Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baka chanja ba kana ji kana gani zaka rasa Nana jawaheer, kana kallo da idonka za'aba wani ita da sunan mijinta kuma ba yanda zaka yi tunda kai ka jama kanka...


"Hmmm MAN kenan, wa ya gaya maka in Nana tayi aure zanyi kuka? To ko damuwa banyi balle har kuka,kai da kaji zaka iya daukar rainin mata kaje kai ta fama da shi, amman ni Sadiq Musa zan iya jure komai amman banda Wulakanci, balle Wulakanci ma na mata, su fa mata Man da zaran sun ga kana wasa da dariya dasu shikenan sun samu hanyar raina ka, balle ma kace masu kana sonsu, wai abun ma bai faduwa...


"Kai dai ka sani Sadiq, ni wallahi har tausayi kake bani, kana son Nana sosai amman girman kai yana son ya cuceka, sai nan gaba zaka gane gaskiya nike fada maka, "ni dai yanzun ba wannan ba Man tasho muyi wannan tutorials din kasan dai gobe muna da test ko? "Eh hakane mu fara....


____________________________________


*NIGERIA*

"Ke Nana, wai wa kika ajiye yayi maki wannan wankin? "Ke Khadija, ke' na ajiye ki yi man wankin dan uwarki, wai Khadija yaushe na zama sa'ar uwarki ne? Da zaki dunga gaya man magana marar dadin a cikin gida? To wanki bani duk gida ba wanda ya isa ya sake sani wani wanki can na banza....


"Yanzun Nana, ni ki ke zagi ko? "Ai Inna gaskiya ta na fada, wallahi bazan sake yi maku wanki ba a cikin gidan nan, nayi maku na arziki, yanzun kuma na gaji, "ai ko dai ubanki zaki ci dan ubanki, ka ji man yar'iska mai mugun hali irin na uwarta..



"Nagode ma Allah daya bani mugun hali irin na uwata, Inna duk abunki a cikin gidan nan karki kara zagin man uwa, "kam bala'i ke Nana, Inna kike gaya ma haka?



" *ALHMDLILLAH* , Allah nagode maka nima na
haifa, kai Sabi'u daga yau ni Talatu na baka damar ka dunga cin uban wanann matsiyaciyar a cikin gidan, "ai Inna wallahi duk wanda yace zai gaya maki wata maganar banza a gidan nan dole na ci uwar mutun ko waye shi ko..


"Ai ko sai dai muci uwar juna, ku tsaya kuji yanzun komai kuke ji dashi cikin gidan nan daga ku har uwar taku, wallahi dai-dai nike da ku baki dayan ku, tunda nima dai naga gidan ubana ne, dan haka dole nayi abunda nike muradi ba..



"Aiko zamu ci ubun juna Nana, Khadija ke fadi haka, "wai Sabi'u mai muke jira da wannan banzar da har yanzun bamu fara cin ubanta ba,kazo muci ubanta sai dai komai za'ayi, ayi shi a yau din nan..



Nan fa, fada ya kaure tsakanin Nana da su Inna, sun mata taron dangi sunata bugu, dan itama tana ramawa, amman kunsan a ce sarkin yawa ya fi sarkin karfi, balle kuma Sabi'u shi namiji ne yafi Nana jawaheer garfi nisa ba kusa ba, amman duk da haka Nana sai da tarama, suna cikin fada Malan ya dawo gida ya tadda wannan bakin ganin a cikin gidan shi..


"Subuhanalillah, mai zan gani haka ni Adamu, ke Talatu, kashe man ita zaku yi ko? "Ai na fi son na kashe ta sai ayi duk abunda za'ayi a cikin gidan nan..



Tas! Tas!! Malan ya wanke Talatu da lafiyen yun mari yana cewa"To bari a yi abunda za'ayi tun kafin ki kashe ta, ku kuma yau wallahi duk sai naci ubanku, har da ku ake buhun yayarku ko? "Adamu ni ka mara saboda da Nana? "Eh an mareki kiyi abunda zaki yi, kuma wallahi yanzun na fara marinki a cikin gidan nan in dai a kan Mamana ce..


"Ai ko ka maranma kanka bala'i, kuma ai ba gidan kake yini ba zaka barni da ita cikin gidan nan, sai dai kullun ko kai ta marina, ni da ku shege ka fasa, "haka ki kace ko Talatu? "Eh haka nace ko baka ji ba na sake maimaitawa?



"Shinekenan jeki ni dake ne kuma cikin gidan nan, ke kuma Mamana daga yau komai tayi maki ki rama bance ki kyaleta ba, daga ita har yaranta, kina jina? "Eh Baba naji insha Allah, "yauwa tashi ki shiga daki ki huta, ku kuma da yake baku da hankali shine kuka baye ma uwarku kuna bugun yayarku ko? "Aah Baba dan Allah kayi hakuri,ba zamu sake ba Insha Allah, Khadija ke fadin haka tana kuka, dan taji tsoron Baban nata..



Nan fa Malan yai ta yi masu fada, ya kuma ja masu kunne a kan karda su yarda ya sake kamasu da kallar wannan laifin, inko ya sake kama su shi kadai ya san abunda zai yi masu...

________________________________


"Noor ya na ganka cikin farin ciki, ko dai yau anyi dace? "Tabbas Fulani yau Jawaheer ta kulani ta saurareni, "Ta amince da bukatar ka ko? "Tace zatayi tunani, shiyasa zan bata kwna biyu sai na sake koma wa naji wani matsayi ta ajiye ni a cikin zuciyarta...




"To Noor Allah yasa muji alkhari, "Amin Fulani, wai Fulani sai yaushe Baffah zai dawo, na kira layin shi dazun no reachable? "Eh Insha Allah sai jibi zai dawo, "gaskiya nayi missing din shi sosai Fulani..


"Yanzun ga abinci can yana jiranmu a dinning table, tashi muje muci abinci, sai kaje kayi wanka ka huta domin nasan ka kaso gajiya, "aiko Fulani na kaso gajiya sosai da sosai, Woow Fulani delicious, gaskiya ina son abincin ki Fulani, Allah yasa Jawaheer itama ta yi kallar wannan delicious food din Fulani, "Amin, yanzun kai dai kaci abinci, ka tsaya kana ta yin santi, "To Fulani...

________________________________


Sulaiman "Naam Hajiya, "ya kuka yi da shi Adamun? "Eh Hajiya yace na bashi lokaci tukun nan,"To shikenan Allah yasa mudace, "Amin Hajiya, to ni Hajiya zani shiga ciki nayi wanka,"To shikenan a fito lafiya, "Allah yasa Hajiya..


"Dadyn Aiman, ya ku kayi da Yaya? "Eh. Cewa yayi zaiyi tunani na wani dan lokaci sannan zai yi man magana komai kenan, "To Allah yasa muji alkhari, "Amin ya Allah, "Yanzun ka tashi kaci abinci sannan kayi wanka, "To momyn Aiman, kamar kin san ko na kaso yunwa da kuma gajiya sosai..





*Allah yasa munyi azumin nan cikin sa'a da rabo, Allah yasa mu cika da imani da kyaukyawan karshe..*




```Yanzun tunda nagama azumi lafiya, zaku ringa samun posting sau daya watarana kuma sau biyu, amman ba ko wace rana za ku ringa samun biyu ba, Allah yasa mudace duniya da lahira amin..
```


_By jameelah jameey πŸ–‹_




Share and comment pls


πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•
*NANA JAWAHEER*
πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•

*STORY AND* *WRITING BY*
*Jameelah A Belloh*
*(Jameey)*


*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–Š*
*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.πŸ€™πŸ»```

_________________________________


*BISSIILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*




```Gaskiya yau my Fans kun sani farinciki sosai dan naga ruwan comments dinku sosai shiyasa Nima nace dai yakamata a maidama kura aniyarta😜, shiyasa nima yau zanyi maku posting sau biyu..```


*Wannan page din nakune masoyan NANA JAWAHEER,gashi nan kuyi yanda kuke so dash, much love my fans🌹🀎*


Page 1⃣5⃣







Bayan Alhaji Sulaiman ya gama cin abinci, sun Kara tautauna wa da matar shi akan a dawowar Nana Jawaheer gidan shi da zama, nan ya shiga bedroom yayi wanka ya dan kwanta huta, bayan ya huta yake kiran Sadiq waya yana gaya mashi yanda suka yi da Yayan nashi...


"Sadiq kaji dai yanda mukayi da Abbanku, ammn ni naga kamar wannan karan zamuyi nasara a cikin lamarin..


"To Dady nima ina tunanin haka gaskiya, Allah yasa mudace dai, "Amin ya Allah, yauwa Yaushe kake fara exams ne?"next week insha Allah Dady, a cigaba da yi mamu addu'a dai Dady, "insha Allah, da'man kullun muna yi maku addu'a bakin dayan ku ma Son, "To Dady mun gode, yanzun dai ina karatu, "To shikenan, Allah ya baku sa'a, "Amin..


A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah, yanzun Nana ta shiga a biyar a secondary school, har sun gama first term ma, a cikin wannan kwanakin abubuwa sun faru masu dadi da mararsa dadi ma, saboda da Nana da Talatu zama ba dadi sai dai a ce abun sai addu'a, tunda ita Nana idan Talatu suka yi Mata sai ta rama take cewa..


Ya yin da Nana ta Amince da soyayyar DR KHALID,soyayya suke mai kyau da burgewa, da taimakon Zee wanann soyayya ta kunlu, yanzun abun ya kai da Nana bata iya bacci in ba ta ji muryar sahi'binta ba, Malan yayi ko'kari ya saya ma Nana wayar tecno da ita Nana ke wayarta da rabin rain'ta wanda yanzun take ji idan bashi ba sai dai rijiya... (Lol😜)
_________________________________


*NEW DELHI INDIA*

Sadiq yanzun sauran shekara daya ya gama MSC din shi, yanzun sun gama yin lecture, sai dai project da yasa a gaba yanzun, bai da wani guri da ya wuce ya ganshi kasarshi Nigeria, Lukman kuma da Salma soyayya suke yi cikin natsuwa da fahimtar juna, sun fahimci junansu, sun san abunda wannan ke so da wanda ba ya so, suna yi ma juna son gaskiya da Amana, ba mai son ya ga bacin rain dan uwanshi, yanzun itama Salma tana final year tana karanta BSC NURSING, Alhmdulillah Salma itama tana da mai da hankali a kan abunda ya kawota, bata da wasa ba ko shirme a cikin karatun ta....

________________________________


*NIGERIA*

Wooow masha Allah, wata kyaukyawan budurwa na hango ita da wani saurayi, shima kyaukyawan karshe ne a wajen kyau da fari, ita dai yarinyar black beauter ce idan tana magana sai kayi tunani kamar ana tilasta ma yin maganar saboda da ajinta da natsuwarta, tana da idanuwa masha Allah dan idanuwanta sexy eyes ne, ga bakinta dai-dai masha Allah, hancinta dogo da shi idan tana magana har dimple queen dinta ke lotsawa duka size dinta biyun, bata da hayaniya ko kadan dan ita bata cika son yawan magana ba sosai, Allah yayi halinta a jikin Nana Jawaheer , ga booos dinta sun fito masha Allah, ga shape da hips nan sun fito suma, yanzun Nana an zama cikarkiyar budurwa tunda yanzun tana shirin zana exams din NECO da WEACE na aji shida, yanzun takai shekara 18 a duniya, Saurayin da Nana take tsaye dashi ba kowa bane face Khalid dinta, Wanda suke ma juna wani kallar so, wanda suke gani mai rabasu sai ya shirya dan sunma juna alkwarin aure..


Wata budurwa ce fara na hango masha Allah, ta taho tana yi ma Nana magana..


"Haba Nana wai miyasa yanzun kike son muringa yin late a sch?, "a fuwan Zee yanzun nike shirin fitowa wallahi, "yanzun dai tashi mu tafi kinsan yau muke final Exams kings bah kamata muyi late a scholl ba, kinga mungama Secondary sauran university tunda Allah yasa mun samu jamb din mu, "aiko dai, wai waya ga Nana a university, hahahahaha, Zee za'asha kallo dai..


Nan dai suka isa school suka zauna exams hall suka zani final exam din su nan suka fito anyi hotona suda kawayensu na ban kwana sannan kowa ya wuce gida....


__________________________________

*NEW DELHI INDIA*


Yau Sadiq da Lukman da Salma suke kan'mala karatunsu, suna ta murna ba kamar Sadiq da yake ji kamar an cire mashi kalba a kashin bayan'shi, gobe zai ga Aiman din shi da su Hajiya, shi kuma Lukman da Salma suna murna zasu ga yan gida, amman basu jin dadi saboda zasu yi nisa da juna na wani dan lokaci, tunda ita Salma a kano state take da zama shi kuma Lukman a katsina state yake da zama, washe gari, su Sadiq sunyi parking sun shirya sosai domin yau flaying din zai tashi zuwa kasa Nigeria, karfe 10 na safe jirgin su Sadiq ya tashi zuwa kasarsu ta haihuwa Nigeria..

________________________________


*NIGERIA*

Yau gidan su Momy sun tashi da aiki tun safe dan tarbar Sadiq da ya gama karatun shi na MSC suna ta shirya zuwan nashi dan Momy da Ammi duk yau basu zauna ba suna kitchen suna ta sauwar da zasu tarbi dan lailan nasu sunyi sunasir da miyar naman kai shi kuma suka yi *BANANA* *PENDDING JUICE*

yanda ake yin juice din..
_Banana pudding_


_Abubuwan hadawa_

```Ayaba5,Kwai 2,Lemun tsami 1,Suga,Filebo (flavour)```

_Yadda ake hadawa_
```Uwargida da farko za ki bare bawon ayabarki ki tsaga tsakiyan, ki cire bakin tsakiyan, sai ki yanka ki sa a blender.
Sai ki fasa kwanki ki matse ruwan lemun tsaminki, sai ki kada sosai ya kadu, sai ki zuba shi a kan ayabarki.
Ki zuba suga ki yi blending sai ki juyeshi ki sa flavor, ki juyashi sosai, sai ki sa a cikin oven ki sa wuta kadan dan, ya yi kamar minti biyu sai ki cire.Shike nan banana pudding na ki ya kammala.

```

Bayan sun gama hada komai su Momy suka shiga wanka domin su shirya kafin Dady ya dawo daga dauko shi..



Bangaren Lukman ma haka ta kasance Mamin ta shirya ma d'an nata tarba ta musanman dan itama ba'a barota a baya ba dan white rice tayi mashi da kayan lambu da kuma miyar soup. Yanda ake yinta.


_White rice da kayan_ _lambu_

_Abubuwan hadawa_

```shinkaf,carrot,green beans (pies``` )

_Yanda ake hadawa__

```Da farko zaki samu tukunyarki mai tsata, ki daura a saman gas, sai kisa ruwanka wada tace, indan ya tafasa sai ki wanke shinkafarki sosai ta wanku, ki zuba a cikin takuya, kafin ta dahu ki samu carrot dinki ki yanka shi kanana sai ki wanke shi sosai, ana sauran bai fi 30min ki sauke shinkafar ba, sai ki zuba carrot din da green beans dinki, sai ki juya su yanda zasu hade da junansu sosai, in sun yi kamar 20min sai ki yi per boiling din shinkafan, Kinyi per boiling water din da kamar 5min sai sauke ki sa a cikin cooler...
```

_Soup_
```tittasai(pepper),tarigu,albasa,curry,thyme, seasoning, kayan dan'dano, Mai,jan Nama, garlic (tafarnuwa)```

```Da farko dai uwar gida zaki wanke namanki ki sa a tukunyarki, sai ki daura tukunyar a kan gas, ki dan sa kayan dan dano kadan da albasa da garlic da yar citta kadan(kun san dai citta tana fidda karnin nama), sai kisa dan ki shirinki shima kadan....```

```uwargida, zaki samu pepper dinki ki gyara shi sosai, shima tarigun ki gyara shi sosai, albasa ma ki gyara ta, ki hadasu ki wanke su sosai, sai ki yanka su kananu ki zuba a cikin blender dinki ki blending su sosai, ki samu container din ki ki zuba shi markaden kayan miyar..
```
```Sai ki dauko tukunyarki ki daura a gas dinki, ki sa mai dinki ya dan soyu kisa yar albasa kadan gun soya man, sannan kin dauko kayan miyar da kika blending ki sa a cikin tukunyar, in kayan miyar sun fara soyuwa, sai ki dauko dan'danonki ki zuba, ki gyara garlic din ki kasa a ciki, sannan ki yanka albasarki itama ki zuba, ki dauko tafashen namanki shima ki zuba, da roman tafashen da ki ida miyarki, inta dahu sai a sauke..

```

Sannan kuma tayi mashi Lemun cucumber da danyar citta yanda ake yin shi.


_Lemun cucumber da_ _danyar chitta_


_Abubuwan hadawa_


Kukumba (3)Citta (4)SugaLemun tsami (5)



Yanda ake hadawa


Da farko zaki sami kukumbarki ki wanke ki yanka kisa a blender.
Sai ki wanke cittarki ki goga da abin goga kubewa ko ki yanka kisa a blender ki hada da kukumba ki markada.
Sannan sai ki tace ki sa suga da lemun tsami.
Daga karshe, sai ki sa a firinji ko kisa kankara.

Sanann taje tayi wanka tana jiran dawowar tashi..

Bangaren Salma ma haka ta kasance Ummun ta tayi Maylta tarba ta musanman, tayi mata mai-mai (alala), ita Salma tana son mai mai sosai, sannan tayi mata Lemun kwakwa da madara yanda ake yin shi.


_lemon kwakwa da_ _madara_ .


_Abubuwan hadawa_


kwakwa 2, 3Madara 2SugaFilebo (flavor coconut)

_Yadda ake hadawa_

Da farko uwargida za ki fasa kwakwarki ki kankare bayanta ki wanke sai ki yanka.
Ki sa a blender ki markada sai ki tace ki sa madara da suga da filebo.

Sai ki juya sosai sai ki saka kankara ko ki sa a firinji ya yi sanyi.Shikenan sai sha idan ya yi sanyi.


Bayan ta gama tayi wanka ta shirya tana jiran dawowar autar ta ta

________________________________


*KANO STATE*

Aminu kano international airport, woooow wani handsome guy ne na hango yana taka benan jirgi yana saukowa fuskarshi kun she take da farin ciki, duk da black glass din dake man ne a fuskarshi a hakan ba zai hana ka gane yana cikin farin cikin dawowa kasarshi da haihuwa ba, hmm Sadiq kenan..


masha Allah wani guy ne ya biyo bayan shi yana dariya yana cewa welcome home, hmm Lukman kenan matashin saurayi mai ji da class da kudi...


Allah mai halita anan wata cute baby ce na hango ta saukowa daga cikin jirgi, fuskata sanye da glass rado, tasa wata arniyar atamfa wanda dinki yayi mata kyau ya kare fiddo Mata kyaun'ta da kuma farinta), tana godema Allah daya sa ta gama degree dinta lafiya ta dawo gida lafiya, Salma kenan...


Nan fa wannan matasa masu jini a jiki sukayi bankwana da juna, Sadiq ya cema Lukman sai sun hadu dan anzo daukarshi nan yabar Lukman da Salma suna Kara yin bankwana, akan Lukman zai shigo ba da dadewa ba...




"Oyoyo Dad, "Sadiq welcome home, "thank you Dad, nan bayan sun gama gaisawa suka dauki hanyar katsina state, a kan hanyar ne, Malan Adam yake kiran kanin nashi yake ce'mai yazo ya dauki Nana Jawaheer yau din nan ta koma gidan shi zama, dan ya gaji da wannan rashin hakanlin da suke yi mai cikin gida ita da Talatu, nan fa Dad yake gaya ma Sadiq, suna isa katsina sai da suka biya ta gidan su Nana jawaheer suka tafi da ita bayan taje ka gaya ma Zee sun rabu ba dan sun so ba, dan ma zasu ringa yin waya, ga kuma sun samu adimissinon tare a Umaru Musa yar'adua katsina, an'ba Nana Jawaheer BSC BIOLOGY, ita kuma Zee an bata BSC(ED) BIOLOGY..


Sun isa gidan Dadyn lafiya anata murna da dawowar su baki daya, bayan sunci sun sha, sannan Hajiya tace Nana a wajenta ta zauna..













_By jameelah jameey_ πŸ–‹







Share and comment pls



πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•
*NANA JAWAHEER*
πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•

*STORY AND* *WRITING BY*
*Jameelah A Belloh*
*(Jameey)*


*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–Š*
*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.πŸ€™πŸ»```

__________________________________



*BISSIILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*





Page 1⃣6⃣










Bayan Nana ta huta, Hajiya ke yi mata magana , "yauwa takwarata, barka da zuwa wannan gida mai albarka, gidan da kowa ke sonki yake tausayinki, nasan kina da tambaya da yawa a bakin ki, kiyi man duk tambayar da ta fito daga bakin ki ni kuma insha Allah ina da ansa duk wata tambayarki...


"To shikenan Hajiya, insha Allah yanzun zan fara yi maki tambaya kuwa...


"Hajiya dan Allah wai miyasa Baba ya saki Ummana? "Gaskiya takwara nima bansan abunda Aminatu tayi ma Adamu ba, wannan ansa tana wajen Adamu...


"Hajiya mai yasa tuni baku zo kuka daukeni ba a wajen Inna sai yanzun da na mallaki hankali na na san ciwon jikina?"


"Wannan kuma Nana laifin Baban'kine, ba yanda bamu yi ba ya bamu ke mu rike, Amman ya hana mu shi a dole Talatu zata rike ki.


"Amman yanzun gaki kin dawo inda zaki ga gata da soyayya, ni dai fatana Nana shine ki tsare mutuncin ki da darajarki, kinji takwara ta!? "Eh naji Hajiya insha Allah...


"Yauwa Hajiya, daman inasan na yi maki wata tambayar kuma!!


"To Nana, fadi tambayarki Allah yasa ina da ansarta ita ma, "Hajiya da man ina san kiyi man wata alfarma, "wata alfarma ce wannan? Nana fadi man, "eh daman ina san ki tambayarman Dady ya barni ina tsaya wa da wani wanda nike so na aura...


"Au wai da itace alfarman ma?ai mu wannan abun farin cikin ne a wajen mu, to ki bari anjima in munje cin abinci zan yi mashi bayani kinji albarka, "To shikenan nagode Hajiya ta..

_________________________________


Khadija! Khadija!! Khadija!!!, wai dan ubanki ba magana nike yi maki ba kinyi banza kin kyaleni? "


"Haba Inna wai mai'ye haka zaki matsaman da kira tunda uwar safiya sai kace wanda tayi maki sata? Ni wallahi Inna kin fara matsaman a cikin gidan nan..


"Yanzun Khadija ni kike cewa na fara matsa maki? Khadija yanzun inba ki fito kika kama man aiki ba wa'zai tayani tunda ita Nana yar'So dangin uba sun ansheta, "To nidai maganar gaskiya Inna bani iya aikin da Nana ke yi maki a gidan nan, domin ni dai ba jakka bace ai shine, dan haka tun wuri kin san yanda zaki yi da aikin gidan ki...


"Khadija,nice fa kike gaya ma haka, "eh din kefa ce , ai nasan kece Inna, kuma dole na fadi maki gaskiya dan kisani tun wuri ba sai nan gaba ba..


Allah sarki duniya, da man haka duniya take, yanzun dai Inna Talatu, Khadija na'san tafi karfin ta, bayan komai Khadija tayi ma Inna ita ta sangar'tar da ita da kan ta, Allah yasa mudace duniya da lahira...

________________________________


"Fulani, yanzun Jawaheer ta dawo nan unguwarmu fa da zama, "Kai masha Allah Noor kace yanzun ka huta da zuwa kofar kwaya kullun?


"Aiko dai Fulani, ta dawo gidan kanin Babanta, insha Allah yanzun ina zuwa dauko Baffah, ina dawo wa zan biya gidan mu gaisa kafin na fara zuwa sosai, amman yanzun maganar registration dinta zamu yi yaushe za'a fara yin registration din..


"To shikenan Noor, Allah ya yi maku albarka baki dayanku, "Amin Fulani, ni zan wuce naje na dauko Baffah, "To shikenan a dawo lafiya Noor, kabi hanya a hankali bani san wannan gangancin naku na samarin Zamani kuna driving kamar baku san rayuwarku inkuna karfen nasara wuta bayan kunsan ba tabbas ne dashi ba, dan haka kabi man Miji a sannu dan ban shirya takaba ta dan yanzun, "Hahahhahha! Fulani shikenan nidai na wuce, ai nima ban shirya zama maraya ba dan yanzun...


________________________________


"Tashi muje muci abinci, lokaci yayi, idan mun'dawo kin kwanta, "To Hajiya, Ammi mu tafi ko, "ina zaki Nana? "Hajiya tace na tashi muje muci abinci, "ai nan ake cin abincin ga dinner area can, suma yanzun su Sadiq zasu shigo, wuce mu tafi, "To Ammi..


Tuwon semo miyar danyar kubewa su kayi nan kowa ya zauna, Nana tana kusa da Sadiq, a role din gidan in ana cin abinci ba'a magana sai angama sannan suke tashi su zauna parlon Hajiya sannan suke yin firar dare, bayan sun gama cin abinci Hajiya ta fara magana..


"Sulaiman, "Naam Hajiya, "daman ina san nayi magana da kai, a kan yarinyar nan Nana, "to Hajiya, nima da man ina san mu zauna muyi magana, amman ban samu lokaci ba, sai yanzun..


"To yanzun dai ita Nana Allah ya yarda ta gama wanann makaranta ko? "Eh Hajiya Alhmdulh ta gama secondary school, yanzun saura jami'a, "minene wanan haka kuma wai jami'a Sulaiman? anya kuwa Sulaiman yanzun saboda Allah ace kamar Nana har yanzun ba'ayi mata aure ba?


"Ai Hajiya za'ayi mata aure insha Allah, duka duka yanzun

Please Login or Register in order to submit comment