike nufi ba Nana, kawai dai ina son ki rage wata wahalar kinji yar kanwata...

"To shikenan nagode,"Aah karki damu, nidai nafi son naga mutun ya zama jarumi ba sauko ba, kinji?"eh naji....

"Yauwa mun iso, sauka muje a gyara maki bakin, naga Kamar a kawai rauni a hannunki ko?, "eh yankewa nayi da albasa, "to duk muje a yi maki dressing din wajen...

Haka suka je, akayi ma Nana dressing din, dan harda allura tatanos

Please Login or Register in order to submit comment